Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sultan, kawai dai basa nuna maka ne, amma deep down suna sonka sosai, maybe more than yadda nake son ka ma" ya sakeni yana kallon fuskata yace "don't say that, in kina son kwantar min da hankali na say something else amma ba wannan ba, cos nasan basa sona, tun kafin in san menene so nasan basa sona. They hate me and I don't know why, wannan shi yafi komai bata min rai, why do they hate me so?" Bance masa komai ba saboda bansan me zance masa din ba. Ya zauna akan kujera ya zaunar dani a kusa dashi yace "tunda ya fara wannan maganar ba zai bar ta ba har sai yaga ya raba mu, I know him, zan shirya mana barin kasar nan, shine kadai hanyar da zamu bi mu tsira daga gare shi" na girgiza kaina nace "Sultan barin kasa ba shine mafita ba, iyayen mu ne, we are nothing without them and we can't runaway from them. Mafita shine mu zauna muyi facing din su mu yi duk abinda suka ce mu bar duk abinda suka hana mu. In mukayi haka to Takawa will have no reason da zai sa ya takura mana ko yayi tunanin raba mu. Amma in dai muka ce zamuyi retaliating ko kuma zamu bar kasar to anan ne zamu bashi damar yi mana duk abinda yake so" ya girgiza kansa yace "baki san halinsa ba, he will not stop, baya bukatar reasons, in dai yana son yayi min abu to tabbas zai yi min ne ko nayi laifi ko banyi laifi ba, ballantana yanzu yana ganin yana da dalili a hannunsa. Yanzu nasan Daddy zai kira ya nuna masa picture dinki da bindiga ya kuma gaya masa cewa nace nine na baki. The next thing you will know Daddy zai zo yace ki fito ku tafi an gama auren kenan" nace "then you don't really know Daddy. Daddy ba zai taba yanke hukunci ba tare da bincike ba, ni kuma in ya tambaye ni zan san yadda nayi nayi masa bayani yadda zai gane, kuma nasan zai gane din ma. Yanzu abinda nake so muyi magana akai shine; wa kake tunanin ya kaiwa Takawa pictures din nan?" Wani murmushin takaici yayi yace "tunani? Am sure it is Abbas, ba yau ya fara ba ai, but this will be the last time da zai shiga harkata, dan wallahi sai jikin sa ya gaya masa. He shouldn't have touch you" yadda ransa yake a bace na tabbatar idan ya kama Abbas sai dai wani bashi ba. Na kama hannunsa ina shafa gashin hannun a hankali nace "wannan shine exactly abinda Abbas yake so kayi, so yake ka taba shi yadda Takawa zai sake samun karin dalilin raba ka dani. He got your weak point, me. Yasan cewa you will react exactly like this, yasan cewa in Takawa yayi maka magana zakace zaka dauke ni mubar musu kasar, yasan kuma Takawa zai ce ba zaka tafi dani ba. Ya lissafa cewa duk abinda ya faru shine mai riba, in ka tafi kabar kasar dani shikenan he got rid if you, in kuma bamu tafi ba zaku yi ta rigima da Takawa shima nan shine da riba" He seems calmer now, yana sauraro na sosai, yayi ajjiyar zuciya yace "yanzu mai kike ganin zamuyi?" Nace "kar mu bawa Abbas abinda yake nema. Kar muce zamu je ko'ina. Kuma kar kace zaka dauki fansa akan Abbas, just let him be, duk abinda zai yi kar ka kula shi. Sai kuma muyi taka tsantsan, kar mu yarda muyi wani abinda muka sam Takawa baya so. You already got your job, ka cigaba da abin ka, duk sanda kake bukatar fatherly care ko wata shawara, go to Daddy. The last and the most important thing shine mu dage da addu'ah. I believe Allah yana tare damu kuma yana ganin duk abinda yake faruwa kuma ba zai taba barin mu ba as long as muma bamu barsa ba. Yadda ba zamu bar Allah ba kuma shine ta hanyar ibada da addu'a. Kuma ka saka a ranka cewa I will never leave you, Ever. Duk ma wani abinda zai faru, we will face it together" na dago hannunsa na kai baki na nayi kissing, nace a hankali "I love you" ga mamaki na sai naga yayi murmushi, genuine murmushi, yace "I love you too".
A ranar Asma'u tazo, da gudu naje na rungume ta ina murna, itama murnar take yi, tace " me sunan daada in dai girki kike so ki koya to ki tabbatar kin samu, dan bazan bar gidan nan ba sai na tabbatar babu wani abincin da baki iya ba" na nuna mata kitchen ta shiga tayi surveying ta fito ta fara lissafamin abubuwan da babu ina rubutawa, muna gama wa na bata kudi isassu nace taje ta siyo, shatar taxi ta dauko daga kasuwar saboda yawan kayan da ta siyo, ni dai ina ta mamakin wai duk wadannan kayan a ciki za'a zuba su. A ranar tare mukayi lunch da ita da sauran yara na, banyi aikin ba ina dai zaune ina kallon su suna tayi amma asma'u tana yi min bayanin komai da suke yi da dalilin da yasa suke yin komai. Har aka gama aka shirya table, for the first time yau anyi abinci a gidana, duk da cewa bani nayi ba amma naji dadi, nayi feeling cewa nayi gaining wani abu. Sam na manta ma da Takawa da Abbas and their problems. Sultan ma naga ya saki ransa. Da yamma muka fita muka tafi orphanage gurin surprise party din mu, a hanya muka tsara muka saya musu gifts, kowa sai da muka sai masa toy, mata baby dolls maza bindiga, yan kananan kuma mota, shigar mu cikin yaran ya kara saka wa muka manta da komai. Sunyi organizing abin sosai, harda drama da sport suka yi mana, aka kawo mana cake muka yanka sannan na zauna na yayyanka na bisu na bawa kowa a baki. Nan take naji yaran sun kwanta min a raina, na sake sosai a cikin su mukayi ta wasa, sultan har mamaki na yake yi saboda ganin bamu da yara a gidan mu. Bamu dawo gida ba sai bayan magrib, muna zuwa dama a gajiye muke, dan da kyar muka ci abinci, na fara shirin wanka kenan aka zo aka ce min wai nayi ba'ki, na kalli agogo naga 8:30, nace "wadanne irin ba'ki ne kuma yanzu?" Yarinyar tace min "Hajiya ce, tare da wadansu mata" wata irin faduwa naji gabana yayi, a daki na nake, sultan ya tafi nasa. Nace yarinyar ta shigo dasu palo na tace musu ina zuwa, fasa wankan nayi sauri na zura doguwar bakar riga nayi rolling veil na fesa turare na fito. Su uku ne na tarar a zaune suna karewa palon kallo, Hajiya, sai wata mata kusan sa'arta sai kuma khulsum. Na tattaro murmushi na shimfida a fuskata na karasa gurin su, na tarar already an kawo musu drinks da snacks da fruits, na durkusa na fara gaishe da Hajiya sannan na gaishe da daya matar dana lura suna kama, suka amsa min duk da fara'a a fuskarsu. Na juya na kalli khulsum nace "nayi fushi, sai yau zaki zo gidan nan" ba tare data mayar min murmushina ba tace "abubuwa ne suka yi min yawa. Kuma yanzu ba gashi nazo ba" Hajiya tace "dazu kuma nace ki tsaya sai da na fito na tarar ba kya nan" na sunkuyar da kaina bance komai ba, ta cigaba "ko da yake nasan ba laifin ki bane, yaron nawa ne sai a hankali, amma ace kwana nawa da bikin nan bai kai ki kin gaishe mu ba, sai da Takawa ya kira ku da kansa, sannan kuma ace kunje din ma bamu samu mun gaisa ba. Shi yasa na taho yanzu da kaina ni inzo mu gaisa din, in ga dakinki kuma in saka muku albarka" daya matar dana fahimci kamar 'yar uwartace tace "to yanzu 'ya'yan zamani ne sai a hankali, dan da ka haifa ma yaya ka kare dashi ballantana dan da yake ganin ba kai ka haife shi ba. Ke dai kawai Allah ya saka miki da alkhairi na abinda kike yi masa, dan ko uwar data haife shi iyakacin abinda zata yi masa kenan" Hajiya tace "Ameen dai" ta juyo gurina "ina yake ne? Kar dai kice daga gama biki har ya cigaba da yawon daren nasa? Wannan yaro na rasa yadda zanyi in raba shi da wannan yawon daren. Kullum ya fita hankali na a tashe yake saboda bansan me yake aikatawa a wajen ba" ban katse taba sai da na bari takai aya sannan nace "yana daki" suka kalle ni sannan suka kalli junansu sannan Hajiya tace "to kirawo shi mu gaisa" na tashi na tafi part din sultan. Ya fito daga wanka yana shafa mai, na shiga da sallama, ya juyo yana kallona, ya kalli kayan jiki na yace "why are you all dress up sai kace fita zakiyi" nace "we have guests" ya kalli agogo yace "su waye?" Nace "Hajiya" take yanayin fuskarsa ya chanza, ya ajiye tiraren hannunsa yace "me suka zo yi?" Na karaso na dauki tiraren ina fesa masa nace "zuwa sukayi mu gaisa suga gidan mu si saka mana albarka" yace "bull shit" na shiga closet na dauko masa wata doguwar riga na taimaka masa ya saka, sannan nace "please sultan, don't give them abinda sukazo nema. Kaje kawai ka gaishe su sai kayi dawowarka daki". Da kyar na samu ya biyo ni hannunsa cikin nawa, muna shiga palon duk suka juyo suna kallon mu, nima kallon nasu nake daya bayan daya ina studying din kowannen su. Khulsum kallo daya tayi mana ta dauke kai, she obviously still loves sultan and is jealous, matar da suke tare da hajiya ta danyi blushing alamar taji kunyar ganin hannuna ha sultan ya rike, Hajiya kuma gaba daya hakoranta a waje tana murmushi, tace "yaron kirki, da fatan bamu tashe ka daga bacci ba" yayi kamar bazai amsa ba sai kuma yace "ban kwanta ba ai dama" ya zauna a kasa na zauna a gefensa, yace "barkan ku da yamma" suka amsa su biyi a tare, bai kalli inda khulsun take ba, Hajiya ta fara masa jawabin abinda ya kawo su, ni kuma nayi using wannan opportunity din na fara studying dinta, she looks so calm and happy on the outside, duk wanda ya ganta zai dauka duniya babu wanda take so sama da sultan, but inside she is full with hatred, she is boiling witj bakin cikin ganin mu tare da sultan, a lokacin na kara fahimtar komai. Hajiya may not be responsible for rabuwar iyayen sultan, amma ta tsane shi, tsana ta sosai, she may not be dalilin daya raba sultan da mahaifinsa in da first place but tana da hannu wajan kara huruwar wutar al'amarin. She succeeded so far, amma yanzu na shigo cikin rayiwar sultan kuma sam bata jin dadin changes din da sultan yake samu, tana kallona a matsayin wacce tazo zata tarwatsa mata plans dinta. Tasan ba zata samu nasara akan sultan ba sai ta raba shi dani, and she plans on doing that. Sai kawai na samu kaina ina murmushi, nayi studying psychology ne saboda haushin yaudarar da nake tunanin Ibrahim yayi min, amma sai gashi ilimin nawa ba akan Ibrahim yake min amfani ba akan Sultan ne. Allah mai tsara lamarin sa yadda yaso kuma a lokacin da yaso. Na dawo da hankalina kan maganar da take cewa naji har yanzu fada take yi mana akan mu zauna lafiya mu bawa marada kunya. Tana gamaws daya matar itama tayi nata, daga ni har sultan babu wanda yace musu komai. Suna gamawa sultan ya mike yayi musu sallama ya koma part dinsa. Bayan ya tafi matar da suka zo tare ta kalli khulsum tace "me yasa baki gaishe shi ba? Ba mun gaya miki cewa maganar nan ta wuce ba? Ya kamata ki manta da komai ku cigaba da zumuncin ku" gaba na ne ya fadi saboda nasan wata maganar suke son fada min kuma daga dukkan alama ba zata yi min dadi ba, ban dago kaina ba ballantana in nemi ba'asin me take nufi da maganar ta. Jin bance komai ba sai ta cigaba da cewa "Maimunatu gwara kiji daga bakin mu kar wani ya gaya miki kiga kamar mun boye miki. Tun khulsum tana yarinya karama sultan yake son ta, babu yadda baiyi ba abashi aurenta iyayen mu suka ki saboda a ganin su babu uban da zai yarda ya hada 'yarshi aure da yaro irin sultan. Hajiya babu yadda batayi ba akan iyayen mu su yarda da auren amma suka ki. Bakin cikin abin ne ya saka shi ya fara shaye shaye. Daga baya da yaga da gaske ake ba za'a aura masa ita ba shine yayi kokarin bata mata rayiwarta, Allah ya taimake ta bai ci nasara ba" kallonta kawai nake yi ina tunanin how can someone, mai shekaru kamarta, lie like that? Murmushi na tattaro na dora akan fuskata nace "na sani, ya gaya min komai daya faru tsakanin su, and I still love him".
N

Episode Seventy Seven : Amina
Kadan ya rage dariya bata kubce min ba saboda ganin reaction din fuskokin su. Sam ba haka suka yi tsammani, su a tunanin su babu matar da za'a gaya mata irin wannan maganar ta hadiye sannan ta bayar da amsa irin wacce na bayar. Hajiya tace "kin sani? Kina nufin ya gaya miki exactly wannan maganar?" Ita kanta tasan cewa nasan karya suke yi, Nace mata "eh ya gaya min, ai baya boye min komai. Ya gaya min komai na labarin sa har labarin asalin fara shan giyarsa" a take naga kalar idonta ya chanza, murmushin fuskarta ya kau. I got her exactly where I want her. Na gyara zamana na harde kafafuwa na irin zaman da Sultan yake yi, na cigaba da cewa "nasan komai akansa, nasan duk abinda ya aikata a baya nasan kuma wanda bai aikata ba, nasan kuma abinda zai aikata nasan kuma abinda bazai aikata ba" daya matar tace "kuma duk kinsan halayensa kika yarda kika aure shi? Shi fa aure ba abu ne na wasa ba, in kika auri mutum kamar kin zabe shi ne ya zama uban 'ya'yan ki" nayi mata murmushi nace "ai in kana so kasan mutum, ranki ya dade, ba wajansa zaka kalla ba, ko kuma abinda mutane suke fada akan sa ba. Abinda zaka kalla shine his inner self, deep down waye shi. Sultan deep down is a good person, very good person, ni na gani kuma nayi niyyar fito da wannan goodness din nasa waje yadda kowa zai gani. Alhamdulillah, na fara samun nasara, dan duk wanda yasan sultan shekara daya data wuce in ya ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa." Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me. I can read your mind as well as I can read time from an analog clock" na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su na daga musu hannu sannan suka tafi. At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But am ready, Allah yana tare dani and am not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran.
Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na shiga closet dina, na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wasu deep red kaya, robber, three quaters wando da half vest. Na saka su ba tare dana saka komai a ciki ba. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kayan sun bi jikina like a second skin, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita. A palon sa na tarar dashi, yana zaune da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know wanne film suke yi. Ba'kin naki sun tafi ne?" Ban bashi amsa ba, ya fara kokarin chanza station, na chire hijab din jikina a yar a gefe nace "pss" ya juyo da sauri yana kallona, a hankali remote din hannunsa ya zame ya fadi kan carpet, ina kallon idonsa naga duk wani tunani da wata damuwar sa suna disappearing har sai da ya zamanto babu saura. Ya saki ido da baki da hanci duk yana kallona, a hankali ya furta "ya Ilahi save me, wannan rayinyar so take ta haukata ni" sai kuma naji kunya nadan rufe idona kadan da hannayena wadanda suka sha jan lalle tun na biki na. Yace "come here" babu musu na taka naje gabansa na tsaya, tun daga fuskata ya fara kallona har 'yan yatsun kafata. Ya hadiye wani mugun yawu daya sa na kara jin kunyar sa. Ya gyara zamansa yace "sit here" yana nuna min cinyarsa, nan ma babu musu na zauna. Ina zama na fahimci sako na ya samu karbuwa dan message din yaje har inda nake so yaje, na danyi dariya kadan, ya saka hannu yana shafa bare fatar cikina, murya can kasa yace "dariya kike yi min ko? Zan rama ne nima" na saka hannayena duk biyun na zagaye wuyansa sannan nace "sai dai ka rame" yayi murmushin gefen baki yace "really? Wanna bet?" Nace "yes" ya dora hannunsa akan kirjina ya fara shafawa a hankali, na lumshe ido na jikina yana amsar sakonsa na bude su akan fuskarsa mai dauke da murmushin mugunta yace "you still wanna bet?" Wannan karon ban bashi amsa ba, ya cigaba da abinda yake yi, nace cikin sarkewar murya, "ka takura musu da yawa fa" ya dan bata fuska yace nine na takura musu ko sune suka takura min?" Ya saka both hannayensa ya kama straps din half vest dina ya jawo ta kasa ya dawo da ita kan cikina, yace "better, yanzu sai muga waye ya takura wa wani a tsakanin ni da su" ina kallon cikin rinannun idonsa nace "in suka rame bashi kenan ba" yayi replacing half vest din da hannayensa yana kara lumshe ido, yace "wa yace miki ramewa zasuyi? A cikin 'yan kwanakin nan baki ga har girma suka kara ba sabida kulawar da suke samu? Nine dai nake ramewa saboda takura min da suke yi, sun hanani sakat, sam bana iya dauke ido na daga kansu, bana samun nutsuwa sai ina tare dasu, in ido na biyi tunanin su nake, in bacci nake mafarkin su nake......" Tun ina jin abinda yake cewa ina kuma fahimta har na daina fahimtar abinda yake cewa, na daina fahimtar komai, shima kansa mai maganar bana jin yana fahimtar me yake cewa, daga baya ma maganar ta gagara gaba daya. Mun manta da duk abinda ya faru a ranar, babu Takawa and his threats, babu Hajiya and her hypocrisy, babu khulsum and her food, a lokacin hatta Mommy da Daddy basa gabana, Sultan ne kadai a gabana, only him existed in my world kamar yadda shima ni kadai ce a tasa world din. Sai da akayi first round aka zauna break sannan na bashi labarin yadda mukayi dasu Hajiya, ban boye masa komai ba na gaya masa duk abinda suka ce min da amsar dana basu. Kamar yadda nayi tsammani, bai nuna damuwar sa koya tada hankalinsa ba sam, sai nuna min jin dadinsa da yayi akan yadda nayi tackling maganar da kuma trusting dinsa da nayi. Daga nan muka bar maganar muka cigaba daga inda muka tsaya. Hint ga matan aure, irin wannan time din shine best time discussing sensitive issue da mai gida, especially mai gidan da yake da temper ko kuma wanda baya daukan shawara, a lokacin he is relaxed, in body and in spirit, kan sa is fresh,and he is very excited, da wahala ki fadi abinda zai bata masa rai a lokacin. Amma fa bance ayi using time din wajan roko ba, ko kai tsegumin kishiya ba, gwara ayi amfani da time din gurin bawa mai gida shawara mai kyau wacce zata kara kafa miki fadar ku a gurinsa.
Washegari kamar yadda Sultan ya saba, in ya tafi masallachi baya dawowa sai gari ya waye, wanda na lura yana zama ne acan yayi karatun al'qurani, ni kuma wannan time din nake using in gyara dakunan sa, mostly daga nan bacci muke koma wa amma yau kitchen na tafi na barshi, yana ta mita wai shi bai ga amfanin in ce sai na koyi girki ba, tunda dai shi zan ke yiwa girkin nan kuma yace baya so ba shikenan ba sai in hakura. Ina shiga kitchen na tarar already Asma'u tana ciki, yau ma cewa tayi in cigaba da watching and learning, tana yin komai tana yi min bayani, ni kuma na bude kaina sosai ina fahimta, in naga abin tambaya in tambaya, har muka gama komai muka jera a dining sannan na tafi zanyi wanka. Ina shiga dakina wayata tana fara ringing na duba naga Daddy. Duk da cewa tun da nazo gidan kullum sai ya kirani ko kuma ni in kira shi mu gaisa amma yau sai da naji gaba na ya fadi. Nayi bismillah na dauki yawar, muryarsa naji wasai babu alamar damuwa a cikin ta, na sauke ajjiyar zuciya na gaishe shi, mun jima muna hira yana gaya min gobe zai tafi England kuma zai dan jima kafin ya dawo, nayi masa addu'ar fatan alkhairi, sai da muka gama maganganun mu sannan yace "jiya da daddare ai nazo palace, mai martaba sarki ya kira ni akan maganar ku, ya nuna min wasu pictures da banji dadin su ba, amma abinda na sani shine na yarda dake, tunda har baki kira ni kin gaya min menene ya faru ranar nan ba hakan na nufin kina ganin zaki iya handling koma menene, amma ina so ki sani, as much as I like sultan I like you more, amma hakan ba wai yana nufin bana son sultan ba, ina sonsa sosai kuma ina alfahari da abinda kike yi a rayuwarsa, but be very careful my daughter, your picture with a gun almost give me a heart attack, idan kinga abin yana kokarin yafi karfin ki just give me a call, ko ina kasar nan ko bana kasar nan I will always be there for you. Idan wani abin ya same ki a dalilin auren nan I will never forgive myself, saboda ni na amince ba saka ki a ciki duk kuwa da sanin sarkakiyar

Please Login or Register in order to submit comment