Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dama ji yake inama ya mutu ya huta da kyamar da al'umma suke nuna masa.


A tsukin kwanaki goma su Radhiya sunyi yawo a garuruwan Nigeria lungu da sako suna hira da sojoji ko iyalansu. Kuka kam ba'a cewa komai. Darakta Bigman ya ga wani salon rayuwa da basu taba sanin akwai ba. A irin yawon sun hadu da matan da suka yi sa'ar samun wani abu na kyautatawa daga daga dangi ko abokai ko kuma cikin abinda ake bawa mazajensu daga wurin aikin. Sai dai da yawansu babu abinda yake daga musu hankali kamar kewar mazansu na bakin aiki ko wadanda suka rasu. Abin da ban tausayi matuka. Masu nakasar dole a dalilin rashin wata gaba da suka yi a bakin aiki su ma tasu rayuwar yana cikin garari. Da dama cikinsu kuma sai su kasa rungumar wani aikin saboda tsaro suka sani shi su ka fi iyawa. Tafiya ce irin wadda ake kira mabudin ilimi suka yi.


Wuri na karshe da suka je shine garin Onitsha (Onicha) wurin Christie. A wata makarantar kwana ta 'yan mata suka sameta inda take aiki a matsayin malamar Geography. Christie tayi kukan sake ganin Radhiya sai da ta hadasu a waya da Ummi kamar yadda ta hadasu da Maman Dolapo. Ta amsa tambayoyin da Radhiya tayi mata inda take tambayarta yadda ta sami kanta a aikin koyarwa.


Sa'arta daya sai da ta hada NCE dinta sannan tayi aure. Bayan labarin mutuwar mijinta ta koma gida ashe tana da ciki. Da Radhiya da camera man suka bita cikin gidanta da tace su shigo. Kofar wani daki ta bude yarinya budurwa na kwance tana bacci ga kafafunta a lankwashe.


"Rebecca sunanta. Kashinta bashi da kwari bata tafiya ga matsalar kwakwalwa. Saboda ita ban sake aure ba ga rashin kudi da kyar na sami wannan aikin na koyarwa. Matsalar farko da na fara samu shine rashin mai kula min da tunda bani da kudin da zan biya mai raino. Wurin aikin suka ce na dena zuwa da ita a bayana lokacin tana da shekara goma na fara. Nasan wasu zasu daukeni mara imani amma bani da yadda zanyi. A gida nake kulleta naje aiki na dawo in tarar tayi kashi da fitsari. Ko ta mirgina inda zata iya jin ciwo daga baya na soma daureta idan zan fita shima da kaina naga rashin dacewarsa. Shine fa nake takura mata na hanata baccin dare har ta saba sai da safe tayi har naje na dawo. Albashina dashi muke cin abinci da sayan magungunanta duk sati. Rayuwarta akwai tsada sosai shiyasa na kasa daukar mai aiki har yanzu"


Dole mai imani ya zubar da hawaye idan ya ga rayuwar Christie da 'yarta. Itama dubu hamsin Radhiya ta bata inji Ummi da katin gayyata.


An sha wahala amma ana fatan bukata ta biya. Tare suka koma Abuja harda Darakta Bigman saboda zai duba video din gabadaya bayan an gama editing. Arifah da Radhiya kamar kada su rabu ance sabo turken wawa. Gashi dai suna gari daya amma saba su kwana daki daya suyi komai tare. Kafin ayi bacci kuwa kowacce zata raba lokaci da masoyinta idan an kare su koma hirar samarin nasu suna dariya. Kwanaki bakwai ya rage mutan Nijar su zo kawo gaisuwar Arifah. Yousuf kuwa jiransu yake yi su dawo dama ya taho domin kara gina kansa a zuciyarta.


Kowacce ta shiga motar da mahaifinta ya turo daukarta. Cameraman da Bigman motar su Arifah suka bi za'a saukesu a hanya sai jibi idan sun kammala aikin hadawa zasu je gidan Major General Zayyan.


A guje Radhiya ta shiga gida ta kwakume Ummi tana murna. Itama Ummin tayi kewarta sosai gidan kamar ba shi ba. Zayyan da taya bera bari kuwa dagata yayi yayi juyi da ita ai kuwa yasha nishi. Ummi ta rinka dariya. Abinci taci sosai Zayyan yana ta tausayinta wai ta fada tana gamawa tace bacci zata je tayi sai jibi da safe a tasheta.


"Ana la'asar zaki ji bugu idan baki tashi ba" cewar Ummi


"A tasheni sallah amma banda cin abinci. Na gaji sosai Ummi"


Tana sauke hakarkatinta akan gadon sai bacci kamar an jibge kayan wanki. Da kyar take tashi tayi sallah ta koma. Bayan isha ne Daada yace Ummi ko kunu ne ta dama mata baya so ta kwana da yunwa.


"Sai kace wata jaririya..idan taji yunwa zata fito ne"


"Ni dai ki dama don Allah. Baki ga yadda tayi zuru zuru ba kin kuma san meye a gabanta. Ni bazan kai 'yata gidan miji a bushe ba azo ana mata gori"


"Oh ni Mairama, waye zaiyi mata gorin?"


"Awwab mana. Yanzu tana murmurewa a gidansa zai ce kamar ba ita ya dauko a bushe ba."


Tafa hannuwa ta shiga yi tana dariya "Wannan uban amarya mun ga ta kanmu."


Lallabata ya koma yi saboda da gaske yake dan wuya ya gani ta fara yi saboda rashin hutu "taimaka kinji 'yar albarka Mairama baiwar Allah"


Ba yadda ta iya haka taje ta dama kunun gyada ta tafi dakin. Wata irin kwanciya Radhiya tayi a wargaje tsabar ta tara gajiya a jikinta. Ummi kuwa ta sakar mata duka a cinya ashe Zayyan ya gani "A'a Wallah ki bari fa. Daga cewa ki bata kunu sai cin zali"


"Dubi yadda ta kwanta fa"


Murza idanu Radhiya take yi ta tashi tana tura baki "Ummi me nayi?" tace cikin magagi.


Zayyan karasa shigowa yayi ya zauna a gefen gadon kusa da ita "tashi kisha kinji Innata kada ki kwana da yunwa"


"Na koshi" tace da kyar idanunta na rufewa.


Allah Sarki ji yayi bazai iya bari ba yana tausayin 'yar tasa. Da tare dashi suka girma Allah kadai Yasan irin yadda zai shagwaba kayarsa. Gyara zama yayi ya dora kanta a kafadarsa idanunta a rufe "rinka bude bakinki kinji Alheran sai Ummi ta baki"


Baki Ummi ta wangale ta ma rasa me zata ce masa. Wannan sangarta har ina. Shi kuwa kiss ya hura mata wai ta rufe bakin ko ya matso. Daure fuska tayi tana nuna masa Radhiya dake zaune kanta a kafadarsa ido a rufe.


"To ki bata ko yanzu..."


"Naji, naji. Ke bude baki ko na kwara miki kowa ya huta"


Da rarrashi Zayyan ya samu take bude bakin Ummi na bata yana shafa mata baya har ta shanye. Ta bude na karshen Ummi tace "ai sai ki rufe bakin ya kare"


Zamewa ta soma yi zata kwanta Zayyan yace ta dan yi hakuri ko yaya cikinta ya sassauta. A daddafe tayi minti biyar sannan ya gyara mata kwanciya ya kashe fitilar dakin sannan ya rufe kofa yana dariya shi kadai.


"Kalau kuwa Sojana" 


"Lafiya kalau...yau dai mafarkina ya tabbata. Kin tuna na taba ce miki ina son komai na Alheran ayi dani. Ko wanka kike kyuyar yi mata ni zanyi saboda bana son missing komai na rayuwarta tun kafin cikin Zayyan. Na rasa abubuwa da dama amma kafin ta koma hannun Awwab sai dai ku rufe ido"


"Sojana ba fa babyn da ka tafi ka bari bace. Kaima duk ka wani tsufa shine zaku yi mana kara'i"


"Ba don kada abin nawa yayi yawa ba har goyata sai nayi"


"To ni a goyani mana" suka ji Emzee yace yana hawowa saman saboda bai ga kowa kasa ba.


"Karasa min shi zaka yi?" Ummi tace suka sa dariya.


"Yau daya dai nima inyi shagwaba irinta Adda" Emzee ya zagaya bayan babansa ya sako hannuwansa suka zagaye wuyan baban.


"Anya Zayyan ba zamu jira idan matarka ta haihu nayi goyon ba..na jika ne kamar buhun siminti" Zayyan yace yana riko hannuwan nasa  da suke wurin wuyansa.


Ummi ta yi gaba kuwa "Ah to ku bari na tafi don kada ma na dorar"


Emzee zai sake shi kenan ashe Zayyan shammatarsa yayi sai ji yayi ya raba kafafunsa da kasa ya zagaye falon dashi. Kunya sosai ta kama Emzee sai gashi zai gudu daga falon Zayyan ya janyoshi ya rungume. 

"Allah Yayi muku albarka"


"Amin Daada" ya amsa da 'yar kwallarsa. Kasa yayi da gudu Zayyan ya kife akan kujera.


"Fillo yau fa sai kinyi min tausa"


"Kai da kake jin goyo nima bari nazo na hau"


Wani kallo yayi mata kasa-kasa ta tashi tayi gaba da sauri. Har yanzu tana jin kunyar mijin nata da baya rabo da tsokana kamar ba babba ba.


***********

Kwana biyun nan Radhiya bata komai sai bacci. Ita bata san ma ashe basa samun hutu ba sai da ta dawo gida. A rana ta biyu sai ga Yousuf ya iso. Yayi wani fes dashi aka fara tsokanarsa ya kusa zama ango saboda yadda Babban Arifah ya matsu da tayi aure bai ga dalilin jira ba. To shima baban Yousuf din ya matsu nasa tilon dan yayi aure shiyasa tun a waya su ka gama daidaitawa da Excellency. Abu ne na manya kuma kowa yana ji da nasa.


Da yamma Emzee ya kaishi gidansu Arifah yace to ya nemi mai dawo dashi don yasan yau din ta dabance a wurinsu. Shi kuwa gobe zai koma Kaduna makaranta yana da abubuwan yi. Yana komawa gida an kawo copy na farko na aikin su Radhiya. Sakawa akayi a falon Daada, Ummi, Bigman da Camera man da uwar gayya. Taken National Anthem aka fara kafin nuna mutane a garuruwa daban daban na kasar da muryar Radhiya tana bada takaitaccen uwa ma bada mama Nigeria uwar 'ya'ya da yawa.


Daga nan fa aka shiga shirin sosai. Komai yayi tamkar kana kallon film da aka bata lokaci wurin kawata shi. Abin ya kayatar da Zayyan matuka. Mai camera dai Excellency ya sallame shi amma duk da haka Zayyan yayi ihsani sosai. Bigman kuwa cewa yayi rabin kudin zai karba saboda shi kiransa kawai da akayi ya bude masa ido da abubuwan da bai taba tunaninsu ba bare ya damu. Hasali ma dai bai dauki soja da wata daraja ba da ta wuce idan ya gansu suna checking a hanyoyi ya zagesu sama da kasa ya wuce abinsa. Alfarmar da yake roko shine idan wannan shiri zai cigaba don Allah yana son zama daraktansa kada su nemi wani. Inda baiyi musu ba sai a fada masa ya gyara shima yanzu yake wayewa da aikin. Su Ummi sunji dadi nan take Radhiya ta turawa Supervisor dinta sannan ta kara da doguwar wasika game da zato da suka yi mahaifinta soja ya rasu da dawowarsa. Cikin minti talatin matar ta kirata a waya ta tayata murna kuma ta yaba matuka da aikin na awa guda da aka yi a Nigeria. Sunyi mamakin saurinta tunda wata biyar aka bata. Basu san dan Nigeria da dagewa bane. 


***********

Bayan kwana biyu Radhiya tana ta rubutu ta saka computer a gaba tana hada report akan project dinta a daki. Sanye take da dogon wando da rigar sanyi tayi parking gashinta a tsakiya ba a nutse ba wani ya zazzaro ta gefe da bayan. Ummi ce ta shigo da plate din fruits da ta yanka ta mika mata.


Fuskarta a sake take tace "Gashi 'yar gatan Daada kun maidani 'yar aiki ko" sai dai har ranta Alheran tana burgeta. Waye zaice yarinyar za ta nutsu haka har ta bawa karatu mahimmanci.


"Ummina yi hakuri so nake na gama ne kafin jibin da zamu tafi Sumaila"


"Wasa nake yi miki. Nima ina so inga kina kokari ai." Leka aikin tayi ta dan karanta wasu layuka ta koma ta zauna akan gado "kin kusa gamawa ne?"


"Inzo?" Ta tambaya don tasan kila akwai abinda Ummin take son cewa.


Kujerar gaban working table din ta juya zuwa bangaren Ummi tana fuskantarta. 


Murmushi Mairama tayi kafin ta soma magana a nutse "Alheran maganar aurenki da Awwab ce ta taso"


Gabanta taji ya buga da ta tuna wancan karon yadda abubuwa suka kasance. Umminta ta kula sai ta kwantar mata da hankali.

"Wancan karon na rabaku ne domin samar da maslaha. Yanzu kuwa sai inda karfina ya kare babu mai rabaki da Awwab sai Allah"


Kunya ta kama Radhiya saboda Ummi bata saba yi mata magana haka ba. Dauke kai tayi kamar bata kula da 'yar ta ta ba ta cigaba da magana.


"Nasara ta fada min cewa idan iyaye maza sun zo jibi akan maganar Arifah da Yousuf zasu roki alfarmar ayi auren karshen watan nan saboda basa son a ja lokaci kuma a ganinsu sauki nw tunda zasu zo taron baban naku dama. To shima maigidan nata ya fadawa Daada shine Daddy dinku ya yanke shawarar idan anyi finalizing maganar a haka to za'a daura auren Arifah ranar asabar ke kuma lahadi domin kawo sauki. Zai kama 27th da 28th December. Biki sai bayan sati biyu lokacin kinga an gama taron karrama Daada sannan munyi namu"


Ai jikin Radhiya sai yayi sanyi da ta gama lissafi a kanta kwanakin basu fi sha wani abu ba. Nutsuwarta ta nema ta rasa duk ta wani firgice.


Hawaye ta soma "Shikenan ni daga dawowar Daada sai aure" 


"Ki godewa Allah da yanzu haka za'a aurar dake mahaifinki yana kasa"


Kuka ta fashe dashi sosai Ummi tace ko tayi shiru ko ta kira Awwab tace masa ya nemi wata ita ta fasa. Da saurinta ta dago kai sai taji kunya.


"Ki kwantar da hankalinki na yarda da Awwab kuma kema kin sani zuri'ar su Mami sunfi karfin komai wurinmu. Sannan ki zama cikin shiri daga Sumaila wurin Innawuro zaki zauna sai ana kwana uku daurin aure tace gyara zata yi miki. Mun riga munje da Daada da kina can aiki"


Tashi Radhiya tayi ta dare gadonta da tsalle "ni ko gadon ban mora ba Ummi zaku koreni"


"Sai ki zauna morar gado sarkin shirme"


Bayan kwana biyu suka tafi Sumaila ita da Ummi taron da Malamijo ya shirya. Emzee ya riga ya koma makaranta bazai fito ba sai gab da taron da za'ayi. Washegarin zuwansu sauran 'ya'yansa kowa ya gama zuwa. Su Habu da Bature sun ajiye iyali shima Ayuba saura watanni kadan bikinsa. 


Tun dare aka fara soye soyen nama da kayan miya kai kace biki ne za'ayi washegari. Yara da manya abin ya zame musu sabo amma kowa murna yake yi. Shadaya na safe washegari kowa da kowa ya hallara a katuwar tsakar gidan da aka saka mata rumfa da tabarmi. Kujera daya ce a tsakiya Malamijo ya hakimce abinsa bayan an bude taro da addu'a yace kowa ya tashi ya gabatar da kansa masu 'ya'ya kana gama fadin naka yaranka su fadi nasu.


Salame ce ta fara tashi tana ta hura hanci tasha leshi mai kyau amma fa ita daban shima daban. Yadda ta matsawa Halifa lamba cewa tayi idan ya bari aka ganta a wulakance to kansa ya wulakanta. Cikin shagunan mahaifinsa yaje ya siyo mata mai kyau kuwa bai tsaya kanta ba ya siyowa duka yaranta sannan ya bawa Hibbah na Rahima yace ta kai dinki amma kada ya kai girmanta. Har kofar gida ya kai mata sai taji dadin zuwan nasa fiye da kayan. Ciki ta kaishi wurin kakarta ta kasa boye farincikinta tana ta cewa ga yayanta na Kano. Babanta ya saya mata mayafi mai kyau daidai aljihunsa da ya dace da kayan sai gata tayi wani irin kyau kakarta tayi ta wasa ta kafin ta fito. Da ta iso gidan a cike daya daga cikin kannenta ta gani ta tambayesu ina Ummansu yarinyar a tsiwace tace mata ta duba mana ko ta bata ajiya ne. Ajiyar zuciya tayi ta rinka dubawa ta ganota a can gefe taki sakarwa 'yan uwanta jiki. Yawan mutane yasa ta zauna a kusa da wata mai kama da larabawa sai wani irin kamshi take yi tayi kyau cikin jar atampa super.


Radhiya ta dukufa yiwa Awwab text bata kula da ita ba sai ta taji Salame tana fadin sunanta ta ajiye wayar a cinyarta ta koma saurarenta.


"Sunana Salame kamar yadda kuka sani kuma mijina Alhaji ne don ya sauke farali tun kafin wasu su fara rike naira"


Rahima cusa kanta tayi a cinyarta saboda kunya Halifa yaji kamar yayi tsuntsu ya bar wurin.


"Babban dana ma da babansa duka alhazawan ne yayi karatu a kasar Misira ne ko ...." neman Halifa ta rinka yi da ido ya dukar da kai.


"Zauna haka Salame bari yaran suyi da kansu za'afi gane juna" Hajjo ta dakatar da ita. Malamijo ya samu ta dawo bayan ta gama fushin yanzu sannu a hankali yake binta.


"Halifa sunana a Kano muke da zama"


Salame tayi caraf ta amshe "waye zai ganeka a haka? Ka fada musu sunan babanka Alh Salisun kwari wanda kowa yake gani a talabijin"


Duk da ita ta haifeshi ko kadan baiji dadi ba dama ga kadaicin rashin zuwan Emzee saboda makaranta. Yana zama Rahima ta mike a kunyace. Ita bata san mutanen gidan sosai ba Radhiya kuwa ta bita da kallo.


"Sunana Rahima Usman" ta kara da sunan mahaifinta a zatonta haka ya kamata tayi tunda taji an yiwa Halifa fada.


"Kin manta baki ce musu me buga iska a titin...."


"SALAME!!!" Malamijo yayi mata wata irin tsawa da shi kanshi baya jin ya taba daga murya irin haka. Wata irin dabi'a ya karance ta da ita yanzun nan. 'Ya'yan da ta haifa da masu kudi sune mutane Rahima kuma bata da amfani. Da girmanta ta janyo wa kanta zubewar mutumci a gaban kannenta da 'ya'ya.


Ummi sai tayi saurin mikewa domin katse shirun da ya ratsa wurin ana ta kallon Salame.


"Sunana Mairama daga Adda Salame sai ni" 


Harda masu ihun murna cikin kannen saboda tuni ta fara janyosu a jiki tun bayan yadda ta sake ganin rigimar Mami da kannenta.


Kallo na bakinciki da hassada Salame take wurga mata. Mairama dai atampa ta saka super itama amma duka wurin babu wanda ya kama kamar kyaun da suka yi ita da Radhiya. Fatar jiki ta nuna hutu da jindadi gami da kwanciyar hankali.


Radhiya ta tashi ta fadi sunanta itama sannan tace akwai kaninta yana makaranta bai sami zuwa ba. A sanyaye take magana saboda hawayen da take gani Rahima na zubarwa a boye. Komawa tayi ta zauna ta kama hannun Rahiman guda daya ta rike amma bata ce mata komai ba sai ma matsawa da tayi jikinta ta saka daya hannunta ta dan rungumota a jiki. Sai da tayi mai isarta a hankali nutsuwa ta rinka zuwar mata ta dago jajayen idanu ta kalli Radhiya.


"Abu ne ya fada min a ido fa kada ki zata kuka nayi"


"Mai karya" Radhiya tace tana kada kai.


"Ai dai baki ji na rantse ba"


Murmushi suka yi wa juna Radhiya taji kanwarta ta ta shiga ranta yayin da take tunanin hanyar da zata bi ta kartawa Gwaggo Salame rashin m ko dan kadan ne taji idan da dadi gwasale mutum a bainar jama'a.[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Sai da kowa ya gabatar da kansa aka kare akan jarirai Hassana da Usaina. Malamijo ya gyara babbar rigarsa yana kallonsu wai gabadaya tsatsonsa ne wannan. Bai taba tsayawa ya duba wannan babbar baiwa da Allah Yayi masa ta 'ya'ya ba. Kafin yanzu kallon nauyi da matsala kawai yake yi musu yana ganin matan da yake aura basa kyauta masa kowacce tana zuwa sai ciki. Babu wanda bai tara ba cikinsu da nagari da shakiyai. Akwai nutsatstsu ga kuma fitinannu. Biyu ma dai cikinsu kauraye ne 'yan chau-chau. Malamijo ya kusa shekara bai sasu a idanunsa ba kuma bai damu ba saboda sunfi zama a gidan kakaninsu na wurin uwa tunda babarsu daya. A can suka koma kaurayen saboda 'yan uwan babar tasu irin mafarautan nan ne masu yawo da karnuka. Ba'a tsaya nan ba duka dai cikin yaran nasa akwai rikakken dan jagaliyar siyasa wanda yayi suna akan rashin mutumci indai aka taba 'yan jama'iyyarsu. Ga dreban adaidaita sahu da karamin dan sanda mai mukamin kofur. Ga Mal Ayuba mafi rikon addinin cikinsu. Akwai mai sayar da kayan fruits a wheelbaro a cikin Kano. Bature shi da yake yayi NCE koyarwa yake yi, Habu kuma yana sayar da kayan masarufi. 'Ya'yan dai sai son barka kowa da inda yafi kauri.


A bangaren matan ma dai babu wata mai ilimin da ya wuce secondary sai Mairama da ta koma lokaci daya da 'ya'yanta. Da yawansu basu gama makaranta ba. Na gidan mijin kalilan ne ga zaurawa biyu. Akwai uku marasa jin magana daya saurayinta dan daba, biyun kuwa samari ke daukar nauyinsu. Ba dai yawon ta zubar suke yi ba amma ana kanwar ta zubar din kai na hayaki suna jinsu daidai da kowa. 


Abinda Mal Ali Gidado Malamijon Sumaila bai saba ba kuma bai taba tunanin zaiyi ba ne yayi masa bazata. Hawaye ne masu zafi yake fitarwa saboda tun bayan wata nasiha mai nauyi da Ayuba ya cire kunyar mahaifinsa yayi masa jikinsa ya mutu murus. Duk wata guntuwar hayaniya sai ta dauke wurin yayi shiru. Mairama da bata hada son Malamijo da komai duk halinsa kuwa sai kuka.


Salame ta kalleta shekeke ta tabe baki "sabon salo" 


Gyaran murya Malamijo yayi ya gama karya zukatan matansa musamman masoyiya Hajjo da Nene wadda yace dole tazo 'ya'ya nata ne itama "abinda zan fada muku ba yawa ne dashi ba, don Allah ku yafewa min"


Yaran nasa ma sai gashi daidai da daidai matan nan suna yarfe kwalla da wannan kalami nasa.


"Babu wani abu da nayi muku wanda zan bugi kirji dashi a gaban Allah game da rike amanarku. Haka Ayuba yace min jiya ko ba haka ba...Aradun Allah kasa bacci nayi duk ya tsoratani"


Wasu na dariya wasu na murmushi saboda yadda yake maganar bai dauketa da wasa ba.


"Nayi alkawari zan gyara sha Allahu kafin na mutu zanyi kokarin gyara laifina."


Radhiya don ta rage musu nauyin da ya saka musu a zuci ta dauko zancen da tasan baya so "dama ana cewa siituna aw saba'una tafiya tayi nisa"


"Don kaniyarki shekarata hamsin da bakwai watan azumin tsofaffi zanyi da takwas" yace fuska a tamke don yaki jinin zancen mutuwa.


Gabadaya wurin ya kaure da dariya da mugun tsakin da Salame take saki. Sarai Malamijo yaji kuma ya kudiri niyar saitawa 'yar tasa zama. Nasihar hadin kai ya dora musu da ita sai gashi sannu a hankali wadanda basu magana a da ko dai don rashin jituwa ko don rashin sabo da juna hira ta fara barkewa a tsakaninsu. Abinda Malamijo bai sani ba shine gabadaya 'ya'yan nasa ba kin junansu suke yi ba rashin tsayuwar uba a rayuwarsu ita ce babbar nakasun da suke fama da ita. Yau gashi zaune dasu babu hantara babu zagi kowa ransa wasai. Yadikko ganin haka tace me zai hana suna cin abinci yaran na zuwa gareshi yaji me kowa yake yi kuma ya bincike matsalolinsu. Abin yayi masa dadi matan cikinsu masu kuruciya suka tashi aka zubo abinci ga nama shar dasu. Hayaniya kuwa sai da Radhiya ta kira Emzee tace tana ta tausayinsa saboda yayi missing. Sun dan taba hira ta ajiye wayar.


Rahima ta kalleta a kunyace saboda ganin kanta take wata muguwar local akan Radhiyan tace "shine kanin naki da kika ce yana makaranta?"


"Eh bari ki ga hotonsa saboda kada ku hadu baku san juna ba" tace tana binciko mata hotonsa a wayarta. Wanda yake sanye da khakinsa yayi wani kyau ta nuna mata. 


Shiru Rahima tayi tana kare masa kallo lokaci guda taji wata irin kunya saboda wani kallon kasa-kasa da Radhiya take yi mata "kema sojoji suna burgeki ko?"


"Uhm ni dai tsoronsu nake ji" 


"Kice dai irin halin Fulanin zaki yi na tsoron duk mai uniform"


Dariya suka yi tare wata yarinya da bata fi shekara goma ba ta kawo musu tray shakare da shinkafa dafaduka taji kayan lambu tayi kyau. Karamar uwa ce dai tunda 'yar Malamijo ce suka karba su hudu da wasu matan kusan sa'annin Rahima duka 'ya'yan gidan suka fara ci. Radhiya duka burgesu take yi kana ganinta kaga wayayyiyar 'yar boko ga gayu amma da ta shiga cikinsu ajiye komai take yi ta koma daidai dasu kamar yadda Umminta take yi.


Abinci suka fara ci sauran matan suna yiwa Rahima korafin tana cikin garin amma bata son zuwa gidan duk ba'a saba da ita ba.


Murmushi tayi kanta a kasa ita kowa ma kunyarsa take ji "Zan rinka zuwa yanzu sai kun koreni"


Daga sama suka ji muryar Salame babu wanda ya kula da zuwanta sai hannunta da ta kama kunnen Rahima dashi da karfi "gani nazo tunda ke baki da hankalin idan kin shigo ki zo ki nemi uwarki ki gaisheta"


Kunnen zugi yake kamar zai tsinke ta soma hawaye idanu sun fara dawowa kansu anata bata hakuri ta wani hade rai ita me 'ya.


"Umma kiyi hakuri a makare nazo kuma bana son tsallake mutane na ga kinyi nisa"


"Tunda an samo abinda babu a gidan tsoho ai dole kice nayi nisa. Maza kici ki tashi ki koma"


"Umma!" Halifa yace a zafafe yana tahowa wurin ransa yayi mugun baci. 


Kafin

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment