Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SOJA SHINE JARUMIN DA IDAN YA GA AN KAWOWA KASARSA HARI SAI YA DAUKI KOWACCE MACE A MATSAYIN MATARSA , 'YARSA KO BABARSA SANNAN KOWANE NAMIJI BABANSA KO DANSA YAYI KOKARIN CETON SU KAMAR NASA. Wannan shine zai sanya ku jajirce wurin taimako da kariya batare da tunanin bambancin addini, yare ko akida ba. Sadaukarwa irin wannan kuwa sai ga haifaffen soja jarumin kasata."


Tunda ya fara magana ya tafi da hankulan da dama daga cikin mutanen dake wurin. Sojojin kuwa ya kara musu wani karsashi da son aikin da suka zaba suna jin babu ranar yin nadama a shirye suke kodayaushe su bada rayuwarsu domin zaman lafiyar kasa. Sowa da tafi aka rinka yi bayan ya gama jawabin nasa ya koma mazauninsa. Arifah da ya gama burgeta tayi masa murmushi "I am proud of you Dad"


"Ba dadin baki ba saura anjima inji kin fara rokona wani abu" yace yana dariya.


Juyawa yayi ga Commandant din yace masa zai tafi yana so ya wuce Abuja a yau. Gwamnan Kaduna baya kasar a lokacin shiyasa ba'a gayyace shi ba balle yace zai kai masa ziyara tunda garinsa yazo. PA dinsa ne ya kira dreban ya kawo mota inda ya ajiye shi dazu domin su tafi. 


Sun kusa tashi kenan Commandant ya soma wani bayani da ya dauki hankalin His Excellency ya dan dagawa PA dinsa hannu cewar yana zuwa. 


"Kamar yadda kuka sani sati biyar da suka wuce an sami gobara a daya daga cikin hostels dinmu sanadiyar konewar socket. Babu wanda yaji ciwo duk masu 'ya'ya a wannan hostel din sun sani. To amma abinda da yawanku baku sani ba shine waye ya yi sanadiyar ceton rayukan mutum sama da hamsin single handedly. Nafi kowa mamakin jarumta da kaifin tunani na wannan yaro da yake shekararsa ta farko a makarantar nan. A lokacin da kowa yake gudun ceton nasa ran wannan Cadet din ya koma ya rinka buga kofofin dakunan wadanda basu sani ba saboda abin ya faru cikin dare ne. Bai tsaya a nan ba duk da kiran da abokansa da malamai keyi yaje inda fire extinguisher take da zafin wuta da hayaki da komai ya cirota ya tsaya a kofar dakin da wutar ta fara ci yana kokarin kashewa yana kuma commanding sauran 'yan uwansa cadets da su bi dakuna su tabbatar kowa ya tashi." Yana kaiwa nan yayi musu alama da hannu "Please lets all stand in honour of Cadet Muhammad Zayyan Tureta"


Baba Hadir ne ya fara tashi zumbur da yaji an kira sunan dansa. Ummi kam tamkar ta saka ihu duk da ance sati biyar kenan da yin gobarar. A tunaninta Karami ya dena miskilanci ashe abu irin wannan zai faru ya boye mata? Bata san lokacin da ta soma hawaye ba. Major bai tuna kowa ba sai nasa Zayyan din. Karin maganar bahaushe ya tuna da ake cewa barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba. Duka duka Emzee shekarunsa da yasan ya koma ceton rayuwar wasu.


His Excellency Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ji yayi tamkar an saukar masa da guduma a tsakar kansa. Kunnuwansa sun jiye masa da kyau kuwa? Ya san  nasa Zayyan Muhammad Tureta din yau kuma yaji ana kiran Muhammad Zayyan Tureta. Me yake shirin faruwa ne? Bai karasa tsinkewa da lamarin ba sai da kyakkyawan matashin mai dauke da fuskar da ko yasha giyar wake baya jin zai taba manta ta ya taso cikin shigarsu da dalibai wato cadets da hularsa a karkace yayi matukar kyau ya hawo kan stage din inda Minister of defence zai bashi kyautar Cadet of the Year.


Emzee kenan, yasan da award din shiyasa ya matsawa Umminsa dasu Daddy akan su zo domin yayi surprising dinsu.


Excellency fa sai yaji tsayuwa tana neman gagararsa ya lalubi kujera ya zauna kansa ya daure gabadaya. Masu hoto suka yi caaa akansu lokacin da Minister yake baiwa Emzee award din. Da murmushi a fuskarsa ya rinka baza idanu har Allah Ya bashi ikon hango iyayensa. Daga kambun da aka bashi yayi ya nuna shi saitin inda suke yana kara fadada murmushinsa.


Sosai ya burge Minister ya dafa kafadarsa suna tsaye a gaban loudspeaker yace "Cadet baka da abin cewa?"


Wadanda suke kusa zasu iya ganin kunyar da ta bayyana a fuskar Emzee. Duk da haka ya dan saita bakinsa a jikin speaker din yayi godiya ga Commandant dinsu, dukan mutanen academy din sannan ya kare da cewa "I dedicate this award to my late father LT. ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"


Ummi kuka Mama kuka suka rungume juna. Kukan farinciki, famin ciwo da kuma tsantsar godiya ga Allah akan kowane yanayi take yi.


Emzee zai sauka daga wurin har lokacin baiyi nisa da speaker din ba ga mamakin dumbin jama'ar da suke wurin yaji hannu ya sauka a kafadarsa an damke shi. Da sauri ya juyo ya ga mutumin da aka kira da gwamnan Plateau ne sai yaji ya firgita.


Idanun Excellency sunya ja sosai hankalinsa tamkar baya jikinsa yace "sunan mahaifinka Zayyan Muhammad Tureta?"


Emzee ya gyada kai a dan tsorace. Ummi tashi tayi daga seat dinta tana jin me yake fada tana kuma tsoron ko dan nata yayi laifi ne.


Kwalla ce Emzee ya tabbata ya gani a idanun Gwamnan sai kawai ya rungume shi a bainar jama'a. Commandant din yana ganin haka ya kira wasu da zasu jagoranci taron shi kuma ya duka kadan yadda Excellency din zai ji yace "kana bukatar kebewa tare da yaron ne"


"Kwarai kuwa dan kanina ne, zaku iya bashi pass na kwana daya? Shekaru sama da shabiyar nayi zaton sun mutu"


Sai da Commandant din ya girgiza da jin wannan magana daga bakin Gwamnan yace su tafi. Emzee yaji mamaki matuka da furucin mutumin nan. Yana rike da hannunsa motocin suka yo gaba aka fara sakin jiniya suka sauka Arifah tana take musu baya itama mamaki ya kamata. Da sunan Zayyan Tureta a bakin mahaifinta ta girma yau ace ga dansa bayan Dad din da kansa yace mata iyalinsa sun mutu. 


Kafin su shiga motar Ummi tayi gaba hankalinta a tashi Gwamnan garin da ba nasu ba kuma basu da mahadi dashi yayi mata gaba da danta. Major da Baba Hadir suka nufo stage din aka nemi hanasu hawa. Daga murya yayi yace "danmu ne aka tafi dashi kuyi mana bayani."


Commandant sai ya zaro waya ya nemi PA din gwamna ya sanar dashi ga iyayen yaron fa.


"Fada musu guest house din da zamu je. Ina bukatar magana dasu privately."


Ibrahim ke jan mota daya dreban Daddy yana jan dayar suka bi bayan motocin. Dakatawa ma akayi suka shiga tsakiyar convoy din sannan suka wuce cikin garin Kaduna. Wata unguwa da ta yi nesa kadan da hayaniya ga maka makan gidaje suka je. Emzee ya dena tsoro sai mamakin yadda tunda suka shiga motar Gwamnan yake rike da hannuwansa yana kallonsa yana murmushi ya kasa cewa komai. Abin ne da matukar mamaki da daure kai. Dan Zayyan dinsa ne yake gani a gabansa.


Sun shiga harabar gidan aka fito daga motoci. Excellency yana rike da Emzee su Ummi suka firfito daga mota yana jiransu. Kan kace meye wannan an bude gidan da ya wadatu da kayan alatu. Arifah da PA dinsa ne kadai suka bisu cikin wani wawakeken falo. PA din yace su zauna amma duka hankulansu basu kwanta ba sai da gwamnan da kansa yace su zauna. Tambayar farko da ya fara watso musu ita ce "ina Alheran?"


Idanu ya ga sun dora masa kawai yayi dariya sosai ko ya tsorata su ne? Farinciki ne ya cika masa ciki da zuciya tamkar kirjinsa zai fashe.


"Bari na faro muku daga farko dai. Sunana Nasiruddeen Aliyu....." bai dire labarin ba sai da ya kai zuwa lokacin da aka harbe Zayyan yana rike da hannunsa bayan ya sauko ya taimaka masa "duk abinda na zama a rayuwa wallahi Zayyan ne sila, ina kuka shiga aka ce min kun mutu? Ina matar Zayyan da yace min yana kiranta Fillo, ina 'yarsa Alheran Radhiya...kada kuyi mamaki ban taba manta Zayyan ba. Da Allah Ya sake bani haihuwa babu makawa idan namiji ne sunan da zai amsa kenan" yace idanunsa na fitar da kwalla.


Wani irin kuka Ummi take yi wanda duk mai sauraronsa zai tausaya mata matuka. Kirjinta kawai ta dafe tana jin wannan sabon al'amari. Emzee bai san komai akan mahaifinsa ba sai hoto sai labari amma ya tayata kukan saboda girman abinda suka ji.


Daddy da Baba Hadir sai suka ji abin kamar almara. Daddy ya kada baki yace "kana nufin kace min Zayyan bomb bai tashi dashi ba?"


Excellency yayi ajiyar zuciya ya sake yi musu bayanin ainihin abinda ya faru na binne landmine din karya da 'yan tawayen suke yi "tabbas bomb ya tashi domin har zuwa lokacin rasuwarsa Zayyan yana ta fargabar bomb din ya shafi 'yan uwansa Hadir da Major Mustapha ko kuwa Allah Yasa sun tsira. Kamar yadda na fada muku ni da Zayyan munyi wata irin rayuwa ne da bamu da sirri ga junanmu. Zayyan was my last patient daga kansa ban sake iya duba wani mara lafiya ba."


Hawaye ya gani sharkaf a fuskar wanda tun zuwansu baiyi magana ba. Mai yin maganar kuma wato Daddy sai sunkuyar da kai yayi ashe shima hawaye yake digarwa. Kaddara ta riga fata. Ashe da rabon Zayyan zai sake ceton rayuwar wani shiyasa suka yi masa zaton mutuwa. Yau gashi mutumin ya zama gwamna bayan yayi dan majalisa da sanata.


"Kunyi shiru ina Fillo na manta ainihin sunanta"


Mama ce tayi karfin halin nuna masa Ummi wadda kuka ya hanata katabus.


Abin ya taba Excellency sosai ya sake cewa ina Alheran ita yake son gani.


"Tana karatu a France" Ibrahim yayi karfin halin bashi amsa.


Murmushi ya sake "Alhamdulillahi rayuwarku bata lalace ba kamar yadda Zayyan yayi ta jin tsoro. Ko sati banyi da dawowa ba naje har gidan iyayensa wani da yace min shi yayansa ne yace matarsa ta haifi da babu rai kuma sunyi hatsari sun rasu ita da Alheran"


Gyaran murya Major yayi da kyar ya iya tattaro kuzarin cewa "nine Major Mustapha, wannan kuma shine Hadir"


Tashi yayi yazo inda suke ya tsaya "daya daga cikinku kafarsa ta fita a ambush din Liberia?"


Kafar damansa Major ya taba yana kwankwasata "katako ce"


Hannunsa Excellency ya kama ya damke sosai "nice to meet you Major" sannan ya koma ga Hadir "dan uwan Zayyan baka ce komai ba"


"Maganarsa ta dauke tun ranar da abin ya faru....." Major bai dire ba shima sai da ya bashi labarin tashin hankalin da suka fuskanta da rayuwar da suka yi su duka har tasu Mairama. Yau din sai ta zama wata rana ta tuna baya da kuka a garesu. Sannan kuma rana mafi farinciki ga His Excellency Nasiruddeen na haduwa da mutanen da baisa rai dasu ba. Sai dai wani tunani da ya darsu a zuciyarsa ya sanya shi dagowa kana iya ganin fushi mai girma a idanunsa.


"Who the hell is Maikudi? 


"Yayan Zayyan ne amma ba uwa daya ba. Ina tunanin kaina dashi kuka hadu"


"Sai yayi nadamar kallon tsabar idanuna yayi min karya. Na dawo da hope na daukar nauyin komai na rayuwarsu mutumin nan yace min sun rasu" yace cikin bacin rai da jin inama dai yayi ido hudu da Maikudi yanzu.


"Your Excellency mun riga mu sa an kama shi. Gidan magada an karbe sannan wanda ya gina da kudin da na turo da kudin hayar gidan shima yanzu haka mun saka a kasuwa saidawa za'ayi. Family dinsu na Nijar sun shigar da kara sai da yayi wata shida a rufe sannan yana kan biya tara" Major ya sanar dashi.


"Ahaf, wannan tsakaninku ne ai. Kowa kawai ya dauki tasa fansar shine zan fi fahimta."


Baba Hadir sai da yayi dariya mai dan sauti yana ganin yadda mutumin nan ya dace da 'yan uwantaka da Zayyan saboda yanayin halinsa.


Murmushi shima yayi yana kallonsa "na baka dariya ko? Seriously ni yanzu ko Zayyan ne da kansa bai isa ya hanani kulle Maikudin nan ba so please a bar maganar. Zan sa a kira CP har gida za'a je a dauko min shi. Gobe idan an nuna masa maraya ba kudin maraya ba ma ko kallonsa bazai yi ba"


Ummi ma dai murmushi tayi tana jindadin ace hali nagarin da Zayyan ya nunawa wadannan bayin Allah shine yasa su tsayawa domin kula dasu. Addu'a take ta yi masa a zuciyarta na fatan dacewa da Rahamar Allah.


Hira sosai Excellency ya rinka jansu da ita yana cewa su saki jikinsu shi dasu zumunta ce mai karfi da Zayyan ya hada. Abinci aka rinka shigo dashi kala kala na alfarma yace kowa ya ci abinda yake so. Idan babu ra'ayinka ma ka fada a nemo.


"Arifah ga uwayenki ki kaisu wancan falon nasan zasu fi sakewa"


"Okay Dad" ta mike tsaye da fara'arta. Dauko musu abinci wani cikin guards din baban nata yayi aka kai musu inda yace. Kamar mahaifinta sai gata ta saki jiki dasu tana hira da tambayarsu sunayen yaransu mata su zama kawayenta.


 Bayan sun gama ci a bangaren mazan Excellency ya nemi jin ko suna aiki. Major dama Daddy Haroun ne yake nema masa, to rabuwar yaransu ya sa yaji kunyar sake tuntubarsa. Shi kuma rashin samun wani abin kirki yasa baiyi masa magana ba.


"Major me zai hana in nema maka aiki a NITDA (national information technology development agency) tunda software engineer ne kai. Hadir kaima fa dole ne ka fita. Tunda jikinka yana motsi sai a nemi aikin da ba sai kayi magana ba. Rashin shiga mutane ma lalura ce mai zaman kanta "


"Your Excellency kada ka dorawa kanka nauyi daga haduwarmu yau don Allah" cewar Major.


"Wane irin nauyi? Bari na fada maka abinda baka sani ba. Ka ganni nan, ko da nayi retire amma har yanzu zuciyar tana tare da Army. Soja shine yasan soja. Mune muka san fadi tashin juna saboda haka dani daku bamu da zabin da ya wuce rungumar juna a matsayin 'yan uwa. Ko kuna ganin haduwar tamu anyita ne aci abinci a tashi ana shafa tumbi?"


Dariya yake yana maganar suma dole suka dara. Wannan mutum da saukin kai yake tamkar ba gwamna ba. Sai bayan la'asar suka kama hanyar komawa bayan yace zai sanar dasu ranar da zasu taho duka da iyalansu. 


"Sannan a bawa Alheran numberta zan kirata da kaina ku tabbatar dai an fada mata matsayina gareta. Tana samun hutu a turo min ita don Allah."


Mota guda ya bayar aka mayar da Emzee makaranta bayan ya jikasu dukkansu da kyautar kudin da bai san adadinsu ba.


**********


Radhiya tasha bayani kala kala daga wurin dukkaninsu. Ranar itama kusan kwana tayi kuka tana tausayawa Umminta don sai da Nasara taji babu dadi an sa mata 'ya kuka.


Kwanaki kadan bayan haduwarsu sai ga offer din aiki har gida ga Major da Hadir. Kasar wa ka sani wa ya sanka kenan. Ba tare da bata lokaci ba an gama duk wani abu da ya kamata cikin sati guda. Major sai yayi wani course na wata uku a nan cikin sabuwar ma-aikatar tasu. Shi kuma Hadir an samar masa aiki mai sauki a Ministry of defence. Abu na karshe da yayi musu shine kama musu wasu gidaje flat a estate daya kusa da juna guda uku harda na Ummi wai idan tayi hutu ta taho ba sai ta takurawa kowa ba. Sai suka rasa da me zasu kwatanta karamcin wannan mutumi. A nasa bangaren kuwa yana musu kallon sun cancanci fiye da haka. Shine ya zauna da Zayyan a karshen rayuwarsa, shine suka ga kisa da mugunta tare zahiri suna kwantarwa juna hankali. Saboda haka nauyin iyalin Zayyan a wuyansa yafi cancanta.


Daddy sunyi waya da Mami yana yi mata bayanin komai sai hamdala take tana jin kamar ta taho. Dama kuma Ummi bata iya shiru ba Mama tana yin pt ta tabbatar ciki gareta ta kirata ta fada mata. Kwanaki hudu a tsakani Zahra ta sunkuto jaririnta kyakkyawa tubarakallah. Mami sai dada godewa Allah take da aka amincewa aurenta da Raji. Dan zaman da tayi dasu ta kara sakankancewa ba karamin so yake yiwa diyarta ba. Da yake kuma ba bahaushe bane babu ruwansa a gaban kowa matarsa ce tauraruwarsa. Kullum Zahra tana cikin annashuwa babu ta inda mijinta ya rageta. Ranar da jariri ya cika kwana bakwai aka saka masa suna Olufemi Abubakar Assiddiq amma suna kiransa Femi. Maman Raji kusan ita take komai na gyara da kula da maijego shiyasa suna cika sati uku lokacin Mami ta wuce wata a garin tace ita dai gida zata dawo. 


"Mami bazaki jira nayi arba'in mu tafi tare ba?"


"Lada ya isa haka nima a barni na tafi wurin mijina"


"Laaaaaa Mami" Zahra tace tana dariya.


"An fada miki ku kadai kuka san kula da miji, ki fadawa Raji ya dawo min da booking dina jibi Allah guduwa zanyi sai kun taho"


Mami fa da gaske ta tubure dole aka fara shirin komawarta. Shatara ta arziki Raji ya hada mata da alkawarin suna hanya da zarar Femi ya cika wata uku. Da Awwab yaji labari da kyar ya samu ta kara kwana hudu akan yadda tayi niyya don su koma tare. Ba karamin kewar gida yayi ba duk da shi ya zabi rashin son komawa lokuta da dama. A ganinsa kawai an hade masa kai an biyewa su Mummy anki aura masa Alheran. Har lokacin kuma yaki saukowa daga fushin da yayi da tace bata son aurensa. Ko yaya ya tuna sai yaji bacin rai. 


Awwab mai sakin fuska da yawan wasa yanzu ya zama a lallaba. Ba wai fada yake yi ba, shiga sabgar mutane ce gabadaya ya ja baya da ita. Ya rasa walwalarsa daga ranar da Alheran tace bata son aurensa.


Siyayya sosai ya yiwa Femi kamar yadda ya yiwa Jawad dan Fauziyya. Munirat kanwar Raji ce ta kawo masa yaron Mami da Zahra suna zaune dashi an kawo masa abinci. Ya kara kyau da jiki ga wani gashin baki da gemu da ya hada ya zagaye kyakkawar fuskarsa sai gyara da ya sha an rage shi sosai ya kwanta a fatar fuskar ya sake fiddo kyaunsa. Rike yaron yayi yana jin inama nasa ne da Alheran...tsaki ya yi batare da ya sani ba da sunanta ya fado masa.


"Lafiyarka kuwa?"


"Mami gajiya ce kawai. Zahra ki barmin shi kawai ki haifi wani" yace yana shafa kwantacciyar sumar kan yaron gwanin sha'awa.


"Ba dai ka tsaya tuzuranci kake jira ya cimmaka ba. Allah Ya bada sa'a. Idan rabon ayi aurenku tare da 'ya'yan naka ne mu ai bamu da ta cewa" Mami ta fada tana kawar da kai. Wai shi zuciya sai tayi masa maganar Radhiya yace ai sune suka bata izinin tafiya shi bazai bita ba. Mami takan ce masa maji ma gani idan rabon ka ga katin auren Radhiya ne ba shikenan ba. Duk lokacin da tace haka a zuciyarsa sai yace ba amin ba.


'Yar halak sai ta zabi daidai wannan lokacin ta kira Zahra. Har wani dan murmushi Zahran tayi tana dauka ta saka wayar a speaker ta karbi Femi da yake kuka za ta shayar dashi. Mami ta tashi ta koma cigaba da hada kayanta.


Awwab bai san me tayi ba kawai sai jin zazzakar muryar Radhiya yayi "Adda please please ki saka min naji muryar babyna"


Zahra tana kallon yadda ya dauke wuta ko motsi ya kasa yi. Wani irin yanayi na shauki ya bakunce shi. Shekara guda da watanni rabon da ya sanyata a idanunsa ko yaji muryarta.


"Adda kina jina?" Tace tana karyar da murya.


"Ina jinki Radhiya...fushi muke ni da Femi yau kwana uku baki kiramu ba"


"Exams....gidan ma bana zama sosai fa. Yanzu dai ki dan zungure shi kadan yayi kuka naji"


Duk abin Awwab sai da yayi murmushi suna hada ido da Zahra ya cigaba da tsakurar abincin dake gabansa. Tana nan da halinta wato.


"Dan nawa zan zungura Radhiya? To ko dai balotellin kike so nayi miki? Ina da sabon scisssors mai kaifi"


Dariya tayi da tasa tsigar jikin Awwab tashi saboda yadda yaji muryarta har tsakar kansa. Dannewa yake kada Zahra ta sami damar tsokanar shi tace tayi galaba a kansa.


"To ni shikenan bazan ji muryarsa ba" ta fada cikin shagwaba.


Idanunta akan Awwab tana ganin wani annuri da yake bayyana gareshi a hankali tace "zan ga ranar da zaki girma. Anyway yaushe zaki je Nigeria?"


"Saura na exams biyu amma Yousuf yace na jira mu tafi tare nan da kamar two weeks I think. Zamu fara zuwa Agadez ne sannan mu taho"


"Yousuf dinnan yana ji dake" Zahra tace tana dage gira daya tare da kawar da kai daga kallon Awwab da ya tattaro hankalinsa garesu batare da niyya ba.


"Kawai yana da kirki ne. Kiyi min addu'ar exams"


"Allah Ya bada sa'a, ni dai ki tabbata kinzo lokacin da zani"


Muryar namiji Awwab yaji yana kiranta da Alheran ya tashi a fusace ya bar falon. Meyasa shi bazai kirata Radhiya ba kamar yadda kowa yake fada. Da takaicin wannan abu ya kwana. Washegari jirgin dare suka bi zuwa Abuja. A hanya ya rasa yadda zaiyi ya tambayi Mami waye Yousuf kada tace har yanzu ya damu da Radhiya. Shi ba damuwa da ita yayi ba kawai dai curiosity ne.


Dreban Daddy da Ibrahim ne suka je daukarsu. Mummy ta kasa boye murnarta da suka shiga estate din. Wai sune a gida irin wannan mai kyau kuma Major ya sami aiki. Awwab ma yayi murna sosai ya kuma yaba da unguwar da iyayen nasa suke.


Nata gidan da sauran gyara na kayayyakin da zasu saka saboda bata nan. Abubuwa kadan ta iya fadawa Daddy a dauko mata daga Katsina. Sauran kuwa sai tazo da kanta.


Daddy yana gidan Baba Hadir saboda Mama da Ummi sun hadu a gidan Mami suna girki. Suna shiga Awwab yayi ido hudu da Ummin da yake yiwa wasan buya.


"Allah Ya kamaka Awwab babu alkawari...oh ni Mairama 'yan sa ido sai su zuba ruwa a kasa su sha sunyi nasarar shiga tsakanina da dana"


Mama sai dariya "wai 'yan sa ido, kaga Awwab gara ka kamani don Ummi da Mami 'yan hamayya club ne"


Shi dai kunya ma suke bashi ya gaishe su duka yana neman wurin zama Ibrahim ya nuna masa dakin da aka tanadar masa don zaman hotel ya kare masa a garin tunda babu fuskar zuwa gidan Mummy.


"Kunga yadda Awwab ya sake zama babban mutum kuwa? Ni dai gaskiya ayi masa aure haka nan" cewar Mama


"To ya hau dokin zuciya yana ta fushi damu akan tafiyar Radhiya" Mama ta bata amsa.


"Shashanci kai, yana nan wallahi buzayen can zasu fara kawo mata hari. Wami hotonta da ta turo min fa Allah nayi mamakinta sosai. Ki turo min shi Mami idan kun huta ya kamata na karanta masa fari da baki"


Ummi tace "gidana zai fara zuwa akwai tamu dashi, duk abinsa sai yaje gidansu Ghazalatu ya gaishe da iyayensa wannan karon"


Mami ta ce "ni dai a nuna min nawa dakin naje nayi wanka yunwa nake ji"


"Ummi inkiya akeyi mana mu fita fa...kinga ni nayi nan kafin ki fara jin gyaran murya Daddy ya zo oyoyo"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Zainab baki da dama wallahi. Amma zan fada masa tunda sharrin naki harda shi"


"Rufa min asiri don Allah" sai da ta kusa kai bakin kofa ta juyo "yo ai dai gaskiya na fada idan kin musa mu dawo mu tayaki wuni"


"Allah Ya shiryeki kina nan kina zance sai ya shigo" Ummi tace ta rigata fita.


Dawowa da baya Mama tayi tana nunawa Mami fridge "nayi miki ajiya fa ya kamata ki fara dubawa ki sha..." 
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Mami sai da ta waiga baya ta tabbatar su kadai ne sannan ta girgiza kai "kinyi sa'a da yara a gidan nan da na miki dan biki. Zan zo har gida na sameki"


Da dariya Mama ta bi bayan Ummi saboda yadda ta tsani gidan nata. Komai warinsa take ji ta rinka amai kenan. Ibrahim abu duk ya dame shi Allah bai sa ya fahimci kani ko kanwarsa ke tafe ba. 


**********


Kwana biyar da dawowarsu Mami Major ya sami waya daga His Excellency yana shaida masa ya shigo Abuja ko zasu zo shi da Hadir su gaisa.

Mami ya fadawa ta rike baki "yanzu Daddy gwamna da kansa yake kiranka?"


"Mutumin kirkinsa yayi yawa har ina jin tsoro. Ni bana son shigewa 'yan siyasa"


"In sha Allahu alkhairi ya kawo shi garemu. Allah Ya sani bamu cuci kowa ba bazai hadamu da macuci ba"


"Shiyasa nake son Hassanata."


Dariya tayi tana jindadin yadda mijinta yake yaba mata komai kankantar abu.


"Ki sanar da danki ya shirya muje tare"


"Yau kuma? Awwab ya ga ta kansa. Umminsa ta saka shi

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment