Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsole mata ido. Abu kadan ne zata yi ta kai mata hannu da duka amma Mairama bata taba tankawa ba. Lokuta da dama wurin Yadikko suke zama ko Hajjo idan 'yan mutumcin suna kusa.


Wata rana ta gama zobonta da lamurje ta kukkulle a leda santana suna cikin wani katon baho a nan bakin famfon tsakar gidan inda take aikinta ta tashi ta tafi jawo ruwa a rijiya zata wanke wurin. Salame tana ta fakonta don dama ta gane yanayin aikin nata. Idan ta gama kullewa sai ta janyo ruwa ta wanke wurin sannan ta dauka ta kai firig dinta ta jera. Su kan wuni da wuta amma da wuya ta kwana. 


Tafasasshen ruwan zafi Salame ta taho dashi a bokiti tayi daurin kirji kamar mai niyar shiga wanka sai da tazo daidai bakin bahon da kayan Mairama suke ta sheka musu ruwan nan. Ledojin dole suka yi laushi sunyi tsamo tsamo babu dadin tabawa. Salati ta soma yi wai wucewa zata yi ta sirka ruwan wankanta don ta ga kamar famfon wurin yana diga an kawo ruwa. Mairama ci gaba tayi da diban ruwanta sai da ta ciko bokiti tana zuwa ta ajiye shi sannan ta cira hannu ta kwashe Salame da mari mai gigitarwa don tana kallon yadda komai ya faru.


Ihu ta kurma gidan da suke neman abin gani kuwa aka fara fitowa bawa ido abinci.


"Ni kika mara Mairama?"


Rai a bace Mairama tace "ko zaki rama ne?"


"Kan bala'i, billahillazi baki mari banza ba sai na rama"


"Gaki ga kumatun Adda Salame. Na gaji da wannan abubuwan da kika tsira tun kafin muyi aure har yanzu ana abu daya. Kece dukan min yara, yada min habaici da bakaken maganganu duk akan me? Me na tsare miki?"


"Dole kice haka mana tunda kin rabani da wanda nake so"


Yadikko na jin haka ta kora yaran gabadaya tace su shiga dakinta. Hajjo ba kunya ta bisu don jin ba'asi. Salame kasa karasa bayanin tayi don tasan ita ce da jin kunya. Tabarmar kunya ta nade da hauka wai Mairama tana yi mata gani gani saboda ta fara rike kudi.


Da daddare da Malamijo ya dawo Yadikko ta bashi shawarar ya raba musu daki mana.


"Babu wadda ta bani ko asi domin ginin gidan saboda haka idan zasu cinye kawunansu ne ma su cinye bai dameni ba. Wadda taji haushi ta kawo miji tayi aure"


"Idan bazaka rabasu ba ka taimaka ka zame musu uba na kwarai ka kawo karshen wannan rashin jituwa da yake tsakaninsu. Kafi kowa sanin cewa da ba haka suke ba"


Shu'umar dariya yayi kafin ya turo hularsa gaba ya bata amsa "ki kan bani mamaki wani lokacin kamar baki san zafin zawarci ba. Kodayake baki taba danawa bane amma cuta ce mai zaman kanta. Shiyasa kika ga suna harin junansu. Babu mai tayar min hankali ni dai"


Babu yadda ta iya haka ta tashi ta bar dakin nasa tana kara godewa Allah da bai bata haihuwa da Malamijo ba.


Mairama ta gama yiwa Karami shirin bacci ta goya shi tana jiran kanwarta ta kawo Radhiya da take wasa a wurinsu Salame ta shigo ta dawo daga zance da dan gayun saurayinta. Matashi ne ko auren fari baiyi ba. Baje ledar da ya bata ta tsire tayi a gefen katifarta da burin cusawa Mairama haushi. Abin dariya yadda take ci tana shuu da baki.


Tana ganin Radhiya ta sake bude ledar da kyau. Yarinya tace "Ummi nama"


Mairama ta dauko wata leda babba ta mikawa Na'ima kanwarta tace suje su raba sannan ta dauko wata 'yar madaidaiciya ta bude ta janyo hannun Radhiya ta bata cinyar gasasshiyar kaza. Sai yanzu take gode Allah da haka nan ta bawa Bature kudi ya siyo kajin nan guda uku. Ta dauki daya ta basu biyu su raba. 


Ai kuwa Salame ta shaka har wuya ta shiga fadin maganganu wai gara su suna kwance ake basu. Wahalallu kuwa sai sunyi da karfin jikinsu kafin su dandani zakin nama.


Shiru ma magana ce. Mairama bata ce mata komai ba haushi ya kamata tsiren ya fice mata a rai.


"Dazu nace kin rabani da masoyina baki tambayi ko waye ba bare ki bani hakuri"


"Indai Salisu ne nayi imanin bazai sakeki saboda ni ba. Allah kadai Yasan dalilin mutuwar aurenki sai kuma ku kanku"


Kallon cikin ido ta yiwa kanwar tata "Mairama, na rigaki ganin Zayyan kuma na rigaki fara...."


A harzuke Mairama ta tashi duk wani kulli na kanta yana kwancewa. Yanzun ta gama gano duk abubuwan da Salame tayi mata sunfi kama da kishi. Duk da mijin nata baya raye amma tana tsananin kishinsa itama.


"Ya isheni ba sai kin karasa ba, na fahimci da aurenki kike son nawa mijin. Idan abinda Salisu ya gano ya sakeki kenan sai ince Allah Ya dada karawa."


Daga haka bata koma cewa komai ba sai da ta tabbatar Salame tayi bacci ta sha kuka ta godewa Allah. Ta tabbatar Zayyan ya sani shiyasa shima baya son Salame saboda kada yaci amanarta. Sabuwar kewarsa ke ratsa duk wani sassa na jikinta tana inama yana nan tare da ita.


***********


Shekararsu biyu a gida Salame tayi aure. Kafin auren Mairama ta tuna cewa Salisu abokin Hadir ne a lokacin ta kwantar da kai wurin sau uku tana tambayar Salame kwatancen gidansu Salisu. Ita kuma ganin ta matsu tasan ko meye yana da mahimmanci shiyasa taki fada. Gashi baya zuwa garin don idan za'a kawo mata Halifa aiko drebansa yake likkafa ta kara ci gaba.


Bayan auren Salame ne Idris dan gidan Mal Kallamu abokin Malamijo ya sami aikin koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati ta cikin Sumaila. Da yake suna shiri da Mairama kamar wasa ya gabatarwa Headmaster da ita akan ko 'yan aji daya ne ta samu ta rinka koyarwa. Shine ya amince aka yi mata cuku cuku sai gashi ta sami aikin a karkashin L.E.A. Kwalin karatun nata iyakarsa sakandire shiyasa bata wuce aji daya ba a koyarwar. Ita dai ko yaya ne hakan yayi mata don albashinta yana mata rana ga cinikin zobo da lamurje.


Haihuwar Salame daya aurenta ya sake mutuwa. Wannan karon lalaci da rainawa miji ya janyo mijin ya saketa. Duk abinda zai kawo mata sai ta karba a wulakance tace ba haka baban Halifa yake yi ba. Sai da ta kaishi makurar da yayi mata duka ya sakota.


To yanzu ma an sake dawowa gidan jiya. Dan da ta sake haifa shima babansa ya kaiwa yarsa. Ta dawo gida an sake komawa zaman zawarci ga rashin abinyi. Bakincikinta ya karu da yadda Mairama da yaranta suke rayuwa ta rufin asiri. Duka suna karatu a inda take koyarwa. 


Ta soma saka gilashi ne a lokacin da ta fara fama da matsanancin kaikayin ido da gani dishi-dishi. Ta sha wahalar idon sosai ta kuma kashe kudi.


**********


Sun dawo gida da Emzee ya shiga dakunan duka matan gidan su hudu don tuni Malamijo ya sake cike gurbi. Yadikko tana nan a matsayin uwargida Hajjo kuma ta biyu sai amare Hanne da Binta.


A gajiye take ta kwanta tana murna anyi hutu. Sallama taji anayi ana kwala mata kira ta tashi a zabure Salame tana kwalliya zata je wurin mamanta.


"Uwar yarinyar nan Alhihi take ko me kace Danmama?"


Danmama ya zumburo baki "Alheran amma Radhiya naji ana cewa. Ita ce ta mareni kuma Anti batayi komai ba saboda 'yarta ce"


"Allah gamu gareka" Mairama tace a ranta kafin ta fita tsakar gidan zuwa wurin matar.


"Hajiya kiyi hakuri rigima ce irin ta yara kuma tun a wurin an hukunta su"


Rai a bace tana nuna bayan Danmama ta ce "a hukuncin ne aka yi masa bulala biyar ita kuma biyu saboda son kai. Dama wane adalci kuke yi idan kuna koyarwa a makarantun da 'ya'yanku suke. Daga yau sai yau ki jawa 'yarki kunne. Idan ta sake taba min yaro bazan yarda ba"


Hakuri Mairama ta bata duk kunya ta isheta. Radhiya ba dai dauko magana ba. Idan anyi magana tace ita 'yar soja ce. Yadda take alfahari da aikin babanta sai ka rantse ta tashi tare dashi. Ko ina ta tsaya ma yanzu bata sani ba. Bari dai ta dawo yau mai rabasu sai Allah.


Ashe gidan Mal Kallamu ta bi Uncle Idris. Can taci abincinta a bangaren amaryar Idris din sannan ta fito suka hadu da Malamijo a kofar shiga. Harararta yayi kamar ya kwadeta jiya taje gonarsa ta sami wani sabon maikaci da yayi ta nuna masa wata tinkiya wai Malamijo ne ya aiko ta fada masa a yanka ya dau kai da kafa. Ana cikin fida yazo ya gani jikinsa na tsuma yayo kanta tace gani tayi ta kasa. Kunnenta ya damko tana ihu 


" 'Yar kundun uba ta ina kika ga ta kasa din?"


Ba yadda ya iya a dole jiya gidansa aka ci dafge kowa ya warwasa. Dakinsa ta bishi yana gwawiyar kashi tace "Malamijo ashe kaima kana son naman dai. Allah Yasa in ga wata ta kuma kasawa" da mafici ya biyota har yana tuntube.


Ita ce a gaba ta hango Umminta da Danmama da mamansa. A guje tayi niyar komawa Malamijo ya riko wuyan rigarta ya kaita gabansu.


"Mairama ki jawa 'yarki kunne idan ba haka ba wannan karon idan kunje hutun Sakkwato ki barta a can. Yarinya ce kamar aljana. Dubi kaninki nasa salihancin har haushi yake bani. Ke kadai kina mace kin tattaro duk halayen kiriniyar kin dorawa kanki"


Kallon da ta ga Mairama na yi mata tasan yau jiki zai fada shiyasa tana tura baki da magana ciki-ciki tace "to ba shine yake wakar wai Malamijo tsolon rake ba, rama maka fa nayi"


Jikin Malamijo da na uwar Danmama sai yayi sanyi. Danmama yayi wiki-wiki da idanu hakan ya tabbatar ba karya take ba. Babarsa kuwa ta talle masa keya tana cewa ya bashi hakuri. Yara kuwa sai dariya suke a hankali Malamijo yaji kunya ya shige daki. Kunnen Radhiya Mairama ta kama tace ta wuce daki. 


Da yamma ranar sai ga Alh Ado Indararo da kansa yazo bayan matarsa ta fada masa abinda Danmama yayi. Sun saba ciniki da Malamijo baya son kasuwar ta watse don yana dukan hancin Malamijo akan dabbobinsa sosai batare da shi ya sani ba.


Ya bashi hakuri ya nemi Mairama itama ta fito da babban mayafi ta gaishe shi. Kallon farko Alh Indararo ya fada kogin kauna baya ji baya gani. Tana komawa ciki baiyi kasa a gwiwa ba ya fadawa Malamijo bukatarsa. Zani ce ta tadda muje mu. Shima kwadayin kudin Alhajin yake yace ya bar masa wuka da nama.


A daren ya sanar da ita tayi tsalle ta dire tace bata da sauran aure a duniya. Sun fara rigimarsu bayan kwana biyu ta tattara ta tafi Sakkwato kamar yadda ta saba duk hutu suna zuwa suyi sati daya ko kwana goma.


Duk gidajen 'yan uwan Zayyan na jini da makusanta irin su Mal Aminu sai taje. Kuma bata fasa zuwa barikinsu ba ko zata sami labarin Zainab da Mami. Gidan iyayen Zainab yanzu wasu ne a ciki. Ta matsu tasan halin da suke ciki amma babu dama. Haka kuma har yau babu wanda ya kirasu akan wani kudi na ihsani ga jaruman da suka rasu.


Suna hira da matar Maikudi da Jume Maikudin ya shigo yana hade rai. Shi yafi kowa sanin babban dalilinsa na kin zuwansu garin amma bazai iya fadawa kowa ba. Yaran dama baya sakar musu fuska. Sai dai suna da kyakkyawar mu'amala da 'yan uwansu wato jikokin gidan. Satinsu daya suka juya Jume kamar a bar mata su. Babbar damuwarta shine rashin kowa daga bangaren Innar Zayyan wanda Jume tace har yau itama tana zuba idanu ne.


Maikudi bai sami sukuni ba sai da suka bar garin. Sirrika biyu yake boyewa Mairama saboda mugunta da kuma son kai irin na dan Adam.


Na farko dai wata shida da rasuwar Zayyan kawunsa Sidi yazo bisa shawarar 'yan uwa. Ashe ya tura musu wasika da zai tafi ta tasha. Sidi yazo gari Jume da matan gidan sun tafi Tureta biki. Maikudi kawai ya samu su Badaru basa gida. Lokacin yana tsaka da jin haushin rashin mutumcin Malamijo kuma yasan idan mutanen nan suka san da zamansu ba karamin alheri zasu rinka musu ba. Wanda zai koma jikin Malamijo a karshe. Saboda haka ya matso hawaye ya sanar dashi mutuwar Zayyan da kuma hatsarin da su Mairama suka yi ita da 'yarta suka rasu gabadaya. Wannan shine dalilin da yasa aka dena ji daga garesu.


Abu na biyu kuma shine aike duk karshen wata daga kasar Germany wanda Retired Major Mustapha bai taba dena yi ba tun bayan samun lafiyarsa da aiki a can din kusan shekaru hudu. Kudi ne yake turowa ta hanyar wani soja da yake karkashinsa a da kuma ya yarda dashi. Wannan mutumi duk wata Maikudi yasan ranar da yake zuwa har barikinsu ya karbi kudin da suke mazaunin kudin makarantar Radhiya da kuma tallafi ga Mairama. Soke abinsa yake ga gidan Kano ya saka 'yan haya. A takaice dai yana ta gina kansa don ya sayi fili a cikin Sakkwato yana ta makara gini da kudin marayu.


**********


Mairama ta koma ta tarar da babbar kura. Malamijo ya karbi sadakinta daga hannun Alh Indararo an saka biki wata uku kafin ya gama yi mata gyaran gida. Ta shiga matsanancin tashin hankali har Nene Marka tazo amma kowa cewa yake tayi auren ko zata sami hutu itama. 


Tayi kukan, tayi haukan duk a banza bata da mai tsaya mata. A bangare daya kuma duniyar Salame ta juye. Mutum kamar Alh Indararo ace yana son mace kakarta ta yanke saka. Shine wannan karon ma irin abinda take muradi ya tafi ga Mairama. Rantsuwa tayi cewa hakan bazata sake sabuwa ba.


Gidan Malaminta da suka saba kashewa kudi domin a dawo mata da Salisu taje. Bayan dogon bugun kasa yace ta saka ranta a inuwa akwai rabo yana iya gani tsakaninta da Alh Indararo amma sai an kawar da Mairama.


"Malam rufa min asiri kanwata ce fa. Ni dai bazan iya kasheta ba"


Gemunsa na munafurci da suke cutar jama'a dashi ya ja yana murmushi "waye yace sai kin kasheta. Idan kina so nakasa kawai zamu dora mata wadda zata saka ya fasa."


Kwana biyu tana tunani kafin ta hasko me take son ayiwa Mairama. Magani ya bata ta wuce gida ta saka a inda ya umarceta.


Kwana uku a tsakani kuwa wata safiyar lahadi Mairama ta tashi bata gani sai dususu komai yayi hazo. Cikin maganin digawarta na ido Salame ta zuba mata maganin. Cikin wata guda idanun Mairama sai suna. Duk abinda ya rage mata ya kare a neman maganin ciwon idon amma asibiti basa ganin komai.


Kuka ashe bai kare mata ba. Bata gane kowa sai duhun inuwa. Tashi guda Radhiya ta koma idanunta madogararta. Alh Indararo ya canja sheka bazai iya auran musaka ba Salame har ta tare abinta.


Karatun yaran ya tsaya yau da gobe Malamijo ya gaji da dan mikawar da yake yi. A bisa dole ta hakura da karatun Radhiya da Emzee. Tana kuka kan kuka amma mahaifinta bazai iya kulawa da ita ba bare 'ya'ya, iyakarsa dasu shine za'a dafa abincin gidan dasu. Radhiya ta fara hankali tasan cewa mahaifiyarta tana bukatarta shiyasa bata fita idan ba aike ba. Emzee kuwa dama daddawar daka ne shiyasa bata hadu da matsalar ace suna yawace-yawace ba. Rayuwar Mairama matar soja ta cika da wahalhalun da suka sa take bukatar a dube ta.


***********


Maza ne uku a karkashin bishiyar darbejiya wadda ta yiwa wurin yalwatacciyar inuwa. Daya yana zaune  akan kujera sauran biyun kuma suna gabansa ne kana gani kasan mai mulki ne da wadanda yake mulka.


Gyaran murya na kan kujerar yayi suka dawo da hankula gareshi "Mal Gide"


"Ranka ya dade" wanda yafi manyanta cikinsu ya amsa.


"Habubakari"


"Allah Yaja zamaninka" na biyun ya amsa.


Dan murmushi yayi domin kuwa su biyun yayun matarsa ne Innawuro.


"Mal Gide kaine babba saboda haka ta kanka zan fara. Ba tare da jan zance ba magana ce akan sakacinku da zumunci saboda wani abu can da ya faru shekarun baya"


Mal Gide ya hadiyi yawu yana kallon Habubakari shima kuma yayan nasa yake kallo.


Ardo Barkindo ya dan duku da kansa kadan daga kan kujerar "wannan zumuncin da kuka banzatar ina mai tabbatar muku sai Allah Ya tambayeku akansa. Kune kuka ci bashi kamar yadda naji a bisa dole. Dole tasa kuka biya bashin da kanwarku sai gashi daga karshe ya sakota ya bukaci kudinsa ko. 'Yar uwarku ta sadaukar da farincikinta saboda ku amma shekaru sun tasanmu talatin marainiyar da ta bari baku san cinta ba baku san shanta ba"


Habubakar wanda abin shima ya dame shi amma tsoron Gide ya hana shi furtawa ya sharce kwalla "Ardo zamu gyara, wallahi nima abin ya dameni. Ali bashi da kirki ko kadan. Allah ma yasa tana da rai yarinyar nan"


"Yarinya da ranta amma tana cikin mawuyacin hali. Yanzu da na kiraku dama sanar daku zanyi cewa zan daukota ko dan kwanciyar hankalin Innawuro"


Nan ya sanar dasu komai game da Mairama kamar yadda yaji daga bakin mijin Nene Marka bayan ya soma binciken nemota.


Mal Gide sai hawaye. Bakar zuciya tasa ya umarci 'yan uwansa da babu su babu zuri'ar Malamijo, ciki kuwa harda 'ya daya tilo ga kanwarsa Mairo wadda ya yiwa auren dole da Malamijo.


"Da kaina zanje in daukota da yaran su zauna a gidana Zan gyara wannan abu duka laifina ne"


Ardo Barkindo ya kada kai yana murmushi "haba dai Gide ai bazamu yi haka da kai ba. Yarinya a wurin babarta zata zauna. Duk na gama wahalar neman sannan kace zaka daukota ka kwashe ladan"


Murmushi ya maida masa "duk yadda kace ranka ya dade, kamar yaushe zamu tafi?"


"Jibi in sha Allahu. Ina so ku tattaro kan 'ya'yanku har na gidan aure da suke rugar nan da kewaye maza da mata. So nake muje mu cika musu ido mu wanke gorin dangin uwa da na tabbatar ansha yi mata."


Sun tashi da fara'a kowa yana jin kamar an sauke masa nauyi daga zuciya. Ardo Barkindo ya nisa yana tunanin ya boye musu makantar Mairama saboda yasan duka hankulansu zasu tashi. Idan sun je zasu ganewa idanunsu. Ko matarsa ya kasa fadawa ita da ta uzzura masa akan neman 'yar yayarta da take bi.


Mal Gide kuwa har ya isa gida yana tunanin da yardar Allah zasu kula da ita bakin iyawarsu su daidaita tsohuwar baraka. Tunawa yayi da umarnin Ardo ya tura guda cikin 'ya'yansa da yaje ya fara sanar da yayyensa cewa suna da zuwa Kano jibi daga rugarsu wadda take cikin karamar hukumar Giade a jihar Bauchin Yakubu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: WAIWAYE....



Zainab tayi kuka har ta gode Allah. Hadir dinta ne kwance baya iya motsa kowace gaba a jikinsa sannan baya iya magana. Idanunsa kadai ke aiki idan anyi magana kuma yana ji amma babu damar amsawa. Tun iyaye na rarrashinta har suka kyaleta ta koka ko zata ji sa'ida.


Zuwansu Kano kenan aka kaisu tsohon dakinsa inda yake zaman jinya. A hankali ya bude idanunsa ya saukesu a kanta. Murmushi yayi wanda ya hado da zubar hawayensa. Sunanta yake kira amma babu mai jin sautin saboda baya iya motsa harshensa. A guje ta fita da ta ga ya tashi ta dauko Ibrahim yana wasansa a dakin kakarsa. Dakin ta koma dashi ta kama hannun Hadir ta hada da nasa.


"Idan ni bazaka tabani ba ka tashi ka dauki danka. Don Allah...don Allah Hadir ko Ibrahim ne ka rike da kanka"


Runtse idanunsa kawai yayi. Yaya zaiyi da iyalinsa? Allah ne gatan gidansu sai shi da guntun albashinsa. Shikenan rayuwarsa da tasu ta tsaya saboda lalurar da ta same shi? Ina Major Mustapha? Yayi rai ko shima ya rasu? Ina Mairama da Radhiya? Akwai amanar takardun kwafin gidansa a wurinsa. Ta yaya zai isa ga wannan mutane da yake tausayawa duk da halin da yake ciki.


Kanwar Hadir ce ta jiyo Zainab tana surutai ita kadai tazo ta fitar da Ibrahim sannan ta fadawa mamansu halin da take ciki. Tun zuwansu ko ruwa bata sha ba sai kuka. Umman tasu taje har dakin tace mata ta taso ta ci abinci shima ta barshi ya huta. Kamar ba da ita take ba tana ta magana taki tashi sai cewa take ta koshi. Babansu Hadir aka kira shima yazo yace indai kuka zata rinka yi to ta fita daga dakin.


Hannu ta dora a baki da sauri "na dena, wallahi na dena" tana magana hawayenta da na Hadir yana karuwa.


Baban ya fita yana cewa Umma ta kyaleta dama sun sani dole tayi kuka. 


Bayan fitarsu hannunsa ta kama tana shafa kumatunta "Hadir kana ji na?"


Jikakkun idanunsa ya kifta mata yana son yin murmushi "kin fiye rigima" yace a ransa.


Shagwabar da ta saba yi masa take kokarin yi kuka yana cin karfinta "ka taimakeni ka tashi, kaga Ibrahim ya kara nauyi yanzu. Ni kadai kake so na rinka daukarsa? So kake ya buda min kirji irin naka?"


Lumshe idanu yayi yana sauraronta tana ta yi masa magana. Can ya soma jin fitsari, ya rasa yadda zaiyi tun yana kokarin rikewa har ya saki a kan katifar kamar kodayaushe yanzu ya zamewa kannensa wani karin nauyi.


Lura da danshin Zainab tayi ta mayar masa da hannunsa inda yake ta fita wurin Ummansa tana neman tsumma da ruwa.


"Fitsari yayi ko?" Umman tace tana jin babu dadi.


Murmushi Zainab tayi "eh Umma, yanzu zan gyara wurin"


"Barshi Zainab ki huta kinji. Idan kannensa sun shigo sai su gyara. Yanzu zaki ga daya daga cikinsu. Sun san yanayin nasa shiyasa basa yin nisa ake barin guda a kusa"


Kai ta dukar "danshi zai dame shi. Zan iya gyarawa"


Bata jira cewarta ba ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi sai kansa da ya juya yana kallon sama sabanin dazu da yake kallonta. Wani kululun bakinciki yaji ya rufe shi a lokacin. Ya gama wahala ya dawo da ransa amma ya zama kaya irin haka. Zainab dinsa abar tattalinsa ita ce haduwarsu ta farko bayan watanni zata kare a gyaran fitsari. Kuka zuci ya rinka yi har ta gama mirgina shi ta sauya masa kaya sannan ta cire zanin gadon ta shimfida zanin goyon Ibrahim a gefe inda ta ja shi ya kwanta.


Zama ta kuma yi ta dora kansa a cinyarta "Hadir"


Bude idanu ya sake yi sai ya ga ta duku da kanta ta sumbaci lebensa. Zuciyarsa tayi nauyi matuka. Ga matar da yake so take son shi amma ko yatsanta bazai iya rikewa ba.


"Ka ga alamomi zamu fara koya yadda zan rinka ganewa idan kana bukatar wani abu"


Ido ya kifta don ya nuna mata ya fahimceta. Ta gyara zama tana yawo da yatsunta a kansa "idan kana son abinci ko ruwa sai ka juya kanka barin dama. Idan kuma bandaki kake son zuwa sai ka juya hagu. Ni kuma sai ince abinci ko ruwa idan dama ne. Sai ka kifta ido sau data shine eh, sau biyu kuma a'a"


Ta jima ko lokaci bata tunawa tace sai sun kwatanta. Ummansa da kanta ta dawo tace lallai tazo taci abinci. Ko da ta diba dakin nasa ta sulale ta koma taci. Shi sai su kunu ko koko ake bashi da ruwa. Asibitin da aka kaishi a Kano ne suka ce kada a bashi mai nauyi har sai ya soma sabawa da sabon yanayin jikinsa. Kudin da aka nema na gwaji da aikin da ake tunanin yi masa kuwa ko yana daukar albashi kila sai ya shekara biyar zai tara su. Aiki a lakarsa ta kashin baya ba karamin tsada bane dashi.


Da daddare ko keyarta basu gani ba a ciki. Hadir ya sake matsuwa cikin daren tana rungume dashi tana bacci haka ya saki fitsarin nan ya bata musu jiki saboda bashi da damar tashinta. Tana tashi da asuba gyaran wurin ta soma yi sannan ta goge masa nasa jikin tayi masa alwala.


Satinsu daya babanta ya koma. Zainab ita take yiwa Hadir komai banda zuwa bandaki saboda yayi mata nauyi. Wannan tana ganin yayi alamar take sanar da kaninsa.


Wata guda suka yi a haka babu wani cigaba kullum yana nan a yadda yake sai ma hawan jini da ya kama shi saboda yawan tunani. A wata na uku mahaifanta suka dawo dubiya. A lokacin ne kuma baban Hadir a gabansa da Ummansa da iyayen Zainab ya bijiro da maganar kashe aure.


Kofin kunun hannunta ne ya subuce bata sani ba kuma bata damu ba.


"Kashe auren wa kenan?" Babanta ya tambaye shi.


"Zainab da Hadir"


Zubewa tayi a kasa ta fashe da kuka "Umma kuyi hakuri idan wani abu nayi zan gyara."


"Ko daya Zainab. Wannan shawarar da wahala muka iya yanke ta. Zamanki da Hadir babu alfanu sai tarin

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment