Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zancen ramuwa ko tafiya gida" Mami tace tana hararar bangaren da su Zahra suke.


Kumbura baki tayi "ni dai wallahi sai dai a zabi daya"


Mairama taji kunyar kada a fara ganin ko harda sakacin tarbiya a halayen Radhiya. Fada ta soma yi mata tace ta tashi ta koma ciki ta zauna.


"Allah Yasa naji kinyi fada da wani, zaki ga yadda zanyi dake. Ana lallabaki kina wani botsarewa mutane"


"Laifinsu ne fa ki kyaleta, zo nan kinji Radhiya"


Kin tashi tayi tana kallon Zainab din tace "kema Mama na ga kamar kin danyi dariya da aka bude kan"


Mairama ta sake fusata Daddy yace duk suyi hakuri laifinsa ne amma tayi hakuri.


"Ku kuma manyan ku daku kuna tsokanarta na kusa bata kambun girma a gidan nan. Kwanannan zata zama yayar kowa da kowa a cikinku sai na ga wanda zai sake gane mata askinta" murmushi yayi amma bata ji haushi ba tunda ya yi mata alkawarin zata zama yayar kowa.


Da yake ba riko gareta ba sai ta saki fuska ta harari wannan ta harari wancan "kun dai ji me Daddy yace, kuma daga nan ma soja zai kaini abuna. Hahaha idan na dawo gidan nan za'a ga kawuna"


Zayyana sai tasa hannu ta rike nata kan tana kallonta a tsorace "yanke mana kai zaki yi?"


"Inaaa yarinya kan Balotelli zanyi muku in huce haushin yau"


Ibrahim ya tuntsire da dariya harda fadowa daga kan kujera. Zainab ta daka masa duka a baya ko a jikinsa sai dariya yake "zan rike miki su 'yar uwa, ai dai baki ganni ina dariya ba"


Major ma dariyar yake yadda ta hakikance abinta. Sauran matan babu wadda ta damu da ball ko 'yan ball balle su fahimci me take nufi da Balotelli din. Hakuri dai yayi ta bata tana kara jaddada masa burinta na zama soja tunda ta ga yana lallabata.


"Soja mai babban mukami zanyi miki amma ta cikin gida, yanzu dai ku tashi amma idan kun shiga ciki kada ki kula kowa"


"Daddy gaba fa kenan?" Tace tana ware idanunta ta rike haba.


Su Zainab sai dariya, Major ya dage yana ta bayanin cewa ba gaba yake nufi ba. Kada ta kula su dai azo ana rigima.


"Au ho...ai na hakura tunda idan na dawo daga soja zan dauki mataki. Baba zanyi kyau da soja ko?" Tace tana kallon Hadir.


Kai ya gyada mata yana murmushi. Hannunsa taje ta rike tana durkushe a gabansa ita dai tana son sa sosai, sai da Daddy yace ta bi bayan 'yan uwanta zaiyi magana da iyayenta ta fita. Da taje dakin daga bakin kofa ta wulla jakarta ciki sai gasu suna darewa da sauri don ba karamin tsoro ta basu ba. Wata shu'umar dariya tayi wani abu ma sai an dawo daga makarantar sojoji. Babu wadda ta tanka mata ta shigo ta haye gado ta kwanta. Wayar Zahra aka kira ashe Awwab ne ya ya tambayeta size din takalmin Radhiya saboda yasan suna gidan. Kintata kawai tayi ta fada masa saboda ita dai bazata tambayeta ba a yau dai sannan a gabanta bazata taba mata takalmi ba don tsoron me zai faru take ji.


A falon Daddy kuwa bayan fitarsu Mairama ta shiga basu hakurin halayyar Radhiya. Gani take kamar laifinta ne ko sakacin tarbiya ne ya kawo hakan.


"Kowane da da irin halayensa da dabi'u da ake haihuwarsa dashi. Kuma yadda take dinnan Allah kadai Yasan wace irin tarin baiwa Yayi mata. Ki dena damun kaki watarana zaki ga kamar ba'ayi ba"


Mami ce da wannan dogon jawabi sauran suna gyada kai. Daddy ya bijoro musu da zancen da sukayi da su Ardo.


"Hada Awwab da kanwarsa abu ne da na kudurta tun ranar da na dora ido a kanta. Hadir ya amince ina fata Allah Yasa ku ma ku bani goyon baya"


Gabadaya matan nan uku bakunansu murmushin jindadi suke nunawa. Mami tana maraba da wannan hadin domin bazata taba kyamar tsatson Mairama da Zayyan ba. Tafi kowa sanin mahimmancin yin hakan a wurin mijinta. Zai kara sakawa yaji a ransa cewa bai ya da iyalan Zayyan din ba. Ya so Zayyan tun basu saba ba duk ranar da suka je training zata kwana yana bata labarin fitinannen basakkwacen nan. Lokaci kalilan ne Radhiya zata waye tayi zarra cikin sa'anni. Zainab ma taji dadi don burinta su hadu su baiwa Mairama da 'ya'yanta dukkan farincikin da suka rasa. Allah Ya sani ba don sa'anni suke da Ibrahim har ta bashi watanni ba itama da zata so hadasu ne.


Farincikin Mairama yafi na kowa. Wadannan mutane masu dimbin karamci a gareta ace babu kyamar yadda su suka kara wayewa ita da 'ya'yanta suka sake ci baya ta fannin wayewa da sanin ababen rayuwa amma su nemi hada Radhiya da Awwab, Awwab dinta dai wanda ya mayar da ita da mijinta iyaye tun farkon haduwarsu. Hawaye ta shiga yi tana mika godiya garesu.


"Bani da bakin godiya, Zainab kunji wani karamcin kuma?"


"Idan kina haka sai mu ga kamar a wurinka Radhiya da Zayyan ba namu bane Ummin Awwab"


"Haba Mami kada kice haka mana, farinciki ne kawai yayi min yawa"


Mami ta tambayi Major "yaushe kake tunanin auren?" 


"Kuna ganin zamu iya hadawa da na su Zahra? Idan hakan yayi in sha Allahu karshen sati Alh Baba zai dawo daga Umara sai na fada masa"


To waye ma zaice baiyi na'am da wannan hadi ba. Bakinsu duk yazo daya, abu guda ya rage a sanar da Alh Baba sai ayi shiri aje a nemi aurenta wurin wadanda ya dace wato dangin mahaifinta na Sakkwato da kuma marikanta ta bangaren uwa su Ardo Barkindo.


**********


"Banza jaka bace min da gani ko inyi kwallo dake. Har yau ina tsananin mamakin yadda akayi na kwaso ki Salame"


Janye tsumman jikinta tayi da ya gama karewa ya tsotse babu wani tudu a jikinta bayan cikin jikinta na wata shida. Gabadaya ta mokade baka ce Salame bace da tauraruwarta ta taba haskawa a gidan Salisu. Aure dududu bai wuce shekara takwas ba amma haihuwarta biyar ga cikin na shida. Da kyar take tafiya yunwa ta yiwa hanjinta mugun lahani ga yara tun asuba suke kira mata yunwa suna kuka.


Ba ta daddara ba ta sake hada hannuwa a gaban Alh Indararo "Alhaji ko naira hamsin ce ka bani don Allah, bani da karfin karbo wankau da bazan tambayeka ba"


Kallon kin ma rainani ya jefa mata "sai ki tafi inda kika saba zuwa gidan tsoho aje a ci abinda ya sauwaka"


Duk magiya da rokonta ta bayan kunnensa tabi sai da ranta ya baci sosai ta tsaya masa kerere a gaba. Tulun cikinsa kadai ya isa ya tureta dashi ta fadi.


"Ka sakeni in koma gidan ubana ai ba a titi aka daura mana aure ba. Wannan wace irin rayuwa ce ace matanka tsakaninka dasu bai wuce ka dirka mana ciki ba. Ci da sha da sutura sai dai mu yiwa kanmu. Ko kunya baka ji duk kudinka. Mune wankau, surfe da duk wani aikin kaskanci don mu ciyar da kanmu da 'ya 'yanmu"


Marin da ya zabga mata ne yana faman nade hannun malum malum ya gigita ta ta kasa cigaba da maida martani.


"Ki fita idona Salame, wannan jarababben auren naki kuma yanzu muka fara babu inda zaki je"


Fuuuu ya fice daga gidan sai dariyar Maman Danmama da ta cika mata kunne. Bata saurara ba sai da ta fito daga dakinta tazo gaban Salame tana mata dariyar mugunta.


"Mu dai sai dai muce Allah Ya kara karawa. Ki koma wurin bokanki kice masa kwabarki tayi ruwa. Irin wadannan ranakun tsakaninki da Alhaji su kan sani nishadi da wanke min zuciya. Anyi walkiya Salame mun ganki tsamo tsamo"


Dan sauran kuzarin nata na fada marin da ta sha ya tafi dashi, shiyasa ta kasa maidawa Maman Danmama. Ita kuwa batayi shiru ba.


"Ohhh ni 'yasu. Kamar ba'ayi zamanin da kike sa Alhaji ya zage ya zanemu a cikin gidan nan ba. Kika dawo kika saka shi sakin kowa banda ni wai na zauna nayi raino kema a gidanku uwargidan babanku aikinta kenan. Ai ance tsafi gaskiyar mai shi. Kinyi kin gama surkullen tazo ta kare miki"


Wani dukunkunannen hijabi Salame ta saka taki kula Mama ta fita tare da yaranta ta nufi gida.


A soro suka yi kicibus da Malamijo zai fita. Girma ya kara kama shi sai dai akwai kyan jiki tunda babu kiba kuma yanzu ya yarda da ci da sha wa kansa mai kyau a waje. 'Yar fara'ar da ya taho da ita sakamakon faranta masa da amarya tayi kafin ya fito ce ta bace yana ganinta.


"Allah Yayi dare gari ya waye an kwaso jiki an taho cin banza. To baki isa ba Salame. Tunda na aurar dake ko dan ihsanin nan na tsakanin da da mahaifi bai taba giftawa tsakaninmu ba sai ma dai ki karkace ki fada min magana idan kinso. Amma 'yan kwanakin nan kullum ana fada min sai kinzo, kuma ba kya tashi zuwa sai kin daidaici an gama abinci. Ki kwaso yara rabe-rabe azo aci bati. To na gaji, ki juya sawunki a likkafa ki koma inda kika fito"


Jikinta har bari yake saboda yunwar dake sasakarta fushi da maidawa mahaifinta martani ba nata bane yau dinnan idan ba so take daga ita har yaran yunwa ta kar su ba.


"Ku shige gani nan zuwa" tace tana kadasu ciki.


"Ya ina cewa ku koma kina turasu? Salame, Salame ki kiyayeni." Yace yana nunata da yatsa.


"Gaisawa kawai zanyi dasu mu tafi"


Tausayinta ya dan ji saboda ya tabbatar yadda ta fige dinnan tabbas kila mijin da har shi take iya yiwa rashin kunya a kansa ya juya mata baya ne.


"Jeki amma daga yau na sake ganinki zanje na sami Alh Indararon inji ko har ya cinye sadakinsa ne shiyasa zamu fara raba nauyin. Mairama ma da take ruga ta fiki abin arziki. Makanta, rashin miji da nisa basu hanata yi min alheri ba."


Kunci taji ya ziyarci zuciyarta saboda ya ambaci kamwarta da ta mayar kishiyarta ta karfin tsiya. Duk ita ce silar komai tunda dalilinta taje wurin boka aka rabata da Alh Indararo saboda kawai bata son ta ga tayi gaba ta barta ba wai don ita din sonsa take yi ba. Da asiri ta rinka cin galaba akansa da matansa komai na tafiya daidai ta kuma saki jiki tana ta haihuwa don ta tara magada sosai. Cikin jikinta na da wata biyu bokan nata yace ga garinku. Shikenan duniya tayi mata atishawar 'yan tsaki. Komai ya lalace wai ita da take mulkin gidan a tsakar gida Alh Indararo ya kalleta yace yaushe ya aurota. Da bakinsa yake cewa ina Mairama kanwarta. Rai a bace ta shige ta ce da yaranta su taso su tafi.


"Ki barsu yanzu zan zuba musu abinci Salame" Yadikko tace mata tana kallonta da tausayawa. Ko bata ce komai ba kana kallonta kasan akwai yunwa daga ita har yaran.


"Tafiya zamuyi, kai ku tashi mana"


"Umma ki bari muci abinci" babbar 'yarta tace idonta cike da kwalla.


"Ko ku tashi ko jikinku ya gaya muku ku duka. Aikin banza kai."


Duk yadda Yadikko taso kin zama tayi saboda kawai an yabi Mairama ta gwammace su sake kwana da yunwa.


**********


Karfe biyar da rabi Awwab ya sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport da yake birnin tarayya. Ya saba tafiye tafiyensa babu wasu kaya sai 'yar jaka karama da yake saka kayan sakawa biyu ko uku ya danganta da kwana nawa zaiyi a garin. Wannan karon kuwa sai da ya hado da akwati mai kyau na turawa dan madaidaici. Jin kansa yake wasai babu tarin gajiyar nan saboda a fasinja ya taho ba pilot ba, tun daga tasowarsu sai minti goma kafin saukar jirgin ya farka.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Zainab baki yaki rufuwa "Awwab, Masha Allah sannu da zuwa...zauna, zauna kasha hanya"


Shi dai murmushi yake yi amma hankalinsa gabadaya yana wurin wannan kan dake kwance akan kujera. Allah ne Ya taimaka Zainab ta kula da me yake kallo tayi saurin dora yatsanta a baki wai yayi shiru. Dankwalin da Radhiya ta rufe kafa dashi shi ta dauka a hankali ta mayar mata dashi kanta. Sai lokacin ya iya dauke ido daga kanta ya mayar garesu. Gaban Hadir yaje ya durkusa ya rike masa hannu yana jin kwalla ta taho masa.


"Nasan ka gama jin duk wani labari a wurinsu Mami kuma ka gama kukanka. Kayi hakuri ka saki zuciyarka muyi murnar sake haduwa" Zainab tace tana kallon yadda Awwab din ya koma ingarman matashi.


Motsi Radhiya ta soma yi dankwalin yana neman faduwa aka yi sa'a ya zauna. Ita dai Zainab a tsorace take kada ta tashi a hagu su rasa inda zasuyi da ita.


"Ina Ibrahim da Zayyan karami?" Yayi tambayar har ransa yana fatan Allah Yasa ba wannan na kwancen da ya kasa tantance waye ba za'a kira da daya daga cikinsu. 


"Sun fita cikin gari amma nasan suna hanya"


Iska ya furzar yana fadada murmushinsa "da gaske? Huhhh Alhamdulillah"


Zainab sai tayi tunanin yana murna ne don tace suna hanya. Sake kallon Radhiya yayi shi dai hankalinsa gaskiya bai kwanta da ita ba. Kamar ta san tunanin da yake a kanta kuwa tayi mika ta tashi zaune. Dankwalin ya zamo daidai lokacin da ta sauke idanu akan fuskarshi. Shi ma ita din yake kallo daga sama har kasa don ya tabbatar da jinsinta sai dai fuskarta ta tsaya masa har ya kasa magana. Kai a lailaye ga fuskarta harda janbaki. A hankali idanunsa suka fara saukowa daga fuskar a kokarin kure mata kallo sai ya tsaya cak a wuyanta ya kasa karasawa yana jin wani yanayi da bai saba ba a jikinsa. A hankali ya furtawa kansa "mace ce".


Tsuke baki Radhiya tayi tana jin ba don Innawuro ce tayi mata askin nan ba wallahi da abinda zata fara yi idan ta koma rugar Barkindo shine ta sauke mata nata gashin. Waye wannan da ya cika mata ido ta kasa sakin baki a gabansa ya gane mata sirrinta. Motsa bakin ta sake yi ko ihu ne ta kwarma musu amma ta kasa. Kumatunta na dama da yake lotsawa idan tayi yunkurin magana shine ya sake daukar hankalin Awwab ya kuma kallonta da kyau.


"Kaddai? Nooo it can't be." Ya nanatawa kansa da sauri. Girgiza kai yayi shi kadai gamo da Radhiya yana nema tafiya da nutsuwa da tunaninsa.


Su Fauziyya da suka taho yi masa barka da zuwa kowacce tayi shiru kamar ta hadiyi kota suna jiran su ga me Radhiya za tayi. Dankwali dai gashi nan amma rabin kai a bude yake. Hannunta ta dora a ka taji iya ina ne a bude. Tana ji ta janyo dankwalin a hankali ta tashi bata ce komai ba ta bar falon.


Karar kofa suka ji da karfi wadda ta gwara saboda bacin rai.  Zainab ta girgiza kai su Zayyana jiki yayi lakwas. Awwab yana lura da yadda suka sauya su duka ya daure yace "Alheran?" Da sigar tambaya yana tsananta addu'a kada ace wannan ce da ta tashi yanzu.


Kamar jiransa suke suka bushe da dariya gabadayansu. Alheran din da yaci burin gani har ya kasa zaman Katsina ce. Babu wanda ya tsammaci zuwansa Kano a yau ana tunanin zai zauna ya huta amma doki ya hana. Ghazalatu har fushi tayi ya bata hakuri da alkawarin zai dawo washegari. Kin zama tayi a gidan yayi mata shiru da yawa ta tafi gidan Alh Baba wurin kakarta.


"Ita ce ta shige ciki yanzu" Zainab ta bashi amsa da dan murmushinta.


Da ba don da kanta ta amsa masa ba zai ce ko wani salon tsokana ne kuma suke yi masa don ansan yadda ya damu da ita kuma ya matsu ya sake haduwa da ita.


Da hannu ya nuna hanyar da ta bi ya marairaice fuska "wannan din?"


Basu dena dariyar ba kuwa Zainab tace "yau idan kuka shiga hannunta ko kafata bazaku gani ba"


Rige rigen bashi labarin Radhiya suka shiga yi kowa tana fadin nata. Awwab bai san lokacin da ya saki murmushi ba wato bata chanja ba kenan daga sanin da yayi mata. Shiru kusan minti ashirin bata dawo ba abinda bata saba ba. Hadir yana ta kallon kofa Zainab ta fahimce shi tace su dubo mata ita.


"Mama gaskiya ki tura Zayyana ita ce karama"


"Wani sabon abu ne kuka koya a aikeku ku tsaya zaben mai zuwa?" Awwab yace yana dan bata rai.


"Radhiyan ce ai Hamma" 


"Come on tashi ki karawo min ita Zayyana"


Tana zumbura baki ta shiga kofar hanyar dakunan. Tun kafin ta karasa take jin shesshekar kuka. Da dan gudu tayi sauri ta bude kofar dakin. Radhiya ta gani kwance akan abin sallah tana kuka fuskarta har tayi ja.


"Uhmm Adda Radhiya kizo inji Hamma Awwab"


Zumbur ta tashi zaune Zayyana ta dan ja baya kadan ta share kamar bata gani ba, cikin yanayin damuwa tace "shi wannan na falon shine Hamma Awwab din?"


"Eh"


"Kunci amanata! babu wanda yace min zai zo kuma aka ki tashina daga falo da zai shigo" Radhiya tace tana sake fashewa da kuka. Yanzu da wane ido zata kalli mutumin da taci burin haduwa dashi saboda irin labaran da ake bata. Ance mata sun shaku da tana karama kuma yana sonta sosai. Ashe ma ya zama dan gayu irin haka kamar likita amma aka bari ya ga askinta.


Zayyana komawa tayi tana jin tausayin Radhiya. Ko ita ce da kwalkwal bazata so ace kowa ya gani ba.


"Ina take?"


"Kuka take yi Mama"


Da 'yar damuwa a fuskarta tace "Yanzu dai Awwab duk kaine ka janyo wannan rigima da ka ga kanta, yau ban san yadda zamuyi ba"


"Ni kuma me nayi daga zuwana" Su Zahra ya tsare da idanuwa "me yasa baku tasheta ta rufe kan ba?"


Kusa dashi Zayyana ta zauna "haka tace wai munci amanarta da bamu tasheta ba ma"


Samun kansa yayi da rashin jindadi, ba haka ya tsara haduwarsu ba. Garin yaya ma aka yi mata aski irin haka don Allah? Sallamar Ibrahim da Zayyan ita ta katse tunaninsa. Zaratan samari ne dake ganiyar tashinsu.


"Kunga Hammana" suka ji Zayyana ta fada tana murmushi ta nuna shi.


"Naki ko namu?" Ibrahim yace yana mika masa hannu.


"Da gani kaine Ibrahim, sau biyu Zayyana tana kawo min kararka. Baka san ba'a tsokanar autar Daddy ba?" Awwab yace cikin sakin fuska.


"To kace ta dena shagwaba ko muma mu fara ko Emzee, mu dinma duka autoci ne"


Kalmar tasa ta karshe ta sanyasu dariya. Awwab ya kalli Emzee yaron is very calm sai murmushi da yake yi kawai. Ji yayi ya burge shi, a fuska ya tuna masa da babansa Zayyan sosai amma wannan Zayyan din da gani ba mai hayaniya bane. Hannu ya mika masa suka gaisa Emzee yana dari-dari ba kamar Ibrahim mai saurin sakewa da sabo ba.


"Dama kai nake jira taimaka ka fito min da yayarka wadannan duk matsorata ne" ya nuna su Fauziyya.


"Kin fitowa tayi?" Ibrahim yace da mamaki "kullum fa zancenta idan ka dawo zata dena kula kowa a gidannan"


" 'Yan cin amana sun saka mana ido ya muka iya yau sunci amanarmu" Awwab yace yana aron kalmar da Zayyana tace tayi amfani da ita.


Ibrahim yace "Mama me suka yi mata?" 


Zayyana ce ta bashi labari kafin Zainab ta soma magana. 


"Anci amana gaskiya, bari na koma cikin gari na kwana don ga dukkan alamu yau mutanen gidan nan zasu kwana da balotelli"


Emzee ya daki kafadar Ibrahim suna dariya kafin ya nufi dakin. Tana nan zaune hanci ya kumbura, idanu sun kankance sunyi ja saboda kukan da tasha. An cuceta da aka aske mata kai. Da an bar mata na zaman falon da ta roka ko babu komai zai rufa mata asiri yau.


"Adda kizo inji Hamma Awwab"


"Ni fa gida zan tafi"


Daure fuska ta ga yayi "ke babu dama ranki ya baci sai kice zaki je gida? Idan Ummi taji abinda kike yi a gidannan zata ji dadi ne? Kowa na tsoron bata miki rai kina jin dadi kamar abin kirki"


Mamakinsa ta soma yi. Emzee din da babu ruwansa ko me tace ta zauna shine yake mata fada. Jan hanci tayi "to ba kaina suka bari ya gani ba"


"Ance iska kika je sha, kina da wannan kan da kike boyewa ki rasa wurin shan iska sai falo. Yanzu da Kawu Zakari ne ya zo fa?"


"Bakinka ya sari danyen kashi, wannan ai mugun fata ne." tace tana harararsa ta tuna wanda ya dan gani a gidan Baffa Gide.


"Tunda Allah Ya rufa miki asiri ba shi din bane ba sai kawai ki basar ba irin a zuwan baki ma san me ya faru ba. Da nine ke fa wallahi da magagin baccin karya zan bar falon"


Sauran hawayen ta goge da bayan hannunta tana dariya harda kyakyatawa "shege Emzee ka iya bada shawara Yasin"


"Shine zaki zageni to" ya harareta yadda take masa.


Dan ture shi tayi bayan ta daure kanta da dankwali ta saka hijab "wasa ne dalla" ita ce a gaba yana bayanta. Sai da suka zo bakin kofar ta kasa fita tana jin kunya. Emzee na zuwa ya turata ta soma turjewa amma da ta ga kowa ita yake kallo sai ta dake yadda yace mata ta basar.


Duk da kumburin fuskarta bai hana Awwab sake gano kamannin wannan Alheran din mai askakken kai da 'yar karamar kanwarsa mai rigima ba. Ta girma amma tana nan da dan jikinta don tafi karfin a kirata ramammiya sannan baza'a ce ta shiga sahun lukutaye kai tsaye ba. Radhiya a dire take ta ciko ta ko ina. Da kadan ta dara Zayyana a tsayi ita da ake yiwa kallon doguwa saboda tsayin kafa. 


Yayin da Awwab ke kokarin hada ido da ita, ita kuma su Zahra ta kalla tana ta kokarin kada ta kalle shi. Tunda Emzee yace ta basar to fa basarwar zata yi.


"Shine baku tasheni nayi sallah da wuri ba Adda Zahra"


"Naga baccin naki yayi dadi ne"


Sai ta maida hankalinta ga Ibrahim "ka fadawa Umma ina gaisheta?"


"Tace kafin ku koma kije kiyi mata kwana biyu"


"Mama gobe zaki sa ya rakani?"


"Sai dai jibi Radhiya. Gobe asibiti zan kaiki ko har kin manta?" Asibiti za ta kaita saboda makeron da yaki barin gashinta yayi abin kirki.


Awwab sai binta yake da ido tana ta jan mutane da hira banda shi kamar ma baya wurin. Sai da Zainab tace "wai baki ga Awwab bane?"


Radhiya ta wani bude baki da idanu irin mamakin nan "laahhhh Mama yaushe yazo? Hamma, oyoyo"


Emzee tashi yayi ya sulale daga falon saboda tsabar kunya. Radhiya halinta sai ita. Yace ta basar kamar ba'ayi ba shine zata nuna bata ganshi ba gabadaya. Ji yayi kamar ya saka kuka da ma bai bata wannan shawarar ba.


"Baki ma ganni ba sai yanzu?" Yace yana kallon fuskarta. Dimple dinnan da yake saka yatsansa a ciki idan tana dariya yake kallo yana tuna masa rayuwar da.


Dakewa tayi abinta "ina na ganka na fito ina ta hira da 'yan uwa, yaya hanya? Ka ga Ummi?"


"Baki ganni ba da kika tashi daga bacci dazun nan?"


Radhiya an koyi basarwa da gaske ta wani langabe kai "yaushe? Ka dade da zuwa ne?"


Wai raina masa wayo zata yi ne? Kowa kallonsu yake yi ana dariya kasa-kasa. Hadir kansa murmushinsa ya kusa zama dariya da ya gane so take ta nuna bata ganshi ba. 


Awwab da bai fahimta ba dama shima anyi masa tambarin wauta idan abin dan farin nasa ya tashi yace "dazu fa kin farka har muka hada ido."


Tsuke baki ta soma yi. Ya kamata idan ta basar sau daya kawai a wuce wurin amma sai neman jan zance yake yi.


"Ni din? Bacci fa nayi a kan kujerar nan sai farkawa nayi na ganni a daki su Adda Zahra sun rikeni sun kaini saboda nauyin baccina, ban san lokacin da ka shigo ba"


Zahra ta soma kifta masa ido akan ya bar zancen haka shi kuma ya dage sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi.


"Lokacin da abin kanki ya zame haka " ya kwatanta da dan jan dankwalin Fauziyya " har na ga kan...."


Ihu ta saka ta tashi da sauri tana jin kamar taje ta toshe masa baki kada ya karasa fadin ya ga kanta. Kamar zata yi kuka take kallonsa "idan nace ban ganka ba sai kawai ka yarda haka ake yi ko Em..." shiru tayi ta shiga waige da ta ga baya wurin "ina Emzee?" Tayi tambayar tana kallon Ibrahim da dariya tasa ko magana ya kasa.


"Ya fice"


"Ku ga min shegen yaro, shi yace idan na basar kamar ba'ayi ba komai zai  wuce."


Gabadaya falon ya sake kaurewa da dariya. Zainab ta tashi ta kama kujerar Hadir "bari naje na bawa babanku magani, Fauziyya ku kawowa Awwab abinci ko ruwa bai sha ba tunda ya shigo kun saka min 'ya a gaba"


Gani tayi ya

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment