Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muga jikin nasa" idon takawa ya kada yayi ja saboda bakin ciki, a ransa yana cewa "wannan yaron Amir yake kowa? Zaman sa ya kare a gidan nan" amma kuma a fili ba zai iya musa wa hakiman sa ba, musamman king makers, sune kamar shugabanni dan dattijai ne sosai, sune suka nada babansa, suka nada shi, sune suke da alhakin zaba da nada sarki. Dole Takawa ya mike, gab daya sauran hakimai suka mike, Galadima ne akan gaba. Amir yana ganin su yasan tarkon sa yayi kamu, ya shiga motarsa yayi gaba su kuma duk suka biyo bayansa. Gaba daya mutanen asibitin ranar sai da suka fito kallo, ga sarki da hakimansa gaba daya sunzo dubiya, direct dakin da sultan yake kwance suka nufa. Dakin bai dauke su gaba daya ba dan haka wasu ta taga suka leka suna gano sultan a kwance har yanzu yana bacci, Amir yaje kusa dashi yana shafa kansa yace "Sultan ka tashi ga Takawa yazo duba ka" a hankali idon Sultan ya fara budewa kadan kadan yace murya can kasa "Daddy? My Daddy?" Galadima ya rike hannusa yace "eh Sultan, babanka ne yazo ya ganka. Ya jikin nasa" Sultan ya kalle shi, ya dan hadiye yawu sannan ya fara kallon mutanen dakin, idonsa ya tsaya akan Takawa da yayi kicin kicin da fuska, ya karbe hannu sa daga na galadima ya mika gurin sarki yace "Daddy?" Gaba ki daya kowa idonsa yana kan Takawa dole ya karasa ya kama hannun sultan ya rike, hawayene ya fara gangarowa a idon Sultan, amir yaji wani iri a jikinsa, tun da suka girma, tun sanda aka kaisu lagos, bai taba ganin hawayen sultan ba sai yau, masu raguwar zuciya a gurin sai da suka taya sultan kokawa saboda babu wanda bai san kiyayyar da sarki yake yiwa sultan ba kuma babu wanda yasan dalili, a hankali sultan ya fara kukan kuma sai kukan ya fara karuwa har da sheshsheka, ya rike hannun Takawa yaki chikawa. Wani abu takawa yaji ya tsaya masa a zuciyarsa ya tokare, ya kasa hadiye koma menene, ya kasa fahimtar me yake ji. Muryar sultan yaji yace "Ummee na, Ummee na". Kan Takawa ne yayi bala'in sarawa, ya cika hannun sultan ya rike kansa da hannu biyu yana ambaton sunan Allah, ummee na, ummee na, a ina ya taba jin wadannan kalmomin, wani dan karanin yaro ya hango a idanuwansa wanda bazai wuce shekara biyu ba a hannun baba gaji yana ta zunduma kuka yana miko masa hannu yana cewa "Daddy na, Daddy na, ummee na, ummee na" a lokaci daya komai daya faru ya dawo masa tas a cikin kansa, take ya yanke jiki ya fadi sumamme a gaban gadon da sultan yake a kwance.
Hmm. Things are not always what they seem.


Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
A hankali Takawa ya fara dawowa haiyacinsa, ya bude idonsa da sauri yana kokarin ya dai dai ta tunanin sa, ya ilahi wannan wanne irin mugun mafarki yayi haka? A mafarkinsa wai an raba shi da khairat, a mafarkin sa kuma wai baya son Little Love, a mafarkinsa little love shine abinda yafi tsana fiye da komai, kuma wai har anyi shekaru da yawa har Little Love ya girma yayi aure. Oh wannan wanne irin mugun mafarki ne haka? Ya yinkura ya tashi zaune yana duba gefensa dan ya tashi khairat ya bata labarin mafarkin da yayi, amma sai me? Babu khairat a gurin, kuma wannan gadon ba nasa bane ba, ya kalli dakin shima, wannan dakin shima ba dakin sa bane ba, yayi kama da executive dakin asibiti, amma kuma haduwar dakin babu abinda ya raba shi da dakin gida sai drip daya gani a hannunsa. A karshen mafarkinsa an yi forcing dinsa ya je asibiti duba little love daga nan kuma bai san me ya faru ba sai ya farka daga mafarkin, to ko dai still har yanzu mafarki yake yi ne? Ya matsa ledar drip din yaji zafin shigar ruwan, mutum ai baya jin zafi a mafarki. Ya tashi zaune sosai ya cire drip din ya mike tsaye, gaban taga yaje ya daga labulen tagar, tabbas nan asibiti ne. Ya ilahi what is happening? Kofar toilet ya bufe ya shiga dan ya wanke fuskarsa maybe ko zai dawo haiyacinsa sosai, abinda ya gani a cikin madubi shine ya saka ya daskare a bakin kofa, he looks exactly like yadda yake a cikin mafarkinsa, older, thirty years older, ya karasa gaban madubin yana taba fuskarsa, shi din ne dai kuma tabbas wannan ba mafarki bane ba. Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu duk abinda ya faru da gaske ya faru kenan? Yanzu shekararsa talatin rabonsa da khairat? Tana ina yanzu, shin tana da rai ko akasin haka? And Little Love, my poor innocent Little Love. A toilet din ya durkushe yana rusar kukan dashi kansa bai san ya iya irinsa ba.
30 years back
Tabbas Prince Sadiq Abdallah yayi soyayya da Khairat Faisal Abdallah a Oxford, England. Khairat full blood balarabiya ce kuma she too is of royal blood, born and raised in Riyadh, Saudi Arabia. Soyayya suka yi mai tsanani wadda har suke ganin cewa kamar they share the same soul but different bodies. Amma duk wannan soyayyar da suke yi iyayensu basu da masaniya a cikin al'amarin, wannan kuma ya faru ne kasancewar khairat balarabiya dan larabawa da wahala su dauki 'yar su su bada ita aure ga bakar fata, bahaushe. Khairat bata taba ganin anyi haka a familyn su ba, in fact a familyn su ma mostly auren dangi ake musu, dan already ma ita da akwai wanda aka riga aka ajiye mata zata aura in ta gama makaranta. Wannan shi yasa duk nacin da Sadiq yake yi mata akan ta barshi yaje gidansu taki yarda. Lalube kawai suke yi a cikin duhu. Sadiq yasan da irin kalubalen da yake gabansu amma shi bashi da tsoro sam, kuma ya riga ya saka a ransa cewa khairat tasa ce ko da kuwa sama da kasa zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da ita. A haka har suka gama makaranta, iyayen Khairat suka zo suka dauke ta suka mayar da ita gida. Wannan ba karamin tayar da hankalin Sadiq yayi ba dan ya san da maganar wancan hadin da ake so ayi mata a gida. Babu shiri shima ya tattaro ya dawo Nigeria gurin sarki Abdallah, ya shigar da maganar yana son sarki Abdullah yaje can Riyadh ya nemo masa auren Khairat. Sarki Abdallah yasan abinda dan nasa yake nema is close to impossible, ba zasu bashi auren khairat ba, musammam tunda an riga an yi mata miji, ba zasu karya alkawari ba, hakan yasa yayi kokarin tausar zuciyar dan nasa akan ya hakura da auren ya dawo gida ya nemi auren ko wacece a Nigeria zai nema masa aurenta, amma Sadiq was as hard as stone, dan haka ya tubure shi lallai ita yake so kuma ita zai aura. Da Sadiq ya fahimci cewa baban nasa bashi da niyyar honoring wish dinsa ga kuma time yana kurewa dan yasan a koda yaushe za'a iya daura wa khairat aure, dan a halin yanzu ma tayo masa waya tana kuka cewa maganar auren ta tashi kuma ta fadawa babanta cewa ita bata son wanda za'a aura mata kuma shi sadiq din take so, tana fadar haka baban ta ya saka aka kaita daki aka rufeta yace ko palo kar a barta ta ta kuma fitowa. Wannan ba karamin tayar da hankalin sadiq yayi ba, dan a lokacin ji yake yi da ace ya rasa khairat gwara ya rasa ransa, sai ya hada kayansa bada sanin iyayensa ba ya gudu daga gida. Riyadh ya tafi ya kama hotel ya zauna yana plan din abinyi, ba'a karbe wayar khairat ba dan haka suna waya da ita, ita take kara encouraging din sa ma akan yazo din, suka shirya plan dinsu sosai, plan A da plan B. Plan A shine zaizo gidan su ya nemi aurenta a gurin uncle dinta. Plan B kuma shine idan plan A yayi failing an hana shi auren nata zai salallabo cikin dare ya sace ta su gudu. Sadiq yasan cewa Saudi Arabia ba Nigeria ba ce ba, suna da tsatstsauran doka, idan aka kama shi zai iya rasa ransa, babu wanda zai kalle shi ya matsayin Prince tunda su a gurinsu he is not a Prince, amma soyayya ta rufe masa ido. Ya shirya tsaf yaje ya aiwatar da plan A, amma ko kyakykyawan kallo bai samu daga uncle din Khairat ba, in fact warning ma ya buga masa kuma yace ya bashi two days yabar kasar in ba haka ba zai turo masa askarawa suyi out dashi. Sadiq zuciya kamar zai mutu dan bakin ciki, wai yanzu saboda tribe dinsa da kalar fatar sa shi yasa za'a hana shi auren wacce yake so? Menene aibun sa? Yana da asali, yana da addini, yana da ilimi, yana da dukiya kuma shi cikakken namiji ne bashi da tawaya ko kadan amma saboda shi bakar fata ne an hana shi aure duk kuwa da cewa yarinyar shi take so. Nan take ya kira khairat ya gaya mata plan A failed, initiating plan B. Khairat ce ta tsara masa duk yadda tsarin gidan nasu yake shi kuma ya zana, tayiasa bayanin dakin da take da komai. Tayi wa mahaifiyar ta dabara ta saci spare key din kofar gidan ta jefa ta window, ta kira sadiq ta gaya masa shi kuma yazo ya dauka, ta kuma gaya masa exactly a inda ake ajiye keys din gidan. Ana gobe daurin auren khairat Sadiq yazo, bai samu matsala ba saboda su a Saudi Arabia babu burglary dan haka ba wani security. Tunda kowa yasan hukunci babu wanda yake shiga gidan wani. Yana zuwa ya bude kofa da key ya shiga ciki, duk gidan suna bacci banda khairat da take yi masa magana ta waya tana kara yi masa bayanin inda zai bi, a haka har yaje har dakin mamanta ya dauko key din dakinta. Ya fito ya tafi dakinta ya bude, already a shirye take dama dan haka ko magana basu yi ba ta biyo shi da sauri suka fita daga gidan suka shiga motar daya zo da ita, a dakinsa na hotel suka karasa kwana, da sassafe dama yayi musu booking plight suka tafi airport, around 7, jirginsu ya tashi zuwa America. Sun zabi America ne saboda it's a free country, babu wanda ya damu da wani, kuma sun san za'ayi wahalar samun su a can saboda girman ta. Plus England shine guri na farko da za'a fara zuwa neman su. Sadiq bai san ya debo da zafi ba, a saudiyya, ka shiga har gida, kuma gidan masu sarauta, ka sace musu yarinyar da za'ayi bikinta gobe, ka gudu da ita ku bar kasar gaba daya. Chafdi.
Kwanan su daya a America, saboda suna gudun sabawa ubangijin su, suka nemi wani imam suka bukaci a daura musu aure, liman ya nemi waliyyanta khairat tace ita marainiya ce bata da kowa a america, daga ita sai iyayenta kuma iyayen yanzu sun mutu kuma bata taba zuwa garin suba ballantana ta san danginta, sadiq ne duk ya tsara mata wannan yace in sunxo ta fada. Imam din ne ya zauna a matsayin waliyyinta, yace duk wani problem da ya tafu da auren ta zo gurinsa, ya zama shine babanta, Sadiq kuma shi ya tsaya a waliyyin kansa, aka daura aure Sadiq ya bada sadaki, mutanen da suke masallacin sune shaidu. Daga nan sukayi signing marriage certificate sun zama islamically and legally married. Daga gurin daurin auren direct airport suka nufa suka shiga jirgi sai Nigeria. Shi sadiq a tunanin sa uban yaki yadda da auren ne saboda yana jin tsoron zuwa neman auren, dan haka yake ganin yanzu tunda yaje ya aikata abinda ya aikata ai shikenan komai ya wuce. Yana zuwa gida da khairat tun kafin yayi wa sarki Abdallah bayani sarkin ya fahimci abinda ya faru, sato khairat sadiq yayi. Sosai hankalin sarki da Yaya ya tashi dan su sunsan menene zai je yazo. Sadiq ya gaya musu cewa ya riga ya auri khairat dan haka iyayenta babu yadda zasuyi dashi, amma sarki ya san cewa auren nata da yayi shi zai kara mayar da case din worst, saboda zasuyi charging dinsa da forced marriage wanda babban laifi ne a saudiyya, sarki Abdallah ya nuna wa Sadiq cewa lallai ya dauki yarinyar mutane ya mayar da ita gidansu, jin haka Sadiq ko amsa bai bashi ba ya kamo hannun khairat suka fice daga palace din. Shi a tunaninsa yama za'a ce ya sake ta ya mayar da ita gida duk uwar wahalar da yasha kafin ya same ta? A gidan wani abokinsa anan Abuja suka kwana, da safe suka kuma hawa jirgi sula koma America. Sun yanke shawarar gwara suyi zamansu su kadai tunda iyayensu sun kasa fahimtar irin son da suke yiwa junan su. Shikenan kuma suna zuwa america aka shiga honeymoon. Rayuwarsu kawai suke yi suna jin su on top of the world, babu mai saka su babu mai hana su, babu abinda suke sai soyayya kamar su chinye junan su, sun zama Americans sosai. Sadiq ya nemi aiki da takardunsa kuma bai sha wahala ba ya samu, suka nemi gidan haya suka kama, khairat taso neman aiki itama amma sadiq ya hana yace albashinsa ya ishe su, su biyu kadai basu ajiye kowa ba.
Wata daya da auren su khairat ta samu ciki, nan fa murna a gurinsu kamar me, Sadiq yana kallon cikin a matsayin hanyar komawarsa gida, idan babansa yaga cewa ya haihu da khairat ai dole ya hakura ya karbe ta da duk wani challenges din da auren nata zai taho dashi. Su biyu suka yi renon cikin su cike da soyayya da kulawa, da watan haihuwar khairat ya kama kuwa sadiq a jiye aikin sa yayi ya dawo gida gurinta yana kula da ita, hana ta yin komai yayi, komai shi yake yi mata, ko ya kuwa yaga ta dan bata fuska sai hankalinsa ya tashi. A haka labor ya zo mata, hankalin sadiq ya tashi sosai gani yake kamar mutuwa zatayi ballan tana da ta fara bashi wasiyyar ya kula da babyn su, ya kaishi gurin 'yan uwanta ya basu hakuri. Kusan akan chinyarsa ta haihu dan zama yayi dirshan akan gadon ya rungume ta yana yi mata alkawarin daha wannan haihuwar ba zai sake bari ta samu ciki ba saboda ba zai sake bari ta sha wannan wahalar ba. Ana haihuwar Sultan sadiq ya karbe shi ya rungume a kirjinsa, ko goge shi ba'a yi ba, dariya kawai yake yi saboda murna, shi a rayuwarsa bai taba ganin kyakykyawan yaro irin wannan ba, ya sunkuyo gurin khairat da ake gyarawa yace "look at our Little Love, He looks just like you". Nan fa suka ninka soyayyar da suke yiwa junan su suka dora akan Little Love dinsu wanda yaci sunan babansa, Abubakar, sukan zauna kawai su saka shi a gaba suna kallo, watan Sultan biyu a duniya Sadiq yaga cewa ya kamata su gwada zuwa gida suga yadda zata kasance, suka shirya amma basu kwashe kayansu ba saboda basu da tabbas din za'a karbe su a gidan. Sadiq ya shiga gida hannunsa na dama dauke da two months old Sultan, hannunsa na hagu kuma rike da Khairat. Da fushi sarki Abdullahi ya taho, yana zuwa Sadiq ya mika masa Sultan wanda a lokacin kwuiya ce dashi amma kawai sai akaga ya tafi gurin sarki yana bangala masa dariya yana ta ba masa fuska, Sarku Abdallah ji yayi ya kasa fadan kuma, niyyarsa yana zuwa ya kora su su koma inda suka fito amma sai ya kasa, wata soyayyar yaron yaji tana ratsa zuciyarsa. Kowa a gurin sai ya koma kallon su, sultan tamkar ya saba da kakan nasa, Khairat da Sadiq sai dariya suke yi suna mamaki. Dole Sarki Abdallah ya karbi surukarsa da jikansa. Aka ware musu dakunan su suka tare, suka tattaro kayansu gaba daya suka dawo gida. Nan take Khairat tayi farinjini a gurin mutane saboda kirkin ta, ba ta iya hausa ba amma koya take har a gurin bayin gidan, bata damu cewa wai ta fita daban a cikin su ba harkokinta kawai take yi tana kula da mijinta da Little Love dinta. Sarki Abdallah ya karbi surukarsa amma a cikin ransa ya san cewa this is not the end of the story. Dole wata rana sai iyayen khairat sun gano inda take, ko kuma ita khairat din da kanta ta nemi zuwa gurin iyayenta. Takanas ya tura kaninsa zuwa Riyadh dan ya bincika masa yaji me iyayen khairat suke ciki, labarin da aka kawo masa sam baiyi masa dadi ba, iyayen khairat sun dauki maganar very serious dan haka ruwa a jallo ake neman sadiq. Charges dinsa suna da yawa, akwai trespassing tunda ya shigar musu gida ba tare da izinin su ba, ga kidnapping tunda basu yarda cewa ita ta bishi ba sun barshi a cewa sace ta yayi, sauran changes din kuma sai an ganta an ga a halin da take ciki, kuma sarki Abdallah ya tabbatar suna ganinta da baby zasu kara da raping da forced marriage, a takaice indai suka kama Sadiq to sai ya biya da ransa. Sarki Abdallah kuwa is not ready to give up his son, tunda dai aikin gama ya riga ya gama. Ya kira Sadiq yayi masa bayanin duk abinda ake ciki, Sadiq ya daga kafada yace "they can't catch me now" sarki Abdallah ya girgiza kansa a ransa yana cewa 'ta yaro mai take bata karko, kuma komai nisan jifa kasa zai fado'. A bangaren khairat kuwa kullum tana tuna iyayenta amma sai tayi sauri ta kawar da tunanin daga ranta, saboda tasan haduwa dasu yana nufin rabuwa da Sadiq da kuma Little Love dinta, wanda bata jin zata iya hakan. Sarki Abdallah yasan tabbas iyayen khairat zasu gano inda take wata rana za kuma su zo neman ta, dan haka kullum yana cikin tararradin zuwan nasu.
Iyayen Khairat basu samu nasarar gano inda take ba sai da Sultan ya shekara biyu a duniya, lokacin shekarar ta kusan uku rabonta da gida. Da daddare suka iso, babanta mahaifi da kanin babanta, a fusace suke gaba dayan su, tun daga bakin gate da suka ce mai martaba sarki suke nema, aka gaya mudu ya kwanta bacci suka ce basu damu ba. Ganin cewa ba kananan mutane bane ya saka daga bakin gate aka yo waya cikin gida aka fada, sarki Abdallah yana ji yasan ko su waye. Da sauri ya fita, yana ganin idan aka bi abin a sannu za'a iya samun maslaha. Amma yana zuwa ya fahimci babu maslaha, dan sun dauki zafi sosai, saboda abin ya bata musu rai da yawa, domin khairat tana daga cikin yara masu tarbiyya a zuri'ar su, wannan nema dalilin da yasa aka barta ta tafi karatu England, suna ganin duk yaron da har ya iya ya hure wa khairat kunne har ta juya wa iyayenta baya to lallai yafi shaidan shaidanci, cewa sukayi sadiq is a devil kuma ya kamata ayi eliminating dinsa a society, bai kamata ace wai shine crown Prince din da zai jagoranci al'umma ba. Sun dau alwashin cewa sai sunyi hanging dinsa sun nuna wa duniya yadda mulki yake a Nigeria, in dai ire iren su ne shugabannin Nigeria to ya kamata a dau mataki a kai. Wannan maganar ta bala'in bata ran sarki Abdallah, dan shi yana ganin cewa dansa ba mutumin banza bane ba, dan duk a cikin 'ya'yansa yafi na'am dashi, his only fault is falling in love with a wrong girl, amma kuma mutane ba zasu duba cewa the girl lead him on ba, in irin wannan case din ya faru koda yaushe laifin namiji ake gani ba'a duba macen, da bata bashi fuska ba da ba zaiyi hakan ba. Da aka taso abdallah da khairat basu san me yake faruwa ba sai da suka shigo gurin tukunna, Khairat da gudu ta juya zata koma uncle dinta ya damketa, kuka take yi kamar ranta zai fita tana kiran sultan da sadiq. Da kyar aka samu masu rike Sadiq saboda neman zauce musu yayi. A lokacin Yaya ta shigo da Sultan ya hannunta wanda bacci yake yi hayaniya ce ta tashe shi, ita Yaya ta shigo da Sultan ne wai tana ganin kamar in suka ga dan zasu hakura su bar masa uwarsa amma sabanin haka, suna ganin sultan suka gane dan Khairat ne dan haka baban khairat yace shima Sultan din tafiya zasuyi dashi, ai Islamically da na uwa ne har sai ya girma sannan zai zaba, wannan kam sarki yace ba'a isa ba, da kansa ya karbi Sultan wanda ya fara kuka ganin ummeen sa tana kuka, Sarki yace babu wanda ya isa ya karbi Sultan, dole suka hakura saboda an fi karfin su. Aka uncle din Khairat ya dauke ta ya fita da ita tana ihu tana kiran Sultan wanda shima kukan yake yana kiran Ummee na, duk da baisan me yake faruwa ba, da sauri sadiq ya kwace daga rikon da akayi masa ya bisu har wajan mota yace "Khairat, I will come for you, no matter what, no matter how long" a take babanta ya juyo ya dawo gaban sadiq yace "then I will hang you, If you ever step on Saudi land, I will hang you" daga haka suka ja mota suka tafi.
Tashin hankali ba'a saka masa rana, inda Allah ya rufa asiri ma da daddare ne duk gidan kowa bacci yake yi. Da kyar aka mayar da Sadiq daki sarki ya saka akayi masa allurar bacci, amma har yayi baccin yana rantsuwa sai yaje ya karbo matarsa. Sultan kuwa bai koma bacci ba dan gaba daya ya rikice shi ummeen sa da daddyn sa. A ranar sarki Abdallah bai koma bacci ba shima, yana lissafin abinda ya kamata yayi. Duk da yasan cewa gaba da gabanta amma kuma ya tabbatar ba zasu iya taba Sadiq a Nigeria ba, amma yana shiga saudiyya ya zama nama. Sannan kuma ya tabbatar cewa sadiq sai yaje.
Tunda assuba ya aika a kirawo masa babban malamin sa da yake saka yayi masa addu'oi idan wani abin ya shige masa duhu a harkar sarautar sa ko kuma a harkar cikin gidansa. Malamin yana zuwa sarki Abdallah ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki bai boye masa komai ba. Malamin yayi shiru yana tunani sannan yace "to yanzu Allah ya taimaki sarki mai kake so ayi?" Sarki yace "so nake idan da wani sirri da kake dashi wanda zaka cire masa ita daga zuciyarsa kwata kwata ya manta da ita" malamin yace "akwai Allah ya taimake ka, za'a iya yin hakan. Amma kuma ran sarki ya dade akwai da a tsakanin su, idan an mantar dashi uwar shi kuma dan fa? Duk sanda ya kalli dan dole ya tuna da uwarsa, musamman ma da yake dan da uwar suna kama" sarki ya danyi tunani kadan sannan yace "to ya kake ganin za'ayi? Malamin yace " za'a iya raba su din kamar yadda ka bukata amma kuma ina tsoron abin zai shafi yaron. In akayi aikin, adadin soyayyar da uban yake yiwa dan zai juye ya koma kiyayya. Zai zamanto kamar mun raba da da ubansa ne Allah ya taimake ka, ina tausayin yaron tunda kaga yanzu babu uwa kuma azo ace uba yana tsanarsa ai abin zaiyi masa yawa, tarbiyyar sa nake tunani" Sarki Abdallah ya daga kansa sama yana tunani. Tabbas in aka raba Sadiq da Khairat an shiga rayuwar Sultan. Amma kuma in ba'a raba su bafa? Ya lissafa abubuwan da suke at stake, na farko rayuwar Sadiq din gabadayanta, Sadiq shine sarki yake sa ran zai gaje shi, shine yake sa ran ko bayan ransa zai rike gidan, zai rike sarautar kuma zai rike al'ummar da suke karkashi sa baki daya, ba rayuwar Sadiq ce at stake ba, family name dinsu da family future dinsu gabadaya is at stake, ba family dinsu kadai ba, hatta martabar musulmin Nigeria gabadaya is at stake, ba musulmin Nigeria kadai ba, ita kanta

Please Login or Register in order to submit comment