Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rage min" na zauna a kan bedside ina kallonsa har ya gama cin abincin sa ya tattare kayan sannan koma ya zauna ya dauko wata takarda ya warware yace "come let me show you something" na zauna kusa dashi, ya fara nuna min wani zane yace "this will be our home, anan zamu rayu muyi raising kids dinmu" ya fara min bayani dalla2, na jima da sanin cewa sultan ya kware a aikinsa amma sai yau na gani in reality, gidan ya tsaru iyakacin tsaruwa, kuma katon gaske ne, dan in baifi gidan mu girma ba to zasu yi kai daya. Sai da ya gama yi min bayanin gidan ya ninke takardar sannan yace "baki tambaye ni a ina za'a yi ginin ba?" Nace "a ina" yace "a palace. Nayi magana da galadima zai gayawa Takawa, ba cikin palace din bane ba, daga bayansa ne wani daji ne babu abinda ake yi da gurin, in ya yarda gobe zan aika ayi clearing gurin. Ta gate din palace din za'ake shiga sai kuma a zagaya baya" nayi mamaki sosai, ban taba tsammanin sultan zai yi tunanin zama a cikin palace ba, amma kuma sai na tuna cewa sarauta a jininsa take, yana sonta sosai, kawai dai yana basarwa ne saboda kar ya kara wa kansa bakin ciki, na tuna motar daya siyo min 'Her Royal Highness' it means deep down he is considering himself as 'His Royal Highness' kenan. Banyi masa maganar ba saboda bana son spoiling mood dinsa.

Washegari kamar kullum ya fita da sassafe, sanda ya dawo lunch yake gaya min har ya aika za'a fara clearing din gurin, it means Takawa ya yarda kenan. Daga nan kuma yace galadima yana kiransa, bamu sake magana ba sai da daddare yace ba'a nan zai kwana ba saboda sa sassafe zasu tafi 'yalleman din, ta kano zasu biya su dauki uncle Aliyu shi zai raka su. Washe gari nayi wa Amira waya na gaya mata me yake faruwa sai gata nan tazo zata tayani zaman jira. Muna zaune sai ga message ya shigo min ta WhatsApp daga Sultan, hoto ne, ina budewa na saki baki ina kallonsa. Sultan ne, yaci ado da kayan sarauta, babbar riga, rawani, da alkyabba, maroon color da adon fari, rawanin kuma fari da adon maroon. Yayi kyau karshe, ban taba ganin sultan yayi kyau irin wannan ba, sarauta a jinin sa take, he is a real prince, a kasan hoton ya rubuta 'do u know this man?' Take na chanza dp dina na mayar hoton, sannan nayi masa reply, 'no, i have no idea who he is, but whoever he is tell him that I love him so much" yayi reply "ohh God, am jealous" sannan wani message din 'and I love you too"

Gaskiya ina jin dadin sakonnin ku sosai, jiya nasha dariya musamman a WhatsApp, ansha rigima tsakanin #teamSultam da #teamIbrahim. Da fatan dai ba'aji ciwo ba lol. I love you guys alot, stay blessed.



Episode Sixty One : Save the Date

Afuwan nayi mistake gurin numbering episodes, nayi fifty eight guda biyu, so daya shine fifty nine, daga nan kuma sai sixty.

A episode sixty kar kuji nace Sultan ya shiga dakin Moon ya kwanta a gado wata ta gayyato nata saurayin daki, duk abinda ya faru babu ruwan maman maama. Kai kuma saurayi kar kaji labarin sultan ya shiga dakin Moon ta taga kai ma ka kama katangar gidan su budurwarka ka haura, idan aka kamaka ba zan zo ceto ba, ehe. Remember, this is just a fiction.

Wajan azahar su Sultan sukaje 'yalleman. Sun samu tarya sosai dan an sanar da baffa zancen zuwan su, kusan duk uncles din Moon su zo taryan manyan baki. Kofar gidan baffa kam cika yayi da mutanen gari da suka zo kallon sarki, a cewar su. Hakimai uku ne suka tafi tare da galadima, sultan kuma cousins dinsa guda biyu da amir ne suka raka shi. A palon baffa aka sauke su, aka gabatar da sultan, ya gaishe da baffa, baffa yana ta tsokanar sa, daga nan aka sallame su suka tafi gidan nuraddeen suka bar manya zasu yi magana a tsakanin su. A gidan nuradden suka ci abincin da akayi ta kawo musu kamar babu gobe, Sultan ya zauna yayi ta shan fura yana santi wai dama abinda Moon take sha kenan in tazo 'yalleman shine bata taba gayyatar sa ba. Nan da nan suka saba da nuraddeen, yana ta bashi labarin Moon sanda tana yarinya. Suna zaune Moon ta kira shi, nuraddeen ne ya dauka, "ke wato yau kadai din ma ba zaki bar mana shi ba ko? Sai kin dame mu da waya?" Tayi dariya "kai yaya, kira nayi fa in ce ya bani kai mu gaisa" yayi dariya "ni zaki yiwa yawo ko? Har da wani yaya sai kace da yayan kike ce min" suka yi dariya gaba daya sannan ya bawa sultan, tace "so...how are you?" Yayi murmushi yace "ke dai ki fadi gaskiya, kin kira kiji yadda nake ko kuma kin kira kiji me ake ciki?" Tayi dariya tace "yanxu shikenan bani da right din da zan kira ka? I just want to know ya kuka je" yace "lafiya lau muka zo love, and maganr kuma da kike so kiji ni ma ban sani ba, suna can suna maganganun su" tace "ni ba wannan ne yasa na kira ka ba, so nake inji ya akayi aka saka maka hular rawanin nan da wannan gashin na kanka?" yayi shiru bai bata amsa ba, ta fara dariya, tace "don't tell me aski aka yi maka" ya bata rai yace "don't laugh, give it a week, zai dawo ne. Besides, ba du aka aske ba ai" tace "can I see it?" Yace "never, ba zaki taba gani ba har sai ya dawo yadda yake"

A wajen su baffa kuwa sosai suke ta shan hira abinsu, da yake baffa mutun ne mai barkwanci nan da nan bakin suka saki jiki da shi suke ta hira. Sai bayan sunci abinci sunyi sallah sannan galadima ya gabatar da maganar data kawo su, suna nemawa dansu Abbakar Sadiq Abdullahi auren Maimunatu Muhammad Dikko, daga nan ya aika aka shigo da wata jaka cike da kudi, aka ajiyewa uncle Aliyu aka bude, mint ne 'yan 1000, galadima yace "ga kudin aure nan, muna fatan zaku karba" kowa ya saki baki yana kallon kudin, uncle Aliyu ya kallu kudin da yasan zasuyi daga miliyan biyar zuwa sama, ya saka hannu ya dauki rafa guda biyu ya ajiye a gefen sa yace "mun gode sosai amma wannan ya isa, albarkar auren muke nema, wannan ma mun dauka ne saboda al'ada ne" Tafida ya matso zai yi magana, baffa yace "abinda zamu iya karba kenan. Tun sanda labarin yaron yazo mana na tura Aliyu yaje har Abujan yayi mana bincike akan yaron, kuma yace min ya gamsu da abinda ya samu, dan haka tunda shine waliyinta na yarda da maganarsa. Na bawa Abbakar Sadiq auren Maimunatu, Allah yayi musu albarka baki daya Allah kuma ya sanya alkhairi" gaba daya aka ce "Ameen" uncle Rufa'i yace "to sai maganar sa rana kuma, yaushe kuke ganin za'ayi?" Tafida yace "ni ina ganin kar aja kwanaki da yawa, matsalar dai kawai yaron bai kammala ginin sa ba, dan haka ina ganin a bashi wata biyu, insha Allah kafin nan ya kammala, ita ma amaryar kafin nan ta shirye2n hidimarsu ta al'ada" kowa yace "wannan yayi, Allah ya kaimu" daga nan nan akayi addu'ar neman alkhairi aka tashi. Sultan kam da aka gaya masa me aka yanke ji yayi kamar ya dora hannu aka yayi kuka. Tun a hanya yake mita "wai wata biyu, ko garin abuja zan gine gaba daya ai iyakacin kwanakin da za'a bani kenan, aikin ginin nawa da a cikin sati daya zan gama shi, aikina ne fa" Ahmad, cousin dinsa yace "why are you whining ne Sultan? Tunda ance an baka ba shikenan ba? Me kake yiwa sauri ne wai" Sultan kawai tsaki yayi yace a ransa 'ba zaku gane ba'

A abuja kuwa kiran gaggawa Daddy ya samu daga fada, nan da nan ya tafi, yana zuwa mai martaba sarki ya nemi a basu guri zasu gana, yace "Muhammad dama abinda kake shiryawa kenan? Dama dalilin da yasa ka dauki yaron nan kenan" Daddy yace "Allah ya taimakeka sam ba haka bane, mayar da Sultan gida na daban da alakarsa da yarinyar wajena" Takawa yace "bakasan halin yaron nan ba labarinsa kakeji, duk inda tunanin ka ya kai to ya wuce gurin. Ina tausayawa yarinyar nan, she have no idea what she is in for. Ka taimaka mata ka janye maganar auren nan. Bana son abinda zai bata zumuncin da yake tsakanin mu. Nasamu labarin itin tarbiyyar da ka bawa 'ya'yanka, sam yarinyarka bata dace da yaron nan ba. He don't deserves her" Daddy yayi shiru yana tunanin amsar da zai bayar, sai yace "Allah ya taimake ka ni bani na hada yaran nan ba, hadin Allah ne, kuma magana ba'a hannu na take ba tunda tun dazu suka ce min har sun isa 'yalleman gurin baffa na, yanzu maganar tana hannun sa. Ni ina ganin mu zuba ido kuma muyi addu'ah mu ga zabin da Allah zai yi mana" Takawa yayi shiru kamar ba zai sake magana ba, sannan yace "mu dai mun gayama gaskiya, wanda bai ji bari ba kam tabbas zaiji hoho. Fatan mu shine duk abinda ya faru kar kazo gurin mu. Zaka iya tafiya" Daddy jiki duk ba kwari ya mike ya fito, har yaje gida yana lissafin lallai da akwai wani abu a tsakanin Sultan da babansa wanda duk bincikensa bai sani ba, koma dai menene, it is something big.

Moon
A dakin Hafsat muka zauna, hira kawai muke yi muna dariya abin mu, muna ta labarin Haihuwar Hafsat da irin shagalin da zamu yi ranar suna. Edd dinta ya riga yayi kawai haihuwa ake jira. Hira nake ina dariya amma can kasan raina ina tunanin abinda yake faruwa a 'yallemam. Muna cikin haka naji shigowar kiran Sultan, na daga ina kallon sunan jikin screen din 'my Sultan' na tuna ranar da yayi saving sunan da kansa a waya ta, ranar dinner din Hafsat, a lokacin ban taba tsammanin zan dauki kiran saba ko da ya kirani sai gashi yanzu ya zama tamkar wani sashe na jikina wanda ba zan iya rabuwa da shi ba. Yanzu gashi wai yana kirana ne ya gayamin an bashi aure na ko ba'a bashi ba, sai naji na kasa daukan wayar har ta katse, ya sake kira shima naki dauka. Amira tace "in ba zaki dauka ba bani shi nan, har wani Sultan akewa kunya? Baki san ance kunyar mara kunya asara bace" na mika mata wayar, tana karba aka sake kira, gani nayi ta taba rai ta dawo min da waya ta, na duba screen naga 'Amir" dariya nayi dan nasan drama dinsu da Amir na dauka, yace "wai kunyar amarcin ce za'a fara yi mana tun yanzu?" Nayi murmushi kawai bance komai ba, yace "gamu nan mun taho, amma na san sai dare zamu karaso Abuja, tell that your ugly friend ta shirya mana abinci dan anan zamu fara sauka" nayi kamar banji ba, na saka shi a hands free nace "me kace?" Yace "wannan kawar taki mummuna, bakar nan masifaffiya, kice mata ta dafa mana abinci kafin muzo" ai kuwa Amira ta warce wayar daga hannuna ta kama yi masa masifa "yanzu har kai zaka kalli wani ka kira shi da ugly? Anya kuwa kana kallon fuskar ka a mudubi kuwa? Duk baki na wallahi ni balarabiya ce akan ka" ni dai dariya nake yi Hafsat tana taya ni. Sai bayan isha suka zo, iyakacin samarin ne suka zo nan manya kowa ya kama gabansa, uncle Aliyu ma yazo ya taho da Amina wacce daga jin zancen biki ta rude ta hado kayan ta. A palon su Sultan suka sauka nan aka shiga hidimar kai musu abinci, sai da suka gama sukayi sallolinsu sannan muka je, ni da Amira da Amina. Muna shiga aka fara drama da Sultan dan fir yace babu wanda zai ga fuskata, ai an bashi ni yanzu dan haka i am no longer in tha market. Su Ahmad suka yi ta naci su kuma lallai sai sun ga fuskata tunda takabas dan su ganni suka zo, da kyar dai Sultan ya yadda na bude fuska ta, shima kuma ya kasa ya tsare yace babu dogon kallo, ni dai dariya kawai nake yi musu. Nan fa Amira da Amir suka dora daga inda suka tsaya, Amina ma da yake mai surutu ce sai ta shige cikin su suke tayi. A hankali sultan ya mike ya je bakin kofa sannan yayi min alama da in zo, tsam na zame na bishi ba tare da duk sun lura mun fita ba. Ina fita sai naga ya kama hanyar garden na bishi a baya.

Akan kujera ya zauna nima na karasa na zauna a kusa dashi, ya juyo yana kallo na nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa ina murmushi, dariya yayi sosai yace "wai ni kike jin kunya kuma? Tsafdi, lallai kin hadu da aiki" ni dai bance komai ba, ya kamo hannayena duk biyun yana kallon su, sannan a hankali ya shafa zoben sa da har yanzu yake makale a danyatsa na. Sannan yace "wata biyu suka ce, what if something happens a cikin watanni biyun? Na kalle shi naga ya sunkuyar da kansa yana kallon hannayen mu a hade, nace " Sultan, babu abinda zai faru kaji? Kullum muna addu'ar zabin alkhairi, tinda har Allah yasa suka ambaci wata biyu to sune mafi alkhairi a gare mu. What if da ace baffa cewa yayi NO? Ya zakayi kenan?" Ya dago da sauri yana kallon idona yace "then I will definitely be your patient, dan kwakwalwata zata iya bugawa" na same hannu na daga nasa na tallafo fuskarsa dasu ina kallon idonsa nace "babu abinda zai same ka, shi Allah baya taba dorawa bawansa abinda yasan ba zai iya ba" ya katse ni yace "then Allah ba zai raba mu bama, saboda yasan ba zan iya dauka ba" idonsa gaba daya ya chanza kala, nayi saurin chanza maganar nace "Askin ka yayi kyau" Hannu biyu ya saka ya rufe kan sa yace "ash, ya akayi na bari kika gani" nace "really yayi kyau, I like it" ba duk gashin aka aske ba, an rage masa tsaho dai, sai ya fi dacewa da sajen sa, fuskarsa kuma ta kara fitowa sosai. Ya shafa kan yace "thank You" sannan ya cigaba da magana "tom yanzu cikin two months din nan me za muyi?" Nace "kamar me fa?" Yace "to kill the time" nace "as usual, kai already ma ai aiki yayi maka yawa, ga office ga harkar gini, ni kuma I will just be here, waiting" yace "driving lessons din mu fa?" Nace "bayan ba wani abin kirki kake koya min ba, for over one month amma ace har yanzu ban iya driving ba" muna cikin haka muka ji muryar Amir "to in kun gama soyewa sai kuzo muyi sallama mu zamu tafi gida" na tashi ina dan jin kunya, muka fito muka tarar har sun dauko mota mukayi sallama suka tafi, Amir kuma ya dauko motar sultan guda daya, yana zuwa gurin mu nace "Amir dan Allah ga Amira nan ka kaita gida, kaga dare yayi sosai" a tare suke ce "what?" Ni da sultan sai dariya, sultan ya bata rai yace "gaskiya Amira in ba zaki shiga motar Amir ba to sai dai ki hau taxi, dan ni na gaji ba zan kai ki gida ba" Amir yace "to ni an gaya maka ban gaji bane? Ballantana wannan unguwar tasu mai shegen nisa, kuma ni ba ma nason a ganni da ita a mota a daukar ko budurwata ce, ai sai aji na ya zube" nan Amira ta hayayyako "Allah ya kiyaye min shiga motar ka, ni da in shiga motar ka ba gwara na tafi a kafa ba" yace "ai kuwa zaki tafi a kafar" har yaja mota sai kuma yayi reverse, yace "get in" kawai sai muka ga Amira ta zagaya ta bude ta shiga sun tafi, daga ni har sultan duk sakin baki muka yi muna kallon su, Sultan yace "munafukai, a hankali sai asirin ku ya tonu"

Rayuwa ta koma normal, abubuwa suna tafiyar mana yadda muke so, sultan ya dukufa haikan akan aikin gininsa duk da kusan tare muke aikin dan dai ni bana fita field dinne amma komai tare muke tsara shi, komai za'a saka a gidan sai ya kawo min samples na zaba tukunna, ba karamin kudi yake narkar wa a aikin ba dan ni har mamakin inda Sultan yake samun kudi nake yi, gani nake kamar aikin sa ba zai shigo masa da wadannan uban kudaden ba. Rannan mun fita koyon mota sai yace min yana so zamu je wani guri. Hanyar barin gari naga mun dauka amma ban tambaye shi ina jamuje ba. Gani nayi yayi packing, na fito ina kallon gurin da muka zo, orphanage, a kafa muka shiga cikin building din. Babban guri ne sosai, ga dakunan yara, maza daban mata daban, ga gurin wasa, ga kitchen sannan ga offices din staff. Muna shiga ma'aikatan gurin suka fara gaishe mu da girmamawa sosai kamar zasu kwanta a kasa, ni har mamaki nake yi, idonsu kawai zaka kalla kaga tsantsar soyayyar sultan da kuma respect dinsa, ya fara tambaya "where are my kids?" Da sauri wata tace "suna playground suna wasa" muka tafi gurin, ina ta kallonsa naga wani excitement a fuskarsa, real love, ai kuwa muna shiga gurin wasan gaba daya rayan suka taho a guje wasu har suna faduwa suka rungume shi, sai da suka kai shi har kasa yana ta kyalkyala dariya, in ba tare da ni ba ban taba ganin sultan cikin wannan fara'ar ba, da kyar ya samu suka daga shi, ya zauna a zaune suka zagaye shi kowa yana kokarin bashi labari, ga mamakina duk yasan sunan kowa kuma yasan me yake ciki, ni sam bana fahimtar me suke cewa saboda yadda suke magana gaba dayan su a tare. Sai da suka dan numfasa sannan ya tashi ya kamo hannuna yace "na kawo muku bakuwa yau, Mommy zaku ke ce mata, she is going to be my wife" masu wayon cikin su suka kama murna marasa wayo kuma kawai suka tsaya suna kallona, har cikin dakunan su ya shiga dani na gani, ko wanne yaro da gadonsa sai 'yan kanana ne ake musu shimfida a kasa saboda kar su fado, gurin tsaf tsaf babu kazanta, ko wanne yaro da locker din kayansa, ga kuma inda suke cin abinci shima a tsaftace, muka shiga kitchen masu aikin girki suna ta gaishe mu, suka bashi list din abubuwan da suke bukata nan take ya bada kudin yace a saya, muka shiga dan karamin clinic dinsu shima ya nuna min sannan yace yana son ya dan yi musu 'yar karamar makaranta amma sai nan gaba tukunna, yanzu dai van ya saya musu ake kaisu kamaranta kullum ake dawo dasu. Har zamu tafi wani yaro yazo da gudu yana bata fuska yace "Daddy kace in ka dawo zaka kawo min bindiga kuma gashi ka dawo baka kawo min ba" Sultan ya sunkuya har kasa yana shafa kan yaron yace "sorry Halifa, na manta, amma gobe insha Allah zan bawa uncle Amir ya kawo maka" yayi masa kiss a goshi, yaron ya tafi yana ta murna. Ji nayi kwalla ta taru a idona, yanzu na fahimci inda sultan yake samun kudi, as long as kana kyautatawa mutane da dukiyarka, musamman marayu, to Allah zai yi ta ninka maka kofofin arzikin ka, abinda ka bayar sai Allah ya biya ka da dubun sa, mutum kamar sultan ba zai taba talauci ba. Muna shiga mota ya kama hannuna daya ya rike yake tuki da dayan hannun, babu wanda yace komai, can nace masa "da ka gayamin nan zamu zo at least ai da na taho musu da wani abu ko?" Yace "you are welcome, duk sanda kike son zuwa zan kawo ki" na sake yin shiru a raina ina mamakin mutum irin sultan.

Tafiya muke a hankali kamar ba ma son zuwa gida, kowa da tunanin da yake yi, har yanzu kuma yana rike da hannuna, sai da muka yi nisa nace "Sultan ya kamata kaje gurin Takawa kuyi maganar bikin nan dashi" ba tare da ya kalleni ba yace "naje ai" da sauri na kalleshi ina mamakin ya akayi bai gaya min ba, packing yayi sannan yace "Abbas ne ya kira ni a waya ina office yace min inje Takawa yana kirana, da naje gurinsa na gaishe shi bai amsa ba, kin san me yace min?" Na girgiza kaina, yace "check book ya jeho min duk yayi signing pages din yace 'ka dauki duk adadin kudin da kake so kayi duk abinda kake so dashi, amma ina son ka fasa auren yarinyar nan, she doesn't deserve someone like you" yayi shiru fuskarsa tana nuna bacin ransa, a hankali na tambayeshi, "me kace masa kuma" ya daga kafada yace "na ajiye masa check book dinsa na ce masa bana bukatar kudinsa, abinda da nake nema daga gare shi ma yanxu bana bukatar sa" ya juyo yana kallona yace "all I wanted before is love, yanzu na samu daga gare ki, kowa ma yaje ya rike nasa, your love is enough for me" hawaye naji yana fitowa daga idona (is it possible to love someone so much that it makes you cry?) Ya saka hannu yana goge min hawayena yace "just promise me that you will never leave me



Episode Sixty Two : The Manager

Na kalli cikin idonsa nace "I will never leave you, dama parents dina kawai nake ji, tunda yanzu na samu go ahead din su babu abinda zai saka in rabu dakai" a hankali yanayin fuskarsa ya fara chanzawa daga bacin rai zuwa murmushin da ya saka nima na fara murmushi yace "then I don't need anybody else" Mun dau hanyar gida again naji wayata tana ringing, na daga naga Mommy, ina dauka tace "ya akayi har yanzu baku dawo ba? Ku zarto asibiti mun tafi da Hafsat yanzu tana labor" a rikice ta katse wayar ina kallon sultan nace "Hafsat....labor... Hospital" nan take Sultan ya gane abinda nake nufi ya juya kan mota muka tafi asibitin da Hafsat take antinatal. A hanya na dauko wayata ina neman number, sultan yace "wa zaki kira?" Nace "Zayed" yace "No, ki bari sai ta haihu tukunna" na mayar da wayar na ajiye. Muna zuwa da sauri na fita na bar sultan a mota, a waiting room na samu Mommy da Amina, Mommy tana ta faman jan charbi. Na samu guri nima na zauna. Ba'a jima ba aka leko aka ce wata a cikin mu ta shiga ta zauna da ita, da sauri na tashi na shiga. Zan iya cewa tare muka yi laborn da Hafsat, in tana kuka nima sai in kama kukan, in tana addu'ah in taya ta. A haka mukayi ta fama har dare ya raba, Sultan yana ta kira yana tambayar jikin Hafsat, a lokacin na kara jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha a gurin haihuwa, a lokacin kuma na kara jin haushin duk matar da zata haihu ta dauki dan taje ta yar, kuma na kara tsanar duk dan da zai ki yiwa iyayensa biyayya. Hafsat ba ta haihu ba sai da alfijir ya fara keyowa, ta rike ni gam tamkar zata ballani sannan ta haifo kyakykyawar 'yarta mace, ana goge yarinyar na karbe ta na rungume ina jinsonta yana shiga zuciya ta, Hafsat ba kunya babu tsoron Allah tana samun kanta tace in bata 'yarta, har nurses din wajan sai da suka yi dariya. Na dora mata ita akan cinyarta ta fara shayar da ita (shayar da baby a wannan lokacin yana taimakawa wajen tsayar da jini da kuma saukin fitar mabiyya, kuma yana taimakawa jariri wajan saurin koyon shan nono da wuri kuma wannan ruwan nonon na farko yana da matukar amfani a gurin jariri). Gari yana wayewa

Please Login or Register in order to submit comment