Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana musu zancen tafiya hotel Excellency yace ko ruwa bazai iya sha ba sai ya ga Zayyan tare dasu.


**********

Kararrawa aka buga lokacin cin abincin dare yayi 'yan prison din suka soma fitowa daga dakunansu da aka bude. Kusan kullum cin abincin tamkar yaki ake yinsa kowa na sauri ya sami abin arziki.


Tafiyar nan tasa da dogayen kafafunsa yake yi cikin nutsuwa ya isa layin ya tsaya kenan wani kato yazo ya sha gabansa. Sai ya ja baya ya bashi wuri saboda gudun rigima. Sati uku da kwanaki da tafiyar Chibuzor dan guntun hope din da yake dashi gabadaya ya tafi. Fadawa kansa yake yi ya cigaba da hakuri da kaddarar rayuwarsa me yiwuwa shi da iyalinsa sai a lahira. Shi da kasarsa kuma sunyi bankwana kenan. Rikici ne ya kaure daga gaban inda ake rabon abincin garin dambe aka zubar da kulolin abincin a kasa. Mutane kuwa suka dira akansa suna wawaso ga gandirobobi suna ta kokarin raba su.


Yau ma bashi da abinci kenan zaiyi kwanan yunwa ya juya a nutse zai koma dakinsu. Da rana wani tsoho ya barwa nasa saboda ya taho zai zauna irin shakiyan nan wani yasa masa kafa yayi tuntube ya fadi. Yanzu kuma abincin duka an zubar. Ya kusa isa dakinsu yaji da karfi ance.


"LIEUTENANT ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"


Tunda ya shiga kurkukun nan sunansa 3810 sai ko mutanen da suka san sunansa kalilan amma su dinma  numbar tasa suke kira. Gabansa ne yayi mugun faduwa ya juyo da sauri. Babban prison Warden dinne da kansa ya shigo wurin. Wannan salon tafiyar tasa da shi kadai ya iya kayarsa yayi zuwa gaban mutumin. Ga mamakinsa sai ya ga ya cire hularsa ya maketa a kasan hannu daya sannan ya gyara tsayuwa ya sara masa. 


Habawa sai idanu suka tattaru a kansu shi ma sai yayi saluting mutumin yana jin idonsa ya soma ruwa domin hasken da ya fara hangowa na rayuwar 'yanci


"This way Sir" Chief Warden yace masa ya bi bayansa. Sun fara tafiya ya juya ya kalli prison din da jama'ar cikinsa sai ya tsaya at attention ya kame yayi saluting dinsu. Da yawansu su ma sai suka yi masa wadanda suka taba jin cewa soja ne suna taya shi murna.


Wani office aka kaishi Chief Warden ya bashi takarda ya saka hannu a kai sannan ya kuma gyara tsayuwa.


"Kai jarumi ne da ban taba ji ko ganin kamarsa ba. Kasarka bata san kana raye ba tsahon shekaru ashirin da biyu sai yau zaka koma gida. Ba kai nake tausayi ba sai ire irenka da dama da suke da rai a hannun abokan gaba ko kurkuku irin wannan batare da an sani ba. Goodbye Lieutenant"


Musabaha suka yi sannan ya kuma nuna masa kofa suka fito tare. Wani gate da bai raba sanin akwai shi ba duk tsayin zamansa a wurin suka bi sai ga motoci biyar a jere na Nigerian Embassy dake Liberia a baya kuma wasu uku ne na sojojin kasar.


Motar tsakiya aka nuna masa ya shiga yana jin kansa kamar a ire iren mafarkan da yake yi na komawa gida. Cikinta ma sojoji ne da sai suka yi saluting dinsa suka shiga aka tayar. Jiniya ce tun daga prison din har babban ofishin jakadancin Nigeria dake Liberia. 


Awwab ya kasa zaune ya kasa tsaye haka ma Excellency. Duka a waje suke daidai kofar shiga tare da Ambasadan suna tsaye zugar motocin nan suka jeru a gabansu.


Kafin ya yunkura an bude masa kofa ya sako kafarsa waje sanye da takalmin roba da ya mutu murus. Kayan jikinsa a kode suke sosai. Fatarsa kuwa bai san cewa ta shiga wani yanayi ba sai da ya ga mutanen dake tsaye a wurin sun zuba masa ido.


"Uncle" yaji ance da muryar da ya sani. Chibuzor ne ya taho wurinsa da hawaye yabe yabe a fuska. Zayyan ya rungume shi.


"My son I owe you my life"


"And I owe you mine" yaji wani ya fada daga bayansa. 


Sannu a hankali ya juya yana kallon mutumin dan lukuti ga tumbi amma komai nasa yana nuni da cewa ba karamin mutum bane. Ina yasan fuskar nan yake ta tunani.


"Baban Alheran kayi hakuri banzo da wuri ba"


Zuciyarsa ta nemi bugawa don bai manta mutumin da yake kiransa da wannan sunan ba. Sai yanzu yaso ganin kama. Bakinsa yana rawa yace  "Baban Arifah? Col. Nasiruddeen?"


Rungume shi yayi suka fashe da kuka a tare mutane na kallonsu wasu suna yi. 


Ga Awwab kuwa babu inda baya rawa a jikinsa. A yau ya yarda soja daban namiji daban. Duk yadda yake son ya dake kwanansa nawa yana kuka saboda jin cewa Babansa Zayyan yana nan amma babu tabbas sai ido ya gani. Shekarun da yawa amma tabbas shine wannan mutumin da ya ga duniya kuma duniya ta ganshi.


Muryarsa tana rawa yace "kaine Tureta?" Yadda ya taba yi masa farkon haduwarsu.


Zayyan ya dago kansa daga kafadar Excellency yayi masa murmushi "nine yaro. Ka sanni ne?"


Tsigar jikin Awwab har tashi tayi a lokacin da ya kamo hannuwan Zayyan duka biyun "sunana Muhammad Awwab Mustapha...ka tuna ni?" Ya kare tambayar da kuka.


Wasu sababbin hawayen suka sauko daga idanun Zayyan jikinsa shima yana rawa ya sanya hannuwansa biyu a gefen kumatun Awwab da suke tsayi kusan daya.


"Awwab din Mairamata?"


Awwab ya gyada kai nasa hawayen suna gudu kamar famfo baya tunanin yin komai domin tsayar dasu.


"Major da Hadir fa?"


"Suna cikin koshin lafiya"


"Mairama?"


"Na barota lafiya"


"Alheran dinka?"


"Tana jiran Daadaa yazo ya aura mata Awwab" yace yana murmushi mai hade da kuka. Zayyan ma sai ya fadada murmushinsa.


"Cikin jikin Umminka?"


"Alive and well sai munje gida zaka ga ko mene"


"Awwab?"


"Daadaa"


"Nayi kewarku, nayi kuka, nayi hakuri nayi hauka duka a rashin sanin makomar rayuwata. Ku kaini gida...ku kaini wurin iyalina"


Kankameshi Awwab yayi suna kuka sosai abin tausayi da tsinka zuciya.








 
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Da ya fito Chibuzor yana tsaye can gefe ya gaji da magana ya koma yana sabunta tunani da nemarwa kansa mafita. Baiyi zaton haka abin zai zama ba gabadaya ya shiga cikin tashin hankali saboda tsoron kada ya kasa fitar da Zayyan.


Wancan mutumin ne ya dawo gareshi yace masa akwai mai wannan sunan da ya taba zama amma yanzu baya nan.


Wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa "a ina zan same shi? Sako nake dashi mai mahimmanci"


"Kana iya fada min sai na gani sakon yana da amfani ko babu"


Da dukkan murnarsa yace "na hadu da dan uwansa ne a prison...."


"You must be crazy" Sojan ya daka masa tsawar da ta janyo hankalin sauran da suke gefe. Shi kuwa Chibuzor jikinsa rawa ya soma yi. Tun ba yau ba yaki jinin duk wani abu da zai hada shi da hukuma. Sauran suka taru a kansa ana ta daga murya ya gigice. Fada suke yi kawai akan yazo musu da zancen banza. Meye hadinsu da prison da zai ce ya hadu da dan uwan dayansu. Dadin kayan haushin ma wanda yake magana a kai baya nan. Basuyi masa uzuri yayi musu bayanin da ya dace ba suka nemi dukansa ya gudu. A gajiye ya koma hotel din da yayi masauki ya kira matarsa Emma ya fada mata yadda ta kasance.


"Ka koma gobe ka dage sai sun barka kayi magana da wani mai mukami a ciki. Banda abinsu waye yake yanke hukunci babu sauraron bayani?"


"Gaskiya bazan iya komawa ba. Akwai matsalolin tsaro a kasar nan. Nayi sa'a da basu kamani sun rufe ba. Kallon wani mara hankali ina jin suke yi min"


"Yanzu me kake tunanin yi a kai?"


"Ban sani ba" ya fada cike da damuwa.


"Darling, me zai hana kayi amfani da media? Ka tuna nima fa a TV kawata ta ganka a news lokacin da aka kamaka a airport shine ta fada min"


Ihun murna Chibuzor yayi yana gode mata. Sam baiyi wannan tunanin ba yaje zai jefa kansa ga wahala.


Karfe goma washegari a gidan talabijin na NTA reshen garin tayi masa. Filin cigiya da sanarwa ya nema saboda a ganinsa gidan TV musamman na kasa wato NTA zai fi saurin zama hanyar yada cigiyar. Idan ya gama da nan niyarsa ya nemi gidan rediyo kuma a nan Sakkwato da Kano. Wata ma'aikaciya ce tayi masa bayanin cewa zai biya bayan ya fadi na kwana nawa yake so a rinka sanya sakon. Da suka gama da wannan ya fahimci komai ta bashi form da zai cike abinda yake nema.


"Idan akwai hoton wanda kake nema ko naka idan sun san fuskarka sai ka kawo"


"Babu hoto sai sunaye"


"Rubuta min a nan..." ta saka yatsanta a inda take bukata.


Chibuzor bai rike sunayen duka ba amma ya rubuta abinda ya tuna.


(Ina neman iyalin Lt. Zayyan Muhammad Tureta na Giginya Barrack Sokoto wanda ya tafi Liberia a 1993. Sunan matarsa Mariyama, yarinyarsa Al.....) duk yadda yaso ya kasa tuna sunan Radhiya da Zayyan ya fada masa wato Alheran (abokinsa Hadir da Mustafa da kuma Col. Nasiruddeen Aliyu). Sunan karshe shine wanda yafi zama sosai a kansa. Matar ya mikawa takardar zata duba domin tsara yadda sanarwar zata kasance ta karanta bayanin nasa bai wani gamsar da ita ba. Dole sai sunyi masa tambayoyi kenan yadda zai iya fadar me yake bukata kada ayi asarar kudi.


"Su wadannan baka san sunayen iyayensu ba domin saurin gano su?"


"Akwai matsala ne? Ban sani ba" ya bata amsa yana fatan kada tace bazai yiwu ba. "Amma ai wannan na rike, Col Nasiruddeen Aliyu.."


Daga bayansa wani ya taho rike da takardu ya dakata da sauri "Col Nasiruddeen Aliyu dai gwamnan Plateau? Me yayi? Ke akwai sabon news ne?"


"Ka sanshi ne? Nemansa nake" Chibuzor yace shima da sauri.


"Gwamna ne fa, waye bai sanshi ba? Me yake faruwa ne?" Ya tambayi matar.


Hannunsa Chibuzor ya rike "shi gwamnan soja ne? Yaje Liberia tsakanin 1993 da 1994?"


A dan tsorace mutumin ya zame hannunsa "tsohon soja ne yayi retire, amma ban sani ba ko yaje Liberia"


A gigice Chibuzor ya fito da wayarsa daga aljihu ya rattaba sunan Col. Nasiruddeen Aliyu a google search. Tashin farko sai ga bayanai sun bayyana game dashi. Inda yasan ana saurin samun bayani ya fara dubawa wato wikipedia. Karatu yake yana tsallaken layi kamar wani zai riga shi.


(Tsohon sojan kuma kwararren likita a wancan zamani ya tsunduma cikin siyasa ne wajajen 1996 inda tauraronsa ya rinka haskawa yayi suna cikin kankanin lokaci. Mutane suna alakanta wannan nasara tashi da cewa an sanshi a matsayin sojan da ya kwashi kimanin watanni takwas a hannun 'yan tawayen kasar Liberia kafin Allah Ya kubutar dashi wani dare da sojoji suka kai sumame a mabuyarsu. Tausayi da jarumtarsa da aka gani yasa bai taba tsayawa takara ya fadi ba)


Mahaukacin ihu Chibuzor ya saki yana dariya "thank you Jesus" sannan ya kaiwa mutumin nan wawura ya rungume shi kamkam sai da takardun hannunsa suka fadi. Bai tsaya bata lokaci ba ya dire mutumin ya fita daga ofishin a guje.


Kai tsaye hotel din ya koma ya tattaro kayansa ya tafi airport. Ba shi ya sami kansa a kofar gidan gwamnatin dake Jos ba sai yamma. Tunda ya gane wurin shawara ita ce ya nemi masauki gobe ya dawo. Haka kuwa akayi domin washegari takwas ma a bakin gate din ta riske shi. Ganin gwamna ba abin wasa bane. Masu gadi suka saka shi a gaba aka fara masa tambayoyi akan dalilin zuwansa.


"Sako ne zan bawa Col. Nasiruddeen"


Ganin wani mara da'a suke yi masa. Idan ba mara da'a ba ya za'ayi ya kira sunan gwamna a kofar gidansa kai tsaye irin haka. Shi kuwa dadewa rabonsa da Nigeria da kuma idan yazo ba yawo yake irin haka ba yasa ya manta abubuwa.


"Nasha wahala ku taimaka min"


"Ka koma ka nemi appoitment dashi ba wai kazo haka kawai gida ba. Idan kowa na iya ganinsa a gida duka garin nan zasu tare a nan kenan"


"Naji ta yaya ake neman appointment din?"


"Ka je office dinsa ka nema a can. Idan kayi sa'a ka ganshi a wata daya"


Suka kece da dariya. Wannan ko kadan baiyi kama da wanda Gwamnan nasu zai saurara nan kusa ba saboda ayyuka da suka sha kansa 'yan kwanakin nan. Sannan kuma ai ba haka nan ake ganinsa ba, akwai matakai da ake bi.


Bai hakura ba yace "yana gida yanzu ko office?"


"Yana office"


"Nagode"


Gefe ya koma abinsa ya tsaya a jikin katangar gidan. Da sauri cikin masu gadin mai kayan sojoji yazo yace ya bar wurin. Gaba ya kara amma duk inda yayi sai ace ya matsa wai ba wurin tsayuwa bane. Chibuzor baiyi zuciya ba don biyan bukata yafi dogon buri. Ainihin titin da ake yin kwanar dama a kansa a shigo titin gidan gwamnatin yaje ya sami inuwar wani gida da filawoyinsa suka hauro ta saman katanga ya tsaya. A nan ya wuni ko ruwa bai matsa ya saya ba saboda tsoron kada ya rasa abinda yake nema.


Gajiya, yunwa da shigowar sanyi wanda baya yiwa  mutane da sauki a garin na Jos sune suka sarke shi amma da yake mutum ne mai juriya da amana bai gajiya ba. Tunawa kawai yake yi da shekarun Zayyan a prison dinnan yana ji a ransa da yana da hali ko sakan daya bazai bari ya sake yi ba.


Tara da rabi na dare sai ga jiniyar motocin gwamna sun taho a sukwane. Ko kallon titin da zai tsallaka baiyi ba ya bi zugar motocin nan a guje yana harin ta tsakiyar wadda yafi tsammanin ita ce gwamnan ke ciki.


"Zayyan Tureta is alive"

"Zayyan Tureta is alive"

"Lt. Zayyan Tureta"

"Liberia prison"


Wadannan kalmomin ya rinka maimaitawa yana bin motocin yaki sauraron ihun da sojoji suke yi masa.


His Excellency Nasiruddeen yana bayam mota tsabar gajiya har soma gyangyadi yaji kalmar TURETA da LIBERIA. Firgigit ya bude idanu ya soma cewa "stop da car" cikin gaggawa. Dreban sai da ya tsorata amma shi da PA sun kula kamar ba a hayyacinsa yake ba duk ya rude shiyasa ya danna trafikato zuwa barin dama sauran motocin bayan suka tsattsaya suma. Yau babu batun jiran a bude masa kofa da kansa ya bude don sauri ya kusa faduwa saboda babbar rigarsa da ta harde shi. Wurin da sojoji masu tsaronsa suka danne Chibuzor a kasa ya isa yana yi musu tsawar su daga shi. Kowa darewa yayi gefe da suka ga ya durkusa ya tayar da Chibuzor zaune. Cikin harshen turanci yace masa

"Me kace?"


Jikinsa babu kwari sosai ya dago kai yana kallonsa "kaine Col. Nasiruddeen Aliyu?"


"Nine, nine" ya rinka nanatawa yana gyada kai.


Yana jin wata kakkarfar ajiyar zuciya da yaron ya saki don bazai fi sa'an Awwab ba.


"Sir, Lieutenant ZAYYAN MUHAMMAD TURETA..."


"Ina jinka, Tureta nawa kake nufi? Wa ya aikoka? Daga ina kake?" Ya rinka jero tambayoyin yana jijjiga shi.


"Liberia prison, the Lieutenant is waiting"


Hularsa ya tuge bai sani ba saboda yadda ya tashi tsaye da sauri "Lieutenant Zayyan fa kace"


"1993 Liberia Peace Keeping Troop"


Zuciyarsa bugawa ta rinka yi da sauri da sauri yana tsoron kada ya gaskata maganar mutumin ya tashi yaji ashe mafarki yake yi.


"Daga ina kake?"


"Liberia Prison"


"Innalillahibwa inna ilaihi raji'un" yace gumi na karyo masa "Zayyan yana da rai dama?"


"Yace akwai Hadir ko shima yana da rai?"


Hannuwansa Excellency ya riko ya tayar dashi tsaye "nasan Hadir, nasan Mustapha, nasan matarsa da 'ya'yansa kowa yana nan"


"Ahghhhh" Chibuzor yace da kyar saboda murdewar da cikinsa yayi ga dukan da ya soma sha.


Excellency da kansa ya tallabo shi a jikinsa ya ja shi zuwa motarsa jama'arsa suna kallonsa da mamaki. Wani ne yayi karfin halin cewa


"Your Excellency kawo shi mu saka shi a motarmu"


"Noooo muje kawai" ya amsa yana kankame Chibuzor a jikinsa.  Da suka isa daidai kofar shiga cikin gidan ma da kyar ya bari aka shigar masa dashi ciki. Kansa ya kulle so yake yaji gamsasshen bayani. Matarsa da Arifah a ranar suka tafi Abuja daga shi sai ma'aikata. Abinci yasa aka kawo masa yana zaune yana jiran ya gama ci ya kara yi masa bayani. Shima a nasa bangaren baya jin zai iya yin komai sai ya sauke wannan nauyin.


"Sunana Chibuzor Kalu"


"Ci abinci tukunna sai muyi magana" ya fada batare da maganar ta kai zuci ba.


"Bazan iya ba..."


Cikakken labari ya samu daga wurin wannan yaro tun daga rabuwar Zayyan dasu Hadir zuwa yanzu. Sai ga His Excellency the Executive governor of Plateau state yana zubar da hawaye. Shekaru daidai-daidai har ashirin da biyu rabon Zayyan da iyalinsa. Kurkukun ce ta fado masa yaji wani kunci yana sauka a ransa. Garin yaya bai taba tunanin komawa su duba wurare ko za'a same shi ba? To amma a gaban idonsa aka yi masa harbi guda biyu ya fadi kamar matacce.


Wayarsa ya zaro wadda mutane kakilan suke da layin ga gumi duk ya jika tafin hannunsa saboda girgiza da yayi ya soma neman sunan Major Mustapha. Bai kai ga dannawa ba ya kwabi kansa. Bincike ya kamata ya fara yi ya tabbatar ba wai ya tayar musu da hankali bisa abinda bashi da tabbacinsa ba.


**********


Kwanansu Radhiya biyu da zuwa kuma gobe Tante da Yousuf suke sa ran tafiya Nijar. Jiya da Ummi tace suje gidan Daddy Haroun kafin lokacin fitar tasu dreban Major ya kawo rahoton wahalar mai da aka fara tun daren jiya shima bai sami labari da wuri ba. Yawancin masu ababen hawa kowa yana kan layin mai ko kuma ka daure ka saya wurin 'yan bumburutu idan kana da hali. Awwab na ji yace idan sun fita sai suyi full tank a wurin nasu. Raji ya nemi fassarar bayani a wurin Zahra da ta kawo masa dankadafinsa Femi ta fada masa da turanci. Sai cewa yayi wai yana son yayi experiencing bin layin mai irin wannan. Shi da kanwarsa a Germany aka haifesu kuma bai taba katarin samun wannan matsalar ba a duk zuwansa Nigeria.


"Raji ba fa wurin shakatawa bane, nima ban taba bi ba amma nasan labarinsa. Wahala ce kawai harda fada wani lokacin"


"To ba sai mu kafa tarihi ba" cewar Yousuf da yake jin hausa sosai kasancewar babansa ba yarensu daya da Nasara ba. Hausar Nijar suke yi mai kamanceceniya da Sakkwatanci.


"Gaskiya ba dani ba" Awwab ya fada zai gudu daga falon saboda ya ga zasu jajibo masa wahala baiji ba bai gani ba.


Magana har wurin Daddy saboda Raji ya matsa wai yau daya dai su dana. Ba don yaso ba aka ce ya tuna bakinsu ne ya karramasu da abinda suke so. Sai da suka yi la'asar suka bar gidan. Raji yasa Zahra ta hada masa 'yar jaka da irin pillon nan na matafiya a jirgi na kafada, abin rufa, touch light da 'yan kayan ciye ciye. Awwab da baya son zuwa sai gashi yana dariyar mugunta. Wai shi nan Raji hango abin yake kamar wani picnic ko camping. Yousuf ma da nasa shirin suka shige mota Awwab ya bi bayan dreban da daya motar.


Sa'arsu daya yau tun safe garin dama da hazo da sanyi sanyi ba kamar jiya da suka iso ba. Amma fa abu tun ana dariya sai gasu sunyi kicin kicin da fuska zukata sun matso kusa. Layin mai ma ana alfarma. Ga rigimar cin layi da dai sauran abubuwa marasa dadi da kan biyo bayan zama a layin mai. Layi har dare ko tafiya suka ce zasu yi yadda wurin ya cushe da wahala su sami hanya ta dadin rai. Haka suka zauna dare ya gabato sauraye suka ce salamu alaikum sanyin da zai koresu bai kankama ba gara suma suyi full tank. Dukkansu jikinsu ya fada musu kuwa. Ba su suka koma gida ba sai hudun dare. Zahra da Ummi ne kadai ido biyu. Take taken Raji na makalewa Zahra yana ta korafin wahalar da yasha yasa Awwab bin Yousuf bangaren Ummi yana girgiza kai. Zahra na ta zillewa amma yaki barinta. Awwab na jin yana cewa da a gida suke wanka yake so ta taimaka masa yayi ya dauki kayan bukatarsa ya fita. Baya son ganin abinda zai dame shi yazo yana jin kunya shi da kanwarsa su zama surukan juna. Gara ya basu wuri ko yaya ne ta kula da mijinta. Radhiya ce ta fado masa a rai lokacin da yake kwanciya a kan bargon da ya jefa a kan kafet din dakin Emzee ya buga tsaki shi kadai yana ayyana wai ta cuce shi da yanzu shima...kwafa yayi kawai ya kwanta.


"Kasan babu dadi ko? Ka dawo nan gadon zai ishemu" Yousuf yace da ya jiyo tsakin.


"Its okay mantuwa nayi mai mahimmanci, kaji ina tsaki ko" a rayuwarsa babu abinda yake masa wahala kamar kwanciya kusa da mutane. Sai yayi ta ganin kamar zai takura musu kuma shima baya son tasu takurar.


Karamar dariya yaji Yousuf yayi yana cewa "Raji yayi mana wayo. Mun sha wahala tare wato shi mai mata ya gudu"


"Kai me kake jira" Awwab ya tambayeshi cikin duhun dakin yana fata kada yace abu guda suke so. Yinin yau kadai Yousuf din ya kwanta masa akwai ilimi amma a wani kamfani yake aiki ba likita bane. Ko me yasa jiya yaji Mama tace likita?


"Da dai na fara shiri amma na kula kamar bazai yiwu ba." Yanayin maganarsa zaka san abin baiyi masa dadi ba sai dai a rayuwarsa bai yarda da cusa kai inda ba'a nemansa ba. Yana son Radhiya kuma kanwa ce gareshi har kullum amma jiya shi kadai yasan me ya gani suna yi da sunan cin abinci. 


"Allah Ya musanya maka da mafi alkhairi"


"Amin, amma meyasa nake ji kamar kasan da wa nake?" Ya kuma yin dariya.


Wayancewa yayi shima yana dariyar 

"Ban sani ba fa...kawai fatan alkhairi nake maka" 


"Sai ka tayani nema tunda kasan irin wadda nake so"


Abin rufa Awwab yaja ya rufe kansa yana dariya lokacin da Yousuf yace kuma idan ya cigaba da jan rai zai ji ana biki a Nijar. Yasan so yake ya nuna masa ya gano wa yake so, shi kuma sai yaji kunya kada ya nuna abinda zai iya sosa ran Yousuf din. Da kyar suka yi sallar asuba jam'i su biyu don sai da aka idar Awwab ya iya farkawa saboda gajiyar da suka tara.


***********

 Yau da Radhiya akayi aikin breakfast ita da Ummi suna yi tana kara yi mata bayanin project dinta. Abin ya kayatar da Ummi matuka tace me zai hana tayi magana da Daddy sai a nema mata alfarmar samun adireshin wasu daga cikin matan da suka zauna tare a Sakkwato wadanda mazansu suka rasu ta saka su a sashen shirin nata da ta kira da (Hidden Heroes). 


"Ummi kece ta farko a cikinsu sai dai bazan iya saka ki a ciki ba saboda kuka zamuyi ta yi" tace da kwalla a idanunta.


Da murmushinta mai ciwo tace "Allah Ya jikan Daadaa dinku. Halinku kadan ne da bambanci. Shi baya shagwaba irin wadda kika koyo wurin Nasara sai dai ya shagwaba wasu" 


Dan tsalle tayi tana son hirar babanta "Ummi yana shagwabani?"


"Kamar ba gobe" ta amsa mata tana tuno rayuwarsu ta da murmushi na kufce mata.


"Kema yana shagwabaki ko?" Ta tsare Ummin da idanu tana daga gira daya da wani dan banzan murmushi.


"Kaniyarki, fita ki bani wuri" ta biyota da cokalin miya. Dariya ta saka ta gudu daki.


"Na fa zata ta kintsu ashe nutsuwar ta karya ce" Ummi ta cewa kanta ita kadai tana girgiza kai. Mai hali baya fasa halinsa. 


Yau ma atampa ta saka amma riga da skirt. Ita kadai take juyi a gaban madubin bayan ta gama kwalliya ta karkata nan ta karkata can tana turo baki.


"Fita mana kije kiyi a gabansa sai ya fada miki inda yake bukatar gyara idan akwai"


Ta madubin ta harari Fauziyya kamar idanu zasu fado ta zagaya karbar Jawad zata shirya shi Fauziyyan tayi wanka sai ga Zahra kamar an korota ta shigo da sauri kana ganinta farkawarta kenan.


"Jama'a na shiga dubu a gidan nan yau"


"Me ya faru Adda?"


Kasa fada tayi wai saboda Radhiya ba aure gareta ba. 

"Babu komai dai"


"Ina fa babu komai dazu Mami ta aiko Zayyana da Femi wai tana ta zuba ido jiya da daddare kije ki karbe shi taji shiru ko kinzo kin kwanta ne kin bar mata shi. Bai dade da komawa bacci ba yana dakin Ummi"


"Duk dad dinshi ya ja min" tace kamar tayi kuka.


Fauziyya ta zauna a gefen gadon kusa da ita harda rage murya za'ayi gulma "kwana kika yi a can tare dashi?"


Duka ta daka mata a cinya kafin tace "dawowa yayi fa duk cizon sauro yayi wani iri...daga hada masa ruwan wanka bacci ya daukeni"


"Allah Sarki...kinsan bacci babu ta yadda baya zuwa. Ina fata dai kinyi ya isheki" Fauziyya tace tana dariyar ta dago me ya sami yayartata.


Radhiya taji sun sakata a duhu ta kasa fahimtar me suke nufi ga

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment