Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi fushi, na kara matsawa nace "aunty Zaliha zamu tafi" tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka bata sake cewa komai ba. A waje na samu daada a kusa da mota nima na tsaya, musbahu ne yazo yana murmushi yace min "so... Har taimakon gaggawa yazo kenan?" Nayi murmushi, yace "there you are, gashi har kina murmushi, abinda tunda kika zo banga kinyi ba" sai yanzu nima na tuna yaushe rabona da murmushi? A hankali nace "thank you" bai ce komai ba, daada ta kalleshi cike da zargi tace "kai ka bata wayarka ko" murmushi kawai yayi mata, ya miko min kati yace "call me when you get your phone back, and ki gaida Sultan. Adios for now Moon" nima nace masa "adios" lokacin abba ya fito da sauri ya shiga gaban motar driver dinsa ne zai tuka, mu kuma muna baya. Na kalli gidan ina jin a raina kamar wacce na bar prison na samu freedom. Tun kafin mu fita daga gari na kwanta nayi pillow da cinyar daada na fara bacci. Sai gab da assuba muka isa Tahoua, already abba ya kira wani abokinsa yace gamunan zuwa, dan haka muna zuwa can muka je, ni kam na jima banyi bacci mai dadin na yau ba, muna zuwa muka yi sallah muka huta muka yi breakfast. Karfe tara muka sake daukan hanyar Niamey, da yake hanyar me kyau ce kuma motar lafiyayya ce karfe biyu muka isa, daada ce ta ringa yi masa kwatance har muka zo gidan kawu sharu wanda yake yayane a gurin daada kuma a gidansa muke zama duk sanda muka zo Niamey. Muna packing naga manyan motoci da number din Nigerian embassy na Niamey nasan daddy yazo, da kyar na iya controlling kaina saboda excitement, amma ina shiga compound din gidan naga palon kawu a bude da takalman mutane a bakin kofar, bansan sanda na zubar da takalmana a gurin na shiga dakin a guje ina rarraba ido ina nemansa, yana ganina shima ya mike tsaye ya bude min hannunsa, ai kuwa a guje na karasa na shige ciki na kankame shi tare da sakin wani kuka mai ratsa zuciya. Sai da nayi kuka na na gama sannan ya raba ni da jikinsa yana kallon fuskata, fuskarsa sam babu fara'a, kallona yayi tayi sama da kasa kamar mai tabbatarwa babu abinda aka gutsira a jikina, sannan yace "are you OK?" Kaina kawai na gyada masa. Na juya ina kallon sauran mutanen dakin, sai a lokacin naga mommy, tana zaune a kan carpet ta harde kafafuwanta a guri daya,fuskarta tayi ja, akwai uncles dinta su biyu na gurin uwa dana guri uba, na saki daddy na tafi na fada kan cinyarta, bata cemin komai ba sai dan bubbuga bayana da take yi. Daada ta shigo tare da abba suka gaisa da mutanen gurin. Daddy ne ya soma fada, daga dukkan alamu dama fadan ya keyi kafin mu shigo yanzu cigaba yayi "ta nuna min ni ban isa ba. Ta dauke min yarinyar ba tare da sanina ba kuma nayi nayi ta gayamin inda take taki. Ko wanne laifin yarinyar tayi au kamata yayi ace an gayamin first sannan kuma sai mu hadu ni da ita musan irin hukuncin da zamu yi mata, amma a haka ai ta nuna min ban isa da 'yata va kenan" kawu sharu ne yace "tashi ki shiga cikin gidan Maimoon" daga dukkan alamu daddy ya manta ina gurin. Na tashi na shiga cikin gida amma jikina duk yayi sanyi. Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mommy da daddy suna musu ba ballantana fada, dan ina da burin ace wata rana ni da mijina mu kasance tamkar mommy na da daddy na. Har daga cikin gidan ina iya jiyu muryar daddy yana fada, sam ba halinsa bane ba, dan da wahala kaga daddy yana fada, ballantana a gaban surukansa. Ji nayi gaba daya komawa Nigeriar ma ya fita daga kaina. Na zamanto dalilin samun matsala a tsakanin iyayena, kowa a cikin su is trying to put me first. Nasan duk abinda mommy tayi tayi ne dan tana ganin shine dai dai a gareni, amma ni abinda ban fahimta ba shine dalilin ta na kin gayawa daddy bayan kuma nasan komai tayi sai ta gaya masa. Ina nan kwance abin duniya ya ishe ni gwoggo Sa'a ta shigo tace in tashi inyi sallah inci abinci, bayan na gama ne ta tambayeni "Maimoon wai me ke faruwa ne tsakanin mommyn ki da daddyn ki?" A raina nace wannan tsegumi take so kenan, na daga mata kafada alamar bansani ba, daga nan bata sake cewa komai ba. Mommy suka shigo tare da daada, ko kallon inda nake bata yi ba ta shige toilet tayo alwala tazo ta tayar da sallah, daada tana ta 'yan mitocinta "ba shikenan ba, sai kije ai ya aura miki ko ma waye yaga dama, duk abinda ya fari kuma daga baya kar ki zo gurin mu, ki je can ku karata ke da baban naki" ni duk maganganun da take yi ban fahimci me take nufi ba dan haka kawai kallonta nake yi, mommy ta idar da sallah ta mike ta tsaya a bakin window tana kallon waje, muna haka sai ga dan aike daga waje "wai Maimoon tazo su tafi" na mike ina saka hijab dina nace "mommy ance mu fito" ta juyo ta kalleni tace "ance ki fito dai, ko kinji an ambaci sunana?" Na yar da hijab din hannuna na karasa kusa da ita nace cikin rawar murya "mommy ba tare zamu tafi ba?" Ta juya min baya tace "no, am going to stay here for a while, go with your father " na durkushe a gurin duk farin cikin komawa gida ya gushe daga zuciya ta, na rike kafarta nace "mommy ni bazan koma gida ba tare da ke ba, mommy dan Allah kiyi hakuri ki zo mu tafi, mommy in dai akan maganar Sultan ne zaku samu matsala da daddy wallahi ni na hakura da shi. Kun fiye min dubun sultan wallahi. Dan Allah mommy kiyi hakuri kice kin yafe min" kuka nake sosai. Ta dago ni ta rungume ni tace "ni na yafe miki tun tini Moon. I just wanted to clear the mess you created" nayi sauri nace "to in kin hakura kizo mu tafi gida tare" tace "that's not up to me, daddyn kine yayi fishi bani ba" na chika ta da sauri nasaka hijab dina na fita, a compound naga daddy tare dasi kawu, ina fitowa yace "taho da sauri mu tafi dare yana yi" ina zuwa na durkusa akan gwuiyoyina ina hawaye nace "daddy dan Allah kayi hakuri, wallahi ni na hakura da koma menene yasa kuka samu matsala da mommy, it's all my fault. Dan Allah kuyi hakuri mu koma gida gaba daya, ni ba zan iya rayuwa babu mommy ba kuma bazan iya babu kai ba" ya dago ni yace "it is not your fault Moon, kowa akwai destiny dinsa a rayuwa. Ita kuma mommyn ki ita tace tana son ta zauna anan for sometime, bani nace ta zauna ba, if you can get her to go with us then I will be more than happy" na koma ciki da sauri nace "mommy daddy yace ki zo mu tafi tare" tana kallona tace "shi ya gaya miki hakan?" Nace "eh" kafin ta sake magana kawu sharu ya shigo ya kama bambami "ya zaku ke wani abu ne kamar yara Fatima? Kece me laifi kuma kece mai fushi? Shi kenan kuma kinyi laifi sai kice ba za'a yi miki fada ba? Dan kin samu miji mai hakuri ko?" Ya juya kan daada A cigaba "duk kece kike daure mata gindi ai, kin barta sai abinda taga dama take yi, ai ba gata kike mata ba" sai da ya wanke su tass sannan yace mommy ta fito mu tafi. Fuu ta wuce ni tayi gaba, da sauri2 na bita a baya.

Ina fita na kalli motoci guda biyu da suke jiran mu, a lokacin idanuna suka sauka akansa. Yana tsaye ya jingina da jikin mota, light brown eyes dinsa a kaina. Shadda ce doguwar riga da wando dark brown a jikinsa, kalar shaddar ta kara fito da uniqueness din fatarsa, hularsa da takalmin sa light brown kalar idonsa. Yawan sumar kansa ta saka hular bata shiga kan sosai ba. Ya cire hular ya saka hannu ya hargitsa gashin sa sannan ya mayar da hular still idonsa a kaina. Kafafuwana naji kamar ba zasu dauke ni ba, what is he doing here? Muryar daddy naji yana cewa "Sultan ina Walid din kuma ya tafi? Ku zo mu tafi mana, weather din sahara is unpredictable"



Episode Fifty Four : Her Father's Daughter

Hannu na saka na murza ido na, ni dai nasan ba bacci nake ba ballantana in yi tunanin ko mafarki nake, idonsa yana kaina kamar yadda nawa yake kansa. He looks different, but it is still him. Ya rame shima. Ban taba ganin sa da manyan kaya ba maybe shi yasa naga ya kara chanzawa, but God he looks more handsome than ever. Kamar in ruga da gudu in taba shi dan in tabbatar ba hallucination nake ba. Muryar daddy naji kamar daga sama yace "Sultan, da kai nake magana fa" yayi sauri ya dauke idonsa daga kaina tare da sunkuyar da kansa kasa yace "sorry daddy" sannan ya zaro wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kana ina ne? Daddy fa har ya fito, kayi sauri" ya kashe. Muryarsa ce, so it is really him. Ya bude wa daddy kofar baya, bayan daddy ya shiga ya gyara masa rigarsa sannan ya rufe. Yana rufe kofar ya juyo ya sake maida idonsa cikin nawa, with all my psychology amma a lokacin kasa reading dinsa nayi, so clouded. Daddy ne ya sauke glass dinsa yana kallon sultan sannan ya kalleni, wannan karon nice nayi saurin dauke idona na sunkuyar da kaina sannan kuma sumi sumi kamar munafuka na tafi motar da naga mommy ta shiga, na zauna a baya a kusa da ita. Ta window na cigaba da kallonsa duk da yanzu bana ganin fuskarsa, bamu jima ba naga yaya Walid ya taho da dan gudun sa ya shigo gaban motar da muke ciki, ina kallon sultan ya bude gaban motar da daddy yake ciki ya shiga. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, can mommy tace a hankali "yana motar daddyn ku ko?" Ban fahimci me take nufi ba kuma nasan ba dani take magana ba shi yasa nayi shiru, ya Walid ne ya amsa "yes, mommy" tayi kwafa tare da dafe kanta. Ina son in tambaye su maganar wa suke yi saboda in tabbatar wanda na gani shi dinne dai ba wani ba, amma kuma bazan iya ba. Na runtse idona ina so in fahimci me yake faruwa. Wata na uku da sati biyu rabona da Nigeria amma ji nake kamar wadda nayi shekara daya. Me Sultan yake yi tare da daddy na? A iya sanina ko haduwa basu taba yi ba. Me ya faru bayan tafiya ta?

Kafin Moon ta samu amsarta mu bara mu koma baya mu riga ta sani.

Nigeria bayan tafiyar Moon

Walid da Habeeb suka bi bayan motar mommy da kallo. Walid ya juyo ya kalli Habeeb yace "ina zasu je?" Habeeb ya daga kafada yace "oho, nima kawai ganin su nayi suna shiga mota" Walid ya kalli agogon hannunsa, 7 ma bata yi ba, where can they possibly go to at this hour? Jikin sa dai bai bashi dai dai ba. Yace "OK, mu jira su su dawo kawai" ya juya ya koma ciki. Sai around nine mommy ta shigo gidan ita kadai, babu Moon babu Daada, a palo ta same su suna breakfast, ta shige ciki, har ta shirya ta fito suna palon, ta zauna tana hada tea, Habeeb yace "mommy ina su Moon suka tafi ne da sassafe haka?" Ba tare data kalleshi ba tace "inda ka aike su nan suka tafi" daga nan babu wanda ya kuma cewa komai, daya bayan daya suka mike suka bar palon, tabi bayan su da harara. Tana gamawa ta shirya ta tafi office. Sai karfe biyar ta dawo, tana yin packing wayarta tana yin kara, ta duba screen din 'dear' tayi ajjiyar zuciya, tasan maganar dai, tun jiya maganar daya ce, tasan dole zatayi facing wannan challenge din but she is ready. Moon is weak, too soft, tun da aka haife ta haka take, she trust too much, love too much and gives her all in everything she do, she is her father's daughter, shima haka yake, dan haka ita mommy dole ta zama strength din su, ba zata taba barin wani ya yi taking advantage of her sweet daughter's innocence ya cuce ta ba, not that so called Sultan and not that stupid munir. Tasan plan din munir, so yake a tilastawa Moon ta aure shi, ita kam ba zata taba barin ayiwa 'yarta auren dole ba da mutun kamar munir ba, over her dead body, abinda yayi recently ya tabbatar mata da ba son Allah da annabi yake yiwa moon ba, idan da ace yana sonta da ko ita data haife ta ba zata san abinda ya gani ba. Kiran ya sake shigowa wayarta, tayi taking deep breath sannan ta dauka, 'salamu alaikum" da sauri ya amsa sannan yace "ina kika shiga ne haka? Wajen five missed calls?" Ta danyi murmushi tace "kasan aiki yayi min yawa tunda na dawo dinnan. Ina office sai yanzu na dawo gida. Ya kake?" Ya danyi murmushi "am fine mommyn kids, busy body, ya kuke?" "Lafiya lau, just missing you" "wai Moon har yanzu wayarce bata gyara ba? Tun shekaran jiya rabon da muyi magana da ita. Please in tana kusa bata wayar" ta shirya abinda zata ce masa dama "bata gida yanzu, kafin in fita dama tace zata je gidan su Amira, yanzu na tarar bata dawo ba, nima bana son rashin wayar tata amma tace she is taking a time off" ya tare ta "ba wani time off, tell her in ta dawo na turo mata kudi taje ta siyo wani wayar, and also tell her to call me ASAP" tayi dariya sosai tace "to daddy, an gama" shima dariyar yayi, suka dan taba soyayya kadan ta kashe. Ta jima tana kallon wayar, ta san halinsa akan son 'ya'yansa especially moon amma bata yi tsammanin zai tada hankalinsa da wuri haka ba. Ta gyara packing ta shiga gida.

Karfe takwas na dare Munir ya shigo gidan, tunda yazo garin dama hotel ya kama, baya son zaman gidan saboda baya son asaka masa ido, gwara hotel yadda zaiyi abinda yaga dama. Yayi packing tare da dauko wayarsa yayi dialing number din Moon, switched off, ya tabe baki, shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa hakura da yarinyar nan, tun ranar daya fara ganinta yasan cewa he must have her, no matter what. Duk da kiyayyarsa da yake gani a idonta amma yaki hakura, she don't love him, she thinks she is too good for him. Bai taba sanin yana da sa'a a rayuwa ba sai shekaran jiya da ya ganta a gaban hotel din daya sauka, ya fito da niyar zuwa neman abokiyar harka kawai ya ganta tare da wannan half breed drunk guy din. Ashe itama A ce bai sani ba? Who would have imagine that the so good daughter of the so good ambassador is a drunk slut? Yayi dariya, yaso ace ya dauki video yadda zai ji dadin nunawa dan afi yarda dashi. Ya bude motar ya fito ya nufi cikin gidan. A palo ya tararda Habeeb shi kadai yana kallo, tunda ya amsa sallamarsa bai kuma kallon saba. Ya dora kafa akan kujera yace "kai ba ka iya gaishe da mutane ba?" Habeeb ya waiwaya ya kare wa palon kallo sannan yace "suna ina mutanen? Ni banga kowa da zan gaisar ba ai" Maimakon munir yaji haushi sai ma murmushi da yayi yace "duk zaku gane kuren ku ne, kuna daga wa mutane hanci kuna ganin kamar kunfi kowa a family ko? Da sannu duk zaku gane kuren ku" ya samu guri ya zauna yace "ina gantalelliyar kanwar taka take? Ko yauma ta fice? Ya kamata kuyi gaggawar saka mata mari ko kuma ku miko min ita nan ni nasan maganin irin su" Habeeb ya mike yace "kaga malam zo ka fita mana a gida, Moon ba gantalalliya bace ba, kuma tafi karfin ka wallahi, kaje kayi ta fadan abinda zaka fada, idan mafadin magana wawane majiyinta ai ba wawa bane. Babu wanda baisan halinka a family ba kuma babu wanda baisan halin Moon ba, babu kuma wanda baisan cewa moon bata son kaba, so go ahead and continue telling the lies, you will end up looking like a fool" a fisace munir ya mike yana nuna Habeeb "kai dama rashin kunyar ka har ta kai haka? Ni zaka cewa makaryaci? Rufa mata asiri fa zanyi in aure ta, bayan abinda tayi wa kake tunanin zai auri ragowar wani?" Kyakykyawan mari Habeeb ya ajiye a fuskar munir, abinka da farar fuska take fuskar tayi ja. Wannan yayi dai dai da saukowar mommy daga sama, munir ya shaki kwalar habeeb ya fara duka, mommy tayi sauri ta danna security alarm, kafin minti daya wajan mutum biyar suka shigo, da kyar suka raba munir da habeeb kowa ya daku a cikin su, mommy tace "ku fita dashi, kar ku sake barinsa ya shigo gidan nan" munir yace "bazan sake zuwa ba sai kun neme ni da kanku, kuma nayi muku alkawarin sai kun neme ni, daga nan 'yalleman na nu fa" ya fincike daga hannun security din ya fice. Mommy ta zauna akan kujera tana dafe kanta da yake neman sara mata, tabbas gwara data dauke Moon daga gidan.

Haka rayuwa ta cigaba da kasance musu har bayan kwana uku, a lokacin daddy is sure cewa something is wrong, tun Moon tana karama bata taba 24hours ba tare da ta yi masa waya ba in dai baya gari ballantana ace yau kwana biyar rabonsa daya yi magana da ita, tun mommy tana masa karya yana yadda har karyar tata ta kare in ya tambaye ta sai tayi shiru. Dole ya ajiye abinda duk yake gabansa ya tafi Nigeria. To him, his family is above everything, har aikinsa. Ya na kokarin handing over to his assistant kira ya shigo wayarsa daga Walid, ya daga da sallama sannan yace "ya akayi?" A hankali Walid yace "daddy you need to come home, something is wrong, Moon is missing" sai da ya jima yana assessing maganar a ransa sannan yace "what? Ban gane Moon is missing ba?" Walid ya bashi labarin duk abinda ya sani, sannan yace "Mommy ta dauke ta tun three days ago, mun tambayeta taki gaya mana inda ta kaita" daddy ya kasa cewa komai, not Moon, not my daughter, something must be wrong somewhere. Yace "OK, I will be home tomorrow, kar ka ce da mommyn ku komai, in nazo zanji duk abinda ake ciki" washegari kuwa ya sauka a abuja a private jet dinsa. Mommy kawai sai ganin shi tayi ya shigo palo, da sauri ta mike tsaye tana twisting fingers dinta, direct yace mata "ina Maimunatu?" Ta bashi amsa "she is safe"

Sultan
Bai taba regretting shan giya irin na ranar ba, yana kallo aka saka moon a mota aka tafi da ita amma ba zai iya yin komai ba saboda bashi da karfi, karfinsa shine babban abinda yake takama dashi, gani yake he is untouchable, amma yanzu gashi anyi touching something that is more precious to him than himself and he couldn't do anything. Da kyar Amir ya chusa shi a motarsa yaja suka nufi gida, babu abinda yake maimaitawa sai "I will kill him, I swear I will kill him" Amir dai bai ce masa komai ba, tun a hanya ya kira family doctor dinsu ya gaya masa su hadu a gida. Da kyar ya kama sultan ya shiga dashi part dinsa, direct bedroom ya kaishi ya kwantar dashi, lokacin jikinsa ya karasa saki gaba daya. Doctor yana zuwa ya duba kafar yaga bayan yankewa da yayi wanda sai anyi masa dinki, ankle dinsa ma ya goce, ya gama masa komai ya gyara masa kafar, yace kar ya taka kafar sai nan da 3days, ya bashi 3days bed rest, zai fita Amir ya kira shi gefe ya roke shi yayi wa Sultan allurar bacci dan yasan ba zai zauna ba, yana watstsake wa zai fita, ba musu doctor ya hada allurar, Sultan ya bude ido yana kallonsa yace "allurar menene kuma wannan?" Doc yace "pain reliever ce" kafin sultan yace wani abu yayi mishi ita. Tun kafin likitan ya fita sultan ya fahimci allurar me akayi masa, cikin magagi yace "I will kill you Amir, shine kasa akayi min allurar bacci ko? Bayan kana kallo yana dukan ta ko? Waya san me zaiyi mata in sunje gida, duk ni na jawo mata kuma sai na rama mata" Amir yana shafa kansa yace "Sultan brother dinta ne fa?" Sultan ya ture hannunsa yace "I don't care koma waye shi, he have no right to hit her" daga haka bacci ya dauke shi.

Har gari ya waye sultan yana bacci, bashi ya tashi ba sai kusan azahar. Yana farka wa Moon ce a ranshi. Ya mike da sauri sannan yaji pain a kafarsa ya tuna ashe yaji ciwo. Ya zauna a bakin gado ya dafe kansa. Jiya baiyi sallah magrib ba baiyi isha ba, ga subh yau sannan zuhr ta taho, baya wasa da sallah, baya yin nafila dai dasu azkar amma baya barin farilla. Zuwa gurin Moon have to wait sai yayi sallah tukunna. Ya tashi yaji zafin ciwon kafarsa har cikin kansa, a hankali yake jan kafar ya shiga toilet, it annoys him, babu abinda ya tsana irin abinda zai takura shi ya hana shi activities dinsa. Ya fara sallolinsa a tsaye amma dole daga karshe a zaune ya karasa sanoda ciwo. Damn it, wannan kafar ba zata barshi yaje yaga moon ba. Yasan ba za'a barta ta fito ba dan haka plan dinsa shine ya haura ya shiga dakinta ta window kamar yadda ya taba yi a England. Dama ya riga ya lura inane dakin ta. Yaji haushin ta akan kin gaya masa zancen project dinta da tayi amma ya yafe mata, ba zai iya yi fushi da ita ba. Ya mike ya koma toilet ya hada ruwan wanka, ya fito yana shiryawa amir ya shigo tare da wata maid dauke da abinci, ta ajiye ta fita, shi ya manta ma da wani abu wai shi abinci, duk soyayyarsa da abinci kuwa, ashe gaba ma akwai gabanta. Amir ya zau a yana kallonsa yace "ya naga kana shiryawa? Ina zaka je kuma? Kasan doctor yace 3 days of bed rest ya baka ko?" Ba tare da sultan ya kalle shi ba yace "fuck the bed and fuck the rest" Amir bai hakura ba yace "at least kafin ka fita eat something, rabon ka da abinci tun jiya da rana" sultan ya sake cewa "fuck the food" ya dauki key din mota ya saka takalmansa yayi hanyar waje, Amir ya bishi da sauri yace "don't do this sultan, zaka saka yarinyar nan in more trouble than she already is" ya juyo ya nuna amir da key din hannunsa yace "fuck you" ya juya ya fice.

Tafiyar da yayi zuwa packing space kadai ita ta tabbatar masa ba zai iya shiga dakin Moon yau ba, har gumi ya hada saboda ciwo, sai da ya zauna a mota ya huta sannan ya tayar da ita ya fita. Daga nesa da gidan yayi packing ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta, shi kansa yasan ba zai samu ba dan ya san da ace da waya a hannunta da yanzu ta neme shi, duk three lines dinta are switched off, har layin ta na England sai da ya kira. Ya jefar da wayar akan seat din motar, sai yanzu yayi nadamar kin cin abincin da yayi, da at least ya dan samu karfi ko yayane. He is not going to give up, no, sultan

Please Login or Register in order to submit comment