Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kyabe fuska "ai ba'a gama film din ba"

"Brush kawai zamuyi mu dawo"

"To kaje ka fara yi kaine babba"

Dariya ta bashi wai nan wayo zata yi masa ya wuce dakin yayi ya dawo "saura ke"

"Kada ka kashe tv din Hammana yanzu film din ya fara kyau" tace tana tashi bayan bata fuskantar komai a ciki. Ko wuka za'a saka mata bata san me akeyi ba.

"Zama zanyi na gane miki inda kika tashi" ya zauna ta tafi.

Tana rufe kofa ya kashe tv din da fitila sannan ya shiga daki ya rufe kofa.

Ai tana jin motsin shigowarsa jiki ya soma rawa ta gama brush din ta kasa fitowa. Sai da tayi minti biyar ta yanke shawarar ce masa ita fa kallo zata yi kawai. Da kwarin gwiwa ta fito yana waya cikin harshen jamus yaki kallonta. Zaune yake akan gado ya mike kafafunsa ya jingina da pillow. Kofar dakin taje ta murda taji a rufe. Ta sami wuri ta tsaya tana jiran ya gama.

Sallamar mutumin yayi ya taso yana tahowa gabanta na kara faduwa. A tsakiyar dakin ya tsaya ya ware mata hannuwansa yana murmushi tare da yi mata nuni da ka. Babu yadda ta iya ta saki hannun kofar ta taka da sauri ta fada kan kirjinsa. Sun dauki kusan minti biyu a haka kowa da nasa tunanin da yake tattare da soyayyar dayan.

Da yatsunsa ya dago kyakyawar fuskarta a tausashe yace "Babyna guduna kike yi kuma?"

"Film din...." sai kuma tayi murmushi ta kasa karasawa.

"Kema kin san baki da gaskiya gashi kinyi shiru. Muje ni inyi miki tausar tunda kin kasa cika alkawari"

"Zanyi maka"

"Fara saka kayan bacci"

Akwatin nata ya bude babu ko daya na lefenta kuma suna Sakkwato za'a wuce dasu Abuja. Wardrobe ya bude inda ya zuba nasa kayan ya dauko mata t-shirt dinsa tana ta kamshi.

"In saka miki?" Yace yana dariya don yasan bazata yarda ba.

Harararsa tayi "da kayana zan kwanta"

"Schatzi" yace hannuwansa na jindadin yamutsa mata gashi ya rasa dalili ita kuwa da kyar take iya bude idanu saboda yadda take ji.

"Naam" ta amsa a raunane.

"Saka riga ko Ango yayi abinda yayi niyya"

Sakinta yayi ba don yaso ba tana ture turen baki ya fita daga dakin don ta shirya a tsanake. Cikin sauri take komai tana yi tana kallon kofa gashi key din ta waje yake. Rigar ko cinyarta bata gama rufewa ba. Tana fesa turare ya turo kofar jikinta ya soma rawa shi kuwa Awwab rufe kofar yayi ya jingina da bayanta tare da harde hannuwansa a kirji yana kallon Alheran a matsayin matarsa abar so da kaunarsa.

Turaren da ta dauka ta ajiye jikinta yayi matukar sanyi tana kallon gadon tana son zuwa ta kwanta ta rufe jikinta amma bata son yin kwakkwaran motsi a gabansa. Tahowa yayi gabanta yasa hannu a waist dinta ya matso da ita jikinsa da dayan hannun kuma turaren da ta ajiye ya dauka ya feshe mata jiki dashi sannan ya saka hannuwansa duka ta bayanta ya dagota jikinsa ya soma juyi da ita a dakin tuni ta kankame shi tana dariya.

"Please, please, pleeeeaaass ka ajiyeni" tace tana zagaye hannuwanta a wuyansa.

"Sai na cire miki wannan tsoron da yake hanaki sakewa"

"Zan sake....Chéri na sake ma.....Hammanaa"

Ajiyeta yayi a hankali tana jin kamar har yanzu juyin suke yi ta kankameshi tana sauke numfashi. Hannuwansa ta sake ji ta bayanta ya tura yatsunsa cikin gashinta da ya mayar abin wasa yana magana can kasan makoshi "na yafe miki tausar nan fa"

Zare jikinta take neman yi ta kasa saboda rikon da yayi mata a hankali tace "nagode"

Dago kanta yayi yana bin bakinta da kallo idanu a lumshe "gani nayi ko da tausa ko babu bazai hanani abinda nayi niyya ba"

Tsoron ya soma dawowa tace "Wai me kayi niyya ne?"

Wani irin kallo mai kashe jiki yake binta dashi yace "Spending the whole night loving you my baby. Ki taimaka ki bani dama saboda ko kinki bazai hana Awwab abinda yayi niyya ba, bani da hakuri indai akan sonki ne Alheran" kasa yayi da kansa ya soma kissing dinta tamkar ranar ya fara samun wannan damar. Radhiya bata iya sake komai ba sai abinda Awwab ya koya mata. Kamar yadda yace ya nuna mata soyayyar da bazata taba hadata da komai ba a rayuwarta. Bacci kuwa sai can cikin dare ya rungumeta tsam a jikinsa ta soma yinsa a wahale tana ajiyar zuciya hawaye har cikin bacci yana jin digarsu a kirjinsa.

"I am sorry my love" yace yana kara karfin rikon da yayi mata.
"I love you so much" duk da yasan ta dade da soma bacci ba zata ji ba.
Hannunsa na dama ya sarke da nata yana shafa kanta a zuciyarsa yana addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya da albarka a zaman aurensu kuma Ya basu hakuri da juna. Soyayyar gudan jinin Tureta da ita ya girma yana rainon abarsa a zuci tun kafin su sake haduwa. Idan da akwai abinda yafi love at first sight kuwa to shi ya fada head over heels akanta. Ita ce duniyarsa, farincikinsa, cikar burinsa.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Kiran assalatu na farko ya farkar da Awwab ya tashi da sauri yayi wanka saboda kada ya makara. A hankali yake komai saboda kada ya tasheta. Da ya gama ya sa dogon wando jeans ya dora rigar sanyi akan shirt din ciki don tun dare garin yake a lumshe ga iskar nan ta tsananin sanyin arewacin Nigeria da asuba. Zama yayi a gefen gadon yana shafa fuskar Radhiya a cikin duhun dakin sai haske kadan da yake fitowa daga toilet da ya bar fitila a kunne. Tashinta yayi yace asuba tayi. Sannu a hankali ta dago kan ta daga pillon ta bude nannauyan idanunta da fitowar hawaye.


Yatsansa ya dora akan lebenta "Shhhh haba babyna kinyi bacci da kuka kin tashi dashi bai kamata ba. Idan bazaki iya tashi ba ki jirani na dawo daga masallaci"


Hannunta na dama ta dunkule ta kai masa duka a kirjinsa tana kara narkewa cike da shagwaba da hawaye "bana bukata tunda ba ka sona"


Awwab yayi murmushi tare da mikewa yana son tayar da ita sosai "zan baki amsa idan na dawo"


Kunyarsa na tare da ita tayi saurin boye fuskarta cikin lallausan duvet din "Allah Ya tsare"


"Amin Alheran" 


Yasa kai ya fita sannan ta tashi tana cije lebe don ma ya fita da ya ga raki da shagwaba mai lasisi. Duk abinta bata so ya dawo ya sameta a kwance saboda tana jin kunyarsa kada yace zai taimaka mata ba yarda zata yi ba. Shawarwarin Mama Zainab da Innawuro tsohuwar kakarta da tun farko ta fara gyara mata jiki da lalle tayi amfani dasu wurin cire son jiki ta gasa kanta da ruwan zafi sosai. Tunda akwai sanyin gari sai ta kara jindadin hakan. Bata bata lokaci sosai ba saboda gudun kada ya dawo ya sameta ta shafa mai mai kamshi da body spray sannan ta mayar da t-shirt dinsa da ya bata kafin su kwanta da dogon skirt dinta. Hijabinta ta dauko a falo tazo ta tayar da sallah tana faman runtse ido.


Lokacin da Awwab ya fito a bakin gate ya hadu da Daddy. Kunya kamar ya nutse a wurin ya ji kamar ya koma saboda wani nauyin mahaifin nasa da yake ji. Samun kansa yayi da durkusawa har kasa yana tambayar Daddy din "an tashi lafiya? Yaya baki su ka kwana?"


Sakin fuska yayi saboda ya fuskanci Awwab din a takure yake da kunya ya ce "Lafiya kalau Captain yaya kwanan diyata?"


Kara masa kunyar yayi ya kasa amsawa sai kai da ya sunkuyar yana sosa keya. Daddy yayi murmushin manya yana musu addu'ar zaman lafiya.


Da aka idar da sallah a masallacin ya so yayi saurin tafiya gida amma idon Daddy ya zaunar dashi. Tsohon sojan ba wuya ya gano bakin zaren shiyasa yayi kokarin katse wani makocinsu da yake neman jansa da hirar zaben da ya kusanto ya tashi su ka dawo.


Gyangyadi Radhiya take yi akan abin sallah ta jingina bayanta da gadon ta ji ana rufe kofa. Cikin sauri ta cire hijabin ta hada da abin sallar ta ninke ta koma gadon ta rufa har ka. Sauran rufar ma a idon Awwab tayi saboda bude kofar dakin da yayi da sallama. A zuci ta amsa masa a zuwan bacci take yi. Yana kallon yadda take ta gyara kwanciya irin na masu baccin karya ya kyaleta sai da ya cire kayansa don yasan ba dadin kwanciya dasu zaiji ba ya saka jallabiya.


Zagayawa yayi gefen gadon bangaren da fuskarta ke kallo ya durkusa. Da sauri da sauri take fitar da numfashi saboda tsabar kaduwa ga hawayen tausayin kanta tana yi. Hannun Awwab ta ji ya janye rufar da tayi ya bude fuskarta. Cikin gashinta da ya bazu akan pillow din ya sarke yatsunsa yana jin yadda ta soma rawar jiki.


Idanunsa yake lumshewa yana budewa a kanta cike da kasala ya ce "Da kinyi soja yau da nayi musu dariya saboda kin basu kunya karshe. Abu kadan sai kuka jikinki yayi ta rawa."


Bakinta ta turo "to ba kaine ba..."


Ya karyar da kai idanunsa a kan bakinta "Saboda kin fini baki Schatzi, nima fa kukan nan ya kamata nayi tunda jiya aka kawoni" 


Dariyar da bata shiryawa bace ta kama ta. Yadda take dariyar ma baiki ya koma gareta ba saboda tamkar wanda aka sakawa magnet haka yake jin kansa. Sai dai yana tausayinta don yasan taji jiki...Allah Ya taimake shi an ware musu wuri ba a cikin gidan aka basu daki ba da an tafka abin kunya yadda ta rinka kiraye kirayen mutane.


"Yaya jikin naki my amazing wife?"


Juyawa take son yi daya barin saboda kunyar tambayar da yayi mata ya rike mata hannu yana girgiza kai.


"Ko zaki juya ki bari na fada miki abinda nayi niyya kafin kiyi bacci jiya" kasa kunnuwa tayi saboda ko me Awwab zai fada mata abin so ne a gareta. Ba tun yau ba ya kware wajen fada mata kalmomin da kan sa ta kwana tana murmushi ita kadai. Idonsa sarke da juna suna aikawa juna sakonni da fahimtarsu sai su din ya soma magana da muryar nan mai tsuma zuciyar Alheran Radhiya.


"Na karbi amanarki kuma na baki tawa. Matsayinki bana jin akwai wadda za ta taba samu a zuciyata. A kanki nasan mecece soyayya kuma nasan amfanin shakuwa. Baby kin faranta min rai sosai jiya duk da kin so cika min kunne da kuka...." murmushi tayi ta kawar da kanta shi kuwa tafin hannuwanta ya bi ya sumbata. Kafin ya cigaba da cewa,


"You have my love" ta dago kai kadan ta dube shi.

"You have my trust" ya matse hannunta yadda ba zata ji zafi ba.

"And you have my respect" ya duka tare da kissing goshinta.


Zai dago Radhiya ta zura duka hannuwanta ta rungumeshi a jikinta. Suna shakar kamshin jikin juna a haka ya dawo kusa da ita ya kwanta karatun nasu ya tattara ya koma na sababbin auren da suke matukar so da kaunar juna. Radhiya tayi dauriyar kin yi masa kuka amma ta kasa daga karshe. Kuka ne da tasan ba na wahala bane kawai harda wata irin soyayyar Awwab mara misaltuwa. Shi ma yana namiji yaya mamakin ganin yana tayata hawaye a lokacin da sabuwar soyayyarta take huda kowane bari na jikinsa tana sake samun mazauni. A take a wannan lokacin jikinsa yake fada masa cewa da wahala matuka wata mace ta sake samun gurbi irin na Alheran....son ta a jinin jikinsa yake. It has always been Radhiyan Hamma Awwab.


Bacci suka koma irin wanda da wuya in sun taba yin irinsa mai tattare da nutsuwa da kwanciyar hankali. Basu san lokacin da Zayyana tazo wurin goma ba tayi ta doka sallama da breakfast dinsu har ta gaji. Kofar net da aka zagaye karamar barandar da ke gaban katuwar golden kofar gidansu mai kyau ta bude ta ajiye kwandon tunda a rufe komai yake da wani kyalle mai kyau. Komawa tayi ta fadawa Mama ita fa taji shiru.


Shadaya saura wayar Awwab ta soma ruri ya dauka da sauri zai kashe saboda kada karar ta tasar masa Radhiya dake kwance akan faffadan kirjinsa. Sunan Mama ya gani babu damar kashewa kenan yayi kokarin zame jikinsa Radhiya ta kara cukwikuye shi tana zumburo baki. Murmushi ya saki ya kawar da gashinta daga kan fuskar yace  "so adorable".


Wani kiran ne ya sake shigowa still dai Mama ce ya danyi gyaran murya kafin yayi mata sallama sannan ya gaisheta.


"Awwab kayi hakuri surukanka zasu wuce ne mutanen Sakkwato da Sumaila shine suke son yiwa Radhiya sallama. Sai na ga ya dace ka fara shigowa kayi musu bangajiya"


"Mama ni kadai zan shigo?" Ya ce kamar zaiyi kuka don tsakaninsa da Allah kunya yake ji ya shiga gidan.


"Ka nemi 'yan uwanka su Bilal kuyi sauri. Ina kanwar taka ina fata ta tashi ta shirya ba jimawa zasu shigo"


Shirun da yayi da guntuwar in'ina ya fahimtar da Hajiya Mama komai. Murmushi tayi mai sauti Awwab ya rasa me zaiyi sai ya ga Radhiyan ma ta farka kawai shiru tayi tana kunyar tashi.


"Bani ita Awwab" yaji Mama tace.


Dora mata wayar yayi a kunne kafin ta soma magana Mama tace "saurareni da kyau Radhiya kin tuna me nace jiya ko?"


"Uhmm" tace a hankali.


"Tau, ki shiga ruwan zafi sosai kinga gobe akwai tafiya gabanmu idan ba so kike ayi ta zancenki ba ki gyara kanki. Zan shigo anjima idan bakiyi ba zan gane kuma kinsan sauran"


Rufe kanta tayi ta mikawa Awwab wayarsa. Tana ji ya tashi ya shiga toilet bai dade ba ya fito ya yaye rufar da tayi sai da tayi masa ihun ganinsa da tawul kadai gashi ya cire mata abinda ta rufe kanta. 


"Muje muyi wanka" kawai yace ya sunkuceta yana cewa ashe buhun sumunti ce bai sani ba. Duk wani zille zille da taso yi bai barta ta fita ba a haka akayi wankan. Bayan sun gama ya hada mata ruwa mai zafi a robar da ta zauna dazu wadda saboda hakan Mama ta saka musu ita.


"Kin sanni da kunne ina jin me Mama take fada" ya kashe mata ido ya fita ya barta da tulin kunya.


Lokacin da ta fito ya gama saka kaya sai wannan kamshin nasa na musamman take ji. Shadda ce ya saka mara nauyi ga hularsa a gefe.


"Ba don ina tsoron kaina ba kuma dai ana jirana da na tsaya shiryaki da kaina baby" yace lokacin da ya ajiye brush din da ya taje saisayayyen kansa.


"Na yafe fita ka tafi"


Kan gado ya fada sai lokacin ta kula ya chanja komai amma kunya ta hana tambayarsa ina ya ajiye wadanda ya cire.


"Kunyar fita nake yi kada a gane" ya tashi yana tafiya a gefenta "tayani dubawa tafiyata bata chanza ba ko"


Bubbuga kafa ta soma yi "Hammana bana so"


"Ba fa dake nake ba, nima bana so a gane ne kinsan manyan nan..."


Daga murya tayi cike da shagwaba ta ce "HAMMAAAA"


Yana kyakyata dariya ya fita. Kwandon abincin ya gani ya dauko ya dora a kan centre table sannan daga inda yake ya fada mata ta tabbatar ta ci kafin ya dawo.


Shiryawa tayi cikin wani hadadden lace tayi daurin da ya bayyana gashinta da tayi packing ta sako shi tsakiyar daurin sannan ta gaban ma ta ja dankwalin ya danyi baya. Fuskarta tasha kwalliya tayi kyau sosai. Sauri tayi ta gama saka awarwaron da ta dauko kalar kayan sannan ta fito falo ta dan karkade kura duk da babu. Turaren wuta ta saka a ko ina kamshi kuwa ya soma tashi kana tahowa bangaren za ka ji.


Fridge ta bude babu komai na kayan abinci sai ruwa da lemo kala kala. Da yake ana sanyi tunda suka zo Katsinan sau daya aka dauke wuta shima bata dade ba aka dawo da ita. Abincin da aka kawo ta bude, doya ce da aka soya da kwai a flask daya sai bread da farfesun kaza ya ji kayan kamshi. Ga kayan tea da ruwan zafi a flask. Kitchen ta kai ta ajiye don bata jin za ta iya cin komai duk yunwar da take fama da ita kuwa sai Hammanta ya dawo. 


Awwab kuwa da gaske sai da Bilal yayi da gaske su ka shiga falon Mami inda iyaye da kakanni ke zaune. Ana ta tsokanarsa sai su Bilal ke ramawa shi kam baki ya mutu Schatzi kadai yake tunani. Da su ka gama fita suka yi zuwa wurin Radhiya an gama saka kayayyakinsu a motocin da zasu bi.


Duk kunya ta isheta gashi babu su Rahima an barta ita kadai da manya kowa da abinda ya ke kara mata na nasiha. Kafin su fita Awwab ya dawo ya shiga daki sai gashi da envelop guda biyu. Daya ya bawa Hajjo dayan kuma ya baiwa Gwaggonta Mubaraka kowa su raba da abokan tafiyarsu. Shi kadai ya rakasu ta biyosu zuwa bakin kofar net din suna cewa ta koma ba sai ta fito ba.


Tunda Awwab ya shigo suka ci abinci tare suke makale da juna sallah kadai ke fitar dashi. Shagwaba kala kala yana gani tana kuma burge shi sai nan nan yake da ita kamar kwai. A haka ma baya samun yadda yake so sosai saboda kunyarsa da tayi mata yawa. Abincin rana ma kawo musu akayi daga ciki wannan karon Rahima ce ta kawo Awwab ya karba. Su Zahra da Fauziyya suka kafa naci kamar bala'i sai sun je wurin Radhiya.


 Mama tace "gulmammu wace acikinku bata ga wannan daren ba eyye. Zaku je ganin kwaf ku gani ko ta sauya tafiya ko..."


Mami sai da tayi dariya don ba karamar kunya suka ji ba har Fauziyyan kuwa. Zahra kamar ta kifa don sauri ta fice daga falon kafin a karasa barota. Mama kuwa sun kunnata bata iya yin shiru ba ta cigaba da sababi.


Kafin magariba ragowar tawagar Malamijo sun iso gidan saboda tafiya Nijar da safe. Salame ce akan gaba ko zama bata yi ba wai sai ta ga dakin amarya. Sakin baki tayi tana kallon kayan kudi sai da Mama taje da kanta ta yo waje da ita wai da bandaki zata shiga ta rage mara tayi alwala ko tunanin cewa bandakin daya ne kuma a cikin dakin baccinsu bata yi ba.


Sai da suka shiga ciki ne ta ga Halifa tare da Emzee da Ibrahim. Duka su ukun sun gaisheta babu yabo babu fallasa sai dai yanayin fuskar Emzee ya tsaya mata a rai fiye da zato da tsammaninta. Ganin Rahima ne ya mantar da ita komai abin mamaki ga ita kanta Rahiman Salame wani mugun tattali take yi mata kamar ta maidata ciki. Tunda Malamijo ya kirata yayi mata tas akan mutuwar idon Rahima tasha kuka kamar ba gobe. 


Ba komai ya tsaya mata a kahon zuciya ba irin yawaitar lokutan da Rahima ke durkusawa a gabanta tana rokon idan laifi tayi mata ta taimaka ta yafe mata. Yarinyar bata da matsala kuma bata santa ba. Burinta daya a duniya ta ga mahaifiyarta ta sakar mata fuska ta kaunaceta kamar kowa. Ita da ta iya zuwa wurin boka ta makanta Mairama da asiri yau an wayi gari 'yar cikinta ta gamu da lalurar da indai wani abu ya sake samun dayan idon mai lafiya to ta makance kenan fa. Tana ganin abubuwa amma ba ta iya rarrabesu. Ranar duk wani guntun rashin mutumci ma nemansa tayi ta rasa. Fatanta bai wuce ta kyautatawa Rahima ba ko ta yafe mata cikin sauki. Ga Halifa fuskarsa kullum a hade idan ya ganta musamman bayan matsalar idon kanwarsa. Baccin kirki kasawa tayi da ta duba hagu da dama sai kaji tana ina Rahimata?


A bangaren su Ummi ranar su ma suka wuce Nijar da Daada. Duk wani boyonta kallo daya Mammee tayi mata ta ja ta uwar daki tana murmushi.


"Mairama ciki gareki ko?" Tace da hausarta mara fita sosai.


Ummi taji kunya sai sunkuyar da kai kasa take. Mammee kuwa tsabar murna ta fito tana shelantawa. Ummi ta rufe kanta a daki ta kasa fita saboda yadda 'yan uwa suke ta murnar wannan rantsatssen rabo. Zayyan yayi ta dariya yace maganinta kenan tunda ta damu a boye gashi anyi mata mai gabadaya. Cikin 'yan uwansa mata harda mai tambayarta wata nawa ne saboda a fara shiri. Ta ga gata muraran don ko cikin fari ne a jikinta karshen abinda zasuyi mata kenan.

**********


Da daddare bayan sun gama dinner Radhiya tana wanke kayan da suka yi amfani dashi bata ji shigowar Awwab ba sai hannuwansa da suka bullo ta gefe da gefen cikinta ya riko plate din da take daurayewa suna yi tare. Jikinta tuni ya fara rawa saboda hatta soso sai ya sarke yatsunsu sun wanke abu tare dashi.


Kiss taji a wuyanta ta kusa sakin glass  cup din da suka gama daurayewa ya ce "hankali baby"


"Ai kaine"


"Ni sarkin laifi me kuma nayi"


Tsuke bakinta tayi ya cigaba da abinda yake yi yana birkita mata lissafi. A daddafe aka gama ta rufe ido kawai ta kwanto da kanta kan kirjinsa sosai na dan lokaci sai kuma ta juyo suna kallon juna "Chèri muje na hada maka kayan tafiya gobe"


"Kin hada naki ne?"


"Suna cikin akwatin da Zayyana ta kawo min dazu da ta kawo abincin dare"


Dakin su ka koma ya dauko wani akwati mai taya hudu daga kasa irin wanda duk nauyinsa mai ja baya ji saboda a tsaye yake rectangular. Na biyun karshen ya dauko ya nuna mata kayan da zaiyi amfani dasu ta fito dasu za ta zuba sai gani tayi ya zazzage nata kayan akan gado.


"Hammana ya ka juye kayan ko basu shiryu bane?"


A akwatin da take zuba nasa ya shiga jerawa "babu amfanin mu tafi da bags daban daban ne"


"Idan ba masaukinmu daya ba fa?"


Janyota yayi suka fada kan gadon yana zagaye fuskarta "nasa Yousuf ya kama mana hotel na kwana biyun da zamuyi"


Ai sai ta kasa hadiyar yawu don fargaba "duk kowa yana nan sai mu tafi hotel?"


"Yes...ta kare min Schatzi kema kin sani" ya cigaba da zana fuskarta da yatsansa "idan da nayi hakuri yanzu bazan iya ba...KEMA.KIN.SANI" ya fadesu dalla dalla kafin ya shiga nuna mata soyayyar da ko rabi rabin abinda ke ransa bai sauke mata ba.


Kayan da basu karasa hadawa ba kenan su da akwati daya da himilin kayansu dake zube a gefe suka kwana a kan gadon. Tun asuba da suka yi wanka ta karasa hada musu kayan ta gyara dakin ta wanke toilet. Basu bar komai a waje ba bedsheet din ma cirewa tayi ta dinke ta turasu cikin ledar da yake ciki da kyar saboda gudun kura.


Motoci harda wanda babu budget dasu mutane sun bi su Nijar ganin kwai da kwarkwata. Kamar kullum karamcin mutanen yana bawa Radhiya mamaki. Kudi ne dasu iyaye da kakanni amma akwai tarbiya da tsagwaron hadin kai a zuri'ar Alh Ghousman Agali. Gidan Alh Sidi Radhiya ta shiga saboda ance Umminta tana nan ta fada dakin da aka nuna mata da murnarta nan ta sami Emzee suna rigima da Mammee tana tura masa nonon rakumi ya damtse bakinsa yaki karba. Kan Ummi ta fada da murnarta Mammee ta sakarwa Emzee robar nonon ta tashi tana fada.


"Alheran yaushe zaki girma ne ni Aghaisha"


Turo baki tayi tana nanikar Ummin "me kuma nayi miki daga shigowata?"


"Dagata kada ki kassara min jika, maimakon ki tayamu tattalinta sai ki tsaya shirme?"


Ina kasa ta bude Mairama ta binne kanta. Emzee ya dago fuskarsa da nono ya watso masa ya kalleta sai wani nauyi ya bakunce shi ya dukar da kai. Radhiya kuwa ihun murna ta saki bilhakki ta sake rumgume Ummin tana murna.


"Wayyo ni, wayyo Umminmu Allah Yasa mace zaki haifa me kama dani" tace tana dariya.


Emzee ya kalli yadda take yi ya kalli Umminsu da kunyar da ta lullubeta sai ya tashi kawai yaja hannunta "Hamma Awwab yana kiranki muje na rakaki"


Zame hannunta tayi "kai Emzee yaushe kuka hadu?" Ta juya zata kuma zama "Ummi wane watttttt" keyyyy haka Emzee yayi waje da ita yaja kofar ya rufe.


Mammee tayi dariya tare da goge 'yar kwalla "sannu da kokari Mairama nasan irin halin Alheran. Haka yayata take kusan komai nata ta dauko. Zama da kishiya ne yasa tayi sanyi amma ko shi Mal. Muhammadu ai yayi fama da kiriniya tun farkon haduwarsu har auren."


Murmushi Ummi tayi tana sauraron labarin uwarmijinta da bata taba gani ba sai a hoto.


Wani falo Emzee ya kai Radhiya ya girgiza kai "ni da kin sani ni na fara fitowa yadda zan iya zaneki son rai. Sam baki kula da kunyar da Ummi take ji ba kike

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment