Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa yi amfani da ita "a'a , akwai babban dana Awwab shine nake son aurawa. Dreban jirgin sama ne yana bakin aiki shiyasa bamu zo tare ba."


"Lallai da gaske kake, amma bana so ka cuci yaronka da auren dole don a baka yarinya. Kasan yanayin zamani"


"Na sani amma ina da yakinin bazai bani kunya ba. Don Allah ku amince. Yanzu ku bari mu tafi dasu har Sakkwato saboda wancan wan Zayyan din. Sai kuma danginsu na uwa dake Nijar su ma ina so na hadasu kafin nan da lokacin bikin"


Tsakaninsu da Allah basu da niyar hana shi yaran ko kadan sai dai magana ta gaskiya sunyi masa haka ne domin kada nan gaba a raina musu. Da mutumcinsu da rufin asirinsu ya nemi daukar yaran ba wai talauci ko maula ya kaisu ba. Sun kara jinjinawa Marigayi  Zayyan domin wannan abu halinsa na kwarai ne ya kawo haka. Idan akwai wani abu na bajinta a rayuwar Mairama da Malamijo ya taba yi bai wuce aura mata dan kwarai irin albarka Zayyan Muhammad Tureta ba.


Innawuro da kanta ta fada musu su hada kaya zasu tafi tare suyi musu kwanaki don kowa ya sani hirar jiya da wadda aka sake dorawa yau tayi kadan ta cike gurbin shekarun da suka yi basa tare.


Radhiya sai murna nan da nan ta shiga jibgar kaya. Zainab ta ja ta gefe tace mata ta debi kamar biyar biyar nata da na Mairama.


"Ni fa na zaci kuna sonmu ne sosai baza ku so muyi kwana kadan ba mu dawo"


Tunda suka farka suke cin dariyar Radhiya ashe abin bai kare ba. 


"Mu kuwa muke son ku Radhiya, ko nima 'Yar sojan zan fara fada ne"z


Turo baki tayi "to meyasa kika ce na debi kayan 'yan kadan?"


"Kinga muna zuwa zan sa a kaiku wurin tela ayi muku dinkuna masu kyau. Ko da wadannan kayan zaki je bikin Zahra da Fauziyya da za'ayi karshen wata mai zuwa?"


Dariya Radhiya tayi kumatunta na dama ya lotsa. 


"To gidan wa zamu fara zuwa?"


"Gidana mana"


Mami da take tahowa daga bayansu ta rike baki "sannu maman yara, ashe wayo kike shirin yi min. To ban yarda ba Katsina zamu wuce"


Zainab ta mairaice "habaaa Mami, mu da zamu zo biki muyi kwanaki. Ki bari a ya da zango a Kano don Allah"


Mairama suka tambaya ina take son fara zuwa tayi murmushi "duk inda mota ta fara tsayawa zan sauka ne."


Ta kashe bakin nasu ta barsu da muhawararsu. Wayar Mami aka kira tana dubawa ta ga Awwab ne. Dariya tayi don jiya yayi ta kira bata sani ba. Tana dagawa a kunnen Mairama ta manna wayar.


Ko gaisuwa baiyi ba ya fara mita "Kai Mami tun jiya nake kira ki bani Ummi mu gaisa kinki dauka."


"To Allah Ya huci zuciyarka dan Ummi"


"La ila ha illallahu Ummi kece?" yace yana mai farincikin sake jin muryarta.


"Nice Awwab, yaya aiki?" 


"Lafiya kalau, kinga sun taho sun barni ko"


"Kayi hakuri, kana dawowa zaka ganmu in sha Allah"


"Ummi ina Alheran?" 


"Tana can wurinsu Zahra tana damunsu da surutu"


Dariya yayi yana imagining yaya ta koma yanzu "ta dena fada ko?"


"Awwab kenan baka manta halin nata ba ashe. Sai kazo zaka ganewa kanka."


"To Ummi don Allah kice Mami ta turo min numbar da zan rinka samunki. Ki gaishe min da Alheran"


Mami ta bawa wayar ya shiga tambayarta wai yaya girman Alheran yake yanzu don tsaraba yake son yi musu ita da Umminsa, Anti Zainab da Ibrahim.


"Kai kana fa da wani kanin Zayyan sunansa. Dama mun rabu Ummin taka ta kusa haihuwa"


Mamaki da jindadi suka baibaye shi nan yayi musu sallama zai fita. Suma aka gama shiri suka rankaya sai Katsinan Dikko.


**********


Mairama ta rasa wa zata goyi baya tsakanin Mami da Zainab. Gobe su Zainab zasu koma Kano bayan sun zo sunyi kwanaki uku a Katsina. Gidan kullum cikin hayaniya yake sun taru sun gama gyara shi an saka komai a muhallinsa. 


"Gaskiya Mami wannan fa amfani da girmanki kike yi kina yi min wayo. Ki bar min 'yan matan nan muje suyi sati. Aure fa zasu yi ina ni ina sake cewa su zo su kwanar min"


"Ai ban hanaki ba, Radhiya ce na hana"


"Ummin Awwab kice wani abu mana"


"Ni ban san yaushe kuka koma haka ba. Ina nan bacci zanyi wadda tayi nasara ta tasheni. Idan zama ne na zauna. Idan kuma Kano ce tayi kira a hada min kaya"


Dariya ta basu daga baya dai an yanke Zainab zata tafi da 'yan mata kuma mazan ma ko don Hadir dole su bita. Mairama ce zata rage tare da Mami.


Taron mata ne a kitchen su Zahra na girki Radhiya na koyo.


"Kunsan nima mai aikacin asibiti zan aura a Bauchi zan zauna. Gara na koya kada aji kunya wata rana"


Emzee da yake shan ruwa sai da ya kware da yaji me take cewa "Adda saurayi gareki bamu sani ba?"


Daure fuska tayi zai bata kunya a gaban mutane "fata nagari lamiri yaro...meye aibu don nayi fatan auren likita?"


Ibrahim ya rinka mata wani kallo kafin yasa dariya "na gama harbo jirgin naki. Wato dai wani ma aikacin asibiti kike so"


"Hhhhhh Adda Kawu Zakari kike so hala? Shi kadai na sani a asibiti"


Yadda tayi da fuska ya karasa fallasata. Suka taru ana tsokanarta, Emzee yace wannan labari duk rugar Barkindo sai ya tona.


Tun tana da bakin ramawa ta gaji ta watsar ta fita ta koma daki. Zayyana ta samu tana busar da gashinta da ta wanke da hand dryer. Sai ta dena fushin hankalinta yayi gaba.


"Shi kuma wannan ya sunansa Zayyana?"


"Hand dryer, kema ki wanke kanki sai na busar miki. Mai kitso zata zo an turota daga gidan Alh Baba"


Tsit Radhiya tayi kamar ruwa ya cinyeta. Zayyana tayi tayi tace bazata wanke ba kanta babu datti.


Da su Fauziyya suka shigo Zayyana ta fada musu. Radhiya ta galla mata harara "kinga ki fita idona, ina ruwanki don naki wankewa ba kaina bane?"


Zayyana ta mike a fusace ta fita "kuma sai na fadaki da Daddy"


"Sannu shasshaka uwar narkewa, shagwabar nan nima na iya. Kuma bazan wanke kan ba"


"Dama masu gashi bakwa son bude kai fa. Shiyasa kullum kina cikin hijabi" inji Fauziyya.


Zayyana kuwa tana kai karar Radhiya wurin Daddy ashe Mairama ta jiyo yana cewa a fada mata yace ta wanke shi zai bada kudin kitson. Idan kuma taki wankewa a gida zai bada kudin salon.


"Daddy fada fa zaka yi mata, kara na kawo"


"Yi hakuri Zayyana ai ko ni bazan taba Alheran ba."


Harda guntun hawayenta tace "kafi sonta akaina"


Ibrahim yana gefensu yace "Daddy ka barni na dan saita yarinyar nan mana."


"Taron dangi zaku yiwa auta. To a kira min Alheran yau sai an wanke kan nan"


Mairama tana ji ta tabo Mami "taimaka ki hana wankin kan nan wallahi idan suka bude mata kai gidan nan yau ba lafiya"


Mami ta tashi da sauri duk da bata san ko meye matsalar ba. Tana zuwa Zayyana ta kai rahoton Daddy. Dama su Zahra sun matsu su ga gashinta saboda na Mairama da suke gani mai tsaho sosai.


Duk sun dauki abin nata wasa suka danneta aka cire dankwalin suna cewa yau sai sun ga gashin da take boyewa.


**********


Shiri Awwab yake da sauri sauri yau kadai yake da damar fita yayi sayayyar da zaiyi gobe ya taho Nigeria. Tun dare yake tunanin me zai saya ya kai musu ya rasa. Ba sabawa yayi da irin wannan abubuwan na mata yayi ba. Dan tunani yayi ya dauki waya ya kira wadda yasan za ta bashi shawara mai kyau. Ringing biyu ta dauka kamar jira take dama. A shagwabe ta soma magana tana korafin rashin kiranta da yayi har na kwana biyu.


"Sorry my G aiki ne"


"Lokacin aiki daban nawa ma daban" Ghazalatu ta sake narke masa.


"Naji nayi laifi shiyasa ma ticket din Abuja na saya don na fara ganinki kafin na wuce gida"


Ihun da tayi sai da ya cire wayar daga kunnensa yana dariya. Yana matukar son Ghazalatu. Ita ta nemi su boye soyayyarsu ma sai ta gama degree dinta idan ba haka ba aure za'ayi mata a gida ta sani. Yanzu wata biyu da yin final exam bautar kasa take jira. Sun gama tsarinsu idan Awwab ya dawo zasu gabatarwa da iyayensu da abinda ke tsakaninsu.


Sun taba hira don ta dena fushin tunda taji zai taho washegari.


"G albishirinki"


"Goro kyakkyawa kamar Yayana"


"Su Mami sun je gidan Ummin nan nawa da nake baki labari"


Yadda taji yana murna dole ta taya shi ba don ta damu ba. Yayi ta fada mata ashe harda kani an yiwa Alheran.


"Na tayaka murna, zan so ganinta gaskiya"


"Ki bini Katsina mana idan na zo"


Dadi taji tayi saurin amincewa. Awwab bai kyaleta ba yace "kune sarakan tsaraba, me kike ganin zai dace da yarinya about 18 to 19 years"


"Friend kayi mace har kake fada min za kayi mata siyayya?" Tace cikin fushi da kishi.


"Nope, Alheran nake son sayawa wani abu"


Duk da haka ranta baiyi mata dadi ba amma bata son bata masa rai yanzu sai yace ya fasa tsayawa a Abujan.


"Ka saya mata takalmi, jaka, turare, kayan kwalliya da jewelleries"


Yaji kayan da yawa to amma so yake ya yi musu abin bajinta "thanks dear" yace da Ghazalatu kafin ya ajiye wayar.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Ruwa yaje ya watsawa fuskarsa yayi brush sannan ya dauko wani karamin hankici kamar tawul iya tafin hannunsa ya goge fuskar. Komawa yayi ya zauna yana jin kansa yayi wani fresh balle da ya tuna mutanen da zai gani. Kayataccen murmushi yayi shi kadai wata matashiya da suke zaune tare ta maida masa saboda ya dan fuskanceta ne yana laluben seat belt dinsa.


"Hi handsome" tace dashi da ingantaccen turancinta.


Sai da ya waiga bayansa ya tabbatar babu kowa sannan ya nuna kansa sai ta gyada kai.


"Hello" ya maida mata da kyar don baya son mace mara kamun kai. Da ace magana tayi masa kawai bazai damu ba. Amma idan kaji ana handsome ko beautiful ai kasan kwanan zancen.


"Kaima bahaushe ne ko?"


Baiyi mamakin da ta gane ba tunda suna zama ya soma waya bai dena ba sai da yaga jirgin ya fara tafiya.


"Kema haka ko?"


Murmushi tayi, a rayuwarta tana son namiji mai kaurin murya. Ba da karfi ya amsa mata ba amma amon muryar ya isa ya sanya mata da yawa muradin son kasancewa da mai ita musamman idan suka hado dashi. Wankan tarwada, dogo, hanci madaidaici da ya dace da kyakkyawar fuskarsa.


"Na kula baka ci komai ba tun tasowarmu."


Bai wani kare mata kallo ba yace "bana jin yunwa ne"


So take hirar ta tsawaita don tunda ta dora idanu a kansa zuciyarta bata kara samun sauki ba. Ta kula mutumin kamar yana da ji da kai sai dai kuma bazata bari shan kamshinsa ya hanata samun abinda take so ba. Dawowarta kenan daga Germany inda taje hutu wurin yayarta. Mahaifinta tsohon soja ne da ya tsunduma siyasa tun lokacin mulkin farar hula. Yanzu haka sanata ne da yake wakiltar mazabarsu a jihar Plateau.


"Suna na Arifah"


"Awwab"


Daga haka ya kafa waya a kunne don tuni sun sauka an bada damar kowa ya tashi. Cikin cabin crew din wata 'yar Nigeria da tasan Awwab tazo suna gaisawa da ya tashi zai dauki jakarsa.


"Captain yau fa ka yi mana wayo. Kasha bacci ka barmu da aiki"


Sai yanzu Arifah ta ga ya sake sakin fuska harda dariya "ki dauki hutu kema sai mu koma tare. Yanzu ina da wata guda na mantawa da kowa sai family dina"


'Yar hira suka taba sannan suka yi sallama. Awwab na fita Arifah ta bi bayan matar da suka gaisa mai suna Chisom ta roketa numbar wayarsa.


"Ki bishi ya baki da kansa, Captain Awwab baya son irin haka don an taba yi masa na gani"


Marairaicewa tayi tana fada mata yadda take son shi tare da rokon ta taimaka mata. Kudi ta dauko daga jakarta za ta mika mata Chisom ta bata rai "ba sai kin sayeni ba, Awwab is a nice man ga number dinsa ki gwada sa'arki"


Arifah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ta rubuce number din da ta karanto mata daga wayarta ta fita da sauri ko zata sake samunsa sai dai yayi mata nisa bata ma san ina yayi ba. Bata da damuwa tunda akwai numbar da zata same shi.


Yana fitowa waje hasken rana ya kwale a sama kamar ba shida ke neman yi ba. Jacket dinsa ya cire ya sakale a hannunsa ya jana jan akwatinsa.


Kamar ance ya kalli hagunsa suka hada ido da Ghazalatu. Taci kwalliya sosai don ta burge shi ta kuwa yi nasarar sanya shi murmushi. Daga ita sai dreba suka zo daukarsa kannenta suna makaranta.


"Yayana" tace da ya zagayo wurin motar tana murmushi.


"My G kinyi kyau fa"


"Ba wani nan, kai dai kawai ka dade baka ganni bane"


Gaisawa yayi da dreban ya shiga gaba ita kadai a baya suna ta hira. Ji take kamar ya dawo bayan motar su zauna tare. Ta rasa gane masa ne ana soyayya amma shi tamkar wanda ya taso a kauye. Baya irin yadda wayayyu suke yi. Ko gidansu taje hutu haka zata karaci zamanta hannu wannan bai san ya rike mata ba ko da su kadai suka fita. Yanzu wata hudu rabon da ya ganta amma simple hug ma su ji dumin juna ya gagara.


Waya ya rinka yi a rabin tafiyar saboda tazarar airport din da cikin gari. Mami ta fada masa su Alheran suna Kano amma Ummi tana tare dasu.


"In sha Allahu gobe asubanci zanyi zuwa Katsina. Sai na ga Ummi zanje wurinsu. Uhmm Mami tare zamu taho da Ghazalatu fa"


"Jiya Gambo ta fada min, sai kun iso. Jirgi zaku biyo?"


"Gamu nan dai sai abinda Mummy tace"


Sunyi sallama Ghazalatu ta rankwafa daidai kansa yana jin numfashinta a kunnuwansa da wuya.


"Daga kanki G" yace yana yin gaba da kansa saboda yadda yake ji.


Komawa tayi ta gyara zamanta "na daga shikenan, dama tambayarka zanyi ko kayi min tsaraba nima kamar kowa"


"Su waye kowa?"


"Yarinyar da ka tambayeni jiya me zaka saya mata"


"Allah Yasa ba kishi kike yi da yarinyar da ni dake duk bamu gani ba" yace yana dariya.


"Akwai dalilin da zanyi kishinta ne?"


"Ko kadan, please kada muyi abinda muka saba daga zuwana. A bar maganar haka ko."


Bata sake cewa komai ba har suka isa gida. Mummy Gambo tasa an hada masa kayan tarbar babban bako. Ranar da daddare da kansa ya sanar da ita abinda ke tsakaninsa da Ghazalatu. Gambo tayi murna sosai tana ta dokin maganar ta kai kunnen Hassana wato Mami. Abu ne da ya shafi dangi gabadaya ta bangarensu da bangaren mazajensu. Ga Awwab din da shiga rai dole taji dadin wannan hadi.


**********


Harun mahaifin Ghazalatu da ne ga Alh Baba. Babansu Mami kaninsa ne na uku yayin da baban Major ya kasance autansu. Harun ne ya biyawa Alhajinsu umara suka tafi tare. Mutumci, shakuwa da kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da Major tasa ya kaishi Germany gashi yanzu shi ma ya tsaya da kafarsa.


Major bashi da wani abokin shawara a dangi kamar Harun shiyasa a daren ranar da ya sanar dasu Mami game da hadin Awwab da Alheran ya kira shi ya fada masa.


"Gaskiya kayi tunani mai kyau ko babu komai yanzu zaka fi ji a ranka cewa ka rike iyalin bawan Allahn nan. Allah Ya gafarta masa Ya nuna mana lokacin"


"Amin Harun"


"Zan fara yiwa Alh Baba maganar yadda muna dawowa za'a je neman aure. Bikin su Zahra duka duka baifi wata daya ba kuma gashi kace gara a hada"


"Gara a hada din muma sai mu sami sauki"


"Hakane, ga 'yarka can Ghazalatu ta tsaya ruwan ido da ta fitar itama ba sai muyi komai mu gama lokaci guda ba"


"Barni da ita, gobe suna hanya ita da Awwab zan binciketa ko akwai wani"


Hirarsu suka yi irin na 'yan uwantaka suna kulla shawarwari game da yadda bikin zai kasance.


Washegari Awwab ya sauka a garin nasu cike da tsantsar farinciki ya rinka sallama a kofar dakin Mami. Tana sane wai sai ta ja masa rai taki amsawa.


"Mami manaaaa"


Dariya tayi "shigo dai ba don halinka ba"


Da saurinsa ya bude kofar idanunsa suka sauka akan Umminsa Mairama maman Alheran. Murmushi take ta yi masa daga inda take zaune wai wannan muryar Awwab ce. Shi kuwa wani dumi yaji a idonsa da sauri ya karasa gabanta ya riko duka hannayenta biyu ya dago kai yana kallon fuskarta.


"Ummi"


Da hannunta daya take bin fuskarsa tana shafawa "Awwab kaine ka zama babban mutum haka"


Mami tana gefe tana murmushin jindadi Ghazalatu kuma ta coge a bakin kofa.


"Ummina kina lafiya? Kin rinka tunawa dani kuwa" yace yana matse hannuwanta cikin nasa. Yau gashi da Umminsa abinda ya dade da cire rai saboda yadda shekaru suke ta yawaita.


Hawaye ta soma yi "ban taba mantawa daku ba Awwab. Ina ma zan iya ganinka da kyau in gani ko wannan tsayin kamar bulala ka dan cike shi da tsoka"


A razane ya kalli Mami sai ya ga tana hawaye. Hannunsa yasa yana yawo dashi a gaban idanunta ya ga ko gezau. Awwab kasa mallakar kansa yayi ya kifa kansa a cinyarta yana kuka.


"Kaji mutum kamar ba namiji ba, meye na kukan? Ai komai ya wuce da yardar Allah"


Hawaye yake da gaske yaji bazai iya zama ba ya tashi ya nufi inda yasan nan ne dakinsa. Mami tace da Mairama ta dena damuwa zai hakura kamar kowa.


Ghazalatu ko shiga dakin bata yi ba ranta ya baci da kukan da wannan makauniyar ta saka mata shi. A take taji wani haushin Mairama ya kamata. Dama akan wannan da kallo daya zai sanar da mutum daga kauye take yake ta damuwa harda kuka. 


"Ghazalatu shigo mana, kinga yayanki na kuka ko? Kada ki damu zanyi masa magana"


Ba yadda ta iya dole ta shiga tana nadamar tahowa don gidan har ya fice mata daga rai. Akwatinta ta tura gefe sai da Mami tace "ga Ummin Awwab ki gaisheta mana"


"Sannu"


"Yauwa sannu 'yata. Yaya gajiyar hanya?"


Mugun kallon da Mami ta watsa mata ya sa ta chanja salon gaisuwar tace "ina wuni" a dakile.


Ba jimawa Mairama ta shiga bandaki ai kuwa Mami rai a bace ta soma yiwa Ghazalatu fada.


"Kar ki yarda na sake ganin irin haka kina jina? Wannan matar da kike gani ba karamar daraja da kima gareta a wurinmu ba. Dangi kowa kokari yake ya tayamu karramata. Bazan lamuncewa dabi'ar banza ba kinzo kina wani cin magan"


Abinka da makaho kunne ya kara fikewa. Mairama tana jinsu tayi murmushi kawai. To dama yaushe zata yi tunanin kowa nasu zai sota. Ita ce fa wadda mahaifinta har yau bai taba bin sawunta ba sai dai ita har sau uku taje kuma tana aika masa da 'yan abinda ba'a rasawa.


"Kiyi hakuru gajiyar hanya ce" Ghazalatu tace da ta tuna Mami ce fa mahaifiyar Awwab.


"A dai gyara"


**********


Fauziyya da Zahra suna kallo a falo Zainab tana duba takardun asibitoci uku da likitann nan ya aiko mata. Ibrahim baya gidan yaje gaishe da kakaninsa Hadir kuwa bacci yake a daki.


Radhiya ce ta fito yau babu hijabi tana dan murmushi fuskarta tasha kwalliua harda janbaki. Fauziyya da Zahra suka shiga gyara dankwalayensu. Zayyana daga shiga deban abinci a kitchen ta kasa fitowa tunda taji muryar Radhiya tana cewa.


"Ha mutum ya fito yasha iskar Allah."


Tana zama su Zahra suka mike, Zainab ta kwashe da dariya. Radhiya ta zama horror tunda tace zata yi musu balotelli. Jiya a gabanta Ibrahim ya nuna musu hoton Mario Balotelli wani dan ball baki na kasar Italy wanda yake kwashe kansa hagu da dama ya bar tsoro guda a tsakiya tun daga gaba har keya.


A karkace ta kallesu "tashi kuma zaku yi daga zamana?" 


"Ni bacci nake ji" cewar Fauziyya


"Fitsari zanyi ni kuma" Zahra tace tana matsawa gefe.


"To sai kun dawo, gumi ne ya dameni yau na saka lasi" kawai sai ta tuge dankwalinta rantal ya bayyana.


Wata irin dariya suka kwashe da ita har Zayyana dake kofar kitchen. Zainab na dago kai ta mayar dashi kan takardu kafin ta soma  dariya itama. Radhiya ta bata rai "ayi dariya da kyau naje soja na dawo. Kuma na dena daura dankwali iska zan rinka sha"


"Ki rufa mana asiri don Allah ki rufe" Zahra tace idonta harda hawayen ganin wannan gashi na Radhiya tsilli tsilli.


"Allah bazan rufe ba iska nazo sha."


Kyalesu tayi suka sha dariyarsu tana cewa su kiyaye kada tayi sanadin da zaa kai amare da kwalkwal. Daga nan hira ta kaure don daga Zahran har Fauziyya basu da girman kai duk da ba sa'arsu bace. Suna cikin hira ta soma gyangyadi Zainab tace ta koma daki ta soma musu irin na masu magagi wai ba bacci take ba. Kafin la'asar ta bingire akan doguwar kujera abinta. Ana kiran sallah duka suka watse sai Zayyana.


Ta wayar Fauziyya Awwab ya kira yace yana kofar gida don dreban Harun ne ya kawo shi. Zayyana da ta amsa wayar taje ta bude masa gate tana murnar ganinsa.


Suna shigowa falo idanunsa suka gane masa Radhiya. Kanta yake iya gani sai rabin jikinta ta rufa dankwalinta daga kasa kuma fuskarta jikin kujera take kallo. Ya dai tabbatar kayan mata ne a jikin mai wannan kan a sanyaye ya karasa shigowa Zainab tana turo Hadir ya kallesu da tausayawa. Da guda daya tilo da suka haifa ashe dan daudu ne jiya da Mami da Ummi suna bashi labarin komai yana kwalla basu hada masa da wannan ba.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Iyakar karfinta tasa suna jan hijabin nata su ma suna ja. Mami na isowa tace su dagata amma an makara don Zahra tayi nasarar cire dankwalin.


Emzee da Ibrahim suna bakin kofa don sun jiyo hayaniya daga dakin. Rasa me bakin magana akayi harda Mami kuwa. Zainab ce ta kawo Mairama dakin, tunda taji shiru tasan aikin gama ya gama.


Zayyana ce ta fara dariya gashi ya  soma lekowa amma saboda makero baifi a kirga ba sai wani uban fari fari kamar amosani kamar kora. Kullum tana shafa mai idan tayi wanka amma yau saboda da mutane a dakin ta hakura ta daure kayanta.


Kowa ta kalla gimtse dariya yake ta harzuka sosai tayi kan Zahra tana ihu "wallahi sai na rama"


"KE! Samu wuri ki zauna kada naji kinyi fada da kowa."


Kuka ta fashe dashi da karfi "wallahi Ummi kada ki cuceni ki barni na rama."


"Zahra bata dankwalinta kafin na saba muku. Wane irin abu ne haka da girmanku saboda Allah." Mami ta soma fada.


Jefa mata dankwalin Zahra tayi don yadda take kallonta kamar kura ta ga nama bazata so hannunsu ya gogi na juna ba. 


Jikinsu sai yayi sanyi saboda kukan da take yi ta dauki dankwalinta ta kulle kan sannan ta mayar da hijabinta. Zainab da Mami na bata hakuri taki kula kowa sai sautin kuka da take karawa. Mairama tace su kyaleta ba shiru zata yi ba. Kowa ya fita daga dakin tana zaune tana kukanta dole Mami taje ta fadawa Major.


"A kirawo min ita"


Zahra ta kalli Fauziyya, a tsorace tace "ba dai ni ba, kece babba kuma ke kika bude mata kan"


"Zayyana...." Zahra ta soma kira ta bari saboda kyabe fuskar da ta ga tayi ta koma gefen Major tana cewa 


"Daddy kace bazani ba" 


"Mazaje waye zai kira min 'yata?" Yace da Ibrahim da Emzee kamar yana rokonsu.


Ibrahim ne ya tashi, Emzee kamar ruwa ya cinye shi. Yana zuwa ya sameta ta gama hada kayanta a cikin jakar da tazo da ita tana bakin kofa zata fito.


"Dariya ka dawo yi?"


"Daddy ne yake kiranki"


Gani tayi ya tsaya kallonta yaki tafiya ta zaro masa idanu "in sake bude maka ka gani da kyau ne?"


Murmushi yayi mata kawai don idan ya sake ya bude baki sai ta saka shi dariyar da baiyi niyya ba. Sai yanzu ya gane meyasa kan nata yake kullum a daure kamar mai tallan magani.


Da jakarta a hannu ta shiga su Zahra suka fara kuskus. Daddy ya gani sai ya shareta  "waye ya saka ki kuka?"


Rage tsayi tayi bakin nan a gaba kowa ya ganta yasan an tabota karshe "Daddy na san komai fa, kaine da kanka ka turo Zayyana su gane min aski na"


Kafin su shigo sai da Mami ta roke shi akan ya taimaka kada yayi dariya. An san soja da dakiya, amma a cikin iyalansu, iyalan ma na Zayyanunsa mantawa yake ya taba zama soja. Ya fi fahimtar ya sake tare dasu ya nuna musu shi uba ne a garesu domin kada a sami wani shamaki tsakaninsu.


"Cewa nayi ace ki wanke kanki fa 'Yar soja uwar sojoji"


Sai da tayi murmushin jindadin kirarin ta sake daurewa "a bani kudin mota in tafi gida ko kuma a barni na rama"


"Radhiya kiyi hakuri da kaina zanyi punishing dinsu. Amma ki bar

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment