Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banji fashi da makami ba, banji kisan kai ba kuma banji labarin yarinyar ta Amira ta fada ba, asali ma duk hotu an nasa babu inda na ganshi da mace, duk tare da maza ne masu shiga irin tasa. Wani hotonsa ne ya dauki hankali na nayi zooming, Sultan ne fuskarsa dauke da murmushi, rike a hannunsa kwalbar giya ce a daga ta alamar cheers. Na runtse idona ina jin zafi a kirjina. So it's true, yana shan giya. Hawaye naji yana kokarin zubo min na yi sauri na mayar dashi. Nayi typing emir of Abuja, nan ma hotuna na gani ba adadi na mai martaba sarki kuma kusan duk hoton yana tare da second son dinsa Abbas, cikin kima da daraja da kwarjini irin na sarauta, mostly a gurin saukar karatu ko bude masallaci ko musabakar alqurani. Nayi zooming wani hoton mai martaba, kana ganinsa kasan shi ya haifi sultan, idonsu, girarsu da shape din fuskarsu iri daya. Na koma nayi searching prince Abbas, nayi ta bincike amma na kasa ganin single fault nasa, he is like a perfect son, komai tare suke yi da mai martaba, duk inda mai martaba zaije tare suke zuwa. Can naga wank hotonsu shida sultan a america gurin graduation din sultan na masters. Nayi shiru ina tunani, mutane criminals irin sultan basa karatu, most of them da wahala suke gama sec sch, amma sultan masters ne dashi kuma a babban field like architecture. What is happening? What am I missing? What are u sultan? A gurin manyan mutane da masu kudi shi criminal ne, a gurin talakawa da sauran marasa karfi shi hero ne. Wanne dalili ne zai saka mutumin kirki ya mayar da kansa mutumin banza a idon mutane. Har zan rufe laptop din sai na fasa nayi typing the gang bang. Ai kuwa naga rubutu sosai a kansu, Amira tayi gaskiya dan daga 'ya'yan tsofaffin shugabannin kasa sai 'ya'yan gwamnoni da manyan masu kudi, a cikin list din naga an rubuta "the drunk prince of abuja" duk da basu fada ba nasan sultan suke nufi. Na rufe laptop din na kwanta ina tunani. Why will Sultan want people to think he is a bad guy while in reality he is good, very good. Yau kusan 3 hours nayi a motar sa daga ni sai shi amma ko da wasa bai kai hannunsa jikina ba kuma baiyi min wata magana da zata nuna cewa dan iska bane. Dear God, what do I do now. Inanan a kwance Amira tazo ta kawo mana abinci har yanzu fushi take yi dani ita wai lallai naki jin maganar ta. Da kyar na samu na bata hakuri nace tayi min addu'a insha Allah komai zai warware. Muna nan muna ta hira har magrib sai Sultan ya kira ni yace min gashi nan zuwa, tun daga nan Amira ta cigaba da bata fuska, naje zanyi sallama da mama tace min "Maimunatu wai me yake damun kawarki ne?" Nace "mama me ya faru? " tace "sam taki kula samari ballantana har ayi maganar fitar da miji, ta gama degree dinta, tayi service, me kuma yayi saura? Ni na gaji da surutun da iyayenta suke yi min wallahi, ni babu miji ita babu miji amma ita sam bata damu ba, shi wanda naga tana nacewa da ya fara zuwa kamar gaske kuma yanzu shiru, ni ko waya ma yanzu banji suna ji ba, idan ba aurenta zai yi ba sai ta rabu dashi ta samu wani" na kalli Amira da alamarr tambaya saboda ban gane maganar da mama take yi ba, Amira ta daga kafada irin oho din nan, nan dai na bawa mama hakuri nace zamuyi maganar da Amira. Muna fita na tambayeta "wanene mama take magana akansa" ta dauke kai tace "nima bansani bafa, ita dai kawai ta damu sai nayi aure ne kuma ai shi aure lokaci ne, idan mijin baizo ba ni zan auri kaina ne?" Jikina ya bani da akwai abinda Amira take boyewa amma sai na rabu da ita, na san in tana son in sani zata gayamin ne da kanta.

Muna zuwa wajen motar Sultan Amira ta rike hannuna tayi masa knocking, ya sauke glass yasha wani bakin glasses a fuskarsa, Amira ta hade rai sosai tace "gata nan na kawo ta, kuma ka sani wallahi duk abinda ya same ta hukuma ba zata bar ka ba" Sultan ya dan sauke glasses din idonsa kadan yana kallonta ta saman glasses din, sai kuma yayi dariya yace "Thank you Mah, zan bi duk kanin umarnin ki" ina jin Amira tana ta kunkuni tana cewa "banza mai kyan dan miciji kawai" ni dai ina ta kunshe dariya ta naje na shiga muka tafi. Kamar yadda ya kawoni a 20 komawar ma a 20 muke tafiya. Ya chanza wanka yasaka riga mai dogon hannu amma kuma sai ya nannade hannun rigar zuwa gwiwar hannu. Wani irin cikar halitta da kyau ne yake bayyana a jikinsa. Kawai sai ji nayi yace "are you checking me out?" Naji wata kunya ta kama ni saboda bansan yana kallona ba. Yayi dariya yace "Thank you for appreciating me" nayi sauri nace "I didn't" yace "OK ni bara inyi appreciating dinki. Kinga kina da kyau sosai da sosai, kina da komai da yakamata ace mace tana dashi. Sannan kina da nutsuwa sosai da kamun kai. Ga ilimi, you are a potential doctor at a very young age, and that's wow. Zan iya cewa babu abinda kika nema kika rasa. Ina so ko yaya ne kiyi sharing abinda kike dashi with me" ya danyi shiru ni kuma bance komai ba, sai ya cigaba "nasan ni ba kowa bane ba, I am nobody and I have nothing, na san kinfi karfina nesa ba kusa ba kuma nasan abinda nake so in fada kamar selfish ne, amma kuma tun ranar da na fara ganin ki na kasa samun sukuni na zuciya na kasa controlling kaina. I want to spend the rest of my life with you" na lumshe idona na kwantar da kaina akan headrest din kujerar inajin sonsa yana kara huda kirjina. A lokacin Ibrahim cewa nayi idan mommy ta sani zata saka ni a turmi ta daka ni ta mayar dani gari, wannan karon kuwa inajin in ta sani sala sala zatayi da nama na tayi kilishi ta cinye, lol.



Episode Forty One : Born for This.

Jin bance komai ba yasa Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "am sorry, maybe it sounded like an insult to you. Allah ya baki hakuri. Kawai dai na fada ne saboda ni bana iya rike abu a raina. I don't deserve you, I know. Kawai dai na dauka for once maybe zan zama lucky" na kalleshi ina girgiza kaina nace "am not saying no Sultan, am just not saying yes. Duk wannan abin yayi sauri da yawa, babu dade da haduwa ba. I don't know you and you don't know me" ya cire glasses din idonsa ya dora akan dash board yace "look ba fa cewa nayi zan turo iyayena ba ko something like that ba, am just asking for your permission to love you" nace "na sani, amma still, indai har soyayya ce dole a kafa ta akan yarda da juna da aminci. Kafin in ce ina sonka ko bana sonka dole sai na sanka first. Sultan I don't even know your real name, babu abinda na sani a tare da kai" guri ya samu a gefen titi yayi packing ya juyo yana kallona sosai, yace "saboda rannan kin tambayeni about my mother shi yasa kike cewa haka ko?" Nace "well, yes, na gaya maka almost everything a kaina amma kai ka kasa gaya min komai, ta yaya kake so in fara relationship da kai ba tare da nasan komai a kanka ba?" Yace "I didn't tell you anything about my mother because I don't know" ya buga hannunsa akan steering alamar ransa ya fara baci. Nayi shiru bance komai ba ina gudun kara bata masa rai. Mun jima a zaune sai ya fara magana "Sunana na gaskiya Abbakar Sadiq Abdallah, for some unknown reason babana ya saka min sunansa, a game da mahaifiyata kuma bansan komai akanta ba, it is as if she didn't exist,babu wanda yake maganar ta, abinda na sani kadai shine sunanta, shima kuma a jikin birth certificate dina na gani. Tun tasowa ta a gidan kakana na taso, kakana wanda ya haifi mahaifina lokacin shine sarki ba Takawa ba. Duk duniya zan iya cewa daga shi sai Amir zan iya nunawa ince wadannan suna sona dan soyayyar da ya nuna min sanda yana da rai ko 'ya'yansa baya nuna wa haka. Tun ina yaro nasan Takawa shine babana amma kuma tun a lokacin nasan baya sona, dan ina tuna lokacin da in yazo gidan zan kama rigarsa in rike ina kuka shi kuma yana ture ni har sai na fadi sannan yayi tafiyarsa. Kakana lokacin shi zai daukeni yayi ta rarrashina. Gata kam a lokacin na gani, duk abinda nake so shi za'a yi min, babu wanda ya isa yayi min tsawa ko fada koda kuwa Yaya ce (yaya itace kakata wacce ta haifi babana), dan haka na taso a sangarce, babu mai sani babu mai hana ni, wani lokacin sai in zauna inyi ta kuka ince ni gurin mommy na da daddy na zanje ko wanne yaro yana gurin iyayensa banda ni, a irin wadannan lokutan ne marigayi sarki ya dauke ni ya kaini orphanage ya nuna min yaran gurin yace 'kaga wadannan yaran su basu san uwarsu ba basu san ubansu ba, basu san kowa a dangin su ba, kai kuma kasan babanka, kasanni ni kakanka, kasan dukkan danginka na gurin babanka to kamata yayi ka godewa Allah', a orphanage din na hadu da Amir" na kalleshi da sauri ya gyada min kai "yes, Amir is an orphan. Babarsa tana haihuwarsa ta dauke shi daga shi har mahaifarsa ko cibiya bata yanke masa ba ta ajiye shi a kofar orphanage ta gudu. Kakana shi ya rada masa sunansa Abdallah shine ake ce masa Amir. Sanda yake kaini orphanage ya hada ni da shi, tun a lokacin muke abota da yake shima fitinanne ne iri na, daga baya in zamu taho sai yayi ta kuka yace sai ya bi mu, sai kawai kakana yayi adopting dinsa ya saka mu a makaranta tare, komai tare muke yi dashi har yau. Lokacin da kakana ya rasu ne rayuwata ta chanza gaba daya, I was ten years old then, nayi ta kuka akayi ta rarrashi na naki hakura, Takawa yana zuwa ya kama ni ya daure min hannu da baki na ya saka ni a dakina ya rufe kofar. Haka na kwana ina kukan zuci babu bakin yin kukan ga uban dauri da nasha, sai washe sannan ya aiko aka kunce ni kuma yace in na sake kuka sai ya kuma daureni. Daga ranar nasan na rasa soyayya a rayuwata. Hankali na bai kuma tashi ba sai da aka nada babana sarki, ya dauko iyalansa wadanda ko saninsu banyi ba tunda baya bari inje gidansa ya dawo palace. Ni na riga na saba duk abinda nake so shi zanyi, tun da ya dawo gidan kuwa sai ya zamana duk abinda nayi no matter how small ba zai yi min fada ko nasihaba sai dai ya saka dogaran sa suyi ta dukana, wani lokacin har Amir za'a hada a daka koda kuwa ni kadai nayi laifin. Daga lokacin muka fara koyon fada ni da Amir, in an saka a dake mu sai ya zamana suna dukan mu muna ramawa. Bayan na karasa primary school, Rannan na tambayi Yaya nace dan Allah ta saka a kaini gurin babata sai tace min itama bata san inda take ba, na tambayeta ko ta san dalilin da yasa iyayena duka rabu? Sai tace min saboda ayi protecting family name. Lokacin ina yarinta ban fahimci maganar ta sosai ba. Lokacin Takawa ya sai wata sabuwar mota kawai sai na dauki fenti na shiga garage dinsa na rubuta 'fuck the family name, I want my mother', nasan abinda na aikata dan haka naje na shirya, na saka duwatsun wuta a cikin safa ta na hada da hannuna wanda na daure da karamin towel na daure, neman kawai wanda zan huce temper ta akansa nake yi, ai kuwa sai dashi an turo wani dogari mai tsautsayi akan ya zo ya dake ni, da na dage na fara naushinsa da hannuna mai duwatsun nan har sai da naga baya motsi, haka aka kwashe shi sai asibiti. Washe gari takawa ya kirawo ni yace "tunda ni ka gagare ni zan tura ka inda za'a koya maka hankali" shikenan abinda yace min, babu Sultan me yasa kayi haka? Babu Sultan ya kamata ka dena haka. Kawai ya saka mu a jirgi ni da Amir sai lagos, gidan kangararru. Wasu iyayen suna ganin gidan kangararru a matsayin gidan da zai gyara musu 'ya'yansu basu san cewa kara kangarar da yara yake yi ba. Sanda ya kaimu na tambayeshi 'why?' Amsar da ya bani shine 'to protect the family name'. Babu abinda ban koya a gidan nan ba, babu abinda ban iya ba, acan na hadu da most of the gang bangs, iyayensu sun kasa basu tarbiyya sun turo su nan. Shekarar mu biyu acan uncle dina galadima yaje a fito damu, yana kawomu gida Takawa kallo daya yayi mana yace ba'a gidan sa ba, a lokacin ne Hajiya ta kira ni dakinta ta ce min zata saka a kaini America a saka ni a makaranta amma sai na mata alkawarin bazan dawo Nigeria ba zanyi zama na acan. Ni a lokacin gani nake yi me zai dawo dani Nigeria tunda babu wani abu da na bari anan, nobody wants me, not even my mother. Sai a lokacin naga birth certificate dina da sunanta a jiki 'Khairat Abdallah' da signature dinta, sai a lokacin nasan cewa a america aka haife ni, dan haka ina zuwa America asibitin da aka haife ni na fara zuwa ina bincike ko zan samu wani information akanta amma ban samu komai ba. Takawa ya saya min gida ya saya min mota ya cika min account dina da kudi. Babu wanda yayi tsammanin zamuyi karatu da gaske ni kuwa na dage da karatu kawai saboda ina sa ran maybe in nayi karatu he will love me, na gama sec sch na shiga jami'a amma ko sau daya bai je ya ganni ba, sai dai duk kudin da nake so zai aika min. San da na gama first degree dina na shigo jirgi na zo Nigeria na kawo masa certificate dina ya karba ya duba, abinda yace min shine "good for you" daga nan ya jefo min takardata, alokacin ne na fahimci cewa ba wai halina ne baya so ba ni din ne baya so, Hajiya tace min ina alkawarinta nacewa bazan dawo Nigeria ba? Dan haka na tattara na koma America na koma makaranta. A lokacin nayi hankali sosai kuma na fahimci cewa duk abinda ya faru a rayuwata ya faru ne saboda babana yana so yayi protecting his family name, ni kuma na sha alwashin sai na bata family name din nasa da yake ji dash, duk tsiya dai shi ya haife ni kuma duk abinda nayi dole sunan nasa da yake ji dashi za'a ambata. Ina zuwa Nigeria hajiya ta fara tambayar alkawarin mu and I told her to fuck off, nasan abinda take so, bata so na a kusa da sarauta saboda tana son abbas yayi sarauta ita kuma bata san sarauta is the last thing on my mind ba, dan haka na fara bribing dinta cewa in dai har tana bani goyon baya ina yin duk abinda nake so to I will leave Abbas alone yayi ta sarautarsa.

Aikina na architecture yana kawo min kudi sosai, dan haka a yanzu bana bukatar kudin Takawa dan duk abubuwan da nake yi da kudina nakeyi, yanzu ba zai sa a dakeni ba kuma babu yadda zaiyi dani dan haka sai ya koma ignoring dina, nuna wa yake yi kamar bai san dani a duniyar ba amma nasan cewa sakonni na suna isa gurinsa sosai" ya juyo ya kalleni fuskarsa dauke da wani murmushin dana kasa gane kansa yace "to Maimunatu, I opened up to you, babu wanda na taba zama mukayi irin wannan maganar dashi bayan Amir sai ke. This is me. Yanzu zaki iya yin making decisions dinki yes or no" yana gama fadar haka ya mayar da glasses dinsa ya tayar da motar. Har muka je gida babu wanda ya sake cewa komai. Ni a gurina kaina ne ya kulle, I need to digest duk maganganun Sultan kafin inyi fully understanding din labarinsa. Yana packing nayi masa godiya, kai kawai ya daga min na fita. Sai bayan na gama da kowa nayi sallah nayi wanka na kwanta sannan na fara rewinding duk maganganun sultan ina reviewing dinsu. Duk abinda yake yi yana yi ne dan ya bata sunan family dinsa saboda yana ganin basa sonsa kuma sune sanadiyyar gurbacewar rayuwarsa. Yanzu na fahimci dalilin soyayyarsa da yara da taimaka musu ta hanyar gina orphanage da saka su a makaranta, saboda yasan ciwon rashin samun kulawa daga iyaye, yasan maraici duk da shi ba maraya bane. And suddenly I know what sultan wants, what he needs, LOVE.

Na dauki waya ta na duba time na lissafa naga rana ce yanzu a England, nayi dialing number din supervisor na, yana dagawa nace "sir I think I found the subject for my research project"

*what do you guys think is more important, Family or Family name?


Episode Forty Two : Born for This

Sultan ya jima a zaune a cikin motar bayan fitar Moon, shikenan ta faru ta kare, haushin kansa gaba daya yake ji, menene dalilin da yasa ya gayawa Moon labarinsa, yanzu ya tabbatar she will say NO to him, babu wacce zata so ta hada zuri'a dashi. Wannan shine dalilin da tun tuni ya kasa yin budurwa saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan rejection daga budurwa kuma, plan dinsa shine yazo Nigeria yayi destroying name din familyn sa sai ya koma America ya cigaba da rayuwa acan. A plan dinsa babu budurwa ballantana aure, saboda yasan aure zai ruguza masa plan dinsa ne tunda in yayi aure dole zai haihu kuma 'ya'yansa will still bare family name din da yake yaki da. Out of nowhere Moon ta shigo rayuwarsa, kallo daya yayi mata and he is hooked for life dan yanzu baya jin zai iya rayuwa babu ita wanda hakan yasan wani babban yaki ne ya dauko. Yasan babanta sosai, Ambassador M D, a very well respected man, tsakanin sa da ambassador MD tamkar hanyar jirgi ne da ta mota. Koda ace yayi convincing Moon baya jin zasu iya convincing babanta. Babansa kuwa yasan ba zai shiga maganar ba ballantana a duba darajarsa a bashi ita. Ya runtse idanunsa yana jin zafi a zuciyarsa. She means the world to him, he can't loose her. Ya tayar da motar ya fara tafiya. Yayi mamakin kansa dazu, he don't normally talk about himself amma kawai ya zauna ya saki baki yayi ta zuba mata magana kamar wadda tayi masa asiri, yanzu ya yarda da ake cewa Love is the strongest magic of all. Ya tabbatar cewa yau ba zai yi bacci ba.

Ko da yaje gida ya kwanta ma juyi yayi tayi akan gado amma ya kasa bacci. Sanda baccin ya dauke shi kuwa mafarkai yayi tayi na rayuwarsa a baya. Sai wajen assuba sannan a samu bacci mai dadi. Cikin bacci yaji wayarsa tana kara, da magagin bacci ya dauka ya saka a kunnensa ba tare da ya buda number ba "Assalamu Alaikum" yaji ance "wa alaika assalam, a tashi daga baccin nan haka assuba tayi" tuni yaji baccin ya watstsake, ya duba screen din wayar da sauri, Love, ya sake mayarwa kunnen sa yaji an sake cewa "in baka tashi ba zan kashe in sake kiranka har sai ka tashi" a hankali ya furta "Love, is that you?" Daga cikin wayar yaji sautin murmushinta ya lumshe idonsa yana hango fuskarta da dimples dinta, tace "yes it is me, ka tashi kayi sallah assuba tayi" still idanunsa a lumshe ya ce "then you are not dumping me, right?" ta danyi shiru inda bugun zuciyarsa ya karu sannan tace "no Sultan, am not dumping you". Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yaji tamkar an cire shi daga ukuba an saka shi a Ni'ima, murya can kasa yace "thank you, i will never let you down".

Na ajiye wayar ina bin screen din wayar da kallo, nasan na debo babban aiki but I can't stop myself, I feel like I was born for this. Jiya na jima banyi bacci ba kuma na yanke shawarwari da yawa, na farko zanyi accepting soyayyar Sultan dan nima ina son shi kuma ina so in chanza masa rayuwarsa in fito da kyawawan halayensa kowa yasan ko waye real sultan, zan bashi abinda ya rasa a rayuwarsa tun kuruciya, soyayya, zan bashi something to care for, me. Zan nuna masa cewa akwai wanda ya damu dashi kuma zan fahimtar dashi cewa idan har bai gyara rayuwarsa ba zai rasa ni. Matsalata daya shine yadda zanyi family na suyi accepting Sultan a matsayin mijina. Daddy na is soft as well as hard, dole in ina son in gabatar da Sultan a gurinsa sai na nemi soft spot dinsa which for now I don't know. Mommy is as hard as steel dan haka bansan ta wanne barin zan shigar mata da sultan ba, wannan dalilin ne ya saka na yanke shawarar zan cigaba da ganin sultan a boye sannan sai in nemi chance dina kuma inyi ta addu'a. Addu'ar ita na tashi nayi da daddaren nayi istikara na nemi zabin Allah, akan sallaya ta anan nayi bacci kuma ina farkawa da assuba Sultan ne ya fara fado min a rai na shi yasa na kira shi na tashe shi yayi sallah.

Tun daga ranar muka dinke ni da sultan, kullum muna tare dashi a waya dan har komawa nayi saka ear piece saboda bazan yi ta rike wayar a hannuna ba. Wani lokacin muna zaune a falo da 'yan gidan mu muna hira at the same time kuma muna waya dashi. Duk sun san cewa nayi sabon saurayi amma basu san ko waye ba saboda bana yadda in kira sunansa a gabansu. In muna so mu hadu kuwa sai in kirkiri fita unguwa, ko ince zanje kasuwa ko gidan kawaye, sai muyi plan din inda zamu hadu dana fito sai in sallami driver na ince ya tafi yawo in na gama zan kira shi, daga nan sai sultan yazo ya dauke ni. Ni kaina nasan abinda nake yi ba dai dai bane amma na kasa samun wata mafitar. A haka har hutun mu ya kare muka fara shirin komawa england. Ranar da na gaya wa Sultan abinda yace shine "kice tafiya England ta kama ni kenan" nace "ban gane ba?" Yace "wai kina nufin zan zauna a Nigeria ke kina England bana ganin ki? You dey craze? Ai bana jin zan iya sati daya ban ganki ba" dariya nayi sosai nace "Sultan aikin ka fa?" Yace "Daga can ma zan iya yi. To in kin tafi ai tunani ma ba zai barni in yi aikin sosai ba" kuma nasan har zuciyarsa yake wannan maganar, yes Sultan loves me that much, wani lokacin har zama nake inyi tunanin me zaj faru in aka ce za'a raba mu? Ni nasan cewa duk ranar da Daddy da mommy suka ce in bar Sultan to kuwa zan barshi har abada duk kuwa da son da nake masa saboda ban taba yi musu gardama ba kuma bana fatan inyi musu, ina son iyayena sama da komai kuma zan rabu da Sultan in sunce in barshi koda kuwa sansa zai zama ajali na. Ana gobe zamu tafi Amira tazo zamuyi sallama nan na bata labarin cewa sultan fa bin mu zai yi. Tace "bangane ba, daki za'a bashi a gidanku ya zauna?" Nayi dariya nace "ke Amira, da akwai gidan babansa

Please Login or Register in order to submit comment