Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

you will be happy with him, a lokacin ban san wanene zaki aura ba, Maimunatu how can you marry someone like him? Is he blackmailing you or your family? Nasan ba dan kudinsa bane because you have all the money you need, kuma yanzu bayan binciken da nayi a kansa na tabbatar ba dan kina sonsa bane, saboda ni na sanki, nasan ba zaki taba son mutum mai hali irin nasa ba. Maimunatu nazo nan a yau, duk da nasan cewa ba lallai ne ya bar ni in fita daga gidan nan da raina ba amma am ready to die for you in dai har hakan zai kawo karshen wannan auren naki ne. I sacrifice my love so that you will be happy, but now after knowing you won't be happy I am willing to sacrifice myself so that you will be free" Tashin hankali ba'a saka masa rana. Poor Ibrahim. You have no idea what you have done. Hannuna naji ya kama ya saka min wani abu a ciki, sannan cikin rada yace "please Moon, run away" ta baya naga an finciki Ibrahim an mikar dashi tsaye, na daga kaina naga Solomon, kyakykyawan mari ya sauke a fuskar Ibrahim. Na mayar da dubana kan Sultan, kofin da yake hannunsa naga ya saki ya fadi kasa, sannan ya fara takowa a hankali idonsa yana kaina, na mike tsaye ina jiran karasowarsa, Hafsat ce tayi sauri tasha gabana, a raina nace "oh no my dear sister, Sultan will never hurt me" chak ya daga ta ya ajiye a gefe, na daga mayafina na karasa bude fuskata ina kallon cikin jajayen idanunsa. Bazan iya cigaba da kallon abinda nake gani a idon sultan ba dan haka na rufe nawa idon, ya dora goshinsa akan nawa yace cikin muryar rada "who is he?" Na kasa cewa komai, ya kara tambayata "who is he?" Da kyar na tattaro yawun bakina daya bushe a hankali nace "please sultan, not here" kamar baiji ni ba ya sake cewa "who is he" kafin in bashi amsa ya kama hannuna ya cire abinda Ibrahim ya saka min a ciki, na bude idona na kalli abin, shima shi yake kallo. Kallo daya nayi masa na gane menene, pink Handkerchief dina ne dana yiwa Ibrahim reply a jiki all those years ago. Sultan ya bude ya karanta rubutun jiki. "I don't know where the path to the future leads, but I want to find out with you"

Hmm



Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2

Ibrahim; 9 hours ago
Ya daga kai ya kalli agogonsa da yake kada karfe goma sha biyu na rana. Ya mayar da idonsa ya lumshe yana jin zafi a ransa. Tun safe yake kwance akan gadonsa, ko breakfast bai yi ba. It is time, yasan yau ne yasan kuma yanzu ne daurin auren Maimunatu dan har katin daurin auren yana dashi. Ya dauko katin yana juyawa a hannunsa, sau nawa za'a bashi katin auren maimunatu ne wai? Kamar yadda ya gaya mata ya hakura, he just want her to be happy, kuma indai happiness dinta will come from wannan auren to dole zai hakura da ita ko da kuwa zai cigaba da zama babu aure har karshen rayuwar sa. Amma tun ranar da yace mata ya hakura din bai samu sassauci na radadin da zuciyar sa take masa ba har yau. Why must his destiny be so cruel ne? Da ya rasa ta ya sha wahala after several years kuma sai gata har office dinsa only for her to tell him cewa bata sonsa yanzu wani take so kuma. Ya mike zaune ya jawo wayarsa ya kira yaronsa ya bashi umarnin ya siyo masa abinci ya kawo masa dakinsa. Ya ajiye wayar yana tunanin wannan abin daya same shi yasan duk alhakin Efi ne. Marainiya babu uwa babu uba aka aura masa amma duk da son da tayi masa haka ya rufe idonsa yayi ta gallaza mata sabida baya santa. Lallai alhaki kuikuyo ne, gashi shima wacce yake so din tace bata sonsa kuma duk da cewa ba tayi treating dinsa kamar yadda yayi treating Efi ba amma zuciyar sa ba karamin zafi take yi masa ba. Shin haka Efi taji itama? Ko kuma taji fiye da haka ma? Ya tuna sunan mijin da Moon ta aura, Sultan, a Prince, ya tabbatar ba zata samu matsala ba tunda at least babban gida zata shiga, gidan daraja, she will be respected in the society. By impulse, kawai ya jawo wayarsa ya shiga Facebook saboda yana son ya rage tunani, yana shiga ya fara scrolling through newsfeed, ya jima a haka kawai yaga hoton Moon tare da wani, ya jima yana kallon hoton saboda irin kyan da yaga tayi masa, yayi sauri ya dauke kansa yana kiran "auzubillah" matar wani ce yanzu, ko kallon mijin nata baiyi ba ya bude labarin kasan hoton. Zuciyarsa ce ta buga da karfi har sai da ya mike zaune, jikin sa ya fara karkarwa, ya sake maimaita heading din labarin "The Drunk Prince of Abuja weds Today" a hankali ya fara karanta labarin, an danyi brief magana akan Sultan, irin halayensa da mutane suka sanshi dashi, sai kuma akayi bayanin yadda bikin ya kasance da irin kudin da aka kashe a bikin. Kafin ya gama karantawa gaba daya gumi ya jika jikinsa, ya fara duba comments din mutane, most of them suna cewa suna tausayawa Moon na 'she looks so young' 'iyayenta sun cuceta' 'poor girl' wadanda kuma basu san iyayenta ba suna cewa 'kudi iyayenta suka gani suka bashi' Ibrahim ya ajiye wayar akan gado ya rike kansa da yake sara masa, ya ilahi, me yake faruwa ne? Mai yasa maimunatu ta auri mutum irin wannan? Ba class dinta bane ba. Ya sake daukan yawar yana ta bincike akan Sultan, anan yaga labarin gang bang da irin abubuwan da suke aikatawa a duk fadin Nigeria. No, no, no, kawai yake maimaitawa "no I will not let Maimunatu destroy her life. But why us she doing this?" Gani yake kamar duk abinda ya faru fault dinsa ne, da ace tun farko bai tafi ya barta ba da duk haka bata faru ba. A ganin sa babu wacce zata auri dan giya tace zataji dadin aure, babu kuma wacce zata auri known criminal kamar sultan tace zata ji dadin aure.

Da sauri ya zura rigarsa ya dau key din motar sa ya fice, yama manta da zancen bai ci abinci ba. Supermarket dinsa ya tafi yayi kamar zai shiga sai ya tsaya, mai gadi yazo ya gaishe shi, yace masa "kasan wani dan Sarkin garin nan kuwa da ake bikinsa yanzu?" Da sauri yace "sosai ma kuwa yallabai, ai wannan babu wanda bai san shi ba a garin nan, tun yana yaro ya gagari ubansa, mai martaba sarku da kansa ya kaishi gidan gagararru, acan ya girma, naji labarin ma har kisan kai yayi a gidan shine suma suka ga ba zasu iya ba suka sallamo shi ya dawo" (kunji mutane ko?hmm) Ibrahim yaji yawun bakinsa gaba daya ya dauke, mai gadin yace "Yallabai Allah dai yasa ba wani abun ne ya hada ka dashi ba?" Ibrahim yace "babu komai kawai labarin bikin naji" daga nan bai shiga ba ya fito da motar sa ya kuma hawa titi, tafiya kawai yake bai san inda zashi ba, mai yasa Daddy ya yarda ya aura wa Moon Sultan? Tabbas da akwai wani abu a kasa. Maybe blackmailing Daddy yake yi, tunda Daddy babban mutum ne, Sultan zai iya hada wata karyar yace idan Daddy bai bashi Moon ba zai fada a gari, irin abinda blackmailers suke yi. Wani gurin cin abinci ya tsaya ya shiga, ya duba agogonsa yaga karfe biyu har da rabi, time is running out, he have to think of something. Dan kadan yaci abincin yaji ba zai iya ci ba, ya tashi yaje gurin biyan kudin sai yaga bayarabe ne cashier din, ya tambayeshi da yarabanci "kasan dan sarkin garin nan da aka yiwa aure kuwa?" Mutumin kamar dama jira yake yace "ni kuwa na san shi, ni da suka hana ni bacci jiya da daddare ba dole in san shi ba?" Ibrahim yace "suka hana ka bacci kamar yaya?" Mutumin yace "ai inda suka yi partyn jiya a kusa da gida nane, shi mai gidan, Solomon, is a known criminal in lagos, ya gagari kowa, he is a kidnapper as well as an arm robber. Gida kawai ya saya a garin nan ya ajiye in yayo barna a lagos sai ya taho nan ya zauna kwana biyu sannan sai ya koma. Jiya a gidansa sukayi partyn su har gari yawaye babu wanda yayi bacci a unguwar nan sabida kida, kwalaben giya kuwa da aka ringa shiga dasu ni dai har kallo na fito yi, da safe makocina ya ce min ta window dinsa yaga ana shiga da mata gidan, mata irin wadanda bana mutunci ba, mu dai jiya Allah ne kadai ya saka va'a kife da unguwar mu ba saboda yawan zunuban da aka aikata a ciki" Ibrahim has heard enough, yayi masa godiya ya fito. Direct gida ya koma, kafin ya karasa gida har ya yanke shawarar abinda zai yi a ransa. He is going to break the marriage, even if it takes his life. Yayi murmushi a ransa, maybe wannan shine destiny dinsa, maybe wannan shine dalilin da yasa Allah ya sake hada shi da Moon few days to her wedding. Yana zuwa gida yayi sallah ya bude locker dinsa da yake ajiye muhimman takardunsa ya dauko handkerchief din Moon daya ke ta ajjiye dashi all those years. Ya karanta rubutunta da still yake baro baro a jikin hanky din "I don't know where the path to the future leads to, but I want to find out with you" ya sake yin murmushi. So, this is it, this is the future, their future, and he will be there for her. Da yake late yayi sallar azahar din sai yaji already ana la'asar dan haka ya sake tashi yayi sannan ya dauko wayarsa. Yasan inya kirata ma ba zata dauka ba. Amma wannan 'yar'uwar tata wacce tayi masa karyar cewa ita yayar moon ce, yama sunan ta? He can't remember. Number din ma bai yi saving ba dan haka yayi ta scrolling call history dinsa har yayi tracing number din, yayi dialing, sai da ya kira wajen sau uku sannan ta dauka, kamar yadda yayi tsammani hayaniya ake tayi, tace masa bata jinsa sosai amma bara ta fita waje ta kira shi. Ba'afi ten minutes ba kuwa ta kira shi, suka gaisa sosai ya tambayeta ya biki tace Alhamdulillah, yace "kuma ku bikin naku na rowa ne ko? Ko gayyatar mutane ma bakwayi" tace "ayyah, na dauka Moon ta gayyace ka ai" yace "a'a, ko daurin aure bata gayyace ni ba. Na so kuma inyi attending ko da event daya ne in yi wa ango Allah ya sanya alkhairi, kuma kinga kema ai da mun sake gaisawa sosai ko?" Ta danyi dariya tace "ai ba'a gama ba, yanzu zamu tafi kai amarya, a can gidan nata kuma zamu yi party da daddare" a ransa yace "perfect, then that is what I will attend" a fili kuma yace "to ban sani ba ko za'a iya gayyata ta can din" ta sake dariya tace "why not, ai har da maza abokan ango. Ka taho kawai bayan Sallar isha, tunda biki ake in kazo palace din zasu barka ka shiga, sai a nuna maka part din amaryar, in kaje can sai ka kirani sai in shiga da kai" yace "kai amma naji dadi sosai, jazakillah bil jannah" tace taba dariya "kai sai kace wani abu na baka? Sai kazo din" ya kashe wayar yana murmushi, sam baya jin tsoro ko fargabar abinda zai je ya dawo. Tsoron da yaji ya kasa tunkarar Daddy shine dalilin faruwar komai, he is no longer afraid, he was a fool, but not anymore. Yana yin sallar isha ya shirya, shi kansa bai san taka maimai me zaiyi ba amma yasan zuwansa gurin a matsayinsa na tsohon saurayin Moon zai bata ran mijinta, tunda dan giya ne ma zai dauka ita ta gayyato shi, hakan kuma zai iya zama sanadiyyar mutuwar auren, shi kuma ko menene zai faru dashi bai damu ba, as long as Moon will be free from this marriage.

Bai sha wahala gurin shiga palace din ba saboda gidan a cike yake da mutane, tun daga gate ya tambaya akayi masa kwatancen inda gidan amaryar yake, da dan nisa kafin ya karasa, yana zuwa yaga gurin a cike da motoci, yayi packing ya fito sannan ya kira number din Amina yace mata gashi yazo, ba'a jima ba ta fito suka sake gaisawa sannan tayi masa jagora zuwa ciki. Suna shiga ya hango Moon a zaune a tsakiyar kawayen ta, sparkling like the moon she is. And he feel like his life doesn't matter any more.

Moon
Na sake rufe ido na ina kokarin saita numfashina tare da kiran "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" repeatedly a zuciya ta. Na bude ido na naga har yanzu Sultan ni yake kallo, jijiyoyin wuyansa da goshin sa sun fito rado rado. Na sake hadiyar yawu da kyar nace "Sultan, this is not what you are thinking" ya kalli handkerchief din hannun sa yace cikin shakakkiyar murya "this is your handwriting. Baki bani amsa taba, who is this man to you? What is he doing here today?" Nayi kokarin rike hannunsa ya matsa baya, cikin rawar murya nace "Sultan not here please. Nayi maka laifi, please ka bari muje wani gurin sai inyi naka bayani". Handkerchief din hannunsa ya dunkule ya jefo min a kirjina, ya juya baya ya koma inda yake dazu. Ban taba ganin bacin rai a fuskar sultan irin wanda nake gani yanzu ba. A hankali na juya gurin Hafsat da take tsaye kusa dani na dora kaina a kafadar ta na fara kuka. Muryar Amir naji yana magana "alright ladies and gentlemen, the party is over, we really appreciate your presence but you all need to leave now" na dago kai ina kallon mutane suna ta fita, friends dina ko sallama basu samu damar yi min ba duk Amir ya tisa keyar su suka fice, Amina da Hafsat ne kadai suka ki tafiya, mazan ma duk Amir ya koresu, amma sai na lura da gang bang ko mutun daya bai fita ba, sai kara samun guri suka yi suka zauna. Sultan na hango shi kadai yana tsaye ya juya bayan sa ya dora kafarsa akan kujera yana shan wani abu a cikin kofi. Gaba na ne ya fadi, oh dear God, no. This is all my fault, tun farko dana bawa Sultan labarin Ibrahim da duk haka bata faru ba. A hankali na fara takawa ina tafiya inda Sultan yake tsaye, na karasa bayansa na dora hannuna a kafadarsa nace "am sorry sultan" ya ture hannuna daga jikinsa ya juyo yana kallona da idanunsa da suka fara sauya color zuwa ja, yace cikin daga murya "why? Na sha tambayar ki in akwai wani wanda ya kamata in san da zaman sa amma kika ce min babu" kafin in bashi amsa naji muryar Ibrahim yace "sai ka tambayi kanka me yasa bata ba ka labarina ba, maybe it is because she is still in love with me" nan take idon Sultan ya karasa yin ja kamar garwashin wuta, ya juyo a fusace yace "please somebody should shut up that man for me" tun kafin ya rufe bakin sa kusan mutum biyar suka yi kan Ibrahim suka fara duka, durkushewa nayi a gurin na dora hannu na aka na fara rusa kuka ganin yadda suke ball da Ibrahim ta ko'ina. Banda Solomon wanda yake zaune a gefe ya dora kafa daya kan daya shan abinda yake cikin kofin hannunsa, wanda ko ba'a gaya min ba nasan irin abinda sultan yake sha ne, a cikin gida na ranar da aka kawo ni. Na rike rigar sultan ina kuka guiwowina a kasa "dan Allah Sultan ka kalle ni kaji abinda nake gaya maka, please ka hana su dukansa dan Allah" kamar wanda na kara tunzura shi ya juyo yace min "why? Me yasa ba kya so su dake shi? Saboda abinda ya fada gaskiya ne, saboda still kina sonsa?" Nayi saurin girgiza kaina nace "I don't love him sultan, I Love You, I chose you, I marry you. Menene kuma ya rage?" Cikin fada yace "you marry me sannan kika gayyato tsohon saurayinki cikin gida na?" Ban san sanda na dake shi a kafada ba nace "how can you say that? Come back to your senses Sultan" bai ce min komai ba sai tsayawa da yayi kamar mutum mutumi yana kallona, ta gefen idona na hango Solomon ya taso ya taho inda muke, yana karaso wa ya mika wa sultan kwalbar da take hannunsa, ba musu ya karba, da sauri na na fincike daga hannunsa na zubar da abinda yake ciki a kasa. Solomon ya saki baki yana kallona kafin ya fara magana "ni dama tunda aka bani labarin cewa our sultan has fallen in love with a good girl, nasan cewa we lost him, Sultan din dana sani ba zai zauna ayi masa irin cin mutuncin da aka yi maka ba, this means nan gaba sharing dinta za ka ke yi da sauran samarinta, only God knows su nawa ne, tunda baka san da wannan ba sauran ma ba zaka sanda su ba sai dai ka gansu a kan gadonta" a zuciye sultan ya juya ya kai masa duka yana cewa "shut up, damn you" ya rike hannun sultan yace "in baka son hakan ta faru then end it here, ka nuna min cewa har yanzu baka yi loosing guts dinka ba over a woman" hannunsa ya saka a aljihu ya zaro wani abu, ganin abun kawai ya saka naji wani zazzabi yana neman ya sauko min, Ya Allah intervene. Tunda nake ban taba ganin bindiga ba sai a film amma yau wai gani ga ita a daren farko na na aure. A hannun sultan ya saka bindigar yace a hankali "shoot him between the eyes, in kayi haka sauran babu wanda zai sake zuwa" gaba daya jiki na karkarwa yake yi dan bana jin bakina zai iya budewa har inyi magana. Amir ne ya karaso gurin da sauri fuskarsa cike da tashin hankali yayi kokarin karbar bindigar daga hannun sultan amma Solomon ya ture shi yace "stay out of this" yaje ya jawo Ibrahim wanda akayi wa laga laga, ya ajiye a gaban Sultan yace "Shoot him" na kama hannun sultan daya ke rike da bindigar nace "Sultan no" a hankali sultan ya dago kansa ya kalli Solomon yace calmly "no, I will not shoot him" ya juyo da jajayen idanunsa kaina ya ce "kince min you chose me over him, let's find out in gaskiya kike fada" ya saka min bindigar a hannuna yace "choose again, me or him" kallonshi kawai nake da mamaki, this is not my Sultan, this is someone else's. "Ki zaba, in har kina sonshi then put a bullet in me, in har kuma ni kike so kamar yadda kika fada then put a bullet in him" sama sama na ke jin sauran maganganun, naji Hafsat tana cewa da Sultan "baka da hankali Sultan? Menene hakan kake yi" na daga mata hannu alamar tayi shiru ba tare dana kalleta ba, no body will get hurt again a saboda ni, naji Solomon yana yiwa Sultan masifa "what if she shoots you?" Sultan yace "then so be it" Amir naji a kusa dani yana magana shima "Moon give me the gun" a hankali na fara jero sunayen Allah a zuciya ta, a take naji duk wani tsoro ya kauce min, na fahimci duk hikima ta ubangiji akan abubuwan da suka faru. This is a battle, Sultan's battle, between his good side and his bad side, I am his good side and Solomon and his other bad friends are his bad side. Yanzu na fahimci komai, na fahimci hikimar ubangiji da ya dawo da Ibrahim cikin rayuwata a wannan lokacin. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, it is destiny amma ba destiny din zamuyi aure ba. Allah ya dawo da Ibrahim rayuwar mu ne saboda yana son yayi amfani dashi yayi testing Sultan, wannan duk jarabawa ce, ni kuma zanyi iya kacin kokarina inga na taimakawa Sultan gurin cin wannan jarabawar. I now understand everything and I know exactly what to do. Na gyara rikon bindigar a hannuna, it is heavier than it looks. A hankali na dago idona ina kallon rinannun idanun sultan, na motsa bakina na furta I Love You amma ba tare da sauti ba amma na tabbatar ya fahimci abinda nace. Na daga bindigar a hankali ina kallonta, cikin second daya na juya ta zuwa kaina sannan na lumshe idona na dora dan yatsa na akan trigger kamar mai niyyar harbawa. Exactly abinda nayi tsammanin zai faru shi ya faru, kafin in dora dan yatsa na akan trigger Sultan yazo gurin ya doke hannun bindigar ta fadi kasa, dama ba wani rikon kirki nayi mata ba, tana faduwa ya kankame ni tamkar zai tsaga kirjinsa ya sakani a ciki, jikinsa gaba daya karkarwa yake yi. This is my chance, a hankali na fara yi masa magana, yadda babu wanda zai ji daga ni sai shi "Na zabe kane saboda ina sonka, na aure ka saboda ina sonka, ban gaya maka labarin saba saboda bana son in bata maka rai, amma ina son ka sani, babu sauran sonsa daya rage min a zuciyata saboda zuciyata taka ce. Bani nace yazo ba kuma bansan menene yasa yazo ba. Na ce maka ka hana dukansa saboda nasan cewa kai mutumin kirki ne, kuma mutanen kirki basa rama sharri da sharri, mutane ne masu afuwa masu tausayi, mutanen da ubangiji yake alfahari dasu. Nayi kokarin hana ka harbin sa not because I care about him but because I care about you. Kisan kai yana daya daga cikin manyan laifuka da Allah baya so, bana son ka dauki zunubin sa akan ka. Na juyar da bindiga kaina ne saboda in nuna maka how much I Love You. I Love you more than my life it self". Ya jima yana rike dani sannan ya sake ni ya juya da sauri gurin da Ibrahim yake yace masa " GO. But I swear to God, in na kara ganin ka ten miles close to my wife I Will Shoot you". Hafsat ce da Amina suka zo gurina, na rungume daya daga cikin su ba tare da nasan ko wacece ba. Ina jin hayaniyar gang bang "Sultan ya za'ayi ka bar shi ya tafi?" "Har cikin gidan ka fa ya shigo gurin matar ka, har yana ce mata ta gudu daha gurinka" "lallai Sultan ka zama nusari, you are no longer one of us" Sultan yace "gida na ne, kuma matata ce, kuma ni nace masa ya tafi. Duk wanda yake da problem da decision dina will settle it with me" ta gefen ido na naga Amir yana fita da Ibrahim da ga gurin, sannan kuma daya bayan daya suka fara fita, Sultan ne na karshen fita.

Gurin ya rage mu uku kadai, ni Hafsat da Amina. Idon Amina kawai na kalla nasan taci kuka ta koshi, tace "Moon dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan da akwai wani abu a tsakanin ku ba, da nasan haka zata faru wallahi da ba zan shigo dashi ba" na dafa kafadar ta nace "it is OK. Komai ya wuce ai. I have won" Hafsat ta dauko wayarta tace "yanzu zan kira daddy in gaya masa, gwara ya san matakin da zai dauka tun yanzu. In auren nan ba zai yiwu ba gwara a fasa shi kawai" na rike hannunta nace "me za'a fasa? Already an riga an daura. Menene amfanin gaya wa Daddy in banda tayar masa da hankali da zaki yi? Tun kafin a daura auren nan daga ni har Daddy mun san challenges din da zanyi facing. Tunda har yau na iya controlling Sultan na hana shi aikata mummunan aiki duk kuwa da cewa yana cikin

Please Login or Register in order to submit comment