Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje, ko ba'a gaya min ba na san Sultan ne, bansan lokacin da naje bakin gate ba kawai nima gani na nayi a gurin, motar Sultan na gani ta daki bishiyar da take opposite din gidan mu, ji nayi tamkar zuciya ta ta fado kasa, ina ganin masu gadi suna tafiya gurin amma ni ji nayi kamar an daskarar dani, ga mamaki na sai naji ya yi wa motar key yayi reverse da ita tare da tarwatsa mutanen da suka tafi kayo masa dauki, gaba daya gaban motar yayi damage amma a haka ya sake figarta ya yau titi. Yana tafiya masu gadi suka fara surutu, 'wai yaron nan me yake kawoshi unguwar nan ne kwanannan? Kar fa yazo ya tattaka mana yara a banza kuma babu mai daukan mataki a kansa" ni dai jiki a sanyaye na koma gida. Sai da na kama hannun kofar shiga palo sannan na tuno da ya Habeeb da kuma alkawarinsa na gaya wa mommy. Ga mamaki na sai naji babu wani tsoro a zuciya ta, gwara a yi ta ta kare kowa ma ya huta, dan ni yanzu ban damu da kome za'ayi min ba, nafi damuwa da halin da Sultan yake ciki, I fear he might hurt himself, ni kuwa nasan ba za'a taba yimin wani physical damage ba. Na murda kofar na shiga da sallama, babu kowa a palon sai ya Habeeb, fuskarsa sam babu rahama a cikin ta, kallo daya nayi masa nayi hanyar kitchen, haushinsa nake ji sosai duk da cewa deep down nasan ba laifin sa bane ba laifi nane, he was only trying to protect me. A kitchen na samu Asma'u, cook din gidan nace "Ma'u ina mommy?" Tace "Mommy taje unguwa, lokacin kina gurin bakon ki, tace in gaya miki sai dare zata dawo" banji dadi ba cos I don't want to delay this any longer. Na sake fito wa na wuce ta gaban yaya Habeeb na hau stairs din part dina. Direct balcony na wuce na saka kujera na zauna. Kamar yau ne na tsaya a gurin nan ina kallon Ibrahim ya fita daga gidan nan ruwan sama yana dukansa. Can't believe it has already been six years. History is repeating it self today. Amma yanzu a shirye nake, I am no longer sixteen years old, I am twenty two. Yanzu ba yarinyar nan bace da ta gama secondary school, wannan double degree ne da ita a second best university in the world. Ba wai zama zan yi in jira abubuwa suke faruwa ba kamar yadda na zauna nayi ta jiran Ibrahim, this time I am going to make things happen. Tashi nayi na koma daki na dauko laptop dina na kunna, email na shiga na rubuta wa daddy sako kamar haka "please daddy check this out" sai nayi masa attaching da duk rubuce2n da nayi akan sultan, na tura masa. Nayi missing Hafsat, da at least in na gaya mata zan dan samu sassaucin radadin da ziciya ta take yi. Na dauko wayata nayi dialing number din sultan, matar mtn ce ta fara yi min bayanin is switched off. Wani murmushin takai ci nayi, exactly haka nayi ta kiran Ibrahim is switched off, it is funny sometimes yadda rayuwa take zuwa wa mutum. Wani tunani ne ya fado min, this is my chance na ganin sultan in tabbatar masa da cewa abinda ya dauka ba haka bane, and most importantly to find out if he is Ok. Dan nasan mommy tana shigowa gidan nan suka hadu da yaya Habeeb to ni da in kara fita sai wani ikon Allahn kuma. Kuma nasan duk bayanin da zan mata ba zata fahimta ba da taji bayanin abbakar din da nake gaya mata Sultan ne shikenan zata toshe kunnuwanta daga dukkan baya ni na. Amma still it will be better in ni na fara gaya mata. Na dauko waya ta nayi dialing number ta, ta dauka suna ta hayaniya a gurin tace "Moon ya akayi ina gurin taro ne, akwai wani abu ne?" Nace "mommy akwai maganar da nake so muyi ne" tace "am very busy yanzu, can't it wait sai na dawo?" Nace "Ok mommy, sai kin dawo din" na ajiye wayar a raina nace "why is everyone not available when I needed them the most?" Ina daki har aka kira magrib ina ta kiran sultan har yanzu switched off, in ma nace zan fita neman sa bansan inda zan same shi ba, to ko gidan su zanje? Tunda gidan babba ne maybe har in fito babu wanda zai san na shiga? Amma fa ni ban taba shiga palace ba, in naje ma bansan inda zan dosa ba. Na tashi nayi alwala nayi sallah na zauna ina adduoi na naji karar wayata, ban dauka ba sai da na kammala, na dauka baga bakuwar number, ina kokarin dialing wani kiran ya sake shigowa, na daga da sallama. "Maimunatu Amir ne, kina ina?' Ji nayi gaba daya yawun bakina ya kafe nace "Amir ina Sultan?" Ya sake cewa "kina ina?" Nace "ina gida, me yake faruwa?" Ya danyi shiru sannan yace "ina gida dazu wani friend din mu ya kirani yake gayamin yaga Sultan a bar, he seems to be injured, to shine naje gurin na same shi, he is injured kuma yaki tashi in kaishi asibiti" da sauri nace "how bad is it?" Yace "not that bad, kawai dai kafarsa ce, kuma tana bleeding har yanzu. Sultan taurin kai ne dashi, ban sani ba ko ke in kika yi mishi magana zai tashi, he has been drinking also" a raina nace "nasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya" ya katse min tunani na da cewa "can you come, please?" Na ce "of cause I will come. Kuna ina?" Yayi min kwatance, nace amma kuma fa ban iya driving ba, bana so kuma in dau driver, ko kuma zuwa zakayi ka dauke ni?" Yace "alright gani nan zuwa" tashi nayi da sauri na chanja kaya zuwa wani material simple doguwar riga, nayi rolling veil sai kuma na saka dogon jihab, na sauka kasa, yaya Habeeb ya tashi daga inda yake dazu ina jin masallaci ya tafi, na samu Asma'u tana shirya dining nace mata "Ma'u kinga kaina ne yake ciwo, na sha magani yanzu zan kwanta, please in mommy ta dawo ki gaya mata ina kwance banjin dadi" da sauri tazo ta dafa goshina, "oh oh, sannu mai sunan daada, gashi nan kuwa jikin ki ya fara zafi, Allah ya sawake" nace "Ameen" na koma kamar na hau sama sai nabi ta kofar baya na fita, ina fita Amir ya kirawo ni yace gashi ya zo, na zagaya ina buda securities, dama in daddy baya nan basu da yawa, guda biyu kawai na hango tare da baba Habu a can gefe a zaune, sai da na zagaya ta side din da ba zasu ganni ba sannan na shige seat din baya na durkusa a kasa yadda wanda yake waje in dai ba lekowa yayi ba ba zai ganni ba. Ina jin baba Habu yana tambayar Amir "har ka karbi sakon?" Shi kuma yace masa eh sannan muka fita. Sai da muka hau titi sannan na zauna sosai ina tambayar Amir "ya jikin Sultan" ya yi murmushi mai sauti yace "He is lucky to have you. Da sauki jikinsa, so nake kawai ya tashi in kaishi ayi dressing kafar kar ciwon ya zama infected kuma a tsayar da jinin" nayi shiru ina lissafi, wannan fitar da nayi ni kaina nasan I am playing a very dangerous game, saboda na bawa mommy damar yadda da duk abinda za'a gaya mata, amma kuma bazan iya barin Sultan ba alhalin yana bukata ta. Wani hotel muka shiga, sannan muka bi ta bayan building din muka tsaya a wani karamin packing space. Ga wanda bai san gurin ba zai dauka babu komai a gurin, amma sai naga mun doshi wata kofa, Amir yayi knocking wani ya leko ya kare mana kallo sannan ya bude muka shiga, wani dogon corridor muka bi muka sake shiga wata kofar sai gamu a wani katon guri. Ga mutane nan birjik kowa yana abinda yaga dama, kowa ka gani da kwalba da cup a hannunsa, wasu da 'yammata wasu kuma su kadai. Fitulun gurin duk dim ne marasa haske. Oh ni maimunatu wai yau nice a gidan giya? Lallai soyayya babu abinda bata sakawa.

Tun kafin mu karasa inda yake na gane shi duk kuwa da juya bayansa da yayi yana kallon bango, light blue din wandonsa yayi staining da jini, a hankali na karasa na jawo kujerar kusa dashi na zauna. Da sauri ya juyo ya kalleni sai kuma ya dauki kofin gabansa ya shanye abinda yake ciki sannan yace a hankali "damn you Amir" ya janyo kwalbar da take gefensa ya sake cika kofinsa sannan yace ba tare da ya kalleni ba "what are you doing here, this is no place for a girl like you" nace "it is also no place for someone like you, dan kai nazo kuma na tabbatar ba zaka bari wani abu ya same ni ba" murmushi yayi me kama dana takaici sannan yace "what do you want?" Nace "first ina so in gaya maka cewa I love you, all of you, sannan na biyu ina so in gaya maka cewa wannan mutumin da yake zaune a gaba na yana shan alcohol is not sultan, it is what you think you are but it is not who you really are" yace "ta ya akayi kika sani? Kinfi ni sanin kaina ne? This is what I am, this is what I have always been" na girgiza kaina nace "no, ba haka bane, wannan shine abinda mutane suka saka ka mayar da kanka" ya danyi shiru sannan ya sake daga kofin gabansa yayi masa kurba daya yana yamutsa fuska. He looks calm, so peaceful, fuskarsa sam babu damuwa, muryarsa kuma a nutse yake magana. Sai da ya ajiye cup din sannan yace "kin san wani abu?, ranar da muka hadu dake na dauki alkawarin bazan taba barin kisan ina shan giya ba, ballantana har ki ganni ina sha" ya daga kafada yace "I was a fool, ban taba wishing for something na samu ba amma na saka ran cewa zan samu wannan wish din. Now here we are" na hadiye wani abu da ya tsaya min a makogwaro nace "wannan bai chanza komai ba a tsakanin mu, kamar yadda nake so abinda ya faru dazu kar ya kasance ya chanza wani abu a gurinka" ya juyo yana kallon cikin idona yace "idan da akwai wani abu da nake da tabbas dinsa a rayuwa shine I will love you, till my dying day. Amma nasan you are just another dream a gurina, and my dreams never come true" nace "wannan mafarkin zai tabbata Sultan, I will fight for us, amma ina bukatar kaima kayi fighting for us. Abinda zaka fara yanzu shine ka ajiye kwalbar hannunka, ka tashi muje a duba kafarka" bai ajiye dinba kuma bai tashin ba, har zan sake magana sai yace "me yasa baki gaya min zancen project dinki ba?" Na sunkuyar da kaina kasa na fara magana "lokacin da aka bani project din ban sanka ba, daga baya muka hadu dakai, ranar da ka fara kaini gidan su Amira muka biya ta wata unguwa har na samu labarin orphanages din da ka gina kuma kake running da kuma irin taimakon da kake wa marasa hali sai naga kafi fitting topic dina, a lokacin na fara rubutu na, I was already in love with you then, nayi tunanin yin rubutun akanka zai sa in kara fahimtar ka sosai, I never meant to hurt you. Ina ta so in gaya maka kullum but ina tsoron yadda zaka dauki abin. You are not an easy person, you easily lost your temper" ya dakatar dani yace "have I ever loose my temper with you?" Na girgiza kaina dan ko mugun kallo Sultan bai taba yi min ba. Na cigaba "tun ranar dinner din Hafsat da ka je Ya Habeeb ya gan mu tare yayi min warning kar ya sake gani na da kai, a lokacin nace masa 'u are not my type' saboda ni kaina a lokacin bansan zan so ka ba saboda a lokacin ban sanka ba. A England ma ya sake ganin mu a Oxford, he threatened me cewa zai gaya wa mommy kuma nasan in har ya gayawa mommy ba za'a barni in sake ganin ka ba. Na ce masa 'I was using you for my project' ne saboda in kara samar mana lokaci together" sai kuma na kasa ci gaba da maganar na rufe fuskata da hannuna ina hawaye sanin lokacin da na samar mana ya kare yau, dan maybe already mommy ta koma gida by now, maybe already sunyi magana da yaya Habeeb. Bai rarrashe ni ba sai ya sake kiran bartender ya karo masa wata kwalbar, yana ajiyewa na dauke na ture ta gefe nace "please Sultan me kake son yi ne? So kake ka kashe kanka?" Idanunsa sunyi jajur, amma abin mamaki banda jan idon babu wani abu da zai nuna maka cewa a buge yake, he seems totally in control of himself. Bai karba ba ya kara zama yace "rannan na miki alkawarin zan baki labarin yadda na far shan giya" ban amsa ba shima bai jira amsa ta ba ya cigaba da magana "ina da shekara goma kakana ya rasu, bayan an yi nadin sarauta babana, Hajiya da sauran siblings dina suka dawo palace, su kuma su yaya da sauran matan kakana sai akayi musu sababbin gini a bayan palace din suka koma can. Ina jin labarin tarewa a sabon waje na fara tattara kayana nima saboda nayi zaton dani za'a tafi, tunda dasu yaya na saba, ban saba da Hajiya da su Abbas ba. Amma ranar tarewa tana zuwa sai akace ban dani, wai Hajiya tace a barni saboda in saba da 'yan'uwana, nan na dasa rigima lallai ni ba zan zauna dasu ba. Sai da Yaya ta kirani ta zaunar dani tayi min bayanin cewa an ce in zauna ne saboda in saba da babana nima yake kula ni kamar yadda nake so, ina jin haka na fara murna nima zanyi family. Sai daga baya na fahimci ba haka bane, ba wai rashin sabo ne ya saka baya kulani ba a'a ni din ne baya so. Gaisuwata da safe baya amsawa, baya cin abinci dani kamar yadda yake ci da abbas, ko dariya yake dana zo gurin zai bata rai. A lokacin abinda ya fi komai bata min rai shine, kullum in zaije fada zai saka a shirya Abbas, a saka masa manyan kaya da rawani da alkyabba, su tafi tare, amma ni bai taba ko tunani zuwa dani ba. Kullum in aka dauki abbas aka barni sai na hargitsa gidan nan dan bacin rai, in farfasa glasses din windows da duk abinda tsaho na zai kai, next thing duka ne zai biyo baya, ko kuma a sakani a daki a kulle ni. In nayi buge2na na gaji sai in zauna in hada kai da gwuiwa inyi ta kuka, I am four years older than Abbas, ni a gani na ni ya kamata baban mu ya kai fada ba Abbas ba, duk sanda aka saka mishi kayan sai inyi ta sha'awa dan nawa wanda nake sakawa sanda kakana yana da rai ma duk Hajiya ta karbe ta bashi tace min sunyi min kadan za'a sayo min sababbi, har yau ba'a sayo min ba. Wata rana ina ta gursheken kukana Hajiya ta aiko akayi kirana dakinta, cikin bedroom dinta, ta tambaye ni tace in gaya mata me nake so, nace mata inaso babana ya soni kamar yadda yake son Abbas, tace min to zata bani maganin da zan ke sha wanda zai saka ya soni fiye da Abbas din ma. Ta dauko shi a kwanba ta zuba min a kofi tace in sha, na dauka da murna ta na shanye, babu dadi amma haka nasha saboda ina son Takawa ya soni, banji dadin taste din ba amma naji dadin feeling din da ya saka naji, zuciya ta naji tayi min dadi, babu bakin ciki ko bacin rai sam, sai wani nishadi da nake ji, I felt very calm and happy. Tun daga nan kullum sai ta aiko naje nasha, ni kuma ina jin dadin yadda nake ji in nasha din, daga baya ma sai ya zama ni nake zuwa da kaina in raina ya baci ince ta bani magani insha, tace min inyi mata alkawarin ba zan gayawa kowa ba ni kuma nayi mata. A hankali na fara zama less active, kullum sai bacci ko kuma in zauna inyi ta kallo ko tv game, wanda da ba halina bane cos I was very energetic child, Amir ne ya fara lura sai ya gayawa Hajiya yace akaini asibiti fa, bani da lafiya tace masa to amma yaga shiru ba'a kainin ba, hakan yasa ya shirya ya tafi gurin yaya ya gaya mata cewa bani da lafiya kuma anki kaini asibiti, babu shiri yaya ta taho cikin gida tazo ta tarar dani ina bacci, jikina babu zazzabi amma nayi weak babu karfin da ta sanni dashi da. Nan ta samu hajiya ta tambaye ta sai tace ai na samu kulawa ne da tarbiyya shi yasa na nutsu, ita kam yaya bata yadda ba saboda tasan yaro mai fitina daban yake da yaro quite, I was never quite and calm dan haka lokaci daya ba zan zama ba. Ta daukeni ta tafi dani gurinsu da sunan zanyi week end acan, kwana na daya na rikice musu suka rasa kaina, daga baya dai nace ni aje gurin Hajiya a karbo min magani na, nan yaya ta saka ni a gaba da tambayar wanne irin magani har dai na gaya mata. I was young then, ba zan iya tuna duk abubuwan da suka faru ba amma dai nasan an yi rigima sosai da yaya, ni dai rigima ta daya ce, a bani magani na. Hajiya ta daina bani, but I was already addicted to it. Ita kadai take calming dina down duk sanda nake tantrums dina. It still does. Duk sanda raina ya baci ita nake sha inji zuciya ta tayi sanyi. Ba abinda rannan kike cewa bane rannan, it doesn't make me do things, it calm me down and stop me from doing things. A lagos kuma su masu kula da mu su nake bribing su kawo min, wani lokacin ma da kansu suke bani saboda in nayi bacci shikenan sun huta da fitina ta. Sanda aka kaini America kuwa tamkar an bani ticket ne, hankali na kwance babu me cemin kar inyi. Sai da na shiga university sannan na fahimci tana hanani karatu, ni kuma a lokacin ina son karatu saboda in faranta ran babana. A lokacin na fara ragewa dan kaina, ya zama bana sha sai in na zama really frustrated yadda ba zan iya controlling anger dina ba. Bayan na hadi dake kuma I cut it down to zero, saboda in raina ya baci da munyi waya dake zan manta da bakin ciki na, I returned to it sanda muka rabu a America but tunda muka dawo ban kuma sha ba sai yau." yayi shiru yana kallon cup din hannunsa kamar mai studying dinsa.

Na saka hannayena na juyo da fuskarsa gurina, still ban cika fuskar ba nace "alcohol doesn't give you calmness sultan, it makes you think it gives you calmness. Haka giya take, shi yasa take addiction ce, zata baka feeling din da kake so saboda ka cigaba da shan ta. Do you believe in destiny Sultan?" Bai bani amsa ba kallona kawai yake yi, nace "I know you do, I strongly believe that we are destined to be together. Zayed ya taba gaya min wata magana rannan wacce kuma na yarda da ita, yace people with good heart da suke suffering a rayuwa are destined for greatness, suffering din da suke yi is like a test da Allah yake musu dan yaga how good they are. Sultan I strongly believe that you are destined for something great" kallona kawai yake yi da jajayen idonsa, amsar daya bani itace "can I kiss you now?" a raina nace 'he is really drunk' a fili nace "no" ya daga kafada yace "OK" sai ya kifa kansa akan table din gabansa. It is time for me to get him out of here, na tabbata mommy ta dawo yanzu, hope dina kawai in taji bani da lafiya maybe ta bar maganar sai safe. Na fara waige waigen Amir wanda sai yanzu na tuna dashi, babu shi babu alamar sa, na bar waya ta a gida ballantana in kira shi, ina Amir when I need him the most? Na tambayi Sultan "ina wayarka?" Idonsa a rufe yace min "Amir" haka ne da ita muka yi waya da Amir. Nace "Sultan tashi mu tafi, am getting you out of here" ya dago kansa idonsa sun kara ja yace "can't stand" tashin hankali, ta yaya zan iya daga sultan, I really need to go back home kuma ba zan iya tafiya in bar sultan a haka ba. Dole somehow in fita dashi waje, fresh air zata danyi clearing head dinsa, daga nan sai in samar masa taxi a kaishi gida, nima kuma in nemi taxi zuwa gida. Na saka hannu a aljihunsa na dauko kudi, roll ne na 1000 notes, na dau guda biyu na mayar masa da sauran. "Sultan try standing up please" ya gwada, nasan kafarsa tayi tsami yanzu, da kyar ya dafa table din ya mike yana cije lebe, yanzu saura tafiya kuma, na a side din kafarsa mai ciwon na ce masa ya dafani mu tafi. Sai da muka fara tafiya sannan nayi nadama, he is very heavy, gashi duk ya sakar min jiki kaman ma naya sane. Sai na muka huta sau bixu kafin mu zo gate. Muna fita gate din na fara rarraba idon inda zanga taxi, nace "Sultan zan saka ka a taxi za'a kaika gida, inna je gida zan kira Amir in gaya masa ya kira doctor ya duba kafar ka sosai. Ana barin taxi ta shiga palace?" Uhmm kawai yace, good, tunda yana gane me nake cewa.

Wata mota ce ta wuce mu har na fara daga hannu sai na lura ba taxi bace na sauke hannuna. Har tayi gaba sai tayo baya kuma, good, maybe it's Amir, tayi packing a gaban mu aka bude kofar da sauri aka fito. "Moon? Is that you?" Na saki baki ina kallon me maganar, Munir. Na kasa rufe baki na ballantana in yi magana. Ya karaso gaban mu, da sauri ya toshe hancinsa. "Moon waye wannan? Me kike yi a gurin nan da daddaren nan? Are u drunk?" Tambayoyin da ya jero min kenan. Sai a lokacin na fahimci what we looked like, kusan rabin sultan a jiki na yake, gaba dayansa warin giya yake dan haka nima warin nake, yadda muke tafiya kuma babu wanda zai ce ba'a buge muke ba gaba dayan mu. A hankali nace "listen Munir, this is not what you are thinking" Sultan naji daga gefena yace "Munir? "



Episode Fifty one : Mommy

Nayi kokarin raba jikina dana Sultan wanda da kyar ya tsaya. Munir ya kara matsowa yana kare mana kallo, dogon hijab dina duk ya chukuikuye yayi squeezing yace "dama abinda kike aikata wa kenan shi yasa ko waya nayi miki ba kya dauka, haka ne fa ya saka na shirya na taho abujan da kaina dan inga me yake faruwa. Ashe abinda kike aikatawa kenan har ake yi min gorin baza 'a bani ke ba dan kin fini tarbiyya? Ina tarbiyyar take anan? I wish uncle Aliyu zai ganki a yanzu sai ya gane tsakani na dake wa ye marar tarbiyyar" da kyar na bude baki nace "Munir kar ka adar da batun da baka tabbatar ba, I was only trying to help him, shi kenan taimako kuma sai ya zama laifi?" Yace "waye shi? Menene tsakanin ki da shi?" Nace a fusace "what is your problem with that?" Sultan ne naji yace "I am her

Please Login or Register in order to submit comment