Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da tafiya ta, ya bude motar ya fito ya sha gabana yana dariya "thank God bada mota kika zo ba da tuni kin gudu, wow, na tsorata da yawa fa" na dago kai na kalleshi, sai yanzu na kara ganin kakkarfan jikin shi. Ya cigaba "ko sunan ki fa baki gaya min ba, and after seeing your face kina tunanin zan iya bacci with out knowing your name?" Direct na bashi amsa "Sunana Hafsat" "I always like the name Hafsat, muje in sauke ki a gida ko?" na girgiza kaina nace "thank you, amma ni ba zan shiga motar ka ba, I don't know you" yace "sunana Sultan, shikenan?" Na sake girgiza kaina. Ya fahimci dai da gaske bazan shiga motar saba sai yace "to dan Allah ki bani address dinki mana" ba musu na bashi address din gidan su Amira, bakinsa har kunne yana dariya yace "ok, saura phone number" ya miko min phone dinsa na karba na saka masa tsohuwar number din Ibrahim da na haddace. Nishadi yake sosai yana jin dadi. Ya tarar min taxi na shiga sannan yazo window yace "it is very nice meeting you Hafsat, i will call you in na je gida" nace masa "ok, nice meeting you too Sultan"

Ga mamaki na sai na samu kaina da waiwayensa bayan motar mu ta ja, yana tsaye yana kallon motar mu ya saka hannayensa a aljihun wandonsa. Sai kawai naji tamkar na bar wani part of me with him. Na runtse ido na "ya ilahi, sultan is not my type, he is a rogue" amma me yasa sanda muke tare dashi naji for the first time na manta da Ibrahim? A lokacin da muka yi dariya ni da shi na manta da duk wadansu problems dina dana fito na bari a gida. Yanzu kam nasan ba lallai ne mu sake haduwa dashi ba, amma kuma nasan bazan taba mantawa da fuskarsa ba.

How do you guys like Sultan?
Masoyan Ibrahim ga rival anyi muku.



Episode Thirty Seven : The Dinner

Gaskiya kalamai ba zasu fayyace muku jin dadi na ba akan yadda labarin nan ya samu karbuwa. Nagode Allah ya bar kauna.

Masoyan Ibrahim kar ku bani kunya mana tun yanzu. Lol

Zaku ga changin yanayin rubutun labarin, nayi haka ne dan a samu fahimta sosai. I hope zakuyi enjoying sabon tsarin. Much love from maman maama 💖

Ya jima yana kallon motar har ta bace. Sannan ya juya ya shiga motar sa ya figa a guje ya dau hanyar palace. Yau dama sam bai yi niyyar fita daga gida ba. Tun daga nesa ya danne horn din motar sa, dama ya saba kullum abinda yake yi kenan, kowa sai yasan sultan ya shigo, ko mutun yayi bacci sai ya tashi. Yana shiga direct part dinsa ya wuce yayi packing a inda yake ajiye motocinsa. Direct bedroom ya nufa, yana shiga ya kalli kansa a cikin mirror sai ya bata rai yana kallon squeezed rigar sa "damn" ya fada kan gado da kayan sa complete har takalmi. Ya lumshe idonsa yana tuno every detail na fuskarta, it is like brain dinsa tayi automatically saving hotonta. "Hafsat" ya furta a hankali. Tunda yake bai taba yin serious budurwa ba, 'yammatan da yake haduwa dasu duk club girls ne da zasu yi rawa tare and that's all. Shi ba manemin mata bane sam, he consider it dirty. Ya dauko wayarsa ya dubo number dinta da yayi saving yana murmushi a ransa yana yabawa kansa dabarar da yayi na karbar number dinta maimakon shi ya bata tashi, dan yasan ba lallai ne ta kira shi ba. Ko ta karasa gida yanzu? No, unguwar da ta yi masa kwatance tana da dan nisa, bara ya bari a dan kara jima wa tukun. Ya ajiye wayar tare da gyara kwanciya. Har after 12 yana kwance a haka kuma baiyi bacci ba, ya sake dauko wayar yayi dialing "The number you are trying to call is currently switched off, please try again later" "damn you MTN" ya fada tare da jan tsaki. A cikin daren ya kira number takai sau goma amma still switch off ake gaya masa, maybe charge dinta ne ya kare, ya fada a ransa, amma baiji dadin haka ba saboda yana son ko yayane ya sake jin muryarta kafin yayi bacci.

Washegari tunda yayi sallar asuba yake zaune yana kallon agogo, jira kawai yake yi yaga gari yayi haske ya kira ta. 8:00 ya sake dialing number ta amma still switched off. Damn it, kar dai ace wrong number ta bashi, in haka ne kuwa to tabbas address din ma wrong ta bashi. Ya mike da sauri ya shiga wanka, nan da nan yayi ya fito. Duk gayun sa yau da sauri ya shirya cikin usual body hug kayansa, yana fitowa ko kallon bayin da suke zazzaune a falo da abincin da aka shirya masa a dining table bai yi ba ya fice. Agogon hannunsa ya duba yaga karfe goma, yasan tunda Takawa yana gari to duk mutan gidan suna falonsa yanzu. Shima direct can ya wuce, duk masu gaishe shi a hanya babu wanda ya kula, yana shiga yaga Takawa a zaune a kan shimfidar da ake masa ta cin abinci a tsakiyar palon, Hajiya tana kusa dashi daga hannun dama Abbas kuma daga hannun hagu, daga gefe kuma saratu ce da Fa'iza. Daga dukkan alamu hira suke suna dariya har Takawan, shigowar Sultan ce tasa Takawa ya hade girar sama data kasa tamkar bai taba dariya ba, Sultan ya karasa gabansa ya durkusa "barka da assuba" bai samu amsa ba kuma dama bai sa ran zai samu ba, ya mike ya koma kusa da Hajiya ya zauna tare da dora kansa akan kafadarta, ta sa hannu tana shafa gashin kansa a hankali "yaron kirki yau kuma da wuri aka tashi haka? Ko wani gurin za'a je ne" ya girgiza kai yace "no Hajiyata, part din Amir zan shiga nace bara in shigo in gaisheku" Abbas yace "yaya Sultan barka da assuba" sultan ya kirkiro murmushi yace "Abbas, ya kake?" Su saratu ma duk suka gaishe shi daga nan sai kowa yayi shiru. Sultan ya danyi jim a zaune sai kuma ya mike yace "Hajiyata bara inje" tace "to yaron kirki, a dawo lafiya" ya karasa gaban Takawa ya sake durkusawa "a huta lafiya" nan ma babu amsa. Sai da ya fita ya turo kofa sannan yaji muryar Takawa sun cigaba da maganar da suke yi da Abbas. Ya runtse idonsa zuciyarsa tana masa zafi sannan kuma ya saka hannayensa a aljihunsa yayi gaba.

Kamar yadda yayi tsammani, rashe rashe ya tarar da Amir yana ta shirgar bacci, Allah ne kadai yasan jiya karfe nawa ya kwanta bacci dan tunda yace Solomon ya zo gari to yasan sai sun raba dare a club. Tsaki yaja ya daddaka masa duka a cinya "kai tashi daga baccin nan haka" Amir ya bude ido cikin bacci yana kallon sa, "what happened naga har ka shirya, ko ta samu ne?" Sultan yace "eh ta samu, babban samu ma kuwa" nan sultan ya zauna ya bashi labarin haduwar su da Moon da yadda wayarta bata shiga, tunda ya fara maganar Amir kawai kallonsa yake yi, sai da ya gama sannan yace "in baka shawara abokina? Kawai kaje kayi ta addu'a dan kuwa ina da tabbacin gamo kayi da aljana" dariya sosai Sultan yayi sannan Amir yace "to in ba aljana ba Sultan ni ban taba ganin ka damu da wata mace ba, daga jiya zuwa yau har kabi ka tayar da hankalinka akanta, tunda har ta baka wrong number ai bata yi da kai ne" Sultan yayi sauri yace "a'a, raka ni zakayi address din mu gani, maybe wayar ta samu problem ne" Amir yace "wai kana nufin yanzu? Haba rankai dade, duk matsuwarka ai ka bari yamma tayi zuwa dare ko? Saboda tsabar kai sabon shiga ne, ka hadu da yarinya jiya da daddare sannan kawai yau da safe kaje gidansu" Sultan ya fada kan gadon kusa da Amir ya lumshe idonsa, a hankali yace "baka san yadda nake ji bane Amir, ba zaka gane ba"

Moon

Tun dana tashi da assuba ban koma bacci ba, muna ta hidimar kamu da mother's eve da za'ayi yau. Sam na manta da wani Sultan duk da jiya da daddare da kyar nayj bacci ina ta tuna abubuwan da suka faru a tsakanin mu. Anyi taro lafiya an gama lafiya babu wata matsala sai rigimar da akayi da Hafsat akan ita fa lallai ba za'a zuba mata nono aka ba, sai da aka rirriketa kamar mai aljanu sannan aka zuba mata, dan muguntar hajja kwarya guda ta juye mata. Mu dai muna ta dariya. Hajja ta juyo tace min "in naki yazo wanka zanyi miki dashi" Munir kam ya zamar min tamkar jela, cikin mata ko cikin maza duk inda nayi sai ya bini kuma sai yayi maganar da zata sa a gane akwai wani abu a tsakanin mu. Washegari da wuri jirgin su Zayed ya sauka shida abokan sa guda biyar, sai Waliyansa su uku. A ranar ne kuma zamuyi dinner da daddare, Zayed ya kawo mana kayan da zamu saka ni da Hafsat, dogayen riguna ne masu kyau, wadanda kuma suka rufe mana jikin mu ruf, iri daya ni nida ita sai dai banbancin color, ta Hafsat golden tawa cream. Ni samun wannan rigar yasa duk na manta da dinkin mu a gurin tailor ni da Amira wanda da muka yi niyyar zamuyi anko ni da ita. Ban tuna ba sai da muna shiryawa ta kira ni tace gata nan zuwa. Ai kuwa ina gaya mata ai ban karbo ba ni na samu wasu kayan ta hau bala'i daga karshe ta kashe wayar gaba daya. Nima nasan ban kyauta mata ba amma abubuwa ne suka yi min yawa shi yasa. Har muka gama shiryawa muka tafi Amira bata zo ba, nayi ta kiran wayarta kuma bata dauka, a karshe na hakura na rabu da ita.

Sultan

A hankali suke bin address din har suka zo gidan. Suna yin packing Amir yace "to munzo, now what?" Sultan ya dan sosa kansa yace "ya akeyi in anzo gurin budurwa?" Amir yayi tsaki yace "ideally kiranta zakayi a waya, to tunda kai baka da number dinta sai ka nemi yaro ka tura shi ya kirata" Sultan ya bude kofar mota ya fito yana ta zagaye ya rasa dan aike, sai da kyar ya samu wani yaro yace masa ya shiga yace ana kiran Hafsat, can yaron ya dawo yace "wai ance babu Hafsat anan gidan" ya juya suka dubi juna shida Amir, Amir ya kyalkyale da dariya yace "sai kazo mu tafi ai, yau dai ka barni inyi bacci tunda ka tabbatar yarinyar nan tayi playing dinka" sultan ya juyo jiki ba kwari ya shiga mota, har zaiyi mata key sai kuma ya dakata yana tunani, can yace "no, bazan hakura ba, tunda har tayi min kwatancen nan gidan to inhar ba gidan su bane ba to gidan 'yan'uwansu ne, ko kuma gidan su kawarta, yes, zan jira inga wanda zai fito daga gidan in tambayeshi ko ya santa" Amir binsa yake da kallo har ya gama sannan yace "you are not serious are you? Kana nufin zama zamuyi tayi a gurin nan har sai wata ta fito mun tambayeta? What if babu wanda ya fito har gobe?" Sultan yace "then I will wait har gobe, in kaga ba zaka jira ba kayi tafiyarka ban hana kaba" tsaki Amir ya sake yi ya kwantar da kujera tare da kunna kida, Sultan kuwa ya fito ya jingina da jikin motar idonsa na kan gidan. Shiru2 har wajan awa daya babu alamar wani zai fito, kuma unguwar shiru babu motsin mutane ballantana su nemi wani information. Amir har yayi baccinsa amma sultan yana tsaye kamar soja. Wannan shine kadai link din da yasan zai same ta dan haka ba zai yi wasa da wannan damar ba. Can kawai yaji motsi daga ciki, sannan yaga an bude karamar kofar gate din. Wata budurwa ce ta fito, doguwa, baka kyakykyawa. Taci kwalliya irin ta kure adaka dinnan, daga gani kasan gidan biki zata je. Suna hada ido da sultan ta danyi baya alamar tsorata sannan kuma ta maze ta rufe kofar tana gyara mayafin ta. Sultan ya karasa kusa da ita yace "Assalamu Alaikum" ta juyo ta watsa masa harara tace "alaikassam, ya akayi" kut, wannan badan information yake nema a gurin taba da sai ya babballata. Ya daure yace "please, wata ce ta bani address din nan gidan tace gidan su ne, sunan ta Hafsat" Amira ta sake yi masa kallon wulakanci tace "ko wacece karya tayi maka, nan babu Hafsat, oyo san inda dare yayi maka" lallai wannan yarinyar bata san hali ba. Daga bayansu suka ji ance "Hey, who do you think you are ana miki magana kina yiwa mutane rashin kunya, da wata mummunar fuskar ki anan, ko ki bashi amsar tambayarsa ko kuma wallahi.. " ta katse shi "ko kuma me Amir? Zaka dake ni ne?" Mamaki ne ya ishe shi yadda ta san sunan shi kuma ta mayar masa da magana ba tsoro. Har ta juya zata tafi Sultan ya sake binta "please, ko cikin kawayenki babu wadda kike tunanin zata bada address dinki?" Kamar ba zata kula shi ba sai kuma ta juyo fuskarta da murmushin mugunta tace "ya kamanninta yake?" Da sauri sultan yace "fara, fulani, very beautiful, tana da dimples manya guda biyu" murmushin mugunta Amira ta sake yi, Amir ya karaso yace "so? Do you know her or not" ba tare data kalleshi ba tace "shut off" Amir ji yayi kamar ya gaggaura mata mari, ko ba yau ba sai ya koya wa yarinyar nan hankali. Ta kalli sultan tace "na gane ta, yanzu ma tana gurin bikin da zanje" wata ajjiyar zuciya Sultan yayi yace "to shigo mota mana mu tafi" ta girgiza kanta tace "no way zan shiga motar ku, Allah ya raba gatari da saran shuka, in kuna son ganinta ku biyo ni" daga haka ta juya tayi gaba. Da sauri sultan ya koma mota ya tayar yana ta yiwa Amir horn dan yayi sauri ya shigo, Amir kuwa bakin ciki ne ya cika shi, wai ba zata shiga motar su ba, wacece ita?. Haka suka yi ta bin Amira a baya har ta fita titi ta samu taxi ta shiga, suka cigaba da bin taxi din har Sheraton. Amir yayi tsaki yace "maimakon kawai tace mana Sheraton, sai ta saka muka ringa binta a baya kamar wasu yaranta. Wannan budurwar taka should better be worth this in ba haka ba akanka zan huce" Sultan yace "believe me, she is worth morethan this" suna fitowa Amira tayi musu nuni da hall din da ake taron tayi shigewar ta ta barsu.

Moon

A matsayina na kanwa kuma babbar kawar amarya nice na ke zaune a kusa da ita a high table, sai Zayed da babban abokin sa Hamad. Ana cikin tsakiyar taron na hango Amira ta shigo, sai da ta gama shawaginta suna gaisawa da mutane sannan ta karaso high table, nan nayi introducing dinta a gurin su Zayed sannan muka dauki hotuna. Sai da muka gama sannan tazo dai dai kunnena tace "I brought a gift for you. Saboda bari na da kikayi babu kayan sawa yau" har ta juya kamar zata tafi nace mata "what gift?" Tace "Sultan, yana bakin kofa" nayi sauri na kalli hanyar shigowa, ga mamaki na kuwa sai naga masu gadin kofar suna ta hayaniya, har mutane sun fara tsayawa kallo. "Damn you Amira"


Episode Thirty Eight : The Shadow

Gaba nane ya fadi da muka hada ido da munnir wanda ya kasa ya tsare yana kallon duk wanda zai yi min magana. Na tabbatar sultan yana shigowa zai hangoni tunda ina kan high table, yana gani na kuwa zai taho, Allah ne kuma kadai yasan abinda zai faru tsakanin sa da Munnir. Na rada wa Hafsat "two minutes, ina zuwa" ta yi sauri ta rike hannuna alamar bata so in tafi in barta, nayi mata alamar yanzu zan dawo. Cikin friends din mu na dan shiga, ina kallon munnir ta gefen idona yana bina da kallo, sai da na tabbatar baya gani na sannan nayi hanyar gate da sauri. Ina zuwa kuwa na ga Sultan ya dunkule hannunsa ya naushi wani mai gadi, nan na nan jini ya fara fita ta hanci ta baki, maybe ma hakori ya fita, wanwar gayen ya fadi a kasa yana gunjin azaba, sultan ya durkusa kusa dashi, na dauka ma hakuri zai bashi, sai naga ya goge jinin daya bata masa hannu a jikin rigar gayen, ya mike tsaye yace "who is next?, dan rainin hankali har ni zanzo ince zan shiga guri ku ce min card admit ne, da card din da admit din duk naci uwarsu gaba daya" da sauri na karaso gurin cikin fada nace "what the hell are you doing" sai a lokacin ya ganni, hannu duk biyun ya saka a cikin gashinsa tare da cewa "shit" na durkusa gurin mai gadin da aka daka wanda har yanzu ya kasa tashi, da sauri sauran guards din suka karaso suka kamashi suka tafi, na mike ina kallon sultan daya kasa hada ido dani nace "what are you doing here?" Ya karaso kusa dani yace "am sorry" sai a lokacin na lura da wanda suke tare, zasuyi kusan tsaho daya da sultan amma bazan tantance kibar saba saboda uban kayan daya loda a jikinsa duk kuwa da yanayin zafin da ake ciki, kansa yasha kwal kwal amma kuma ya bar saje a fuskarsa. Kallo daya nayi masa na maida kallona kan sultan wanda yasha kwalliya dan daga gani wannan shigar ta musammance. Har yanzu ya kasa magana ni kuma na bata rai na tsare shi da ido. Abokinsa ne ce "so, kece Hafsat kenan, kwana biyu wannan sunan har acikin bacci kiransa yake" sai a lokacin na tuno cewa ashe fa ce masa nayi sunana Hafsat. Na sake cewa "uhum, ina jinka, me ya kawoka nan?" Ya sake hargitsa gashin kansa sannan yace "I just wanted to see you ne, please, number da kika bani bata shiga, shine naje address din shima na tarar wrong ne da kyar yarinyar gidan ta kawo munan" nace "OK, ka ganni zaka iya tafiya yanzu" ina fadin haka na juya zan koma ciki, da sauri yasha gaba na, fuskarsa kamar wani abin tausayi "please kar ki koma" nace "serious, bani da lokaci, biki muke yi, na tabbatar yanzu ma nema na akeyi a ciki" da sauri yace "OK, at least ki gaya min sunanki na gaskiya, ki bani number dinki ta gaskiya" ya saka idonsa cikin nawa pleadingly, kawai sai naji na daina jin haushinsa, ya danyi murmushi tare da cewa "pretty please" na danyi murmushi nima kadan. Abokinsa ne yace "OK, lokacin introducing dina yayi" daga ni har sultan babu wanda ya kalleshi, sam ya kasa dauke idonsa daga cikin nawa, ni na fara dauke kaina nace "i really must go inside" yace " OK, sunanki na gaskiya" nace "Maimunatu" ya dauko wayarsa yace " phone number?" Har na fara fada masa sai ya dakatar dani yana karkada hannunsa "not again, an sha ni na warke" ya miko min hannunsa "bani wayarki" na gane me yake nufi dan haka nima nayi dariya tare da mika masa wayar, ya karba ya saka number dinsa yayi dialing, da kiran ya shiga wayarsa sai da ya dauka ya tabbatar shine sannan ya kashe ya miko min waya ta. Ina karba naga an bude kofar hall din an fito, a tsorace na waiga, yaya Habeeb na gani a tsaye yana kallon mu ni da Sultan, sai kuma ya koma ya maida kofar ya rufe. A sauke ajiyar zuciya nace "zan koma kaga already ana nemana" ya gyada kai yace "it is OK, nagode sosai, and please don't block my number" nayi murmushi nace "I won't" na juya na kama hanyar komawa ciki, naji abokin sultan yana cewa "hey, bakayi introducing din mu ba fa" sultan yace "shut up Amir".

Tunda na koma na cigaba da activities dina har aka tashi ban kuma tunawa da wani sultan ba ballantana his troubles, bayan an tashi munje gida duk mun sallami friends din mu, zamu hau samanmu kenan sai yaya Habeeb ya kira ni, na juya na koma duk jikina a gajiye, so nake kawai in ganni a kwance. Ina zuwa naga ya bata fuska yace "dazu dawa na ganki a gurin dinner" sai a lokacin na tuno da wani sultan. Nayi ajjiyar zuciya nace "Sultan ne, dan sarkin Abuja" yace "nasan ko shi waye, kece baki san sultan ba shi yasa har kika tsaya dashi. Duk inda kike tunanin sa ya wuce nan. In ana zancen top criminals a Abuja sunan sultan yana daga layin farko" nace "ya Habibi babu komai fa a tsakanin mu, naga cewa idan ban kula shi ba zai iya tayar da rigima a gurin shi yasa na kulashi, but I know he is a trouble maker and all.. " ya Habeeb ya katseni "trouble maker? He is not just a trouble maker Moon, he is a drunk" ji nayi tamkar ya Habeeb ya watsamin ruwan zafi a fuska, a drunk? Har naje dakin mu jikina a sanyaye yake, can kuma nace a raina, me yasa na damu, it is not as if na damu dashi. Direct toilet na shiga na yi wanka nayi shirin bacci, ina fitowa na ga Hafsat har tayi bacci, nima na kwanta nayi addu'ah. A drunk, but how, me yasa ya zabi wannan rayuwar? Me yasa ya zabi abokai irin su Amir? Dan manyan mutane kamarsa, dan Sarki, sarkin ma na federal capital, how can he be what he is? Me yasa iyayensa ba zasu dau mataki a kansa ba? Waya ta naju tayi kara, na dauka na duba screen "my Sultan" naga an rubuta, nayi murmushi, wato haka yayi saving number dinsa a waya ta kenan. Na ajiye ta na barta tayi ta ringing dinta har ta katse, wani kiran ya shigo sannan wani. A drunk, na maimaita a raina. Take na yanke shawarar in dauki wayar in gaya masa cewa bani da interest a kansa yayi hakuri. Tana fara wani ringing din na dauka "Assalamu Alaikum" naji yace. Assalamu Alaikum, peace be unto you. Wannan itace kalmar daya fara fada min ranar da muka hadu a Hilton. Mutane nawa ne a cikin mutanen kirki suke sallama idan sun kira ko an kira su a waya. Mostly hello ko hi ake cewa wanda ba dai dai bane, amma shi a matsayinsa na known criminal me yasa yake yi min sallama. Ko hakan yana nufin some part of him is good?. Wannan kalmomi na Assalamu Alaikum da Sultan yace min sune suka sa na fasa yanke alakar ta dashi. I feel like I want to know him better.

"Assalamu Alaikum" ya sake maimaitawa, sai a lokacin na samu damar amsa masa "ameen, wa alaika assalam" ya sauke ajiyar zuciyar da sai da naji daga cikin wayar, "sorry I kept calling, ina so ne ko yaya in danji muryarki kafin nayi bacci" nayi shiru babu amsa, yace "ya taron? Da fatan baki gaji da yawa ba" nace "gajiya kam akwaita, sai godiyar Allah" "sorry" na danyi murmushi saboda yadda ya furta kalmar sorry din, ya sake cewa "am really sorry akan abinda ya faru dazu, I came to your party uninvited kuma na yi creating commotion, I just can't hold my temper ne most of the times" nace "it is OK, ya wuce, Allah ya kiyaye gaba" "Ameen, thank you for understanding" kasa2 naji suna magana da wani, nace "kai da waye ne?" Da muryar dariya yace "Amir ne, wai koya min zance zaiyi, wai ni ban iya ba" nace " He is funny" yace "yes he is, bari in barki ki huta kin gaji ko? Na gode da daukan waya ta da kika yi, you have no idea how much it means to me" na runtse ido na inajin kalamansa har cikin raina. Nace "good night" yace "fi amanillah" daga nan ya kashe wayar. Na kara runtse idanuna

Please Login or Register in order to submit comment