Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki. Dazu da safe Mama ta kaita asibitin an tabbatar mata wata biyu ne. Da yatsu tayi masa alama Zayyan harda hawaye "kinga ikon Allah da yadda Yake gwada karfin mulkinSa ga wanda Yaso a lokacin da Yaso. Ina sonki Mairama Allah Yayi miki albarka Yasa ki zama matata har aljanna"


"Amin Sojana...ba ka jiye min haihuwq ga 'ya a gidan miji"


"Itama ta haihu nan da wata tara nake fata. Arziki ne ni dai nagode"


"Nima ai nagode"


"To muje mu kwana kafin na fara jin rubewar panadol din nima" yaja hannunta suka kwanta kamar kodayaushe aka bude sabon babin tsohowar soyayyar da kullum suke aikin sabunta ta.


Da safe da yawa cikin bakin sun tafi musamman na Kano. Na Sakkwato kuwa sun jira su koma tare the next day. Zahra da Fauziyya ko keyarsa babu sai a ranar tafiyar. Awwab yazo yayiwa Radhiya sallama tare da saka mata kudi a jakarta ko za ta bukaci wani abu saboda shi da su Mami Katsina zasu wuce. Ummi, Mama da Tante ne zasu Sakkwaton.


Can ma gagarumin taro aka hadawa 'yar Zayyan don sunyi bajinta sosai 'yan uwansa. Anyi komai an gama lafiya. A ranar 'yan daukar amarya suka zo da ga Katsina da akwatunan lefensu guda takwas da kit. Awwab yayi kokari matuka abu kadan ne ba shi ya saka ba.


 Duk wannan bidiri da akeyi Ghazalatu suna can wani karamin hotel da Nura yana angwancewa. Tayi kuka tayi bala'in ta koma rarrashi duk ya toshe kunmuwansa. Cewa yayi sai ranar da za'a kai amarya Katsina zasu koma lokacin an gama share gidansu domin can zasu wuce. Tana kuka ta kira Mummy Gambo wadda tace mata umarnin Alh Baba ne tayi hakuri ta zauna gidan mijinta da kansa yayi alkawarin idan Nura ya sake tabata zai dauki mummunan mataki a kansa. Ba sa son da kuruciyarta a fara kirga mata aure. Ba haka taso ba amma dolenta ta hakura ko don gudun kada jiki yayi tsami.


Cikin wata hadaddiyar laffaya Mama ta shirya Radhiya aka fara shirin tafiya Katsina da matar Awwab. Ummi dai ba binsu zata yi ba daga nan Zayyan zai zo su wuce Nijar. Har yanzu bata bari kowa ya gane tana da ciki. Dauriya take sosai shiyasa Mama tayi ta kawo mata abin da zai sassauta mata tashin zuciya a boye. An fito tafiya da amarya idanunta a bushe saboda har yanzu ita fa bata ganin an kaita kenan tunda tasan zasu je Nijar sannan a koma Abuja. Abinda ta sakawa ranta kawai wani bikin zasu je a Katsina. An fito tafiya bakwai da mintuna Jume da Gwaggo Ladi sunyi mata nasiha zasu tafi da  iyayenta mata yayyen Zayyan da matan su Badaru ga wasu cikin cousins dinta sai su Yadikko masu komawa Sumaila yayin da Hajjo da wasu yau din zasu tafi Katsina.


Takalmin Radhiya me madauri ne ta durkusa tana daurawa wata tsohuwa tayi zaton kuka take yi tace " 'yar nan sai hakuri ki dena kuka haka kowace mace haka aka yi mata kema da sannu zaki saba"


Dagowa Radhiya tayi innocently tace "Iya ba kuka nake ba takalmina nake daurawa"

(wadda ta tsargu da ita nake.....)


Ummi na gefensu tsabar kunyar da taji bata san lokacin da ta durma mata wani uban dundu ba sai da ta kuma durkusawa cikin fada tace "kuka kike mana, ba na hanaki karya ba shine zaki kalli idanun Iya kice mata ba kuka kike ba"

 

Iya wadda ta kasance 'yar uwar Mal. Muhammadu ta kalli idanun Radhiya sosai "ai kuwa kamar ba kukan take ba Mairama"


"Kuka nake mana Iya baki gani bane kawai...ni ku rikeni na fasa tafiya" Radhiya ta soma yi musu hargowa ana rikota tana komawa ta rungume Ummi. Tsabar takaici ta rasa me zata yiwa yarinyar nan ta huce. Wannan runguma a bainan nasi salon ace basu da kunya.


Fada Ummi ta soma yi mata matar Rayyanu tace "haba Mairama ki rike yarinyar nan taji dumin uwa mana sai ki hauta da fada kamar baki san ciwon rabuwa da gida ba"


Mama ta gimtse dariya tace "kinsan wani idan abu yayi masa yawa kukan ma kasawa yake...tun da muka tashi asuba take sharar kwalla"


Ummi kamar ta hadiyi zuciya da Jume ta fito ga mutane suna ta cewa wai sun basu tausayi wannan uwa da 'ya akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Duk yadda take jin kunyar 'yar fari kuma a gidan surukai Sakkwatawan nan babu ruwansu suke cewa ta shiga daki ta kwantarwa da 'yarta hankali.


Suna shiga Ummi ta juyo a fusace Radhiya ta kwashe da dariya sannan ta nutsu tace "Ummi Allah Ya kara miki lafiya wallahi bani da kamarki duk duniya"


Hawaye ne ya saukowa Ummi ba shiri ta kai mata rankwashi ta goce. Da kanta ta rungumo Radhiyan tana murmushi zuciyarta na sake cika da farinciki "Allah Yayi miki albarka Ya baku zaman lafiya. Banda kiriniya kinga dai aure ba abin wasa bane kuma kin girma"


Tana makale a jikin mahaifiyarta take amsa mata. Gudun kada a leko ta tasata a gaba suka fito aka sakata a mota. Canter guda aka cika shake sosai da kayan gara gari guda kamar masu shirin bude kanti.


Gidan Alh Baba aka kaita inda duka kakanin da matayensu suke zaune suna jiransu. Yau dai wanda baisan Alheran Radhiyan Awwab ba ya ganewa idanunsa. Wasu ma sai tausayin Awwab din ya kamasu yadda Alh Baba ya hana wannan auren da farko. Zukekiyar bafillatana mai jinin buzaye irin wannan har ita ake yiwa yanga. Motocin da suka kawota dama akwai na sojojin da suka biyosu domin kariya kowa yasan ta wuce ajin raini ita da danginta. Yarinya an kawota da gararta abin kwatance sai son barka.


Zahra ce ta shigar da ita falon kanta a rufe ba ta iya dago kai ba amma jikinta ya bata Awwab yana ciki saboda wani fitinannen kamshin turaren da yake amfani dashi yanzu. A gefen kakarsu Maman Biyu aka zaunar da ita Alh Baba yace "dawo kusa da mijinki jikata"


A sanyaye ta tashi Zahra ta ja ta kusa dashi ta zauna a darare ita kuma ta fita. Nasiha tsofaffin nan suka rinka yi musu baka jin komai sai sheshshekar kukan Radhiya da gaske fadan yana shigarta. Da yake ta baza laffayar a kasan inda ta zauna ta karkashi Awwab ya zura hannu ya kamo nata sai da ta zabura amma yaki saki yana matsawa a hankali. Kukan nata ne ya tsagaita Baba Karami yace a wuce da ita gida su samu su huta. 


Uwargidan Alh Baba ce ta fito da ita aka damkata hannun iyaye mata suka wuce gidan Daddy. Dangi ne ko ta ina ga su Hajjo ma sun iso. Ana neman uwar amarya Mama ta fito ta rike hannun Radhiya har dakin Mami suna tare da 'yan uwanta ana hira kamar wani abu bai hadasu ba.


Bayan gaishe gaishe da tambayar hanya Mama ta kama hannuwan Radhiya dake zaune a kasa har yanzu bata bar kuka ba jikinta yayi sanyi ta dora a tafin hannun Mami na dama sannan ta kawo na hagun ta dora a kai ya zama na Radhiya ke tsakiya.


Muryarta babu alamun wasa tace "Mami ga amanar 'yata...."


Mami ta harareta "meye haka Zainab, Radhiya 'yata ce kada kiyi min haka"


Girgiza kai Mama tayi harda 'yar kwallarta "Mami ki barni nima na aurar da 'ya yadda kowa yake yi. Alheran dai a tafukan hannunki ta fado duniya kece kika karbi haihuwarta. Ko da aure ko babu ke uwa ce ga tsatson Mairama da Zayyan. A madadin babansu Hadir ina mai baki amanarta. Kinsan halinta babu wani abu sabo a wurinki. Idan tayi kuskure kinfi kowa sanin ta yadda zaki tsawatar ki sakata a hanya. Na baki amana ne ba don bazaki iya ba sai don taji da kunnenta cewa yanzu da da ba daya bane. Da can 'yarki ce yanzu kuwa jininki ta koma. Ke kuma Radhiya daga yau kin girma saboda haka duk abinda na fada miki a gida ki fara aiki dashi domin ibada kika zo yi"


Zantukan Mama Zainab ya taba Radhiya da Mami suka rungume juna suna kuka. Yadda suka yi ya taba matan dake dakin sosai suna kara girmama wannan kyakkyawan zumunci na mutanen nan.


Mami da kanta ta kama kai Radhiya dakin da Fauziyya suke tana fita kuwa suka fara zolayarta sai dai babu bakin ramawa an kashe mata jiki gabadaya. Bayan sunyi sallar la'asar anci abinci Mama ta hada 'yan uwanta da wasu kannen Mairama suka fito suka zaga kofar baya bangaren Awwab da yake jikin gidan amma kofarsa daga barin hagu ake shiga. Da can dan karamin falo ne da daki sai toilet. Amma ana gab da daura auren Daddy ya fadada masa wurin aka kara girman falon sannan akayi kitchen. Sun saba kowa a garinsu yake zuwa sallah. To haka yake son ta kasance ga tilon dan nasa. Sai kuma ya ga gidan nasu babu yara Zayyana kanta ba dadewa za'a aurar da ita ya zama daga shi sai Mami. Shine yayi wannan gyaran yada idan anzo Awwab ba sai ya nemi wurin ajiye iyali ba ko kuma su rinka rabe rabe a cikin gidan. Lokacin da ya fadawa Baba Hadir yayi wannan gyaran alfarma Hadir din ya roke shi akan cewa kada ya bari Zayyan ya sani haka kuma matansu sun boyewa Mairama. Komai da ya kamata a saka a cikin gidan nan Baba Hadir da Mama Zainab ne suka yiwa 'yar tasu. Daki daya ne aka saka mata wani makeken royal bed mai kyau. Ba'a cika dakin da tarkace ba bayan kayan gadon sai wani irin show glass na gani da fada wanda yasha turarukan wuta na asalin da humra da wasu irin turaruka masu maiko. Labulayen dakin kansu abin kallo ne. Toilet din a cikin daki yake an chanza tiles, tray din wanda, toilet seat da sink gabadaya an zuba sababbi. Kayan cikinsa ma sun hadu kamar ba toilet ba anyi masa kyale kyalen zamani.


Falon bai kai girman dakin ba shi kuma royal chairs ne aka saka 3 sitter da one sitter guda biyu saboda wurin kada ya cushe. Ga katuwar wall tv da duk aka hada kayan kallo akan wani kayataccen tv stand. Centre table dinta da kananunsa na gefen kujeru duka masu kyau sai wani chest of drawer a karshen falon an jera plates da tarkacen kayan kitchen. Ana shigowa falon kofar dakin ce a farko daga dama sai kofar kitchen tana kallonsa daga hagu. Idan ka shiga kamar kada ka fita, gashi dai karami amma komai cikin girma da wadata akayi shi.


Zaman aikin karasa duk wani gyara da yayi saura su kayi. Emzee da Ibrahim ne a kitchen suka hada gas cooker da su fridge. Kafin isha bangaren amarya ya fito fes sai wani uban kamshi har bangaren Mami ana ji. Su Hajjo sunyi mamaki sosai ganin Mairama bata yi musu zancen akwai wani gidan a Katsina ba. Ba tayi kasa a gwiwa ba wurin nemanta inda ta ce musu bata da labari ko kadan itama. Zayyan ta fadawa yace shima bai sani ba. Sun tabbatar aikin su Mama ne wannan ta kirata kuwa ta ma kasa godiyar sai kuka tana cewa "Zainab Allah kada Ya taba bawa shaidan dama a kanmu. Kada Allah Ya bani ikon zama butulu a tsakaninki da Mami"


"Amin amma ki bar magana irin haka kada kisani kuka zan kira anjima" katse wayar tayi ta share kwalla. Me zasu cewa iyalin Zayyan. Gidansa da ya gida da guminsa da gadon mahaifiyarsa dungurugum ya baiwa DK kuma ya sayawa Ibrahim mota. Da shi da Daddy basu taba nuna wata alama da Hadir zai ji cewa bai kaisu arziki ba. Sun dauki kawunansu abu guda basa hangen komai sai soyayyar da suke yiwa juna.


Bayan sun koma ciki ne take fadawa Mami gobe ana gama budar kan bayan magariba sai a kai Radhiya.


Mami ta girgiza kai "a'a fa Zainab abinda biki bai kare ba, ko me za'ayi sai mun gama da Nijar dinnan kowa ya huta lokaci guda"


Mama ta kankance ido don bata da niyar chanza shawara "Mami kuji tsoron Allah, aure kwana nawa ana jawa yarona rai. Yo banda ma dai shi Awwab din anyi mai hakuri da tuni ba sai dai labari ya sha bamban ba. Kullum saka ido nake in ga tafiyar Radhiya ta sauya....."


Da sauri Mami ta mike "ba dai tariya kike so gobe ba? To a kaita dakinta gobe ba sai kin fara barambarama ba"


Shu'umar dariya Mama tayi "haka kawai don dai daga shi har ita ba wayis bane ta wannan fanin ga gabontar 'ya'yan fari da duk mun kwashi kunyarmu a hannu tun a Abuja"


Yousuf tun daga wurin dinner ya zarce da Arifah Nicon ya karbe wayarta sai gobe zasu tafi Nijar. Mom dinta tayi ta korafi Excellency kuwa yace yaro yayi masa daidai. Su basu yi lissafin halin da yaran zasu shiga ba kawai sunyi tsari yadda yayi musu.


Gidan tun safe aka tashi da aikace aikace saboda walima ce babba Mami ta shirya a farfajiyar gidan. 'Yan uwa na nesa da kusa sun taru. Daga shabiyu zuwa la'asar anyi kade-kade da raye-raye Rahima tun tana jin kunya da komawa baya har ta ware saboda Zayyana bata san bakunta ba. Duka kayan da Radhiya ke sakawa Mami ce ta tanada. Bayan la'asar atampa aka bata ta saka super exclusive dinkin sosai yayi mata kyau aka dora mata wata bakar alkyabba tasha ado sai sheki da daukar ido. Wurin zamanta daban an kawata shi ga kujeru a jere aka kira wata babbar malama tazo yin bayanai da nasiha game da zaman aure da hanyoyin samun kyakkyawan zama da miji. Radhiya jikin gabadaya yayi sanyi hawaye kawai take zubarwa don kalaman matar akwai shiga rai da tsoratarwa. Sai da magariba ta gabato sannan taron ya watse bayan addu'o'i daga bakin malamar.


Ciki aka koma ana alwala da sallah. Radhiya ta fito daga toilet kenan Mama ta shiga dakin ta kirata. Dakin Mami ta kaita babu kowa a ciki ta bata wani abu a cikin kofi mai zaki da wani dandano da bata gane ba.


"Maza shanye kuma kada a sake baki wani abu ki sha kada kizo cikinki yayi ciwo sun isa haka. Sannan ki zama cikin shiri idan anyi sallah zamu kaiki kyayi wanka a can don nan ko ina a cike yake"


"Ina?" Tace a firgice murya na rawa.


"Bangarenku mana"


Wani abu taji ya tsirga mata a ciki ta daure tace "Mama wane bangaren kuma?"


Daure fuska tayi ganin Radhiya ta firgice lokaci guda kafin ta tara mata mutane "ina kinsan cewa akwai dakin Awwab a gidannan"


Idanu cike taf da hawaye tace "eh"


"To nan aka gyara miki idan kunzo kinga babu ruwanku da takurawa Mami kuna da komai a can" cewar Mama tausayin Radhiyan ya soma kama ta.


"Amma ba. Ance. Ance sai mun dawo daga Nijar ko Mama?" Tace da sigar roko.


Kafadarta Mama ta dafa tace "Radhiya, aure kika yi ba kwana kika zo yi gidan Mami ba kema yanzu nan gidanki ne. Ina so ki cire tsoro kamar yadda kika ji nasihar malamar nan dazu kada ki bani kunya kinji ko 'yar albarka. Jeki kiyi sallar zan zo mu tafi, kuma banda kuka ki tabbatar kin daure takalminki da kyau dai.." ta kare da zolayarta.


Kasa daurewa tayi tana sallah tana hawaye. Yanzu shikenan sai kowa ya kwana a cikin gidan ita kuma a kaita dakin Hamma Awwab? Da an fada mata da wuri da ta shirya zuciyarta amma wannan bazatan ya shammaceta da yawa.


Sukuku haka tayi sallah ta idar harda su sharar hawaye. Kukanta yasa Rahima rasa walwala tazo ta rungumeta itama tana yi batare da taji dalilinsa ba. Zahra da Fauziyya ne suka shigo Zayyana ta kira su akan kukan su Radhiyan.


Zahra tace "amaryar Hamma me ya faru?"


Kara sautin kukan tayi "wai kaini za'ayi"


Da ido Fauziyya ta yiwa Zayyana da Rahima alamun su fita sannan ta kwashe da dariya "wai, wai, wai....kice yau za'a kwana ana goge janbaki. Gara kisa 24hours shine baya fita da wuri"


Zahra ma dai dariyar tayi Radhiya na kuka tace "sai na fadawa Hamma"


"Tuba nake anti amarya. Tashi muje in baki karatu kinji kanwata yayata"


A dakin Mami kuma Mama ta kira Awwab tace masa shima ya taho da shiri yanzu za'a kai amarya jiya sha'afa tayi bata fada masa ba.


"Ina za'a kuma kaita Mama?"


"Bangarenku mana mun karasa jeren tun jiya"


Wata irin murna ta kama shi yace "Allah Mama?"


Sai da tayi dariya tace "idan ma kayi nisa ni dai yanzu zan rakata kasanta da son shiga jama'a kada taji ka shiru ta dawo cikinmu"


Takalmansa yake sakawa lokacin a gefen gidan Baban Biyu inda sukayi sallar magariba yace mata "gani nan Mama....Mama nagode sosai" ya cigaba da zuba mata godiya sannan ya ajiye wayar ya taso Bilal ya fada masa a ina zai siyo abubuwan da ango ke shiga gida dasu.

**********


Tsokanar Radhiya Fauziyya take tun tana kuka ta dena wani abun ma sai sunyi dariya ita da Zahra. Sallamar Mama taji wadda ta tsinke mata zuciya ta tashi da sauri.


"Taso mu tafi"


"Wayyo Mama banyi sallama dasu Adda Zahra ba" tace a rikice.


Mami taji wani irin tausayinta domin tana kusa da Maman. Duk bakin Radhiya da dakewar zuciya yau babu.


Mama ta rungume hannu a kirgi "to ina nan yi musu sallamar"


Rungumesu ta shiga yi sai ta basu tausayi bare ma Fauziyya kukan take tayata.


Hannunta Mama ta janyo "muje kinji gobe da safe zan turo miki su ayi ta rungume-rungumen"


Mayafi kawai ta yafa ta saka wasu flat shoes masu dan uban kyau suka fito. Wata kanwar Ummi ce ta dauko akwatinta wanda bata san da zamansa ba duk cikin aikin Mami ne wannan kayan da ta dinka mata kala goma. Kayan kwalliya da underware daga cikin wanda ta taho dasu ne aka dibar mata aka zuba. 


Suna fitowa bakin kofa Emzee na danno kai zai shigo. Ai yana ganin tana kuka ya fara tambaya hankali a tashe. Kanwarsu ta bangaren Badaru ce ta fada masa kaita za'ayi. Ya bata rai kuwa.


"Yanzu Mama ana kai kowa a mota amma Adda a kafa"


Hajjo ta kamo kunnensa "To sannu me taya bera bari ina zamu kaita da mota"


"Ni gaskiya ban yarda ba Mama don Allah bari na kaita a mota" yace yana turo musu baki.


Rahima murmushi kawai tayi ganin halayen Emzee mabambanta. Ta dai tabbatar baya hada kowa da yayarsa kuma baya boyewa ma.


Iyaye na masa fada ya kama hannunta ya rike "da so nayi na zagaye gidannan sai biyar dake a mota sannan a kaiki amma tunda sun ki muje na rakaki Addata"


Dariya ya basu ya fuske abinsa wai ai bata da kawaye shine dai babban abokin. Haka ya shige cikin mata abinsa har falonta aka wuce dakin da ita ana musu fatan alkhairi. Ko minti shabiyar basuyi ba suka tafi Mama tace mata tayi wanka akwai kaya a ciki ta nemi wanda bazai takurata ba ta saka.

**********


Tana jiyo hayaniyar mutane sama-sama daga main house din tayi kuri tana tunani wai yau ita ce a gidan nan a matsayin matar aure-matar Awwab. Ita ma bata da masaniya akan za'a ware musu wuri a gidan nan shiyasa take ta mamaki. Kanta ta bude ta karewa dakin kallo a take ya shiga ranta komai ya burgeta matuka. Ta tashi a hankali ta leka toilet, falo da kitchen zuciyarta fes.


Tunowa tayi da gargadin Mama akan tayi wanka ga turaruka da ta nuna mata na humra a showglass da kuma wasu a cikin akwatin da aka zuba mata kaya. Mikewa tayi ta cire kaya tayi sa'a akwai tawul biyu a bandakin kuma akwai heater ta bango a kunne. Wanka tayi kafin ta gama taji ana kiran isha ta dauro alwala ta fito. 


Jakar kayan kwalliyarta ta dauko ta jeresu akan dressing mirror sannan ta shafa mai. Gaban showglass din taje ta bude ta shafa humrar masu daddadan kamshi tazo ta shiga fesa body spray. Gashi dama jikinta yasha dukhani dama cikin kamshin take. Tana durkushe gaban akwatin neman kayan sawa daga ita sai tawul taji an murda kofar dakin za'a shigo. Gabanta ya fadi da sauri taje ta danne kofar tana cewa waye cikin rawar murya.


Murmushi Awwab yayi saboda a haka ma ya iya gano hakikanin firgici da tsoro a muryarta.


"Schatzi masallaci zanje, na ajiye aby a falo ne kada ki gani ya baki tsoro baki san wanda ya kawo ba"


"To"


"Ba zaki bude naga fuskarki ba kafin na tafi?"


Shiru tayi tana kallon kanta yaushe ma zata yarda ta bude.


"Sai na dawo matsoraciya"


A hankali yaji tace "adawo lafiya"


Kasa kunne tayo taji karar rufe kofar gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya. A gurguje ta janyo wasu riga da skirt na wani yadi mai laushi ta gyara fuskarta da kwalliya madaidaiciya ta kuma fesa turare sannan ta saka wani zumbulelen hijab mai hannu har kasa shima ta bishi da turaren. Sallar isha tayi ta hada da shafa'i da wutiri. Bayan ta idar ta zauna addu'a akan sabuwar rayuwarta kafin ta shafa ta ake jin alamun an shigo sai dai yanzu kai tsaye ya bude kofar dakin ya tsaya yana kallonta a zaune kan abin sallah.


Shafawa tayi ba don ta gama ba sai dai kawai kallon da yake mata yayi yawa kuma yaki magana. Yana ganin tayi yunkurin tashi yace ta zauna. Abin sallah ya dauko a inda ta dauki wanda take kai ya shimfida a gabanta. Ta san sallar me zasuyi bata bukatar karin bayani ya ja su suka yi nafilar godiya ga Allah. Addu'a sosai yayi musu tana cewa amin a hankali ta kasa daga ido ta kalle shi.


Mikewarsa ne ya sanar da ita ya gama zai nade abin sallar ta karba da sauri amma har yanzu bata kallonsa. Shi burge shi take yi komai nata. Ta bayanta taji ya tsaya ya zuro hannayensa ya tayata ninke abin sallar. Faduwar gabanta ya sake tsananta lokacin da ya rungumeta a haka ya dora kansa a kadafarta yana mata magana a kunne.


"Dama kin ajiye wannan shirun bani da niyar chanja abinda nayi niyya yau ko da zip zaki saka a bakin"


"Hammana me kayi niyya?" tace jiki a mace.


"Good ashe da bakinki...idan na fito daga wanka zan fada miki, abinda na sani dai shine...." ya juyo da ita suna fuskantar juna tayi saurin runtse idanu. Matso da fuskarsa yayi saitin ta sosai "muna da alkawarin massage idan kin manta zan tuna miki"
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Bai jira cewarta ba ya saketa ya kama rigarsa zai cire. Da sauri ta bar dakin ta rufe masa kofa tana haki ita dai yau ta shiga dari. Awwab kuwa dariya yayi ya wuce yayi wanka shima yayi duk wani abu da ya saba na shiri bacci.

Tana zaune tsuru kamar wadda ta yiwa sarki karya ya bude kofar dakin ta dago kai da sauri suka hada ido. Kayan bacci ne a jikinsa na cotton riga mai gajeren hannu da dogon wando. Wannan kamshin da yake janta gareshi ta soma shaka ta lumshe ido a hankali. Kusa da ita ya zauna ya bude ledar kazar da take da zafi har yanzu sai kuma ya mike ya dauko robar maltina daya a fridge ya dawo.

"Cire hijabin kici abinci"

"Ni dashi zan ci"

"To babu laifi shi ma bazai hana ango abinda yayi niyya ba" yace yana kashe mata ido.

Turo baki tayi cikin shagwaba "ni wallahi tsoro kake bani Hammana. Me kayi niyya"

Mischieviously yayi murmushi "nothing...ahhh bude baki" ya mika mata naman.

Kasa karba tayi ta sunkuyar da kai. Ya kula dai yau da rigima a tare da ita sai ya dauko remote ya danna tunda an jona komai na tv din ya shiga neman channel din da zai bari a nilesat. MBC 2 ya kai ana wani film ya tambayeta ko tana son gani tace eh da sauri.

"Zan barki ki gani amma da sharadin zaki cire wannan hijab din muci naman nan if not yanzu zamu shige daki..."

Kafin ya kai karshe ta yiwa hijabin masauki akan wata kujerar yaji numfashinsa ya tsaya na yan dakiku saboda kyaun da tayi masa. Gashin ta ta kama ya zare ribon din ya zuba a bayanta da kafadu. Wannan lallen da tayi yasa kan yayi kyau sosai inda kalar ta fito ya zura yatsunsa a ciki yana rufe idanu.

"I love this Alheran" ya janyota kusa dashi sosai yana yamutsa mata gashin.

A gefen jikinsa ya rabata ya shiga bata naman yana ci shima. A haka suka koshi yace tayi zamanta ya kwashe komai zuwa kitchen. Sauran ya saka fridge ya wanko hannunsa ya dawo. Miko mata hannu yayi yana son ya taso

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment