Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinyi missing ya wuce ki" daga haka ya mika mata babyn da yake hannunsa ya fita.
Ba'a jima ba suma su mommy suka fita suka bar mana dakin. Sunfi awa biyu a gurina, har akayi magrib, ana ta hira ana daukan pictures da baby, suna ta tsokanar Hafsat wai baby na yafi little khairat kyau saboda sultan yafi zayed kyau. Ita kuma ta dage sai kumfar baki take ita a dole zayed yafi sultan kyau. Sultan ya shigo ya zauna shima ya shiga cikin muhawarar, suka yi ta bugawa da Hafsat kowa yaki hakura, sultan yace zayed bama a class dinsa yake ba, yana class din kasansa, ita ma kuma tana class din kasana, dan haka ita da zayed ba zasu taba haihuwar 'ya'ya irin namu ba. Hafsat ta lakuce wa babyn hanci tace "akan wannan hancin ne dai ake wannan maganar, ita ma kuma khairat tana dashi wanda yafi wannan tsaho ma" sultan yace "kar ki bari ummee ta ganki kina lakuce masa hanci. Kuma ba maganar tsahon hanci ake yiba, maganar kyan hanci ake. Baki san in hanci yayi tsaho da yawa baya kyau ba?" Ina daga kwance nace "sultan don't forget about the lips" Hafsat ta juyo kaina "wannan bakin mai kama da danyen nama har wani kyau ne dashi? Daga ganin bakin irin na ubansa ne rashin kunya zai ringa yiwa yayun matarsa" Sultan yace "ke waye mara kunyar? Ko yayanki walid na girme shi ballantana ke" tace "amma dai baka girmi mijina ba" walid yace "ni din wata nawa ka bani?" Yace "na dai girme ka koma wata nawa ne, ko kwana daya na baka na girme ka" Habeeb yace "amma dai mun girmi matarka, dan haka dole ka bamu girma" Sultan yayi dariya yace "waye yace maka kun girme ta? Ai ni da ita soul din mu daya, gangar jiki ce kawai da ban, so technically she was born the day I was born, jikin ne dai sai daga baya aka haife shi. There is a strong chemical bond between us spiritually" Fadila tace "what kind of chemical bond? Covalent ko electrovalent ko hydrogen bond?" Ya dan bata fuska yana kallonta sannan ya juyo ya kalleni yace "which one is the strongest?" Duk akayi dariya, Aisha tace "ku da kuke da soul daya ai kamata yayi ace duk abinda ta sani kai ma ka sani ba sai ka tambaye ta ba" ya juya gurinta yana kallonta sai kuma yayi tagumi yace "kai Amir, yaushe ka koya wa matarka rashin kunya? Ka gaya mata idan manya suna magana yara basa saka baki shiru suke yi" nan kuma suka koma yi shida Amir. Suna ta sakani dariya gashi dinki na yana min ciwo idan nayi. Sultan sai famfa su yake, duk wanda ya fadi magana sai ya samu amsar da zai bashi. Hafsat ita kuma sai hawa take, har yanzu ta kasa gane halin sultan, a karshe tace wallahi sai an sake wannan hirar in zayed yazo. In kaga sultan a lokacin ba zaka taba cewa wani abu ya bata masa rai dazu ba, hirar sa kawai yake yana dariyarsa. Haka Sultan yake, akwai saurin hawa akwai kuma saurin sauka. Amaren mu ma duk sun ware suna ta hirar su, ina kwance ina dan saka musu baki kadan. Doctor ya shigo da ledar jini a hannunsa, yace su tafi za'ayi min allurar bacci in huta, nan suka fara fita kowa shida matarsa gwanin sha'awa, Amina ma ta kira nata a waya ashe ba nisa yayi ba dan haka yace ta fito gashinan a waje. Faruk yana shafa kai yace da sultan zai kai Huda gida suma suka fita, ya rage daga ni sai sultan da doctor, da baby kuma a kan gadonsa yana bacci. Doctor ya rataye jinin ya kamo hannuna zai saka min, na kalli sultan da ke tsaye kusa da doctor nace "doctor da ka bar jinin nan kawai" ya dakata yana kallona yace "why? Mun gwada red blood count dinki is low. Me yasa ba kyaso" na kalli sultan nace "Sultan ne baya so" sultan ya bude ido da baki yana kallona yace "ke? yaushe na fada miki haka? Sharri zaki yi min a gaban likita ko?" Doctor ya tsaya yana kallon mu yace "what is it doing to be? A saka ko kar a saka?" A tare muka yi magana da sultan, ni nace kar a saka shi kuma yace a saka, doctor ya tsaya yana kallon mu yace "ko in baku guri kuyi magana?" Sultan yace "No doctor, ka saka mata kawai" na gyara kwanciya ina kallon doctor ya gama arranging komai, yayi connecting tube din da cannula din hannuna sannan ya bude jinin, na bi jinin da kallo yana tahowa har naji ya fara shiga jikina. Na kwanta na lumshe idona, ina jin doctor din yayi min allura suka gama maganganun su da sultan sannan ya fita. Sultan ya dawo ya zauna a bakin gadon yana shafa kitsona yace "hey, har kinyi bacci?" Na dan bude ido bacci yana dauka na nayi masa murmushi, ya sunkuyo dai dai kunnena yace "it is not his blood". Abinda naji kenan bacci ya dauke ni.
Sanda na farka kamar tsakiyar dare ne. Na kalli inda baby yake naga bayanan. Na fara dube-dube sai na Sultan a zaune kawai ya rike babyn a hannunsa yana kallo fuskarsa dauke da murmushi. Na jima ina kallonsu amma bai ma san na farka ba. Sai da nayi gyaran murya sannan yayi sauri ya juyo. Sai kuma ya kalli babyn yace "hey Al'ameen, let's go greet Mom" ya taso ya dora min shi a chinya sannan ya taimakamin na tashi zaune. Na dauki babyn na fara feeding dinsa, yana kallon mu ya jawo kujera ya zauna yace "Maimunatu, meet Muhammad Al'ameen. Yaci sunan Daddy, Muhammad, zamu kirashi da Al'ameen saboda gaskiya, rikon amana da jajircewa irin na masu sunan sa. Ina fatan Allah yasa yayi gadon not only their name but har halayyarsu" nace "Ameen. Nagode" yace "don't mention. Daddy yayi min komai a rayuwa, yayi min abinda babu wani wanda ya taba yi min kuma babu wanda zai kuma yi min nan gaba. Babban abinda yayi min shine ya bani ke. He gave me a life. Because you are my life." Nace "Sultan, kafin inyi bacci, naji kamar kace it is not his blood, whose blood is it?" Yace "daddy's. Muna fita zamu je gurin daukan jinin yace ba zai bayar ba. He said idan shine yasan ba zai so jinin tsohon saurayin matarsa a jikin ta ba. So, he wish for me what he wish for himself. I owe him that. Bazan manta ba" naji dadi a raina da hakan ta kasance. God is really amazing.
Washe gari na fara tafiya, aka saka ni exercise na yi ta zagayawa a asibitin. Bayan na dawo daki Takawa yazo. Ummee dama tun sassafe tazo. Takawa ya dauki Al'ameen yayi masa addu'ah. Yana gama wa sultan ya mika hannu zai karbe shi, Takawa yace "au rowar sa zakayi min sultan? Daga dauka har zaka wani miko hannu a baka ko" sultan ya bata fuska "tun safe fa ban dauke shi ba, Ummee tunda tazo ta hana ni shi" Takawa yace "kwantar da hankalin ka, in aka sallameku kuka koma gida har sai ka gaji da daukan sa" Ummee tace "chafdi, ai bin su zanyi gidan nasu" Sultan har da bubbuga kafa a kasa kamar me shagwaba, Takawa yana yi masa dariya har da kyakyatawa. Hajiya ma tazo har asibiti ta duba ni, duk tayi sanyi babu wannan mulkin da dagawar. 'Yan'uwa da abokan arziki kuwa da basu samu zuwa ba sai waya suke min ana min barka, dan har kashe waya ta nake yi in dai ina son in samu bacci. Kwanan mu hudu a asibitin aka sallame mu. Tare muka tafi da daada tunda tana Abuja bata koma Niger ba. Muna koma wa gida ma bamu samu hutu ba, dan kullum gidan a cike yake da mutane. Ummee ta kasa ta tsare, daga baya ma hana daukan Al'ameen tayi sai dai duk wanda yazo ya kalle shi a hannunta ya tafi. Daddy yaji dadin saka sunan sa da aka yi sosai, Takawa kuma yace sunan yayi. Ana jibi suna Amina tazo zamuyi plans na taron sunan. Muna babban palo tare da sultan daya saka ni a gaba sai na cinye uban abincin da Ummee ta zuba min kafin ta tafi gida. Amina ta shigo da sallama, tun kafin ta zauna sultan yace "yana ganki ke kadai?" Tace "gashi can yana juya mota zai tafi" Sultan yace "ba zai shigo mu gaisa ba zai tafi?" Ya tashi ya fita sai gashi ya dawi shi kadai, yace "ya tafi, in ya dawo zai same ni" ni dai kawai kallon sultan nake ina mamaki. Amina tace "ina babyn kuma?" Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "ummee ta tafi dashi" nayi dariya nace "kwantar da hankalin ki, in dai wannan acicin ne yanzu zaki ga an dawo dashi. Ai kuwa ba'ayi awa daya ba sai ga Fa'iza ta dawo dashi, tun suna daga waje muka jiyo kukan sa mukayi dariya, tana shigowa ta miko min shi tace "da kyar Ummee ta bani shi, wai ban iya daukan babies ba, wai sai dai ta kawo shi da kanta, Takawa ya hana shine ta bani shi da kyar" na karbe shi ina yi mata sannu na fara feeding dinsa. Su Hafsat ma duk ranar suka zo muka gama plans din suna.
Ranar suna yaro yaci sunan Daddy kamar yadda akayi masa huduba, za'a ke kiran sa da Al'ameen. Raguna guda biyu Daddy ya aiko dasu na suna, Takawa ma ya kawo biyu. Taf palace ya cika da mutane, both daga part dina da kuma part din sultan. Da sassafe jirgin su Zayed ya sauka, yace akwai aiki a gabansa amma ba za'a barshi a baya ba gurin taron sunan nan, besides shima yayi missing family dinsa, yace wannan karon a England Hafsat zata haihu sai dai duk mai son ganin babyn ya bi su can. Kamar daga sama sai ga Amira sun zo tare da Mahdi, ya gama final exams dinsa ya zo gida, an saka bikin su wata uku masu zuwa. Muka rungume juna da Amira, ta dauki Al'ameen tayi kissing dinsa, na sa aka raka Mahdi gurin su Sultan bayan mun gaisa shima ya dau baby. Kayan barka kam su Hafsat sai karba suke suna ajjiyewa, mun sha kaya sosai dani da baby. 'Yan uwan ummi sunzo sosai daga Riyadh. Wadansu mutanen da suka zo ma ni ban san su ba sai anyi min bayani. Masoya ta ko ina bulluwa suke dan taya mu murnar samun little love din mu. Sultan shima nasa taron daban yake yi a part dinsa, abokan sa sunzo sosai daga parts da yawa na Nigeria. Gang bang sunzo suma, amma kamar yadda sultan ya taba gaya min, they are no longer a gang, kowa daban yazo, kowa ya girma ya samu rayuwarsa, babu sauran ganging kuma. Amira ma tazo tare da mamanta, ta gaya mana an saka bikinta nan da wata uku, kafin nan mahadi ya karasa final exams dinsa ya dawo. Sai dare sannan aka fara raguwa. Bamu muka samu zama ba sai wajan karfe goman dare. Nan kuma aka zauna hira a palo. Ibrahim yazo daukan Amina tare da little Moon, Sultan da kansa ya fita ya shigo dashi, suka shigo suna dariya kamar abokai, sultan ya dauki little moon ya dora akan cinyarsa yana tsokanarta yana ce mata matarsa, ita kuma bata san ma me yaki nufi ba. Amira ta gaishe da Ibrahim kuma ya amsa mata da sakakkiyar fuska sosai, suka gaisa da Mahdi a matsayin mijin da zata aura. Aka zauna aka cigaba da hira. Kadan kadan nake saka baki a hirar. Gaba daya hankali na ya tafi akan lissafin rayuwa, na kalli duk mutanen da suke zagaye dani, they are my friends and family, they are my life. And most importantly, they are happy.
One episode more, and we are done Insha Allah.

Episode Hundred : Not The End.
One Year Later
Daddy yayi retire daga ambassadorship, yace lokaci yayi kuma da ya kamata ya dawo Nigeria ya zauna cikin 'yan'uwa da abokan arzikin sa, tunda dai yasan ya tara da yawa, ya kafa kansa ya kafa 'ya'yansa, ko da ace bai tara dukiya ba 'ya'yansa kadai sun isa su rike shi zuwa karshen rayuwarsa. Yaya Walid yana aiki a kamfanin hakar man fetur na SHELL a matsayin engineer, sosai yake samun kudi kuma da yake shi mai nutsuwa ne sosai da tattali, nan da nan ya fara shiga layin wadanda za'a kira da masu kudi. Yaya Habeeb yana aikin banki, duk da cewa shi mai yawan kashe kudi ne amma dai dai gwargwado yana samun cigaba shima. Ni kam da ni da Hafsat medical doctors ne, duk da dai har yanzu babu wanda ya fara aiki a cikin mu amma mazajen mu sun ishe mu duk bukatun mu. Faruk ya gama service dinsa ya koma masters, tun kafin ya tafi yace a nema masa auren Huda amma Daddy yace sai ya gama karatu ya samu aikin yi sannan za'a yi masa aure, an dai shigar da maganar manya sun sani. Daddy yana dawowa Nigeria ya aika 'yalleman aka daukk inna da Hajja ya dawo dasu Abuja su zauna tare dashi, tunda 'yalleman din kusan babu kowa sai uncle rufa'i, shi kuma ba mazauni bane sosai. Tunda labarin retirement din Daddy ya bazu a Nigeria, nan da nan aka fara aiko masa da offer din aiki, government, ministries, companies amma duk yaki karba yace hutawa yake so yayi. Amma bai dade a gida ba kuma sai yaji zaman gidan ya ishe shi, tunda babu kowa a gidan sai su inna da 'yan aiki, Mommy har yanzu tana aikin ta, dan haka rana daya Daddy yace ya karbi offer din da university of Abuja ta aiko masa akan ya zama next VC idan tenure din wanda yake kai ta kare. Dama shi Daddy harkar siyasa ce baya so, amma yana ganin as a VC zai taimakawa kasarsa without getting involved in politics. Bikin su Ya walid yana da wata goma Zainab da Fadila, wadanda yanzu sun zama kawaye sosai, suka haihu kusan a tare, Zainab ce ta fara haihuwar baby girl aka saka mata Mommy, ranar sunan ta Fadila ta haifi Daddy, dan haka yaran suka tashi kamar tagwaye, small Mommy da small Daddy.
Hafsat ta juye ta sake dauka. Lol. Ta haifi danta namiji watanni biyu bayan haihuwar Al'ameen. Mukaje England muka sha suna, yaro yaci sunan baban Zayed. AbdulMalik, muna kiransa da Ayaan. Watannin Ayaan biyar a duniya Hafsat ta kira ni tace min wani cikin ne da ita, nace "kai Hafsat, wannan ke ai har kinfi Mommy ma" tace "ai dama haka ake yi, idan ka koyi abu a gurin mutum sai kazo ka fishi iyawa kuma" mukayi dariya, tunda dai duk ita da yaranta lafiya lau suke to babu wata matsala.
Anyi bikin Amira da Mahdi, mun je kano munsha hidima. Duk da dai Sultan ya hana ni kwana yace Al'ameen yayi kankanta da shiga biki, ni kuwa nasan bata Al'ameen yake ba, ta kansa yake, dan Sultan yana nan yadda kuka san shi babu abinda ya ragu sai ma ince karuwa yayi. Mahdi ya samu aiki a asibitin malam Aminu kano. Last wayar da mukayi da Amira itama ta gayamin ta kamu. Suna zamansu lafiya lau from all indications.
Ibrahim da Jewel dinsa Amina kam soyayya sai abinda ya kara gaba. Dan ko ziyara mutum yaje gidan su sai ya fahimci suna kaunar junan su. Maman Ibrahim ma ta dauki son duniya ta dora akan Amina dan tana ganin itace sanadiyyar dai daituwar dan ta. Ita kuma Amina ta rike little Moon tamkar ita ta haife ta, in baka sani bama ba zaka ce ba ita ta haife ta din ba. Kullum kaga Ibrahim zaka ganshi cikin farin ciki, alamar cewa hankalinsa a kwance yake. Sosai suke zumunci shi da sultan, dan wani lokacin ma har yazo gidan mu ya tafi bana sani, sai daga baya sannan sultan ya gaya min. Sai dai kuma har yau, duk ranar da muka hadu da Ibrahim muka gaisa sai naga kishi a idon sultan, sai dai baya nuna wa har wasu su gane. I guess some things will never change.
An samu karuwa a gidan Amir shima. An samu namiji wanda a take Amir ya saka masa sunan Sultan. Abubakar Sadiq Abdallah. Kuma ake kiransa da Sultan. Sultan yaji dadi sosai amma sai ya bata fuska yace "ko kara ma babu, sultan zaku ce masa kamar wani sa'an ku? Ina lefin ma ku ringa ce masa Yaya?" A raina nace 'ho, sultan akwai son girma'. Har yanzu amir bai samu iyayensa ba, kuma dama bawai tayar da hankalinsa yayi yana neman su ba, yace "if it is meant to be, then it will be" gwara ya zauna ya gina rayuwarsa tare da mutanen da yake dasu, wadanda ya tabbatar suna kaunarsa akan yaje ya bata lokacin sa gurin neman wadanda ba lallai ne suna son sa ba.
Munir tun rasuwar Baffa ba karamin girgiza shi mutuwar tayi ba, kasancewar tunda akayi masa takunkumi a 'yalleman suke tare da Baffa suna kara shakuwa, mutuwar Baffa sai ta nunawa Munir cewa itafa duniya ba matabbata bace ba, kana cikin shagalinka za'a iya zuwa a zare ranka ba tare da ka tuba ba. Wannan ya saka shi ya kara nutsuwa, ya rungumi matarsa ya kuma rungimi aikinsa. Kowa a dangi yaji dadin chanjin munir, wannan ya saka Hajja tace to tunda dama neme-nemen mata ne ya lalata shi, to gwara a kara masa wata matar dan ya kara nutsuwa. Ai kuwa a take uncle rufa'i ya bashi Rufaida kanwar Amina. Munir baki har kunne saboda murna dan dama ya taba cewa yana sonta ta wulakanta shi saboda halinsa, amma tunda yanzu ya shiryu itama ba'a wani sha wahalar shawo kanta ba tace ta yarda.
Ummee da Takawa ana nan ana bude sabon page na rayuwa, dan idan ina gurin Ummee Takawa ya shigo tashi nake yi in fita, saboda kunya yake sakani ina ji shi kuma babu ruwansa, daga dukkan alamu rashin kunyar sultan ta gado ce. Sultan da Takawa are very much alike, saboda idan suna wani abin tamkar mutum daya ne da kamanni biyu. Ummee ta sayar da business dinta kaf na Riyadh, dukkan kudin ta zubasu a account din sultan. A take Takawa ya sake bata wani jarin ta fara sabon business a Nigeria, nan da nan aka hada mata connection da 'yan kasuwa take shigo musu da kaya daga kasashen waje. Sultan yace "amma Ummee wannan karon ba sunana kika saka ba ko?" Tace "sunan little love na saka" yace "Ummee I don't need money kin sani, in dai ta nine kiyi hutawarki" ta harare shi tace "dama kaine little love din?" Sultan ya tsaya saroro yana kallonta yace "OK. Kun fi kusa ke da shi". Hajiya tun tana saka ran Takawa zai mayar da ita har ta fara kosawa. Shi kam har manta wa ma yake yi da ita a duniya, dan in dai ba zuwa tayi gaishe shi ba baya ma tunawa da ita, duk sanda tazo gaishe shi kuwa sai ya hade rai sosai sannan yake amsa mata, dan baya son ma taga fuska ballantana ta kawomasa wata magana. Da Hajiya taga babu fuska sai ta fara bin manyan su tane rokon a roka mata shi ya mayar da ita. Yaya ta kira su gaba daya suka zauna a gabanta, tana yiwa Takawa maganar ce mata yayi shi ba zai iya mayar da Hajiya ba, tace "saboda me? Saboda kai baka yafiya? Baka son kaima Allah ya yafe maka?" Yace "ai na yafe mata, da ban yafe mata ba da tuni na koreta daga gidana ita da shegen danta. Ba zan mayar da ita ba saboda ina gudun sabawa Allah. Allah yace duk wanda yake da hali to ya auri mata biyu zuwa hudu in har yasan zai iyayin adalci a tsakanin su. Ni nasan bazan iya adalci a tsakanin khairat da wata mace ba, ba Zuwaira kadai ba, dan haka bazan iya mayar da ita ba. Zaman da muka yi da ita a da ma da ace ina da iko dana goge shi daga kwakwalwata na taina tunawa" jin haka yasa Hajiya tace ita kam ba zata iya zama babu miji ba, dan haka tunda ba zai mayar da ita ba to zata fita ta sami wani mijin tayi aurenta, Takawa yace Allah ya raka taki gona, amma kar ta saka ran tafiya da ko daya daga cikin 'ya'yansa, sai dai in nata dan zata dauka to bismillah. Haka kuwa akayi, Hajiya ta sayi gida da kudinta a wajen palace ta koma can da zama, amma kuma mijin aure yaki samuwa, matsalar shine da wahala sarki ya saki mace wani kuma ya aura. Ummee ta sami Takawa da lallami tace tunda shi yace ba zai mayar da Hajiya ba to dan Allah ya samo mata mijin aure da kansa, saboda gudun kar azo a kuma yin wani abin kunyar, tunda har ta fada da bakinta cewa ba zaya iya zama babu miji ba, albarkacin 'ya'yanta, tunda komai tayi dole za'a ce uwar 'ya'yansa ce tayi. Babu jimawa Takawa ya samo mata miji, wani tsohon abokinsa da suka yi secondary school tare, mazaunin garin kauran namoda ta jihar zamfara. Hajiya akayi sabon aure aka tare da ango. Su saratu suka fara nuna rashin jin dadin su akan sabon auren da mahaifiyarsu tayi, Takawa yana ganin haka yace suma duk su fito da mazaje yayi musu aure, dama kowacce ashe da nata saurayin suna tsoron fada ne kar ace sunyi laifi, dan haka babu jimawa muka sha shagalin bikinsu muka kaisu dakunan su. Daya Kaduna daya kuma anan Abuja. Abbas kam ko daga kai bai yi ba akan sabon auren Hajiya, karatun sa kawai ya saka a gaba yana gina sabuwar rayuwarsa.
Kamar yadda mukayi shawara da sultan a Riyadh haka akayi. Sultan ya gina sabuwar obrphanage, amma wannan karon a Kano ya gina ta, yace next time kuma a Lagos zaiyi tunda sune manyan buranen Nigeria. Ya kashe kudi sosai wajen ginin da furnishings. Sannan yazo ya dauki ma'aikata. Sai da komai ya kammala sannan ya damka ta a hannun abokin sa Mahmud, nan take aka bada cigiyar yara wadanda aka yar a titi da kuma marayu da suke basu da galihu, daga 'yan kwana daya zuwa shekaru goma sha biyar, babu jimawa orphanage din ta cika taf, sultan yace shi baya son publicity, ba ya son ma asan cewa shi ya gina, dan haka ya bar ta a hannun Mahmud sai dai duk wata zasu yo masa bill din abinda suke bukata sai ya tura musu. Lokaci zuwa lokaci kuma muna zuwa mu gano halin da yaran suke ciki, kuma sosai muna jin dadin abinda muke gani dan mahmud ya rike amana sosai. Ranar da muka fara zuwa sai da nayi kukan tausayin yaran nan, wadansu jarirai wadansu 'yan kananan yara kuma wai duk marayu ne, amma kuma Alhamdulillah, gaskiya suna samun kulawa sosai dan sultan yana sakar musu kudi, abincin da suke ci ko wadansu yaran da suke zaune a gaban iyayensu ba zasu samu kamarsa ba. Sai dai soyayyar iyaye ce dole sunyi missing din ta. A duk wata sultan yana gama ware mana abinda zamu bukata na watan to next shine orphans dinsa, sai ya ware musu sannan komai ya biyo baya. Kullum kuwa arzikin sultan karuwa yake yi, kowanne wata abinda yake samu yafi na watan daya gabata.
Al'ameen yana da shekara daya a duniya muka nemi admission ni da Hafsat muka koma karatu, an sha rigima kafin su Ummee su yarda in tafi, twin house din na su Hafsat muka karba rent muka zauna a can. Kafin muje Zayed ya gama yi mana duk harkar registrations, dan haka ina zuwa karatu kawai muka fara. Bamu dade da fara karatu ba Hafsat ta haifi third child dinta, a girl, Aaysha. Daga nan kuma sai ta tsaya tace tayi uku sai ta huta kuma. Muna can Amina ta haihu itama, mun sami baby boy wanda yaci sunan marikin Ibrahim,

Please Login or Register in order to submit comment