Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Har karfe goma ina zaune a palon amma sam hankali na baya tare dani. Only God knows a ina sultan yake kuma me yake yi. Na tashi nayi musu sallama na tafi daki, na kira wayar sultan tana ta ringing babu answer. Ko da ace Sultan ya daina shan giya amma temptation fa? Musamman idan ya ga ana sha, ballantana nasan zasu iya bashi su ce sai yasha. A automatic redial na saka wayar na kuma saka ta a speaker na kwanta, kiran yana ta shiga har wajan 30minutes bai dauka ba, ina cikin haka Amina ta shigo, ta kalleni tace "ba dai Sultan kike kira ba? Ke ma kinsan kina bata lokacin ki da battery din wayarki ne a banza amma ba dauka zai yi ba" ina kallonta ta gama shirin kwanciya ta hawo kan gado ta kwanta, nace "Amina, what do you think maza sunayi a bachelor's night?" Tace "hmm, a England an taba bikin wani dan ajin mu, mazan suka shirya masa bachelor's night, washegari very few ne suka zo makaranta, saboda sauran all got drunk the other night ba zasu iya zuwa ba. Na tambayi wani a cikin su,why?, sai yace ai suna celebrating last day of freedom din su ne, in suka yi aure kamar they are bond to their wives babu sauran sakewa suyi abinda suke so. So duk abinda namiji yafi enjoying shi zai yi a daren, in mashayi ne in manemin mata ne sai yayi kayan sa one last time" tayi sauri tace "amma fa ba ina cewa abinda sultan yake yi kenan yanzu ba, it depends on mutun. Ke kinsan Sultan kinsan me zaiyi kinsan kuma menene ba zai yi ba" bance mata komai ba amma zuciyata in ban da zafi babu abinda take yi, har yanzu kira nake kuma har yanzu bai dauka ba. Ba'a jima ba Amina tayi baccinta ta barni, har na fitar da ran zai dauka kawai naji ya dauka, gurin da yake hayaniya ne kawai da kida yake tashi a gurin, yace "Hello, love, bakiyi bacci ba" nace "sultan where are you?" Yace "muna gidan Solomon, wani abu ne?" A hankali nace "Sultan I want you to come back home" yace "why? The party hasn't even started yet" ina jin wani a gurin yana cewa "chafdi, Sultan wannan amaryar taka in aka gama bikin nan ko kofar gida ba zata ke barin ka kana fitowa ba" duk suka kwashe da dariya, Sultan ya dan matsa daga gurin su yace "why?" Nace "ni kawai bana sonka da mutanen nan wallahi" yace "Moon, this is my party, saboda ni suka shirya shi. I can't just leave" naji wani abu ya tsaya min a makogwaro na. Kafin in san me zance masa wani a cikin su ya karbe wayar yace "look amarya, we are going to get your ango drunk today, he is even lucky he don't do women, amma shima in kika sake kiransa we will make him do it even if we have to tied him to the bed" Sultan ya warce yawar yana ce masa "fuck you" da sauri yace min "Moon" ban jira abinda zai kuma cewa ba na kashe wayata. Kafin in ajiye ta ya kira, ban dauka ba, ya sake kira na kuma share shi. Zafi nake ji sosai a raina. Sai da yayi five missed calls sannan ua hakura. Na runtse idona ina addu'ar Allah yasa in iya bacci amma sam babu bacci a idona. Ina tsakiyar tunani na naji wayata ta cigaba da kara, nayi niyyar in sake rabuwa dashi amma na daure na dauka, bance komai ba yace "kinyi fushi ko?" Naji inda yake babu hayaniya, amma duk da haka bance masa komai ba, ya sake cewa "gani a balcony dinki, ki bude min kofa"
I hope duk wacce take karanta littafin nan zata so saurayinta/mijinta kamar yadda Moon take son Sultan, duk wanda yake karantawa kuma shima zaiso budurwarsa/matarsa kamar yadda Sultan yake son Moon. Remember, Love is the strongest magic of all.
Stay loved.


Episode Sixty Eight : The Wedding Night

Na kashe wayar na mike da sauri na zura dogon hijab dina na bude kofar balcony. Yana tsaye ya jingina a jikin railer yana murmushi. Wandon jeans ne a jikin sa army green da farar singlet yayi stocking dinta a cikin wandon ya daure da belt, sai light green din top wadda ya balle duk maballayenta ya barta a bude, iskar da ake kadawa a gurin tana ta diban rigar tasa kamar zata chire ta. Na dan bata rai nace "Sultan me kake yi anan cikin daren nan" shima bata ran yayi yace "to tunda kin hanani zama acan ba sai in taho nan ba. Ni nasan kona kwanta yau ba zan iya bacci ba, ba gwara in taho nan ki tayani hira ba" naji dadi har raina dana fahimci ya bar gurin partyn saboda nace bana so, nasan it was a hard decision but a good one. Na jawo kofar na rufe saboda tinawa da nayi cewa Amina tana cikin dakin, na karaso inda yake na jingina da railer nima ina kallon kasa nace "thank you" yayi ajjiyar zuciya yace "I will never do any of those things da Daniel yake fada" nayi shiri ban ce komai ba, ya danyi dariya yace "they will kill me in suka kamani gobe da safe, dan duk cikin su babu wanda yasan na fito, sai daga baya zasu lura bana nan" ya dauko wayarsa a aljihu yayi switching off ya mayar aljihun sa. Ya kalleni ya fara murmushin muginta yace "but there is a price for everything, tunda kika hana ni kwana a gurin party na to yau a dakinki zan kwana" nima murmushin muguntar na mayar masa nace "bismillah, ina nuna kofa" babu musu yaje ya bude kofar, sai yayi sauri ya rufe ya dawo da baya, dariya nayi sosai nace "ka shiga mana, wallahi in ta fara ihu sai duk mutanen gidan nan sun tashi daga bacci" ya dan jima yana tunani sai kuma ya sake bude kofar, ina hango yadda Amina ta kudundune a cikin bargo tana baccinta, hannu ya saka ta bayan kofar ya zare key din jiki sannan ya mayar da kofar ya rufe yayi locking ta waje ya saka key din a aljihunsa yace "then we will sleep here" da mamaki nace "you are not serious are you?" Yace "sa ido kiyi kallo" daga haka ya tafi ya kwanta rigingine a kan carpet din da yake gurin. Tsayawa kawai nayi ina kallonshi naga yayi pillow da hannunshi ya rufe ido, gaba daya rigar ta bar jikinsa sai singlet din kawai. Nayi sauri na dauke kaina na daina kallonsa na koma ina analysing situation din, nayi tsaki a raina ina cewa 'Sultan, wannan fa shine baccina na karshe kafin aure a gidan mu amma ba zaka barni in kwanta a gado na ba'. A kwai security light sosai a compound din gidan amma duk waje suke haskawa, wannan ne ya kara wa balcony din duhu, ma'a na babu wanda zai hango mu daga waje amma mu zamu ke ganin su. Amma Amina da take daki zata iya farkawa kowanne lokaci taga bana nan. Already jikina ciwo yake min saboda gajiya amma kuma ace zan kwana akan carpet. Amma kuma gwara haka da ace Sultan ya kwana a gurin wadannan mutanen. Sai dai ni ban yarda inje kawai in kwanta a kusa da Sultan ba. Na zauna akan kujerar da take gurin na kudunduna a cikin hijab dina, kadan kadan nake kallon sultan har daga baya bacci ya dauke ni.

Cikin bacci naji ana shafa lips dina, a hankali na bude idona da suka yi min nauyi saboda bacci, fuskar Sultan na gani dab da tawa yana kallon fuskata. A hankali tunani na ya fara dawowa, nayi sauri na mike zaune amma maimakon in ganni a kan kujerar dana kwanta sai na ganni a kasa a kan carpet nayi pillow da damtsen hannun Sultan. Na juya na kalli sultan naga ya chire rigarsa complete yayi pillow da ita sai singlet dinsa kawai. Nayi sauri na kalli nawa jikin naga hijab dina yana nan amma duk da haka ban yarda ba sai da nayi ta taba jikina wai ko zanji wani chanji. Duk abinda nake sultan kallona kawai yake yi yana dariya, sai da ya gama dariyar sa sannan yace "Don't worry yau ne ba gobe ba. And when I touch you ko tashi zaune ba zaki iya ba" na bata rai nace "wa yace ka dauko ni daga inda na kwanta? Ka hana ni kwanciya akan gado na kuma kan kujerar ma sai da ka raba ni da ita" ba tare dana jira amsar saba na mike tsaye ina kallon waje, I don't know the time but nasan assuba ta kusa, ya mike shima yana zuwa rigarsa ya karaso kusa dani yace "zanje in shirya, karfe shida zamu bar nan saboda muje akan lokaci" ban bashi amsa ba ya kara matsowa kusa dani yace "are you scared?" A hankali nace "yes" yace "me too. I am scared I might fail you as a husband. Na sani kamar yadda mutane suke ta fada min koda yaushe cewa I don't deserve you. Ni kaina bansan dalilin da yasa Allah ya bani ke ba, kin fi karfi na nesa ba kusa ba. Amma abinda na sani without doubt shine ke alkhairi ce a gare ni" ya riko fuskata da hannayensa yana kallon cikin idona yace "I promise you like I always did, I will never let you down. Abinda nake bukata daga gareki shine ki kara hakuri dani. I promise you you will never regret marrying me" na lunshe idona ina jin dadin maganganunsa sannan a hankali na bude ina kallonsa nace "kar kake cewa bakayi deserving dina ba sultan, you deserve more than me. Dan haka ni ya kamata inji tsoron kar inyi failing dinka, kar in gaza baka farin cikin da kayi deserving. And I promise you, I will never regret marrying you". Expression din fuskar sa is very clouded, irin yanayin da bana iya karantar sa, ya jawo ni da sauri ya rungume a jikinsa, ban hana shi ba, ya jima sannan ya sake ni ya kamo sannuna ya saka min key din kofar sannan ya haura railer ya juyo yana kallona yace "see you on the other side wife" daga nan ya dirga kasa. Ina kallonsa ya yi hanyar part dinsu da sauri.

Na jima a tsaye a gurin ina kallon hanyar da yabi sannan na juya na shiga daki. Direct toilet na shiga nayo alwala nazo na fara sallali ina rokon Allah alkhairan da suke cikin auren nan da kuma tsari daga sharrukan da suke cikinsa, ban jima ba aka fara assalatu, na tashi na kawo raka'atainil fajri sannan na dora da subh. Ina idar wa Mommy ta shigo tace min "kizo inji Daddy n ku" na mike na bita a baya har part din Daddy, ina shiga na tarar dashi a zaune yana shan coffee, ya shirya tsaf daga dukkan alamu daga nan sai gurin daurin aure. Ba zauna a kasa na gaishe shi ya amsa mun fuskar sa a sake. Sai da ya gama shan coffee dinsa sannan ya fara min magana "maimunatu yau Allah yayi insha Allah nan da 'yan awanni zamu daura miki aure da Sultan wanda ke kika zabe shi da kanki mu kuma muka goya miki baya har Allah ya tabbatar mana da abin. To so far dai babu abinda zance sai Alhamdulillah. Na amince zan aura miki Sultan ne saboda abu biyu, na farko ina kwadayin ladan da zamu samu daga ni har ke in har burin mu ya cika na gyara rayuwarsa, abu na biyu kuma saboda tsananin sonki da naga yana yi, nasan wannan soyayyar zata iya saka shi yayi komai, wanda nake saka ran soyayyar ki zata iya saka shi ya chanza rayuwarsa. Auren Sultan da zakiyi tamkar jahadi ne. Duk abinda nayi a rayuwar sultan tamkar sharar fage ne akan wanda ke zaki cigaba dayi bayan auren ku. Sai kin dage sosai maimunatu. Nasan ke yarinya ce mai ibada amma ina so ki kara akan wacce kike yi da, ki dage da adduoi na neman tsari sannan ki tsarkake zuciyar ki daga dukkan sharri. In sha Allahu Allah yana tare da ke kuma bazai barki ki tabe ba. Ina son ki sani cewa dani da Mommy n ki muna tare dake 100% amma hakan ba yana nufin muna so mu san duk wani sabani daya shiga tsakanin ki da mijinki bane, duk abinda ya faru tsakanin ku mun fi son ya kasance ya tsaya a tsakanin ku, sai dai in har kinga yafi karfin ku sannan sai ki kawo mana shi mu kuma zamu yi iyakacin kokarin mu muga an samu maslaha a lamarin. Allah yayi miki albarka Allah, Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki" Mommy tace "Ameen" ya tashi yace "nina tafi" sai da suka fita shida Mommy sannan na lura cewa kuka nake yi ashe, ba goge hawayen idona ina jin alamar jikina yana daukan zafi kamar mai shirin fara zazzabi. Ina nan zaune har Mommy ta dawo daga rakiyar Daddy ta zauna kusa dani ta kamo hannayena tace "kuka kuma maimoon? Wa yace miki yanzu 'yammata suna kukan aure?" Nayi mamakin yadda Mommy take min magana a hankali cikin rarrashi babu fada, nan ta shiga yimin tata nasihar da kuma bani shawarwari akan harkar auratayya, na koma na kwanta akan cinyarta ina sauraronta kuma ina daukan duk abinda take gaya min. Muna a haka Hafsat ta shigo da khairat a hannunta suka hadu ita da Mommy suke ta kwantar min da hankali, Hafsat tana tsokanata da cewa "ke da zaki zauna ma a kusa da gida? Ko ihu kikayi da karfi Mommy zata jiyo ki" na dan yi murmushi kadan. Wayar Mommy tayi kara aka sanar mata mai gyaran jikina tazo, muka sauka kasa mukayi breakfast first sannan aka fara yimin kitso, dama na gaya mata ina son tayi min kitso shi yasa ma tazo da wuri. Kanana kitso ne irin na bare bari akayi min da kitson gaba da matar tayi masa wata tubka wacce ta rufe rabin ido na na hagu. Kowa yaga kitson nan sai sambarka. Bamu gama ba sai wajan sha daya da rabi. Ni dai duk hankali na baya kan wanda suke tare dani kallon agogo kawai nake yi gaba na yana faduwa, har daci nake ji a bakina. Ana gama yi mun kitson na sulale na gudu na tafi dakin daada, duk babu kowa a ciki dan duk suna part din mu, na shige cikin bedroom dinta na kwanta ina jin temperature dina tana kara hawa. 12:00 nayi na runtse ido na ina karanto duk adduoin da aka koya min a islamiyya. Around 12:30 na jiyo guda cikin gidan mu, gaba daya an dauki hayaniya. Nan take hawaye ya balle min. Kuka nake yi sosai amma ni kaina bansan dalilin kukan nawa ba. Shin na murnar na zama matar Sultan ne ko kuma na menene oho. Nasan ana can ana nemana a cikin gida dan ko waya ta ban taho da ita ba dan kar a kira ni. Suwaiba, wata 'yar uwar mu daga Niger ce ta shigo dakin ta ganni around 1:00 da sauri ta fita ina jinta tana bada sanarwar ai gani can a dakin daada. Kan kace kwabo dakin ya cika, tsofaffi da 'yammata sai tsokana ta suke wai azo aga amaryar zamani amma tana kuka, ni kam kamar kara zugani suke yi dan kuka na kawai nake yi bana sauraren su. Umma ce, babar Amina tazo ta fito dani tace su daina tsokana ta, ta shiga dani har dakina itama ta sakani a gaba da nasiha, Amina har da yimin video wai sai ta nuna wa Sultan dan yasan cewa ashe duk I love you din na karya ne bai kai zuci ba. Ina daukan waya ta naga 13 missed calls daga sultan, a raina nace "wasa ma kenan, kai da kaji muryata kuma ai sai dai acan" .

Sallah kadai na samu nayi dan abinci ma kasa saka shi nayi a bakina, aunty zaliha ce ta saka ni a gaba da kyar na iya cin loma biyar nace na koshi. Mommy ta shigo ta kawo min magani na tace in sha, na karba ba musu na shanye. Idon Mommy kawai na kalla nasan itama kukan ta gama. Ina jin Hafsat tana kiran mutane su zo su ga hoton ango a waya, suna ta yaba kyan da yayi amma ni kam na kasa kalla. Daga baya naji suna waya da Hafsat tana gaya masa wai gani nan ina ta kuka, ta miko min naki karba sai ta saka shi a hands free "kiyi hakuri amaryata ki daina kuka, gani nan akan hanya, ina shigowa abuja zan zo in rarrasheki da kaina. Kuma duk wanda ya tsokane ki ki rubuta min sunan sa ni kadai nasan abinda zanyi masa" daga jin yadda yake maganar kasan shima dariyar yake yi, na karbe wayar na kashe, ni banga abin dariya ba dan ina kuka anyi min aure. Mai gyaran jiki na ta hada min ruwa tace inje in shiga, na shiga na kwanta ina lissafin shikenan fa, yau na taka wani stage na daban a rayuwaya, yau wani nauyi babba ya hau kaina, shi kenan na zama matar aure. Bayan an gama yi min wankan na shafe jikina da wannan man da ta bani na musamman, ta hada min turaren da nake tsugunnawa akai shima nayi. Muma gama wa da mai gyaran jiki mai kyalliya tazo muka fara, na gaya mata yau bana son heavy make up light zatayi min dan haka ba mu dade ba ta gama min. Yau shadda na saka fara tas da bakin aiki a jiki, komai da na saka fari ne. Irin shigar da Sultan yayi kenan ta daurin aure. Da dankwalin shaddar aka yi min gwaggwaro. Mommy ta shigo da wani dan karamin box a hannunta ta fito da complete set din sarkar gold, da kanta ta saka min, nan na kara fitowa tar dani. Ina yin sallar la'asar aka saka farin mayafina aka rufe ni ruf har fuska aka saukar dani kasa zuwa dakin Hafsat, karfe biyar 'yan daukan amarya suka zo, ai ina jin zuwansu na kankame Mommy na fara sabon kuka, itama biye min tayi muka yi ta rusa kukan mu, sai da wata kanwar daada tazo sannan ta kama yi wa Mommy fada. Yaya ce da kanta tazo dauka na, inna ce ta bayar dani ta danka hannuna a hannun yaya, ni dai idona a rufe, ji nayi an lullube ni da wani abu mai kauri yana wani kamshi na musamman, ashe alkyabba ce. Babu abinda nake ji sai guda ta ko ina. Haka ina ji ina gani aka fita dani daga gidan mu aka sakani a mota, da jiniya da komai aka tafi dani palace. Yaya da inna su suka saka ni a tsakiya. Tun da nake ban taba shiga palace ba sai yau. Kuma yau din ma fuska ta a rufe take dan haka babu abinda na gani.

Cikin gida aka fara shiga dani direct part din Hajiya. Ina jin muryoyin su Fa'iza suna tsokana ta amma ban kula su ba. Da fara'a da komai Hajiya ta tarye mu. Duk da cewa fuska ta a rufe take amma na fahimci shima gidan a cike yake da mutane. A nan Umma kuma ta bawa Hajiya amana ta ita kuma tace ta karba. Sai da akayi sallar magrib sannan aka tafi dani gidana. Tafiyar kusan unguwa guda ce kafin gidan. Tun daga waje mutane suke kiran masha Allah, inna ta sakani nayi bismillah sannan na shiga da kafar dama. Direct cikin bedroom dina aka wuce dani, gidan gaba daya kamshi yake yi saboda tun safe Mommy ta aiko aka kara gyarashi aka saka fresheners a ko ina. Ko ina an bude a gidan saboda mutane su gani, part din Sultan ne kawai a rufe. A hankali mutane suka fara watsewa, iyayena duk suka zo sukayi min sallama suka tafi, daga karshe ya rage daga ni dai kawayena wadanda zasu zauna saboda partyn da za'ayi in an jima wanda kuma zai yi serving a matsayin siyan baki.

Amina ce ta mintsine ni tace "to sun tafi, sai ki bude fuskar ai" sai da na leko na tabbatar babu wani babba a dakin sannan na bude idona. Hasiya tace "au ashe kukan ma harda na munafunci a ciki" na murguda mata baki nace "eh din" suka saka dariya. Zulaihat tace "Moon gidanki yayi kyau, masha Allah" nace mata "nagode" Hafsat tace "kunji rashin kunyar ko? Ki bar mu muyi godiyar mana". Anan muka yi sallar magrib da bamu samu munyi ba, ina cikin sallah naji wayata tana kara, Amina ta dauka tace "kunga daya marar kunyar ko? Ba karamin aikin Sultan bane yanzu yace an fasa partyn nan kowa ya tafi a bar masa amaryarsa" ta dauka ta gaya masa ina sallah sannan ta kashe. Ina idarwa nace "ke Amina waye ya baki damar yi min magana da mijina" duk suka kwashe da dariya. Hafsay tace "ina tausayawa angwayen nan yanzu fa dawowarsu daga 'yalleman kenan kuma zasu tarar da wata hidimar ta daban". Bayan munyi sallar isha muka shirya zuwa gurin partyn, a wajen swimming pool za ayi, gurin kato ne amma kuma a zagaye yake, dan madaidaicin swimming pool ne a gurin sai kuma kujeru da aka jejjera. An kawata gurin da fitulu masu color wanda yasa ruwan yake yi kamar shi ma different colors din ne. Kayan da na saka musamman Zayed yayi mana order dinsu daga saudiyya a matsayin wedding gift dinsa, kayan larabawa ne na mace dana namiji, kalar light blue mai kyalli. Nayi rolling mayafin yadda ya rufe rabin fuskata tunda ba'a saui baki ba.

Sai da suka gaya mana sun iso sannan muka fita gurin partyn, kawayena a zagaye dani wai lallai babu mai gani na sai an biya kudi. Suka kaini kan kujerata suka zaunar dani. Hayaniyar da naji ne yasa na fahimci gurin a cike yake da maza abokanan Sultan, a raina nace 'sultan akwai kwashe kwashe shi kam' ina jinsu suna ta ciniki na sai kace wata kaza, har suka gama a take Solomon ya rubuta check ya bawa kawayena, sai da aka basu sannan suka matsa daga gabana na fito fili sosai. Ta cikin mayafina nake leken inda zanga Sultan, tunda aka daura ban ganshi ba, can na hangoshi a tsakiyar abokansa suna ta dariya, fuskarsa kamar gonar auduga, yayo kyau sosai da kayan sa irin nawa. Gurin gaba daya ya hargitse da samari da 'yammata, kusan rabin mutanen gurin a tsaye suke. Ina jiyo amir da sultan suna ta musu, Amir yace tunda an sayi baki sai a bude fuskata kowa ya ganni tunda purpose din taron kenan, a taryi amarya, Sultan kam yace sam babu mai gane masa fuskar mata, ai kowa ya ganni a dinner da luncheon.

Ni dai ina zaune kamar gunki. Wani kamshi dana shaka be yasa zuciya ta ta tsaya ta daina bugawa for some seconds, sannan kuma ta fara bugawa da sauri, Hafsat da take zaune a kusa dani naji ta mike tace cikin muryar rada "what are you doing here?" Muryarsa naji yace "I have come for her" a razane na dago fuskata, Ibrahim na gani a tsaye a gabana, wani jiri naji yana neman daukana 'am I hallucinating?' Yawun bakina gaba daya ya kafe. Na kalli gurin da Sultan yake naga ya juyo yana kallon mu. Ji nayi kamar in tashi in fita daga gurin a guje saboda tsoro. Bakina ya kasa motsi ballantana inyi magana, inajin Hafsat tana masa bala'i murya kasa kasa "ka fita tun kafin su ganka, baka san an daura mata aure bane ba, there is nothing more between you two" maimakon ya fita din sai ya durkusa a gaba na, na kuma kallon Sultan da sauri naga gaba daya attention din su shida friends dinsa ya dawo kan mu. Fitsari ne kawai ban saka a wando na ba. Sama sama nake jin muryar Ibrahim yana magana "Maimunatu, nace miki na hakura ne saboda kince min

Please Login or Register in order to submit comment