Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai neme ni da kansa, saboda nasan da ya fara hankali zai fara neman ina mahaifiyarsa take, kuma nasan Sadiq zai gaya masa labari na kuma nasan zai neme ni. I waited years in and years out amma shiru. Babu irin abinda ba'a yi min ba akan inyi aure amma naki, ba wai sadiq nake jira ba, bana son sultan yazo ya tarar na sake wani family din, kar yayi tunanin na manta dashi ko bana sonsa, I stayed alone for him, very lonely. Ina kallon 'yan'uwana maza da mata kowa yana yin aure yana barin gida amma ni naki inyi aure. Ina ta lissafa shekarun sultan, lokacin da na san cewa he is old enough ace ya mallaki hankalinsa ya fara nema na, a lokacin na kara saka ran zuwanshi, ban taba tsammanin cewa dana bai ma san wacece ni ba, ban taba tsammanin Sadiq ya manta dani ba. Da shekaru suka ja sai na fara tsoron ko wani abun ya same shi shi yasa bai neme ni ba har yanzu" kuka yaci karfinta tayi shiru, sai data tsagaita da kukan sannan taci gaba "I was so lonely and depressed, sai babana ya bani jari yace in fara business, it will keep me busy as I waited for my son, nan na fara kasuwanci, from small scale ina dan siyan kayayyaki ina siyarwa, Allah ya saka min albarka a ciki, nan take arzikina ya fara habaka, within few years na fara aikawa kasashen waje ana saro min kaya ina siyarwa, har na zama dealer nake supplying manyan shagunan garin nan da kaya. Amma dai dai da rana daya ban taba cire ran sultan zai zo ba, tunda na gina gidan nan na dawo duk sanda mota ta tsaya a bakin gate sai gaba na ya fadi ina saka ran shine yazo, amma shiru. Na kebe kaina daga cikin mutane ne saboda bana son maganganun da akeyi a kaina. Nasan Zayed yayi aure amma bansan wa ya aura ba, lokacin da yazo nan shida sister dinki naga cewa she is African kawai sai naji ina sonta, I told her about sultan. You have no idea how I felt sanda kika ce min ke matarsa ce" ta goge hawayenta ta juyo tana kallona "How long do you think zaiyi taking kafin yazo?" Nace "one week, at most, two weeks, shima saboda sai ya nemi visa ne" . Tayi murmushi tace "then we will wait for him, together".

Episode Eighty Nine : Khairat 2
Na taso na dawo kusa da ita na zauna nace "yes Ummee, we will. Nayi miki alkawarin Sultan zai zo gidan nan, kuma in yazo zaki yi mamakin sa, dan duk wannan zuciyar da wannan fushin na dan lokaci ne, haka yake, akwai saurin hawa kuma akwai saurin sauka, I assure you yana ganinki shikenan komai zai wuce, he is just not sure of yadda zaki karbe shi ne, duk wannan girman jikin da wannan kwarjinin a ido ne kawai, in side him he is the kindest man I have ever known, yana da tsananin tausayi da kuma kokarin kyautatawa mutane, ko da kuwa wadanda suka zalince shine bai damu ba, he said kyautatawa mutane makes him feel good shi yasa yake yi, ballantana ke da kika haife shi, kallo daya zaiyi miki and it will all be over, he will take you in his arms and cry on your shoulders, he will love you fiye da yadda kike tsammani, zai zamar miki 'da daya tamkar da dubu, he will feel Lucky to have you as his mother" sosai Maganganu na sun kwantar mata da hankali dan har murmushi na gani akan lips dinta, ta kama hannayena duka biyun tace "Maimunatu bansan me zance miki ba daga ke har iyayenki, you are really an angel a rayuwar dana, bani da bakin da zan gode miki sai dai in dawwama har karshen rayuwata ina yi miki addu'ar" na dora hannunta daya akan cikina tace "ubangiji Allah ya jagoranci rayuwarki, da duk kanin zuri'ar ki, ya baku kyakykyawar rayuwa fil duniya wal ahkhira, Allah ya daga garajarki da duk kanin ahlinki, Allah ya kade duk wani sharri dake cikin rayuwar ku ya tabbatar da alkhairi a duk al'amuranki, Allah yayi miki sakayya a bisa duk abinda kika yi a rayuwar sultan. Allah ya albarkaci zuri'arki yasa su zamo sanyin idaniya a gare mu baki daya. Allah kuma ya kara soyayya a tsakanin ki keda mijinki, ya dauwamar da zaman lafiya a tsakaninku, ya sa ku kasance tare har karshen yaruwar ku" duk abinda take fada ina cewa amin, kuma ina jin dadi har raina, sai da ta gama yi min addu'ar sannan ta jawo ni jikinta ta rungume tace "Nagode Maimunatu".
Kwana biyu bayan nan, ni gani nake yi ma kamar nafi sultan damuwa, komai nake yi hankali na yana kansa, da kaina nace Hafsat ta bani sim card dina amma taki, kullum sultan yana cikin kiran wayar Hafsat, tun yana yi mata masifa har ya koma bata hakuri yana lallashinta, ita kuma tace sai ta rama fadan da yayi mata, innaji suna waya sai in ji kamar in kwace wayar amma nasan muna yin magana da sultan zai kalallame ni yace in dawo Nigeria, I don't think I can resist him in inajin muryarsa. Little khairat ce ta zama babbar kawara, tana ta rarrafenta ko'ina har ta fara tsayawa, in tana gurina babu abinda yake kaita gurin Hafsat sai in zata ci abinci. Ummee kuwa sosai muka kara sabawa da ita. Kamar yadda tayi min alkawari haka ta zage wajan koyamin girki, irin abincin larabawa iri iri haka take koyamin, babu abinda take so irin in zauna inyi ta bata labarin sultan, wannan kullum shine abin hirar mu. Hotunan sa kuwa na waya ta ta gansu yafi a kirga. A wayar Hafsat na hada ta da Mommy suka gaisa, nan take suka kulla kawance. Mommy ta gaya min ta yaba da ita tun kafin ma ta ganta.
Ranar dana kwana biyar a Riyadh, muna dinner da daddare sai ga kiran sultan a wayar Hafsat. Ta nuna min screen din sannan ta daga. Sun danyi magana sannan tace min "yace in ba zaki karbi wayar ba in saka shi a speaker zai yi miki magana, na kalli Ummee naga alamun anticipation a fuskar ta, she has never heard her son's voice tun da suka rabu, na gyada wa Hafsat kai, ta saka wayar a speaker ta ajiye a kusa dani, naji muryarsa "Moon please listen to me, why are you punishing me for the crime I didn't commit? Ni laifin me nayi wai? Kina so zuciyata ta buga in mutu ko?" Na danyi murmushi, dadin baki yake so yayi min, ya cigaba da magana, "Love please, nasan kinaji na, kuma nasan me kike so, I promise you zanzo amma kinsan it will take time, dan Allah na wahala haka, kar kice ba zaki yi min magana ba sai nazo, I can't take it kin sani" Ummee ta taso ta dauki wayar da fitar daga hands free ta miko min, na karba na ajiye khairat da take bacci a kan cinya ta, na mike na fita veranda, ina jiyo Hafsat tana gyaran muryar tsokana amma ban kula taba, na saka wayar a kunne na nace "My Love" kamar ba zaiyi magana ba amma ina jiyo numfashinsa a hankali, sannan yace "why are you doing this?" Nace "I just want you to come and see your mother, shikenan" yace "you should have talk to me ai, ki gaya min ga abinda kike so, you know I can do anything for you love" nace "nayi maka maganar ai kaki yadda, babu yadda zanyi da kai ne" ya dan yi shiru sannan yace "you have no idea how damn good it feels to hear your voice" Nace "me too" yace "ba wani nan, da kin damu dani ai da baki kashe wayarki ba, you always say kina sona but nasan ko rabin wanda nake miki ba kya yimin" nace "kai ma kasan ba haka bane ba. Kawai dai we show our love ne in different ways ni da kai. Zuwa na garin nan da kashe wayata da nayi are all ways of showing you how much I love you. Sometimes you have to sacrifice something to get something better" yace "zaki yi min dadin baki ko?" Nayi dariya, nace "tun da nazo garin nan bana samun bacci me dadi saboda babu kai, ba karamin dauriya nayi ba these five days" yace "uhmmm, na ji ki dai amma ban yarda ba, kina can kina sharar baccin ki kin barni da rungumar pillow da mafarkai ko?" Nace "sorry" yayi ajjiyar zuciya yace "so, how is she?" Nace "come and see for yourself" yace "hmmm baza ki fada min ba kenan ko?" Nace "eh din. In kana son kasan ya take kazo da kanka ka ganta" yace "I will come ai, na gaya miki zanzo. Ina baby na kuma? Haka kawai kin raba ta da daddyn ta" nace "na gaya maka namiji ne fa ba mace ba, he is fine. Can you believe Ummee tana taba cikina ya fara motsi" yace "what? You mean she touched your tummy?" Nace "yes, she does, she is really nice Sultan" muka ci gaba da hira, sam ban san time yana ta tafiya ba, haka muke dama duk sanda muke tare da sultan ko a fili ko a waya ji muke yi kamar time ya tsaya. Sanda ba koma ciki na tarar har kowa ya kwanta, dan haka nima na shirya na kwanta, da safe Hafsat tazo ta cillo min sim card dina tace "bani wayata" na mika mata nima na kunna tawa.
Kwana na goma cif a Riyadh Sultan yazo, tun sanda yayo waya cewa zaizo gaba daya ummee ta tayar da hankalinta, ana gobe zuwansa kuwa sam bata yi bacci ba, daga baya ta tashi ta fara salloli tana rokon Allah for courage. Ni kam tausayinta nake ji har raina, ban san ya take ji a ranta ba. Twelve na rana jirgin su sultan zai sauka, abinciccikan da muka shirya masa nasan duk cinsa sai ya gaji ya bari, Hafsat tana dariya tace "Moon gwara ki tanadi maganin gudawa a kusa". Muna gama shirya komai na tafi daki nayi wanka, ina fitowa Ummee ta shigo ta kawo min wata doguwar riga pink mai ratsin blue a sides dinta, sai stones a gaban rigar, da viel shima blue. Tayi kyau sosai rigar. Na karba nayi mata godiya. Kwalliya na zauna na tsara sosai, na saka rigar naga tayi min bala'in kyau, na fito palo na bar ummee itama tana shiryawa itama. Lokacin dauko shi yana yi zayed yazo, nace su tafi kawai shi da Hafsat ni na jirashi a gida, Hafsat ta kalle ni tace "you are wicked" nayi dariya kawai. Nasan halin sultan, ba karamin aikinsa bane yana ganina a airport ya ce komawa zamuyi, ko kuma in babu jirgi yace mu kwana a hotel da safe mu koma, nayi wa ummee alkawarin zan kawo mata sultan har gida and am going to keep that promise. Su Hafsat suna tafiya sai ga Ummee ta fito, ta saka riga irin tawa sai dai tata blue ce da ratsin pink, tayi nadin veil mai kyau, ta zo ta zauna a kusa dani tayi irin zaman da tayi ranar da zanzo, at the edge of the seat da hannayenta a tsakanin cinyoyinta, muna nan zaune babu wanda yayi magana har muka ji karar bude gate, daganan muka ji tsayuwar mota da sound din bude mota da rufewa, naji ummee ta kama hannuna ta rike kam, na kasa kallon fuskarta, a hankali muka ji an bude sliding door din palon, idona na kafa a gurin, na ganshi ya shigo, bakin wando ne geans a jikinsa mai kauri, da farar shirt yayi stocking ya daura bakin belt, gashin kansa a tsatstsaye kamar wanda ya tashi daga bacci, nasan abinda yasa yayi wannan shigar, so yake ya nuna wa ummensa what he used to be. Idanuwansa a kanmu muma namu a kansa, ya saki jakar hannunsa ta fadi a kasa, ummee ta saki hannuna ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, ya kalle ta for some seconds sannan ya dawo da idonsa kaina. Na mike tsaye nima, da sauri ya karaso inda muke, ban ankara ba kawai sai ji nayi ya jawo ni jikinsa ya rungume, na fara kokarin ture shi amma yaki ya sake ni, ya saka fuskar sa a wuyana, a hankali nace "sultan ummee fa tana kallon mu" yace "i know" Nace "go to her" ga mamaki na sai cewa yayi "kunyar ta nake ji" dariya na fara yi kasa kasa, ummee ta zagayo ta bayansa tana kallona tace "me yake cewa?" Ina dariya nace "wai kunyarki yake ji" ta danyi murmushi kwalla ta fara taruwa a idonta, ta dora hannunta a hargitsatstsen gashinsa tana shafawa tace a hankali "my little love" ai kuwa ya sake chusa kansa a wuyana yace "am not little" ta sake cewa "me yace?" Nace "wai he is not little" tayi dariya hawayenta suna karasa saukowa tace "to shikenan, ka koma big love yanzu" har yanzu ya kasa dago fuskarsa ya kalle ta, ni kam dariya kawai nake yi, ban taba ganin sultan yana jin kunyar wani ba sai yau, yace a hankali "yanzu sai tace zata fara pampering dina kuma" tace "ai har na hada maka bottle, yanzu zanje inyi warming in baka" ta dora kanta a bayansa hawayenta yana zuba a jikin rigarsa, ni kam dariya kamar cikina zai yi ciwo, lokaci daya kuma sai ya sake ni ya juya ya rungume ta, take ta saki kukanta gaba daya, na dan ja da baya ina kallon su ina jin dadi a raina, a hankali na sulale na bar musu palon.

Episode Ninety : His Mother's Son
Bedroom din Ummee na shiga na turo kofa, na zauna a bakin gado ina ta murmushi ni kadai like an idiot, reaction din sultan ya bani mamaki kuma ya kara tabbatar min da cewa there is no one like mother. Na san dama zai sauko amma banyi tsammanin saukowar shi da sauri haka ba. Wai kunyar ta yake ji, sultan ne wai da kunya, abin ma abin dariya. Na gaji da zama na jawo pillow na kashingida ina jin farin ciki sosai a raina, burina ya kusa cika, nayi wa kaina alkawarin I will totally change sultan's life around kuma so far babu abinda zance sai Alhamdulillah. Wannan duk ba yi na bane yin Allah ne. Ina nan kwance har akayi sallar azahar na tashi na naje nayi sallah, ina idarwa na koma nayi kwanciya ta, na dauki waya na kira Hafsat tace min sun fita da zayed da khairat, ina nan a kwance sai ga Ummee ta shigo, ta tsaya a bakin kofa tana kallona sannan tace "waye zaiyi serving mijinki abinci da kika zo kika kwanta?" Na dan tashi ina dariya, ta daga gira tace "he has been asking for you, yaki cin abincin ma, wai shi kunya ta yake ji" na tashi na gyara veil dina muka fita tare. A dining na same shi ya tisa abinci a gaba ya zuba uban tagumi, na dan yi gyaran murya, ya juyo da sauri, ina kallonsa har da ajjiyar zuciya ya taso ya taho, na fara waige waigen ummee amma naga bata gurin, na karasa nima gurinsa na shige cikin kirjinsa ya rufe ni da hannayensa, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, sosai nayi missing mijina, na lumshe idona ina shakar kamshinsa da yake kwantar min da hankali a koda yaushe, nace "I missed you, mijina" ya danyi dariya yace "ba zan yi magana ba ni, a aikace zaki ga kalmar missing din" na dan ture shi nace "nan dai gidan ummee ne ba gidan mu ba, dan haka mind your steps" na fara tafiya dining ya biyo ni, yace "ai itama tasan ba zata hanani matata ba, in kuwa ta gwada to akwai rigima" na jawo masa kujera ya zauna, na sunkuya dai dai fuskarsa nace "albishirinka?" Yace "goro" nace "a dakin ummee nake kwana a kan gadonta tare da ita" ya yamutsa fuska yace "da kenan, likacin bana nan, yanzu nazo dole a bani matata" nace "to idan tazo sai ka gaya mata" yace "kunyarta nake ji. Shine dazu kika gudu kika barni tare da ita ko?" Na fara bude masa dishes din gurin nace ya zabi wanne zanyi serving dinsa first, amma ga mamaki na sai naga sam bai wani rude akan abincin ba kamar yadda nayi tunani, ni kawai yake kallo, nace "food always come first, hausawa suna cewa ci shi yake gaba da sallah ma" ya daha gira yace "not to me" sallamar ummee mukaji, ina kallon sultan ya wani sunkuyar da kansa kasa, kamar zanyi dariya na maze na fara zuba masa abinci, ummee ta karaso ta zauna tana kallonsa yadda yake juya cokali a cikin abincin, ta kalleni tace "in bashi yake so ba ki zuba masa wani mana" ya dago kai yana kallona yace 'it is OK, am just tired ne, shi yasa" tace "try to eat something then, sai kaje kayi wanka ka kwanta ka huta" yana kallona nayi sauri na dauke kaina na tafi na fara serving ummee, nima na zuba abinci na na fara ci, ummee gaba daya hankalinta a kansa yake, nima ina kallonsa ta gefen idona, a hankali ya fara cin abincin kuma, sai kuma ya fara ci da dan sauri, muka hada ido da ummee mukayi murmushi, yace "this food is really good" nace "ummee ce ta yi shi, for you, ita ta girka all this food, for you" yana shafa kai ya dan kalleta yace "thank you" tace "bani kadai nayi ba ai, tare da maimunatu mukayi" ai kuwa sultan ya zage yaci abincin sosai, kusan komai sai da na zuba masa yaci, yana ci kuma yana santi, ummee sai tsokanar sa take yi yana zuba mata zance, kunyar ta fara tafiya. Muna gamawa ummee tace "an kai maka kayanka dakinka, maimunatu sai ki raka shi yayi wanka ya huta ko?" Na dan bata rai irin ni bana so din nan, ya mike ya fara tafiya, har yakai bakin kofa ya juyo yana kallona yace, "ban san gurin ba fa, sai anzo an nuna min" ummee ta harare ni tayi min alamar go da hannunta, ni dai duk kunya ta ishe ni, na bishi a baya. Muna fita nayi gaba, nasan gurin dama ummee ta nuna min sanda ta zagaya dani gidan, katon palo ne da three bedrooms, komai na gurin red and cream ne, hatta electronics din gurin. Muna shiga ya rufo kofa yana kallona, nace "welcome to gidan ka da baka san dashi ba" kallo daya yayi wa dakin yace "wato da ba zaki zo ba ko?" Na saka hannu ina shafa sajen sa, ya lumshe ido yana kara kwantar da fuskarsa a hannuna, nace "Ummee tana gurin kuma sai kawai in yi saurin tahowa? Kai ma kanka kake cewa kana jin kunyarta ballantana ni?" Ya dora hannunsa akan cikina, sai kuma ya danyi murmushi yace "ya naji kamar ya kara girma ne wai? How is she?" Nace "He is fine, yayi missing Daddy dinsa". Bedroom daya na kai shi na hada masa ruwan wanka, shi lallai wai sai dai muyi tare ni kuma bana son in bata kalliyata ummee ta gane. Amma ina sam bai fahimci wannan yaren ba, da nayi masa taurin kai ma dauka na yayi har ni har kayan jikina ya saka a tub, ba kwalliya ba har kaya na ma na bata kenan. Ba zan iya lissafa tsahon lokacin da muka bata a bandakin ba, dan anan aka nuna min duk missing din da ake ta fada min kuma na fahimci lallai anyi missing din nawa. Sai daya karar min da duk energy na dan kasa fitowa nayi daga toilet din sai shi ya fito dani ya dora akan gado, ya kunna room heater ya saka jallabiyya ya fita, naji dadin dumin da dakin yayi na fara bacci, cikin baccin naji dawowarsa, na dan bude ido na ganshi da tray a hannunsa, ya ajiye yana cewa " kinsan dai babu kyau baccin la'asar kuma kike yi ko?" Na dan tashi ina kara jan bargo jikina, ya kama bargon zai cire na saka kara yayi dariya yace "as if U don't know what is there" nace "oho dai, ba zan bude ba" to amma dai zaki sha madarar nan ko? Tunda kince na karar miki da karfin ki to gashi nan na biya ki" ya zubo madarar ya miko min, shima ya zuba ya zauna a bakin gado yana sha. Anan yake bani labarin da kyar Takawa ya barshi ya taho, yana so yazo din kuma baya son rabuwa dashi. Muka zauna kowa yana bawa dan uwansa labarin abinda ya faru bayan rabuwa, amma sam ban bashi labarin da ummee ta bani ba, a ganina wannan ba hurumi na bane ba, nafi son ta bashi labarin da kanta yadda hakan zai kara karfafa alakar su. Sai da mukayi sallar magrib sannan muka fara shirin fita, ga kayana har underwears a jike a toilet, na rasa inda zan saka kaina, sultan ya saka kaya yabani jallabiyar sa yace in saka, na saka na dauki mayafin doguwar riga ta na saka, muna fita dakin da aka sauki Hafsat na tafi da sauri dan bana son Ummee ta ganni, Allah ya taimake ni dakin a bude yake na shiga na samu kayan ta na saka sannan na tafi palon ummee, sultan na gani a bakin kofa wai kunya yake ji ya shiga shi kadai, ni kuma nace kunya nake ji mu shiga tare, muna ta muhawara sai gata ta bude kofar tana kallon mu, duk muka sunkuyar da kai kamar wasu munafukai, tace min "shine kika gudu kika barni da girki ni kadai ko?" Na dan sosa kaina nace "I tot abincin dazu zai isa har dare" tace "sai kije kiyi arranging table din" ta matsa ta bamu guri muka shigo, tana kallon sultan tace "welcome little love" da alamar tsokana a muryarta, ai kuwa sultan harda rufe fuska, ni kam dariya nake masa, ni banga abin kunya a uwa ba, tana shiga daki ya biyo ni dining room "wai baki lura cewa she looks too young ba?" Nace "eh na gani mana, amma ai dama jikinsu da namu ba daya bane ba, plus bata hayaiyafa ba, haihuwa kuma tana daga cikin abubuwan da suke saka mata tsufa" yace "ni kunyar ta nake ji wallahi" nace "wai menene abin kunyar a ciki?" Yace "yanzu fa kinsan tayi min tsarki ina baby, nayi mata a mai a jiki" nace "amai kadai? Kayi mata kashi kayi mata fitsari duk a jikinta" da sauri yace "no, banyi ba" nace "in tazo a tambaye ta?" Yace "a'a a bar maganar kawai" nace "she gave birth to you sultan, she nurse you, she fed you, and she loves you more than anything in this world". Kafin mu fara dinner na kira Hafsat tace min ba zasu dawo yau ba, a gidan su zayed zasu kwana saboda suna shirye shiryen komawa England. Muna gama dinner nace da ummee bara in je daki, ina shiga daki nayi kwanciyata sabida dama sultan ya tara min gajiya. Sai wajan ten na tashi nayi sallar isha, na dan bude kofa na leka falo, still sunanan, sultan na gani durkushe a gaban ummee ya dora kansa akan cinyarta, bana ganin fuskarta amma ina jin muryarta tana masa magana da alamar tayi kuka, na mayar da kofar na rufe na koma na cigaba da baccina. Cikin baccin naji tana tashi na, na farka da kyar ina kallonta, tace "tashi ki tafi dakin mijinki, da safe kya dauki kayanki" zance nata a'a tace "I insist" dole na tashi na dan dauki abubuwan da zan bukata, itace ma mai tuna min da wani abin, ni dai duk kunya ta ishe ni, na dau kayana na fita. Ina shiga part din sultan na tarar har ya kwanta, motsina ne ya tashe shi, ya na kallona nace "ta koro ni" har da dan rawarsa yace "uwa dadi" na dan fara kuka

Please Login or Register in order to submit comment