Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Alhajin ne masu cinye miki lokaci?"


Tana ta tura baki suka shiga wajen matan Alhajin daga nan ta bishi falonsa. Sun gaisa yayi masa barka da dawowa shi kuma Alhajin ya bashi karamar robar zamzam da dabino ya karba da godiya. Ganinsu da yayi da jikar tasa ya faranta masa rai sosai. A son ransa zuri'arsu suyi ta auren junansu yadda za'a sami hadin kai mai dorewa har jikoki.


"Dan bamu wuri zanyi magana da yayanki Ghazalatu"


Shikenan za'a sake ci mata lokaci ta ayyana a ranta. Zaman da tayi don ta sami damar fita dashi ne kada Alh Baba ya dauko doguwar hira a tsakaninsu. Iyakarta bakin kofa ta makale daga gefe da zummar idan taji hirar zata yi tsayi ta koma tace ana kiransa. Abinda taji Alh Baba yana cewa ne yasa ta sake matsowa sosai don taji da kyau.


"Munyi magana da iyayenku jiya. Naji dadi kwarai da kuka hada kai da kanwarka. Kuma na yanke cewa ayi auren nan da wata uku. Ina fata zaka iya shiryawa kafin nan."


Wani tsalle Ghazalatu ta daka daga inda take. Awwab godiya yayi masa sosai yana murmushi.


"Sai dai Mustapha ya kawo wani hanzari na cewa ya nema maka auren yarinyar abokinsa batare da sanin kana neman Ghazalatu ba"


Gabanta taji ya fadi don ta sani babu wadda ake nufi ko da ba'a ambaci suna ba sai Radhiya yarinyar nan mai kwalkwalin kai.


Kansa a kasa cike da ladabi Awwab yace "hakane Alhaji"


Tsohon ya gyara zamansa yana kallon jikan nasa "tun a jiyan na fada masa sai a basu hakuri tunda kana da wadda kake so bai kyautu ace sai ka aureta ba. Ni a tsarina ma Allah Ya gani nafi son ku rinka auren junanku. Ita idan aurenta ya tashi sai yayi mata duk abinda uba yake yiwa 'yarsa"


Wannan shine son kai. Babu yadda za'ayi Awwab yayi shiru da wannan magana ya karbi hukuncin Alh Baba batare da ya gabatar masa da nasa uzurin ba.


"Alhaji kayi min izini na auresu su biyu. Ina iya fara auren Ghazalatu sai na aureta daga baya"


Rai a bace ya soma fada "abinda uban naka ya turoka ka fada min kenan. Wato saboda jiya nace ban yarda ba shine kai ka shafawa idonka toka zaka yi min rashin kunya?"


"Alhaji kayi hakuri ba haka bane"


"To nace na soke bazaka aureta ba. Banda son dorawa kai wahala ina zaka kai mata biyu Muhammad? Idan kana son yiwa mahaifinka biyayya ne kaje abinka shima ai karkashina yake"


Ran Awwab sai kuna yake ya kasa daurewa "Alhaji wallahi ina sonta"


Kallon da Alh Baba ya watsa masa a lokacin kallo ne na tsananin bacin rai.


Ghazalatu da ta gama jin komai hankalinta bai tashi sosai ba sai da taji furucin Awwab. Kuka ta fashe dashi ga bakinciki ga kishi ta bar wurin a guje. Daga Alhajin har Awwab sun jiyo muryarta.


"Ka tashi kabi sawun kanwarka ku daidaita. Na gama magana Muhammad bana son sake jin wata magana"


"Alhaji...."


"Ka tashi ka tafi nace"


Yana fita daga falon waje ya nufa ya shiga mota ya kifa kai akan sitiyari.


"Ya Allah" ya furta a hankali ko ina na jikinsa yana cikin tashin hankali. Bazai taba iya hakura ko rabuwa da Alheran ba. Ya barta a kira shi da me? Butulu ko mayaudari? A cikin abinda bai gaza sati biyu ba ya fada matsananciyar soyayyarta kuma itama ya koya mata sonsa. Akwai kunya da nauyi sosai tsakanin iyayensu wanda bai cancanci a sanadiyarsa ya kawo wata baraka a tsakani ba kamar yadda baya fatan kawo baraka ga danginsa. Shi da Ghazalatu sunyi dumu dumu a cikin dangi. Idan baka dubesu ta nan ba zaka dubesu ta can. Hadi ne tun daga kakanni an cakude da juna.


Dakin mahaifiyarta Mummy Gambo ta wuce kai tsaye tana kuka kamar ranta zai fita. Babu abinda yake mata yawo a ka sai jin da tayi Awwab da bakinsa yace yana son wannan yarinyar.


Mummy ta taso ta tarbeta da sauri "me ya sameki?"


"Mummy Yaya ne...Yaya Awwab baya sona"


"Ban gane ba, idan wani shirmen fadanku ne dama kada ki soma gaya min. Kije can ku sasanta"


"Mummy wata yake so. Yaci amanata wallahi 'yar wannan makauniyar da ta zauna gidansu yake so"


Nata hankalin sai yafi na Ghazalatu tashi "dena kuka bari na kira Hassana naji daga bakinta."


Mami tana daki da Zahra wadda take ta kuka tana bata hakuri Mummy ta kira. Shawara ta yanke gara ta sanar da ita ko Hussaina su tayata bawa Zahra baki.


Sai da ta saita muryarta don ita din ma zuciyarta a karye take "Mummyn yara yanzu kuwa nake shirin nemanki."


"Kina shirin nemana ki fada min kun yiwa Awwab mata ko" tace cikin gatse.


Mami da bata san wainar da ake toyawa ba tayi dariya "hala yazo ya fada miki. 'Yar wajen Mairama ce. Kin ganeta ai wadda tazo ta kwana mana biyu matar ....."


Kit taji shiru Mummy ta kashe wayar. Kallon wayar hannunta tayi da mamaki sai kuma ta soma kiranta missed calls  biyar bata dauka. Abin ya dameta ta lallaba Zahra ta fita ta tafi dakin Daddy.


Mummy Gambo ta cika tayi fam. Ita Mami zata wulakantawa 'ya har tana fada mata wadda suka zabawa Awwab. Kenan basu aminta da ya auri Ghazalatu ba. A tunaninta tafi karfin haka a wurin 'yar uwarta ta. Kallon Ghazakatu tayi da take ta kuka tana rarrashinta ta kira Daddy Haroun a waya don ya fita unguwa. Cewa tayi kawai ya dawo gida babu lafiya yace to.


Mami tana zuwa dakin Daddy shi kuma ta same shi yana waya da Alh Baba yana ta ban hakuri. Alh Baba yace ya fadawa Awwab lallai aurensa da Ghazalatu babu fashi. Wurgi ta ga yayi da wayarsa ta karaso kusa dashi da sauri.


"Daddy lafiya?"


"Ki bari muyi maganar nan bayan bikin su Fauziyya kamar yadda Alh Baba yace"


"Wallahi hankalina ya tashi. Tun jiya ka chanja min gabaki daya. Yanzu Gambo ta kirani tana cewa munyiwa Awwab mata nace mata eh kawai ta kashe wayar kamar wadda na yiwa wani abu"


Ran Major tuni ya soma baci kuwa. Yasan Gambo da masifa amma baya son duk abinda zai sosa ran Mami. Ga dadin haushin akan 'yarta ne ake son kirikiri a gwada son kai. Meye matsalar ya auri mata biyu da za'a ce dole sai an janye maganar Radhiya. Radhiya diyar Zayyanunsa.


Sallamar Awwab din suka rinka ji kana jinsa kasan baya cikin nutsuwa. Izinin shigowa Daddy yayi masa yana zuwa ya zube masa.


"Daddy Alh Baba yace bazan auri Alheran ba. To wallahi idan bai amince ba itama Ghazalatun na rantse da Allah ko an daura sai na saketa"


"Kai Awwab, kana cikin hankalinka kuwa? Daddy me yake faruwa ne kun kara sakani cikin duhu"


"Fita ka tafi dakinka" Daddy yace ransa shima a baci. Dakin gabadaya ya juye walwalar ma'abotansa ta fi kamar an kadata da iska.


Tattaro nutsuwarsa ya daure yayi ya fadawa Mami halin da ake ciki. Boyewar bata da amfani tunda Gambo ta sani.


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yanzu sai Gambo ta ga kamar da gangan nayi"


"Gambo kike ji ko kuwa halin da Awwab zai shiga da yaran nan"


"Daddy ni fa ban ga wata gagarumar matsala a cikin wannan abu ba. Awwab namiji ne saboda haka zai iya aurensu duka. Ciki mu mun isa muce ga wadda zai zaba ya bar dayar? Babu wadda mahaifinta baiyi mana halacci ba saboda haka ka kwantar da hankalinka in sha Allahu komai zai zo da sauki"


A sanyaye yace "Alh Baba yace bazai auri mata biyu ba kuma su Baba sun amince"


Kanta ta dora akan kafadarsa ta kwantar da murya domin kwantar masa da hankali "mu bi komai a sannu saboda kuskure daya zai iya janyo mana rikici a dangi ko tare da iyayen Mairama wanda bana fata. Gobe muje mu roki arzikin suyi hakuri su amince ya auresu su biyun"


Kalamai masu kwantar da hankali ta rinka amfani dasu wurin sanyayawa mijinta rai suka dauki dogon lokaci suna shawara akan wannan matsala.


Tunda Awwab ya shiga daki bai fito ba sai asuba. Kallo daya Major yayi masa ya san cewa da wahala idan ya runtsa. Soyayyar Awwab da Alheran daga Allah ce. Ya tabbatar duk wannan tashin hankalin saboda an hanashi aurenta ne.

**********


Da wuri aka gama komai na sallamar Ummi daga asibiti. Abin da mamaki matuka ta shafe shekaru kusan goma da makanta yau ita ce take da idanun kallon Radhiya da Karami. Bayan an bata gilashinta tana kallonsu ta fashe da kuka. Karami bai baro mahaifinsa da komai ba sai fari da ya dan dara shi wanda ta alakanta shi da kuruciyarsa sai kuma tsaho da shi Zayyan din yafi dan nasa. Radhiya kuwa tafi dauko kamanni da ita sai dai ta rasa inda ta samo wannan kirar jiki. Mairama doguwa ce siririya mai kyaun sura da daukar ido yayin da Radhiya take a murje babu rama amma baza'a a kirata mai kiba ba. Jikinta a cike yake ko ta ina. Yanayin hancinta sam baiyi kama da na Umminta ko mahaifinta ba. Idan tayi murmushi sai kaji kamar ka dauketa saboda yadda fuskar take nuna zallan yarinta idan kumatunta ya lotsa ciki.


Lokacin da suka hada ido da Zainab sai sabon kuka.


"Haka kika koma wata 'yar gayu Zainab dina"


Yaran suna dariya iyayensu suka rungume juna. 


"Muje gida kafin ki bar garin nan sai kin zama 'yar gayu kema. Ba biki zakuyi ba....hmmm Allah Mairama sai nasa idanu sun koma kanki a wurin bikin nan" suka yi dariya.


A gaban mota Ummi ta zauna Radhiya da Nene Marka suna baya. 'Yan samari kuwa adaidaita sahu tace su shiga su biyo bayansu.


Sunje gida Ummi ido ya bude ta ga halin da Baba Hadir yake ciki. Tana kuka Zainab tace mata kada ta jangwalo idanun tayi hakuri haka. 


Motsi kadan Radhiya sai ta kalli wayarta babu kiran Awwab. Yadda baiyi bacci ba jiya yau ma hankalinsa gabadaya ya tashi ne saboda rigimar dake neman kunno kai a gidansu. Mami da Daddy sunje har gidan Alh Baba akan ya duba lamarin wanda zuwan nasu ya sake harzuka shi. Mummy da ta sami labari ko kallon arziki ta kasa yiwa yayarta. Ga Ghazalatu ta kwana kuka kuma tsabar wulakanci ko aurenta ba'ayi ba ace suna rokon a auro harda wata. Domin su tsayar da abin haka suka yanke shawarar bari a fara bikin da Ghazalatu. Idan yaso bayan ko da rabin shekara ne Daddy zai sake yiwa su Alh Baba maganar. Kwanaki biyu suka yi ana wannan tashin tashina. 


A Kano kuma Mama ta bude wuta wurin gyara 'yar uwarta Ummi da 'yarta Radhiya. Salon ta kai Mairama da aka gama gyara kan akayi steaming sai ta sake komawa yarinya kyaunta ya kuma bayyana. Radhiya ganin Umminta a steamer harda kuka wai ita ya kamata a yiwa wannan gyaran amma saboda Innawuro bata sonta gashi yanzu tana ji tana gani babu damar shiga. Mai salon taji sai mita take tana fulatanci tana hausa ana ta kiran Innuwuro tace mata tazo ta shiga.


"Soya min fatar kai zaki yi ko"


Matar tayi dariya "gyara dai kanwata"


Bisa tsautsayi ta tuge dankwalin Radhiya wai zata yi mata gyara kyauta sai abin arziki ya bayyana kowa ya gani. Allah Yasa kan ya hade yayi baki sidik gashi ya soma tofowa. Amma duk da haka ranta ya baci ta tashi ta hade fuska tana kallon matan da ake yiwa gyara.


"Yasin mace tayi dariya in rangada mata balotelli ta tafi dashi gida"


Kana ganinta kasan ko bata aikata ba to dai zasu ji ba dadi. Mai salon ta koma bata hakuri sannan tace tazo tayi mata gyaran farcen hannu da kafa da steaming din fuska. Shikenan ta manta da fushin ta shiga jerin gyara tana ta firirita yau gata a salon. Kafin su bar wurin tasa mata da yawa dariya. 


Washegari ana gobe zasu tafi mai kunshi tazo ta rangada musu baki da ja. Ummi dai safa ta saka a kafarta tana jin wani iri. Rabonta da ado haka tun Zayyan bai tafi Liberia ba. Yanzu kam wa zata yiwa. Nene kuwa sai zuga Mama take yi wai a gyare mata 'yarta ta samo miji dan ubansu.


Radhiya da Emzee suka taru suka rafka mata uwar harara sai da Mama ta hade kawunansu ta gwara.


"Nenenmu kuke harara"


"Mama wai miji fa take cewa, Ummi ke da aure sai a aljanna ke da babanmu" Emzee yace da dukkan seriousness.


"Maza iyayen kishi" Mama tace tana tuna lokutan da Ibrahim yake yi mata kunkuni akan me yasa ta tafi tabar babansa.


Ranar wuni suka yi ana ta gyare gyare saboda tafiyar su Mama da ta matso kusa sosai. Ibrahim zai koma gidan kakaninsa ya jira dawowarsu. Da safe ta kaisu tasha. Nene tayi ta yi musu addu'a ita da iyalinta tana fatan Allah Yasa a dace mijinta ya sami lafiya ya dawo da kafafunsa. Kamar kar su rabu ita da Ummi. Emzee ma dai dokin budewar idanun Ummi yasa zai bisu Sumaila. Ba don haka ba jira zaiyi sai sun tashi nan da kwana biyu sannan ya koma.


Sai da suka tashi Mama ta koma gida tare da Ibrahim mai nuna hanya. Suna isa Aisha 'yar wajen Alh Musa ta kirata. Sun gaisa da ita da kanwarta tace mata ga Mamansu su gaisa. Matar mai mutumci suka gaisa da tambayar juna iyali.


"Antin yara na bugo ne nayi miki godiya irin dawainiyar da kika sha da yaran nan. Na dawo gidansu biki ya matso babu abinda baki saya kin ajiye ba. Don Allah ina rokon mu cigaba da zumunci."


"In sha Allahu. Nagode"


"Ina fata kuma zaki zo bikin 'ya'yan naki"


"Ahhh banyi alkawari ba."


Nunawa tayi bata ji dadi ba har tana tambayarta ko don sun rabu da Alh Musa ne. Mama tayi dariya tace mata tafiya ce a gabanta zata kai mijinta asibiti. Maman su Aisha ta tausaya mata ta kuma jinjina mata wannan sadaukarwa da ta hanata zama gidan mutum kamar Alh Musa mai kudi da halin dattako. Bata yi kasa a gwiwa ba bayan ya dawo daga wurin aiki ta fada masa. Abin yafi taba shi duk da yasan ta koma gidan tsohon mijinta amma sai da yaji wani iri. Soyayyarta da tausayinta duka a hade. Nasa salon kaunar shine ya tura mata miliyan biyu da rabi a matsayin gudunmawa. Mama tayi kuka a ranar yadda Allah ke budawa bawanSa a lokacin da bai taba tsammani ba. Aurenta da Alh Musa ta yarda silar arzikinta ne da nemawa Hadir waraka.


A Sumaila kuma su Ummi sun isa gida ya fara cika da 'yan biki. Yawanci 'yan uwansu ne na bangaren Malamijo. Washegari kuma sai ga dangin iyayen amaren mata su ma sun fara zuwa. Innawuro da matan su Baffa Gide duka sun iso. Ranar ne za'ayi Kamu amare kowacce dangin uwa na kokarin rufa mata asiri. Shi dai Malamijo tunda ya bada abinda zai iya ya janye hannuwansa. Duk wannan abu da akeyi Salame bata samu zuwa ba saboda bata ma da kayan sawa ta shiga taro ga yunwa kamar taci babu ita da 'ya'yanta. 


Ranar da yamma Nene ta rufa mayafi ta tafi gidan Salamen. A gaban murhu ta sameta tana ta uban kauri. Tsaki ta samu zata yi musu danmalele ita da yaranta suci. Girman kai ya hana ta kwantar da kanta gaban mahaifinta komai lalacewarsa ta nemi taimako. Taji labarin Mairama tana gidan amma bata gabanta tunda tasan ba ido gareta ba bata da abinda zata tsinanawa kanta ma. Kauyen da akace ta koma na dangin babarta ta tabbatar kila wahala kawai take sha daga ita har yaran. 'Yan lokutan da suke zuwa Sumaila lokacin tana shanawa a jikin Indararo bata ma zuwa gidan don kada a fara yi mata bani bani. Sai gashi a kasa da shekara guda duniya tayi mata juyin waina...sama ya koma kasa.


Idanu jazur ta dago tana fyace majina da gefen mataccen zaninta sannan ta kakalo murmushin dole.


"Nene kece a gidan namu yau?"


Rai a bace Nene Marka tace "nice Salame, cewa nayi bari nazo na gaishe da hamshakiya matar Alhaji tunda kinfi karfin kowa."


Kamar wata gaula tana fama da cikin da yake neman rinjayarta tace "to ni me nayi"


"Ban sani ba Salame. Mahaifinki ya kwanta ciwo yaci ya cinye har ya warke babu ke babu inuwarki balle asa rai da mijinki ma zai je. An kai lefen kanenki baki je ba yanzu don tsabar bakin hali ana biki a matsayinki na babbar 'ya a gidan kin gagara zuwa kuna gari daya. Anya Salame kin dauko hanya mai bullewa kuwa?"


Da kunya taje gidan nan bayan kowa ya santa a lokacin da take tsaka da jindadi dama kiris 'yan bakinciki suke jira ayi mata dariya. Jiya Ta Madina tazo har gidan itama ta kare mata tanadi wai kanwarta ta haihu bata je ba. Yaran da suka gama rainata suke murna da talaucinta.


"Kin dai ga yanayin da nake ciki dama shi kuke buri shiyasa babu wanda ya damu dani"


"Kaniyarki, idan zakiyi fitsararki kada kiyi min bazan miki da dadi ba. Idan ban ganki a wurin bikin nan gobe ba wallahi sai na saba miki. Mutuniyar banza wadda bata sawa zuciyarta komai ba sai kyashi da hassada. Malamijo ya cuceku wallahi"


Bayan fitarta Salame kuka ta saka. Tana ji tana gani ta zama bolar gida kuma miji yaki ya saketa ko tasan matsayinta. Tana cikin wannan halin ne kamar daga sama Halifa yazo. Matashin saurayi dan gatan Alh Salisu. Yaron babu abinda ya nema ya rasa a wurin mahaifinsa sai dai abu guda. Da matukar wahala babansa yake bashi kudi idan zai zo Sumaila. Da can yana bashi sai ya zamana Salame tana karanta masa bukatunta idan zai sake zuwa. A hankali Alh Salisu ya fahimci cewa kudaden da yake bawa dan nasa aikinta ne ko kunya babu. A yadda yayi matukar tsanar halinta tuni ya dakile hakan. Taje can ta karata idan Halifa ya soma sana'a yayi mata da nasa gumin.


Tsabar murna ji tayi kamar an ga watan sallah. Ta rasa inda zata saka kanta don dadi harda yada habaici wa Maman Danmama danta yazo. Shi dai kunyar irin wannan abubuwan nata yake yi to amma uwa uwace. Bai wani dade ba da zai tafi ya bata dubu biyar cikin abinda ya rage masa. Salame duniya tayi dadi ta rasa ina zata kai farinciki. Dreba ne ya kawo shi kuma yana jiransa ya tafi dashi. Dan cikinta a wannan hadaddiyar mota harda dreba. Kai inama dai ta kwantar da hankali a gidan Alh Salisu.


Washegari bayan sunci fara da mai harda hadin salak da kifi sukunbiya ta shirya 'ya'yanta kowa cikin kayan sallarsa na bara kafin Alh Indararo ya banzatar dasu. Itama wani leshi ta saka cikin irin alkhairin da ta samu albarkacin aikin malamin tsibbunta wanda ya fita yayi yanzu. Mayafin ma irin mai bakin leshi da ta dade da dena sakawa ta dauko don na yayin duk sun mutu babu na mora.


Tana tsakiyar yaranta dayake tafiyar kafa ce zata kaita gidan tana murmushin jindadi. Yau 'yan bakinciki sai dai su mutu. Tana nan kuma har yanzu tana damawa don tasan da wuya a sami mai dressing irin nata.


Ta kusa gidan bai fi taku kadan ya rage ba ta ji dirin motoci a bayanta sun taho a guje. Kana ganinsu kasan tafiya ce ta jerentawa wato convey. Motoci ne da suka amsa sunansu mota masu masifar kyau da daukar ido duka a maimakon nambar mota an rubuta G. AGALI wato Ghousman Agali kakan Zayyan Muhammad Tureta na wurin uwa.


Guda takwas ne sai kuma helux guda biyu da aka ciko su shakare da buhun hunan kayan abinci da lemuka na kwali da na roba. Mota cikon ta tara da ta fita daban da sauran duk da cewa itama tana da kyau sosai Awwab ne a ciki. Shine yayi musu rakiya zuwa garin Sumaila domin cika umarnin mahaifinsa da hada masoyiyarsa da dangin mahaifinta. Daga ita har Ummin an kasa samunsu a waya bare a sanar dasu zuwan bakin.


Sanye yake da wando chinos mai kyau coffee da shirt cream wadda ta dan kama shi. Idanunsa ya karesu da bakin glass wanda ya kara haska fuskarsa ya kuma boye bacin ran da yake kwana yake tashi dashi tun komawarsa Katsina. Umarnin Daddy yake son bi na kauracewa Radhiya har zuwa ayi bikin gidansu sati mai zuwa a gama sannan su sake tayar da maganarta. Yana ganin wayarta da text wanda bayan kwana biyu babu reply ta dena yi. A tunaninta ya koma ga Ghazalatu ne ya manta da ita shine take kishi tayi fushi ta share shi. Matsananciyar kewarta ce ta sanya shi cewa zaiyi musu rakiya batare da an nema ba. Daddy yasan dalilinsa kuma yana tausaya masa. Lokaci guda har ya soma rama ga maganganu sunki ci sunki cinyewa a dangi.


Salame dai sakin baki tayi tana mamakin wadannan kyawawan mutane mazansu da matansu da suke fitowa daga motocin alfarma irin wadannan wurin wa suka zo? Ko sunyi batan kai ne? Kila bakin Chairman ne ko gidan Hakimi.

***********


Su Alh Ghoumar tun kafin su iso cikin garin Katsina suka sanar da Major suna tafe. Da suka zo gabadayansu sun kwana a wani hotel ne da safe shi da Alh Sidi da mutum biyu cikin 'ya'yansu suka je gidan Rtd Major Mustapha. Yayi farinciki da zuwansu ya sake basu labarin duk yadda ta kasancewa Mairama da su Radhiya. Guda cikin wadanda aka je dasu wanda shine auta a 'ya'yan Alh Sidi mai suna Ridwan yace zai maka Maikudi a kotu domin ya ha'incesu ya fada musu karya game da iyalin dan uwansu.


Major baiyi yunkurin bada hakuri ba yace idan sun dawo daga ganinsu din sai su je Sakkwaton. 


"Amma meyasa baku ce a kawo muku su ba kuka taho gabadayanku?" Ya tambayesu da murmyshi a fuskarsa.


"Domin mu nunawa duniya cewa Mairama, Alheran da Zayyan dangin mahafinsu suna kaunarsu. Waye zamu samu ya rakamu saboda drebobin namu biyu ne kawai 'yan kasar nan"


Awwab kamar jira yake dama yazo gaishesu ne da Mami tace sun iso shine yace zaije. Daddy bashi da niyar hana shi saboda tausayinsa yake ji yana mamakin irin wannan soyayya mai karfi da ta shigi dan nasa farat daya.


Fitarsu daga gidan ko awa daya ba'ayi ba Mummy Gambo da Hussainar Mami suka zo. Ba da mutumci suka zo ba su Fauziyya na gaishe su babu wadda ta amsa.


"Ina babar taku?" Hussaina ta tambaya a dakile.


"Hussaina kenan, gani...kai ku bamu wuri" tace dasu Zayyana, suka tashi kuwa suka yi daki da sauri.


Zama tayi domin su gaisa Mummy ta soma fadan da ya kawota.

"Saboda wata yarinya can bare da babu wata alaka tsakaninku Hassana kike neman bata mana zumunci? Awwab da bakinsa yace yana son auren Ghazalatu amma tashi daya zance ya sauya saboda kuna son ku burge wasu"


"To banda ma abinta akwai wani abu da ita yarinyar tafi Ghazalatu ne? Alh Baba da su Babanmu sunce basu yarda ba ba sai ku hakura ba. Amma ace da kanki kuka je har gabansa don ya amince a bar danki shafaffe da mai ya yi auren gata mata biyu lokaci guda"


Daurewa take yi suna ta caba mata maganganu a ganinsu ita ma bata son 'yan uwanta su rabeta ne.


"Banda naci irin na Ghazalatu nace mata ta hakura da yaron nan taki. Wallahi ba don tana son shi ba har yanzu bazaki sake ganina a gidan nan ba. Nayi zuwan karshe ne inji menene ya sanya baki son auren nan?"


"Gambo idan Hussaina bata fahimta ba ta biye miki kun hade min kai nayi zaton ke zaki fahimta tunda mun zauna tare kin kuma san komai game da iyalin Zayyan. Wallahi da munsan da batun Ghazalatu Daddy bazai taba zancen wannan hadi ba. Ku duba irin kunyar dake tattare da ya koma yace musu an fasa auren nan"


"Ke kuma gara a kuntatawa 'yar kanwarki da yaji kunyar cewa 'yan kauye an fasa auren 'yarsu. Na tabbata 'yar dubu hamsin aka mika musu magana ta mutu har abada" cewar Hussaina.


"Ki barta tunda Umma tace mu kyalesu mu zuba musu ido daga ita har yaya Mustapha din. Saboda rashin sanin darajar zumunci kun shirya batawa da kowa..."


"Ke har zaki fada min zumunci Gambo" Mami tace rai a bace su Fauziyya suna jiyota daga daki kamar yadda Daddy yake jiyota daga falonsa da bai taso ba bayan tafiyar su Awwab.


"Kinsan me na rasa saboda zumunci? Farincikin 'yata, irin wanda kike nemawa taki 'yar amma saboda zumunci, saboda bin umarnin iyaye, saboda kada nayi sanadin rushewar ginin da iyayenmu suka fara nasa kafa na take farincikin Zahra"


Daga cikin dakin nasu Fauziyya ta zubawa yayarta ido yayin da Zahran ta fashe da

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment