Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dace su baiwa yaran wuri don ba ta biye musu ana tunzura Radhiya ba. So take Awwab ya so kanwar tasa da wuri, gara su fara sabawa da juna. Taimakawa Hadir tayi ya kwanta ta dauko takardun asibitin ta koma kusa dashi tana yi masa bayanin kowanne don neman shawararsa. Da ido da yanayin chanjin fuska take fahimtar abubuwa da dama da yake nufi idan tayi masa tambaya.


Sakale tayi tana kallon Awwab yana murmushi "ban san haka kike so ba, to koma ki sake fitowa. I promise zan tayaki basarwa"


Ita ma sai da abin ya bata dariya ta koma ta zauna tana jiran fitowar Emzee ko ma ina yaje ya buya. Dama idan ba ganganci ba me zaisa ta karbi shawararsa. Wautar kanta take gani na biye masa.

 Yana jiyo me suke yi a inda ya tsaya ya girgiza kai. Bawa Radhiya shawara wataran kamar zuba gari ne a rariya. Kana fada yana zuba. Ibrahim da Zayyana suka tashi suka bi bayan shi zuwa waje. Ibrahim na cewa ta dena binsa ta murguda masa baki tace ita wurin Emzee zata je ba shi take bi ba.


Ya rage su hudu a falon Awwab ya watsawa su Zahra idanunsa "bazaku bani abincin bane?"


Da sauri Radhiya ta tashi don yau dai taji kunya fiye da yadda ta saba "bari na kawo maka"


"No, dawo ki zauna"


Inkiya yake musu su basu wuri sumsum suka tashi suna dariyar dramar Radhiya.


Kai ta sunkuyar karon farko da zata iya tunawa a rayuwarta ta rasa bakin magana saboda kunyar da ta bawa kanta. Dan gayu kamar wannan kyakkyawa daga ita sai shi a falo ai dole harshe yayi nauyi tace a zuciyarta. 


Nazarinta Awwab yake yi ya dago kansa daga jinginar da yayi da kujera yana mamakin wannan yarinyar ta gabansa ita ce Alheran dinnan da yake dauka suyi ta yawo a barrack shekarun baya. 


"Alheran" ya ambaci sunanta a hankali taji wani yarr a jikinta saboda yadda muryar ta ratsata.


"Uhmm"


"Kin dena magana ne kuma?" Ya tsokaneta da ya ga kamar ma a takure take.


Girgiza kai tayi sannan tayi kwafa da guntun tsaki "Wallahi kunya naji, ashe ba haka ake basarwa ba. Bari Emzee ya dawo zai gamu dani"


"Balotelli zaki yi masa?"


Dago kai tayi da sauri ya dage mata gira yana jin komai nata na burge shi. Ba haka yayi zaton ganinta ba. Yana ta kissima wata budurwa mai ji da kai da gayu sai ya hadu da Radhiya wadda kwatancenta sai wanda ya santa. Amma duk da haka yaji tayi masa a yadda ya sameta cikin kankanin lokaci.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Gulmata suka rinya yi maka?" Tayi maganar a cikin shagwabar da batayi niyya ba. Hakan yasa Awwab sake yin murmushi. Daga shigowarsa gidan zuwa yanzu idan ma yana da damuwa to tabi ruwa tabi iska Radhiya ta dauke masa ita.


"Kinki zuwa na ganki ba sai na nemi labarinki ba"


"Ba ga su Mama ka gani ba maimakon kayi hira dasu shine zasu kawo maka zancena?" Ta sake marairaice masa.


"Kinsan me yasa na kasa zama na huta duk da tarin gajiyar da nayi?"


"A'a" tace tana girgiza kai.


"Because I missed you Alheran" yace suna hada idanu tayi saurin lumshe nata.


Tayi karatu bare ace bata jin turanci bata fahimce shi ba. I miss you ai sai masoya a iya saninta. Shiyasa taji wata irin kunya ta saukar mata.


Ko a jikinsa don iyakar gaskiyarsa kenan. Murna da sanin cewa ga inda take ya wadatar dashi ya hana shi sukunin duk wani hutu idan ba haduwa suka yi ba "sai da nazo na ga ashe ni kadai na damu dake, kina kallona kina basarwa"


Maganarsa ta bata dariya kamar yadda ya fadeta yana yamutsa fuska shi ba'a kyauta masa ba "wasa ne wannan amma ni fa ban iya tuna ka ba ne sai labarin da Ummi ta bani"


Hannu yasa ya karbi lemon da Fauziyya ta tsiyaya masa. Sai da ya kurba sau biyu ya sake kallonta "ko kadan?"


"Me?"


"Rashin tunawa dani din"


"Ka ga fa nayi kankanta lokacin"


Gefen girarsa ya shafa "kinga wannan tabon?"


Daga inda take tana ganin duhun layin "bille ne ya karkace? Ko ka hadu da wanzamin da bai san aikinsa ba. Me ya hada tsakiyar goshi da gefen gira? Ko irin na gefen nan mai uku-uku aka so yi maka?" Ta rinka jero masa tambayoyi.


"Na hadu da wanzamiya dai"


Fauziya za ta fara dariya don gidansu kowa yasan tabon aikin Radhiya ne ya kalleta sai ta sake tashi. Wai meye ne Hamma yake korarsu...kodai, kodai...dan murmushi ta saki amma kuwa da tayi farinciki idan haka ne. Abincin da Zahra ta gama hadawa ta karbo don so take ta sake ganin gulma.


"Ana wanzamai mata dama?"


"Alheran sunanta ma"


"Da gaske?"


"Yakushina fa kika yi" yace yana kallon yadda ta ware idano ta saman kofin hannunsa.


Tasowa tayi ta dawo kujerar gefensa yadda zata gani sosai tana ta karkata kai hagu da dama "Allah Hamma, ko dai don nace ban tunaka bane zaka dora min" ta rinka dage girarta duka biyu a tare tana cewa "eyye, eyye?"


"Cute" ya furta a sanyaye ya rasa me yake damunsa tun da ta fito daga dakin. Wasu abubuwa take yi da suke tado masa da memories din kuruciyarsu. Ta bude ido ta lumshe, ta turo baki ta sha kunu ko murmushi.


"Da kina yarinya kin fiye rigima da fada...uhmm harda kuka. Gashi naga alama babu wanda kika dena cikinsu."


"Tsokanata akayi ne, amma yanzu na dena fada"


Fauziyya da ta duka za ta zuba masa abincin a plate tace "A yaushe kika dena fadan?"


"Babu ruwanki da hirarmu bar abincin ma zata zuba min idan na tashi ci. Tafi kawai ki barmu kinsan ba wurinku nazo ba"


Dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha yace ba wurinsu yazo ba. Kai na rawa tana jujjuya idanu tace mata " yehhh sai a tafi kinji me Hamma Awwab dina yace. Dama na fada muku idan ya zo zai dena kula kowa sai ni, nima kuma in dena kula ku ehe"


"Shikenan ka bata damar cigaba da raina mu ni da Zahra"


Kallon tuhuma yayi mata "wai haka?"


"Fada kawai take yi don ta hadamu, kowa ya shaideni a gidan nan wurin girmama manya ba daga nan ba" yanayin maganar kadai zai gane karya taje yi. Bata da innocent face, kana ganinta kasan akwai jini a jika.


"Allah Ya shiryeki Radhiya" Fauziyya tace tana tafiya za ta je kaiwa Zahra tsirku.


Abincin ya nuna mata ta soma zuba masa "ba kya son na kula kowa?"


Ta dago kai "eh wallahi, ko na yau kawai kada kayi musu magana su gani duk kafi sona. Ni kadai ce kanwarka banda su"


"Gobe zan koma Kt ba kya so nayi hira dasu Ibrahim?"


Dena zuba abincin tayi tana jin babu dadi a ranta "gobe kuma Hamma ko sabawa bamuyi ba zaka koma?"


Wannan karon shi ya fara janye idanunsa daga gareta. Ya rasa gane me yasa suna kallon juna sai yaji abu ya taba zuciyarsa. Ya dai alakanta hakan da dawo masa da tunanin baya da take yi ne.


"Akwai wani sabon da ya rage msna bayan wanda muka yi in less than an hour?"


Wuya ta shiga sosawa irin na marasa gaskiya tana sunkuyar da kai da murmushi. Dimple dinnan ya sake kallo ya miko hannu kamar zai saka yatsansa yadda ya saba yi mata a baya ya tallabo habarta da ragowar yatsunsa sai kuma yayi saurin janyewa. Alheran is not a child anymore ya yiwa kansa fada.


"Na yarda kayi hirar minti goma goma da kowa su Baba kuma awa daya, sauran kuma duka nawa ne."


"Bazaki gaji dani ba?" Bai san me ya kaishi yin tambayar ba. Yayi saurin datse bakinsa bayan ta fito.


Da ido daya ta karkace kai tana kallonsa "hmmm na gane wato ka gaji dani ko? Nasan komai idan ana yi min irin haka saurin fahimta nake yi. Kora da hali kake min irin na Ummi idan ta gani da hirata"


Hannu ya daga yana bata hakuri "ba haka nake nufi ba, yadda kike so haka za'ayi. A lokacin kowa ma sai a cire minti daya da rabi in kara miki"


Murmushi ta saki tayi masa gwalo "na maka wayau"


Girgiza kai kawai yayi yana jin nishadi da farinciki suna ratsa shi.


**********

Malamijo ke zaune a tsakar dakinsa akan filo yana sharba gumi. Zafi ya ishe shi daga shi sai dogon wando Hajjo da tayi karkon zama kamar Yadikko saboda bakinta dake kwatarta a wurinsa tana masa firfita.


"Ya kamata kaje asibiti fa, ka kwana ka tashi da abu daya ba'a zauna a gida ba" 


Daure fuska yayi ga azaba ta ishe shi da kyar yake magana "zaki biya min kudin asibitin ne?"


"Lallai ma Malamijo, to don Allah zauna kada kaje ka gani idan zan damu. Ka bar kudin kar ka tabasu idan ciwo ya karasa ka a raba mana gado. Nasan a lalace idan ban saka dogon buri ba zan tashi da a kalla shanu uku manya."


Ido ya ware yana jin kamar ya shakota amma jikinsa babu kwari. Ta turo dankwali gaba tana lissafi da yatsunta "kaga mafi girma a ciki in sa a danne a yanka min. In soya, in gasa, inyi miya. Kai har tafasasshe sai naci. Sauran biyun kuma in sayar nayi sababbin dinkuna kafin Allah Ya kawo bazawari"


"Mmmugguwa, saaai kin riga..rigani mutuwa"


"A hakan, karmai-kamai da kai kamar kazar mayu?"


"Akwai mayyyyyyar da ta wuccceki ne?" Yace yana cije lebe.


Yadikko ta dago labule ta shigo fuskarta da damuwa "Malamijo anya zaku cigaba da zaman nan kuwa haka? Use da Asabe fa suma irin lalurarka ta same su. Asabe sai kuka take da kyar na bata hakuri na fito"


Hajjo na jin haka ta tashi da sauri "Yadikko kice ciwon na ango ne da amarensa. Wannan abu shi ake kira guzurin masoya. To ni nayi nan. Kayan lefen can da aka gama gani zan je in killace kada ayi sibare inzo banci nanin ba nanin ta cinyeni ace don ba ni na haifesu ba ina musu bakinciki na bari an kwashe musu kaya"


Fita tayi tana rangaji da dariyar mugunta. Malamijo da amarensa duka sun kasa fitsari. Duka duka Asabe watanta uku a gidan ya cike gurbi da Use. Auren sati uku an wayi gari sun kasa fitsari. Shi tun jiya ya fara gashi yace a matse yake amma ko digo ya kasa yi.


Bata gama gyara kayan ba Yadikko ta shigo babu walwala a fuskarta saboda yadda ta kula yana jin jiki.


"Hajjo me ya kamata ayi ne, rashin fitsarin nan fa ba karamin abu bane. Malamijo sai zufa yaje yi yana numfarfashi"


"Sai kiyi ta damun kanki Yadikko. Akan me? Nan yayi auren nan fa ya soma mana wulakancin da ya saba. Saboda alhaki kwikuyo ne da yace mu dena girki wai ya bamu hutu kannenmu suyi ai ga sakamako nan ya samo. Banda kwadayi irin na namiji yaran da basu fi yayi jikoki dasu ba wai sune kannenmu"


"To dai a bar tone-tone mu kira su Habu yazo ko da motar da yake haya ne a kaisu asibiti. Zan tura a fadawa Salame ke kuma  ki kira Innawuro ta fadawa Mairama itama su zo babansu ba lafiya sannan ga karbar lefe ma da basu san anyi ba"


Ido Hajjo ta zaro "Ni shegiya inji dan daudu, da wane bakin zan fada musu mahaifinsu ya kamu da tagomashin soyayya? Kyaleni naji da aike gidan waccan mara mutumcin Salame. Amma Mairama ai akwai kunya taakaninmu, yarinyar mutumcinta yasa yanzu kunyarta ma nake ji"


"Meye kuma tagomashin soyayya ni Yadikko?"


"Sunan da ya dace da ciwon nasu kenan ai"


Yadikko ma dariya ce ta kama ta. Sai yamma aka samu biyu cikin mazan gidan suka dawo. Dama daga Mairama sai taron maza. Matan da suka taso kuma halin Malamijo ke korar musu manema. To yanzu anyi sa'a mutum hudu cikinsu abin yazo tare. An aikawa Salame dan aiken ko kallo bai isheta ba kamar ba kaninta ba. Mairama kuma Bature ne ya kira lambar Baffa Habubakari ya fada masa. A daren ya nemi layin Major ya sanar dashi cewa a fada mata.


**********

Hankalin Mairama ya tashi duk da bata san me ya sami Malamijo ba amma tunda aka fada mata tana ganin ba karamin abu bane. Major ya tsara musu tafiya washegari ganin duk ta tashi hankalinta. Dama motocin da yayi order biyu an riga an kawo su. Daya domin bukatarsa dayar kuma saboda Mami da kuma kai Zayyana makaranta da suke jiran a koma hutu ta fara SS1 sabon zangon karatu mai kamawa.


Jibi zai tafi Sakkwato kaninsa zaiyi masa rakiya su kuma yace washegari su tafi sai su tsaya a Kano su dauki yaran.


"Amma ina ganin motar zata yi muku kadan. Bus din da aka kai Awwab Kano kuma yace gobe zasu dawo. Dreban ya kamata ya huta haka shiyasa ba zan ce ya kwashe su ba"


"Awwab ya tuka ba sai ya bimu a baya ba" Mami tace su kuma dan gidan Hussainarta Abdallah ne zai tuka su.


"Bana son tukin Awwab a babbar hanya gudun nan nasa kamar yana iska".


Mairama ta fara musu godiya sannan tace "da kun barshi Daddy a hakan ma nagode sosai wallahi. Ba sai an sake wata wahalar daukarsu ba. Shima Awwab din yana bukatar hutu"


Mami ce mai kwantar mata da hankali tace "haba Ummin Awwab ki bar wannan godiyar mu dake duka daya ne. Babu matsala in sha Allah" 

 

Babban abinda zai kai Major wanda zasu hadu da Baffa Gide a Sakkwaton shine binciken dangin Zayyan na Nijar. Idan da gaske rashin idonsa a duniya yasa suka zare hannunsu daga kan iyalinsa ko kuma su ma karya Maikudi ya shara musu duk zai jiyo. Shi kanshi sojan da yake tura kudin zai baro bakin aikinsa ya taho don ransa ya baci fiye da ba Major akan rainin hankalin da Maikudi yayi masa. Idonsa idon Maikudi kawai yake jira.


**********

Tun dare anyiwa Zainab waya game da zuwa Sumaila duba Malamijo. Ita bazata sami zuwa ba saboda Hadir gashi asibiti zasu koma. Tunda ba kwana zasuyi ba Mairama da su Radhiya ne kadai zasu kwana sai ta yiwa Ibrahim izinin fita duk da shine karfin taimaka mata akan babansa sai Emzee da yake taya shi sosai.


"Yaya zakiyi da Baba"  ya fara cewa da tace yaje.


"Gara na fara sabawa, daga kai har Karami WEAC dinku ake jira a nema muku admission. In kana makaranta zanyi ta jiranka ne?"


Godiya yayi mata don yana son bin 'yan uwansa amma baya son kwana saboda kada aikin yayi mata yawa.


Dakin da aka sauki dreban gidansu Ghazalatu yaje ya tarar da Awwab ya karbi mukullin motar. Kudin mota da Zainab ta bayar a kai masa da zai koma Katsina yaje kai masa. Iyalan gidan su ma duka sati mai zuwa zasu taho Katsinan saboda bikin da yake na gida duka a garesu.


Shi kadai ya koma ciki Awwab ya zauna akan dan ginin da ya zagaye flowers din da aka shuka daga jikin bangon gidan. Waya yake son yi da Ghazalatu yau tun da ya taho tana fushi basu sake magana ba.


Da sauri ta dauka da ya kira sai kuma tayi shiru don ta nuna masa fushinta na kin kiranta da wuri.


"My G fushin ne ya tashi?" Nishadi yake ji sosai yadda suka rinka hira da Alheran kamar basu rabu ba. Kusan komai na rayuwarta da zata iya tunawa ta fada masa sai yake ga kamar a gabansa ta tashi. 


"Idan nayi magana kace na fiye kishi ko korafi. Tun yaushe ka isa amma ko text ban samu ba talkless of waya."


Sai yaji babu dadi don ya sani bai kyauta mata ba. Hakuri ya bata don bashi da girman kai ko kadan. Yayi mata laifi dole ya kwantar da kai ya rarrasheta. Kusan wayar minti talatin suka yi sai da yaji ana masa warning na karewar credit.


"Zan kiraki gobe in sha Allah, zamu je duba baban Ummi a garinsu. Dawowarmu sai wurin jibi kenan dasu Mami"


"Mami ba tana gida ba?"


"Zasu taho da Ummina gobe sai mu wuce tare"


"Yayana kace mata zani please. Da saasafe sai na koma gidan mu taho tare"


Yaji dadi sosai saboda shima ya soma kewarta. Suna gama wayar yace ta kira Mami din credit dinsa ya kare. Ta kirata ta wayance da cewa wurinsu Zahra take son zuwa. Mami tace to ta zauna su zasu biyo su dauketa.


Falon ya koma ya same su kowa na  cin abincin dare banda Radhiya da tasa plate a gaba tana kallonsu.


Akan doguwar kujera ya zauna ya kwantar da kansa baya. Alamun idanu yaji a kansa ya dago. Ai kuwa duka shi suke kallo har Radhiya

"What?" Yace yana kallon kansa.


Fauziyya ta nuna masa plate din gaban Radhiya. Taliya ce fara da sauce din ganyen alayyahu da ugu sai balangu mai dan karen dadi da Ibrahim da Emzee suka siyo. Dama yanzu sune 'yan zuwa aike.


"Me ya sami abincin Alheran?"


Kunya taji ta kasa fada masa bayan cika bakin da ta gama. Zayyana kuwa tace "kowa shaida ne Adda Radhiya zaki min gyaran akwatina tunda kin kasa"


"Dama akwai abinda zaki kasa?" Yayi tambayar yana kallonta.


Ta dai yi saranda inji bature kaudin nata bai kai nan ba ashe ta gama cika baki. Tana ganinsa taji ko da wasa bazata iya fada masa zaman me take yi ba.


"Emzee me ya kama bakin yayarka ne ta kasa magana?"


"Babu ruwana ni dai" ya cigaba da cin abincinsa yana murmushi.


"Ni bari na fada maka Hamma" Ibrahim yace yana kallo Radhiya ta daure fuska "Zayyana tace kafi sonta shine Radhiya tace don bata nan ne dama. To shine Zayyana tace mata ita fa ko me take so kana yi mata. Idan kana gida hatta abinci tare kuke ci. Shine Radhiya tace wai wannan na gaban nata kaine kace ta zuba muku tare kafin ka shigo. Betting su ka yi"


Zamowa yayi daga kan kujerar yana  janyo plate din gabansa bayan ya tankwashe kafafunsa.


"Babu ruwana da wasanninku, Alheran matso mu ci yunwa nake ji"


Bude baki su kayi cike da mamaki harda ita Radhiyan. 


Kifta mata ido Awwab yayi a kunyace ta matso ya dauki fork a kan tray din da aka kawo kwanukan abincin.


"Muyi kama-kama irin na yara?" Yayi magana yana kallon idanunta. Tsabar kunya tashi tayi zata gudu.


"Ba fa ki isa ba, wannan abincin na mutum biyu ne so just sit mu cinye"


"Kaci ka rage min Hamma Awwab" tace tana kallon su Zahra tana neman taimako. 


"Tare zamu ci kada a barki da gyaran akwati"


"Babu komai zan iya"


Hade rai yayi "ina wasa dake ne?"


Ba shiri ta zauna tana bashi hakuri sai kuma ta waiga tana kallon kowa an zuba musu ido "don Allah ka bari su gama duka su tafi kunyarsu nake ji"


"Kin tabbata zaki zauna muci idan sun tafi?"


"Eh mana"


"Kamar gaske"


Bude baki tayi za ta sake magana kawai ya tura mata fork din da ya ciko da abinci tun dazu. Ibrahim ya dora hannu ya rufewa Emzee idanun da ya zaro sun ga abinda basu saba ba. Zahra ma sai ta rufe nata ta sakalo hannuwanta akan idanun Fauziyya da Zayyana suna faman dariya.


Radhiya kasa motsi tayi sai idanu da take ta kiftawa ba kakkautawa. Awwab yayi murmushi duk da yayi ne kawai saboda kannensa amma abin ya tsaya masa a rai dakewa kawai yayi ya dauko kofin da aka cika da juice ya miko saitin bakinta.


"Sorry na cika miki baki, hadiye ki sha wannan"


A guje Radhiya ta bar falon kafin ta kasa numfashi. Yau ta gamu da gamonta. Ita bata taba kunyar wani mahaluki ba kamar yadda taji Awwab ya gama da ita ba yau.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Bata tsaya ko ina ba sai daki ta cire hijabin da dankwali ta fada kan gado. Wani tunani ne ya shigeta haka kawai kada a sake tsautsayi ta dauki dankwalinta ta daura.


Awwab kamar bai san me yayi ba ya shiga cin abinci hankali kwance yana jin matan suna kuskus a junansu. To meye ma a ciki daga bata abinci. Da ace sun tashi tare baya jin akwai abinda zai kasa yi mata sai dai a taka masa birki tunda mace ce. Allah ne Ya hada jininsa da na iyayenta sai Ya sanya masa matukar kaunarta tun tana tsumman goyo.


 Emzee yaso dauke kai amma ya kasa. Karshe ya dauko wani littafi a kusa dashi ya bude shi ya kifa akan fuskarsa yana dariyar da ba sauti. Gaskiya yaji kunya kamar shi aka bawa abincin. Ibrahim ne ya fara tsokanarsa sai kawai ya tashi da plate dinsa a hannu zai koma daki.


"Dawo ka zauna ka gama cin abincin nan" Awwab yace ko kallonsa baiyi ba. 


"Na koshi"


"Kira min Alheran"


Ba musu yaje ya fadi sakon, maimakon amsa sai ta kara dukunkune kanta ta tura a karkashin filo. Murmushi yayi kawai ya fita ya dawo ya fadawa Awwab taki tashi. 


Sai da yaci rabin abincin ya mika masa plate din "ka kai mata nata, sai da safen ku"


Tashi yayi zai tafi dakin Ibrahim inda aka yi masa masauki Zayyana da ta kasa hakuri ta fara shagwabe fuska "Hamma ni baka taba yi min irin haka ba, harda bata a baki"


"Ba kiji ta fada muku cewa a rashinta nake kulaki ba" ya fada da wasa.


Kukan shagwabar da ta saba ta fara  "kuma sai na...."


"....fadawa Daddy" Ibrahim ya karashe mata yana kyabe fuska yadda take yi.

Awwab ya kusa kofa don idan ya biye mata karshenta a daren sai ya ga wayar Daddy. Juye juye ta soma yi Emzee ya dawo daga ajiyewa Radhiya abinci ya ganta.


"Wa kike nema?"


"Kai mana"


"Inyi miki me?"


"Ba Hamma Ibrahim bane yake tsokanata"


"In fada miki sunan Fulatancinsa ki rama?"


Cikin sauri Ibrahim yazo ya tura shi daki yana magiya da yayi shiru. Tun da Radhiya ta fassara masa ma'anar Surbajo yake gudun sunan kuma dashi Emzee yake samu ya dan kashe bakin idan ya dame su.


Da yake Mami ta fada musu cewa sammako zasuyi su baro Katsina su ma basu yi sanya ba wurin tashi da wuri. Zuwan 'yan matan ba karamin dadi ya yiwa Zainab ba. Su tayata hira ayi ta barkwanci sannan basa bari tayi komai. Zahra da Fauziyya sun jima da gogewa wurin aikin gida da girki. Saboda Mami taran safe zuwa taran dare tana gidan aikinta. Su ne suke komai. Shiyasa Zayyana ta shaku dasu sosai wani zubin bazaka ce yayyenta bane da suka girme mata da yawa.


Kowa ya shirya cikin kayan kirki Radhiya ta bude jakarta kenan bayan ta gama shafa mai Zainab ta leko tayi kiranta. Dakinta ta bar musu dama. Yanzu kuwa da ta kai Hadir falo bayan ya gama breakfast sai ta kirata dakinsa. Ledoji uku ne a gabanta manya ta tura mata daya.


"Ga naki kafin ku tashi daga bacci telan ya kawo"


Radhiya ta bude baki tana kallon kayan da Zainab din take zarowa. Atampa guda uku, material daya, shadda daya da wasu yadika combination biyu. Kwalkwal tayi ta idanu zata yi kuka. Duk wannan ita kadai.


"Bana son kuka fa kin sani ko yanzu naje na fada a hanaki yin sojan."


"Mama nagode" tace hawayen yana fitowa. Yarinya ce mai rike abu a rai shiyasa bata manta alkhairi ko sharri. Da yake dai wasa da shirme sunyi mata yawa a ka shiyasa sai ka ga kamar bata da damuwar komai.


Banda kaddara da Zayyan yana raye Zainab ta sani da yanzu sun kai wani mataki a aikinsu. Yadda yake da kwazo da himma tasan 'ya'yansa sai dai wani yaci arzikinsu. Babban dalilin kiran dama so take ta shirya Radhiya da kanta. Mama Zainab 'yar kwalliya ce ajin karshe. Idan ka ganta a yanzu da take cikin farincikin kasancewa da Hadir duk da a zahiri za'a iya cewa nauyi ne shi a gareta amma fes take kullum. Gogewarta a soyayya duba da tarihin rayuwarta yasa tun jiya ta daukarwa kanta nauyin sake hada Awwab da Alheran domin su cimma burinsu cikin sauki akan yaran. 


Kallo daya zaka yi musu kasan sun dace da juna amma idan ka san kowannensu ta fannin zamantakewar rayuwa dole ka chanja shawara. Awwab dan boko ne tashin turai. Yana da ilimi, wayewa da kudi domin kuwa pilots masu aiki da kamfanin KLM suna cikin mafiya samun kudi cikin tsararrakinsu. Alheran Radhiya kuwa yarinya ce da ta tashi a rugar fulani a cikin wata karamar hukuma. Wannan kadai ya isa zama wawakeken bambamci tsakaninsu indai zaman aure zasuyi wanda babu soyayya. Abubuwan da ya sani ko yake so bata sansu ba bare ta so su. Wayewarsu ba iri daya bace. Tayi nata karatun daidai gwargwado amma baza'a taba hada shi da nasa ba tunda iyakarta secondary. Shiyasa indai ana so zaman aurensu yayi karko to a samu soyayya mai karfi da za ta zama igiyar dauresu. 


Wani kaya Zainab ta

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment