Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin haske ne wal ya shiga cikin idonta ga alamun mutum tana gani sai wani matsanancin ciwon kai kamar an kwada mata guduma. Rike kan tayi da hannuwanta biyu sosai tana ji kamar zai fadi.


"Ayuba....wayyo Allah kaina Ayuba"


Da sauri ya dawo gabanta ya durkusa sai dai ciwon da take ji yayi tsananin da ya sumar da ita. Ayuba ya hanzarta fita yana kiran su Yadikko a lokacin Radhiya da Awwab suke tahowa dakin zai bawa Ummin wayar da ya siyo taki karba suka ga ana tururuwar shiga dakin ana cewa Mairama ta suma. A guje Radhiya ta shiga ta samu ana shafawa Umminta ruwa a fuska amma ko motsi bata yi. Kuka ta saka Awwab yace su fito da ita zai je ya matso da mota kofar gidan. Shima a kidime yake musamman ganin irin kukan da Alheran dinsa take yi.


Ayuba yana ganin haka yace su kyale masa ita su matsa gefe. Radhiya dai babu inda zata je sai ma kan Ummin da ta dora akan cinyarta. Da alwalarsa dama ya dauko littafi mai tsarki ya bude suratul Baqara ya soma karantawa yana yi ya umarci Radhiya ta rinka shafa mata ruwan tofin nan. Atishawa tayi mai karfi a hankali ta soma bude idanuwanta wanda suka sauka akan fuskar 'Yar Soja Alheran 'yarta da Zayyan. Murmushi tayi ta daga hannu ta shafa fuskar Radhiyan wadda bata gane me yake faruwa ba sai da taji tace.


"Ashe ma na fiki kyau"


Tana kuka tana dariya tace "Ummi kina ganina? Me nake yi yanzu?" Ta murguda bakinta gefe yayin da Awwab ya dawo ganin me ya hanasu fitowa.


"Hmmm bakin tsiwar kenan ake murguda min"


Wata wawiyar runguma Radhiya ta kai mata tana murna. Kowa a dakin sai san barka. Ayuba kuwa cewa yake kuyi ta kabbara yau ko waye ya yiwa Adda Mairama asirin nan Allah Ya dandana masa abinda taji.


"Malam da kanka?" Inji daya daga cikin amaren da za'ayi bikinsu nan da 'yan kwanaki.


"To na janye...mu godewa Allah da wannan ni'ima da Yayi mana. Da kaina zanje wurin Malamijo a gona nayi masa albishir"


Dariya suka yi Ummi tana binsu daidai da taimakon murya tana ganesu. Kyakkyawan matsashin da ta gani a jikin kofa yana murmushi fuskarsa mai cike da annuri ta yafito da hannu.


"Haka Awwab dina ya koma"


Hannunta ya kama ya rike gam ya kalleta ya kalli Radhiya da nata bakin itama yaki rufuwa. Wayar Ummin tasu ta dauka cikin hanzari ta kira Emzee ta fada masa wannan daddadan albishir.


"Ki taimaka ki rufe fuskarki da zani sai na dawo ta ganmu tare" yace yana fita daga dakinsu zuwa falo ya fadawa Mama Zainab.


"Sorry yaro ni ta fara gani"


"Bata wayar"


Ummi na karba ya soma rokon ta rufe ido ta bar ganin mutane haka sai ya dawo. Dariya dan nata ya bata. Sun gaisa da Zainab tace zata turo su a yau don bata jin Karami zai iya bacci.


Awwab ma Mami ya fara kira ya fada mata sannan ya kira Major da yake hanyar komawa gida daga gidan Alh Baba.


"Ina ka shiga ina ta kira tun dazu?"


Hakuri ya fara bashi sannan ya fada masa abin alkhairin da ya faru "ina isowa na kiraka nima"


"Na gani ina tare da Alh Baba ne."


Murnar budewar idanun Mairama ta hana shi tambayarsa meye tsakaninsa da Ghazalatu. Zai jira shi ya dawo din sai suyi magana. Sai dai ciwon kan da take ji wanda da alamun haske ne yayi mata yawa ya fara addabarta. Awwab yace gara a kaita asibiti ko akwai abinda zasu bata.


Shi ya kaisu asibitin suka bata magunguna aka koma gida. Hudu har gota Ummi tace yayi hakuri da tafiyar sai da safe. Abinci aka kai masa tsakar gida wurin Malamijo sai ga Radhiya ta tazo tace ciwon kan na Ummi ya sake tashi ko bude ido ta kasa. 


"Ko dai babban asibiti zaku kaita. Dama can fa tana da lalurar idanun kafin wannan makantar" cewar Nene Marka.


Rabon ayi komai da Awwab yazo Sumaila a ranar. Nene, Ummi da Radhiya ya dauka suka nufi Kano domin a samu ta ga babban likitan ido.


**********

Maza ne manya manya majiya karfi masu kirar da kai tsaye zata razana mutum su biyu aka budewa kofar karfen da mukulli ne kadai zai iya budeta saboda tsananin karfinta. Mutum hudu suka tarar a ciki kowa da katifarsa a jikin bango. Uku hira suke a junansu cikin wani yare yayin da cikon na hudun yake zaune ya tankwashe kafafunsa akan katifar yana tunani.


Dogon mutum wankan tarwada wanda kallo daya zai sa ka gane wahala ce ta kara masa shekaru ba don ya kai hakan ba a zahiri. Kana iya ganin furfura kadan a cikakken bakin gashinsa. Dukkan wata cikakkiyar kamala ta mutumin kirki ta tabbata a fuskarsa. Sai dai zuciyarsa wadda kuncin rayuwa ya yiwa dabaibayi tasa baka ganin walwalarsa.


Wanda yafi girma cikin mutanen yana zuwa da izgilanci yaje ya take katifar da kafa daya yana karkada masa yatsa a gaban fuskarsa.


"Tashi nan nake son na rinka kwanciya"


Dayan na bayanshi yana dariya a nan din ma sai sun gwada rashin mutumci irin wanda yayi musu sanadin fadowa wannan gida.


Maza ukun da hira suna ganin abinda ake yi masa suka taso suna nade hannuwan riga "idan kana da matsala a dakin nan ka nemi daya daga cikinmu amma ba'a taba 3810"


"Ku kiyaye Boss dina baya son raini fa"

Dayan da suka shigo tare yace musu yana zaro idanu.


"Alamu sun nuna kun shigo prison da zafin kai, sai dai ko zaku gwada hali kada ku taba shiga harkar OUR ZAYYAN. Muna jurewa komai banda bacin ransa"


Basu daddara ba dayan ya daga hannu zai mari Lt Zayyan Muhammad Tureta mai lambar prison 3810 wadannan maza uku suka far musu fada ya kaure a tsakaninsu. Yana nan zaune inda yake har gandirobobi suka shigo rabasu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: TUNA BAYA



"Daga hannuwanka ka dora a bayan kanka" akace daga bayansa da gurbataccen turanci.


Ruwa, iska hade da hayakin wutar da take ci sakamakon tashin bom din wurin yasa ganinsa yayi rauni amma duk da haka ya fahimci ba mutum daya bane a wurin. A kalla sun kai su takwas ko sama da haka kowannensu yana nuna shi da bindiga. Hankalinsa ne yayi mummunan tashi da ya tuna cewa muddin aka harbe shi dole zai daga kafarsa daga kan wannan land mine din. Yana dagawa kuwa banda wadannan mutanen harda Major da Hadir a cikin wadanda zasu iya rasa rayukansu. Dole ne ya kara musu lokacin yin nisa da wurin kafin mine din ya tashi. 


"Kuyi hakuri ko me kuke bukata daga gareni zanyi muku amma kada ku harbe ni. Akwai landmine a kasan kafata"


Dariya suka kwashe da ita tamkar basu fahimci nasa turancin ba. Bai hakura ba ya cigaba da cewa su taimaki kansu suyi nesa dashi kada su mutu tare don bai san karfin abinda ya taka ba.


"Get down" wani gabjeje yace masa fuskarsa babu digon imani a cikinta. 


Zayyan ya sake cewa akwai bomb a kasan kafarsa. Mutumin a fusace ya matso gabansa ya daga kasan bindigarsa wurin fadin ya maka masa a gefen fuska. Wani mahaukacin zafi, radadi da zugi yaji a take turame biyu cikin hakoransa suka fita ya furzar dasu tare da jini. Duk da haka kafarsa yake kokarin dannewa a kasan kada ya tayar da bomb din 'yan uwansa basuyi nisa ba. Idanunsa suna kan hanyar da Hadir ya bi.


Mutumin ya bi wurin da kallo ya yiwa wani nuni da ka. Sai gashi a gaban idon Zayyan mutumin ya cizge irin abin kasan mulmullalan bomb dinnan ya dage ya jefa shi hanyar da suka bi din. Wannan shine bomb din da Major da Hadir suka ji wanda karfinsa yayi sanadiyar fadawarsu kwazazzabon da firgici yasa Hadir bai kula dashi ba.


Mutum biyu suka zo suka damki Zayyan wanda ya saki ihu sosai sakamakon tashin bomb din yana mai cike da tsoron ko ya shafe su. Zuciya ce ta debe shi ya tuna irin ta'asar da suka yiwa gabadaya rundunar da suka taho wurin da niyyar taimako. Mutane biyun ya sakalawa hannuwansa a wuyansu ya daga kafar da niyar dukansu su mutu tare akan sai sun tafi ya mutu shi kadai. Ko babu komai ya sadaukar da rayuwarsa ya rage mugun iri. Runtse ido yayi yana jiran yaji ya tashi sai dai maimakon kararsa sai sautin dariyar muguntarsu yaji. Wani cikinsu ne ya taho daga shi sai dogon wando da singeletin da ba lallai a gane ainihin kalarta saboda mugun datti yazo ya durkusa a gabansa ya ciro abin da suka binne a wurare daban daban masu yawa domin danawa mutane tarko. Duk wanda yayi tunanin landmine ne yaki dauke kafarsa ya zama nama a wurinsu inda zasu fito daga mabuyarsu su kama shi su azabtar domin neman bayanai.


Zayyan yana ganin haka yayi kukan kura ya kwace jikinsa daga wadancan biyun ya fada kan wancan. Abinda yaje dauka yayi sa'ar samu wato bindigar da take aljihun wandonsa ta baya. Baiyi wata wata ba ya saita kansa ya sakar masa harsashi. Wadancan suna daga inda suke suna kokarin harbe shi da bindiga yayin da ogan nasu yayi wani irin ihu saboda kaninsa ne Zayyan ya kashe ya sake saita mutane biyun da suka fi kusa dashi suma ya harbesu yana daga durkushe. A take wurin ya hade sai sautin harbi kake ji amma karfin ruwa ya bawa Zayyan damar kubcewa. Ya sadakar dama yau mutuwarsa tazo amma bai hakura da harbin ba sai da ya sake kara mutum biyu sannan aka same shi a hannun da yake harbin dashi. Dole ya saki bindigar kafin ya farga wannan ogan nasu ya kafta masa bindiga a tsakar kansa ya fadi a wurin sumamme.


Wani irin abu yake ji kamar ruwa yana zuba a fuskarsa amma kuma a shake yake. Yayi ta yunkurin bude idanu amma ya kasa sai wani irin abu kamar an like idanun suna ta radadi. Duk wani tunaninsa ya tsaya cak kwakwalwar ta cushe. Sai bayan wani lokaci yana cikin wannan yanayi na shakewa da ruwa ya soma turjiya ya gane kafafunsa daure suke a jikin wani abu sannan hannuwansa ma an daure su ta baya. Hannun da aka harba dama tamkar ba a jikinsa yake ba saboda kumburi da ciwo. A kokarinsa na mikewa tsaye ne ya gane cewa akan kujera yake a zaune. An daure kafafunsa da jikin kujerar hagu da dama. Hannuwansa kuma suna daure ne ta baya harde da juna. A takaice ma tsumma ne aka dora akan fuskarsa ana kwarara masa ruwa wani ya rike kan ta bayansa.


Sai da suka tabbatar ya azabtu iyakar azabtuwa aka cire tsumman. Tari ya rinka yi a wahale ruwa na fita ta baki ta hanci. Idanunsa sun juye ya kasa tantance a ina yake ga rashin wadatar haske a dakin.


Hargagin mutane yaji aka bude kofar hasken rana kwal ta mamaye dakin.  Wasu mutane ne suka shigo kai tsaye wurinsa suka nufa. Bayan sunyi magana da yare ne suka koma turanci aka tambaye shi mutum nawa ne a sansaninsu da sauran. Sojoji nawa ne Nigeria ta turo domin kwantar da tarzoma kuma a ina da ina suka kafa sansani. Idan ma zai iya magana bazai fada musu ba saboda duka jikinsa hatta bakinsa da hakora suka cire jiya da suka dauko shi ciwo suke yi. Dukansa suka fara yi saboda yaki yin magana sai yaji muryar wani shima a wahale yake yace suyi hakuri ya sami lafiya sai ya basu amsar da suke nema.


Marinsa wani yayi suka ce yayi musu shiru. Sai da suka sake yiwa Zayyan ligi-ligi sannan suka yasar dashi a kasa suka tafi. Mutanen wasu tsageru ne cikin 'yan tada kayar baya da gwambatin kasar ke nema ruwa a jallo. Su kuma suna son dakile taimakon da kasarsu take samu na jajirtattun sojoji musamman daga kasarmu mai albarka Nigeria. Shiyasa suke yi musu dabaru suna kashesu suna kama na kamawa domin neman bayanai. Har yanzu dai babu nasara domin sojojin sun dauki amanar kasarsu jini da tsoka. Idan suka kasa samun abinda suke so sai su kashe mutum.


Bayan fitarsu dayan mutumin da yake dakin ya janyo shi da kyar zuwa wani dan lungu. Tsohuwar katifa ce a wurin da 'yan tarkacen asibiti. Kwantar da Zayyan yayi akan katifar ya farke hannun rigarsa da ya kumbura. Ga dukkan alamu bullet din da ya same shi yana ciki ga uban kumburi fitar dashi zaiyi wahala. Shi kanshi mutumin wahala ta zuge shi duk ya rame.


Wata siririyar wuka ya dauko ya kunna lighter da take ajiye a gefe ya rinka saka tsinin wukar a cikin wutar na dan lokaci ya dauki zafi sannan ya mika masa wani tsohon yagwalgwalallen filo ko riga babu.


"Put it in your mouth"


"Wwwwhat?" Ya fada idanunsa akan filon da babu kyaun gani. Bai rufe bakinsa ba mutumin nan ya tura masa filon lokaci guda kuma ya danna wukar cikin hannunsa saitin inda yake iya ganin alamun bullet din ya shiga. A maimakon kara Zayyan cizo ya kaiwa filon har hakoransa suka kusa hadewa ta ciki don azaba. Juyi biyu mutumin yayi da wukar sai ga bullet ya fado kasa.


Zayyan yayi gumi ba kadan ba idanunsa sunyi jazur sai jijiyoyin kansa da suka mike. Kwanciya yayi mutumin yana masa sannu. Babu bakin amsa sai kai yake gyadawa. Daga wannan lokacin bai kara sanin me ya faru ba sai farkawa yayi yana jin kamar ana dukan wani ga dare. A take ya wartsake ganin mutumin da ya taimaka masa ne ake yiwa dukan kawo wuka. Mantawa yayi da ciwon jikinsa ya tashi a fusace yayi kansu. Ransa ya kara baci ne da ya fahimci dalilin taimakonsa da mutumin yayi ne ake masa haka. Dukan ya koma su biyo ake yiwa amma Zayyan bai hakura ya janye jikinsa ba. Sai da suka gaji don kansu suka fita aka barsu a kasa kowanne jiki yayi laushi.


"Allah Ya isanmu tunda kunfi karfinmu....ashhh bakina" hannu ya dora daga gefen kumatunsa bangaren da hakoran suka zuba. Wahalalliyar dariya wancan mutumin yayi daga inda yake. Zayyan ya dinke fuska don ya jigata sosai yace "baka daku bane kake dariya, ni yanzu suka sake dawowa suman karya zanyi"


Dagowa mutumin yayi da kyar Zayyan sai ya koma turanci "are you okay?"


Dariya mutumin ya sake yi sai abin ya dan bashi tsoro ya ja jikinshi kadan ba dai mai matsalar kwakwalwa bane ko.


"Duk wannan dukan da muka sha ka sani dariyar dole" kallon mamaki Zayyan yayi masa yana jingina bayansa da bango ya dora da cewa "ina kallonka nayi tunanin kaima bahaushe ne"


"Kaima dan Nigeria ne?"


"Soja kamarka" yace da muryarsa da take a kausashe kamar wanda ya tashi daga bacci ko aka shake masa wuya.


Zama Zayyan ya gyara yana kallon mutumin sosai. Wannan zai girmewa Major Mustapha sai dai rashin khaki a jikinsa yasa a haka bazai iya gane mukaminsa ba.


"Lt Zayyan Muhammad Tureta, Giginya Army Barrack Sokoto"


"Colonel Nasiruddeen Aliyu, Bukavu Army Barrack Kano"


Soja ya ga ubangidansa, da ciwon hannun nasa haka Zayyan ya yunkura ya mike yana dafa bango ya dan kame jikinsa yayi masa salute.


Kai Col. Nasiruddeen ya kada yana dariya "baka daku bane shiyasa kake iya tashi, ni yanzu suka dawo cewa zanyi mace ne ni da kayan maza"


Ga wahala ga ciwo Zayyan sai da ya bushe da dariya. Sun dan zauna shiru kafin Col. Nasiruddeen ya soma bashi labarin dalilin zuwansa wurin.


Col. Nasiruddeen Aliyu mutumin karamar hukumar Wase ne ta jihar Plateau. Likita ne na sojoji wanda yake kwararren consultant a asibitin sojoji na Bukavu barrack a Kano inda yake base dinsa. Rabon wannan wahalar da kansa ya nemi a sanya sunansa cikin masu tahowa Liberia saboda burinsa na taimakawa sojojinsu. Sai aka shi turo a matsayin Cheif Medical Officer tare da wasu mutum uku su ma duka sojojin ne kuma likitoci. A lissafinsa yayi a kalla wata biyar tare da mutanen nan. Watarana sun sami rahoton rigima tsakanin sojojin kasar da abokan rikicin nasu inda mutane da yawa suka jikkata ana bukatar likitoci domin taimakon gaggawa. Shi da sauran da suke sansani guda inda yake a matsayin wurin kula da masu rauni suka dunguma da kayan kula da marasa lafiya da magunguna. Rabin tafiyar suka yi kamar yadda aka shammaci su Zayyan su ma haka aka yi musu. Bayan musayar harsashi an kashe mutum biyu cikinsu sauran kuma aka kadasu aka tafi dasu. Akan idanunsa saboda sun san shine babba a cikinsu aka rinka kashe na kasa dashi don sunki bada bayanan da ake bukata. Akwai takardu a jikinsa na bayanin sojoji masu tahowa, ranar isowarsu da ma adadin makamai, abinci da magunguna da zasu taho dashi. Tsoron kada a cutar dasu ya sanya ya fakaice su ya dunkule takardar ya cusa a bakinsa ya hadiya farat daya. Stapler din da take jiki wadda aka mannesu tare ita ce a lokacin hadiyar yana ji tana kartar masa wuya har ta wuce. Bai fahimci mugun rauni tayi masa ba sai da aka zo yi masa tambaya yana bude baki sai jini ya rinka zubowa ga uban radadi daga cikin wuyan nasa. Ya sha wahala sosai karshe muryarsa ta koma haka bayan wani lokaci. Babu ko mutum daya saura cikin abokan tafiyarsa duka an azabtar dasu an kashe. Shi kuma sun mayar dashi likitansu. Abubuwan da ya gani da idanunsa mutanen suna yiwa bayin Allah ba kadan bane, jiran amfaninsa ya kare kawai yake yi shima su kashe shi.


Zayyan ya tausaya masa shima ya fada masa yadda ya fado hannunsu. Ranar hirar da suka yi kenan kafin wahala ta sa suyi baccin dole. 


Wurin da suke ba cikin daji bane hasali ma a cikin gari ne mutanen suka samu wani tsohon gini da rigima ta kori masu shi suke dabdalarsu a ciki. Tsaron da suke masa yasa har yanzu ba'a gano suna zuwa wurin ba. Sanyin asuba ne ya farkar da Zayyan ya tashi ya ga Col Nasiruddeen shima ya farka. Gefe yaja jikinsa ya bubbugi kasa ya dawo.


"Rabona da sallah tun la'asar ta ranar da muka fito"


"A haka zaka yi sallar babu alwala ko tsarki?"


"Akwai ruwa ne a kusa?" Zayyan ya tambayeshi yana leka lungunan gidan.


"A'a sai dan wanda suke kawo min tare da abinci. Idan yana da yawa dashi nake yin alwalar nayi sallolin da suka samu"


Murmushi Zayyan yayi masa "shiyasa Allah Ya hore mana taimama domin saukakawa a inda ruwa yayi karanci."


Col. Nasiruddeen bai nuna girman kai ba ya bari Zayyan ya koya masa. A zaune duka suka yi sallah jiki ya kara tsami. Zayyan ya dade yana yi saboda yasan wanda suke kansa da yawa. Addu'a yake ta yi Allah Ya tseratar dasu, Yasa su Hadir sun tsira kuma Ya maida shi ga iyalinsa.


Sai da rana tayi sosai aka miko musu plate da wani abu da Zayyan bai gane shinkafa ce, gero ko wake ba. Gashi nan dai a cure wuri guda. Col. Nasiruddeen yunwa ta galabaitar dashi ya rinka turawa kawai. Shima Zayyan sai ya ga bashi da zabin da ya wuce ya taya shi ci. Ba dadi ba dadadawa amma haka ake basu wannan abincin suna ci.


Sabo ne ya rinka shiga tsakanin wadannan bayin Allah da suke rayuwa a inda iyalansu da kowa nasu yake tunanin sun mutu. Kullum dare bayan 'yan tawayen nan sawunsu ya dauke daga dakin hirarsu sai ta karkata ga iyalansu. Dukkansu har jiran dare suke domin su saukewa juna nauyin zukatansu. Matsananciyar kewar iyalansu tana damunsu tana ci musu zukata. Yau ma bayan wata daya da kama Zayyan suna hira Col. Nasiruddeen yake cewa.


"Idan Allah Ya fitar dani daga wurin nan ina komawa abu na farko da zan fara yi shine yin ritaya. Zayyan na bar aikin soja har abada wallahi"


"Ka dena fadin haka Sir. Ni ka ga a duniya ban taba gani ko sha'awar wani aikin ba bayan shi."


"Da kuruciyarka ni kuwa girma ya soma zuwar min. Sa'annina da kannena suna kwance comfortably da iyalansa a wannan lokacin ina zaune a inda Allah kadai ya sani cikin wari da kazantar najasata. Babu wanka babu abinci mai kyau sannan duk abinda zamuyi sai dai mu yi shi a inda muke kuma mu kwana a ciki"


"Saboda abinda Allah Ya zaba maka kenan. Ya halicci mutane bayan kariyar da yake bamu da IkonSa kuma ya sanya mu garkuwa a garesu masu taimaka musu. I believe we soldiers are not made...we are born to protect (na yarda mu sojoji ba yinmu ake yi ba....haihuwar mu ake yi domin bada kariya)"


"We are special, nima na yarda...." Col. Nasiruddeen ya amsa da murmushi a fuskarsa "amma bazan cigaba da sacrificing rayuwata ga mutanen da basu san nayi musu ba. Ni da wannan aikin sai dai idan mutuwa nayi a wurin nan"


Dariya ya bawa Zayyan yadda ya hade rai da gaske ya gama da aikin soja "wannan magana fa kamar a kunnen Arifah. Nasan zata so ka cigaba da aiki muna biye daku"


Kafada ya noke kamar yaro "ko me zata yi sai dai tayi kuwa. Idan na mutu bakin aiki wa take dashi da zai kula min da ita? Burina kawai na koma gida na cigaba da bata kulawa. Shekara da shekaru ina neman haihuwa amma don ganganci ban tashi barin gida ba sai da na sami 'yar. Idan na mutu fa duka duka shekara hudu muka yi tare. Kila ma ta manta dani gabadaya"


Sai kuma ya bawa Zayyan tausayi. Col ya fada masa yadda ya kwashe shekaru shabiyar da aure tun da kuruciyarsa babu haihuwa sai akan Arifah. Yana son tilon 'yarsa kamar rai. Ranar da zai taho Liberia da kansa ya kaita makaranta nursery da take ta rinka kuka sai ta bishi. Zuciyarsa ta karye, ya baro mamanta tana nata kukan a gida itama tana yi kuma daga nan Lagos zasu wuce. Da kyar ya rarrasheta aka karbeta daga cikinsa tana ihu ya bar harabar makarantar.


Ranar da yaji labarin iyalin Zayyan ya tausaya masa matuka. Cewa yayi kada Zayyan ya kuma kiransa da wani abu da zai alakanta shi da soja sunana Baban Arifah shi kuma yana kiransa Baban Alheran.


Kwana uku a tsakani Zayyan ya soma tunanin hanyar guduwa. Sai da Col. Nasiruddeen yayi ta bashi shawarar kada ya fita ya fishi dadewa kuma shima ya gwada babu sa'a amma yaki hakura. Ta yaya zai hakura bayan kullum sai anzo an bashi wahala domin ya bada bayani shi kuma yaki. Sai ma zancen kashesu da aka fara wai zasu bar wurin an kusa gano su. Shiyasa yaga ya dace dole su nemi hanyar tsira.


Lallabawa yayi yana neman hanyar fita  ya hango tawagar 'yan tawayen sun shigo wurin a guje. Masu gadin nasu da wasu kowa hankalinsa ya tashi. Cikin ikon Allah ya hango mutum biyu da kayan sojojin kasar amma umarni suke badawa a tabbatar babu wanda ya tsira a cikinsu. Su duka masu laifi.


"Shot on sight" (a harbe duk wanda aka gani) yaji ana bada umarni daga waje.


A guje ya koma ciki ya gano wani bari na katangar da ya dade yana tunanin haurawa sai kuma ya fasa ya shige inda suke ya tada Col. Nasiruddeen da yake bacci.


"Baban Arifah we need to run"


"Baban Alheran nace..."


Harbi suke ji da ihun maza da alamun guje guje. A gaggauce shima ya mike suka nufi wannan katanga. Zayyan ya haura saman ya miko hannu domin taimakawa Col. Nasiruddeen amma ya kasa saboda bashi da tsaho sosai. Ga tsira yana gani amma ya gaza. Idanunsa hawaye fal suna jin harbin yana kusanto inda suke yayi saluting Zayyan.


"It was nice meeting you Lieutenant. Take care"


Zukatansu sun karya su duka. Zayyan sai tuno Major Mustapha da dan uwansa Hadir yake yi. Soja shi kadai yasan ciwon soja. Durowa yayi kasa kafarsa tayi kara duk da haka ya kama Col. Nasiruddeen da mamaki mai tsanani ya kama shi na karamcin wannan yaro. A kafadarsa ya dora shi ya mike tsaye.


"Baban Arifah haura"


Col. Nasiruddeen ya mika hannu ya haye katangar bai sauka daya barin ba ya gano sojojin kasar da 'yan tawayen sun taho wurin gadan gadan. Su ma 'yan tawayen katangar suka zo haurawa. A gigice yace "yi sauri Zayyan"


Zayyan ya mika hannu ya hau katangar bai haura da kafafunsa ba bullet ya shiga kafadarsa. Col Nasiruddeen ya ga sanda aka yi harbin ya sa hannu zai janyo shi wani bullet din ya sami Zayyan a baya. Jikinsa ya saki duk yadda Col. Nasiruddeen yaso ko da gawarsa ce ya fitar daga wannan tsinannan gida bukata bata biya ba domin fadawa yayi

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment