Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin hancinsa ya kawar da kansa da sauri "dirty girl wannan kika dora a fuskarki"


"Rashin sani, nasan yanzu fuskata wari take yi ko"


"Ban sani ba" yace yana yin gaba. Daya daga cikin mutanen ya tambaya ina zai sami ruwa yace sai dai a rijiyar da suke debowa dabbobin. Ina wani bambanci da hular da ruwan da ya tabbatar shima bashi da tsafta. Emzee ya kira ya fada masa ruwa yake so da sabulu.


Kallon rashin fahimta yayi masa "wanka zaka yi a nan?"


Awwab ji yayi kamar ya hada shi da Radhiya ya musu duka. Ghazalatu da sauran duka kallonsa suke yi.


"Abu na taba zan wanke hannuna shikenan!"


Kamar yadda ya zata su uku suka tafi siyo ruwan da Ibrahim da Zayyana. Awwab ya koma wurin da Radhiya take zaune Ghazalatu za ta bishi Fauziyya ta sako mata zancen bikin da shirye shiryen da zasu yi. Tayi haka ne don tafi son yayansu da Radhiya su fara soyayya taji dadi fesawa Mami. Bata san su ma burinsu ba kenan ga kuma rashin sanin tsakaninsa da Ghazalatu.


Kin yi mata magana yayi ita kuwa ta ga lagonsa ta biyo shi ta zauna a kusa dashi a kan katuwar jijiyar bishiyar da ta fito.


"Ko ba komai na rama"


"A'a kin dai yi kazanta kinji dadi. Me nayi miki ma da zaki rama?"


Tura baki tayi cikin shagwabar da ta koyi yi masa "Cewa kayi fa bazanyi soja ba" 


Sai da ya fuskanceta sosai yace "haka kawai kamar courses sun kare a universities ki rasa abin zaba sai soja."


"To, to ni ba so nake na gaji su Daddy ba. Kuma Babana ma ai 'Yar soja yake ce min"


" 'Yar soja da Soja daya ne a garinku. Ki cire wannan tunanin a ranki da kaina zan zabar miki course. Kin ci SSCE din dai ko"


Kumbura baki tayi cikin fushi "naci"


"Bayan bikina gida na zaki koma sai kiyi karatun a Abuja. Gara ku fara shiri da Ghazalatu tun yanzu kada na fita watarana ku tayar min da gida"


"Ha'ann lallai ma Hamma ni bazan yi auren ba har sai kayi na dawo gidanka?" Ya ma za'ayi yace haka. To zaman me zata yi musu idan ba housegirl din da Ghazalatu ta kirata ba.


"Ashe aure kike so, gara da kika fada min"


Hannu tasa ta rufe fuska wai ita kunya "kai Hamma to ai kaine wai na koma gidanka nayi karatu...shi kuma abin sai yaushe?"


"You must be kidding" 


"Me kenan ka ke nufi?" 


Dariyar da baiyi niya ba ce ta biyo bayan tambayar ta ta. Yarinya 'yar shekara goma sha tara ke zancen aure. Karatu yake da burin tayi mai zurfi kafin maganar aure. Da kyar ya daidaita kansa bayan ya hango irin kallon da Ghazalatu take jefo masa.


"Okay, seriously kina da wanda yake sonki ne?"


Sama ta kalla kamar me tunani "akwai Kawu Zakari sai na koma gida zai gabatar da kansa sosai"


Ransa yaji ya soma baci to amma yanayin maganarta ke bashi dariya "zai gabatar da kansa wurin su Ummi?"


Innocently tace "a wurina dai, ai bai riga yace min I love you din ba"


"Ya Allah" Awwab yace dariya na sake kama shi sosai.


"Don na fada da turanci kake dariya?" Ita bata ga me tayi ba daidai ba. Wato shi yayi aure ita kuma ya hanata cikar burinta na zama soja sannan bazai barta tayi auren ba ita ma sai kace wata alhudahuda zai rinka kira mata karatu.


Sai da yayi dariya mai isarsa ya fadi abinda yaje mata a bazata "Allah Ka bani Alheran Radhiya" yana kallon kwayar idonta.


Wani irin abu ne ya fizgi zuciyarta zuwa gareshi a daidai lokacin taji farinciki ya saukar mata irin wanda bata taba ji ba. A nasa bangaren sai da maganar ta fito ya fahimci nauyinta. Maganar zuci ne ta fito fili. Sai dai kuma shi ya sani cewa zuciyarsa bata raya masa karya ba haka nan bakinsa bai fadi karya ba. Haduwar kwana daya jinta yake kamar basu taba rabuwa ba. Zuciyarsa ta ginu da son wannan yarinyar tun tana cikin mahaifiyarta. Tsayin shekaru bai sa ya manta da ita ba. Ya cigaba da rainonta a zuciyarsa har zuwa haduwarsu ta jiya a inda yadda ta koma ya sake kayatar da ruhinsa zuwa gareta. Da kwalkwalin kan, shirme, shiririta da fada duk yaji ya dauka yana son abarsa a haka.


Dena kallonsa tayi don duk abinta bata da rashin kunyar da zata iya jurewa kallon da yake yi mata. 


"Ehemmmm ga ruwa ga sabulu a ina zan ajiye?"


Aikin Emzee ne da tun kafin su karaso ya hangosu suna magana. Allah Yasa Ibrahim da Zayyana sunyi wajen wata tinkiya da take haihuwa ya taho wurinsu shi kadai da ledar purewater da sabulu.


Kumatun Radhiya har wani ja yayi don tsabar kunya ta tashi da saurinta zata gudu.


"Da fuskar taki mai warin maza zaki shiga cikin mutane? Dawo ki wanke"


Emzee bai yi wata wata ba ya arce daga wurin. Ya kamata su Ummi su farga da wuri kafin a laluba a nemesu a rasa.


Sabulun ya bata ya farke ledar purewater din ya dauko daya "fara wanke wannan hannun"


Durkusawa yayi a gabanta tana cuda hannuwan yana zuba mata ruwa har ta gama wankewa.


"Saura fuska" yace mata. Sabulun ta sake sakawa ta dage hijab din ta soma cuda fuskarta ya duku gab da ita "wai nan kunya na baki ne kika kasa magana? Kowa yasan Alheran ta Awwab ce baki da wurin zama sai gidansa"


Kirjinta ne ya soma dukan uku uku ta kasa karasa wanke fuskar ya kuma cewa "cire hannunki in wanke miki"


"Me din?" Tace tare da bude idanun ta da sauri tana matsawa kada yaje ya taba ta. Ai kuwa kumfar sabulun ta shige duka idanun biyu ta soma ihu tana tsalle sai da su Fauziyya suka taho garesu da sauri.


"Kinji dadi kin tara min mutane"


"Ka dena min mita ka hure min idona...wayyo yaji"


Su Fauziyya sun kusa karasowa kuma baya son kowa a tare dasu yanzun da yake shirin daukan duka makaman yakinsa ya nemi daidaitawa da kanwarsa.


"To cire hannun mana" 


"Naki wani ne zai shiga"


A daidai nan Fauziyya ta fara zuwa gabanta ya mika mata wani ruwan ta zuba mata ta wanke fuskar. Da kyar ta bari ta hure mata idanun sunyi jazur dasu kuwa.


Awwab da yake jin hankalinsa ya tashi yace mata ya idon. Harara ta maka masa kamar ba shine ya janyo mata ba yana wasu maganganu da suke juya mata tunani.


Ana ta yi mata sannu tace su zo su tafi gida an kusa kiran sallah.


"Mal Da'u yace mu tsaya tinkiyar can da ta haihu yanzu ta kasa" Emzee ya sanar da ita.


Idanun da suka gama yin ja da kumburi ta zaro "ta kasa me?"


"Ta haihu ya kasa cire mahaifar sai shure shure take yi. Yankata zaiyi kawai mu tafi da ita gida idan mahaifar bata fito ba"


"Gida? Da wa? So kake Malamijo yasa ayi muku farfesu na kuci da burodi da safe?"


Ibrahim da Fauziyya suna dariya ta fada musu Malamijo yace ko kazarsa ce wani abu ya sameta ita zai kama.


"Hamma kai ya bawa amana kace ka karba" Ibrahim ya tuna masa.


"Ku muje na ajiyeku kawai na nemi wurin kwana a waje da safe zan dawo daukarku. Naga alama kasawar ma zata yi"


Hankalinta dama a tashe yake ta kyabe fuska yadda Zayyana take yi "bakinka ya sari danyen...."


Da sauri ya dakatar da ita kafin ta karasa fadin kazantar "ahhhhh don Allah kada ki karasa. Bazai sara ba in sha Allah" 


Ya kama kansa kuwa ta sami kofar ramawa tayi shu'umar dariyar da sai ta tashi tsokana take yinta "danyen mangwaro fa zan ce ka hanani. Ka ga bishiyarsa can da nake hawa na tsinko mu rinka dangwala da siga"


Shima harararta yayi na daukar hakkinsa da tayi sannan yace "kwadayi, meye abin dadi a danyen mangwaro da sugar?"


"Kai dai kawai ka tsorata kayi zaton danyen ka...."


Wannan karon shine fuskarsa kamar zaiyi kuka baya son jin kazantar da ta dage sai ta fada "habaaa mana Alheran!"


Sai da ta kalli su Fauziyya tace "yanzu danyen kashu din ma ban isa in fada ba? Shima akwai bishiyarsa daga bayan can"


Hatta Emzee sai da yayi dariya saboda yadda fuskar Awwab tayi. 


"Tsokanata kuke yi ko? Nasan me zanyi muku" yace yayi gaba Ghazalatu tayi saurin tarar dashi. 
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Mota suka nufa cikin sa'a Mal Da'u ya sanar dasu cewa ya fitar da mahaifar tinkiyar ta tashi. Radhiya sai murna kamar wata mutum. Kafin ta bar gidan ta kudiri niyar sai anci nama amma bazata so yau da babu hannunta a ciki ba Malamijo ya kare mata tanadi a bainar jama'a. Kowa wurin zamansa na dazu ya zauna jiki yayi ligib bare ma Ghazalatu da ta hado da tafiya daga Katsina. Suna isa gida sallar magariba suka yi. 


Abin farinciki wurin Radhiya ashe bayan fitarsu Nene Marka ta iso. Danne tsohuwar tayi cikin murnar ganinta. Yau tsakar gidan ta san anyi baki kusan kowa anan ya zauna suna shan iskar Allah suna hirarrakinsu. Ana isha Ghazalatu ko abincin da ake yi mata tayi bata iya kallo ba tayi bacci ita kadai a dakin Zahra ma taji sauki ta fito wurin 'yan uwanta.


"Nene muje in nuna miki wani abu" Radhiya tace cikin rada. Dakin da zasu kwana ta ja ta. Ganin Ghazalatu bacci take yi ta cire dankwalin ta nuna mata kan ta "kinga abinda Innawuro tayi min" tace kamar zatayi kuka.


"Me zan gani ni Marka, aski akan budurwa saboda Allah"


Caraf a kunnen Ghazalatu. Da dabara ta juyo idonta ya sauka akan Radhiya dariya ta kusa kwace mata. Ashe ma babu wani dalili da zai sa ta dami kanta akan wannan namijin. Ji take kamar ta jawo gobe ta ganta a Katsina. Yau din taki karewa tunda tazo yarinyar take like da Awwab. Bata so ta nuna masa zahirin yadda take kin mutanen nan saboda yanzu dai a cikinsu take a cikin gidansu ma. Zata jira ko ma meye sai sun koma inda tafi wayo. Da wayo da dabara sai ta kawo karshen wannan alakar tun kafin rayuka su fara baci. Tana ji Radhiya tana yiwa Nene bayanin makeron da tayi da kwarkwata da suka janyo askin.


"Da kansa zai gudu makeron nan kinji 'Yar soja. Gobe da kaina zan shiga kasuwa akwai wani magani mai kyau idan nayi sa'ar haduwa da matar kanki har sai yafi na da in sha Allahu"


"Yauwa Nene" ta rungumeta tana murna.


Tuwo taje suka ci da su Zayyana. A dakin da mazan suke ma Emzee ya kai musu nasu ba kyama ko nuna gayu Awwab yaci nasa. Jakar kayansa ya duba bayan ya gama babu toothpaste ya manto shi a gidan Mama Zainab. Tun a hanya ya tuna bai damu ba tunda da niyar komawa gida suka taho. Bazai iya bacci baiyi brush ba. Ya ma tabbatar ko Emzee ya tambaya za'a bashi amma ransa yafi raya masa ya fita, fitar ma da Alheran bai gaji da ganinta ba.


"Emzee wane irin toothpaste gareku na manto nawa a Kano"


"Close up ne"


Da murna sabanin rashin jindadi da ya kamata ya nuna yace "kash bana iya amfani dashi, akwai inda zan iya siyowa nan kusa?" 


"Kawo na siyo maka yanzun nan, da wane iri kake amfani?"


Shiru Awwab yayi zancen gaskiya bashi da wani zabi indai yana da kyau yana saya. Da dai sabulun wanka ne to baya tsallake pears masu mabambantan kamshi da sinadaren gyaran fata.


"Colgate nake so, amma zani da kaina kwatanta min"


Emzee da wayo ya gano Hamman nasu. Kallonsu yake daga shi har Radhiya ya ga ina za'a dire wannan abu. 


"Ko in kira Adda ta raka ka ta fini sanin wurare. Idan ba'a samu a wani wuri ba baza'a rasa a wani ba"


Ido ya kafe Emzee dashi yana tunanin ko dai yaron ya fahimci yadda ya damu da ita ne. Ba ya son bawa kansa kunya a gaban yara ba. To amma meye a ciki don ya damu da ita ba kanwarsa bace? Yana can yana musu da zuciyarsa Emzee ya fice ya tafi nemanta. Tana dakin da su Mami zasu kwana sun je ita da Zayyana suna damunsa da hira. Fauziyya da Zahra suna nasu dakin kowacce tana waya.


"Adda kizo inji Hamma"


"Tayi masa me a daren nan tara saura?" Cewar Mami .


"Nima ban sani ba"


Mairama addu'a take Allah Ya daidaita kansu kada a sami matsala. Zama da Radhiya idan babu soyayya fa to akwai daru. 


"Kai Hajiya yanzu bashi da ikon kiran kanwarsa?" Hajjo tayi maganar tana murmushi irin na ta fara gano manufar yaron.


"Radhiya tashi kije"


Sai dai tun suna magana Radhiya tayi gaba abinta. Nemanta suka yi suka rasa suka kwashe da dariya gabadaya.


Ta riga tayi wanka bayan magariba da suka rinka layi ita dasu Zahra kowa jiki yayi datti. Wata riga ce cotton mara nauyi take bacci da ita sai zani da ta daura da hijabi a kai. Shima Awwab can dakin da suke a bangaren samarin akwai bandaki wanda Emzee ya wanke musu shi tas suka yi wanka.


Lokacin da Awwab ya juya bai ga Emzee ba tunanin ina ya tafi ya fara yi sai gashi ya dawo yace Radhiya tana kofar gida inda ya turata yace ta jira shi. Yana fita shi da Ibrahim suka kwashe da dariya.


"Zeezee malamin soyayya. Nima na fara ganosu fa" Ibrahim yace yana mika masa hannu suka tafa.


"Idan ka sami ta ka kuma ka rasa yadda zakayi ka fada mata ka nemeni ka ga aiki da cikawa"


Daure fuska Ibrahim yayi da wasa "an fada maka na shirya ganganci ne. Idan na samu ma sai ranar kai amarya zan tura ka daukota"


"Dalili"


"Kada kaje kayi min kwace kana wannan lumshe idanun da shan kamshi tace ta fasa na fiye surutu"


Emzee sai dariya suka shiga tsokanar juna irin yadda dai matasa sa'o'insu suke yi.


Tun daga ciki ya soma hangota tana tsaye suna magana da wani da sau biyu yana ganinsa a cikin gidan. Me yiwuwa dai shima kanin Umminta ne. Sallama Awwab yayi masa suka gaisa ya shige ciki.


"Emzee yace kana kirana kuma wai a waje"


Hannuwansa ya zura a aljihu yana kallonta "aikenki zanyi dama amma na fasa dare yayi" 


"Yo ni ina tsoron dare ne kamar ba soja ba"


Tafiya ya soma yi kawai batare da sanin inda zashi ba ta bishi suna tafe gefe da gefe. 


"Alheran" ya kira sunanta daga can kasan makoshi sai da taji a jikinta.  


"Uhmm"


"Bana son ki zama soja"


Bata ga alamun wasa ba a fuskarsa shiyasa taji gabadaya ya karyar mata da gabbai. Yau sau biyu yana cewa bazata yi soja ba. Na dazu haushi ya bata sosai amma yanzu da ya fada sai taji tana son sanin dalilinsa na fadin hakan. Me yasa shi da take tunanin zai taimaka mata ta sami biyan bukata zai rinka neman rabata da abinda ta girma dashi a ranta. Kafin ta tambaye shi ya cigaba da yi mata bayani.


"Ban taba tunanin zanyi wani karatun da bai shafi zama soja ba. Infact son da nake yiwa duk wata harka ta military ce tasa na zama pilot. Na rasa abubuwa da yawa saboda aikin soja. Mahaifina ya dawo gida da kafa daya da lalurar da taso dauke masa dukkan tunaninsa, Baba Hadir yana zaune a wheelchair babu motsi babu magana" tsayawa yayi ya juyo sosai yadda zasu fuskanci juna. Ba tsayinsu daya ba amma itama tana da tsaho daidai gwargwado, duk da haka sai taji kamar ta kankance a gabansa "na rasa mutum na biyu a rayuwata da na baiwa matsayin uba sannan kike tunanin Awwab zai iya bari ki zama soja?"


Tambayar ta soki zuciyarta kamar yadda maganganun suka yi tasirin da ya sanya taji kamar tayi kuka. Babu wani abu daya da zata iya tunawa game da mahaifinta idan ka cire kamaninsa na hoto. Amma labaran da take ji game dashi ya sa take da burin zama kamarsa. Tana so nan gaba ko me ta zama idan an tashi ace 'yar Zayyan Muhammad Tureta ce.


"I may be selfish Alheran amma daga jiya zuwa yau keman kin sani cewa bazan so wani abu da zai taba min ke ba."


Kallonsa tayi ta ga idanunsa kyam a kanta sai tayi murmushi "me kake so na karanta?"


"Are you serious? Kin hakura?"


"Ba dole ba kana yi kamar zaka yi min kuka" tace tana dariya. Hamma yafi karfin komai a wurinta zuciyarta ke sanar da ita.


Da sauri tayi hanyar gida dama ba nisa suka yi ba yabi bayanta yana murmushi har suka shiga soron. Tsayar da ita yayi ya koma mota ya dauko ledar tsarabarta ya damka mata.


"Ga naki kayan ledar Allah Yasa komai yayi miki"


Tayi murna sosai ta dauko takalmi daya ta gwada yana haskawa da wayarsa don ta gani saboda hasken soron bashi da yawan da zata gani da kyau. Guda uku ne takalman biyu da jakarsu sai turare biyu, dankunne da sarka da tarkacen kayan kwalliyar da bata san yaya zata yi dasu ba. 


Sai da ta gama godiyarta ta karbi wayarsa tace ya buda mata hotuna ta gani. Daya bayan daya take binsu wani tace yayi kyau wani ta tsokane shi. Da sannu ta iso wurin hotunansa da uniform dinsa. Nan fa ta rude tana ta yaba yadda kayan suka burgeta.


Murmushi yayi mata yace "ko dai ta kusa kare miki ne zaki hakura da dreba"


"Sai soja ko likita"


"Time will tell"


"Me kace?"


"Babu komai"


Cigaba da kallon tayi ta budo wani yana tsaye da members na cabin crew dinsa a wata tafiya da suka yi da ta dace da birthday dinsa. Shi ya ma manta kafin a budewa fasinja su shiga jirgin suka kawo masa cake da gifts saboda yadda suke jindadin aiki dashi. Yana sakewa da kowa ayi raha ya wuce. Kasa yin gaba tayi da hoton duk da yayi kyau sosai amma 'yan matan air hostess din sun wani saka shi a tsakiya. Tayi gaba a hankali sai da ta gwammace bata yi ba. Wata cikinsu ce take tura masa cake a baki sauran suna tafi aka dauka. Abinda bata taba ji bane a rayuwarta na tsananin kishi ya saukar mata a lokacin. Ji tayi ina ma Ghazalatu ce ke bashi akan wannan mai dan skirt din da tasha kwalliya kamar 'yar tsana.


Gani yayi tayi shiru ya fada mata lokacin da aka yi hoton. Daga murya tayi ba da niyya ba sai dai bacin ranta a lokacin ya kai makura "ita ma wannan matsayinsu daya da waccan ne?"


"Waccan?"


Da gatse tace "Matar da zaka aura ba"


"Abokan aikina ne fa"


"To" tace muryarta tana rawa. Duk yada taso boyewa kasawa tayi hawaye kamar famfo suka shiga sintiri a kumatunta. Karbe wayar yayi ya haske mata fuska tayi saurin rufewa da tafin hannunta da kasan hijab din tana kara sautin kukan.


"Ya Allah, me nayi miki kuma?"


"Babu komai"


Hankalinsa a tashe yace "amma kike wannan kukan, akwai abinda yake damunki ne?"


"Nima ban sani ba" ta sake bare baki kukan yana karuwa.


Hoton ya kula tana kallo ya dawo da wayar saitin da zata gani sosai. Gabadaya hotunan ranar birthday din nasa akan idonta yayi marking ya gogesu. Babu kunya murmushi ya bayyana a saman labbanta.


Dage gira yayi yana mata wani irin kallo "silly girl! Kishi ko?  Ko dai ta kare miki dinne ban sani ba?"


Dinke fuska ta sake yi ta tashi. Yayi ta kiranta haushin kanta da kukan da tayi yasa taki amsa masa. Samun kansa yayi da sakin murmushi shima yaji dadi ta damu dashi. Girgiza kai yayi lokaci guda yana kwabar kansa da cewa ya kiyayi wuce gona da iri akan kanwar tasa. Duk abinda yake yi mata 'yan uwantaka da shakuwa ce


**********
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Rtd Major Mustapha tun a hanya suna ta waya da Baffa Habubakari da babban dansa da ya rako shi wan Zakari. Da kuma wannan soja wanda a yanzu yake rike da mukamin Captain shima kansa. Rikon amana da cigaban zamani yasa bai taba gazawa a wurin karbar sakon Major ba. 


A harabar Giginya Hotel inda suke sa ran yin masauki suka hadu. Da motoci biyu hilux cike da sojiji majiya karfi wanda kallo daya zaka yi musu duk wani burbudin fitsara da rashin kunya su kama gabansu Captain Onomza ya zo wurin.


Ya gaisa dasu Daddy ransa a matukar bace yace a yanzu fa zasu wuce a kamo mutumin.


"Calm down Captain, muyi hakuri zuwa wayewar gari"


"I am sorry Sir, I cannot wait Sir" ce amsar da ya bayar yana 'yar dariya saboda har yanzu yana girmama Major.


Major ma burinsa ya ga Maikudi a hannu. Tunanin wadanda suka zo dasu yayi ga gajiya ga kuma firgicin ganin sojojin. To su ma sunyi na'am da a tafin shiyasa babu bata lokaci suka wuce gidan.


Jume ce tsaye jikin bango domin baiwa kanta kariya kada ta fadi saboda zafin kalaman Maikudi.


"Kannenka kayi musu tsawa nima kayi min tsawa ina mahaifiyarka?"


"Idan bakya so sai ki bar wannan magana. Abinda ya faru ya riga ya faru amma sai tado zancen kike. To wa zaki burge cikinsu? 'Yan uwan matar nan suna da arzikin kula da ita da yaranta, meye don nima naci daga arzikinsu. Ba wan ubansu nake ba?"


"Hakkinka ne da zaka ci?"


"Ho Jume, kin ma manta lokacin da ki ka matsawa Zayyanun da kanki akan ya baki kudin gadonsa."


Sai da taji ba dadi da ta tuna irin abubuwan da ta rinka yi wa Zayyan a wancan lokacin. Gashi ya tafi ya bar mata duniyar dan cikinta ya zame mata kadangaren bakin tulu.


"Kinga ni tashi zanyi daga gidannan nan da sati guda zaki huta da ganina. Gobe zan zo da masu aikin kwashe kaya" yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar mahaifiyarsa da kunar rai.


Majalisarsu yaje ya zauna gefen wani gida inda suke wuni suna buga karta, gulmar duk mai wucewa da kallon 'yan mata. Hira suke gasu dai magidanta amma babu mutumci a tare dasu sai kyakyata dariya suke abinsu. Da yake lungun motoci bazasu iya shiga ba daga gefen titi suka yi parking sojoji suka rinka durowa daga motar harda masu bindigogi kirar AK47. Hankulan jama'a tuni suka tashi ana tunanin yau ko lafiya unguwar. Da karfinsu suke tafiya Baffa Habubakari da dansa Manu nadamar biyo wannan zugar sojoji suke yi. Tsoro suke kada su manta cewa tare suke a kafta musu hancin bindiga.


Su Maikudi sai gani suka yi mutane na shigewa gida da sauri ga sojoji suna tafe da sassarfa. Wasu cikinsu zasu tashi ya ce su zauna.


"Meye abin tsoro a soja, kanina ma har ya rasu soja ne. Ko wane mai tsautsayin suka biyo har cikin unguwa don jaraba wa ya sani"


Kamar ance ya kalli tsakiya ya hango wani mutum cikin shadda dinkin tazarce ya karkace hula yana rike da sanda ruwan kasa daga samanta da yake a lankwashe kasan kuma baki ne. Dogo ne kakkaura mai cikar haiba da zati.


"Banten uba" Maikudi yace da ya tabbatar wannan mutumin ne da suka zo neman Radhiya da uwarta kwanakin baya. Jikinsa har mazari yake don tsoro garin sauri ya bar wurin ya cambala kafa a cikin kwatar gabansa. Bai ko damu ba ya soma sauri. Captain Onomza ya gane shi da sauri ya bada dokar a damko masa shi.


"Don't let him get away" yace da karfi.


Mutum daya ne yayi kukan kura ya kwaso Maikudi gabadayansa sai gashi kwance a gaban Captain Onomza.


Hanjin cikin Maikudi ya buga wani uban sauti shi ba na yunwa ba shi ba na lalacewar ciki ba. Kallonsu yake tsakanin Major Mustapha da Captain Onomza wanne ne zaifi dan dama dama wurin sassauci. Yawun bakinsa duk ya kafe ya laso lebe ga gumi ya fara jika shi. Muryarsa kamar an takewa muzuru jela da takalmin karfe yace da Major "me yayi zafi ne haka ranka ya dade? Yarinyar nan da kaina zan kaika garin da suke. Ko makon da ya gabata naje na fada musu kazo kana nemansu shine uwar tace babu inda zasu je. To amma yanzu tunda anyi haka ina maka rantsuwa irin ta addinin Islama ko a ka ne zan dauko Radhiya na kawo maka. Kai harda kanin nata Zayyanu."


Gigitacciyar tsawar da Captain Onomza ya daka masa ita ta janyo mararsa ta saki fitsari ya soma tsartuwa. Mutane har sun fara fitowa kallo tunda sun fuskanci an kama wanda aka zo dominsa.


"Nine ka yiwa kerya yace min wife na Lt Zayyan yayi aure, baby ya mutu and you have the girl with you. Ko ba anyi haka ba"


Idanun Maikudi kamar an kasa kwai a faranti sunyi tsilli tsilli yace "ni ban fahimci me kake cewa bare na baka amsa"


Wawan mari ya dauke Maikudi dashi sai ji kake garam-garam masu leke suna komawa inda suka fito ana rufe kofofi.

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment