Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muhammadu yace sun zabi bashi nasa a kebence ne saboda sanin halin Jume da Maikudi. Shawara suka bashi ya tabbatar ya boye domin sun sani wannan kudi ba karamin gata zai masa ba. A nan hannun aminin mahaifin nasa Mal Aminu ya bar kudin kafin yayi shawarar me zaiyi dasu. Daga nan suka wuce gidansu tare.

Kamar yadda ya sanar da Zayyan haka Ghoumar ya sake yi musu bayani. Liman aka kira da wasu malamai biyu suka kasafta kudin tsakanin Jume, ‘ya’yanta shida da Zayyan. Ana mikawa kowa nasa Maikudi ya tashi yana kumfar baka.

“Yanzu kuke cewa Zayyanu akwai nasa kason a matsayinsa na danta. To kuma banda tsantsar mugunta me zai sa rabon mahaifinmu a sake kasaftawa dashi?”

Ghoumar ya harare shi “rabon gado ba da ka ake yinsa ba malam. Abu ne da Allah Ya tsara da kanShi. Zayyan yaci rabon kasancewarsa danta sannan yana da rabo a kason mahaifinsa”

Rigima ce ta kaure inda Jume da yaranta musamman Maikudi suka dage akan baza’a raba da Zayyan ba. Da ya ga abin yaci tura yace ya yafe amma Ghoumar da Mal Aminu suka ce sam sai ya karba.

Tsiya tsiya aka rabu babu dadi. Ghoumar rai a bace yace idan ya kuskura ya basu wani abu a wancan kudin nasa na shi kadai bai yafe masa ba. Dariya ya bawa Zayyan ya dai yi masa nasiha da kuma horonsa da rikon zumunci duk da yasan yanayin aikinsa abin zaiyi wuya.

Suna tafiya kuwa Jume ta kira shi dakinta suna zaune ita da Maikudi sai kumburi yake shi kadai.

“Zayyanu munyi magana da yayanka tunda kai a bariki kake rayuwa ka bashi kasonka ya cigaba da juya maka”

Magana ce ta rainin hankali ya gode Allah da wayonsa sarai amma sai ya biye mata “to Jume amma da na riga na barwa Kawun ne ya yi min kiwon a can Nijar”

Tsuke fuska tayi “kana nufin kai ba kudi aka baka ba?”

“Rakuma ne da dabbobi”

Maikudi ya tashi kamar zai buge shi don zuciyarsa na fada masa karya Zayyan din yake. Wani kallo mai firgitarwa Zayyan ya watsa masa allurer soja ta motsa. Da kansa yayi lakwas ya koma ya zauna yana kallon Jume.

“Kina kallo a gabanki yaron nan yake min kallon banza ko Jume?”

Bata kula shi ba ta sake kallon Zayyan fuska babu walwala “abinda za’ayi sai ka kawo wanda aka baka a gabanmu ya hada ya juya muku din”

A ladabce yace “Gobe da safe in Allah Ya yarda zan je wurin Mal Aminu na karbosu.”

“Shi ka barwa don kana bakinciki da karuwata?” Maikudi yace yana kallonsa shekeke.

Bai tanka shi ba yana sauraron Jume tana fada masa gobe da sassafe yaje ya karbo kudin ya kawo mata. Daren ranar har bacci ya kwashe shi yana mamakin wannan karfin hali da iko da aka ki dena nuna masa duk da ya mallaki hankalinsa.

Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke game da kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano gidansu Hadir.
[7/4, 7:38 PM] +234 806 334 4334: C
Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke game da kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano gidansu Hadir.

***********

“Ka koma ka fadawa wadda ta aiko ka na fada na kara ‘yata bazata tafi kwadayi gidan kowa ba.” Cewar Malamijo yana karkada dan jikinsa duk don ya nuna da gaske fa yake.

Yaron wanda ya kasance kanin Salame da suka hada uwa ya tashi ya bar wurin Salame na zubar hawaye. Wata tsawa Malamijo ya daka mata ta shi babu shiri jiki na bari.

“Kwalamammiya tashi ki bani wuri. Ku babu mijin babu wata sana’ar kawo dari da kwabo sai dai aci a cika min shadda da bayan gari. Mtww Kallamu kwoi mugu, ya rinka rudata sai da na kaiku bokon banza bokon hofi gashi ban ga komai a kasa ba”

Mairama da ke wanki a tsakar gidan ya nuna da bakinsa da yake turawa saitinta “ke kuma sai bakin hali ba uhm ba uhmm uhmm kinbi kin tsaneni ina mahaifinki. Ko rokona abu ba kya yi. To duk jarabar mutum dai ba’a sake uba. Nine nan dai uban naki don ko makaho ya shafaki ya shafani yasan akwai jini. Da namiji kika fito ma sunana zan maida miki Yasin”

Wankinta ta cigaba tana yi hawaye na diga a cikin bokitin ta jiyo muryar Yadikko daga dakin girki.

“Ka dai ji kunya Malamijo, kana abu yana damunka shine ka rasa da wadda zaka rinka wannan magana kamar wata sa’arka sai ‘yar cikinka. Rashin roko tayi min daidai. Masu yi din banda bakar magana me kake tsinana musu bayan sun gama keta billensu”

Hularsa ya turo gaban goshi a karkace “mutum dai ya shiga taitayinsa dani don ni dadewa bazata sa na kasa sallamar ‘yan hamayya ba”

Daidai nan Nene kanwarsa da ta kawo musu ziyara daga wani kauyen Gaya inda take aure ta idar da sallah. Magana take da niyyar yi masa akan yadda yake yi da gidansa duk da dai ba yau farau ba suka ji an banko kofar gidan.

Ta Madina ce babar Salame ta shigo ko sallama babu “gani nazo da kaina a bani ‘yata Malamijo ko in nuna maka ba kai kadai aka haifa a watan tijara ba”

Tuni tsakar gidan ta kaure da ‘ya’ya da matansa an fito kallo. Salame jikinta har bari yake tana kuka.

“Yanzu ke baki ji kunyar shigo min gida ba? Koda shike naji labarin yanzu ma zawarci kike kina neman mafaka”

Daga murya tayi cikin fada ta nuna shi da yatsa “Ali ba tsoronka nake ji ba. A bani ‘yata biki zamu na ‘ya’yan ‘yar uwata a Kano”

“Bazata ba” yace a takaice.
Fada Innar Salame ta soma yi Nene ta sa baki “Ke Salame wuce ki hado kaya kizo ki bi mahaifiyarki. Malamijo idan baka bari yaran nan suna rabar dangin iyayensu mata za’a sami matsala nan gaba”

Wani karkataccen kallo ya bita da shi kafin ya kada baki yace “ke da kika lallabo cin arziki ina ruwanki da iyalina bayan baki san zafin haihuwar ba?”

Jikinta ne yayi sanyi ta dukar da kai “Malamijo ni???”

Shima sai yaji nasa jikin ya saki don kuwa yana ji da Iyalle ko a cikin dangi “ba haka nake nufi ba. Ke Salame zo ki bi uwarki kuma sati guda na bada aka dara ban yafe ba”

Innar Salame tana tsaye tana karkada kafa daya tana jiranta ta fito. Mairama tana rakube a jikin bango wurin da suke shanya tana jin inama ita ce zata je wurin dangin tata mahaifiyar. Sai dai ina zata sami wannan damar. Mutanen da suke fulanin tashi basu nan basu can. Auren ma da Innarta anyi ne kawai saboda sauke bashin da Malamijo yake bin babanta a lokacin. Hangota Innar Salame tayi sai taji yarinyar ta bata tausayi.
“Mairama kema ko zaki bimu ne?”

Malamijo yayi wani tsalle sai gashi a gaban Mairama “wannan kuma kinyi tsararo Ta Madina, babu inda zata je”

Iyalle da kanta tazo taja hannunta ta kaita dakinsu “hada kayanki ki bisu zanyi maganin abin”

A tsorace Mairama ta hada kayan saboda gudun kada ya hanata tafiya. Basu dade ba a dakin Yadikko ta kwala musu kira suka tafi dakinta.
“Ni da Nene mun roka muku alfarma ya bari kuyi kwana goma. Idan kunje ku tabbatarwa da kanku bazaku wuce lokacin da aka dibar muku ba”

Murna a wurin Mairama kai kace bikin na dangin tata mahaifiyar ne. Salame kuwa har ta gama tsoro bai bata damar sakin jiki ba.

Da zasu tafi kashedi Malamijo ya rinka yanka musu kusan minti goma yana abu daya. Nene da Yadikko sunyi masa shigar sauri sun kuma hade masa kai ba don haka ba Ta Madina bata isa ya bata Salame harda karin Mairama ba.

**********

Kano ta Dabo tumbin giwa, birnin na Kano a yau yayi manyan baki daga garin Sumaila wato Salame da Mairama. Wata unguwa da basu san sunanta ba suka wuce zuga guda ta ‘yan biki daga Sumaila. Yadda Mairama ta saki jiki cikin mutanen sai ta baka mamaki da tausayi. Tun tasowarsu ita dai bata taba zuwa wani wuri da zata ji dadi da sa’anninta ba sai makaranta. A can ma ba wani sakin jiki gareta ba saboda tana ganin kowa yafi karfinsu. Gasu dai da uba mai kudi amma daga kayan makaranta da akwati baya basu komai. Dan siyayyar nan ta provision sai dai su gani a kwanar wasu. Shiyasa an rainasu sosai musamman Salame da sunanta ya dace da halinta.
Anyi Kamu a ranar da suka sauka da daddare inda amare aka kunshesu a daki tsakiyar ‘yan mata kawayensu da ‘yan uwa, dangin angwayen su ka zo aka feshesu da turare.

Washegari kuwa lanchin (luncheon) za’ayi a filin wani katon gida mallakar kanin baban amaren biyu.

Salame ta sami kaya kala biyar sababbi, biyu daga yayar innarta uwar amare sai uku daga Ta Madinan. Guda ta cire a ciki ta baiwa Mairama tace ta saka kada ta fita daban tunda su dai ba wasu suturun arziki na shiga taro garesu ba. Mairama sai murna da godiya ta sanya atampar da akayi mata dinkin riga da zani buba anyiwa rigar cin baki da irin lace dinnan na adon kaya a wuya da hannaye. Tayi kyau abinta gwanin sha’awa haka itama Salamen. Motoci bus bus ne aka haya suka rinka kwasarsu aka kaisu wurin bikin.

Salame tana manne da kanwarta duk da cewa dai tana sakin jiki da ‘yan uwanta suna hira. Teburinsu su bakwai ne da yake a zagaye yake suna fuskantar juna ana ta tsokanar wata cikinsu da tayi saurayi daidai kofar shigarsu gidan. Karaf idanun Salame suka sauka akan Zayyan ya nisa suna magana mai matukar mahimmanci da Hadir. Daya daga cikin angwayen dan uwa ne ga Hadir din.

Iyayensu maza ciki daya suka fito. Shiyasa da Zayyan ya iso Kano aka sanya shi cikin abokan ango. Cinikin fili suka gama kafin zuwansu nan a unguwar gandun albasa. Shi dai Zayyan ya ga wurin babu gidaje sosai amma dillalin yana ta cika masa baki cewa nan gaba kadan unguwar zata hade harma a rasa filin saidawa. Shima da yake ba mazauni ba sai ya amince ya biya kudi bisa shawarar Hadir. Zancen gini kuma a hankali zasu yi tunda har yanzu ko rabin kudin da aka bashi bai taba ba.

Takardun filin ne kwafi biyu da sa hannayensu ya mikawa Hadir daya yace gata nan ya ajiye masa shi kuma zai aje daya a wurinsa. Sai da suka gama komai duk motsinsa akan idon Salame sannan su ka koma cikin samari ‘yan uwansu. Ba karamin tafiya yayi da imanin Salame ba lokaci guda taji sonsa ya game zuciyarta.

Mairama kuwa an sami sake hira tayi hira an kawo abinci kowa plate dinta shake da jallof din shinkafa da yankan naman sa da aka soya sai salad, tumatir da albasa. Wayyo dadi jikinta har tsuma yake kuma wai aka kirga su aka sake ajiye musu ledar tsire ga kuma lemon kwalba. Kar kaso ka ga idanun Mairama hankalinta yayi kwano na Salame kuma yayi kan Zayyan da bai san da zamanta a wurin ba.

Police band suna wakarsu amma kusan kowa abinci yake ci babu ‘yan rawa. Kwalbar fanta chapman Mairama ta faki ido ta daga tana kwankwada asalin dadi da sanyi yana ratsata ta manta da kunyar idanun jama’a. Bata samu ta sauke kwalbar mai 35cl ba sai da ta shanye shi tas. Daga lokacin da ta soma waige ta tabbatar babu mai kallonta har zuwa sanda ta ajiye kwalbar Zayyan yana gani. Baki ya rike yana kallon yadda ko da ta shanye sai da ta sake daga kwalbar ta kwakkwafeta a bakinta. Kasa cin nasa abincin yayi komai tayi sai yaji ya burge shi shi kadai ya rinka murmushi. Teburin kusa da nasu Mairama ne duka matan dama su uku ne su ka tashi a tare. Mairama tana ji suna cewa sallama zasu yiwa amaren su tafi. Tana ganin sun bace cikin jama’a ta wayance ta tashi da kwalbar lemonta ta ajiye a wurin ta dauki wata mirinda da ko rabinta ba’a sha ba. Plate din nasu ma basu wani ci sosai ba ga nama sun bari. Kamar ta dauka shima sai dai ta hakura lemon yafi mahimmaci a gareta.
[7/4, 7:38 PM] +234 806 334 4334: D
Banda wanda ta dauka sai da ta dan kurbi na kusa dashi sannan ta juya da sauri da taji ana kiran sunanta.

Hadir ya tabo Zayyan da yake kyakyata dariya shi kadai da ya hango Mairama tana zaro idanu. Matan da suka bar teburin ne suka dawo daya ta soma cigiyar lemon da ta bari. Mairama tayi tsit don kuwa saura kadan ma ta shanye mirindar.

“Kai lafiyarka kuwa?”

Idanu ya lumshe yana kallon kyakkyawar bafulatanar ta tsure karshe ta kuma rungume kwalbar ta boye cikin lullubinta.

“Mata nayi”

Hadir ya tura kujera baya da sauri “nuna min ita muje mu tsarata wallahi”

Zayyan ya mike da sauri “naki din, kai fa satar budurwa kake yi”

Sauran mazan wurin suka sa dariya shi kuma ya kwashe lemuka uku da ba’a bude ba yayi gaba.

Salame tana ganin ya nufosu ta tattaro dukkan nutsuwarta tana murmushi don tun dazu suke hada ido yana murmushi a zatonta ita yake yiwa yayin da hankalinsa kacokan yana kan Mairama ne.

Sallama yayi musu matan teburin gefen ana ta masifar rashin ganin lemo ya mika musu biyu sanna ya dubi Mairama da tsoro ya hanata motsi ya mika mata chapman irin wadda ta fara sha. Dan rausayo kai yayi ya duku wurin kanta.

“Kanwata ga wannan ki kara”

Sai lokacin ta dena jin mitar wadancan matan ta tsuke baki batare da ta juya ba

“rike kayanka bana so”

“Haka ma zaki ce? To ki shirya kuwa don zan tona” yace yana rage murya sosai daidai kunnenta.

A firgice ta waiga idanunta suka sauka cikin nashi. Ko ma me tayi niyar cewa makalewa yayi a wuyanta ta sami kanta da manta a ina ma take na ‘yan dakiku. Lallausan murmushi ya sakar mata wanda ya sake fito da kyaunsa da cikar sa.

“Muje can na fada miki me da me na gani” ya nuna can jikin katanga wurin wata katuwar bishiyar darbejiya.

Ko dogon nazari bata tsaya yi ba ta bi bayansa kuwa don ta gama tsorata kaddai ace ya ga lokacin da ta dauke musu lemon. Wani mugun daci ne ya taso ya tokare wuyan Salame har suka isa bakin bishiyar tana binsu da kallo. Me yake shirin faruwa tsakanin kanwarta da mutumin da take jin bata taba son wani abu makamancinsa ba a rayuwarta. Kallon da yake yiwa Mairama kadai ya isheta amsa. Sauran ‘yan mata kuwa sai shewa itama zasu kwana suna tsokanarta kenan.

Suna isa wurin bishiyar yace “da farko dai sunana Zayyan, ni soja ne”

Idanunta suka yi kwalkwal da hawaye suna barazanar saukowa. Murya na rawa ta fito da kwalbar da ta boye cikin mayafinta “me yayi zafi ni ‘yasu. Daga shan lemo sai dauko sojoji. Ni wallahi nayi zaton sun tashi kenan. Don Allah kuyi hakuri kada ka kamani” tace tana kallon Hadir da ya iso inda suke.

Maganarta dariya ta bashi ya mikawa abokinsa hannu da nufin gabatar dashi a gareta “Zayyan Tureta…”

Wani kallo ta watsa masa tsoron yayi nasa wuri ta yatsina fuska za ta gwada musu tsiwarta “ya tureni? To Bismillah dan halak ka fasa. Mutum ya tabani ba hakura zanyi ba”

Kasa cewa komai suka yi sai dariyar da suke yi mata tana karkada hannuwa. A ranta tana jin tsoronsu zaratan samari irin haka amma kuma bata so ta basu damar cutar da ita.

“Kinga ‘yan mata sunansa Zayyan Muhammad Tureta ba tuureta na hankadewa ba, garinsu ne a Sakkwato”

Kunya taji sosai ta rufe fuska “lahhhhh”

Shima Zayyan sai ya biye mata yace “lahhhhh”

Hadir yana dariya ya basu wuri Zayyan ya kura mata ido “yaya sunanki”

“Mairama” ta amsa da karamar murya.

“Kamar Maryam yake?”

“Haka dai aka saka min a gida ni”

“To fillo ni dai Mairam zan ce. Ina ne gidanku?”

Kallonsa tayi na dan lokaci tana son yin nazari shin kamata zaiyi ko kuwa dai wani abin ne daban.

“Ba kamani kazo yi ba?”

“Kwantar da hankalinki babu mai sanin kin saci mirinda”

Yadda yayi maganar yana kasha mata ido ya sanya hankalinta ya kwanta itama harda dariya. Kwatancen gidansu ya nema daga gareta da bayanin kansa sannan yace duk da karancin lokaci yana son ganawa da mahifinta domin ya nemi aurenta. Kunya sosai ta lullube Mairama don itama a ‘yar hirar tasu har ya shige zuciyarta. Ta fada masa gidan da suke yanzu da kuma kwatancen gidansu yace zai zo da daddare su sake fahimtar juna.

Kusan da gudu-gudu ta koma teburinsu ‘yan matan suka soma zuba mata tambayoyi. Jiki na rawa ta fada jikin Salame tana dariya.

“Bazaku ji komai ba sai ma gama shawara da Addata”

Wani murmushin yake Salame tayi a ranta tana nadamar tahowarsu da Mairama. Ita kuwa dadi ya cikata ta fada mata yadda suka yi.

Cikin gatse tace “kice dai wannan tafiyar taki ce”

Bata fahimta ba shiyasa tayi murmushi “gaskiya tawa ce, yace zai tambayi gidan da muke sai yazo anjima. Ai tare zamu fito ki ganshi da kyau. Hmmm Hausarsa sai ta baki dariya, sakkwatanci yake”

Kamar wanda ta hadiyi kota Salame tace “umhumm”
Taro ya watse amare da angwaye suna farinciki, Zayyan da Mairama suma suna nasu. Bayan isha ba dadewa kuwa sai ga aike cikin gidan ana sallama da Mairama. Ta Madina tayi dariya tace idan al’amari ya kankama tukwuicinta mai tsoka ne tunda ita ta kawota. Kunya ce ta kama Mairama taje ta janyo Salame wadda taso nokewa suka fita.

Maza uku ne a wurin. Zayyan, Hadir sai kuma wani abokin Hadir din tun kuruciya layin gidansu ma daya Salisu. Tunda suka fito shi kuma ya kyallo Salame shima tasa zuciyar ta lula kogin kauna.

Gaisawa suka yi a mutumce Hadir ya sake yi musu bayanin waye Zayyan da manufarsa akan Mairama. Zuciyar Salame kamar ta fashe don bakinciki a ganinta cin fuska ne ma suke mata. Bayan an gama bayanin Salisu yace shima fa yaga matar aure nan dai aka hau gabatar da kai. Salame ko kadan bata yi farinciki ba. Salisu dan kasuwa ne a kantin kwari tun da kuruciya yake da zafin nema bata sani ba yana da arziki sosai.

Mairama da Zayyan sun rabu akan cewa jibi kafin ya bar gari zai sake zuwa don a hada shi da mai yi masa rakiya Sumaila wurin Malamijo. Idan ya tafi zai gabatar da maganar ga magabatansa don bashi da burin a ja lokaci. Salisu ne dai bai wani sami hadin kan Salame ba hanlinta yana kan hirar su Zayyan yace Mairama ta taya shi neman fada.

Bayan sun tafi a cikin gidan ana ta tsokanar Mairama ta kuwa biye musu tana yi tana sako yayarta aciki. Salame kunci da bacin rai ya sanya ta fashe da kuka mai cin rai. Shiru kowa yayi Mairama tayi juyin duniya taki cewa komai. Ta Madina aka sanarwa tazo itama tana tambayarta sai cewa tayi wai gida take son komawa.
Ashar Ta Madina ta kunduma mata “ke har wani gida gareku a Sumailan kike son komawa?”

Fuskarta har ta soma kumbura tace “ni dai tafiya zanyi tsoro nake kada mu koma Malamijo yayi fada don baiso muka zo ba”

Ba wani abu ke cinta ba face zallar kishi da kanwarta. A ganinta idan tasa su ka koma gida Zayyan bazai san gidansu ba bare yabi Mairama shikenan kowa ya rasa.

Abu kamar wasa Salame ta tubure sosai. Ran Ta Madina a bace tace gobe da sassafe zata sakasu a mota kuma ta kwana da sanin cewa bazata sake neman daukota ba, idan Malamijo zai cinyeta ne a gidansa babu ruwanta. Dayake ido ya rufe maganar ta inda ta shiga ta nan ta fice.

Mairama a daren bata damu ba sai da ta tuna Zayyan yace zai zo hankalinta ya tashi. Har daki ta kira Salamen ta roketa alfamar ta bari su sake kwana. Kallon da bata taba yi mata ba ta jefeta dashi wanda ya haddasawa Mairama tuhumar kanta ko ta bata mata rai ne.

“Kinzo kin wani shige cikin danginmu sai wani cusa kai kike yi. Dadin abin dai duk tsiyar mutum da danginsa na jini zaiyi tinkaho. Mu dai munyi sa’a muna da dangin uwa”

Mairama sai taji ranta ya baci itama “nima ba daga sama tawa uwar ta fado ba. Idan don nazo bikin danginku ne Allah Ya baki hakuri bazan kara ba”

“To dama waye zai gayyaceki?”

Kasa bata amsa tayi ranta a jagule ta karasa hada kayanta ta dauko wanda Salamen ta bata na taron da akayi da rana ta saka ta mika mata. Bata damu ba ta karbe duk da a farko niyarta ta bar mata kyauta ne.

Tasha aka kaisu suka hau
mota suna harare hararen juna. Mairama ita gorin da akayi mata ne ya bata mata rai don bata san me tayiwa Salame haka da zafi ba. Sun isa gida kafin azahar Malamijo yana gidan gonarsa wurin dabbobi.

Babu wanda ya aikesu bare yayi murnar dawowarsu gidan. Basu rufa awa guda ba ma Dije ta taso Mairama tazo tayi mata aikin fura da take yi ta sayarwa saboda ciyar da yaranta. Tana tsaka da aikin Inno ta kira Salame ita kuma aka bata surfen masara. Haka suka yi ta aikin babu mai yiwa ‘yar uwarta magana. Mairama ke satar kallon Salame cike da damuwa, ita kuma da sun hada ido sai ta galla mata harara.

Washegari wuraren goma na safe aka aiko wani yaro wurin Malamijo. Dan aiken da ne ga wanda yake taya shi aikin kula da dabbobinsa. Yaron yana haki don gudu yayi zuwa gidan ya sanar dashi wani katon san sa yana neman kasawa ya bada izini a yanka shi. Tamkar an soki kahon zuciyarsa ya zabura zai bi bayan yaron sai ya tuna babu takalmi a kafarsa ya koma ciki da sauri.

Lokacin da ake sanar dashi san ya kasa dan sa daya na wajen Inno mai suna Habibu yana ji ya juya cikin gidan kafin ya ankara da tsayuwarsa. Inno tana gaban murhu za ta hada wutar girki yazo yana haki.

“Inno yau kece a turaka?” ya tambaya babu alamun damuwa a fuskarsa sai ma farinciki. Yaran gidan musamman masu uwaye sun san ranakun girkin iyayen nasu saboda abincinsu yana fin na sauran ranakun auki.

“Idan bani bace uban me zanyi a nan da zafin ranar nan kwal a kaina”

Dariya ya saki har wawulunsa na gaba su ka bayyana “san Malamijo ne ya kasa Inno yau akwai cin nama.”

Kamar wadda aka bawa kujerar hajji Inno ta saki dariyar farinciki ita ma. Su da nama sai dabba ta kasa. Gashi ya fada girkinta sai yadda tayi kenan. Bakin dan nata ta toshe lokacin da yake cewa ta cire musu manyan tsoka idan an soya irin na wancan karon.

“Allah Ya sa wani ma ya kasa mu samu da yawa” ya kare da addua.

Tsaf Malamijo ya gama jin me suke cewa ya shiga tafa hannuwa “ba amin ba, billahillazi baa min ba. Kuji min ‘yan bakinciki masu fatan tsiya. Idan ba kun jawowa kowa wallahi mahauta zan saidawa bazaku ci ba”

Yaron sai ya kama kuka nan da nan iyalan gidan su ka cika tsakar gidan. Don kada ayi biyu babu Inno ta fada musu sa ne ya kasa kuma wai baza’a kawo musu kamar yadda aka saba ba. Iyaye mata suka hau jimami yaransu harda masu dan wayo suna kuka. Kuka na gaske suke ana rokonsa ya taimaka. Shi abin nasu tsoro ya bashi ma ya ja baya ya manne a jikin bango yan raba idanu.

“La-e-lafi qureshin wallahi idan ku mayu ne Allah Ya fiku” yace yana tottofe na kusa dashi “ko ku matsa ko na dauko sarkin mayu yazo ya kama min ku kafin ku karasa ni. Haba ko da naji, kullum zukewa nake jiki babu wata mamora kamar ba Ali mai garken dabbobi ba”

Magana yake yana kallon jikinsa yadda yake sai tsayi da uwar rama ya kula Mairama tayi murmushi abinda bata saba ba. Tun haduwarta da Zayyan take jin zuciyarta fes babu wannan mugun kuncin na gidansu. Mamaki sosai ta baiwa Malamijo don kullum ya tarasu yana irin wannan hade rai take abinta bata kuka bata bada hakuri kuma. Sai yaji wani dan dadi a ransa haka kawai.

Yadikko ce ta bashi amsar maganarsa “ta ina zaka yi kiba ka tara hakkin mutane sun fi talatin a wuyanka”

“Ta, ta, ta uwar zance nasan sai kin tanka. Indai sa ne zaku ci amma yau akan

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment