Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daada?"


Ummi ta amshe da fada musu sakonsa na dazu "sai ku shirya zamu tafi tare. Zamu barku a can mu wuce Sakkwato daga can muje Nijar"


Radhiya ta rike baki "Ummi wai ni din da gaske yace ko dai kin fada ne kawai don kada nace baya sona"


"Kaniyarki" ta kai mata duka Zayyan ya tare yana cewa babu mai taba masa uwa.


"Da gaske nake Daada, cewa fa yake yi idan yaji muryata gabansa faduwa yake yi" ta turo baki da takaici.


"Gonarsa take zuwa tace wai dabba ta kasa tasa a yanka. Ka kuma sanshi da dabbobinsa sarai" Ummi tace tana murmushi.


"Amma anya lafiya kuwa yake nemanmu?" Emzee yaji abin ya daure masa kai. Malamijo fa ko waya baya kiran kowa sai dai a kira shi.


Kowa da tunaninsa amma sunfi kawowa da gaske akwai matsala. Ko ma dai meye jibi da wurwuri zasu bar Abuja. Gara suyi su dawo da wuri Radhiya ta fara aikinta. Zayyan yaji dadin wannan program da zata yi yace idan tana bukatar bayani game da halin da sojojin suke riskar kawunansu a filin daga a shirye yake. Basu ankara ba suna wannan hira sai gani suka yi daya da rabi na dare. Dole aka tashi ba don sun so ba saboda hirar tayi musu dadi. Suna jindadin yadda iyayensu ke zolayar juna. Ummi tace mijinta dan saurayi ne wanda ya tafi yanzu an kawo mata wanda ya fara furfura.


 Zayyan yace "ko kiyi shiru ko na tona miki asiri su san cewa a wurin bin kwalaben mutane a gidan biki kina shanye ragowar mirinda muka hadu"


"Bonono rufe kofa da barawo...ai ka gama tonawa"


Emzee da Radhiya dariya harda hawaye. A zahiri idan kewarsa ta ishi Mairama tana bawa yaranta wannan labari amma yadda ya fada yana kwatanta yadda tayi da ya kamata dole suyi dariya. It was a time well spent a tsakaninsu.

**********


"Ikon Allah jama'a dama Zayyan yana da dan uwa da suke mugun kama banda wadda na gani a wurin Zayyan karami?" Alh Salisu yayi magana a lokacin da suke shiga gidan Baba Hadir shi da yaransa ya kasa dauke ido daga kallon Zayyan din.

 

"Nine dai Salisu ba kama bace" 


Gabansa yaji yayi wata irin faduwa ya shiga kallonsu yana jira wani yace wasa suke yi amma shiru kake ji. Radhiya ce tayi dabarar kiran su Halifa da kannensa su ka bita wurin Ummi.


Zayyan tasowa yayi ya kama hannun Alh Salisu wanda jikinsa ya fara rawa sai kuma ya soma hawaye "kai din ne don Allah? Hadir Zayyan nake gani. La ilaha illallahu....Zayyan dai nake gani."


"Nine Salisu Allah Ya dawo dani"


Mamaki da al'ajabi ne ya kama shi sosai da aka yi masa bayanin dawowar Zayyan. Wannan al'amari da daure kai yake. 


"Gashi a hanya muke ina da taro gobe da sassafe na 'yan kasuwa. Don Allah ku tsaya a gidana idan kun shigo goben." Ita ce abinda ya fada musu karshe lokacin da suka gama hira ya tashi. 


Aka tura kiran yaran sai ga Halifa tare da Emzee yace a tafi a barshi zasu taho gobe in sha Allahu shima yana son zuwa Sumailan. Alh Salisu yace babu matsala a turo 'yan matan. Kusan minti goma suna jiransu suka taho da Zayyana za'a rokawa Hibbah itama ta kwana. 


Yayi dariya "Kuna tsareni da ido na isa na hana ne" 


Kananan ma sai suka hau rigima saboda kaunarsu dasu Jawad da Femi.


"A'a kuma kada abin yayi yawa. Ku wuce muje su ma zasu taho gobe"


"Ka kyalesu mana nan da can duka gida ne. Dama su Alheran zamu ajiye a Sumaila mu Kanon zamu kwana sai a kawo su gida"


Alh Salisu yaji dadi da Zayyan bai nuna fushinsa ba da ya fada masa laifinsa na rashin kula masa da iyali. Dreban motar yaran ya roka arzikin ya koma can gidan nasa ya kwana gobe sai yazo su tafi shi kuma ya shiga mota suka tafi.


Ga alamu Halifa ya damu kwarai da Radhiya komai ya kira ta ko ya sakota a ciki. Yanzu ma hira suke yi take tambayarsa yaushe rabonsa da zuwa wurin Malamijo yace ya dade sosai.


"Gaskiya kazo muje ka ganshi. Kila ma har Gwaggo Salame ba ka zuwa gidanta ko?" Ta dan dage gira.


"Bazan miki karya ba ita ma bana zuwa yadda ya dace da ya ziyarci mahaifiyarsa. Gidan nata ne ko hadiyar yawu bana iyawa ga yaran nan nata ko sunayensu ban rike ba sai azabar roko"


Dan bata rai tayi "ba cikinku daya ba Halifa, ko zaka so ace wani bare suke roko? Wai kuwa ina dayar nan bana rike sunanta"


"Rahima? Tana can nasu gidan" yace da rashin damuwa.


"Ni kuwa da zaka gyara zumuncinku da ka burgeni. Dube ku duk bamu saba da juna ba haka su Ummi ma. Ita da Gwaggo Salame ban san yaushe suka hadu karshe ba"


"Ke Ummanmu ko gidan Malamijo bata zuwa in fada miki."


Yanayin zumuncin nasu baiyi mata dadi ba. Shi kuma da yake babba a nasu gidan sai taji ya kamata ta bashi shawarar gyara tsakaninsa da kannensa. Ko ba komai yana cikin rufin asiri zai kyautu ya rinka dan taimaka musu. Sunyi nisa suna tattaunawa Awwab ya shigo yaci karo dasu suna dariya hira tayi dadi. Tuni fuskarsa ta chanja ya koma ya kira wayarta. Tana dauka fito kawai yace ta  tashi.


A bakin mota ta ganshi ya jingina bayansa ya harde kafafunsa  da hannuwa a kirgi.


"Sannu da hira" yace fuska babu fara'a.


"Hira kuma?"


"Ba ita kike yi ba na taso ki"


Duka girarta biyu ta rinka dagewa tana wani juya masa ido da dariya "Chèri kishi kake yi? Oh my, my , my sai naji na koma wata sarauniya"


Sakin baki yayi ya kalleta kafin ya girgiza kai "mutum ma baza'a barshi ya nuna bacin ransa ba"


Kashe masa ido tayi tace "no chance baby" Wani irin kallo ya bita dashi ta tsure "kasan Allah subutar baki ne ba baby zan ce ba"


"Ah kawai kice kin girma. Daga fara saka min sunaye nan gaba ni din zaki dauke"


Kamar tayi masa kuka ta sake cewa fitowa yayi kawai.


"Saboda shine a ranki ko? Kinji me Daada yace dai ki fara hada kayanki"


Dagewa tayi bisa subutar baki ne shi kuma yayo ta zolayarta sai gashi sun koma hirarsu mai dadi. 


"Please ni dai bana son yadda yaron nan yake shige miki. Nasan dan uwanki ne bazan rabaku amma ni dai a kula kinji ko. Ina kishinki sosai Schatzi"


"In sha Allah Cheri amma nima fa kada kaje kana yiwa 'yan matan jirgin nan masu dan skirt dariya wallahi. If not za ka ganni a mafarki muna fada"


"Naji...kuma banda zuwa rugar Barkindo ki rinka zuwa hira wurin Dr Zakari. Nasanki da likitoci ba sauki"


Dariya ya bata sosai. Ita sai yanzu ta gane ashe lab attendant ne ba likita ba "ka doke kowa fa ni sai dreba ko ba abin hawa"


Sunyi ta hira  kamar kada su rabu don washegari karfe bakwai zai bar gida. Da safe da wuri ta tashi don suyi sallama duk da wayar da suka dade suna yi cikin dare don ma ya dage sai ta kwanta. Bayan tafiyarsa ba jimawa su Zahra su ma suka dauki hanya ita da Raji sai kuma tawagar su Ummi. Gidan sai yayiwa su Mami shiru don ma Fauziyya tana nan amma Ibrahim da Zayyana duk sun bisu. Shi Ibrahim zasu yi kwanaki kadan da Emzee a Sumaila su dawo Kano gidan nasa kakannin.


***********


Tun dare Malamijo yake ya da habaici a cikin gidansa wanda Hajiyayye bata fahimta ba.


"Gobe iwar haka watan tatse rashin mutumcin wasu zai tsaya."


Hajiyayye tana sakace hakori zazzaro masa idanu "me kenan kake nufi"


"Zancen zuci ne ya fito fili. Ko an hana magana ne ban sani ba?"


"Kayi abarka. A dai kula ne kada yawan surutun ya tasar min yara kasan halinsu. Yanzu duk naman da suka ci sai kaji suna neman kari"


Dauriya kawai yake a kai gobe amma yana cikin tashin hankalin rashin sanin ina shanunsa. Yau tun asuba yake gonar. Tsagerin yaron nata da yaje daukan wasu sai ya kasa saboda ganin idonsa da wasu bakin fuskoki dole ya tafi.


"Allah Ya hada fuskokinku da sarkin mayu dai amaryata" Malamijo yace harda hade hannuwa irin na mai addu"a.


Cikin Hajiyayye kuwa ya cure wuri guda a take kamar zata yi zawo "wannan wane irin mugun fata ne Malamijo?"


"Ban gane mugun fata ba. Yanzu kamar ni kinsan dadin da zanji duk ranar da na hadu da Mai Martaba Sarkin Kano Dan Lamido kuwa?"


Rai a bace tace "to meye hadin sarkin Kano da sarkin mayu?"


"Meye ne naga kin soma gumi? Namu sarkin shine sarkin Kano. Ke kuma naku Sarkin mayu. Yadda nake son ganin namu kuma nake kaunarki shine ne nake miki fatan haduwa da naku kema"


"To ba amin ba...kaga ni kudi nake so kamar dubu dari karshen wata yaran nan namu kowanne ana yi masa yanka shi kadai saboda rage karfin maitar"


Allah Yaso shi ba don abinda yaji da kunnuwansa ba da yanzu hankalinsa in yayi dubu ya tashi akan neman kudin. Amma yanzu sai cewa yayi tayi hakuri zai tanadar mata zuwa dare gobe.


Saboda samun wuri harda yi masa tsaki tace "to a hanzarta"


"To ranki ya dade"


Matsawa tayi akan katifar tana nuna masa wuri "taho mu kwanta ni bacci nake ji"


Hadiyar yawu yayi saboda sai yanzu da yake sansano tsira ya kara tabbatar da kazantarta da muguwar rama. Wa ya aike shi kwanciya kusa da ita karshe kasusuwan jikinta suje suyi masa sartse ko su soke shi.


Karfe takwas na safe ya soma kiran Ummi wai yana fata yaran sun taho tace masa tare zasu zo da ita harda Halifan Salame. 


"In kin barni na ma manta da sunansa tunda uwarsa bata san mutumcina ba. Wannan yaro ina tsammani kamaninsa ma sun bace min. Kinga sai kun taho dai. A hanzarta do Allah"


Ta gama tabbatarwa lallai babu lafiya gidan nasu. Sun kimtsa kowa ya fito suka yi sallama dasu Mami da Mama.


Emzee da akace ya sako kayan makaranta sai ya sami irin shirt dinnan da ake yi da zane zanen khakin sojoji ya saka akan bakin wando. Radhiya kuma atampa ta saka da mayafi tayi kyau sosai. Umminta kuma wani lace ne dan ubansu mai tsada da kyau ta saka green da orange ta dora orange din mayafi da farin gilashinta tayi kyau sosai Zayyan ji yayi kamar a dage tafiyar ko na awa guda ne ya samu ya yaba mata yadda ya dace. Dadinsa ma mota guda Daddy ya bashi da dreba daga shi sai ita. Motar gidansu Halifa kuma mai wuri uku ce yaran suka duru a ciki.


Abinka da tafiyar sammako da kuma rashin tsaye tsaye a hanya karfe hudu suna cikin garin Sumaila. Shekarun baya ne suka rinka dawowa Zayyan. Zuwansa garin nan na karshe lokacin da Mairama tazo yawon arba'in din Alheran ne. Yanzu gashi Alheran dinsa aure yake shirin yi mata. Bacci ko na minti biyar bai iya yu ba sai kalle kallen chanjin da aka samu. Kafin su karasa gidan Malamijo motar da su Radhiya suke ciki ta tsaya daga bakin wata kwana. Halifa ne ya sauka ya taho wurin motar su Ummi ya leka ta taga.


"Gwaggo Mairama nace bari naje wurin Umma na fada mata kunzo tazo ku gaisa kafin ku wuce Kanon"


Zayyan bai manta da wace Salame a baya ba kuma har yanzu ba wai yana dokin ganinta bane. Ya kula Halifa yaro ne mai nutsuwa daga jiya da suka kwana gashi uwa uba da ga Alh Salisu. Jiyan da Mairama taso sanar dashi cewa sun rabu da baban Halifa saboda kada yayi masa maganarta sharewa kawai yayi.


"Ta san da zuwan naka ne?" Ummi ta tambayeshi.


"Bata da waya amma nasan zata zo ko don ta tayamu murnar dawowar Daada" ya kare da murmushi.


Suna kallo ya gangara daga baya sai ka rantse wani babban Alhaji ne. Girman jikinsa da irin shaddodi da yadikan da yake sakawa suke kara masa cika ido.


Malamijo yau ko kofar gida bai leke ba yana jiraj zuwan bakinsa. Abinci biyu akeyi yanzu a gidan nasa. Nasu Yadikko daban na amarya da iyalinta daban. Kunya tasa bai iya fadawa Yadikko zuwan bakin da bai ma san suna da yawa ba kuma. Ita ranta ya dade Hajiyayye kuma babu dalilin da zaisa ya fada mata. Dirin mota yaji yana kashingide a tsakar gida daga shi sai dogon wando da 'yar shara duk sanyin nan ba ji yake sosai ba ya tashi da sauri kai baka ce tsoho bane mai shekarunsa sam baya jin jikinsa. Silifas dinsa ya saka yana washe bakin nan Hajiyayye ta fito daga kitchen da katuwar cooler shakare da farar shinkafa 'yar gomnati ta dafawa 'ya'ya zasu zo su ci banza.


"Ina kuma zaka je kake wannan saurin? Ga abinci ka jira in dan tsakura maka ladan ganin ido ko"


Bai ma jira masu tare masan sun shigo ba ya dora hannuwa a kugu ya daure fuska "a cikin gidan nawa kike zancen tsakura min abinci? Ashe baki da mutumci ban sani ba. To ki jira in dawo ciki zaki ga yadda zanyi dake mutuniyar banza"


Ta tsorata sosai amma sai ta dake kada tayi saurin nunawa "ni Hajiyayye kake yiwa wannan magana? Ko magagin baccin da ka soma ne bai sakeka ba?"


Kallon banza yayi mata harda su juya idanu yau take sallah fa a wurinsa ya fita a gaggauce. Kiris ya rage ya saki fitsari da ya ga 'ya'yan Hajiyayye ne ashe a akori kura manyan mazan su uku katti dasu tamkar ba daga cikinta suka fito ba. Dirowa suka yi daga bayan motar suka cewa dreban yaje gidan gonar ya jirasu. Zasu ci abinci ne su zo a dauko shanu ko hudu ne idan motar zata dauka. Idanun Malamijo sai suka kawo ruwa ya fara kokawa da kwalla. Samarin suka sauko kai cikin gidan suna muzurai su a dole mayu 'ya'yan mayya. Tsabar wulakanci basu duba tsufansa ba suka ringa bangazar kafadarsa suka shige cikin gidan. Jiki a sanyaye ya juya zai koma sai ga wasu galla gallan motoci guda biyu sun doso gidan.


Ihu ne kawai baiyi ba don tsananin murna ya koma daga soron ya tsaya yana jiransu. Jin kansa yake daidai da kowane maye da yake cikin gidansa.


Emzee da Ibrahim ne suka fara shigowa ya tarbesu cikin nishadi. Sai 'yan mata Hibbah da Zayyana sannan Radhiya ta biyo bayansu.


"Malamijo nawa" tace tana murmushin da ta saba idan zata yi masa tsiya.


"Yanzu ace kin zo kasar 'Yar soja bazan ganki ba sai nayi cigiya? Ina Mairaman take? Duniya Mairama duk tafi sona kaf 'ya'yan babu mai girmama maganar Malamijo kamar ta." Yayi maganar batare da korafin Radhiya kada tayi masa wani abu ba daidai ba a cikin gidan.


"Uhmm Malamijo tare fa muke da..." Emzee ya soma fada masa saboda yana tunanin gara ya sani kada abin yazo masa a bazata.


Hannu ya yarfe gefe yana kallon Mairama da wani mutum yasha yadi na maza mai masifar kyau da tsada cikin wanda Baban Arifah yasa aka dinka masa.

"Ko ma waye su zo ku hadu ku ci uban 'yan iskan gidan nan"


"Su wa kenan?" Radhiya tace da doki sai dai Malamijo baya ma jinta ko kadan. Mutuwar tsaye yayi hannunsa a kahon zuci yana farfar da idanu bakinsa ya kasa hada kalmar Zayyan da yake son ambata.


Zayyan na karasowa da murmushinsa ya mika hannu ya riko hannun daman Malamijo. Ai hannuwansu na haduwa Malamijo yayi sharaf a sume ya fado masa a jiki.


Dama sun sani dole ya tsorata. Emzee ya rugu zai daga shi Zayyan yace ya wuce su gyara inda zai kwantar dashi ya ciccibe shi shi kadai tamkar ya dauki yaro karami. To abu ne babu body babu alamar body. Dama ya lafiyar kura...tuntuni babu jikin Hajiyayye mayya tazo ta karasa gawar da ba tata ba.


Tsakar gidan babu kowa sai gayyar su Hajiyayye rashin wadatar dakin yasa ta dawo dasu nan duk da ma dai akwai sanyi garin. Banda cooler din shinkafa a gefe ga ta miyar da ta wadatu da nama na tinkiyar da suka dauko jiya ga salad da su tumatir yau din bushasha za'ayi saboda jiya sun tarki sa'a. Shanun da suka dauka suna ajiye a gidan Talle ranar kasuwar dabbobi zasu kai a kwashi naira.


Da sauri Emzee ya shigo sabuwar tabarmar da ta shimfida yaran nata sun soma zama ya murtuke fuska duk da bai sansu ba "kai ku tashi"


"Yaro kai kuma daga ina?" Babban cikin nasu ya tambaya yana masa kallon raini. Ido kawai Emzee ya watsa masa yaja baya da sauri. Tsabar training sai budewa kwanjinsa yake yi musamman daga kirji, hannuwa suna murdewa irin na kakkarfan namiji. Rigar jikinsa ma kusan ta kama shi ita ta karasa tona asirin yanayin jikin nasa. Wanda ya rage akan tabarmar mai bin babban ya kalla yayi masa alamar ya tashi.


"In naki fa?"


Emzee bai sake tunani ba ya ja tabarmar ya kifar dashi a wurin ya koma gefen dakin Malamijo ya shimfide masa ita sannan ya shiga ya dauko masa filo. Radhiya dakin Yadikko tayi da sauri ta same shi a rufe da karamin kwado sai ta je na Hajjo. Nan ta tarar da komai ba yadda ta sani ba sai karajin Hajiyayye daga bayanta.


"Ke daga ina kuke ne kike leka min daki?"


Da mamaki tace "dakinki? Ina Hajjon kuma?"


Daidai nan Zayyan ya shigo da Malamijo a hannu ya kwantar dashi a inda Emzee ya nuna masa Ummi tana take masa baya hankali a tashe.


"Ku su waye ne?" Hajiyayye ta matso inda suke ta kalli Malamijo ta watsar.


Cikin salama Ummi tace mata "ni 'yarsa ce wadannan kuma yarana ne da babansu"


Tsaki taja duk da suturun jikinsu sunyi mata kwarjini amma bata so raini ya shiga tsakaninta dasu. Yadda uban yake tsoronta to kowa ma fa yaji tsoro kada a kawo mata wargi ba dauka zata yi ba.


"Me ya same Malamijon?" Tace a dakile wanda tuni ran kowa ya sosu.


"Tsorata yayi ya suma" Ummi ta bata amsa.


"uhmmm" ta tabe baki "bana son hayaniya kamar yadda shi uban naku ya sani a kiyaye"


Hayaniyar da take yi ce tasa mutanen cikin gidan suka fara lekowa ganin da wa take yi. Na'e ce kawai da wasu cikin yaran. Yadikko sun tafi asibiti da Atine guda cikin jariran babu lafiya ko ta kan Malamijo bata bi ba da zasu tafi. Ita yanzu burinta kawai Atine tayi arba'in yaran su kara kwari itama ta tafi. Shekaru sama da arba'in tana zaune tamkar sharar gidansa ta kula masa da yara ya bude baki ya fada mata magana son ransa.


Kannen Mairama da suke zawarci su biyu da sauran kannensu duk sunyi zuru zuru amma ganinta sai gasu sun fara sakin fuska suna yi musu barka da zuwa.


Hajiyayye ta wani daka musu tsawa saboda tsaurin ido "ba cewa nayi idan yaran nan sun zo cin abinci kowa ya zauna a daki ba? Ko shi Malamijon bai nanata muku ba kafin shigowarsu?"


Mayunwatan yaran kananun suka matso suna jira ta zuba musu ta kalli tabarmarta "ku shiga dakinsa akwai tabarma a bani tawa zan ciyar da yaranmu"


Zayyan da Mairama sun tsaya ne kawai kallon wannan mata mai zubin mahaukata tana ta bada umarni a gidan. Daurewa tayi ta tambayi wata kanwarta matsayinta a gidan.


"Amaryar Malamijo ce"


"Amarya kuma?" A iya saninta babu sauran wuri a gidan nasu to wa ya saka. Sai gashi kafin ta tambaya ma ta bata amsa da cewa Hajjo ya saki "Malamijo Hajjo?" Tace kamar tayi kuka.


Kanenta da suke karatu a Kano gidanta su Laila duka lokacin da suka zo kafin ta wuce Abuja tasa sun tafi hutu wurin iyayensu mata. Ta san da tuni ta sami labari a wurinsu.


Babu wanda yayi motsi da Hajiyayye tace su dauke Malamijo daga kan tabarmarta ta doki cinya tana sababi wai zai farfado ya sameta ne sai ya yiwa bakin nan bayanin matsayinta.


Abin takaicin ya ishi Zayyan zaiyi magana Ummi ta dakatar dashi ta nuna masa Radhiya da take bin matar da wani irin kallon raini 

"Baki ga suma yayi bane kike zancen a baki tabarma ku ci abinci?"


"Yarinya kada kice zaki yiwa Hajiyayye rashin kunya wallahi sai na farfasa miki jiki yanzun nan a wuce wurin" babban yace a kule yunwa na cin hanjinsa an tsaya ana bata musu lokaci. Ko kadan daga uwar har yaran basu da da'a.


Sai da ya gama Radhiya ta tafi gaban kulolin da ta kula suna yiwa kallon mutumci ta bude da ta ga miya ce nama ya kusan cika ta.


"Wa ya baki izinin taba min abinci? Ke idan Malamijo ya farka zan iya sawa ya hanaku sake zuwa gidan nan"


Emzee da Ibrahim Radhiya ta nunawa kulolin da hannu tamkar ba da ita ake magana ba "bros ga fa abinda ya kawomu Sumaila kuzo mu fara aiki"


Tamkar masu jira suka je zasu dauki kulolin nan yaran Hajiyayye suka yi kukan kura tamkar mayun gaske. Duk abinda suke yi Malamijo ya farfado ya ma dan bude ido da ya ga abu ya soma kankama ya runtse kayansa ya cigaba da kwanciya. Ummi da Daada wuri suka samu suka zauna saboda abin kunya ne ace suna da su Emzee su rinka saka baki suna magana da yara irin na Hajiyayye. Ummi tana da yakinin indai da yaranta a wurin bata da matsala don ko da Radhiya kadai ta barsu ta ishesu.


Wurin ke neman kacamewa Radhiya ta kira Zayyana ta nuna mata kula daya tace ta zauna a kai itama ta zauna akan daya ta dora kafa daya kan daya. Tsagerun Hajiyayye suna son tashinsu amma yadda take kada kafa ga wasu maza a tsaye a gefe wato Emzee da Ibrahim kowa ya tamke fuska duk sai suka sha jinin jikinsu. Malamijo da yaji abin baiyi masa ba ya dan kyallo ido daya yace "Zayyan"


Uba da da ne suka amsa a tare. Wai shi Malamijo a tunaninsa ko dai Hajiyayye mayar gaske ce take son tsorata shi da fatalwar surukinsa zai daure ai ba'a san Fulani da tsoro ba ya dauke kai kamar bai ganshi ba ya cigaba da cewa Emzee "ina rundunar sauran sojojin da kace zaku zo tare?"


Ba yaran ba Hajiyayye ma sai da cikinta ya bada sauti "soja kuma"


Emzee ya sake mazewa sai lokacin ta kula da kayan jikinsa ma. Hankalinta yayi mummunan tashi kuwa a tsorace ta cewa manyan su fita zata san abinyi. Su ma da sauri suka fita din kada rundunar sojojin su iso. Tana kallo Radhiya ta kira yaran gidan suka debo kwanaku yau ko biki ake a gidan sai haka. Abincin nan tas ta rabe musu harda kwakkwafe kular bata bar ko kwayar shinkafa ba. 


Zayyan kallonta yayi ya saki murmushi kawai tana kara burge shi. Haka yake kaifi daya kuma haka yake son 'ya'yansa. Kada su cuci kowa kuma kada su bari a cuce su. Bayan ta gama ta tura kular wurin wanke wanke ta dawo kusa da Malamijo ta zauna. Hajiyayye ta rasa me ya kamata ta yi saboda bacin ran da take ciki. Wannan wane irin mutane ne suka shigo gidan da yake karkashin mulkinta suna neman chaza mata kai. Kwafa tayi ta bar wurin ta tafi daki zugar yaranta suna biye da ita ana kukan nama. 


Malamijo sai lokacin ya bude ido yana murmushi a hankali yadda babu mai ji sai na kusa dashi yace "Alakakai gayyar mayu daga nan ma sai gidan tsoho"


Radhiya tace masa "fadi da karfi mana taji Malamijo a haka bazata san kana yi ba"


"Barni da ita a hakan ma kun more min su. Bana so taji ne ta dawo"


"Barka da yamma Malamijo" Zayyan yace bayan yaran sun gama dariyar kalaman Malamijo.


Jikinsa ne yayi wani mugun sanyi kamar an sare masa gwiwa ya juya ya tabbatar Zayyan din ne dai yake gani kawai sai ya koma ya kwanta ya rufe idanu.


"Mairama kirawo matar nan tazo ta tsallake ni."


"Tsallakewa kamar wata mayya"


"Yo ba mayyar bace? Aure ne na kaddara na kwasowa kaina. Yanzu don bala'i ko yaya na kalli bangaren arewa maso gabashin inda kike zaune sai in rinka gane gane"


Ibrahim da Emzee ne suka fara dariya Ummi ta hararesu. Zayyan da ya gane dashi ake dole ya rike tashi dariyar a gaban suruki.


"Kamar me da me kake gani?" Radhiya ta tambayeshi tana danne dariyarta.


Fuskarsa sai tayi kalar tausayi ya kalli Ummi yana girgiza kai "ina tsoron fada in saka babarku kuka". Kasa daurewa yayi da ya kyalla ido ya kuma ganin Zayyan a zaune " 'Yar soja mai kamar mahaifinku matar nan tana son yi min cune. Dadin abin ma dai tsakanina dashi sai alheri har muka rabu muna mutunta juna"


Dariyar kowa a take ta fito fili Zayyan ya

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment