Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsorata da yanayin da ta ganta, ta taba wadda ta fi kusa da ita "what is wrong with her"

"Ahhh Mama Radhiya...Papa Dolapo don die oooo"

Ita ce amsar da ta doki kunnenta taji gabanta ya yanke ya fadi. Zainab ta matso kusa da ita tana fada mata wai yanzu aka sanar dasu rasuwar tasa. Cholera ce ta kashe shi Zayyan ne ma ya sallace shi, sannan anyi masa sutura a can kasar.

Kuka su ka taya Mama Dolapo aka kaita cikin gidanta. Bayan kwana biyu sai ga 'yan uwanta da yayan mijin suka zo daukansu ita da yaranta guda hudu zasu koma Akure. Ranar ma wani sabon kukan ne ya barke a tsakaninsu domin da yawa sun sani da wahala su sake sanya juna a ido har abada. Maman Dolapo ta tafi ta barsu da kewa da kuma fargabar labarin wa zasu sake samu kuma.

**********

Jaruman kasarmu suna can suna aiki tukuru bisa umarnin da kasa ta basu na wanzar da zaman lafiya a daya daga cikin kasashen gamayyar ECOWAS.

A yayin da magidanta suke tashi da safe su je ofishoshinsu yamma na yi su koma gida ga iyalansu, su ci, su sha mai kyau, su kalli matansu da 'ya'yansu su ji dadi wadannan sojoji suna cikin dokar daji suna fama da cizon sauro da wasu nau'in kwarin, rashin abinci mai gina jiki, karancin tsaftataccen ruwa balle ayi maganar wanka kullum da sauransu. Masu aure a cikinsu suna kewar matansu amma babu halin kasancewa dasu.

Yau da gobe kunnuwa sun saba da jin harbi da karar tashin bomb. Da idanunsu suke ganin 'yan uwansu, abokansu harsashi ya huda wani sassa na jikinsu sun mutu a take. Ko kuma bomb ya tashi dasu kana kallon mutumin da kuke tafiya kuna hira dashi ya tarwatse gabobin jikinsa sun watsu ko ta ina.

Jaruman nan sun yarda sun aminci su sadaukar da rayukansu a duk lokacin da kasa ta bukata domin zaman lafiya da kwanciyar hankanlin al'ummar kasarsu. Babu ruwansu da addini, kabila ko wata al'ada. Sun hadu akan abu daya ne wato TSARO na rayuka da dukiya.

A yayin da wahala tayi wahala, anga jiya anga yau a fanin rashin makusanta ko a kama mutum a sansanin abokan gaba a gana masa azaba domin ya fadi wani sirri da za'a iya cutar da nasa 'yan uwan sai ka ga zukatansu sun bushe ana yi musu kallon mutane marasa tausayi da imani. Sai dai abubuwan da idanunsu suka gani da wanda kunne yaji wani fa har ya bar duniya bazai taba kusantar abu makamancin wannan ba.

Jarumanmu ababen alfaharinmu, sadaukanmu da babu albashin da kasa zata basu da zai wanke ciwuka na zahiri da badini da suke dawowa dasu daga filin daga. Ga kuma iyalansu a yashe madogaran nasu, bangon jinginar nasu basa nan.

Wata hudu da tafiyarsu Zayyan sun fara jiyo kamshin komawa gida wata rana da yamma gari ya hade yayi bakikkirin ruwa zai iya saukowa a kowane lokaci wani mutum yazo wurin gaje gaje dashi da shiga irin ta mutanen wani kauye a kusa dasu. Jikinsa duk raunuka yace 'yan tawaye sun yiwa garinsu kawanya suna harbi kan mai uwa da wabi.

Sun riga sun san mutanen suna yin haka shiyasa su ka shiga motarsu ta yaki su ka durfafi kauyen da hanzari. A bakin wurin da yake kamar gate dinsu ne su ka hadu da motar su Major Mustapha. Ya fake da aiki ya taho ganin kannensa.

Duk da bambancin matsayi bai hana Zayyan zuwa ya rungume shi ba. Major yayi turus yana cewa.
"Stand at attention Lady"

Zayyan ya dago yana gyara rigarsa ya dan basar "Sorry Sir"

Major Mustapha sai yayi murmushi yana mikawa Hadir hannu.
"My Ladies are all grown up, sun dena dariya"

Zayyan ya kara gyara fuska sai dai dole dariya ta kwace masa. Karar bomb suka ji mutumin da ya kawo rahoton yace ‘yan tawayen sun kai mota shida. Su Major Mustapha sai kawai su ka bisu.

Sai da suka yi rabin tafiya kawai babu zato babu tsammani sai tashin bomb suka ji a gabansu ga ruwa ya fara sauka. Mutane ne suka fara bullowa ta tsakanin bishiyu da yawa ba na wasa ba sun zagayesu. Babu wata mafita sai fitowa suka yi suna musayar harsashi ga wuta motarsu ta kama saboda tankin mai da aka harba.

Bayan wani lokaci a cikin wannan yanayi ruwa mai karfi ya soma sauka kamar da bakin kwarya a cikin jejin gari yayi duhu baka ganin komai sai tashin kura, hayaki da wutar da ruwan bai gama kashewa ba. A gefe guda kuma Zayyan da Hadir ne suke gudun ceton rayukansu sakamakon bomaboman da suka tashi a wurin har uku ga harbin bindiga da bazasu iya tantance takamaimai daga ina yake fitowa ba.


A motocin yaki uku suka fito banda babbar range rover da suka ciko ta su Major Mustapha. A lissafe sun kai mutum ashirin da takwas amma su biyun suka rage wanda kusan da taimakon Zayyan ne Hadir bai mutu ba. Duk inda ka juya gawarwaki ne kwance cikin ruwa da jini. Kallo daya zaka yiwa wurin zuciya ta tsinke kaji inama dai mafarki ne. Duk mai imani bazai so koda makiyinsa ya tsinci kansa a wurin ba. Suna cikin wannan jeji dumu-dumu a tsakanin abokan gaba. Hankulansu a tashe kunnuwansu basa jin komai sun dode saboda karar bomb ya yi musu karfi.


Zayyan ne ya hango Major Mustapha wanda a bisa la'akari da matsayi shine shugabansu a wannan fitar. Mutumin da yake tsananin mutuntawa kwance yana daga hannu. Baya yayi da sauri Hadir yayi masa kallon mamaki don bai iya ganin komai shi saboda karfin ruwan "kada kace min komawa zakayi? Kazo mu bar wurin nan don Allah"


Kallon Hadir yayi ya sake kallon Major din ya koma gareshi a guje. Dago shi yayi da zafin nama sautin harsashi yasa shi komawa ya kifa a kansa suka fadi tare. Wata siririyar kara Major Mustapha ya saki mai cike da tsananin azaba wadda ta saka shi kai duba gareshi. Wani mummunan firgici ne ya saukar masa ganin kafar Major din ta dama a gutsire bomb ya tarwatsata. Zuciyarsa ce tayi nauyi ya soma kokarin daga shi domin su gudu.


Wata damka yaji ya kai masa ruwa yana wanke musu fuskoki "Lieutenant get out of here"


Bai saurare shi ba ya ciccibe shi duk da cewa ya fishi girma sosai ya saba shi a baya. Ture shi yaji yana yi yana dan dake muryarsa "this is my final command to you Tureta. Go!"


Sojoji sun horo da tsananin biyayya ga na gaba amma wannan karon bazai bi ba. Gudu ya soma yi dashi suka nufi inda Hadir yake tsaye hannunsa na zubar jini sakamakon harbinsa da akayi suka soma yankar daji.


Cak ya tsaya ya dena tafiya har Hadir yana cewa "muje mana"


Gabansa ke lugude ya kalli kafarsa ya dago a razane "Karbe shi ku bar wurin nan"


Major ya dan leko da kansa ta saman kafadar Zayyan "Lieutenant?"


Wata ajiyar zuciya ya sauke kafin Hadir ya karbi goyon duk da shima yana da raunuka. Matsawa yace suyi nesa dashi sannan ya dago idanunsa da suka jike da hawaye sosai. Kamar mai rada yake musu bayani.


"Bomb ne"


Su biyun duka suka kalle shi a gigice. Bai nuna damuwa ba ya cigaba da magana hawayensa suna tona asirin firgicinsa. Motsi kadan zaiyi bomb din wanda aka binne cikin kasa ya tarwatsa shi. Daya bayan daya yake kallonsu


"My friend..." yace da Hadir

"....Major am afraid this is the end"


Abinda Major ya dade baiyi ba ya soma shima sai kuka duka su ukun babu mai rarrashin dan uwansa.


Kafarsa ce ta danyi rawa cikin karaji yace su bar wurin. Ba yadda suka iya dole suka bar wurin a guje zukatansu suna kuka idanu na hawaye. Basuyi nisa sosai ba suka jiyo muryarsa mai dadin sauraro idan yana yi musu limanci.


"Mairama, Alheran waye zai dubi iyalina?"


Kuka ya fashe dashi sosai a hankali ya soma karanto kalmar shahada yana ji a ransa wannan ma dama ce da Allah Ya bashi.


Sunyi gudun rabin kilometer suka ji wata gigitacciyar kara wadda tasa su biyun faduwa su ka gangara kasan wani katon rami. Kafin su kai kasansa daga Major Mustapha har Hadir tunaninsu yana ga Zayyan Muhammad Tureta. Zayyan sarkin barkwanci, mutum mai tsananin so da kaunar iyalinsa da basu da wani wanda zasu jingina dashi suji dadi idan ba shi ba ya mutu a bakin aiki bayan yayi matukar kokari wurin tseratar da rayukansu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Dattijuwa ce goye da yaro tana gurfane a gaban gadon Salame wadda take hakimce tana bata umarnin ayyukan da zata yi a cikin gidan. Banda kudi sune masu gida rana yaushe wannan mata da a shekaru zata girmi Ta Madina ace ita ce Salame 'yar cikin cikinta take yiwa rashin kunya son rai tana kada kafafu tayi daurin Mayam Babangida.


"Kada ki sake na fito baki gama aikin nan ba Kande" ta kare cikin fada.


"Sha Allahu ma zan gama da wuri." Sai ta dan kwantar da kai "nace ko na kwantar miki da Halifa tunda ya riga yayi bacci? Aikin nawa zai fi sauri"


Wata uwar harara da Salame ta galla mata ya sanya ta tashi da sauri ta fita daga dakin. Tana fitowa ta sami wani matashi yana sallama. Kallo daya tayi masa ta gane ya hada jini da matar gidan shiyasa tace ya zauna. Ruwa ta kawo masa sannan ta sanar da Salame tayi bako. 


Sai da ta gama bata lokaci sannan ta fito tana takaicin hanata hutu da akayi. Tun aurenta da Salisu bazata ce ga wata rana da take cikin farinciki sosai ba. Haka dai take rayuwa daga fada sai masifa sai kuma muguwar hassadar Mairama da tayi sake ta kama zuciyarta sosai.


Dago labulen dakinta tayi ta fito. A wulakance take kallon kanin nata "ah'a Bature kai ne dama"


Zamowa yayi daga kan kujerar ya gaisheta. Bai manta zuwansu da sallah ba inda ta karesu musu tas wai sun haye kujeru abinda ba'a saba ba. Da suka koma gida kowa yana korafi suna cewa da Adda Mairama ce bazata musu haka ba banda shi don ransa ya baci. Ya dai ci alwashin idan ba aike ba babu abinda zai sake kaishi gidanta. Gaisuwar kuwa albarkacin mai aikinta da ya gani ne kada ace basu da hadin kai. Kusan halinsu daya da Mairama shiyasa Malamijo ya aiko shi don sauran babu mai yarda yazo.


"Wani abin ne ya faru kazo ko kuwa?"


Shigowar Salisu kenan yaji yadda take yiwa kaninta magana. Shi ya rasa dalilinta na kin 'yan uwanta yanzu kaf bata son mu'amala ta hadasu. Nashi dangin ma bata raga musu amma yana daf da magance matsalar nan.


Bature ya gaishe shi ya amsa a mutumce sannan yace ta biyo shi daki. Bakin nan a gaba ta bi bayansa.


"Me yake damunki ne? Yaro ya taho tun daga Sumaila babu wata tarba me kyau sai me ya faru? Yanzu ke da 'yan uwanki babu wanda zai zo don sada zumunci wurinki sai da wani dalili?" Ya jero mata tambayoyin cikin bacin rai.


Juya idanu tayi "ai dai 'yan uwana ne ba na mutum ba"


"Ni kike yiwa magana haka ko Salame?"


Bata saurare shi ba ta fice don sallamar Bature ya koma inda ya fito. Salisu ashe yana bayanta sai ganinsa tayi ya zauna yana tambayarsa mutanen gida.


"Kawo masa abinci mana Salame" ya umarceta.


Cire baki tayi ta kwalawa Kande kira.


"Ki kyale Kande aiki na ga tana yi. Kuma shi Halifa ba'a kwantar dashi ne? Kusan a bayan matar nan yake wuni ita bata huta ba shi ba'a barshi ya sake yayi wasa ba"


"Idan ta sauke shi damuna zaiyi. Kuma dai tunda biyanta akeyi meye a ciki?"


"Babu komai kuwa tunda kudinki ne Hajiya"


Magana suke yiwa juna a hasale kowa rai a bace. Bature da bashi da sha'awar kwanar musu a gida ya katse rigimar ta hanyar fada musu abinda aka turo shi ya fada. A tare suka juyo kansa. Salisu hankali a tashe Salame kuwa numfashinta taji ya tsaya na wucin gadi.


"Wane Zayyan din?" Salisu ya tattaro karfin halin tambaya.


"Mijin Adda Mairama."


"Salame kin..." kasa karasa magana yayi ganin ta tafi luuu kamar zata fadi ta saki kara iya karfinta.


Maimakon Salisu ya tarota sai mamaki ya kama shi har ya kasa motsi. Salame ce fa da yasan bata kaunar kanwarta. Me zai sa ta shiga wannan yanayi kamar ance mata shi da kansa ne ya mutu ko mahaifinta.


Bature ma abin ya daure masa kai "Adda cewa nayi mijin Adda Mairama fa ba Malamijo ba"


Zama kawai tayi dabas akan kujera tana kuka sosai. Shikenan Zayyan ashe bata da rabon zama dashi. Salisu ya kawar da kai daga gareta.


"Bature yau zaka koma ne?"


"Yanzu ma kuwa in sha Allahu. Gobe za'a tafi gaisuwa"


Zumbur ta mike "ku biyo min, ko kuma dai ka jirani na shirya"


Tsawa Salisu ya daka mata "koma ki zauna. Bature muje"


Bakin gate ya raka Bature ta bashi kudin mota sannan ya koma ciki. Tana nan tana rusa kuka Kande na bata hakuri. Yana zuwa ya finciko hannunta sai da Kande ta tsorata. Dakinsa ya kaita ya jefata kan gado  iya karfinsa. Fuskarsa a daure babu wasa ko kadan ya jefa mata tambayar da ta kada mata hanji.


"Tun farkon haduwarmu dama Zayyan kike so?"


Shiru tayi sai faduwar gabanta da ta tsananta.


"Ki bani amsa mana!" Ya sake yi mata tsawa sai da ta firgice.


Wasu sababbin hawayen ta soma yi yaji kamar ya rufeta da duka.


"Kin cuceni, ban dade da aurenki ba zuciyata ta bani cewa ban yiwa kaina adalci wurin zabar matar aure ba. A tunanina na auro mace mara son zumunci ne kawai da raina na kasa da ita. Ashe kin wuce haka. Salame mijin kanwarki kike so kuma har kike kishi da ita alhalin kina gidan naki mijin"


Har yanzu ta kasa magana sai kuka. Shi din ma nasa idon da hawaye saboda bai taba kawo hakan a matsayin dalilin da yasa take yiwa Mairama haka ba.


"Bazaki je Sakkwato gaisuwa ba" kallonsa tayi da sauri ya sake hade rai "ke daga yau sai abu yayi tsanani sosai zanyi miki izinin fita kina ji na. Idan kika karya min doka wallahi, wallahi sai na shayar dake mamaki"


**********


Ranar da aka sallami Mairama a ranar Mal Aminu da Jume su ka amince da a kwashe kayanta ta koma gidansu Zayyan. Idan iyayenta sun zo sai su tafi da ita gida. 


"Ku wuce da ita su Mubaraka sai su zo a kwashe kayan gobe tunda zaman barikin babu amfani"


Mairama tana jin haka ta ajiye kunyarta a gefe "Kawu ina son zuwa don akwai abubuwan da nake son hadawa da kaina"


Caraf a kunnen Maikudi "ko ma meye muma din jinin Zayyanu ne. Kije ki huta ni da kaina zan jagoranci zuwa a debo kayan saboda kada wani abu ya salwanta"


Soye idanu tayi don bazata yarda a hanata zuwa ba. Ta nuna musu akwai makota da take son yiwa sallama irinsu Christie wadda bata kara gani ba tun lokacin da tace zata je yi mata girki. 


Mal Aminu yace "Ka barta taje Maikudi. Daga nan ma sai mu bincika muji ko akwai wani abu da zasu bawa iyalin mamatan. Mu bari jikinta ya kara kwari ko nan da kwana biyu ne" 


Ransa baya so saboda ya kula tunda ta dage sai taje akwai dukiya dankare a gidan da bai taba zuwa ko kofarsa ba. 


"Ina mukullin a bani na rike saboda 'yan barka da gaisuwa kada wata ta dafe"


"Maikudi kenan, ko ma wacece ba sai dai muce Allah Ya bada sa'a ba. Sata a gidan soja, gidan sojan ma a cikin bariki kamar mutum ya tashi da burin karar kwana" Gwaggo Ladi ta gwaba masa magana.


Bai sake magana ba su ka tafi gida. Jume tasa matan su Badaru gyarawa Mairama dakin Innar Zayyan. Tana shiga ta tuna ranar sunan Radhiya da hotunan da suka yi da Zayyan da Awwab a ciki. Idanunta da basa rabo da hawaye suka fara abinda ya zame musu jiki yanzu. 


Jume da kanta tazo tace mata ta shirya ta fito zata yi mata wankan jego. Jariri kuma Gwaggo Ladi ta dauka tayi masa wanka irin wanda bai samu ba tun ranar haihuwarsa saboda kasancewarsu a asibiti.


**********


"Ya muke ta bin lungu ne yaro? Nayi zaton a irin unguwannin nan da suke malale da titi gidan yake" 


Rayyanu ya kalli Malamijo ya sake daure zuciyarsa a karo na barkatai ya bashi amsa akan irin wadannan tambayoyin da yake ta yi masa.


"Gidan iyayenmu ne a nan unguwar. Zayyanu a cikin bariki ya zauna da iyalinsa"


Malamijo sai murmushi "Auhooo ko da naji. Ca nake a nan Mairaman tawa ta zauna ne"


Su hudu ne a ayarin tafiyar banda Rayyanu suka biyo motar haya. Nene Marka, Malamijo, Hajjo da kuma Salisu. Gidan yanzu Yadikko da Hajjo ne kawai a gidan, ya saki Dije da Inno yana shirin karo wata. Tun a tashar Kano ana cewa a kawo kudin mota Malamijo ya shiga tarin karya, daga baya ma sai yayi gaba yana dukan kirji sai da ya hango Salisu ya biya musu kudin motar su duka sannan ya dawo yana cewa kwarewa yayi.


"Sai ji nayi wani abu siririt ya wuce min ta makoshi. Kwarewa babu dadi, ammm nawa ne kudin motar ne?"


Nene tasan dalilin tafiyar tasa sai kawai ta dauke kai. Hajjo ce ta fada an biya yayi wata barazanar zura hannu a aljihu zai dauko kudin ya bawa shi. Sal da Salisu yace ya bari duk daga ne.


Iyaye da dangi duk lalacewarsu sunfi ace baka da kowa. Sallamar Malamijo kawai Mairama taji ta sa kuka sosai. Kuka ne na ganin babban gatan da ya rage mata duk fadin duniyar nan. Shine bango abin jingina a gareta wanda take sa ran idan tayi kukan rashin miji zai rarrasheta yace ta barwa Allah komai. Idan tayi kukan rayuwar marayunta zai yi mata alkawarin matsawar yana numfashi 'ya'yanta bazasu tagayyara ba.


Jikin Nene Marka ta zube suna kuka tare. Malamijo ya tausayawa Mairama sosai ya mika hannu ya dauki Radhiya. Zayyan wanda duka gidan an rasa mai kiran sunansa har Maikudi kuwa saboda tuna musu da marigayi da yake yi matar Badaru ta kwanto daga bayanta ta mikawa Hajjo.


"Iko sai mai shi, Malamijo dubi yaron nan don Ma'aiki."


Radhiya tana gefensa ya karbi jaririn yana kare masa kallo. Salisu yazo ya karbe shi shima ya ga kama sosai da mahaifinsa.


"Allah Ya raya mana kai karamin soja

"

Mazan sun koma waje inda ake zuwa yi musu ta'aziyya matan kuma suna daga ciki. Sai dare ne Mal Aminu ya sanar da Malamijo za'a kwaso kayan Mairama sai su tafi da ita.


"A'a a bar yarinya a gidan mijinta. Idan akwai wata dukiya da bazata iya juyawa ba ni sai na tafi da ita ba wani abu."


Maikudi yayi saurin cewa "dukiyar marayu zata fi dadi a hannun dangin uba. Saboda haka gobe zamuje ayi duk yadda za'ayi ne. Gida kuma ba nasu bane na bariki ne. Tunda ya rasu dole ne su tashi komai dadewa"


A hankali zantukan nasu suka fara neman komawa rigima. Maikudi da Malamijo kowa ya nuna zalamarsa a fili. Shiyasa kowa cikinsu yake ganin dole ya tsaya akan dukiyar da basu da tabbacin akwaita.


Shabiyun rana kuwa washegari suka isa kofar gidan da ya kasance na Mairama da Zayyan kwanaki kadan da suka wuce. Ta kalli gidan Zainab a rufe har yanzu. Tana son sanin halin da suke ciki da mazansu amma yanzu babu hali sai komai ya daidaita a nata bangaren. Gidan Christie ma a rufe yake. Bayan ta bude nata gidan sun shiga da yayyen Zayyan mata da kuma Hajjo sai ga wasu cikin abokan zamansu na kusa. Gaisuwar mijinta suka yi mata da barkar Zayyan karami. Ta tambayi ina Christie wata ta bata amsa da cewa ranar da ta haihu Christie tazo tayi mata girki kuma ta farfadawa makota haihuwar. Ta koma daidai lokacin da Mairama ta suma. A nan take jin duka sojojin sun rasu ciki kuwa harda mijinta. Bata iya shiga ba ta koma gida bayan ta sauke musu Radhiya. Shine aka sami wani da ya san gidansu Zayyan aka fada musu. Ita kuma Christie ta tafi garinsu ta fadi mutuwar har yanzu bata dawo ba.


Duka matan abin tausayi musamman wadanda mazansu suka tafi a bayan su Zayyan. Suna cike da tsoro da fargabar me zai je ya dawo.


Wasunsu sun saka hannu wurin tattare kayan kitchen da na falon Mairama ana hade komai wuri guda ana fitarwa. Cikin dakin ta shiga zuciyarta tayi matukar rauni. Shikenan daga yau duk wasu memories da suka gina da Zayyan a gidan nan cikin wannan dakin sai dai zu dawo mata a tunani. Kukanta Hajjo ta jiyo ta shiga dakin da sauri.


"Haba Mairama ashe bazaki sakawa zuciyarki salama ba? Ni ko kadan ban so aka ce wai azo kwasar kaya da wuri kamar ana korarki ba. Su dakata ki sami nutsuwar zuciya sun ki"


Mairama ta bude wani akwai ta dauko envelop din da Zayyan ya bata hannu na rawa ta saka a jakar hannunta sannan aka fara hada kayan gidan.


Malamijo yana waje yaki shiga ba don kunya ba sai don bakinciki. Shi kadai a ransa yake nanata an yaudareshi aka ce masa Zayyan soja ne. To yaji sojan ne amma ba wani mai mukami bane ashe. Ji dai wannan akurki da ya ajiye masa 'yarsa ya raya a zuciyarsa. Kuma ashe ma ba nasa bane. To duka kudaden da yake masa alheri dasu a ina yake samowa? Faduwar gaba yaji da ya tuna indai fa babu wani abin kirki da ya bari komai na Mairama da 'ya'yan wuyansa zai dawo. Hodijan inji mutanensa, aradun Allah bazai iya karawa kansa nauyi ba. Yanzu fa yara goma sha bakwai gareshi. Salame ce kadai a gidan miji tunda dai Zayyan ya rasu. Gata ta tunda tayi aure ta ari rigar rashin mutumci ta saka.Tsaki yaja sai hankalinsa ya koma ciki inda yake jiyo muryar Maikudi.


"Kai wannan takadirin yaro da gani zaiyi mugunta. Me kuma yake nema a cikin mata?"


Shiga yayi da Salisu ya sami Maikudi yana fada "ki fito min da duk wani kudi ko takardun abubuwa masu mahimmanci na Zayyan. Dukiyar magada sai da saka ido. Ba wai da ka zaki dauke komai ki rike ba"


Salisu ya riko hannunsa "kaga Mal Maikudi duk abin nan ba na rigima bane. Mairama ba jahila bace da zata ci dukiyar mamaci. Sai dai fa ina so ka sani duk danginku babu mai gadon Zayyan sai Mairama da 'ya'yanta"


Kamar zai kaiwa Salisu duka ya soma fada "ni nasan ba banza ba kuka taho kwanku da kwarkwata. Ashe da manufarku. To babu wanda ya isa yayi sama da fadi da dukiyar magada muddin ina raye"


Mairama dai sai kuka. Malamijo ya zakalkale yana ta zubar musu da daraja a gaban 'yan uwan Zayyan. Idan Maikudi yayi shi za'a ce da sauran kuruciya. Shi kuwa yana mahaifinta ga jikoki har uku amma har yau bai fasa halinsa ba. 


Mal Aminu da kawunsu Zayyan sun shigo sun  same su ana ta mayar da magana. Sam Mal Aminu baiji dadi ba. Ga Mairama sai ajiyar zuciya kawai take yi.


"Daga can ofishin nasu nake an kaini har wurin wani babba cikinsu a nan munyi magana. A takaice dai muna da yawa da muka rasa 'yan uwa a wurin nan. Amma yace muyi hakuri ba'a turo komai daga gwamnatin tarayya ba da zasu sallami iyalan sojojin ko kuma masu rauni"


"Ikon Allah, yanzu ace mutum ya rasa rayuwarsa a bakin aikinku amma babu sallama ga iyalansa da maraici ya kama su?" Cewar Salisu


"Don ma baka je wurin bane. Mutanen da yawa wallahi. Sun ce kuma sojojin da aka rasa suna da yawa ba wai na nan bane kadai. Kuma wai gwamnati bata da kudi amma zasu neme mu idan an sami wani abin"


"Wannan ai zancen banza ne, bata da kudin take kashe mana 'yan uwa? Ni bazan hakura ba. Wannan magana kuma bazan bari ta mutu a nan ba." Maikudi yace yana tashi tsaye "idan ma an fada ne don a sa jikina yayi sanyi kada na tsayawa marayun nan wallahi sai naje" ya zubawa Mal Aminu idanu.


Murmushi yayi kawai yace motar daukan kayan tazo. Kawunsu ne ma ya rinka yi masa fadan baya son rashin kunya. To amma da yake duka talakawa ne maganarsu bata wani tasiri a wurinsa.


 Abu kamar wasa Mairama da tazo barikin nan a matsayin amarya kasa da shekara biyu wai har anyi zaman an gama. Mijinta abin kaunarta ya tafi ya barta a hannun wadanda basu damu da halin da take ciki ba, kawunansu kawai

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment