Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ambata ko agidan ku aka ambaceta sai fuskarki ta sauya. Idan ma wani abin ne ya hadaku ki shirya jibi zamu wuce Sakkwaton sai ku sasanta”

Kallon wulakanci ta jefa masa duk da taji tsoron tsawar da yayi mata “ba zani ba idan ka matsu da ganinsu kaje kai kadai”

Ransa ne ya soma baci shima “na fasa a gobe ma zamu tafi, haba yarinya mai nutsuwa da kunya baki da aiki sai na kusheta da jifanta da bakaken kalamai”

“Da kasan tana da halayen kirki me ya hana ka nemi aurenta ka barni na auri wanda nake….”

Tasss taji saukar mari a kumatunta sai da ta ga haske, rai a matukar bace Salisu ya nunata da yatsa “bar ganin ina lallabaki wallahi sai nayi miki shegen duka a gidan nan. Ke wace irin mutum ce ne? Kina ta abubuwa ina kawar da kai to amma tura ta kai bango tunda har jininki baki raga musu ba. Ki shirya gobe zamu tafi sannan ki tashi ki hada ruwan omo da dettol ki bi duka gidan nan ki goge min. Su bayan kofofi da kujeru duka ki tsaftace min gida ko ina warin yawu ya isheni. Idan na sake kamaki kina tofa yawu nan ba a wancan abin ba wallahi jikinki ne zai gaya miki. Tashi ki bani wuri ni”

Ba karamin tsorata tayi ba ta kai mai hakuri bango. Tsoro ne da ita tun da can, soyayyar Zayyan da ta bari a zuciyarta da kyashin kanwarta su ne suka maidata haka. Jiki na rawa ta tashi yace ta dawo sai ta gama cin abincinta tukunna.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: I
*KANA NAKA…*

Shirye shiryen tarbar bakin da zasu zo suna ya kankama. Zayyan ya dage a gidan mahaifinsa za’ayi taron duk da cewa kawunansa da Mal Aminu sun ce gara ya yi a nasu saboda gudun bacin rai da ga Jume ko ‘ya’yanta. Ya riga ya gama tsara yadda zai bi da su domin gujewa hakan. Gidan yaje har daki ya same ta ta hakimce tana taunar goro.

“Hutawa akeyi ne Jume? Kawarki tana gaisheki”

Tabe baki tayi tana kallonsa ya zauna a kan yagaggiyar ledar dakin “kawarsu dai wadanda aka haifawa. Ni a su wa kuma?”

Basarwa yayi ya tankwashe kafafu “dama alfarma nazo nema, ina son ayi taron sunan a gidan nan ne”

“Dama jiranka nake naga iya gudun ruwanka tun da aka fara shigowa da bokatan fenti dazu. Ita matar taka basu da dangi ne da bazata koma gidansu ba? Naga haihuwar fari ce, ya dace ace tana gaban iyayenta. Tsabagen rashin ta ido ka barta a gidanka kuna kwana daki guda.”

“Cikin masu zuwa sunan akwai matar babanta da zata zauna har ayi arba’in tare da ita. Ni zan koma wani gidan a cikin barikin kafin su gama”

Maikudi ne ya shigo fakam fakam ya sami guri ya tsaya ayi zancen dashi. Zayyan ya sake fada mata yana son sauke baki da ga Nijar da kuma mutanen Sumaila a gidan nasu tunda babba ne.

“Ince ko ka ga nayi kama da baiwar gidanku da zan zauna tarbar baki. Kaga Zayyanu tun wuri ka san me kake ciki da bakinka”

Murmushi ta ga yayi maimakon ya tashi ma sai ya gyara zama “to babu matsala zan yiwa su Kawu magana. Sai abu na biyu nace idan an kawo kudin rakuman wace sana’a Maikudi zai fara?”

A tare su ka taso masa kamar zasu zaune sh. Maikudi ya zauna a gefensa yana fara’a kamar gonar auduga, hakansa zai cimma ruwa. Jume ma sai ta saki fuska kamar ba ita ba.

“An sayar da rakuman naka ne?” Maikudi ya tambayeshi da zumudi.

“Eh, zasu taho min da kudin, jibi nake sa ran isowarsu” ya bashi amsa.

Sai ga Maikudi ya tashi jiki na rawa “Bari na kira yayyenka malalatan banza su zo a fara gyara gidan nan, mu gidanmu da yake da wadatar dakuna kamar ramin bera, Jume yaushe zaki ce sai ya nemi su Kawu don iya tonawa kai asiri”

Matsowa tayi kusa da Zayyan tana dariya “shima yasan wasa nake yi masa. Ka nemi masu fentin su zo ayi a gama da wuri sai a share dakunan ayi shimfida.”

Mayar da kansa wawa yayi suna ta bidirinsu yana biye musu. Maikudi da son banza harda cewa an hutar dasu yin fenti tunda su ma baifi wata uku ya rage dukkansu su ukun zasuyi aure ba.

**********

Cikin ikon Allah baki sun iso an kaisu masauki, washegari za’ayi taron suna. Zayyan ya wadata iyalinsa da duk abin da ya dace. Wani hadin kai da ga bangaren sojojin su ma sun hada masa gudunmawa sannan matayensu sun zage dasu ake komai kamar yadda su ka saba idan dayarsu ta haihu ko wani taro ya tashi. Salame da Nene Marka kanwar Malamijo a gidan zasu kwana sauran kuma duka suna gidansu Zayyan.
Su Nene sun riga isowa ga yamma jama’ar gidan sun watse sai ita da Mairama da Zainab. Mami ta wuce gida Fauziyya tana fama da zazzabi. Salisu na tsayar da mota a harabar gidajen da suke jere a wurin ta fito da sauri gabanta yana faduwa ta barshi yana yiwa security din da yayi musu rakiya zuwa gidan godiya.

Ciki ta shige tana fatan yin tozali da Zayyan. Sai dai idanunta akan na Mairama su ka sauka tana shayar da jaririyarta. Wani kululun bakinciki ya taso ya tsaya mata a wuya. Mairama tayi wani mugun kyau ta ciko ko ta ina. Kallo daya zaka yi mata kasan cewa hankalinta a kwance yake. Da sauri ta cire yarinyar da ga bakin abincinta ta tashi ta fada jikin Salame tana murna da tsalle sai da Yadikko tace tayi a hankali saboda yanayin jikin haihuwa.

“Wayyo Adda Salame nayi kewarki sosai ashe kina hanya. Ina yayan namu?”
Da kyar ta amsa “yana waje, ki tura mijinki ya bashi masauki”

Tsabar murna duk ta rude ma tayi hanyar daki neman mayafi sai ta jiyo muryar Zayyan din suna magana da Salisu. Salame cikin zakuwa ta juya “bari naje mu gaisa da angon karni”

Nene ce ta dakatar da ita “wa yake ta angon karni baki ga ‘yar taki ba, dawo kiyi zamanki nasan zasu shigo”

Ba haka taso ba amma dolente ta zauna. Mairama ta gabatar da Zainab wadda ta tashi tana tayata hadowa su Salame abinci da sha.

Daga nan Zainab din tayi sallama ta tafi Yadikko kuma ta shiga wanka. Baby tana kwance akan wani bargon yara mai kyau Mairama ta sake komawa kitchen ta soma kuka. Har wannan lokacin Salame dama bata yi karar cewa a bata ita ba bare ta dauketa saboda bata ma son ganinta har ranta. Kukan ya tsananta Mairama tana ji ta kasa cewa ta dauketa tunda ai ba kurma bace sannan tana jin nauyin ta fito ta dauketa a ga tayi rashin kunya.

Nene tana da ga bandaki kukan ya isheta tana tunanin me ya sami yarinyar. Harara Salame ta jefa mata sannan tasa hannu tana dan taba gefen jikinta wai rarrashi. Daga sama ta bayan kujerar ta ga an zuro hannuwa an dauketa.

Waigawa tayi da sauri idanunta su ka gane mata Zayyan Tureta. Sanye yake da khakinsa ya zura hularsa cikin wani abu da aka yiwa maballi daga kafadar rigar. Yayi matukar kyau da haske aure ya sake gyara shi. A kafada ya dora ‘yarsa yana shafa mata baya.

“Waye ya taba min mamana? Sojoji basa kuka fa ‘Yar soja”

“Zayyan ina wuni?” Salame tace cikin sanyin jiki. Bata san zai shigo ba da ko don ta burge shi ta dauki ‘yar.
Tamkar bai ga mutum ba ya shareta ya shiga kwalawa Mairama kira. Tana tsaye dama daga kofar kitchen din duk abinda Salame tayi ta gani tunda kujerar ta bata baya ne. Mamakin wannan mummunan canjin daga ‘yar uwarta take yi. Ashe ko me ya hadasu tun kafin suyi aure bai kare ba har yana son shafar ‘ya’ya. Hawaye taji ya soma sauko mata tana kallon bayan Salame a inda take zaune kamar gunki saboda yadda taji kunyar abinda ta yiwa jaririyar a gaban babanta.

Hawayen nata Zayyan ya gani ya matsa gareta da dayan hannun da yake shafa babyn ya janyota jikinsa da karfi ya rungume da hannu daya.

“Kada na sake ganin kin bar min yarinya ita kadai a falo. Idan babu kowa ki goyata ki shiga kitchen din…kinji”

“Kayi hakuri baza’a kuma ba, na ga Adda tana wurin ne” tace tana karbarta daga hannunsa. Salame ta juyo kamar mai ciwon wuya tana neman kalaman wanke kanta.

Kamar bai ji ba sai cewa yayi “Taimaka ki hada min abinci da zan tafi dashi inda zamu kwana da Salisu. Zan kaishi yayi sallah da wanka na dawo na dauka. Amma ki fara cikawa wannan sojar ciki”

Hannunta daya ta dora a gefen ido tayi masa salute “Yes Sir”

Matsowa yayi yana neman sumbatarta ta goce tana dariya. Mutuwar zaune Salame tayi. Shi kuwa Zayyan da biyu yake yi don ji yayi ya kara tsanarta. Ba don ta hada jini da Mairamansa ba da sai ya saka ta a guardroom ko na sa’a daya ne ya huce kukan ‘yarsa.

Da ya fita Mairama ta kawo mata sauran kayan abincin batare da ta sake yi mata magana ba ta zauna bawa ‘yar nono.

“Ki kwashe ba ci zanyi ba don yanzu ba komai ke zauna min a ciki ba”

Wai nan so take ta sanar da ita itama tana da cikin. Sai Mairama ta gwada mata halin matar soja da ta fara koyon yadda yake juya zance musamman idan ya fuskanci abu kake son sanar dashi da dabara don ka bashi haushi.
"Adda yaya hanya? Ya zaman Kano?"

Sai da Salame ta kara kallonta irin baki ji me nace dinnan ba sannan ta chanja zancen tace lafiya. Zaman kurame su ka koma har Nene ta fito tana tambayar me ya sami baby dazu take kuka. Babu wadda ta amsa mata a cikinsu duk sun daure fuska sai ta kyale su ta sa tv a gaba tana kallon tashar NTA.

Zaman ne ya ishi Salame ta tashi ta shiga daki wai zata yi wanka. Mairama ta bi bayanta taji ko akwai abin da zata bukata. A tsaye ta sameta tana karewa dakin kallo tana tabe baki.

"Af...ke fa gadon da Malamijo yayi mana dashi aka kawoki ko? Amma naga labulayen kamar sababbi ga TV ma a falon da firij. Kin fara sana'a ne ko Zayyan din kike tatikewa?"

"Yo Allah na tuba Adda mace da mijinta har sai kinji yaya ake kudi ke fita har a gyara mata gida? Dadin zama ne kawai da iya tafiyar da miji"

Ta fadi haka ne saboda gorin da Salamen ke shirin yi mata. Ita kuma Salame sai ta dauka cin fuska ne ko ta gane ta son sa.

"Ki dai bi a hankali maza basu da tabbas. Canja mace a wurinsu ba wata tsiya bace"

Zaro idanu Mairama tayi da mamaki. Har fatan aurenta ya mutu kuma Salame take yi? Indai haka ne dole ta kama kanta don bata ga me ta tsare mata ba da take nuna mata hassada irin haka. Kowa ya shaida mijinta yana da kudi ta rasa gane bakincikin na meye.

Karfe goma na safe a gidansu Zayyan tayi musu. Anyi taron suna na kayatarwa don Zayyan ya sakar musu yadda zasu fita kunya. 'Yan uwansa mutan Agadas sunyi masa halacci duk da rashin mahaifiyarsa sun zo da yawansu tare da gudunmawa mai yawa. A cewarsu basu sami bikinsa ba dole a fanshe yanzu. Gashi jaririya ta gaji sunan 'yar uwarsu.

Mutan Sumaila ma sun sha kallo ganin irin suturar da Zayyan ya wadata Mairama da su na fitar suna. Abin nasu ya burge sosai musamman da wata kanwar innar Zayyan ta kawo kayansu na gargajiya na kabilarsu ta Tamasheq ta bawa Mairama.

" 'Yata ga wannan ku saka ke da maigidanki da jikarmu ayi hoto. Dashi nake son tafiya saboda wadanda basu zo ba su ganku."

Mairama sai godiya take su Zainab suna tayata. Riga ce fara kamar buba ta zarta gwiwa da kadan gaban ta sha aiki da shudin zare sai zani shudi. Ga kuma sarkoki da yari duka irin nasu da abubuwan sakawa a ka. Mami ce ta karbi Radhiya yayin da wasu 'yan mata biyu kusan sa'annin Mairama su ka ja ta dakin da su ka kwana. Da taimakonsu ta shirya komai su suka yi mata. Abin hannu da na wuya da kunne harda hanci kowanne yayi mata cif. Na gashin kuwa sai da daya ta yi mata kalba kananu guda uku-uku a gefe da gefen kunnenta ta zubo mata dogon gashin irin nasu sannan aka dora mata shi ya zauna daga gaba kai kace wata sarauniya ce. Hatta fuskarta kwalliyarsu aka yi mata leben nan ya sha fenti yayi baki. Da yake fara ce ba karamin kyau tayi ba ta saje dasu. Wata guda ta soma ji daga tsakar gidan aka dora mata shudin yadi irin na zanin wani irin yafawa yadda suke yi sannan su ka rike mata hannuwa aka fito da ita.

Turus tayi ga wata irin kunya kamar sabon aure da su ka hada idanu da Zayyan. Yayi kyau har bata san yadda za ta kwatanta ba. Shima kayan gargajiyar ne a jikinsa na ciki farare babbar rigar da kuma rawani duka shudi.

Kanta a kasa shi kuwa ya zuba mata idanu, manya cikin 'yan uwan nasu suna ta guda. Da shirinsu suka zo da sunan yi masa nasu bikin. Taro ya kayatar da jama'a ba kadan ba duk da iyakarsu cikin gidan. Salame tamkar ta bude ido ta ganta a matsayin Mairama. Ganinsa cikin wannan kaya ba karamin sake fama mata ciwon son sa da yake nukurkusarta yayi ba.

Mai hoto aka kira yazo akayi ta dauka. Gwaggon Zayyan tace suyi su uku zata kai hoton gida. Days suka dauka a tsakar gidan a tsaye tana rike da Radhiya shi kuma a gefenta. Dayan kuwa dakin Innarsa yace su shiga a kan tsohon gadonta ya zauna da 'yarsa a hannu ita kuma a kusa dashi. Daga nan ta kira danta Awwab ta dora masa kanwarsa tana tallabe da kanta daga bayansa ta dan duka aka yi musu sannan Zayyan ma ya shiga.

Ranar idan ka gansu dole su baka sha'awa. Mutan Agadas har irin abincinsu sun dafa duk na bikin dansu Zayyan da murnar haihuwar Alheran Radhiya.

A gidan maijego ta kwana ranar tare da danginsa ana ta bata labarin 'yan uwansu da irin yawan danginsu. Gwaggon Zayyan tace mata cikin gurbatacciyar hausarta da ace Zayyan ba soja bane gida Nijar suka so komawa dashi bayan rasuwar Mal Muhammadu.

"Idan ya sami saukin aiki ku kawo mana ziyara kinji Mairama. Zayyan dan gata ne saboda yana zagaye da dangi masu kaunarsa saboda maraicin uwa. Da mahaifinsa ya amince min naso tun rasuwar Alheran na dauke shi."

Hawaye ta ga dattijuwar tana gogewa shiyasa taji zuciyarta ta karye "In sha Allahu zamu zo"

"Allah Ya nuna mana"

Mairamu a ranar tayi kwanan farinciki da bakinciki duka lokaci guda. Soyayyar da ta samu daga wurin dangin mijinta ta tsaya mata a rai tayi matukar farinciki. Sai kuma tunanin dangin Innarta da babu wanda zata iya nunawa tace nata ne ta wannan bangaren. Sun manta da ita da shafin rayuwarta saboda rashin uwa da tsanar da suka yiwa Malamijo akan rikon sakainar kashin da ya yiwa 'yar uwarsu a gidansa.

Asubar fari aka fara tashi saboda masu shirin komawa. 'Yan Sumaila ne farkon tafiya aka bar Nene zata zauna wanka idan sunyi arba'in su tafi Sumailan tare. Mutan Agadas ma kaf sun gama shiri wai basa son dorawa Zayyan nauyi idan suka cigaba da kwanaki. Kawunnansa biyu ne a cikin tawagar Ghoumar da Sidi. Shatara ta arziki suka yi masa kyautar kudi da irin abin amfani nasu na can. Kamar kada su tafi haka Mairama taji har kofar gidan inda bus guda biyu zasu daukesu tayi musu rakiya.

Daga nan gidanta ta koma tare da Yadikko da Salame su ma a ranar zasu wuce.

Manya akwai kaifin tunani da hangen nesa. Cikin kankanin lokaci Nene ta gane manufar Salame akan Zayyan. Tasha mamaki ba kadan ba saboda a da tana yi mata kallon wadda zata iya sadaukar da komai domin farantawa kanwarta. Ashe abin ba haka yake ba. Ta ciki na ciki ne. Jan bakinta tayi ta tsuke bata tona ba sai dai ta jasu su biyun tayi musu fada akan sabon yanayin alakarsu.

"Nene gara da ki ka kula, ki tambayeta idan na mata laifi ne na bata hakuri"

Kallon Salame Nene tayi ta dauke fuska tare da janyo jakar kayanta tana shan kunu.

Nene tace "Salame idan ma da sabani na kula kece kike jansa. Tun zuwanki ina lura dake ko da wasa wallahi baki dauki Radhiya ba."

Saurin kallon Mairama tayi don kuwa hakan ne. Mairama tuni ta gane shiru kawai tayi.

"Nene bana jindadi tunda nazo garin nan shiyasa. Mairama Allah Ya baki hakuri...shikenan ko" tace a kagauce tana son fita daga dakin.

"Juna biyun shine zai sa ki kasa daukar 'yarki? Ki dai yiwa kanki fada don rayuwa bata da tabbas"

Mairama bata ma tanka ba ganin za ta rana musu wayo. Da zasu tafi Salisu ya kawo kudi ya bayar a sayawa Radhiya kaya harda cewa inji mamanta Salame. Godiya suka yi masa sun san kuma kara ce kawai yayi amma babu wani inji Salame.

Sun shiga gidan Nene ta goya Radhiya ta shige daki wai garin akwai sanyi. Ga gida mai daki daya tana rufo kofar Zayyan ya rungume Mairama harda ajiyar zuciya.

"Na wahala Mairam, na wahala sosai"

"Taron jama'a ko?" Tace tana kokarin kwace jikinta kada Yadikko ta fito.

"Wane jama'a, a kaina suke? Rashinki ne ya addabeni."

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya dago habarta "dadina da mutum kunya. Yaci ace mun wuce wannan matakin fa, ga 'yar soja can kina gani"

"Ni dai kazo ka tafi kada ta fito ta sameka"

"Kin yarda zaki yi min irin kwalliyar jiya idan ta tafi?"

"Na yarda"

Rungumeta ya sake yi sosai "Ina sonki Mairam, shigowarki rayuwata ya sanyani farinciki mara misaltuwa. Karo na farko naga da dangin Innata su ka zo da yawa haka saboda ni. Kuma duk a dalilinki ne da kyautar Alheran da kika yi min. Nagode"

"Ina fatan Allah Ya bani ikon cigaba da kyatata maka Sojana. Kayi min komai a rayuwata. Ka rabani da kunci da bacin rai. Ka zame min miji, aboki kuma dan uwa"

Kashe mata ido yayi "ina ma daga ni sai ke a gidan nan kike wannan kalaman"

Ta gano manufarsa ta shiga dariya a hankali. Kofar dakin aka taba ya tashi a guje ya fice ita kuma ta dake fuska kada Yadikko tace me suke yi.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ***********
Kyakkyawar kulawa da gyara Mairama take samu daga wurin Nene Marka. Ita da Zainab da Mami shakuwarsu sai gaba take kara yi. Idan kaga Awwab baya gidan to makaranta ce ta tsare shi ko dare ya tafi yayi bacci. Amma kullum yana wurin Mairama da kanwarsa Radhiya. Zahra da Fauziyya suna shan gori yayi ta cewa su Antinsu bata kawo baby ba har yanzu. Idan ya fadi haka Zahra sai tace ai nata cikin ya kusa fashewa ne su ma bazasu bari ya taba musu baby ba.

Zayyan ba karamin kewar matarsa yake ba. Ko yaya Nene ta dan bada wuri sai ya faki ido ya rungumeta yana fada mata yadda yake kewarta da matsuwa ayi arba'in dinnan kowa ya huta. Jaririyarsu Radhiya ta kara yin bulbul gwanin sha'awa. Idan kayi mata kallo daya sai ka rasa wa ta debo cikin iyayen. Bafillatanar mahaifiyarta ko sojan babanta da yake surki tsakanin mutanen Agadas da na Tureta. Yarinya ce mai matukar shiga rai musamman idan tayi murmushi gefen kumatunta na dama ya lotsa. Awwab har yatsa yake sakawa a wurin don kawai tayi masa murmushi.

Ranar da su ka cika wata biyu Zayyan ya kwashesu a motar haya sai Sumaila. Mairama bata taba tunanin zata yi kewar gidansu ba sai yanzu. Sun isa yamma likis 'yan uwa ana ta tururuwar ganinsu.

Malamijo yana jin isowarsu daga gona ya zari takalmansa ya yo gida. Fadi yake 'yarsa mai auren soja ce ta iso tare da jikarsa. Abin arziki kaza guda ya bayar irin 'yar sati goman nan aka yanka Yadikko ce da girki tayi musu shinkafa da miya.

Daki aka gyarawa Zayyan ya kwana. Da safe abin mamaki sai ga Salame wai bazata iya jiran su iso gidanta ba tana kewar Radhiya. Mairama taji dadi balle da ta ga yadda take haba haba da Radhiyan harda su goyo duk da ana hanata saboda nata cikin ya fara fitowa.

Zayyan dauke kai yayi saboda shige masa da take yi tana ta so ko magana yayi mata. Allah sai Ya dauke hankalin Mairama daga garesu bata kula ba.

Kwanansu biyu sannan su ka wuce Balan a karkashin karamar hukumar Gaya inda gidan Nene yake. Tana da kishiya guda daya mai yara shida. Maigidansu manomi ne babu wani kudi sai rufin asiri. Irin kyautar da Zayyan yayi mata Mairama kanta tayi mamaki. Nene Marka harda kuka tana masa godiya.

"Nene mune da godiya, Allah Ya saka da alkhairi. Idan ta sake haihuwa ke zaki dawo ko?"

Mairama ta tashi daga wurin da sauri saboda kunya. Nene tayi masa dakuwa tana murmushi "kuji min dan kaniya, wato a gaban nawa kake rashin kunya ko Zayyanu"

"Fada nayi fa saboda kada ace wata daban ce za ta zo." Tare su ka yi dariya don ta saba da barkwancin surikin nata.

Kofar dakin ta kalla ta tabbatar Mairama tana wurin kishiyarta sannan ta dan matso fuskarta babu alamun wasa "Zayyanu nasan kana sane da son da Salame take yi maka"

Gabansa ne ya fadi ya dago kai yana kallonta da kallon kofa "Nene ki bar zancen nan, yau ko Mairam zata fadi ta mutu bazan auri Salame ba. Matar da aure bai hanata nunawa mijin kanwarta soyayya ba"

"Tun yaushe ta fara son ka?"

"Kafin muyi aure...don Allah bana son kowa yaji. Ni dai babu abinda ya taba hadani da ita"

Hankalinta taji ya kwanta "nagode Zayyanu. Ka rike min amanar Mairama. Ga maraici ga rashin dangin uwa har yau mun rasa a wace rugar ma suke zaune. Duk tsiyar Malamijo yana ta kokarin nemansu domin ya faranta mata. Salame kuma ka barni da 'yar banza. Idan ta nemi tada muku hankali da kaina zan gyara mata zama don ba gagararmu tayi ba"

Kafin azahar sun koma Sumaila inda ta sake kwana biyu suka bar garin bayan ihsani mai tsoka da ya yiwa Malamijo da matan gidan. Mairama har mamakin ina ya sami kudi haka takeyi saboda ita tasan duka duka albashin nasu babu wata tsokar kirki.

Sun baro Sumaila tana sa ran za su wuce Sakkwato sai gani tayi sun shiga cikin Kano zuwa wata unguwa yana yiwa dreba kwatance. Gaban wani gida zubin zamani a wancan lokacin mai kyau da tsari tun a waje aka ajiye su. Mukulli ya dauko da ga aljihunsa ya bata yana dauke da Radhiya.

"Bude mana da sunan Allah"

Kallon tuhuma take masa yayi murmushi da ka yayi mata alamar ta bude. Ba musu ta bude yana cewa ta shiga da Bismillah. Farfajiyar gidan tana da dan girma daidai mota guda daya. Sai kuma ainihin ginin wanda flat ne gidan. Yana gaba tana biye dashi zuciyarta da tarin tambayoyi har ciki.

Wani korido su ka fara bi a karshensa kofa take inda suka tarar da katon falo ga kofofi a ciki. Daya bayan daya suke shiga yana mata bayanin. Kitchen, dakuna hudu, store da kuma bandakuna ko ina da fenti amma babu kaya. Daki daya ne aka shimfide da leda ga katifa sabuwa da filo biyu sai zanin gado a cikin ledarsa ko budewa ba'ayi ba.

"Sojana ina ne nan?"

"Mairam ga gidan mijinki na halak yau kin shigo"

"Gidanka ne nan?"

Takowa yayi gabanta ya hadeta da Radhiya ya kankame.
"Gidanmu dai Mairam"

Zaunar da ita yayi ya mata bayanin kudin gadonsa da ya narkar a wannan gini domin inganta rayuwar iyalinsa. Ya zabi zuwa Kano saboda gujewa fitina daga bangaren su Jume. Dama yanzu matsanancin fushi suke yi dashi saboda an gama taron suna basu ga komai ba. Da Jume da tado zance yace gida dai shima na mahaifinsa ne, idan basa son ya rabesu a raba gado ko dakin mahaifiyarsa a bashi. Sunyi rigima ba kadan ba ya fito musu gar da gar dinsa a soja mara daukar raini ko kadan. Suna ji suna gani dole suka hakura da haram din da suka kwallafawa rai.

Addu'a ta rinka jerowa yana amsawa daga nan yace to fa ta shirya jiya da ya taho cikin Kano siyayya yayi musu yana so ko sati suyi a

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment