Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba dama"


Hannu tasa ta share hawayenta bayan ta gama rarrashin kanta ta shiga gidan da sallama. A can mota kuwa Awwab da Ghazalatu an bude sabon shafi sai dai a wurinsa babu wannan dokin jikinsa kamar wanda aka yiwa duka haka yake ji. Su ma tana shiga suna shigowa.


Tabarmi ne aka shimfida daga can gefe inda inuwa take don dakunan gidan babu mai girman da zasu zauna a wadace da su da kuma tawagar Malamijo da suka zo kallon 'yan gayu. Akan abin sallah yake zaune ya mike kafafu dawowarsu kenan daga asibiti an zuke fitsarin an hadosu da tulin magunguna. Sallamar baki yasa aka kawo masa babbar riga ya saka ya rufe kasusuwan kirjinsa.


Radhiya ya hango zai fara tsokanarta sai da ta matso ya kula idanunta sunyi ja sosai.


"Kukan me kika yi ke kuma?"


Kamshin turaren Awwab kawai ta ji a bayanta ta gane ya shigo shima. Gashi ana ta kallonta idanunta sunyi ja haka saman hancinta. 


"Ji nayi kamar ana kuka ance ka tafi shine na fara nawa nima. Ashe ashe kana nan."


"Kaniyarki" Malamijo yace ya yi mata dakuwa "Mairama ki rasa da wa zaki zo gidan nan sai da wannan aljanar 'yar taki, ko wancan hutun da kika turo su ni banji dadin zama da ita ba. Sau biyu tana yi min barna a gona"


Awwab sam hankalinsa kasa kwanciya yayi da aka ce tayi kuka. Bayan ya gaisa da mutanen gidan da suke wurin fuskarta ya rinka lalube yana son hada ido da ita amma fafur taki. Baya so ya zama sanadin kukanta ko kadan. Muryarta ya tsinkaya tana cewa "wai me ya sameka ne Malamijo, ciwon me kake?"


Hajjo ta soma dariya za ta tona masa asiri a gaban 'yan gayu yayi saurin cewa "zazzabi ne mai zafi ya damkeni kamar bazan kai labari ba. Ai naci wahala ba kadan ba. Yanzu ma daga asibiti nake"


Sannu da adduar samun sauki suka yi masa. Yadikko ta soma cigiyar Emzee shine Mairama tace ya tafi sayen gurasa da tsire wai yana sha'awa. Hakanan Malamijo ya tsargu ya daure ya cije yace a kira guda cikin samarin gidan ya yanka kaji uku ayi musu farfesu.


Mami ce tace " Kada ka damu Baba muna sallah zamu juya akwai tafiya a gabanmu. Ibrahim idan Karami ya dawo ku shigo da kayan nan ciki"


Nan fa hankalinsa ya tattara yayi waje. Ba dadewa Emzee ya dawo da ledoji a hannu. Ya sayo gurasar da nama a wadace harda lemuka irin su cway, lacasera da maltina masu sanyi. Ashe 'yan matan yunwa suke ji. Kafin Hajjo ta gama dafa shinkafar da Malamijo ya aunar mata bayan ya koma daki daga buhu daya cikin wanda su Mami suka kawo don kwarewa a tsiya har sun koshi.


Sallah kasaru suka gabatar azahar da la'asar sannan suka ce zasu koma. Idan sun isa da wuri ma Katsina zasu wuce kawai saboda kada su yiwa Zainab yawa a gida.


Da sauri Radhiya ta dago kai rike da gurasa a hannu sai lokacin take ci ta kalli Awwab. Hada ido su ka yi shima tun dazu ita yake kallo. Kin kula shi da take yi shine yake damunsa. Kwana biyar Mairama tace zasuyi a nan sannan su wuce Rugar Barkindo. Sai bikin su Zahra ya rage sati daya zasu koma Katsina. 


"Wannan dan samarin baici komai ba zaku tafi. Radhiya ko saurayinki ne kika kawo baki gabatar min dashi ba?"

Malamijo yace yana kallon Awwab. Yaron da gani akwai maiko maiko zai so ya auri jikar tasa.


Murguda baki tayi da ta ga Ghazalatu ta sha kunu "idan ma kishi kake yi to ka dena Malamijo, ka jira sai na sami mai matsayi daidai da naka amma ba wannan ba."


Yanzu ya gano bakin zaren. Da gaske maganarsa ce ta bata mata rai harda kuka don sai da ya gano ja da kankancewar da idanun nata suka yi. Da ya juya kalaman a bakinsu sai ya ga rashin dacewarsu a dazun.


Mami haka nan ta fara zargin ko Awwab din ya yiwa Radhiya wani abin ne ya bata mata rai. Bazasu so ayi aure basa son juna ba. 'Yar dabarar manya ta kirkiro wadda bata baude da yanayin Awwab din ba a yadda ta san shi "haka yake baya son cin abinci, ga tuki a gabansa mai nisa"


"Ke zuba masa abinci ki kai masa wajen soro tunda babu kowa a wurin. Kila kunya yake ji ko dan Ummi" Mairama tace tana murmushi.


Hakan yayi masa daidai har ransa. Abincin da Hajjo ta dafa da wanda Emzee ya siyo ta zuba masa a plates biyu ta dora akan tray tayi gaba batare da tayi masa magana ba. Ghazalatu kamar ta bisu sai ta tuna bayan fitarta dazu daga motar yadda ya jaddada mata son da yake mata. Tayi ta gama iyayinta ta koma kauyensu kowa ma ya huta.


Wurin yana da fadi daga kan tudun dazu ta ajiye abincin ta koma daukar tabarma suka yi kicibus. Wai sai tayi masa murmushi a zuwan komai lafiya shima ya maida mata. Da ta kawo tabarmar yana zaune a gefen abincin ta shimfida ta sauke masa a kasa.


"Hamma sauko kaci kada kuyi dare"


Kura mata idanu yayi sai da taji kallon ya hanata motsi sannan ya sauko ya zauna a kan tabarmar ya tankwashe kafafunsa.


"Zauna mu ci"


"Na koshi"


"Ban isa da ke ba ko?" Taji yace a hankali yana daukar cokali.


Bata so yana magana irin haka sai ta taji zuciyarta tayi wani iri. Zama tayi a daya bangaren tray din ta tankwashe kafa yadda yayi. Cokali daya ne a ciki ya debi abincin yaci ya mika mata. Satar kallonsa tayi ya dage mata gira da ido yayi mata nuni da taci. Sai da ta sauke numfashi tana kunyar wannan abu ta rufe ido taci da cokalin da ya fito daga bakin Hamma Awwab.


Karba yayi ya sake ci ya kuma mika mata. Za tayi magana yasa hannunsa a kan lebensa sai ta hakura. Duk loma daya sai ya mika mata har suka cinye abincin gabadaya. 


"Wannan gurasar dai bani da inda zan cusa ta ki mayar ciki"


Dama ta kagu ta tashi ta kinkimi tray din za ta gudu ya danne gefensa.


"Ban gama magana ba"


Komawa tayi ta zauna ba don taso ba taji yace "I am sorry Alheran. Nazo ina ta yi miki laifi ba da niyya ba"


Sake karyar mata da zuciya maganarsa tayi. Shi kam bashi da girman kai. Wai ita dinnan kanwar bayansa 'yar kauye yake bawa hakuri.


"An daure harshen ne? Talk"


Rufe ido tayi sai hawaye sharrr kamar famfo. Ta rasa gane irin emotions din da suke yawo a zuciyarta yau dinnan.


Hankali a tashe yace "Ya Allah, me nayi miki kuma?" 


"Nima ban sani ba Hamma" tace tana kara fashewa da wani kukan. Me ya sami zuciyarta ne a cikin kankanin lokaci? Rabonta da kuka tun farkon zuwan su Mami rugarsu da ana bada labarin abinda kawunsu Maikudi yayi.


Kuka tayi harda shessheka Awwab bai hanata ba har ta gama don kanta ya bata tissue irin ya ledar nan karama ta goge idanunta.


"Feeling better?" 


Ta gyada kai tana kallon kwanukan gabanta.


"Good, yanzu ki fada min tsakani da Allah me ya same ki? Nine ko?"


Rasa me za ta ce masa tayi ta kare da cewa "ba kaine kake murna zaka tafi ba"


"Ke kuma ba kya so na tafi?"


Kada fa ya fassarata ta soma tunani "dena fada kada budurwarka taji. Duk baka tambayeni labarin komai nawa ba zaka koma kila bazan kuma ganinka ba sai an dade. Shine naji raina ya baci"


"Sai nake ji kamar dai maganata ta dazu ce ta baki haushi. Amma nima bana son tafiyar ko sabawa bamu gama yi ba ko" yayi yar dariya.


"Eh, ko askina ban fada maka me yasa akayi min ba"


Sai da yayi dariya sosai yace "an gaya miki ni bana tsoron kiyi min balotellin ne? Ina sane naki tambaya kada na janyowa kaina"


"Ashe kai matsoraci ne" ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.


Sweet ya dauko daga aljihunsa irin mai mint dinnan ya bare ya jefa a baki yana dariyar matsoracin da ta kira shi. 


"Dazu ka raba abin leda baka bani ba yanzu ma a gabana ka shanye alawar? Kuma nice karama ni ya kamata ka bawa"


"Sorry gashi in kina so" ya cirota daga bakinsa dama niyyarsa kenan.


Wata zuciyar tana kwabarta wata tana ingizata har ta mika hannu tayi saurin janyewa "wayo zaka yi min, na tuna me kace dazu"


"Ke dai kina kyankyamin abin bakina kawai"


"Haba dai..." bata rufe bakin ba ya saka mata sauran da ya rage har hannunsa yana taba lebenta. Saurin tashi tsaye yayi ita kuwa ta rasa me zata yi ma.


"Ki rage min kinga kadan na sha"


Lumshe ido tayi tana tsotsar alawar yana kallon yadda bakinta yake motsawa yana jin kamar ya taya shi. Girgiza kai yayi da sauri. Lafiyata kalau kuwa ya tambayi kansa.


"Ahhhh" Radhiya tace ta bude bakin ta mike tsaye yadda zai gano cikin bakin nata sosai. Ta shanye alawar saura yar kadan.


"Cewa nayi ki rage min fa"


"Nima bata isheni ba. Babu kari?"


"Zan gamu dake ne, muje ciki su fito bana jin zamu iya wucewa a yau sai dai mu kwana a Kano" tafiya ciki ya soma yi.


"Hamma gashi" ya juyo ta miko masa yar karamar sweet din ya karba yana kallon cikin kwayar idonunta ya saka a bakinsa. Bata sani ba ko shima yaji amma ita dai wani abu ne ya zarga mata har kasan zuciyarta.














 
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Basu dade da fita ba Daddy ya kira Mami yana tambayarta hanya da mai jiki, su ma shigarsu Sakkwato kenan. Ya bukaci gaisawa da Malamijo wanda hakan ba karamin dadi yayi masa ba. Da Mami ta sake karba ne yake bata shawarar me zai hana su kwana washegari su kama hanya da wuri. Banda dare da ya tabbatar sai sunyi a hanya yana ganin ko babu komai itama Mairama sun mutunta ta. Zata ji dadi su kwana yadda itama taje nasu gidajen ta kwana. Mami dama harda tsoron dora musu nauyi da take yi yace duka babu komai kwana daya dai ta sanar da Ummin Awwab yasan zata yi farinciki.


"Ummi yanzu Daddy yake cewa gara mu kwana saboda dare"


Murmushi Mairama tayi da ya nuna jindadinta kamar yadda Major yayi hasashe. Baza a rasa dakunan da za'a sauke su ba. Abinci kuwa bata da matsala tunda da 'yan kudadenta. Zata bayar ne a siyo abinda zata fita kunyarsu.


"Wannan murmushi Ummi to me yasa baki fada min kina so mu kwana ba? Duk daya muke fa"


"Nasan kinyi haka ne don kada ki dora min nauyi. Amma zanfi so ku kwana ko daya ne a gidan da bani da tamkarsa"


Yadikko da Hajjo ta sanarwa Malamijo na ji yasa aka taso kannenta ya bada umarnin a gyara dakuna biyu daya domin mazan dayan kuma na 'yan mata. Ita Hajjo tunda ita ke da girki 'yarta zata gyarawa Mairama da Mami nata dakin. Baki masu alheri irin wannan karramasu ya zama wajibi a wurin Malamijo ko don ya kara samun wani ihsanin kafin su tafi.


"Karami jeka ka fadawa yayanku ya nutsu yaci abincin tunda babu tafiyar"


**********

Kallon kallo suke yi daga bayan Awwab da ya juyawa kofa suka ji ana gyaran murya. Ba kowa bane illa Emzee wanda ya gama ganin musayar sweet. Shi ba abin ya juya ko yace bai gani ba. Murmushi ne ya subuce masa da suka hada ido da Awwab.


"Dama Mami tace na fada maka yanzu Daddy ya kira yace ku hakura da bin hanya yamma tayi"


"Bari naje na sameta, ko Kano muka koma mun rage wani abin"


Tafiya yayi Radhiya ta tsaya dauko kwanukan da tabarma. Emzee ya karbi tray din tana nade tabarmar yace "Allah Sarki bawan Allah"


"Wa?"


"Dr Kawu Zakari mana"


Gabadaya daburcewa tayi "me...me..ya same shi?"


Dariyar da bai fiye yi ba ya yi mata ganin duk ta rude irin na marasa gaskiya "babu komai na tuna irin son da kike yi masa ne a raina nace dan gata. Idan ku ka yi aure alawa zaki rinka bashi"


Borin kunya ya kamata ta fara fadan da babu gaira babu dalili. Dariya ta sake bawa Emzee ya sakalo hannunsa a wuyanta "kinga dai bance komai ba, idan kika tona kanki ba ruwana"


Baki ta bude tana harararsa, wai me yake nufi ne. 


Aljihunsa ya rinka lalubawa ya zazzagesu yana cewa "rufe bakin mai alawar ya shiga ciki ni kuma ko kuli babu a jikina"


"Kwana biyu jikinka bai karbi sako ba shiyasa kake damuna" tace tana daga hannu za ta kai masa duka ya gudu tana jiyo dariyarsa.


Har yanzu babu wanda ya tashi daga tsakar gidan. Awwab ta nemo da ido ya dan durkusa a gaban Mami yana rokonta ko Kano ne su tafi. Mairama tana jinsa tace wato bazai iya kwanan kauye ba.


"Ba haka bane Ummi, bana so ki bawa kanki wahala ne kawai"


"Wace wahala ga kannenka ko ta ina, yanzu Karami zai gyara muku dakin da zaku kwana. Yau kowa zai dana kauyenmu"


"Ko don kada kice ina gudun kauye dole na kwana."


Matsawa yayi gefen Malamijo da yake ta bawa Zayyana da Ibrahim labaran kiriniyar Radhiya. Awwab yaso su tafi da gaske. Ya rasa gane kansa da zuciyarsa akan kanwar tasa. Zuciyarsa ta gaza nutsuwa balle ya fahimci me yake damunsa. Har yanzu dandanon sweet din da ta bashi yake ji a bakinsa na daban da lokacin da ya fara sha. Shi kadai yake murmushi yana satar kallonta tana wurin wanke-wanke tana magana da karamar Antinta cikin amaren da za'ayi bikinsu su hudu. Hajjo ta yiwa Mami da 'yan matan tayin ganin lefen kannen Mairama. A lokacin Mairama tace tunda bikin haka yake kurkusa gaskiya ta fasa komawa Rugar Barkindo. Zata jira ayi bikin a gama nan da kwanaki sha biyu sai su wuce Katsina kuma. Idan an gama biki kaf su tattara su tafi. Tasan Innawuro da matan Baffaninta ma zasu zo idan an aika musu. Dakin Hajjo suka tafi su duka kafin a gama gyara inda zasu kwana. Radhiya ta biyo bayansu zata shiga kenan Malamijo ya kwalawa Emzee da ya zage abinsa yana shara kira yana hura hanci shi mai arziki.


"Zayyanu yaka zo, bar wannan aikin zan sa a karasa. Ka raka wannan samarin gonata su gani" 


Da baya da baya Radhiya ta dawo "ai wallahi tunda naji muma sai munje. Bari naje na kira su Adda Zahra"


"Ban gayyaceki ba fitinanniya, idan sai kinje ne na fasa kowa ya shiga daki ya kwanta dama kun kwaso gajiya"


"Ni din? Ashe yau rabon kosashiyar saniya za ta kasa ne"


"Buhun ubaki mai idanu a tsakar ka, Qur'anin Allah kika yi min barna a gona sai an biyani" yunkurin tashi yake don ya riga yasan hali. Muddin tace zata yi to da wahala idan basu dawo gida da nama ba. Shi yadda yake tsoronta ma yana tsammanin da kanta zata iya yiwa shanunsa rauni kawai don a yanka.


Awwab da Ibrahim sai dariya suke yadda ta dage sai taje Malamijo ma ya dage.


"Malamijo da dai ka kyaleta tunda kasan ko ka hana sai taje" Emzee yace da sigar laluma.


Malamijo ya tamke fuska yana kallon Awwab "yaro ga amana, idan kuka je ko kaza ce ta sami matsala sai kun biyani."


"An gama Malamijo" Awwab yace yana murmushi. Tsohon burge shi yake kamar yadda Zayyan Tureta yaji farkon haduwarsu.


"Ni nafi zargin ita wannan ce ya kamata ta fito a namijin shi kuma salihin nan ya fito a mace sai aka sami mushkila. Yasin duk mai auren 'Yar soja sai yayi shiri da gaske"


Murmushin Emzee ya fadada ya saci kallon Awwab da duk motsin Radhiya sai ya kalleta a ransa fata kawai yake ya ga ranar da za'a ce sunyi aure. 


"Kirawo su idan basu gaji ba" Malamijo yace yana binta da harara. Fatansa Allah Yasa suje su dawo lafiya kada yaji labarin da zuciyarsa bazata iya dauka ba.


Da murnarta taje ta fada musu zasu je gonar Malamijo ganin dabbabinsa. Ghazalatu tana kashingide akan gadon Hajjo tace ita babu inda zata je. Gabadaya ranta ya gama baci da kwanan garin nan. Kana ganin gidan duk girmansa kasan gidan talakawa ne sai wani so ake a burge su. Tana ji lokacin da Yadikko ta tunawa Malamijo kajin da ya bayar ya hadiyi yawu don yayi zaton kajinsa sun sha kafin a sake shawarar kwana. Ba don yaso ba yace a dauka ayi miyar tuwon dare dasu.


Zayyana da Fauziyya tuni suka tashi aka gyara fuska suna murna zasu je. Zahra ma tace bazata iya zuwa ba kan ta ya soma ciwo. Ita dama bata da juriyar tafiyar mota daga amai sai ciwon kai.


Zasu fita Mairama ta dakatar da Radhiya "don Allah kada kije ki yiwa Malamijo barna kinji ko, kuma ana magariba ku dawo"


Dariyar shakiyanci tayi tana kissima me zata yi don babu yadda za'ayi taje ta fito sikau basu ci nama ba. Jama'ar gidan dashi kansa mara lafiyan da amarensa da ta gani kowa yana bukatar protein. 


"Haka fa ya cewa Hamma wai ga amanata kada na taba komai. Ni yanzu Ummi da girmana me zanje in taba a gonar nan?"


Da yake Mami ta san waye Malamijo yanzu tun bayan labarin gidan da Mairama ta basu ga kuma sanin da ta yiwa 'yar tata sai ta rinka dariya ita ma. Ghazalatu na jin Radhiya tace Hamma ta diro daga kan gadon tana cewa ita ma zata bisu.


Radhiya ta tabe baki bata manta me tayi mata ba dazu "ba yanzu kika ce bazaki ba?"


"Iska nake son sha" tace fuska ba annuri. Indai Awwab zaije kuma Radhiya ma zata dole ne ta bisu. Bata son wannan likewar da take yi masa daga gani irin abin nan ne na 'yan kauye an ga dan birni ana so a cusa kai ko Allah zaisa yace yana so.


Emzee yace gonar a bayan gari take da 'yar tafiya shiyasa Awwab yace gara su je a mota tunda yamma tayi. Da sauri sauri Ghazalatu ta riga kowa fitowa. Awwab na bude mazaunin dreba lock din ko ina ya bude ta kama kofar gaban mota ta bude ta shige kamar wadda take tsere da wani. Burinta ta riga Radhiya shiga. Awwab na zaunawa ta kalle shi tana murmushi ya daure ya mayar mata. Ji yayi yafi son Alheran dinsa ta zauna ko da irin zaman dazu ne ta juya masa baya.


Duk abinda Ghazalatu tayi na saurin zama a gaban Radhiya ta gani. To dama ita dinma yanzu bata ra'ayin gaban. Bata son zama kusa da Awwab din saboda yadda yake sawa tajita kamar ba ita ba. 


Kusa da Zayyana ta zauna a tsakiya tana ta zuba surutu. Awwab ya kasa hakuri ya gyara madubin motar yadda zai rinka ganinta da kyau. Yana saita madubin suna hada ido da Emzee. Hade girar sama da kasa yayi da Emzee ya dago masa hannu yana murmushin tsokana. Kansa ya janye gefe Awwab ya hango Radhiya tana nunawa Zayyana makarantar da tayi primary.


"Ranar hutun da muka gama primary 5 muka yi dambe da Danmama a wurin bishiyar can, ko me yake yi yanzu oho"


"Damben fada kika yi dashi?" Zayyana tace da mamaki. 


"Ke baki ji wulakancin da yayi min bane. Malamijo suke zagi ni kuwa na nuna musu matsayinsu."


"Zan so sake ganin Danmama, yanzu sai dai muyi gaisuwar mutumci idan an hadu"


Wani azababben kishi ne ya turnuke Awwab "duk yawan 'yan uwanki basu ishe ki ba sai kin hada da abokin fadanki? Wai shin ke namiji ce ne ma kike fada da maza?"


Ita me tace da zai rinka yi mata fada daga labari. Kallonta yayi ta madubin ta murtuke fuska "kuma idan na zama soja ....."


"Stop dreaming babu inda zaki. Idan bazaki yi karatu irin na kowa ba sai ki hakura"


A duniya ita tana da burin da ya wuce zama soja ne? Duk mai son hanata bai nemi zaman lafiya ba. Ko da kuwa Hamma Awwab din da take ji dashi ne. A take ta bata rai "ai dai Daddy yace zai nema min"


"To zamu gani" yace yana shiga kwanar da Emzee ya nuna masa.


Fauziyya tace "Hamma ka barta tayi kawai mu sami soja mace. Ni har hangota nake yi. Kasan Radhiya bata daukar raini kowa zai shiga hankalinsa" 


"Idan kin haifi taki 'yar sai ki turata amma wannan dai na gama magana"


"Kai Hamma kada fa mu ganku a rana wannan kanwar taka bata iya fada ba. Sai ku kwana kuna yi"


Bai ce komai ba yayi parking a gefen gonar. Tun daga inda suke suna iya hango shanu da tumaki. Malamijo fa akwai kudi arziki ne kawai babu don bashi da zuciyar fitar da kudinsa a mora. Kowa ya fita saura Ghazalatu da Awwab a motar. Gani yayi bata da niyar fita ya koma ya zauna yana tambayarta me taki fita.


"Yayana kaki zama muyi hira, nayi maka wani abu ne?" Ta marairaice masa.


Tausayinta yaji domin daga baro Abuja zuwa Katsina, Kano da Sumaila duka tayi dominsa ne.


"Kiyi hakuri, kinga ban samu na zauna bane"


"Amma ka sami lokacin hira da kanwarka ko?" Tace cikin yanayin da ke nuna tsantsar kishi.


"Me yasa Alheran ta tsaya miki a rai ne?"


"Shakuwar taku tayi yawa Yayana, bana son abin ya koma wanda bazai mana dadi ba a gaba"


"Idan zakiyi min adalci Ghazalatu kin sani cewa duk wanda yasanni da su Mami to dole ya taba jin zancen Daddyn Alheran, Umminta da ita kanta ko da sau daya ne. Family dinsu suna da matukar daraja a idanun iyayena" tunawa yayi da zancen rasuwar Zayyan da Daddy yayi masa a daren da zai taho Kano da nanata masa ko bayan ransa ya taya shi rikon amanar iyalinsa. A daren sai da ya zubar da hawaye. Yayi zaton idan ya ga Radhiya kawai shakuwarsu ta baya zai tuna kila ya ga ma ta sauya daga sanin da yayi mata. Sai ya zamana abin ba haka yake ba. Ganin kwana daya Alheran nema take ta shige kowane bangare na jikinsa.


"Tunanin me kake yi ne?"


"Fito muje ba dadewa zamuyi ba" yace yana fita.


Dole tabi bayansa a ran ta tana jin dole ne ma suna komawa ya sanar da nasa iyayen idan ma kudin aure ko saka rana za'ayi duka ayi da wuri kafin abin yazo yafi karfinta.


Yawo su Radhiya ke yi sosai ga masu kiwon dabbobin suna ta bin bayansu ana musu karin bayani. Wurin wata saniya suka je ana tatsar nono. Mutumin da yake tare dasu yace ta haihu ne wani sa ya tunkuye dan makarakin bai shura ba. 


"Ina son yin tatsar nima" Zayyana tace da Radhiya wadda lokaci lokaci sai ta waiga baya ta gani ko su Awwab sun fito. Haushi ne ma ya kamata saboda yace bazata yi soja ba a gaban mutane ta yi gaba cikin takaici tana jin zuciyarta tana nauyi.


"Muje na koya miki" Emzee yace da Zayyana bayan ya gama karantar yayarsa.


Irin hular kaba da suke sawa su kare rana mai fadin kasa Radhiya ta gani wani cikinsu ya cire ta dauka ta kwama a kanta ta sami kasan bishiya ta zauna akan wani dutse tana kallon su Fauziyya harda Ibrahim kowa tatsar nono yake yi. Idan wannan ya gwada sai ya matsa wani yayi.


Awwab da Ghazalatu ta gani suna tahowa taji wani abu na taso mata daga kirji har wuya. Rufe idanu tayi ta ja hular ta dora akan fuskarta. Duk abinda take yi Awwab na kallonta har ya karaso inda take. So take ta bude fuskar saboda wani sihirtaccen hamami da yake tashi a ciki amma bata san ta ina Awwab ko Gayanatunsa zasu bullo mata ba. Babu wanda take son gani cikinsu. Wari ne ya isheta ba arziki ta cire hular tayi jifa da ita sai a cinyar Awwab da zamansa kenan.


"Wai Allah, wannan shi ake kira gumama inji takari. Wannan uban wari....."


Kasa karasawa tayi tana kallonsa da hular a cinyarsa tsabar mugunta ta rinka dariya. Shi da budurwarsa suka janyo mata saka hular ai.


"Kina da matsala, kin gama bata rai kin zo kina dariya" yace yana kara rungume hular


"Na ga ka kama hula ka rungume ne kamar ta ka"

 

Miko mata yayi ta goce da sauri kada ta sake tabawa "nagode, ungo abinki tunda taki ce"


"Warin maza take wallahi" ta kwashe da dariya da ta ga ya tashi da sauri hular ta fadi kasa.


Yamutsa fuska yayi yana kallon yadda take jindadi hankali kwance "wannan wace irin kalma ce haka ko dadin ji babu?"


Idanunta da ya yarda suna dauke masa hankali ta watsa masa "wace kalmar? au wai warin maza. Kada kace min baka ji ba. Dauko ka sansana"


Dukawa tayi zata dauko yasa kafa yayi ball da hular yana kada kai yana kai hannuwansa

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment