Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babi alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira, why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba. Ina zaune rike da kaina Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year ta turomin message tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, i can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Efi" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada. Yace "yes, na auri efi shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her, ba zaka bincika ba, ask around, ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look" Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yadda cewa it hurt me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened"
"Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I cannot stay away from you. I thought i was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, .nadabazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida kin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sanki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Kafin muje ibadan zazzabi ya sake rufe ni, da muka je sai mai motar ne ya karbi number din baba a wajena ya kira ya gaya musu halin da nake ciki, nan suka zo suka dauke ni sai asibiti, na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Hadiza, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it has something to do with you. Bayan na samu lafiya an sallamoni sai na yanke shawarar tafiya Lagos, da akwai wani uncle dina a can wanda kudin inheritance din mu yake hannunsa yana business dashi, mama taso ace na zauna a ibadan na nemi wani aikin amma naki, gani nake aikin government babu abinda zai kawo min. Ina zuwa lagos uncle dina ya fara koyamin harkar business, cikin 'yan watanni na koya sosai, ya dauki kudaden mu gaba daya ya bani na fara nawa daban. Duk abinda nake yi kowacce rana, kowanne hour, kowanne minute kowanne second kina cikin raina maimunatu. A lokacin na fara trying kiran number dinki da sabuwar number ta, at least duk da cewa ina ganin lokacin dawowata bai yi ba amma ina so in san ya kike, amma ga mamakina your phone was switched off, kullum na kira a kashe, bani da number din kowa kuma a gidan ku sai taki. Tun a sannan na fara zama very frustrated. A haka har shekara ta kusa ta zagayo. Ban wani tara kudin kirki ba amma bazan iya jure zama babu ke ba, a dole na fara shirin tahowa Abuja in neme ki. Kamar hadin baki, ina zuwa ibadan baba ya shigar min da maganar auren Efi, a take nace masa a'a, wannan ba karamin bata ran mama yayi ba, saboda bata taba zaton zan iya cewa da baba a'a ba, tunda ban taba ce masa a'a ba. Ta fara fada baba yace a tambaye ni uzuri na, nan na gaya masa maganar ki, na nuna masa sosai irin yadda nake sonki, shi kuma ya goya min baya yace inzo abuja muyi magana da daddy in ya amince sai inzo in fada su kuma sai suje ayi maganar manya. Washegarin da muka yi maganar dashi na taho Abuja, har a lokacin wayarki bata shiga. Nazo unguwarku naga gidan ku babu alamar movement kamar wancan zuwam nawa, bana son wulakancin securities din ku dan haka na tsallaka gidan opposite dinku na tambayi me gadin kuna nan kuwa? Sai yace min ai kun tashi daga kasar ma gaba daya, sosai hankali na ya tashi, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa wayarku bata shiga. Bansan a gurin wa zan samu labarinki ba ballantana contact dinki. Na tuna da kawarki Amira itama a abuja take da zama kuma nasan tabbas zan samu labarinki a gurinta. Na tafi tsohuwar makarantar ku gurin principal na roke ta ta nemo min file din Amira, a ciki na samu address din gidan su, ina zuwa gidan su na aika a kirata aka cemin ta tafi makaranta, anan na zauna nayi ta jiranta har magrib sannan ta dawo. Sosai tayi mamakin ganina a kofar gidan su, kuma tayi murna sosai. Sai yanzu na fahimci dalilin murnar ta, ta dauka gurinta naje, ni na manta ma da cewa tana da wani feelings for me, na dauka tunda na gaya mata baki da baki cewa bana sonta shikenan magana zata wuce. Bayan mun gaisa ta kawo min ruwa nasha sai na gabatar mata da abinda ya kawo ni gurinta, cewa ina neman hanyar da zan same ki ne ko kuma number dinki. Abinda tace min shine 'au baka sani ba? Na dauka ta gaya maka ai' nace mata 'me fa?' Tace 'zancen auren ta mana, ai ranar da kaje gidan su Daddy n ta ya ganka, kana tafiya ya tambayeta waye kai ta gaya masa yace babu ita babu kai, shi ba zai bawa bayarabe 'yarsa ba, data takura ta daina cin abinci ta daina yiwa kowa magana sai ya dauke ta ya kaita 'yalleman, bata fi two weeks acan ba aka hada auren ta da wani cousin dinta a can' ji nayi tamkar ta zuba min fetur a jiki na ta kyatta a shana. She is your best friend, how can I not trust her words? Besides, nasan dama ba kowanne bafulatani ne zai yadda ya bawa bayarabe auren 'yarsa ba. Ganin irin yadda hankali na ya tashi ne yasa ta fara lallashina, tace in ban yarda ba zata kawo min sample din IV daurin aurenki kafin in bar gari. Ta gaya min cewa duk 'yan gidan ku suna England yanxu ke kuma kina 'yalleman. Anan ta karbi number ta da niyyar zata kawo min IV din. Daga gidan su Amira da kyar na samu taxi ta kaini hotel na kwana, ranar nayi kukan da ban taba yin irinsa ba a rayuwata, na tausaya miki na tausayawa kaina saboda ina ganin soyayyata ce ta jawo miki aka miki auren dole aka kaiki kauye aka katse miki karatun ki, alhalin ga 'yaruwarki can a England tana karatun ta. Washegari da ciwo na tashi dan ko fitowa ban iya yi ba har Amira tazo da yamma ta kawo min IV din, naga sunan ki da sunan wani Abdulaziz a matsayin mijin. Ganin ina kokarin in mutar mata a hannu yasa ta kira mai taxi suka kaini asibiti, a take aka kwantar dani dan sosai nake neman rasa numfashina. Kwana na uka a kwance Amira tana ta dawainiya dani, ranar dana warke nayi mata godiya nace zan tafi, amma dan Allah she should at least call you and let you know cewa I came back like I promised. Ina komawa ibadan na yiwa baba karya nace na samu Daddy yace yanzu kina karatu in bari sai kin gama tukunna. Mama tana gurin ashe ta gane karya nake yi. Rashin lafiyar ce dai bata barni ba dan tunda na koma ina kwance. Ban san ya akayi mama ta bincike kayana taga IV din da Amira ta bani ba. Bata ce min komai ba har na samu sauki na koma lagos. Ashe bayan na tafi ta nuna wa baba IVn ta gaya masa cewa yarinyar da nake so anyi mata aure, kuma wannan shine sanadin duk wannan ciwowwukan da nake. Ba tare da baba ya sake bi ta kaina ba ya yanke shawarar daura min aure da efi, a cewarsa macece kadai zata saka in manta da ke. Sam babu wanda ya gaya min labarin za'a yi min aure har aka daura ban sani ba, sai da uncle dina na Lagos ya je daurin auren ya dawo sannan ya kira ni ya gaya min, ranar naga tashin hankali, na gaya masa sunyi mistake, ni bana son efi ba zan iya zaman aure da ita ba dan a matsayin kanwa na dauke ta. Ya gaya min lallai in shirya in tafi ibadan inje ayi biki in taho da amaryata. A dole na shirya amma maimakon in tafi ibadan sai na zarto Abuja, direct gidan ku naje, wannan karon na tarar gidan da alamar mutane a cikin sa, ban shiga ba wannan karon a waje na tsaya sai da wani yaron gidan ya fito sannan na tambayeshi ko kina nan? Sai ya ce min ke baki zo ba, amma sauran mutan gidan sunzo, abinda na fahimta a lokacin shine mutan gidan sunzo daga England ke kuma baki zo ba tunda kina 'yalleman. Wannan shi ya goge min duk wani sauran doubts akan auren ki. Na tafi gidan su Amira, wannan karon a gida na same ta. Na gaya mata yadda mukayi da yaron gidan ku tace min eh ke kina 'yalleman, 'yan gidan ku ma sunzo suna ne saboda haihuwar da kika yi, har ta nuna min hoton babyn a wayarta. Ta gaya min cewa kunyi magana da ke kince mata in na sake zuwa ta ce min I should move on, ke kinyi moving on nima I should do the same thing. Zancen haihuwarki ba kara min tayar min da hankali ya kuma yi ba dan ina zuwa ibadan na zube wa mama a tsakar daki, mama hannu ta dora aka tana rusa kukan ta shiga uku danta zai mutu. Babane ya saka ni a gaba da nasiha da addu'a da fada har na dan samu na saki raina. Nan aka fara shirye shiryen biki. Sosai baba da mama suka kashe kudi a bikin nan a niyyarsu ta son suga sun faranta min rai. 'Yan uwana duk sun zo daga side din babana, side din baba da kuma side din mama, kowa was there to make me happy. Bana so in nuna musu kamar wahalar banza suke ji dan haka na ware sosai tamkar na karbi auren har aka yi biki aka gama. Bayan an gama biki ne mama tace mu tafi Lagos tare da efi sai nayi mata bayanin cewa bani da gida a lagos nima a gidan uncle dina nake, amma tunda a lokacin kudi suna shigo min sosai, inna koma Lagos zan sayi gida sai inzo in dauke ta, a haka muka rabu dasu na tafi Lagos. Na sayi gidan kamar yadda nace amma fir naki dauko efi. Nace ni bana son in ci zalinta kuma ni bazan iya zaman aure da ita ba. Sai da Efi ta shekara guda da aure akan ta amma tana zaman gida. Kwata kwata ma na daina zuwa ibadan saboda kar ayi min maganar tafiya da ita. Gashi arzikina kullum karuwa yake yi. Rannan kawai akayi min waya cewa baba babu lafiya, ba shiri na tafi ibadan, kwana na daya da zuwa Allah yayi masa rasuwa. A lokacin nasan mutuwar uba tunda sanda mahaifina ya mutu bani da wayo. Bayan komai ya lafa nace zan tafi, mama ta saka ni a gaba har da kukan ta akan lallai in tafi da matata, yanzu bata da kowa, ba uwa ba uba, ga mijin da dashi da babu duk daya, duk ta lalace ta fita daga haiyacinta. Kukan da mama tayi min ne ya saka na tafi lagos da efi".
Muna zuwa lagos na kaita gidan uncle dina na kama gaba na, ban kuma komawa ta kanta ba. Muna yawan yin waya da Amira, nakan kira ta inji ya kike da su Hafsat, kullum tana ce min lafiya lau kuke, tace hankalinki a kwance yake yanzu baki da wani problem. Kullum tana min maganar ya kamata in ajiye maganar ki a gefe in san me nake ciki a rayuwa amma sam na kasa. Ina waya da ita ne saboda she was the closest thing i have to you. Rana daya kawai sai ga mama tazo Lagos, nan naga bacin rai a gurinta data fahimci abinda na aikata. Efi cewa tayi ta hakura da auren, ita a raba auren kawai duk son da take yi min ta hakura. Mama kuma tace ban isa ba tunda bani na haifi kaina ba. Dole efi ta dawo gidana ta tare. Mama ma anan ta zauna tare da mu ta saka mu a gaba" yayi shiru for the first time tunda ya fara magana. Na kalleshi naga yana kallon can gefe. Ya cigaba da cewa "a duk zaman da muka yi da efi bazan iya tuna ranar da na ganta cikin farin ciki a dalili na ba, ta samu gangar jiki na, amma zuciya ta da ruhina ni kaina basa tare da ni ballantana in bata. I kept blaming iyayen mu da suka hada auren duk da cewa sun san bana sonta. Ba kowanne namiji ne zai iya rayuwar aute da matar da baya so ba. Bamu dade tare ba ta samu ciki, cikin yana girma mama ta dauko ta suka dawo ibadan ni kuma nayi zamana a lagos. A ibadan ta haihu, anan kuma Allah ya karbi ranta a gurin haihuwa. Allah yaso zamuyi sallama nazo kawo musu kayan da mama tace in siya, ina xuwa ta fara labour na kaita asibiti, tana haihuwa jini ya balle mata wanda shine sanadin ta. Inda Allah ya taimake ni na nemi gafarar ta kafin ta mutu da nasan alhakin ta bazai taba barina ba. Bayan na koma lagos naji duk zaman garin ya ishe ni, da kadan na fara sayar da business dina ina dawowa nan garin, a hankali na gina wannan gurin na sayi gida sannan na dawo garin nan da zama. Bayan dawowa ta garin nan na fahimci cewa Amira still have something for me sai na yanke alakar dake tsakanin mu saboda ban taba jin son ta a raina ba, ban taba jin son kowacce mace a raina ba bayan ke. Ina yawan bin hanyar gidan ku with hope wai ko wata rana zan ganki koda kuwa daga nesa ne. Rannan kawai naje unguwar sai naga gate din gidan a bude, kamar ana biki a gidan. Nayi packing daga dan nesa ina jin dadin maybe zan ganki. Na kira Amira a waya nace mata nazo gidanku na tarar ana biki, sai tace min bikin Hafsat akeyi. Ta fito ta same ni tace ta gaya miki nazo kince please in tafi kar mijinki ya ganni, tace kince you are happy with your life and I should leave you alone" ya sake yin shiru yana kallona, fuskarsa tana nuna irin bacin ransa. Ya cigaba da cewa "tun daga ranar ban sake zuwa gidan ku ba. Nayi concentrating akan business dina. Amira tasan ina garin nan amma bata san me nake yi ba, she had no idea nan guri nane, dan haka da kuka zo bata taba tsammanin zata ganni anan ba"
Tun da ya fara maganar nake hawaye har ya kammala, ya tashi ya je gurin water despenser ya debo ruwa a cup ya dawo ya miko min na karba na shanye ina jin dadin yadda sanyin ruwan yake sanyaya zuciyata. Maimakon ya zauna a kujerar daya tashi sai ya hau kan table din gabana ya zauna, exactly yadda yake yi sanda muna makaranta. Na dago kai na kalle shi, he was grinning from ear to ear. It is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Involuntarily na kai hannuna kan zoben Sultan na fara wasa dashi. A hankali Ibrahim yace "it is alright now, we are together now" a hankali na far girgiza kaina hawayen fuskata yana karuwa, ya saka hannu zai dago fuskata na matsa baya. Nace "married or not married, ba dai dai bane kake taba ni ba, ka sani kuma" yayi dropping hannunsa a sides dinsa, yace "bani naki labarin inji, what have you been doing all these years" a hankali na fara magana nace "I waited for you, for five years, I waited" yace "six, almost seven" nace "I met someone after five years of waiting for you" nayi shiru ina kallon yadda yanayin fuskarsa ya fara chanzawa, yace "what? Who?" Nace "it doesn't matter who" ya sauko daga kan table din ya koma wajan ruwa, this time kansa ya zuba wa yasha, sannan ya tari wani ruwan ya zuba a kansa, ya juyo yana kallona da wani yanayin da bazan iya fassarawa ba, nayi sauri na dauke kaina dan ba zan iya juran kallonsa a haka ba. Yana daga tsayen yace "do you mean to tell me that you are in love with someone else?" Na yi shiru ina jinjina kalmar love, in nace love sai inga kamar na rage darajar what I feel for Sultan, it is more than love, na gyada kaina a hankali nace "yes" da sauri ya karaso gaba na ya durkusa "maimunatu please, please don't say that, zuciya ta zata iya bugawa please" na runtse idona ina jin zafi a raina, I hate to hurt him like this amma dole in gaya masa gaskiya, nace "I loved you, but not anymore" ya mike da sauri ya fara safa da marwa a office din yana cewa "you don't mean that, dan dai bana nan ne, you still love me, i know you do, I just need you to give me a chance in dawo miki da soyayyata" ya sake dawowa gaba na "maimunatu please ki sake bani chance" na sunkuyar da kaina ina kallon zoben Sultan a raina ina ayyanawa idan da ace sultan ya san inda nake kuma yasan tare da wa nake, zai iya harbo igwa ta tarwatsa building din gaba daya, a hankali na sake magana nace "there is no time, bikina saura kwana goma" da karfi yace "what?" Na gyada masa kai, ya sake mike wa ya buga hannun sa a table din yace "NO" da dan karfi. "No Maimunatu, destiny brought us together today. Da Allah baya so mu kasance tare da ba zai kawo ki office din nan yau ba. Da in zamu hadu ma sai da auren ki tukunna. Please call off the wedding" na girgiza kaina da sauri nace masa "not possible. I can't do that. Ko da ma ace bana son wanda zan aura ai bani nake bada kaina ba, an riga an bashi ni, an gama komai, bazan taba zuwa in ce bana son auren sa ba. It doesn't work like that" ya sake tsugunna wa kamar zai dora hannayensa a kan lap dina nayi sauri naja kujera ta baya, ya dora hannayen aka, sannan ya shafo fuskarsa. Idonsa ya sauka akan zoben sultan da nake ta aikin murzawa. Ka kalle ni yace "his ring?" Na gyada masa kai, ya sake cewa "who is he?" Na sake amsa masa "it doesn't matter" kamar amsar tambayar sa sai waya ta ta fara kara, a tare muka kalleta, 'my sultan' a hankali ya furta "sultan" ban dauki wayar ba saboda bazan iya yin magana da Sultan a yanzu ba, har ta gama ringing ta katse ya sake kira, nasan halin Sultan in yaso abu, bazai daina kira na ba har sai na dauka. Na mike tsaye, Ibrahim ma ya mike yace "please don't go" na kalle shi for some seconds sai na juya zan tafi, hijab dina ne ya jawo wani frame din hoto daga kan table din ya fado kasa, na durkusa a hankali na dauki hoton ina kallo, wata yarinya ce zata yi shekara uku a duniya, naga fuskar Efi a fuskarta amma idon Ibrahim, she looks very cute a cikin English wears tana murmushin da yake bayyana cleft chin dinta just like her father's. Nace "she is very beautiful" ya zagayo ta bayana yana kallon hoton yace "yes she is, just like the Moon I named her after" da sauri na juyo na kalleshi, yace "yes, sunan ki na saka mata, maimunatu, and I call her Moon" da sauri na hadiye kukan daya taho min, her mother died giving birth to her, but he named her after me. Daya frame din da yake kan table din na dauka, numfashina ne ya tsaya chak, hoton mu ne nida Ibrahim, duk bama dariya, fuska ta kamar zanyi kuka, yana tsaye a bayan class din mu ni ma ina tsaye a kusa dashi, na dan kwantar da kaina a kafadar sa shi kuma ya juyo kadan yana kallona. I remember sanda aka dauki hoton, Hafsat ce ta dauke mu da wayar ibrahim ranar da zamu bar makaranta. We were so young then, and so much in love. Na kalle shi da sauri naga yana murmushi, it is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Na ajjiye pic din da sauri na yi hanyar waje ina jinsa yana cewa "maimunatu please" exactly yadda yake cewa in yana ya son ya lallabani in yi masa wani abu. Da bibbiyu nake hada stairs ina sauka, idona almost a rufe na fita na doshi motar sultan da nazo da ita, na bude na shiga nayi mata key, a lokacin na hango shi ya

Please Login or Register in order to submit comment