Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka fito dasu dakin hutu, nan fa dakin ya cika da 'yan ganin baby, ina ta Allah2 in kira Zayed ashe har Sultan ya riga ni, Mommy da Daddy sai rige rigen daukan baby suke, Hafsat kam cewa tayi ayi mata allurar bacci dan tana son hutawa, tayi kwanciyarta a ciki mu kuma muka taho daya dakin muna ta hayaniyar mu. Bayan azahar sultan ya kirani a waya, ina fita na tarar dashi a mota ya ce min "shigo" ba musu na shiga, naga ya tayar da mota, nace "ina zamuje?" Yace "gida zan kaiki kije ki huta, jiya baki yi bacci ba throughout" nasan gaskiya yake fada dan haka na kira Mommy nace mata zanje gida in anjima zan dawo, ina zuwa kuwa na tafi daki na na kwanta sai bacci, ban koma asibitin ba sai da daddare muka tafi tare dasu asma'u da suka dage sai sunje sun ga baby ba zasu jira su dawo gida ba, muna zuwa Zayed ya kira daddy yake gaya masa cewa ya samu delay din flight dinsa amma dan haka daddy yayi wa baby huduba da sunan Mommy, Fatima Zahra, Mommy kasa rufe baki tayi dan murnar an yi mata takwara, kowa sai murna har Hafsat taji dadi sosai, Daddy ya karbe ta yayi mata huduba ya miko min ita, Amina ce tace "to Hafsat yanzu me zamu ke ce mata kenan, tunda dai ai mu ba zamu kira ta da sunan ta ba" Hafsat ta daga kafada, sai gaba daya suka juyo suna kallona, ni aka barwa zabi kenan, na kalli babyn sosai ina ganin tsantsar kyawunta na larabawa, nayi murmushi nace "Khairat, we will call her Khairat" a tare Daddy da Sultan suka juyo suna kallona, nayi kamar bansan sun gane me nake nufi ba, Mommy tayi dariya tace "perfect, yayi sosai, Allah yasa ta zama sanadin alkhairi a gare mu baki daya" nan kowa yace "Ameen" Hafsat ma murmushi take da alama sunan itama yayi mata dadi, sultan bai yi magana ba sam, ni kuma ban kalle shi ba, sai daga baya na lura ya fice daga dakin. A mota na same shi ya kwantar da kujera ya rufe idonsa kamar mai bacci, na zauna kusa dashi nace "in bacci zakayi ka tafi gida mana" ba tare daya bude idonsa ba yace "why Khairat? Why do you want her when she doesn't want me?" Bance masa komai ba saboda babu abinda zance masa, jin nayi shiru ya saka ya bude idonsa yana kallona yace "yanzu zaki tafi gida ne?" Nace "a'a, anan zan kwana ai" yace "OK, but ki tabbata kinyi bacci sosai, kar ki biye wa little Khairat" nayi murmushi na fita, na tsaya nace "good night" yace "good night love". Washe gari da safe aka sallame mu muka koma gida, a ranar kuma Zayed yazo. Sati yana zagayowa akayi suna, anyi taro sosai, kayan barkan da Sultan ya hado in wani ya gani zai iya tunanin shi aka yiwa haihuwar. Ana gama hidimar suna Mommy ta juyo kaina, tace yawo ya kare, babu inda zan ke zuwa. Shirye shirye ake yi sosai, dan har gyaran gida Daddy yayi, Amira da Amir sune chairman da chairlady din committee n shirye shirye, Sultan yace shi big wedding yake so, a cewarsa it will be the biggest day of his life, dan haka dole yayi celebrating. Ni nafi so ace anyi komai kadan amma mutane sunfi karfi na, dan anko sai Amira ta fitar da kala biyar, wai kowanne event sai anyi masa nasa ankon, kawayen mu na secondary school duk sai da Amira ta je ta gayyato su, ni dai ban samu damar zuwa ba saboda Mommy ta hana ni fita sam. Takanas Mommy ta dauko wata mata daga maiduguri wai zata min gyaran jiki, ni dai kawai jinsu nake dan banga abinda za'a gyara a jikina ba. Ranar farko da matar tazo muka shiga daki da ita, ta shiga toilet ta hada wani ruwa a tub, tace in cire dukkan kayan jikina in shiga ciki sai nayi awa daya tukunna, ina jin haka na dau waya ta da ear piece na je na shiga na kwanta na kira Sultan lokacin yana office muke ta hirar mu, ban ma san sanda awa dayar ta wuce ba, sai ganin matar nayi ta dawo da wani soso a hannunta, na yiwa Sultan sallama nace mata "wannan soson fa?" Tace "dashi zanyi miki wanka yanzu da wannan sabulun" na bata rai nace "ni zaki yiwa wankan?" Tace "eh, ai wannan ruwan da kika shiga kamar jika ki nayi yanzu kuma zan chuda ki ki fita tas" ni dariya ma abin ya bani, wato ana nufin duk wankan da nake yi ba fita nake ba shine yanzu za'a yi min wani. Bana son in gwale matar nace mata "OK, bani soso da sabulun, ni zanyi wankan da kaina" tace "ai ba zaki iya da kanki ba, anfi so wani yayi miki saboda zaki fi fita" yau naga rigima, ni kam babu yadda za'ayi in zauna kamar wata jaririya ayi min wanka. Ganin na dage da gaske nake ba zata yi min ba yasa ta fita ta kirawo Mommy, Mommy tana zuwa ta karba tace ta bata ita zata yimin da kanta, ai kuwa kam nasha durza kamar za'a ciremin fata, ni gani nake duk wahalar da ni suke yi suma suna wahalar da kansu, ban tashi sanin bani da wayo ba sai da na fito na kalli kaina a mudubi, gani nayi kamar wadda aka cire min fata ta aka saka min wata, a hankali nasa danyatsa na taba jikina, wani laushi da santsi naji jikina yayi. Ina fitowa kuma aka hada wani kaskon turaren wuta aka saka na tsuguna akai, wani irin kamshi ne mai tsadadden dadi yake ratsani, bargo matar ta saka ta lullube ni, sai fuska ta ce kawai a waje, sai da nayi 30 minutes a haka. Bayan na tashi kuma ta dauko wani mai ta bani tace duk in daina amfani da mayuka na sai shi kadai har lokacin biki na, kuma tace in na tashi shafawa a duk jikina zan shafa. A haka muka rabu da ita tace bayan kwana uku zata sake dawowa ta sake yi min wani wankan da turaren. A raina nace wannan me kuke so in zama kafin lokacin bikin? Ta kara jaddada min kuma banda fita rana, sam ba'a son rana ta taba ni.

Hafsat ma kanta ranar dana zauna a kusa da ita sai da ta rinka shanshanani tana cewa ya akayi ita ba'a yi mata irin wannan ba lokacin bikinta, amma tace in dai tayi arba'in itama sai anzo anyi mata. Ranar kam kin zuwa gurin sultan nayi saboda bana son ya saka ni a gaba da tambayar wanne turare na chanza, shima kuma da yake yanzu kullum a gajiye yake sai bai wani matsamin inje ba, a waya dai muka karaci hirar mu. A hankali komai na ginin sultan ya kammala, Hafsat da aunty Maryam kawar Mommy da gwoggo Aisha, matar uncle Aliyu ne suka je suka gano gidan saboda siyayyar kayan daki, tunda suka dawo suke santin kyau da tsarin gidan, Hafsat har dare zancen gidan nan take yi har sai da Mommy tace "ya ishe mu haka, munji yayi gida mai kyau, congratulations to him" sannan Hafsat tayi shiru. Har yanzu Mommy ba wani son sultan take yi sosai ba amma dai ba kamar da ba, duk da yanzu ta daina ce masa tsagera da sauran sunayen da take kiransa dasu amma har yanzu bata ambaton sunan sa, sai dai tace masa wannan yaron. Dama tun tuni ni da Sultan mun tsara colors din da muke so ayi furnishing ko wanne daki dashi, da colors din yayi amfani gurin tiling da fenti, dan haka na zauna na tsara wa Hafsat komai yadda nake so ita kuma ta gaya wa Mommy, a cikin sati daya akayi order komai aka kawo, masu interior decoration aka dauko suka je suka saka komai, suka kuma kara abinda suke ganin ya kamata su kara. Ni kaina nasan Daddy ya narkar da kudi a kaina. Tun ana saura sati uku biki aka gama shirya gidan tas aka rufe.

Saboda tsabar gyaran da jikina yake samu gani nake yi kamar in aka tabani jini ne zai fito, fuskata har wani kalli take yi saboda tas din da tayi, idan na zauna a guri kuwa ko bayan na tashi kamshina yana nan. Dole na kara jan jikina daga gurin Sultan dan sosai yake nuna min kwalamarsa a fili, sau da yawa in yana zaune a kusa dani yayi ta shanshana ni har sai na tashi na gudu. Da kadan da kadan gida ya fara cika da mutane, daada ta iso da jama'ar niger, part dinta aka bude mata suka sauka a can, tana zuwa itama ta fara dura min tsumi, kullum da akwai abinda zata bani in sha, daga farko dariya nake yi mata dan ni gani nake duk wani maganin mata kawai fada ake yi, dan mu a likitance bamu san wannan ba, ban gane bani da wayo ba sai da na fara jin chanji a jikina, babu shiri na daina shan tsumin daada, inta bani sai inzo in ajiye a fridge in yi tafiya, data fahimci me nake yi ta tambaye ni dalili sai nace mata ta ajiye min in anyi bikin sai inke sha acan, sosai ta fahimci abinda nake nufi dan haka ta daina bani, sai da hado min su jaka guda kowanne da bayanin yadda zan yi amfani dashi ta bani tace in tafi dashi can, na karba nayi mata godiya, ni sai inta mamakin daada da Mommy, su da basa son sultan kuma me yasa suke yi tayi masa tanadi haka?.

Saura sati biyu biki aka kawo kayan lefe, akwati set goma aka kawo,different colors, ni har kasa tsayawa nayi in kalla saboda kayan sunyi min yawa, duk kayan kuma Yaya ce tayi su, tace tata gudunmawar kenan, dan haka da Daddy ya saka sultan a gaba da fadan kayan sunyi yawa sai ya gaya masa yace shi ko dan kunne bai saya a ciki ba. Kaya ne masu tsada daga gani kasan cewa akwai class. Sarkokin gold akwatin su daban. Kuma komai size dina, daga gani kuma kasan babu abinda aka saya a Nigeria. 'Yan 'yalleman dama basu zoba sai ranar da aka kawo kayan, daga nan suma suka bude part din su inna suka baje tasu hajar. Hajja kam sai yada magana take tana kunkuni 'ai dama sai da jikina ya bani, kudi suka gani shi yasa suka hana yaron nan, duk abinda kuwa aka saka bidi'a a cikin sa ba zai yi albarka ba. Shima Allah ya bashi arzikin da yafi wannan kuma Allah ya bashi matar da ta fita" babu wanda ya kula ta haka ta gama sumbatunta.

Inna kam tana zuwa ita tsarabar data kawomin shine na adduoi, tace "gidan sarauta zaki je dole kina bukatar tsari sosai, tsari daga sihiri, tsari daga mugun baki, tsari daga dukkan sharri na mutun kona aljan" ta babbani rubutu na sha, ta kuma koya min adduoin tsari sosai, sannan tayi min nasihu masu ratsa jiki akan kula da addini, tsarkake zuciya da iya mu'amala da mutane, tace as long as kana kula da addinin ka sosai, ka kuma tsarkake zuciyar ka baka nufin kowa da sharri to Allah ba zai taba bawa makiyinka nasara akan kaba. Shi kuma iya zama da mutane shi zai kara maka soyayyar miji ya kuma jawo maka soyayyar 'yan uwan miji. Naji dadin nasihohinta sosai, sai nake ganin kamar duk ita tafi kowa bani tsarabar gidan miji.

Kamar yadda akayi bikin Hafsat haka nawa ma zai kasance, su Mommy sun shirya kunshi, kamu da mother's eve, su kuma su Amira da Amir 'yan committee sun shirya bridal shower, luncheon, dinner, sai walima for girls, and bachelor's night for the guys. Sai kuma ranar da aka kai amarya Amir ya shirya mana welcome party anan gidan mu da Sultan. Ni already jina nake a gajiye, I have no idea yaya zan iya duk wadannan events din.

Har yanzu wasan buya muke yi da Siltan, dan sosai nake rikita masa lissafinsa in muka hadu, nima kuma tunda daada ta fara dura min tsumin ta na fara ja baya dashi. Yayi mitar har ya gaji, gashi gidan ya fara cika da mutane balllantana yace zai yi abinda ya saba ya shigo min daki cikin dare. Shima kuma yanzu ya dan fara ja da baya da zaman gidan saboda baki. Wani lokacin sai dare yake zuwa sai dai insa akai masa abinci office, da daddare kuma sai in aika masa dashi dakinsa.

Ten Days To The D- Day

Tun safe Amira tana gidan mu, sun hadu ita da Amina suna ta ware min kayan da zan saka a kowanne event, ni kallo kawai nake bin su dashi saboda already Sultan ya bada dinkunan mu ni dashi na kowanne event, anko zamu ke yi, wanda kuma na mata ne kadai shima ya dinka min abinda zan saka, hatta takalmi da jaka babu wanda bai saya ba, hotunan yake turomin ni kuma ina zaba, tunda yanzu mun zama mage da bera bama zama a guri daya. Sai da suka gama shan wahalar su sannan nace "kun gama?" Suka juyo suna kallona nace "to sai ku mayar min da kaya jikin akwati basu zan saka ba" na gaya musu tsarin mu da Sultan, Amira ta bata rai tace "kuma dan wulakanci shine kika barmu muke ta wahala, amma wannan akwai munafukar amarya, shine zaku ware ke da angonki ku tsara abinku ba zaku fada wa 'yan committee ba" nayi dariya nace "'yan committee manya, wai dan Allah me kuke cewa in kun zauna meeting din ne? Yarinyar nan babu abinda ba tace min akan Amir ba amma yanzu in ka gansu suna kus kus sai ka dauka they are lovers" ta kara bata rai tace "lovers fa kika ce? Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni kuwa me zanyi da wannan? Dan Allah yanzu ke a ganin ki mun dace?" Nace "sosai kuwa" tace "to amma kuwa ya kamata kije ayi miki wankin ido" Amina dai dariya take yi tace "Moon kinga yadda kika koma kuwa? Shi yasa yanzu in dai kina guri Sultan ba sosai yake fahimtar magana in an yi masa ba. Oh Allah. My future husband where are you? Am waiting" dariya nayi sosai nace "to ke ki lallaba munir mana?" Ta zaro ido waje "a 'uzubillahi, kije ki wanke bakin ki please. Ai ni da kike gani sabo zan bare a leda. Munir shi kam in aka ce masa gwanjo ma ai an rufa masa asiri" ta jawo ni tazo dai dai kunnena tace cikin rada "gayamin, Sultan sabo ne ko tsoho" na ture ta ta fada kan gado, nace "you will never find out" Amira tace "ni fa har yanxu ban sayi gown din da zan saka ranar bridal shower ba, kowa ya gama shirin sa ban dani, bayan itama da akwai abubuwan da ban saya ba" nayi sauri na zauna kusa da ita nace "kinga kawata, kuje ke da Amina gurin Mommy ku lallabata ta barni in fita, sai muje in kaiki ki siyo, wallahi na gaji da zaman gidan nan. Tunda sunce rana ce basa so in shiga ai yau babu ranar ma" Amira tace "ni kinsan Mommy yanzu ba shiri muke yi da ita sosai ba, sai dai ko Amina" na juya gurin Amina nace "please yaya Amina, kije ki tambayar min" ta bata rai tace "to in kun fita me zaki siyo min?" Nace "duk abinda kike so" nan ta jera min uban list na abubuwan da take so in siyo mata, duk nace naji na yarda. Ta fita muka zauna zaman jira. Sai da tayi wajen minti talatin sannan ta dawo tana bata fuska, har na sare, sai kuma tayi dariya tace "an barki, amma ki saka dogon hijab da nikab" murna kamar in cinye Amina, dan ji nake gaba daya na tsani kaina saboda zaman gida. Na kira Sultan a waya na gaya masa zamu fita da Amira, yace "OK, in kun gama ki yi min magana, nima ina son zamu je wani guri" nayi shiru bance komai ba, yace "please say yes mana, yaushe rabon da in ganki wajan three days" nace "ina zamu je?" Yace "where it all began, ina so muje muci abinci a Hilton, anan na fara ganinki" kawai sai naji ba zan iya ce masa no ba, nace "OK" yana ta murna na kashe wayar. Da sauri na shirya muka fita, har wadanda suke palo basu gane ni ce na fita ba saboda na rufe fuskata, daya daga cikin motocin Sultan na gani na leka naga key a jiki kawai na shiga na tayar, Amira ta shiga muka tafi. A gate mai gadi kin budemin yayi sai da nayi magana yaji muryata sannan ya bude yana dariya. Wani supermarket tayi min kwatance, ni ban taba shigar sa bama ina dai ganinsa a hanya, ita ma tace bata taba zuwa ba an dai ce mata akwai kaya masu kyau a can. Muna zuwa muka yi packing, na chire nikab dina na ajiye a mota, muka shiga, karshen haduwa gurin ya hadu, kaya kam akwai su, ga shi komai a tsare, nan da nan Amira ta fara lodar kaya, ni kam ban sayi komai ba saboda babu abinda nake bukata, a wajen siyan gown tayi ta ruwan ido, nace "wallahi in ba zaki dauka ba zan tafi in barki, Sultan fa yace zamu hadu in anjima" ta tsaya ta saki baki tana kallona, tace "dama rakonin da kika yi na munafunci ne? Dama gurin sultan zaki tafi? Wallahi kinsan ba karamin aiki na bane yanzu in kira Mommy in gaya mata" nayi ta bata hakuri ina lallabata "ba wani gurin zamu je ba fa, abinci kawai zamuje muci a Hilton, kuma motar sa daban mota ta daban" tace ta hakura ba zata fada ba amma sai in barta ta gama siyayyar ta a hankali. Sai da ta gajiyar dani sosai sannan tace ta gama, muka tafi gurin biyan kudi. Da POS ta biya kudin, aka bamu receipt muka fito, muna shiga mota na dauko waya ta da niyyar kiran Sultan naji Amira tace da karfi "what?" Na juyo ina kallonta da waya a hannuna naga wayarta take dubawa, nace "ya akayi?" Ta nuna min screen din wayarta naga alert ne na siyayyar da tayi yanzu nace "menene?" Ta nuna min receipt din, ni har lokacin ban fahimci me take nufi ba, tace "duba ki gani, sun kara min 10k a cikin kudina" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amira, let it go, wallahi na gaji" tace "wallahi bazan hakura ba sai sun biya ni kudina, haka kawai dubu goma a banza, zo muje sai sun biya ni kudina" kamar zanyi wa Amira kuka haka na fita na bita muka koma ciki. A gurin cashier ta fara masifar sai an biya ta kudinta "How can you guys be so incompetent, ku kara min kudi har dubi goma?" Cashier kaman zata yi kuka tana bawa Amira hakuri amma Amira ta shafa wa idonta toka tace sai an biya ta, ni dai ina ta kallon agogo naga har karfe biyar, nasan duk inda six tayi Mommy zata kira ni tace in dawo gida, kuma gaskiya bana son missing date din mu da sultan, na karasa gurin rigimar naji cashier din tana cewa da Amira "madam kudin sun riga sun shiga account din shagon nan, ba zamu iya fitar dashi ba sai dai ki dau wani abun na kudin ki" Amira tace "ni na gama siyan duk abinda nake so in saya, babu abinda zan dauka kuma, kawai kudi na kawai nake so a bani" cashier tace "I can't do that madam, only the manager can do that, sai dai in zaki yarda in kaiki gurinsa inyi masa bayani sai ya biya ki kudinki" naga tsoro karara akan fuskar cashier din, daga alama tana tsoron manager din, nace "Amira ki zo mu tafi, ni zan biya ki 10k dinki" tace "wallahi bazan tafi ba chafdi, nasan sauri kike ki tafi gurin Sultan, in ya kira ki bani shi in yi masa magana" ni dai duk raina a bace, tausayin cashier nake yi, mistake tayi muka maybe zata iya loosing job dinta akan haka, da har nayi deciding inyi tafiya ta in bar Amira su karata amma sai na sake tunanin maybe in na bisu gurin manager din zan iya bashi hakuri kar ya kori cashiet din. Sai da ta fara yin waya ta tabbatar yana office sannan tace muzo muje, ta shige gaba muna binta a baya, ta hau stair muka bita zuwa hawa na uku, da kyar na karasa ina ta haki, taje bakin kofar tayi knocking, aka yi magana daga ciki, ta bude tayi mana alamar mu jira a waje sannan ta shiga ciki, Amira kam ba zata jira ba dan haka ta tura kofar ta shige ciki, nima na zo kofar na tsaya.

Cashier na hango tana ta kokarin yin bayani, muryarta sai rawa take yi, na dan shigo daga ciki dan in hango wannan manager da matar take tsoro haka. Ya dan juya side dinsa, dan haka banga idonsa ba, amma tsaf na gane shi. Familiar scent dinsa ne ya kara tabbatar min da cewa shine. Na kara taku daya cikin katon office din. He is still tall but no longer thin. Yayi kiba, jikinsa ya murje sosai, hakan sai ya bashi almost a giant frame. Doguwar fuskarsa ta cika, siririn sajensa ya kara fadi dan ya tafi da fadin da fiskarsa ta dan yi, dan karamin gemon da da yake dashi yanzu babu, meaning the ustaz part of him is gone. Amira naji tayi catching breath dinta very sharply. Fatarsa ta kara haske, tana kara nuna alamar hutun daya samu. He looks so different but still the same. Lokaci daya ya juyo ya kalleni idonsa ya fada cikin nawa dana bude ina kallonsa. His eyes look the same, babu abinda ya chanza. Suna nan a lumsassun idanun da nayi falling in love with all these years ago. Gabadaya yanayin fuskarsa ya chanza lokaci daya. Da sauri na juya na nufi kofa, bansan sanda ya sauko daga kan kujerar saba har ya zagayo table dinsa ba, ina dora hannuna akan doorknob naji nasa hannun akan nawa, ya jawo ni baya da karfi, cikin tsawa naji ya ce da cashier din data kawo mu "out" na fara kokarin kwace hannuna amma maimakon ya saki hannuna sai ya hada ni da kirjinsa ya matse. Na fara kokarin kwace wa amma sosai ya matse ni, kuka na saka sosai, still bai cika ni ba, ban san adadin tsahon lokacin da muka dauka a haka ba dan har sai da nayi kuka na na gaji dan kaina nayi shiru sannan ya sassauta rikon da yayi min. Ina kwacewa na rarumi wani file akan table dinsa na fara dukansa dashi, har sai da takardun ciki suka tarwatse sannan na kuma daukan wani na cigaba da dukansa ina cewa "why? Why? Why?" Bai hana ni ba har sai da dan kaina na gaji da dukansa na durkushe a gurin na sake wani sabon kukan. A hankali a durkusa a baya na yace "am sorry" na juyo a fusace nace "sorry? Abinda zaka ce kenan? Sorry?" ya sunkuyar da idonsa kasa yace "am sorry, i shouldn't have hug you like that, bai kamata in taba ki ba kina matar aure, am sorry i lost control of myself bayan ganin ki after all these years" na juyo da mamaki ina kallonsa dan ban fahimci me yake cewa ba nace "me kake nufi da matar aure kuma?" Yanayin yadda nayi tambayar yasa ya mike tsaye da saurinsa yana kallona gaba daya ya rude yace "ance min kinyi aure a shekarar da muka rabu, kwanan nan akace min kin haifi danki na uku"


Episode Sixty Three : Amira 3

Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna

Please Login or Register in order to submit comment