Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take ciki. Zan yi yawa da Sultan din shima zamuyi magana dashi." A hankali nace "to Daddy, nagode. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" yace "Ameen" na jima a zaune a gurin bayan mun gama wayar, kawai sai naji hawaye suna zubomin bansan dalilin su ba. A duniya mutum bazai taba samun mai sonsa ba sama da iyayensa, kuma babban dace a duniya bayan kasancewarka musulmi shine samun iyaye na gari. Iyaye na gari sune ginshikin samun rayuwa ta gari.
Amina
Tun ranar da tabar gidan Moon kullum sai ta kira number din Ibrahim sau ba adadi amma har yanzu bai dauka ba. Wani lokacin sai ta ji haushi ta jefar da wayar tace yayi wa kansa, amma kuma in ta huce sai ta kuma dauka ta kira shi, still no response, kuma karin jin haushinta shine number din tana shiga dauka ne ba'a yi. In tayi tunanin ta rabu dashi kawai sai kuma ta yi tunanin to ko bashi da lafiya ne, he might be dying on a hospital bed ko kuma alone a gida for all she knows. Ranar dai da akayi kwana biyar ta shirya da niyyar yau dai zata yi finding out ko ma menene ya same shi. Ta shirya tsaf ta hau sama dakin Mommy ta gaya mata zata fita tana son siyan wasu 'yan kaya, Mommy ta bata kudi tace kuma ta dauki driver amma kar ta dade. Tana shiga mota ta gayawa driver supermarket din Ibrahim, tasan dole zata samu labarin sa a gurin staff din gurin. Tana shiga ta danyi 'yar siyayyar ta kadan tazo gurin cashier ta biya sannan tace "please manager dinku kuwa yana nan? I am a friend of his ina son ganinsa" matar ta danyi jim tana tunanin me zatace sannan tace "eh yana nan ma'am, amma I don't know ko zai ganki, in kina da number dinsa ki kirashi mana in yace ki shiga kinga shikenan" Amina tace "ai number din nasa bata shiga ne, I would have call him, just ki je kice masa Amina tazo tana son magana dashi" matar tayi saurin girgiza kanta "am sorry ma'am, bana son inyi laifi" Amina tace "OK, just show me ina office din nasa yake sai inje ni kadai" nan matar tayi mata kwatance. Ta hau saman benen da aka nuna mata tana kallon kofar offices din da suke a jere, a kofa ta uku taga an rubuta "manager" sai data sauke ajjiyar zuciya sannan tayi knocking, babu response, ta sake yi sannan ta murda hannun kofar, ga mamakin ta sai ta ji kofar a bude, ta tura ta shiga da sallama. Yana zaune akan kujerar sa yana danna laptop din gabansa. Looking as handsome as ever. Ya dago idanunsa ya dora akanta, sanyin AC office din ya saka ta dan rungume hannayenta tana shakar daddadan kamshin sa. Bai ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanu. Ta dan kirkiro murmushi ta karaso gaban desk din sa, tace "Can I sit down?" Nan ma babu amsa, ta dan zauna tana kallon haduwar office din, ta na feeling nervous, damn you Moon da kika saka nayi miki wannan alkawarin. Kamar daga sama taji yace "What do you want?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa, babu dariya sam a fuskarsa, zuciyar ta taji ta fara tafasa, a ranta tace "what am I even doing here? In Moon tana son ta san halin da yake ciki she should come by herself" ta mike tsaye cikin zafin rai tace "am sorry I bother you" da sauri ta fice daga office din kamar zata tashi sama. Har ta fara sauka stairs din sai kuma tayi wani tunani, wannan mutumin kar fa ya dauka wai ta damu da shine ya saka take ta kiran sa a waya kuma har tazo office dinsa, da sauri ta koma saman, ba tare da sallama ba ta kuma bude kofar ta tsaya a bakin kofar tana kallonsa tace "ba wai dan na damu da kai nake kiranka a waya ba, ba kuma wai dan na damu da kai nazo office dinka ba har da zaka wulakanta ni. Moon ce ta roke ni inyi haka, har kasa ta durkusa akan guiwoyinta sannan na yarda zan yi, dan haka save your arrogance for her not me, ka tattara duk wani guntun wulakancin ka and shove it up your handsome face" tana gama fadin haka ta buga kofar da karfi ta juya ta tafi tana murmushin jin dadin ta rama wulakancin da yayi mata, sosai taga yadda expression din fuskarsa ya chanza sanda ta ambaci sunan Moon, ita wannan soyayyar mamaki take bata. Ji tayi ya bude kofar da sauri ya biyo ta, bata waiga ba taci gaba da sauka stairs din yace "Amina wait please" ta juyo tana kallonsa tace "saboda me? Saboda kaji nace sakon Moon ne zan gaya maka? Wait, ya akayi ma kasan sunana? Ka yiwa kanka ai, zan koma in gaya mata kace baka son jin komai daga gareta" ta juya ta cigaba da sauka, tana jin sa ya biyo bayan ta yana kiranta amma bata waiga ba, tana gama sauko wa tayi hanyar fita, sai da takai bakin kofa sannan ta juyo, bai biyo ta ba, the mighty manager ba zai zubar da ajinsa a gaban yaran sa ba. Ta fita ta shiga mota suka koma gida. Tana ta tunani a ranta, wannan wacce irin soyayyace haka, wanne irin so ne Ibrahim yake yiwa Moon, duk da cewa kiri kiri moon ta zabi Sultan, duk irin abinda ya faru ranar nan amma har yanzu mare ambaton sunan ta ya chanza masa lissafi. Ita kam bata jin zata iya yiwa wani irin wannan son. Ta fara tunanin abinda ya faru ranar da aka kai Moon, bata taba tsammanin wai maganar zata wuce shikenan kamar ba'a yi ba, amma Moon wai ko Daddy ta hana a gaya wa, wanne irin so ne haka itama Moon take yi wa Sultan?.
Tana shiga gida ta dauko wayar ta, 6 missed calls from Ibrahim. Dariya tayi a bayyane, she got him right where she wants him, sai ta rama duk abinda yayi mata, sai ta ja ajinta san ranta. Kwanan su biyu a haka, ya turo messages sunfi a kirga, ya kira ta sau ba adadi amma bata kula shiba. Ranar kwana na ukun dai ya gaji, zuciyar sa tana ta yi masa sake saken menene sakon Moon din da Amina zata bashi? Is she OK? Kar dai ace wani abun ya faru da ita ranar nan bayan tafiyarsa. Yana tashi daga office ya biya ta restaurant ya ci abinci daga nan gidan su Moon ya wuce, direct ya doshi gate din gidan yayi horn, mai gadi ya leko ya ga motar bai bude gate din ba ya fito ya taho gurin sa, ya sauke glass din sa yana kallon mai gadin yace "Amina tana na kuwa" mai gadi yace "eh tana nan" ya cigaba da kallonsa, Ibrahim yace "zan iya shiga in ganta ko kuma in tsaya anan za'a kirawo min ita?" Da da sauri mai gadin yace "a'a bara a bude maka ka shiga ciki" still amma yana kallon Ibrahim, sai kuma ya dan yi gaba kamar zai tafi ya kuma juyowa ya kalli Ibrahim, sai ya dawo da baya, yace "ni kuwa bawan Allah kamar kaine ka taba zuwa nan a shekarun baya ka bani sako in bawa maimunatu" Ibrahim yaji yawun bakin sa ya bushe, yace "eh nine baba, ashe baka manta ni ba" baba habu ya washe baki yace "yauwa har naji dadi, ai bana manta fuska, in dai naga mutum ko mai tsahon shekaru ina iya gane shi" ya danyi shiru sannan yace "abinda yasa kaga na tambaye ka shine, bayan na bata sakon, lokacin zasu tafi England, ta bani wata katarda tace in baka. Tunda kuwa suka tafi kusan kullum sai ta kira ni ta tambaye ni kazo? Daga baya ni nace mata ta hakura ta daina kira, in kazo da kaina zan kira ta in baka ita kuyi magana" Ibrahim ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya runtse idonsa yana jin zafi a ransa, baba habu ya cigaba da cewa "ina fatan dai ba wajan ta kazo ba yanzu ba, saboda anyi auren ta satin daya wuce" Ibrahim ya bude idonsa yace "No, ba wajanta nazo ba, wajan Amina nazo, nasan anyi bikinta. Amma baba takardar da ta baka tana nan kuwa har yanzu?" Baba habu ya danyi tunani yace "ai shekarun ne da yawa, amma zan duba maka, inna ganta kafin ka tafi sai in baka" daga nan ya bude wa Ibrahim gate ya shiga sannan ya tafi kiran Amina. Tun da Ibrahim yayi packing idonsa yake rufe yana jin dachi a ransa. She trusted that he will come back shi yasa har ta bayar da letter tace a bashi idan yazo, amma bai zo din ba, he imagine her pain, calling day after day tana tambayar ko yazo? Amma kullum amsar shine bai zo ba. Tace masa five years tayi tana jiran sa, a cikin five years din nan bata taba yin ko da saurayi ba, shi take jira duk kuwa da tasan cewa shi yayi aure. Ya dafe kansa da yaji yana sara masa. Ya bude ido yana kallon gidan, wannan shine karo na biyu daya shigo gidan nan, ya tuna abubuwan da suka faru a zuwansa na farko, a karshe ya juya ya tafi ya bar hawaye yana zuba a idon maimunatu. Ji yayi duk ya tsani kansa. Ta madubi ya hango ta ta fito tana kalle kalle, gabansa yaji ya fadi, she looks so much like Moon, but she isn't Moon. Ya danna horn ta juyo ta kalli inda yake, tana zuwa dai dai window dinsa ta bata rai ganin shine, ya rike kugu tace "what do you want?" Exactly abinda ya gaya mata a office dinsa, bai bata amsa ba ya turo ko fa ya fito, ya jingina da motar ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zu ba mata ido. Sai kuma ta kasa kallonsa ta juya tana kallon gefe, sai da ya gama tsare ta da ido sannan yace "na horu haka, ayi min afuwa, nayi kuskure ba zan sake ba" ta juyo tana kallonsa tace "me kayi?" Yace "laifuffuka na ai suna da yawa, na farko I used you to get into Moon's home, na biyu I ignored your calls, na uku I treated you badly a office dina" Ta dan so tayi murmushi amma ta maze tace "shine abinda ya kawo ka? Ai na dauka kazo kaji sakon da Moon ta bani in gaya maka ne. To tunda ka gama fadar abinda zaka fada ni bara in koma gida" yayi sauri ya tari gabanta yace "to ai baki ce kin hakura ba" ta murguda masa baki ta sake yin gaba, sai kuma ta juyo "au ba zaka tambaye ni sakon Moon din ba" ya girgiza kansa yace "just tell me if she is OK" tace "she is more than OK. Amarya ce fa ko ka manta" daga haka tayi komawar ta gida. Ya danyi murmushi yana jin dadi a ransa, at least maimunatu is OK, she loves mijin da ta aura, abinda ya faru ranar ya tabbatar masa da haka, abinda ba shi da tabbaci a kai shine idan shi mijin nata yana son ta kamar yadda take son sa. Ya koma motar sa ya tayar ya koma bakin gate, yana zuwa baba habu ya kawo masa wata 'ya karamar envelope, yace "ka ganta kuwa na gani" ya karba yayi godiya ya saka a aljihun sa ya tafi. Bai bude letter din ba sai da yaje gida ya gama duk abinda zaiyi yayi shirin kwanciya sannan ya dauko takardar ya bude;
Dearest Ibrahim
I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you.
I miss you
Maimunatu.
Ya ajiye takardar ya dafe kansa da hannayensa biyu yana jin garin yana juya masa. Ya tuna yawan zurga zurgar da ya ringa yi zuwa unguwar su maimunatu, amma Allah bai taba bashi ikon karasawa gurin mai gadin su ba, all this while wannan wasikar tana ajjiye, da ace ya karasa gurin mai gadin ya karbi wasikar ya karanta da duk wata karya ta Amira ta kare. Ba Amira ce ta raba shi da Maimunatu ba, Allah ne ya raba su, saboda ya riga ya kaddara cewa babu aure a tsakanin su. Ya jingina kansa a jikin frame din gadon for some time, sannan ya mike zaune ya dauko wayarsa yayi dialing number din Amina, ga mamakin sa sai yaji ta dauka, bata gaishe shi ba tace "what do you want?" Yace "har zan kwanta na tina baki ce kin yafe min ba har yanzu" tace "to sai na fada? Tunda kazo gidan mu kaga na fito ai na hakuran kenan ko" yace "thank you" tace "good night then" yace "wait. In really kin hakura can we be friends then?" Ta danyi shiru sannan tace a hankali "am not Moon" yace "I know" tace "ok, friends then" yace "to kiyi min dariya mana inji sai in yarda mun zama friends din" tace "I don't have dimples" yace "I know".

Episode Seventy Eight : The Storm
Bayan Wata Uku
Rayuwa tana tafiyar mana sosai cikin jin dadi. Dan ni kam a bangare na bani da problem. Su Hajiya tun ranar da suka zo na kora musu bayani basu sake dawowa ba, su fa'iza su na dan zuwa kadan kuma sam ban taba daure musu fuska ba. Amira ma ta dawo twice, mu kan danyi hira kadan amma sam ba kasa sake wa da ita kamar da, mun koma kamar strangers. Kullum kuma in tazo bata da zance sai na aure, ta gaji da zaman gida yanzu aure take so dan yanzu kullum suna cikin samun sabani da mamanta. A bangaren Sultan kuma tunda ya koma aiki ya zama busy, dan kullum sai dai akai masa lunch dinsa office, sai bayan la'asar yake dawowa, amma kuma in ya dawo din in ba dole ba baya fita ko kofar gida sai dai in zashi masjid, kullum company sa kara habaka yake yi, dan yanzu da kansa yake karbar kwangilar gine gine yana yi, na government ko kuma na private mutane. Sultan ya rike addini sosai dan har mamaki yake bani yanzu, karatun qur'ani kam kullum sai yayi safe da yamma, wani lokacin na yamman muyi tare. Ni kuma babu abinda nake yi a gida sai koyon girki, dan a yanzu Asma'u tafara bari na ina yin abincin da kaina, sai dai ta dan ci gyarana kadan, a raina nakan ce 'ashe ma abin babu wahala, kawai sa kai ne' tun daga kan main dishes, snacks, drinks babu abinda asma'u bata koya min, tace so take yi in na fara yi wa Sultan girki duk abincin da yaci idan ba nawa bane ya ji ci salam. Duk abinda kuwa na dafa ko sultan baya nan sai na ajiye masa na bashi yayi tasting, Sultan kam ko abin bai yi dadi ba cewa yake yi yayi dadi duk da nasan wani lokacin alkunya kawai yake yi min. Soyayya tsakanin mu kuwa kullum karuwa take yi, ni da na dauka da anyi na dokin aure shikenan amma ashe ba haka abin yake ba, stamina din Sultan har mamaki take bani, dole na na yawo jakar magungunan daada na cigaba da amfani dasu. Mun je gida ranar da Daddy ya dawo daga England, tunda akayi biki na sai ranar naje gida, da gudu naje na rungume Mommy, ita kam kallo na kawai take yi dan gaba daya na chanja, nayi kiba na kara chika, fata ta har wani yellow take yi saboda haske. Sau da yawa in kawayena suka zo sukan tsokane ni suce ko ciki ne dani, amma ni nasan bani da komai, dan cikin wata ukun nan ko tsallaken period ban taba yi ba. Ranar a gida Sultan ya barni na wuni. A lokacin ne Amina take bani labarin yadda suka kare da Ibrahim, naji dadi duk da dai tace min yace bayason jin labarin sultan, kawai shi fatansa in am OK shikenan, nan take min complaint cewa he is becoming a little bit touchy, nayi dariya nace "then it is going more than I expected" ta bata rai tace "ya zaki ce haka, ina gaya miki cewa yana yawan tabani kuma kice min kina murna?" Nace "yi hakuri Amina ta, abinda nake so ki gane shine, Ibrahim was born and raised in yaroba land, they are Muslims and then they are yarobas, su a gurinsu it is nothing dan saurayi ya rike hannun budurwarsa" ta harare ni tace "waye yace miki saurayi na ne? We are just friends" Nace "OK let me rephrase my statement, su a gurinsu it is nothing dan aboki ya rike hannun abokiyarsa" yadda na fadi kalmar abokiyar ya saka mukayi dariya gaba daya, nace "nasan ki fa Amina, kuma nasan tun ranar da kika fara ganin sa kika zo kina santinsa" ta tabe baki tace "lokacin ai bansan waye shi a gurinki ba" nace "he is nothing a gurina yanzu, not even my friend, but he will soon be my brother in-law" tace "in ya daina taba ni ba" nace "ai ke zaki hana shi, next time ya rike miki hannu ki bata rai ki ce kar ya kuma ba kya so, daga ranar ba zai kara ba". Sai dare Sultan yazo daukana. Kamar ba zan fito ba saboda duk su yaya Walid suna gida ana ta hira da dariya, a nan na fara matsar kwalla wai ni dan Allah sultan ya barni in kwana sai gobe na koma, ni kaina da nake fada nasan it is impossible, dan in dai zan kwana a gida to tabbas sultan zai biyo ni mu kwana tare. Mommy ce ta rakani har mota amma ita ma kamar ba zata barni in tafi ba, muna jan mota na dora hannu aka na rusa kuka wai ni ya mayar dani gidan mu. Gefen titi ya samu yayi packing sai da ya tsotse hawayen fuskar tas sannan ya dashi motar muka tafi kuma yace in dai na sake wani kukan abinda yafi haka zai yi min ba ruwansa da cewa a titi muke. Na san zai iya aikatawa dan haka nayi shiru da baki na. Muna zuwa gida sai da ya tabbatar ya mantar dani 'yan gidan mu sannan ya rabu dani.
Ranar wata Friday muna zaune palo da asma'u da baba gaji da wasu daga 'yammata na, baba gaji tana ta bamu labaran abin dariya muna ta darawa without a care in the world, ina yi amma ina kallon agogo, nasan sultan yana hanya by now, ai kuwa ba'a jima ba sai ga shi ya shigo. Yana shigowa duk suka nutsu, haka nan sultan yake da wannan kwarjinin, duk inda ya shiga sai kaga mutane suna shakkarsa ko da kuwa bai yi musu magana ba. Ya zauna a kujera, duk suka gaishe shi sannan suka fita, nayi masa sannu da zuwa, ya amsa a hankali yana jingina kansa a bayan kujerar, na tashi na dauko masa pineapple drink din dana hada dazu, na kawo na zuba masa a cup na mika masa, bai karba ba ya zauna yana kallona, nasan me yake nufi nayi murmushi na zauna a cinyarsa na dafa kafadar sa da hannu daya daya hannun kuma na dauki cup din drink din na fara bashi a baki, sai da ya shanye cup din tas sannan ya dauke kansa, na karo masa wani na sake bashi, wannan karon a hannunsa ya karba yace "let me guess, ki kika hada wannan drink din" na washe baki nayi fari da ido nace "you guess right, this drink was made by yours truly, Asma'u bata ma san nayi ba" yace "wow, wannan matar fa so kike ki fi asma'u iya girki, kuma it is like duk abinda kikayi yana da wani unique taste na musamman" naji dadi sosai nace "thank you Darling" ya juya wuyansa, kashin wuyan yayi kara alamar gajiya, nace "you are overworking yourself honey, ya kamata ka ke rage aikin nan kana hutawa fa" ya kwantar da kansa a kirjina yace "I know, shi yasa nake shirya mana tafiya zuwa Maldives, karshen watan nan in sha Allahu" na tashi tsaye na fara tsallen murna yana ta yi mini dariya, sai da na gama murna ta na zagayo bayansa na saka hannayena biyu akan kafadarsa na fara yi masa tausa, he feels so tense, a hankali nake matsa masa kafadunsa zuwa wuyansa, yayi ajjiyar zuciya yace "God, that feels so good" na cigaba dayi masa tausar har sai da naga yayi relaxing sannan na daina na zagayo gabansa naga kamar wani abu yana damunsa, nayi kneel down a gabansa na dora hannayena akan cinyarsa nace "me ya faru ne a office din yau? Ya dan saki ransa yana murmushi yace "why did I marry a psychologist?" Nace "because you are lucky" ya shafa fuskata yace "you are damn right I am" kamar ba zai cigaba da magana ba kuma sai yace "uncle galadima ne yazo office dina dazu. Dama tun dadewa yake cewa zai kawo min ziyara. To yau yazo muka zagaya dashi yaga gurin sannan aka zauna akayi addu'ah" yayi shiru, nace "then what's the problem?" Yace "kafin ya tafi ya kirani gefe yake ce min yana son in ringa zuwa fada ana zama tare dani, wai I belong there, a kusa da Takawa. Ni kuma na gaya masa NO, I am happy now, I have you, I have my job, bani da wani problem. He still insisted wai inje inyi tunani akai" na dan jinjina maganar a raina kafin nace "to yanzu wacce shawara ka yanke?" Yace "my answer is still no. Yanzu ina zaune lafiya Takawa ya dauke idonsa daga kaina, maybe ma ya manta da existence dina, amma ina zuwa kusa dashi shikenan na zama nama, ba lallai ne ma ya barni in shiga ba, zai yi disgracing dina ne a gaban mutane kuma ni na jawowa kai na. Besides, ina shiga gurin people will think kamar I want the throne" dariya na fara yi a hankali, ya tsaya yana kallona fuskarsa da mamaki, yace "menene abin dariya kuma?" Nace "since when did Sultan care about me mutane suke tunani akan sa?" Shima dariyar ya fara yi a hankali ina taya shi, sannan yace "na chanza da yawa ko?" Na mike na koma na zauna a cinyarsa ina shafa fuskarsa nace "yes ka chanza my Darling, and I am so proud of you. Amma yanzu ka ajiye Takawa a gefe, ka ajiye abinda mutane zasu ce a gefe, tell me what you really want" ya jima yana kallon gefe yana tunani sannan ya juyo yana kallona yace "lokacin da ina yaro, lokacin kakana yana da rai, there is nothing I want more than the throne. Kullum abinda yake gayamin shine the throne is mine, kullum idan yana zaune a fada zai saka ni in zauna a gabansa, telling me to learn, saying that one day I will rule. Wannan yana daya daga cikin abinda yasa na zama so furious lokacin da babana ya daina zuwa fada dani, a lokacin ina tunanin sarauta is what I was born for dan haka karbarta kamar an cire min purpose na rayuwata ne, amma as I grow up, musamman bayan haduwa ta da ke, na fahimci cewa there is more to rayuwata than sarauta, and now I don't want it, har cikin zuciyata" tun daya fara maganar nake kallonsa kuma na fahimci har cikin zuciyarsa abinda yake fada haka ne. Nace "tunda haka kake so then that's exactly abinda zaka yi. Amma ni ina ganin no matter how much kake so kayi ditching sarauta it is in your blood. In kana ganin zaka iya why not kake zuwa once a week, kamar on Fridays, just ka gaishe shi da sauran mutanen gurin ka fito, Amir zai iya kula da companyn ka a lokacin. At least kaga galadima ba zai ga kamar ka ki daukan shawarar sa ba" ya danyi murmushi yace "in dai hakan shine abinda my Queen tace to

Please Login or Register in order to submit comment