Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yi yace ko me ya faru kada ta damu. Ummi kuma tace za'a daukar mata lesson teacher a gida. Bayan ta koma wurin Radhiya wayar Malamijo Ummi ta kira ta fada masa.


Fada yayi kamar ya ari baki karshe yace "Mairama kinga hakkinki ko"


Hawaye ta soma yi "Malamijo ka dena fadin haka kaddararmu ce daga ni har Rahiman"


"Ai ko ban fada ba hakan ne. Salame ko kadan bata da hankali. A da bata damu da Rahima ba yanzu kuma hakkin yarinyar nan bibiyarta yake duk inda ta zauna bata da zance sai Rahima kamar wata sabon kamu. Tayi ta nunawa mutane kafarta wai ita tayi mata lalle..."


Dariya ce ta nemi kwacewa Mairama tace "Kayi hakuri ba da niyar bata maka rai na fada ba"


Albarka ya rinka saka mata yace ba da ita yake fushin ba yana dai jira ya gani ko wannan dalilin zai sa Salame ta dawo hayyacinta sosai. A yadda ya tsara Na'e da wasu ne cikin yaran zasu zo Abujan. Yadikko taje Sakkwato ita kuma Hajjo taje Nijar. Maman 'yan biyu dai banda ita a wannan yawon yaranta kananu ne ga zaman mota.


**********

Bikin kwana biyu suka halarta a Jos tare da su Tante Nasara da wasu daga Nijar da suka taho tare. Kudi dai yayi kuka to amma ba abin mamaki bane duba da cewa biki ne na 'ya daya tilo ga gwamnar jihar tasu.


Gabadaya aka dunguma suka koma Abuja wasu a mota wasu a jirgi. A hanya Ummi ta rinka amai kamar zata fitar da kayan cikinta don sosai ta galabaita. Mama tana sannu tana murmushi wanda ya janyo Ummi kai kararta wurin Mami. Hakuri Mami ta bata tana gargadin Mama da ido saboda birkici musu da Ummin tayi. Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa ciki ne duk da bata je asibiti ba hankalinta duk ya tashi ina za ta kai abin kunya a cewarta. Da su ka isa gidan Daada su duka ukun suka sauka a nan ana lallaba patient. 'Ya'yan nasu basu san me yake damunta ba sai hawa suke ana mata sannu. Sai da ya rage su hudu a dakin da Tante Nasara sannan Mama ta kasa hakuri ta soma tambayarta.


Doki ne ya isheta tana dariya "Ummin Awwab anya baki harbu ba?" 


Ummi ta gama aika mata sakon harara kamar ido zai fado "kin manta bindigeni akayi"


Su duka ukun suka sa dariya ta sake hade rai lokacin da Tante tace "abar zancen wasa matar Yaya kamar fa ciki ne dake"


"Wannan ya wuce kama Nasara barka da zuwan Daada ne yake sakata amai. Sai dai muce Allah Ya inganta" cewar Mami.


"Wallahi...wallahi...." ta soma cewa sai kuma kuka sosai tana yi harda sheshsheka tace "ina zan kai wannan abin kunya don Allah. Ciki kamar wata yarinya?"


Mama ta galla mata harara "Allah Ya bamu hakuri" tana dauko DK da yake kwance akan gadon "kai taho kaji dan soyayya in yayeka in samo maka kani ko kanwa."


Fuska jajur Ummi take nunata da hannu ga hawaye yaki tsayawa "Ya isheki Zainab wannan ba abin wasa bane."


"Ni bansan ma me zan ce miki ba. Ki wayi gari bayan shekaru da dama da cikin Zayyan a jikinki abinda nasan ko a mafarki baki hangowa shine kike kuka? Mairama kyauta irin wannan ai sai sadaka da kyautata ibada. Uhmm Mami ga kanwarki nan bari na nemi Emzee ya kaini gida kada ta bata min rai" ta mike za ta fita Tante ta rikota tana cewa.


"Allah Ya shiryeku kuna abu kamar yara"


Mami ta sauke taguminta da tayi tana kallonsu suna aikin hararar juna "ni tunda nake ma na taba ganin matan da suka gagara girma kamar wadannan."


Mama tace "baki jinta ne da wani shirme wai kunya...wannan ba shine babbar shaidar Zayyan ya dawo da soyayyar Mairama ba"


Duk yadda jikin Ummi yake a mace bai hanata jifan Mama da pillow ba itama tana dariyar "Allah Ya shiryeki Zainab"


"Amin Ya shiryemu mu duka." Ta koma tana kallon Mami "saura ke fa ya kamata mu ga shaidar cewa har yau kina qalbin Major"


"Allah Ya tsareni da wannan abin kunya" tayi saurin cewa.


Ummi tace "ooooohhh da shine kuke yi min fata saboda rashin tausayi. Ni na manta yadda ake raino"


"Kin dai san yadda ake samun baby....."


Tante ta hangame baki "Haka kike Zainab?"


"Ta wuce nan Nasara ki kalleta kawai ki dauke kai" cewar Mami.


Tsokanar juna suka cigaba da yi ana cewa Ummi ta tabbatar taje asibiti duk da dai ko yanzu sun fara kirgin watanni. Babu ruwansu 'ya'ya suna shagalinsu suma suna nasu.


Washegari duk wasu masu zuwa daga wani garin sun gama isowa. Radhiya dasu Zahra da wuri suka tafi salon inda Arifah da wata cousin dinta suke jiransu. Gyaran hannu da kafa aka fara yi musu ga fatar jikinsu tana ta sheki anyi gyara har an gaji. Bayan sun gama  aka zo wankin kai. Radhiya na bude gashinta Arifah ta rike baki ganin yadda kasansa yayi wani irin ja mai duhu. 


"Dye kika saka?"


"Lalle ne" ta bata amsa kafin ta hau bayanin yadda ta kwana hudu tana kwana da lallen da take shafawa a a gashin kullum. Kimantawa tayi kamar daya bisa ukun gashin amma daga kasa take saka masa lallen shine yayi wannan kalar. Daga sama zuwa kafadunta baki yayin da kasan ya bada wata kala mai kyau. Ita da bata saka relaxer steaming da stretching aka yi mata ranar wuni guda a nan suka kwasheta.


Yau Laraba ranar da ake jira tayi. Karfe takwas mai lalle tazo dama jiya an yiwa kowa amarya kadai ta rage. Zama na musamman suka yi aka gama ja sannan aka dora baki. Karfe biyar Mama tayo waya don itama gidanta da baki haka na Mami. Su Hussaina, Nura da Hany wadda ta soma jin sauki sun taho. Gidan Mami tayi masauki sauran suna gidan Mummy Gambo.


A jikin katin an riga an rubuta tsarin events ciki harda zuwan baki daga bakwai da rabi tunda ana Magrib shida  da rabi ne zuwa takwas da kwata lokacin da za'a rufe hall a fara event. Mutanenmu da son biki babu mai son a rufe shi a waje shiyasa duk mai zuwa shiri yake da gasken gaske.


Wanka Radhiya ta silla tare da dauro alwalar magrib. Bayan ta shafa mai tayi sallah ta zura kaya don har ita Mama kira take akan idan suka bata lokaci zata saba musu ne. Riga da skirt ne na wani irin material pink da ya amsa sunansa. Rigar daidai da jikinta amma wuyan ya rufe mata baya sai daga gaba aka bude. Hannun dogo daga kasa an bude shi sosai. Shirt din ma sai daga kasan gwiwa aka saka net domin kara masa fadi. Kafin a fara kwalliya Emzee ya kwankwasa kofar dakin yana kiranta. 


Tana lekowa ya saki murmushi "my one and only Sis kinyi kyau"


Itama murmushin tayi "kai Emzee ba ayi kwalliyar ba fa."


"Duk da haka bani da ta biyunki" yace daidai fitowar Rahima ta kada kanta kawai don yanzu ta saba da halinsa. Dakin Daada ya nufa da Addarsa inda suka sami iyayensu suna jiransu. Baki yaran su ka saki suna kallon Ummi da Daada sunyi kyau kamar ranar tasu ce. Ummi lace ne baki a jikinta wanda ya amsa sunansa anyi masa wani irin adon cin baki da sky blue din zare da stones. Anyi mata kwalliya ta fito sosai tana haskawa abinka da mai yaron ciki. Mayafinta, takalmi da jaka duka sky blue ne, ga dankareriyar sarka da abin hannu. Daada kuma shaddarsa ce sky blue din aikin jikinta simple yet elegant. Yana sanye da hula zannabukar wadda ta dace da kayan. Ummi rike take da links tana kokarin balle masa a hannun rigar ta kasa. Shigowar Emzee shine ta bashi ya makala masa.


Daada yace a rufewa Radhiya ido kyauta zai bata. Emzee ne mai wannan aikin sai da Daada ya bude wata hadaddiyar sarka shigen ta Ummi sannan aka bude mata idon. Tsabar murna kuka ta saka masa ta fada jikinsa. Emzee sai ya koma gefe yana daukarsu hoto gashinta ya kwanta a bayanta. Saka mata dankunnen da sarka iyayenta suka yi tana ta musu addu'a da godiya.Kusan minti goma suna kashe selfie a tsakaninsu sannan Radhiya ta tafi aka fara zuba mata kwalliya tayi kyau karshe. Wasu kayan Fauziyya ta daukar mata a wata karamar jaka da kayan gyara kwalliya saboda idan anyi rabin taron an riga an kama musu daki da zasu chanja kaya a cikin Sheraton Hotel inda za'ayi event din.


Kowa ya gama shiri ana ta shiga mota masu tafiya da katinsu a hannu tunda card admit ne. Takwas da minti kadan Awwab ya shigo gidan ya bude wurin da wani irin kamshi mai ruda tunani da sanya shauki. Three piece tweed suit ce a jikinsa burgundy color da dark pink necktie da irin hankicin nan da ake leko dashi ta saman aljihun coat din. Yayi aski da gyaran fuska fuskarsa ta sake fitowa sosai. Yana shigowa daidai da Zayyana ta riko Radhiya saboda tsinin takalminta suna saukowa a hankali. 


Murmushi ya sakar mata ita ta mayar lokacin da zukatansu ke tsananta bugu ya karasa step na biyar inda suke tsaya ya mika mata hannu "shall we?"


Kai ta gyada a hankali tana ta murmushi ya riketa suka sauka. Su Zahra na biye dasu mazansu na waje suka je suka shiga motocin da mazansu ke jiransu. Ankonsu lace ne cream da head golden kowacce ka kalla kara. Zayyana kai tsaye motar Ibrahim ta wuce shi da Emzee su ma suit din ce jikinsu grey amma basu saka necktie ba sai maballin saman da suka bari a bude. Ba shi ba ba Emzee sai ka rasa wanda yafi yin kyau. Rahima tana biye da ita da dan glass dinta kamar a dauketa a boye Emzee ya kasa dena kallonta. Ibrahim da baisan dawan garin ba yace bari su dauki mota daya kawai suka tafi a tasa. Matan na baya suna gaba suna taba hira amma Emzee da Rahima sai uhm da uhmm.


Bakar Limousine ce ta dauki amare da angwayensu zuwa Sheraton Arifah da Radhiya suka zama bebayen karfi da yaji. Kayansu babu bambanci ko daya sai sarkarsu yayin da mazan su ma komai daya ne a jikinsu. 


Kofar hall din katuwar poster ce zaune a kasa gefen dama hoton Yousuf da Arifah wanda suka yi da shadda matan aka saka pin aka danne musu fafaren mayafansu ta tsakiyar daurin da suka sha. A bangaren hagu kuma Radhiya da Awwab sunyi tsayuwa iri daya. Matan na zaune akan kujera suna kallon fuskokin mazansu dake tsaye a gefensu sun dafa hannun kujerar. A tsakiyar hoton an rubuta sunayensu.


Kafin shigarsu iyayen taro suka taho. Kayansu saka iri daya bakin lace na Ummi da sky blue irin shaddar Daada, Mami Caramel irin shaddar Daddy, Mama light yellow irin ta Baba Hadir, Tante Brown irin na Alh Moussa sai kuma na Mom light green irin na Excellency. Idan ka cire iyayen Yousuf sauran hudun zaratan maza ne da suka dandani me ake kira bautar kasa da jiki da lafiya tare da matansu jarumai wurin hakuri da juriya. Taku suke ana daukarau hoto a cikin kayataccen hall din har zuwa mazauninsu. Bayan sun zauna be aka kira angwaye da amare abin gwanin ban sha'awa da burgewa. 


Taro ne na manyan mutane komai cikin nutsuwa da hankali ake gabatar dashi. Bayan an bude shi da addu'a aka gabatar da takaitaccen tarihin angwayen da amarensu.


Wani abin burgewa shine kiran Emzee da da MC Kdm yayi a matsayin babban abokin amarya saboda babu wanda yasan Alheran Radhiya Zayyan Tureta sama da shakikinta Muhammad Zayyan Tureta. Zahra ce ya bada tarihin Awwab sai kuma wani abokin Yousuf da kawar Arifah 'yar kanin babanta suka bada nasu. 


Can cikin taro akwai 'yan gidansu Zayyan da su Hussaina harda Mummy Gambo da yaranta. Ghazalatu ta shiga wani yanayi na tashin hankali ganin yadda Awwab ya fito yayi masifar kyau. Kallonsa take bata ko kiftawa saboda yadda take jinsa a ranta.


Ana tsaka da taron ne su ka ji wani dummm sai wanda ya sanya Awwab da Yousuf tashi lokaci guda kuma hall din yayi duhu sai haske ya koma bakin kofar shigowa. Radhiya dai taji Awwab ya matse mata hannu kadan sannan a daidai kunnenta yace mata yana zuwa. Idanu fa sai suka koma bakin kofa bayan kamar minti daya da rabi sai ga Yousuf da Awwab sun bullo ta katuwar kofar shigowa. Dukkansu sun cire coat dinsu sai ta cikin mai maballai ta gaba wadda suka dora akan farar shirt din mai dogon hannu sannan sun cire necktie sun bude maballai biyu na gaban shirts dinsu. Sanye suke da homburg hats kalar wandunansu an dan turo ta gaba a karkace.


Yousuf ne ya fara magana da mic a hannunsa daga can gefen amaren ta sama aka fara slide show inda hoton Arifah ya bayyana tana zaune cikin fulawoyi tana murmushi.


Sannu a hankali yake takowa zuwa gareta yana magana cikin harshen turanci duk da dai faransanci yafi zama sosai a bakinsa.

("Thank you Arifah Nasiruddeen for being a part of life. Thank you for accepting me to be the man in your life. You are my Queen the most beautiful woman I have ever seen. To the special you I say I love you")


Ba Arifah ba hatta Mom dinta sai da taji wata kwallar farinciki. Hannunta ya kamo zuwa tsakiyar filin idanunsu cikin na juna a lokacin da Awwab ya soma taku daidai zuwa wurin zaman Radhiya.


("Once upon a time an adorable Angel was born") hoton Radhiya ne ya bayyana ranar sunanta wanda aka daukesu tana hannun Awwab yana murmushi ya dan juyo da fuskarta yadda zata fito a camera ("You and I were always meant to be. I love you with all my heart...just so you know, it has always been Alheran Radhiya. The fearless 'Yar soja, my one and only")


Wannan karon Ummi ce da hawayen ta sunkunyar da kai Daada ya matsa mata hannu yana cewa suyi kusu addu'ar fatan zaman lafiya.


Awwab ma riko hannun matarsa yayi zuwa tsakiyar filin kusa da Arifah sannan ya yi mata murmushi shi da Yousuf suka ja baya. Kidan wakar da matasan wurin da dama suka sani ta Umar M Shareef JININ JIKINA ce ta karade wurin hasken wurin ta koma kan Awwab, Yousuf, Emzee, Ibrahim, Bilal da Raji duka sun ajiye coats dinsu kowa ya tsaya a inda ya dace suka fara takun wakar yayin da baitin farko ya cika wurin.


(Da ganinki sai na kamu.. gashi kin zamo jinin jikinaaaa)


Ba tare da kuskuren taku ko tangarda ba domin sun sha wahalar rehearsal da mai koyar da rawar da suka dauko suke miming wakar suna rawar da ko wadanda suka hau ta a film din bazasu nuna musu komai ba. Mamaki tukuru.a fuskar Radhiya da Arifah yayin da jama'a suke kallon wannan abin burgewa ana ta murmushi da dariyar farinciki.


Can gefen slideshow ake yi na hotunam da suka dauka rannan kowa yana bin baiti ana nuna amaryarsa. Saboda basu taba zato da tsammani ba shiyasa mamakinsu da farinciki yayi musu yawa.


Radhiya sai da taji kamar a wurin ta rungume Awwab ta kwana tana fada masa cewa shi kadai ne farincikinta a rayuwa. 


Sai da wakar ta kare a daidai imda suke rawa a tsugunne suna kada hannuwansu su ma su Awwab hakan suka yi wuri kuwa ya kaure da tafi kamar zasu tsaga hall din. Gashi duk yadda manyan nan suka so yin liki an saka wani abu kamar ribbon alamun babu wucewa. Suna gamawa fita suka yi haske ya mamaye wurin MC yace za'a fara cin abinci. Ana ta hayaniya da zancen yadda abu ya kayatar Fauziyya tazo ta ja amaren zuwa dakin da zasu  canja kaya. Lace suka saka coffee color da gold head da sauran accessories aka gyara musu kwalliya. Ana tambayarsu yaya suka ji game da babban surprise din su Awwab sai murmushi an rasa me cewa wani abu. To su ce me bayan amgwayen sun gama musu komai.


A wurin shiga suka hadu dasu Awwab da Radhiya na gaba su Arifah na bayansu. Wannan karon shadda suka saka golden babbar riga da hula. Sun shiga kafin su zauna aka canja waka zuwa ta Nura M Inuwa wato 'Yar amanar da Radhiya ke matukar so. Wannan karon kam iyayensu mata sai da suka fito Awwab da Yousuf basu bar komai na irin takun Zango da ya hau wakar ba suna faman baza babbar riga. Liki akeyi kamar ba'asan ciwon kudi ba Awwab ya makale matarsa a gefe ganin wurin babu masaka tsinke.


Taron ya tashi sa misalin shadaya da rabi na dare anyi hotuna anci an sha rayuka sun faranta. Ghazalatu kamar ta hadiyi tabarya haka bakinciki ya tsaya ya tokare mata wuya. Tana ta bin Awwab da ido bata san ta ina ba sai jin Nura tayi a bayanta ya rungumota a waje da suka fito ana tafiya gida. A fusace ta juyo tace masa bata son wulakanci meye haka zai tabata.


"Dazun nan na mayar dake Ghazy" yace yana shafa keya.


Ashar ta dankaro masa saboda tsabar bacin rai. Tana hangen yadda zatayi ta sami Awwab shine don rashin mutumci ya mayar da ita. Ko sauraronta baiyi ba ya jefata a motar da yazo da ita yace mata yau zasu fara angwanci.


Wuri ya watse saura mutane kadan Awwab ya karbi mota a wurin drebansu wadda yada ya kawo masa ya budewa Radhiya. Yau duk ya kashe mata baki da abubuwan mamaki. Babbar rigar ya cire da hula ya dora mata akan cinya kamshin turarensa ya mamaye hancinta ya shiga mazaunin dreba ya tada mota.


Shiru ta kasa magana sai murmushi ya kalleta yace "tunanin me kike yi Schatzi?"


Kafin ta bada amsa ya zame mata gwaggwaronta da ya zauna das a kanta ta ja mayafin da ta ce a saka mata a jakar kayan ta rufe kanta. 


"Ke nake sauraro?"


Ido ta runtse ta soma magana a hankali "Hammana bani da wani buri da ya wuce faranta maka. Abinda kayi min tun farkon haduwarmu har zuwa yau bazan taba mantawa ba. I love you with all i've got. Alheran is never complete without Awwab. Nagode, nagode, nagode" ta daga hannunta mai zoben da ya saka mata ta sumbata.


Hannunta kawai ya kamo ya rike a haka ya kaisu gida suna kallon juna suyi murmushi. Ita kuwa harda sunkuyar da kai.


Kusan kowa ya dawo ga motoci nan birjik a ciki ya samu wuri yayi parking. 


Rigarsa da hular ya dauke daga cinyarta ya jefa baya inda ya cilla mata gwaggwaro sannan ya juyo da jikinsa yana fuskantarta ya jinginar da kansa gefe.


"Baby" taji yace a hankali sai da tsigar jikinta ta tashi.


"Uhmm"


"Na gaji sosai"


"Ai dole ka gasa jiki ko ka kasa tashi gobe" ta fada gabanta na faduwa.


Hannunsa ya mika mata duk lokacin yana kallonta tana jin idanuwansa a jikinta ta dukar da kai tana wasa da yatsunta da suka sha lalle. Sai da ta sake jin sabuwar faduwar gaba ta mika masa hannun damanta.


Tayi zaton rikewa kawai zaiyi ashe hanya ya nema ya janyota gabadaya jikinsa tana kan cinyarsa. Rungumeta yayi sosai yana sauke numfashi ta soma mutsu mutsun son tashi.


"Kinga" yace yana jan wani dan compartment a gaban motar tayi arba da mukullai "na gidanmu ne, ko dai ki nutsu ko na juya kan motar a biyoki da kayanki gobe"


Da sauri tace "Kai Hammana"


"I am serious baby na gaji sosai...mun kusa wata da aure da yanzu kin fara amai da tashin zuciya...."


Salati ta soma yi kunya kamar ta nutse a wurin "ni dai babu ruwana"


"Da nawa ni kam please ki bani janbakin nan na goge miki ko kuma mu tafi gidan"


A tsorace tace "idan wani ya ganmu fa?"


"Baki ji nace janbaki zan goge ba...haka zamu fada musu ai" ya sake yi mata wani irin riko.


"Wannan fa wayo ne"


"Ki bari nayi miki wayon mana" ya kyabe fuska shi a dole zaiyi mata shagwaba.


Dariyar da ta soma yi ya datse da bakinsa tun tana jin tsoro har ta biye masa suka manta a cikin gidan Daada suke.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Da kyar ta samu ya kyaleta ta fito daga motar ko ido ta kasa hadawa dashi. Shi kuwa ko a jikinsa sai ma murmushi da yake ta yi yana rike da hannunta.


Kashe mata ido yayi yace "yau ba zaki kara shafa wani ba don kada a gane?" 


Motar ta nuna masa "shiga ka tafi ni dai"


Dariya yayi mata sannan ya dora hannunsa akan kirji ya ce "Kora ta kike yi? You are breaking my heart Schatzi, nayi zaton yau babu mai rabani dake" 


"Ba korarka nake yi ba amma yanzu ina shiga ciki kunyar su Adda Zahra zanji. Sun san fa mun taho tun dazu amma kawai sai su ga na dade ban shigo ba?"


"Kin ma bani tausayi, idan kika tare Alheran na rinka baki kunyar nan kenan. Yadda nake so matata ta rinka kulawa dani haka nima zan rinka yi miki" ya janyota jikinsa ya zagaye kwankwasonta da hannuwansa.


Kunya sosai take ji gasu a waje kuma a gidan da yake da mutane tasan ko yaushe wani zai iya fitowa. Kukan shagwaba ta soma yi masa yace to ta shige ya rakata zuwa falo. Sun kusa shiga ta fara cewa ya juya ya tafi ita bata son su Fauziyya su ganshi.


Kai ya girgiza yana janyota ta hanyar dora hannunsa a kafadarta suna jerawa "indai Zahra da Fauziyya ne ina tabbatar miki kowacce tana wurin mijinta yau babu mai kwana a nan. Femi da Jawad suna wurin Zayyana da Rahima"


Baki Radhiya ta rike "a ina zasu kwana?" 


Hancinta yaja a hankali ya juyo da ita gabansa ya rage tsayi tare da hada nasa hancin da nata yana magana a hankali "su na inda muka baro yayyen naki kowacce tasan abinda ya kamata. Wannan tsallen da muka sha sai da tausa..." kwantar da murya yayi mai kashe mata jiki "Allah Sarki Awwab tasa matar kunyar mutane tasa ko tunanin ciwon jikin da zai kwana yana y batayi ba. Dani da na biya sadaki da Ibrahim da Emzee babu maraba"


Hannuwanta ta ware kawai ta shige jikinsa ta kankame shi. Yau dinnan ya gama mata komai da performance dinsu. Hawaye take yi na tsabar son Awwab da kuma rashin son bata masa rai "Hammana kada kayi fushi dani"


"Kin wuce haka a wurina baby. Bazanyi fushi ba amma sai an rama min."


Kai ta gyada da murmushinta "na yarda"


"Ranar da aka kawoki fa..." yace yana shafa fuskarta.


"Na amince" ta bashi amsa a dake.


"Baby kada fa ki chanja shawara ba kyaleki zanyi ba" yace da warning voice yana dariya.


Juya masa idanu ta shiga yi tana jijjiga kai "meye a cikin tausa da ba zan iya ba Chèri? Allah Ya kaimu"


Karamin yatsansa ya dago ya hada da nata "pinky swear?" yace yadda yara suke yi.


"Sealed and stamped" ta kuma bashi amsa da kwarin gwiwa duk da har kasan zuciyarta tasan kawai fada take yi. Tun yanzu ma kunyarsa take ji ga faduwar gaba idan su na su kadai bare kuma ace daga ita sai shi a gida.


"Yanzu zan tafi da kwarina..." sake kissing dinta yayi ya rakata har cikin falon da babu kowa sannan ya juya ya tafi yana mitar wannan kwanaki da ake ta cinye masa na kasancewa da matarsa. Zancen zuci yake yi yana tuki "Allah Ya kaimu dai ki haifa min baby girl. Idan ta girma ana daura aure zan bawa mijinta su tafi don ni dai kam wannan tsarin bazan yarda a sake yiwa kowa ba".

**********


Yamutsa fuska Zayyan ya kula Mairama tana yi tun da suka dawo tayi wanka ta gama shirin bacci ta kasa kwanciya. Kwalbar turaren hannunsa ya ajiye ya dawo kusa da ita akan wata kujerar cushion mai laushi sosai guda daya da take dakin.


"Fillo yaya ne?"


"Warin panadol dakin nan yake yi kuma na duba ban ga inda magani ya zube ba" 


"Panadol kuma? Bana jin komai sai kamshin turaren wutar da kika saka"


Hancinta ta matse ta hanyar sake yamutsa fuska "yanzu baka jin kamar panadol ya rube?"


Zayyan bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba harda buga kafa "rubabban panadol ne dai kin tabbata ba nine na tube din ba ko?"


"Eh tayani dubawa ba wasa nake ba" ta tashi tana kokarin dukawa ya dawo da ita kusa dashi.


"Nace miki na tureki kinki yarda. Tunda kika kin taba jin panadol ya rube?"


Kunya taji tana murmushi "wurin dinner dinma fa haka ya rinka yi"


"Fillo wata nawa ne ki dena ja min rai" yace yana kallon saitin cikinta.


Wata irin kunya ta rufeta wai ita ke da

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment