Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai samu ya gasa musu gyada a hannu kafin ya damkawa hukuma? Shawara daya ce tazo masa ga bacin rai ya dauki waya ya kira Mairama.


A lokacin tana ta koyawa Zayyan yadda ake tura sako a waya yana ta mamakin fasaha da kimiyar nasara sai ga wayar Malamijo. A ladabce ta amsa ga tsoron ko lafiya saboda shi dai baya kira sai dai a kira shi. Ko gaisuwarta bai amsa ba ya soma bambami.


"Yanzu Mairama kin kyauta min kenan? Yarinyar nan 'Yar soja ance tazo hutu amma ni ban ganta ba har yau. Naka naka ne Mairama a rinka zumunci."


"Malamijo kayi hakuri dama satin nan zasu zo da Karami sai wani dalili ya gifta amma suna tafe wallahi"


"To ni dai idan da hali su taho gobe ko jibi. Idan ma kudin mai ne babu zan biya. Ina ta shelar akwai jikata a Faransa abokai sunki yarda. Shi kuwa Zayyanu kice ya taho da kayan sojojinsa idan da bindiga ma ya dauko ko ta katako ce."


Jikinta ne ya bata ba lafiya "Malamijo me ya faru ne?"


Kamar ya fada mata amma zuciyarsa na zargin tana cikin masu murna. Duk wanda yaji me ya same shi cewa zaiyi Allah Ya kara. Radhiya kuwa yasan ko zata yi dariya sai ta rama masa su Hajiyayye bazasu tafi haka nan ba. Zayyanu karami kuma ai soja ne dole ya tsaya masa ko baya so tunda hukuma dai anyita ne domin kare al'umma eheee.


Tana ajiye wayar ta kalli Zayyan da 'yar damuwa a fuskarta "ina jin fa an tabo min uba, akwai abinda ke damun Malamijo"


Dagowa yayi daga kan cinyarta da yayi matashi "tun baki tabbatar ba kin soma hade rai"


"Sai naji duk na matsu nima na ganni a Sumailan. Idan wasu ne suka taba shi ba yarda zanyi ba, ina son tsohona"


"Mairama wai ni wa Alheran ta gado ne? Tawa ce ta fito fili amma kema fa ba jin magana kike ba"


Dariya tayi sosai kafin suka yanke shawarar tafiya Sumaila jibi su ajiye yaran su wuce Sakkwato. Daga can kuma suyi Nijar in sun dawo su tsaya a rugar Barkindo kafin su dawo Abuja.


Zuwansa headquarter dazu an kare komai amma duba da cewa dole ya bukaci lokaci da iyalinsa shiyasa aka bashi zuwa farkon sabuwar shekara wanda daya ga wata ake son yin taron karrama shi. Idan an gama zaiyi wata uku yana daukar training da courses domin ayi updating dinsa tunda Nigeriar da ya dawo ba ita ya bari ba a 1994.


Akan wannan shawarar suka tsaya bayan magariba lokacin su Radhiya sun dawo ya shiga wurin Baba Hadir. Nan ya sami Awwab zaune a kasa a gabansa yana rokon shi dai yana dawowa don Allah ayi aurensu da Radhiya kafin ta koma. Ya kara da cewa ya bada cigiya jiya a cikin estate din block C akwai gida.


A dan littafinsa Baba Hadir ya rubuta masa cewa zai yi magana da ita da kuma su Daddy.


"Ni dai Baba da ka kyaleta wallahi tsoronta nake kada a maimaita irin na da. Kawai ka yanke hukunci shikenan"


"Kada ka bada maza mana Awwab ya haka kake tsoron matarka" cewar Zayyan yana dariya.


Awwab sai ya tashi ya fice yana mai jin kunya. Hadir ne ya rinka masa bayani a rubuce na abinda ya taba faruwa da kuma bukatar yaron har yanzu.


Sai da Zayyan ya gama karantawa tsaf sai ya bata rai "nifa na baro A B C D din a Liberia kayi min bayani kawai."


"Zayyan" Hadir yace yana dariya.


"Kaga yara dai naku ne bani da ta cewa akan komai nasu nima dan gayya ne. Fatana Allah Yasa wannan karon babu wata matsala da za'a samu daga Katsinan"


"Baka ji haushi ba?" Baba Hadir ya rubuta masa.


"Ko kadan dan uwa. Major Mustapha da iyalinsa sunfi karfin haka a wurinmu kaima ka sani. Ya kula min da iyali sannan ya kula min da kai. Me zan nema kuma? Maganar yara wannan mukaddari ne idan akwai rabo sai kaga anyi"


"Zayyan" Baba Hadir ya kira sunanshi kawai don jindadin halin abokin nasa.


Dan daure fuska Zayyan yayi "kada ka karar min da suna. Rinka hadawa da wata kalmar don naji dadi"


"Zayyan...fitina" yace yana dariya.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Kinci albarkacin 'yarki bazan biye miki ba" Maman Danmama tace tana sakin labulen.


Bata bar wurin ba Halifa yayi sallama. Muryarsa kamar a kan Salame akayi recording tuni ta gano ko waye tace ya shigo. Sai da ta fita ta harari Maman Danmama irin abin nan na danta yazo sannan tace ya shigo ciki. Kannen nasa ma an sabar musu idan sun ganshi sun ga kudi ko abincin kirki shiyasa suna ganinsa suka fara murna zasu rungume shi ya dakatar dasu. Kazamai ne na ajin karshe shi kuma tsaftarsa har taso tayi yawa. Zama ma kasawa yayi dakin wari da zarnin fitsari kawai yake yi. Rahima da kanta ke duke tana sharar kwalla ta dan dago da murmushi don tasan sunan ko da suke dadewa basu hadu ba.


"Yaya Halifa barka da zuwa"


Wata muguwar tsawa Salame ta daka mata "tashi dan ubanki kwadayayiya. Wuce ki tafi gidanku ai kin dubani mun gaisa ko."


Zabura tayi ta mike a gigice saboda yadda ta razana da tsawar tayi hanyar kofa Halifa ya fincikota saboda gefen fuskarta kawai ya gani ya gane kanwarsa ce.


"Rahima" ya furta a hankali yana kallon jajayen idanunta. Yarinyar da kadan ta fi rabinsa. 'Yar karama ce wahalar rayuwa ta tsotseta.


"Cikani" tace wasu hawayen masu zafi na sauko mata ta kwace hannunta ta fita. Ta sani Ummansu bata kaunarta amma yadda take nuna bambanci kirikiri yana kona mata rai. Mahaifinta talaka ne futuk amma yana kaunarta tamkar rai. Amaryarsa da ta fara son azabtar da ita dashi da babarsa suka tashi tsaye akan ko ta rungumeta kamar 'ya ko ta koma inda ta fito. Kudin sana'arta da Salame take sakawa ido har nawa ne? Zuwan karshe gabadaya ta tattara mata kudin ta bayar. Wannan karon kuma a kofar gida taji wani makocinsu yana yiwa babanta tijara akan ya ranta masa kudin da ya biya mata WAEC da zata rubuta a farkon sabuwar shekara bai biya ba. Tilas da fito da kudin ta bashi ya bawa mutumin ba don yaso ba. Abin ko kwana uku ba'ayi ba kuma babu wanda ta yiwa lalle bayan nan bare ta sami na zuwa dubiyar. Yanzu abin takaici zani daga akwati Salame ta dauko za ta shimfidawa Halifa saboda babansa yana da kudi.


Ta soma tafiya kenan Halifa ya risketa ashe ya biyota "Rahima tsaya mana"


Cak ta tsaya amma bata ce masa komai ba. Hannunta ya kama ya dora mata bandir din naira dari bibbiyu sababbi "kiyi hakuri da halin Umma. Ki rike wannan zan zo gidan naku muyi magana kinji ko"


"Nagode" sai dai kudin mika masa tayi yaki karba sai kawai ta ajiye akan wani bulo da yake gefen hanyar irin wanda ake zama a kai tayi gaba abinta tana goge hawaye.


Ko kadan Halifa baiji dadi ba. Sai ya tuna da Radhiya tace shine babba ya kamata ya hade kan kannensa. Idan suka tafi a haka tabbas Salame zata ginasu da kiyayyar juna ne. Kana ganin Rahima kasan tana bukatar taimako amma zuciya irin tata ta sanya bazata kwantar da kai tana roko ba bare aji dadin goranta mata. Idan ruwa kadai babanta zai iya bata tasha in sha Allahu zata yi hakuri dashi bazata gaza ba.


Da yake ana ji dashi ko fadan bin Rahima da yayi bata masa ba sai kudurin ko nawa ya bata sai tasa ta kawo mata.


"Zauna mana mu gaisa ka tsaya"


"Sauri nake yi Umma. Dama munzo da baki ne gidan Malamijo shine nace ko zaki zo ku gaisa"


Fuskarta ta nuna bata ji dadi ba "can kuma ka fara zuwa?"


"Ko shiga banyi ba na taho nan"


"Su waye bakin?"


"Su Gwaggo Mairama ne..."


So tayi ta kwada masa mari sai dai kuma kada ta toshewa kanta kofar ihsani dan abinda zai bata ya fasa.


"Mairaman zanje in gaisar saboda ka raina uwarka? Me ya kaika wurinta har kake cewa tare kuka zo?"


Shi fa irin wadannan abubuwan ke kara nesanta shi da ita.

"Umma tare muka zo daga Abuja kuma ba ita kadai bace"


Tabe baki tayi "wato ka fara shege mata kawai saboda ance tana wani karatun banza a Kano kuma suna zuwa Abuja ko. To bari kaji in fada maka duka kwarewa ne a maula ita da 'ya'yan suke zubar da mutumcinsu a gaban masu kudi. Ni nafi tunanin aikatau take yi"


"Umma ni zan tafi idan bazaki je ba. Na rasa me tayi miki ba kya gajiya da aibata ta. Ga wannan" ya mika mata kudi a cikin envelop da ya riko dominta.


"To muje bari na dauko mayafi" tace a sanyaye bata kaunar batawa yaron nan rai. Iyaka idan taje ta yanka mata kashedi ta dena bibiyar danta ba tare suka haifeshi ba.


Ba wata tafiyar kirki suka yi ba suka iso kofar gidan Salame tana ta hura hanci ita mai da. Sauran kuwa a gida ta barsu har wadda ta yaye idan ta sami abinci ta tafi musu dashi.


Emzee da Ibrahim suna bakin mota suna sauko da kaya suka iso.


"Drama ta barka Halifa" Emzee yace yana dariya.


"Ko me akayi a dawo dashi farko gaskiya" 


Salame ta kallesu ta watsar Emzee sau biyu yana cewa Gwaggo Salame ina wuni tayi kamar bata ji ba. Sai yake ya yiwa Ibrahim shima bata amsa shi ba yace wai kila don tana sauri ne bata ji su ba. Ta kai bakin kofa su kuma suna fitowa. Ummi da Daada zasu yiwa rakiya da zasu tafi yanzu. Sai kuma dreban gidan su Halifa shima zai tafi idan sun tashi tafiya Halifa zai kira shi yazo ya tafi dasu.


Gaban Salame wani irin bugu yayi da ta ga Mairama tayi wani irin kyau ta kara haske. Kayan jikinta a hasashen Salame sai kace wata matar gwamna. Wannan 'yar ta ta mai kama da aljanu itama ka kalleta sai ka kara ga wasu 'yan matan Zayyana da Hibba su ma kowacce ta hadu karahe. Bayan wani ta gani kusa da Malamijo suna magana ta wuce su Mairama a fusace za ta shiga cikin gidan.


"Salame babu gaisuwa? Ko ba ita bace?" Zayyan yace albarkacin Halifa da ya tabo shi yana cewa ga Ummansa.


Ba ta iya juyowa ba sai tsuma da take yi tun daga tsakar kanta har tafin kafa. Tasan muryar nan da irin tasirin da ta jima tana yi mata a duk lokacin da taji ta. Sannu a hankali ta juyo idanunta suka sauka akan Zayyan Muhammad Tureta mutumin da har yau babu wani namiji da ya kaishi daraja da kima a idanunta.


Takowa take yi jiki a mace zuwa gabansa ta ma manta da kowa da komai sai tashin tsumin kaunar da take masa. Idanunta suna kwararar da hawaye ta kusa isa gareshi "Zayyan dama kana raye?"


Malamijo gani yayi tana neman wuce gona da iri yasha gabanta "sai ki ka ga mijin kanwarki ko? Ashe tsahon shekarun nan yana daure a gidan yari"

 

"Gidan yari? Allah sai Ya saka mana. Ni dama jikina yana bani baka barmu ba Zayyan" tace tana kuka sosai.


"Zai saka mana kam ni da iyalina. Mairama matso ku gaisa mu tafi" Zayyan yace fuskarsa babu digon fara'a ko kadan. Ji wannan zubar da mutumci da take neman yi a gaba danta, mahaifi da kanwarta kuma matarsa.


Ita Mairama dama tsayawa tayi ta ga iya gudun ruwanta saboda yadda ta kula kamar bata cikin hayyacinta. Da ace bata san tana son mijin nata ba sai tayi tsammanin tsabar kaduwa ce kawai.


"Adda Salame yaya gida da yara? Da Halifa bai taso ki ba ma zamu tsaya a gidan naki ai su gaisa da maigidan naki"


Firgigit ta tuna wai tana da aure. Amma Allah Ya isa Alh Indararo. Wallahi tayar masa da hankali kawai zata yi ya sauwake mata ta huta. Sakin fuska tayi don dole suka gaisa da Mairama ta rakata har bakin mota. Ta bangaren da Zayyan yake zaune a baya ta tsaya yayi saurin danna abin rufe window ya dage glass din. Bata bata rai ba ta dawo bangaren Mairama ta leko da kanta.


"Hmm nace bari nayi miki karambani. Kun dai tambayi malamai game da matsayin auren naku ko. Kada aje ana haramtaccen zama. Idan babu auren gara a san me ake ciki tun wuri"


Da Mairama tana zagi da sai ta hado mai kyau ta zubawa Salame. Wannan jaraba har ina. Daga sake haduwa dashi take kokarin dawo da maitarta a fili.


"Kinsan ba sakina yayi ba kuma ban sake aure ba. Saboda haka auren mu yana nan har yanzu"


"Mu tafi mana" Zayyan yace da dreban rai a dan bace tun bayan dawowarsa. Ba don ta gaji da kallonsa ba ta koma gefe aka ja motar tana tsaye tana daga hannu "bye bye, bye bye" take ta fadi tana murmushi.


Hannun Mairama ya rike yana kallon fuskarta "meye na tsayawa yi mata dogon bayani bayan kinsan akan hanya muke?"


Murmushi tayi ya karawa fuskarta kyau "gani nayi gara nayi mata bayani tun wuri kada tayi tunanin akwai wata kofa da za ta iya samu ta shiga gidanka"


Bude baki yayi ya kalleta "kada kice min ta fada miki"


"Bata ji komai ba ta sanar dani kuma shine dalilin mutuwar aurenta kamar yadda Alh Salisu ya fada min jiya da kana waya da Baban Arifah lokacin da yazo. Cewa yayi nayi hankali da ita mai hali baya fasa halinsa kuma gashi na gani"


"Mairama ina so ki sani wallahi ban taba cin amanarki ba akan Salame"


Kanta ta dora akan kafadarsa ta rufe ido "kada zancenta ya bata mana farincikinmu"


Alamun saka zip yayi a baki yana dariya suka cigaba da hirarsu cikin shauki har suka isa Kano. Gidan da ya gina da guminsa da kuma gadon mahaifiyarsa ya shiga yana tuna baya. Saboda hazo ya fara kura amma da gani an kashe masa kudi wurin gyara da kayan alatu. Mairama ya janyo ya dora kansa a kafadarta yana tsaye a bayanta yace "kin tuna zuwanmu gidan nan na farko?"


Sai da taji kunya Allah Yasa baya ganin fuskarta "ban tuna komai ba"


"Da gaske? Ni kuwa kamar a kaina aka ajiye ranakun da Mairama ta rinka nunawa Zayyan soyayya irin wadda nake sa ran a maimaita. Jikina yana bani a nan kika samo Zayyan fa"


"Ni dai ka kyaleni gyaran gida zanyi" tace a kunyace


"Muje na tayaki ai muna da lokaci. Sai jibi zamu tafi Sakkwato in je mu hadu da Maikudi"


Ajiyar zuciya tayi tana hango wannan haduwa bazata yiwa Maikudi kyau ba ko kadan.


**********


Ranar da daddare bayan Yadikko ta dawo ne Radhiya taji komai game da amaryar Malamijo a wurinta. Taji zafin sakin Hajjo ita ma tayi ta bawa Yadikko baki akan kada ta tafi wa zasu gani su ji dadi.


Shima Malamijon kuma sai ya fada mata abubuwan da Hajiyayyen tayi masa.


"Malamijo ai kowa maye ne sai dai idan baiso nunawa ba. Ka rubuta mata takardarta tun dare gobe zaka bata kuma wallahi Hajjo kadai na yarda ka dawo da ita"


"Ba ma sai kin fada ba 'Yar soja ikon Allah. Na ma gama aure yanzu sai dai ku"


"Wai ni su waye ma suke yi maka waliyai ne a aure auren Malamijo?"


"Kaniyarki mai ido a tsakar ka" yace yana laluben takalmi zai biyota dashi ta gudu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: 'Ya'yan nasu sun hadu a falon Ummi kowa na bawa Daada labarin kansa musamman game da karatu shi kuma yana rike da Daada Karami. Radhiya ta kalli yaron ya kurawa babanta ido tayi murmushi tana tambayar Mami da suke shigowa tare da Mama suna neman wucewa dakin Ummi wai yaushe zasu yi taron sunansa ne.


Mama ce ta bata amsa "babu wani taro fa Radhiya tunda babansa ya dawo me kuma zai bukata? Masu tahowa dai zasu zo amma barka kawai"


"Yaya zaki yi mana haka babu shawara Zainab?" Cewar Mami tana nuna mata rashin jindadi.


"Ni da dana zata yi min karfa karfa to wallahi ban yarda ba" inji Ummi tana goyon bayan Mami.


Zayyan ya daga hannu kamar dan makaranta "idan kun bani dama in raba gardama?" 


"Mun baka" Mama tace da sauri tana neman tsira. Da Baba Hadir suka yi shawarar soke taron kawai kwanaki sun kara ja kuma ma dai dawowar Zayyan ita ce abu mafin dadi garesu. 


Kallon iyalan nasu yayi yana jin tamkar  Allah Ya bashi fiye da abinda yake nema a duniya. Major da Hadir harda Baban Arifah da ya sadaukar da rayuwarsa dominsu batare da tunanin ko kadan zasu saka masa ba gashi sun rike masa iyali da gaskiya. Idan ya biyewa zuciyarsa kuka zai yi musu daga su har matan kwarai da suke aure wadanda suka karfafa musu gwiwa wajen dabbaka zumunci a bayan idonsa. Shi ba butulu bane da zai manta Mami Hassana wadda mijinta Major da Ummi suka bashi labarin cewa aikatau tayi a Germany domin ciyar da iyalinta amma a cikin abinda take samu Major ya rinka cire wani abu kafin ya fara aiki yana aikowa matarsa Mairama. Babu wanda baiyi masa ba amma Allah Ya sani yana jin girman Mami sosai a zuciyarsa. Daga ita har Mama Zainab sun wuce matan abokai a gareshi sai dai ya kira su 'yan uwa. Sun burge shi matuka yadda suka tsayawa juna a matsayinsu na matan sojoji suke kokarin rufawa juna asiri. Ba don a gidan iyayensa an bar kari tun ran tubani ba ai da kamata yayi ace ya dawo ya sami matarsa a tsakiyar matan su Badaru. Abin takaici shine sun tashi babu wannan shakuwar tsakaninsa da 'yan uwansa maza da mata. Jume tun kuruciya ta koya musu tsanarsa a matsayin dan kishiya. Sai dai yaji dadi da Mairama ta fada masa yanzu kam idan ka cire Maikudi tsakaninsu da sauran musamman 'ya'ya da jikokin Mal Aminu abokin babansa sai dai hamdala. Ita ma a nata bangaren rashin shakuwa da 'yan uwanta da kuma rashin tsayuwar uba akan 'ya'yansa ya sake bata lamura. Da ace zumuncin nasu mai karfi ne ya tabbatar ko a daji iyalinsa suke bazasu wahala ba. Duka rayuwar Mairama bayan tafiyarsa ai a cikin gidan mahaifinta tayi kafin ta koma Rugar Barkindo amma rashin wannan zumuncin ya sa ita da wadda bata tare da ahalinta kusan daya. 


"Daada" Radhiya ta dan taba shi saboda nisa da ya soma yi a tunani.


Murmushi yayi a lokacin Awwab, Daddy da Baba Hadir suka shigo su ma yace "indai na isa to na soke taron sunan"


"Kai da danka Daada waye zai hanaka abinda kake so" Mama tace tana murmushi.


Sauran kuwa da gaske sunyi mamaki harda Ummi kuwa. Sai dai abinda yace ya sanya su wani irin farinciki a take.


"A iya sanina Zayyan kaima ba'ayi taron sunanka ba ko" ya kalli Emzee da suke zaune kusa da juna shi da Ibrahim tamkar tagwaye. Dariya yayi yana zaro idanu "Daada ba dai cewa zaka yi a nade ni a shawl a koma baya ba"


Ai kuwa falon ya kaure da dariyar yadda yayi har ya tashi zai bar musu falon da Ibrahim yace "irin jaririn samudawan nan kawai zaka koma".


"Dawo ka zauna in karasa...Zayyanatun Daada kema ba'ayi miki suna ba"


Zayyana sai ta rasa inda zata saka kanta don dadi Zayyan ya fasa mata kai yace ita tashi ce. Ibrahim ya dan kalleta yadda take dariya ta tashi ta koma kusa da Zayyan ta zauna tana narkewa "Daada ba'ayi min ba, ko kayan barka fa bana jin an kawo"


"Kiji tsoron Allah" Mami tace tana dariya.


"Ai kuwa duk wanda bai kawo ba muna binsa bashi. Su Ummi da Mama kowa ta kwance bakin jaka"


Anata dariya ta hada ido da Ibrahim wanda ya kasa gane mata tun ranar da yayi maganar tale baki. Abin ya dame shi sosai ya kasa fadawa Emzee. Yanzu suna hada ido yayi murmushi ita kuwa ta murguda masa baki ta kawar da kai, babu wanda ya kula sai shi.


Zayyan ya dago Daada Karami "kaima bakon duniya nazo na tare hanya ba'ayi maka taro an kawo kayan barka ba. Saboda haka in sha Allahu za'ayi taro na musamman idan komai ya natsa na Zayyan, Zayyan, Zayyanatu da Zayyan."


Hayaniyar murnar da suka cika falon da ita ba arziki Mami tace su tashi su fita. Zayyan ya yafito Awwab da hannu. Tun shigowarsa dama baiyi magana ba sai ma dukufa da yayi yiwa abokin aikinsa text akan abinda zasu yi idan ya koma.


"Idan an gama suna sai mu fara shirin bikin dana. Kunyi min komai daidai amma an bar min yaro ba aure. To mu dai yarinya ko 'yar waye tunda yana so idan ta kama na sato ta ne zanyi na kawo maka kaji ko"


Idanu suka koma kansu shi da Radhiya lokacin suna rige rigen arcewa daga falon. Shi hanyar waje yayi ita kuma tayi kitchen. Su Major ma sai da suka yi dariya.


"Kunga kama kai, yanzu don Allah waye yaji na ambaci suna?"


Da dariya suka fita harda ta kitchen ita ce karshen tafiya. Major yace masa ya fara tara jikoki ya kamata ya rage chalikanci.


"Idan na dena so kake su rinka guduna? Kuma dai shekarata nawa ina danne Zayyan Tureta ta karfin tsiya. Yanzu kuwa lokaci yayi da zai fito yayi kara'i"


"Aiki ya sameki kanwata kiyi a hankali kada mu fara ganinsa da kitso da dankunne irin na matasan zamani" Baba Hadir ya rubuta ya mikawa Mama ta bata. 


Zayyan yana ganin tana dariya yace sai ya gani. Daga nan dai hirarsu ce da bata karewa suka dasa. Sai sakon text Alh Salisu ya yiwa Baba Hadir zai zo suyi sallama gobe zasu koma Kano da yaran. Ya kara da dan korafin wai ko basu hakura bane yana ta sa ran zuwansu gidansa ko su ko yaransu amma shiru. Baba Hadir sai yaji babu dadi ya mikawa Daddy wayar. Kiransa Daddy yayi bayan sun gaisa yace

"Hadir yana mai baka hakurin rashin zuwan nasa. Wani abu ne ya taso amma idan babu takura kuma kana da lokaci kafin ka tafi goben me zai hana ka shigo ka ga uzurin nasa?"


"To Allah Ya nuna mana Yasa lafiya. A gaida yaran don Allah"


Da haka suka yi sallama. Matan na daki suna tsokanar Ummi amarya babu lalle babu gyaran gashi ta ce laifinsu ne. Mama tace ba don jego ba da idan ta fara gyarata sai sun biya mata Hajji da Umra.


"Ni dai naga ranar da zaki girma Zainabu. Ina jin halinku ne Sakkwatawan nan. Daga ke har Zayyan sai ku sa cikin mutum ciwo da ban dariya."


"Cewa zakiyi suyi abu su daure fuska ki rantse ba daga bakinsu magana ta fito ba" Ummi ta fada da dariya.


"Baki ji ba wai zai satowa Awwab Radhiya ya kai masa ita. Uban amarya zai saki layi."


Kowacce ka gani tana cikin walwala da annashuwa suna jindadin zama da juna sai fatan Allah Ya kade shaidanu Ya kara hada kawunansu.


**********


Tun dawowar Zayyan yau ce rana ta farko da su ka kebe su kwadai da 'ya'yansu a bangaren Ummi. Ba kowa ne da wannan tunanin ba kuwa sai Mama Zainab. Bayan sun fita ta tura musu Radhiya da Emzee da sunan su je ko babansu yana son hira dasu. Babu wani boye boye tace ya kamata su bashi lokaci yaji matsaloli da cigaban rayuwarsu kamar yadda kowane uba yake yi. Radhiya taji kunya sosai ganin da su Zahra a wurin. Amma sai ta kula babu wadda abin ya dama sai ma goyon baya da su ka baiwa Mama aka korasu yau su kwana a gidansu.


Ummi da Radhiya ne suka yi girki yayin da Zayyan yake sake jin daukakar da Emzee yake samu a NDA tun shekararsa ta farko. Ya yaba kwarai da dan nasa yana jinjinawa a ransa wannan wai magajinsa ne wanda bai barshi ta ko ina ba...suna da aiki.


A kasa Radhiya ta ajiye musu abincin Zayyan yace ta dauko babban plate yau a kwano daya zasu ci ya ga girman lomar kowa. Da dariya aka soma ci sai gashi su hudun sun buge da zubar hawaye lokacin da ya kallesu daya bayan daya yace "ko yanzu mutuwa ta riskeni zan tafi ina mai farinciki da cika godiyata ga Allah."


Ummi ce ta fara hawaye sai Radhiya ta kama harda shessheka. Emzee ma duk dauriyarsa sai da yayi "don Allah ni dai a dena kukan nan abincin da dadi amma zaku sa ya fita daga raina"


Dundu Ummi ta kai masa "acicin kawai"


"Zancen gaskiya Ummi. Ba abin nayi fuska na gama ci sannan nayi nawa kukan ba na rasa me tayani"


"Ashe haka kake Zayyan? Shiyasa Malamijo yace yana nemanka kaje da bindiga ko ta katako ce"


"Nemana kuma

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment