Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anayi ba. To itama Ghazalatun amsar da Radhiya ta bata tana nan tana ci mata rai.


A daddafe Awwab ya kai asuba kafin takwas yayi wanka ya shiga cikin gidan saboda kofar dakinsa ta waje take. Yayi sa'ar ganin Zahra ta fito da Femi ya fada mata Abuja zai tafi ta fadawa su Mami idan sun tashi.


Muryar Mami yaji tana tambayar shi jikin Radhiya ne yayi zafi ya juya yana sunne kai. Murmushi tayi "bazan hanaka zuwa duba matarka ba kuma hakan da kayi zai farantawa Umminku sosai"


Dakatar dashi tayi tace ya jira ta fadawa Daddy. Sai da yayi wanka ya fito shima dadi yaji da Awwab din yayi tunanin komawa saboda Radhiya. 


"Akwai sauran kayan da Fauziyya za ta kawo ka fito min da akwatunan sai su jera anjima a kai gidan Alh Baba" Mami tace masa.


Kayan lefe ne kusan komai ya hado abinsa da zai dawo amma Mami sai da ta bada kudi aka karo mata atampa, leshi da shadda daga kantin kwari a Kano. Shine take so ya fito da akwatunan da ya siyo sai a jera da sauran kayan a kaiwa kakanni su gani. Sai ranar dauko amarya zasu tafi da kayan Sakkwato. Hana shi tafiya Mami tayi sai da Fauziyya tazo wurin tara da rabi wai idan bai gani yanzu ba babu lallai ya gani. Shi dai kamar yace ba gidansa za'a dawo da su ba yayi shiru dai.


Kaya sunyi kyau komai goma goma Mami ta kara sai da ta tashi ya janyo Zahra gefe saboda ta fi Fauziyya nutsuwa. Kitchen suka koma saboda Fauziyya da ta damu sai anyi da ita. Rasa yadda zaiyi da rigimar Radhiya yasa shi neman shawarar kanwarsa.


Baiyi mamaki ba da Fauziyya ta shigo kamar an korota kafin Zahra tayi magana ita ta soma "wallahi Hamma baka kyauta ba. Baiwar Allah kila ma abinda ya haddasa mata zazzabin kenan" tace cike da jimami.


"Yanzu waye ya sa dake?" Zahra ta harareta "kaga Hamma sai kayi a hankali don naga take taken Ghazalatu. Ita kuma Radhiya kaje ka bata hakuri kafin tayi maka balotelli"


Dariya yayi yana tuna kan Radhiya na da sai kuma ya tuno laushi da tsahon gashinta yanzu yayi murmushi.


Fita daga kitchen din Fauziyya take yi jin ance balotelli tace "ba wani balotelli fa indai za'a shanye janbaki tuni zasu daidaita"


Ba don rannan ya matsa Radhiya akan dalilin sake kwalliya ana kiran sallah ba da bazai san me Fauziyya take nufi ba. Baki ya rike ita kuwa hankali ya tashi da ta fuskanci ya gane me take nufi ta dora hannu a ka tana salati. Zahra ta rinka kyakyata dariya Awwab ya fice yana cewa irinsu ne masu zuwa gulma gidan amarya.


"Idan na ga kafarki a kofar gidana nan da wata uku ma sai na karyata don nasan me ya kawoki"


Ta daure fuska "ai dai gaskiya na fada"


Bakin mota suka raka shi batare da ya sake neman wayar Radhiya ba ya dauki hanya. Karfe uku yana cikin garin Abuja saboda ko mai bai tsaya sha ba yayi full tank a Katsina. Gidansu ya fara zuwa amma wurin Mama ya shiga. Bata nan sai Baba Hadir shi kadai wai Ummi tazo sun koma can gidan tare. Abinci suka ci tare da sallah sannan ya je yayi wanka ya tafi ganin Radhiya. Kananan kaya ya saka bakin jeans da bakar shirt mai maballai da collar ya dora rigar sanyi mai v-neck cream ta saman wuyan ya lankwasa kwalar shirt din ciki. Ba karamin kyau yayi ba yana ta kamshi ya shige mota.


Yana shiga ya tarar da motar Ibrahim dama Baba Hadir ya fada masa can suka tafi duba Radhiya. Ummi da Mama sunyi mamakin ganinsa sosai ya sunkuyar da kai da Mama ta shiga tsokanarsa wai amarya tayi kira.


Murmushi kawai yake yi Ummi ta tura mai aikinsu kiran Radhiya tasa Rahima kawo masa abinci. Bata yarda ba da yace a koshe yake sai da ya tabbatar musu a gidan Mama yaci.


Mai aikin ce ta dawo tace wai bacci Radhiya take yi. Ba dai haka yaso ba kuma fuskarsa ta nuna. Mama ta nuna masa dakin da take ciki a kasa inda suke gyaran jiki. Yau ba'ayi ba amma saboda rashin kwarin jiki can ta shiga bayan an matsa mata ta sauko dazu.


"Shiga tana ciki ka samu ka tursasata cin abinci me yiwuwa kai taji maganarka" 


Ummi ta kalla ganin ko motsi baiyi ba "muje sama mu karasa don naga alama dan naki ba tashi zaiyi ba"


Awwab kunya Ummi kunya. Sai da su ka shige sannan ya tashi da sauri ya tafi dakin da aka nuna masa. Kwankwasawa yayi tana kwance da waya a hannu r muryar Hammanta amma kishi ya hanata kunna waya ta kira.


Tura kofar yayi a hankali yaji tace "Rahima karo min bargo a sama dakin nan akwai sanyi sosai"


"Gani ki yafa"


Muryarsa ce tazo mata a bazata ta dago kai ta tabbatar shi din ne yana tsaye da ga bakin kofa sai kawai ta ja bargo ta rufe har kanta. Murmushi Awwab yayi ya zauna a gefen gado sannan a hankali ya zura hannunsa ciki ya kamo nata tana ta kokarin kwacewa ya rike.


"Idan baki nutsu ba zanyi miki rawar 'yar amana"


Dena motsin tayi yana jiyo sautin dariyarta a hankali yayin da take jin dumin hannunsa yana ratsa ta. Shiru su ka yi duka su biyun na dan lokaci sai daga baya ya soma magana. Hakuri ya bata tare da bayanin ya akayi ma taji shi tare da Ghazalatu a lokacin.


"Ko kinfi so ace mun dena zumunci da 'yan uwana?" Tana cikin bargon ta girgiza kai yace yana dariya "ashe ma zakiyi saurin hakura duk kika tayar min da hankali"


Gefen fuskarta kadan ta bude amma bata iya kallon idanunsa ba tace "ba hakura nayi ba ka tashi kayi min rawar"


"Sai dai muyi tare" yace yana kashe mata ido.


Sake rufa tayi ya kwanto a jikinta tuni ta fara rawar jiki kuwa "ko ki bude in ganki tunda dubiya nazo ko na shigo ta nan" yace yana dan matsa hannunta da ya rike ta kasan bargon. Ja taji yayi ta bude kanta da sauri.


A kunyace ta ture bargon tana sanye da dogon skirt baki sai rigar sanyi da ta kamata mai high neck. 


"Give me a hug" yace yana ware hannuwansa. Bata motsa ba sai kai da ta sunkuyar yace "now please" da wata irin murya. Ji yake kamar ya janyo kwanakin nan su kare da wuri ace an gama biki kowa ya huta. 


Ba yadda ta iya ta dan matso kadan shi kuwa ya janyota jikinsa ya rungume yana shafa kanta.


"I love you Schatzi ki dena kokwonto akan hakan. Bazan taba yin abu don na bata miki rai ina sane ba"


Dama can bata gama kukanta ba sai yanzu ta sami damar yi masa yana ta rarrashi.


"Ni dai ko za ka yi min kishiya bazan zauna gida daya da ita ba"


Kanta ya dago yana murmushi "saboda me?"


Shagwabe masa tayi "Ni dai kawai bana so" 


Goshinta ya yiwa kiss ta runtse idanu yace "saboda kina tunanin zanyi mata wannan?" Ya koma kumatunta hagu da dama "da wannan?" Sai kan hancinta "da wannan ma?"


"Ni dai ban ce ba" 


"Ni nace baby...I miss you so much" yace yana kallon fuskarta idonta a rufe ya soma zana mata lips da karamin yatsansa "yau baki sa janbaki bane?"


Tamkar ta nutse a cikin gadon ta kawar da fuskarta "bani da lafiya fa"


Idanunsa a kanta yace "Ni kuma na taho all the way from Katsina shan janbaki ne fa"


Ciwo dama ya riga ya warke tunda ya iso da sauri ta tashi yana kiranta wai ko vaseline ne ta shafa ta bashi ya shanye ta gudu tana dariya. Bata sake bari sun kebe su kadai ba sai da zai tafi gida tayi masa sallama yana ta korafin bai sha janbaki ba tana dariya. Kafin dare ta ware tas sai karadi da dariyarta da ta cika mutane dashi. Zayyan yana ganin chanjin da ta samu kuma an fada masa Awwab yazo yayi dariya wai dama can ciwon soyayya ne.


"To saura ka fada a gabansu" Ummi tace fuska a daure don kada ya saka ta dariya.


Alamun zip ya yiwa bakinsa sannan ya tashi yana nade hannun rigar baccinsa "bari na gani ko ina da sauran karfi"


Mairama bata ankara ba ya dagata ya dire akan gado. Tana tashi ya danneta yana dariya "kwanta bitar karatunmu zamuyi muma"


**********


Yau litinin ya sati na gaba ya kamata a fara biki gidan gabadaya suka tafi Sumaila tare da Mama, Zayyan kuma ya tafi Sakkwato. Sun isa gidan na Malamijo ya cika da 'yan uwa da abokan arziki. Su Innawuro daga rugar Barkindo, Nene Marka da kishiyarta tare da 'ya'yab kishiyar da jikoki sai kuma 'yan uwan Malamijo da nasu iyalan. Ranar laraba zasu yi Kamu saboda da yawansu ba iya zuwa Abuja zasu yi ba. Emzee yana makaranta har lokacin sai wani satin zai taho. Sunyi waya da Rahima ta fada masa sun taho Sumaila sai dai har yau bai kawo komai ba. Sallah kawai Rahiman tayi ta fadawa Ummi zata je gida.


Envelop Ummin ta mika mata "ga kudadenki na kunshi ki kaiwa Baffanki"


 Da tsananin mamaki Rahima take kallon Ummi saboda da idanunta ta ga Salame da aihinin wanda aka bata ranar da tayiwa bakin Mom Arifah. Sauran wanda tayi kuwa ba wani yawa gareshi ba to ta ina kudin yayi wannan kaurin. Kasa shiru tayi muryarta tana rawa tace "Ummi ba kin bawa Umma wancan kudin ba?"


Mairama ranta taji ya baci a tunaninta Salame ce ta fadawa Rahima ta karbe kudin. So tayi ta rufa mata asiri shine ta sake hada mata dubu dari da sauran kudin da ta samu.


"Wancan kyauta ce zanyi mata ranar babu kudi a hannuna shine na bata naki amma gashi na dawo miki dasu"


Tasan Ummin ta fada ne kawai ba yarda tayi ba. Kuka ta fashe dashi tana kara son kanwar Ummanta da danta Emzee. Cike da farinciki ta tafi gidansu. Baffanta yana kofar gida suna hira da abokinsa ya hangota. Bakinsa kamar gonar auduga ya tashi ya shige ciki da saurinsa yabi bayanta. A dakin Iya suka yada zango suna ta sakin murmushi ta je ta nanikewa Iya a jiki. Sunji dadi sosai yadda tayi fes da ita ta kara cikowa tayi kyau.


"Har kin gama hutun ne Rahima?" Iya take tambayarta tunda basuyi tsammanin dawowarta yanzu ba.


Bayani tayi musu ta cewa Iya don Allah ranar laraba tazo yinin Adda Radhiya. Labarin kirkin su Ummi tayi ta basu da yadda kasuwar kunshi ta bude mata. Da ta basu kudin ba karamin mamaki Baffanta yayi ba.


"Tare zamu je gidan Malamijon idan kin huta nayi mata godiya. Dubu dari harda sha uku a hannuna arzikin Rahimata" yace yana dariya.


Ta tashi taje bangaren matar gidan suka gaisa ba yabo ba fallasa ta dawo Iya ta mika mata kudi a leda "ga wannan Rahima nasa Baffanki ya raba kudin ki kaiwa Salame itama tasa albarka. Dubu talatin ne, Baffanki ma ya dauki talatin sauran kuma zan fara yi miki siyayya kinga ko maburgi baki dashi kada aure yayi mana zuwan bazata"


Ture kudin tayi kamar zatayi kuka tace "A'a Iya Baffa ya rike duka" 


"Kul na kara ji mahaifiya ba abar wasa bace. Maza dauki ki kai mata ki dawo sai kuje can din da Baffanki ko"


Ba haka taso ba tunda zai zama Salame taci bulus harda kari amma bazata iya yiwa Iya musu ba. Daukar ledar tayi ta boye a cikin hijabinta ta kama hanyar gidan Alh Indararo.


A gidan Malamijo Radhiya bata san Rahima ta fita ba sai daga baya Ummi ke fada mata inda taje. Ta taho mata da kaya akwati guda masu kyau wanda bata yi wani amfanin kirki dasu ba kuma bata so dama ta bata a cikin gidan sai kawai ta nemi yaro ya rakata gidansu. Suna fita suka hangota tayi hanyar gidan Salame shine ta bi bayanta.


Da Rahima ta isa tsakar gidan kamar kaji sunyi dambe ko ina shinkafa ce tun wadda aka ci da rana da mai ta watse a wurin. Ga kwanuka a bakin kofofin dakuna wasu a tsakar wurin kadan ne aka ajiye a wurin wanke wanke. A mutumce ta gaishe da Maman Danmama tayi sallama a kofar dakin Salame.


Daga ciki ta amsa mata irin na gatse dinnan "Su Hajiya Rahima ne...shigo mana"


Gwiwa a sake ta shiga ta gaisheta. Bata amsa ba sai kunnenta da ta kama ta murde iya karfinta amma dauriya irinta Rahima bata yi yunkurin kwacewa ba sai hawaye da yake zuba kamar an bude famfo "dama jiranki nake yi ki dawo mai shegen kwadayi. Kin bi Mairama gidanta batare da neman izinina ba sannan da muka je akanki Hajjo da Yadikko ke yi min fada"


"Umma kiyi hakuri" tace idanunta a runtse zafin murdar kunnen tana ratsata sosai.


Salame bata raga mata ba saboda bakincikin yadda har take da bakin cewa dama Mairama ce ta haifeta. Rai a bace take fada "kinje kin sami duniya da bakinki kina cewa ni bana sonki ko? Akwai uwar da kika taba yi min ne da zan so ki? Banda kaddarar haihuwarki me zai kaini gidan fakirin mahaifinki ma. Sai ana magana kiyi ta zarowa mutane idanu"


Maman Danmama tana jinsu amma bata shiga ba saboda ko taje bazai hana Salame abinda tayi niyya ba. Bacin rai sosai Rahima take ji wanda ba don Salame ce ta kawota duniya ba yau da tayi mata fitsara da rashin kunya irin wadda bata taba sani ko ji ba.


Sauran yaran suna dakin suna dariya Salame ta cigaba ido a rufe "daga yau na sake jin kinbi Mairama gidanta sai na saba miki. Har wani arziki garesu da zaki je kamar almajira kina 'yar cikina ana baki kafa da hannu kina kunshi wai ke mai sana'a"


Kasa magana tayi sai gunjin kuka. Babu abinda ke damun Salame sai frustration da tsantsar hassadar Mairama. Yanzu kowa ya bude baki a gidansu ita yake kira a yabeta a yabi 'ya'yanta. Rayuwa tayi mata ba daidai ba ace ita ce yau a kasan kanwarta wadda a da can baya take cin arzikinta. Ga Alh Indararo tayi haukan tayi hankalin duka a banza yaki sakinta. Halifa shima kuma ya koma jikin Mairaman shine itama da ubanta ba kowan kowa ba take neman bijere mata.


"Ba dake nake ba?" Ta hayayyako mata sai ji kake tas ta dauketa da mari saboda taki amsawa. Hancin Rahima sai jini Salame niyarta ta sauke duka bacin ranta yau a jikinta ta kuma daga hannu don ko jinin bata kula dashi ba Radhiya ta damke shi ta watsar dashi gefe. Kusan tare suka shigo gidan da Rahima duka abinda suka yi taji. Zuciyarta har wani daci take yi ganin yadda ake yiwa Rahiman da take kamar kwai yanzu a wurin Ummi. Ashe shiyasa Ummin ta kara janta a jiki don ta maye mata gurbin uwa.


Tayar da ita daga durkusun da tayi a gaban Salame taso yi amma taki tashi sai ma ture hannunta da take yi.


"Ki barta ta kasheni....Umma ki kasheni ki huta indai hakan zai sanyaya miki zuciya ki dena tsanata"


Zuciya a wuya Salame ta janyo wayar rediyo "kina zaton ina wasa dake ne Rahima? Kin tashi a nan ko sai naci ub...."


Wayar ta sauke mata a jikinta ya sami fuskarta sannan ta sake dagawa a kufule sai ta sauka a gadon bayan Radhiya saboda saurin kare Rahima da tayi. A zabure Rahiman ta mike ta kawo hannu za ta riketa ta nuna mata kofa "ki fita ki tafi gidan Baffanki gani nan zuwa"


"Adda ...." tace jikinta sai rawa yake yi kukan ma ya dauke mata.


"Nace ki fita ko sai ranki ya baci" Radhiya tace cikin fada.


Da sauri kuwa ta fita tana hawaye. Radhiya ta juyo tana yiwa Salame wani irin kallo da ya tsirga mata ciki. Idanu ne na Zayyanu Tureta take gani cikin tsananin bacin rai da zafin zuciya. Kujera Radhiya ta janyo ta zauna bayanta yana uban zugi saboda dukan ya shigeta sosai. Yaran ta kalla ta daka musu tsawa tace su fice kafin ta kirga uku. Ko biyu bata kai ba suka kama gabansu a guje ya rage daga ita sai Salame.


A rayuwarta bata taba tsorata irin na yau ba. Gani take kamar an hada mata Zayyan da Mairama a jikin mutum guda ne. Boye tsoron tayi tace "zaki rama dukan ne?"


"Zan so na rama Gwaggo Salame sai dai kinci arzikin Malamijo kuma dukanki zai janyo min fushin uwa. Yau ne na biyu da naga irin abinda kike yiwa Rahima saboda Baffanta talaka ne. Sai dai mijin naki na yanzu ma bana jin zai iya kwatarki daga hannun hukuma ko yaso"


A tsorace ta nunata da yatsa "Ke ki kiyayeni bana son rashin kunya don ko uwar da ta haifeki tayi kadan" 


"Ki dena zagar min Ummina, bansan me tayi miki kika tsaneta ba amma inda ta kai bazaki taba zuwa rabinsa ba har abada da wannan algae (gansa kuka) din na bakinki"


"Wato dai turoki tayi ki fada min magana saboda baku da tarbiya ko?"


"Baki ga rashin tarbiyata ba amma yanzu zan nuna miki"


Emzee ta kira ya dauka zai fara janta da hira tace ya saurareta "motar sojoji nawa zaka iya turowa a kama Gwaggo Salame batare da kowa ya sani ba"


Cikin Salame yace tsuuuu da taji muryar Emzee kuma ana zancen motar sojoji. Ko tunanin cewa shi dalibi ne bata yi ba tsoronta kawai kada a kama ta.


Abinda tace ya saka shi tunani "Adda kada kice min kema kin gano ita ta makanta Ummi"


"What???" Radhiya tace jikinta na bari Salame kuwa sulalewa tayi a kasa saboda ba karamin tsoron hatsabibancin Radhiya take yi ba tuntuni. Yarinya ce kamar aljana bata da tsoro ko kadan.


"Kuna tare ne?" Ya tambayeta saboda bai fahimci zancen ba.


"Ina gidanta yanzu haka. Emzee kayi min bayani sosai"


"Adda dalilin da yasa ta tsani Ummi saboda tana son Daada ne, sannan ita ta yiwa Ummi asiri don ta auri wannan Alhajin da take gidansa yanzu"


Kuka yaji Radhiya ta fashe dashi jikinta yana wata irin rawa sanyi na ratsata. Tsorata Salame da taso yi akan Rahima sai ya koma bakincikin muguntar da ta yiwa mahaifiyarsu.


"Makantar shekara goma Gwaggo Salame na rantse bazamu yafe miki ba" tace tana wani irin kuka.


Maman Danbaba tana jin abinda ta fada ta garzaya ta kirawo Alh Indararo ashe yana cikin daki ya dawo da wuri.


Jikin Salame na rawa ta mike da dafa bango "kizo ki fita daga gidan tunda abin naku ya koma sharri" tana rarraba idanu kada wani ya shigo.


"Adda" Radhiya taji Emzee ya kirata "me ya kaiki gidanta ba dazu kuka iso ba?"


"Rahima na biyo" ta amsa cikin kuka.


Kansa ne ya daure sosai "Rahima kuma?"


"Eh Emzee, don baka ga irin dukan da take yi mata ba"


"Me ya hadata da Rahima kuma? Ko wacce kike nufi na kasa fahimta" yace jikinsa a sanyaye yana tsananta addu'a kada abinda yake zargin tana nufi ya tabbata.


"Rahima dai mana"


"Wadda nake gani tare da Zayyana?" Yace a tsorace.


"Eh" ta soma gajiya da tambayoyin ga serious maganar da ya kamata suyi.


Muryarsa taji kamar zaiyi kuka a raunane "Adda kina nufin Rahima 'yar Gwaggo Salame ce?"


"Kanwar Halifa ba..."


Wayarsa ce ta subuce daga hannunsa batare da ya sani ba yaji kansa yayi mugun sarawa. Hawaye sosai Muhammad Zayyan Tureta ya soma yi a garin yaya Rahima ta cuce shi haka? Meyasa bata taba fada masa ba? Shiryawa suka yi ita da babarta ko kuwa shima asirin aka yi masa tunda ta saba? Ko kuwa ta turota ne domin ta sake bakantawa mahaifiyarsa saboda tsanar da tayi mata?


Duka wadannan tambayoyin basu rage daidai da cikin cokali na soyayyar da yake yiwa Rahima ba sai dai wani irin zafi da yake ji a zuciyarsa domin ko sonta zai kashe shi bazai taba auren irin Salame ba.


"Why Rahima???" Ya durkushe a kasa yana kuka kamar karamin yaro. [7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Cikin Salame kullewa yayi da ta ji muryar Mairama. Yau ko ba'a fada ba ta sani cewa kashinta ya bushe ta kure kanwarta ta. Radhiya kuwa da sauri ta iso bakin kofar dakin idanu sunyi ja sun kankance.


Ummi na ganinta a haka taji hankalinta ya sake tashi yau 'yar kunyar ma babu ta janyota jikinta za ta dubata ta saki siririyar kara saboda bayanta da aka taba.


Ai kuwa da sauri Ummi ta zaro idanu ta juya Radhiyan ta dage rigarta. Ga farar fata ga gyaran da take sha jiki yayi mugun laushi shiyasa wayar tayi mata wani dogon layi da yake tsartuwar jini daga tsakiya. Ruwan bala'i da masifa yau sun tarar wa Mairama ta kama hannun Radhiya ta hada da ba Rahima.


"Kama kanwarki kuje Lucas yana mota ya kaiku MHC"


Mama kallo daya ta yi a kofar dakin ta hango Salame kamar kaya jibge a kasa tayi saurin jan hannun Rahima saboda duk lalacewa baza su so ta ga mahaifiyarta a wannan halin ba. Da taimakonta suka kama Rahiman saboda ta fi Radhiya jin jiki suka fice. Itama bata son ayi a gabanta gara yau dai suyita ta kare a gaban mahaifinsu.


Dama jiran fitarsu Ummi take yi tausayin Rahima ya dakatar da ita. Dakin ta banka kai ciki a fusace Salame ta mike da kyar.


Cike da bacin rai da masifa Ummi tace "zuwa nayi mu saukewa juna iskokan dake kanmu Salame saboda na dade da fuskantar cewa kanki yana da matsala"


Wai saboda karfin hali tana kallon kowa a tsaye ta kumburo baki "saboda na daki 'yar gwal shine kuka yo min taron dangi..." waje tayi sai ta tsaya turus gani ashe harda Malamijo da Nene, ga su Yadikko da Hajjo. A zatonta Mairama ce kadai da Baffan Rahima da ta gano tare da Alh Indararo shima tana jin ramawa tasa 'yar yazo yi. Bude baki tayi za ta sake yin magana Malamijo ya kai mata wani wawan marin da bazaka taba kawowa a ranka dan hannunsa zai iya ba. Hannu ne na tsohon kashi ya sake bata a kumatun hagu. Wasawasa sai da yayi mata yafi biyar wani tukukin bakinciki yasa ta kasa kuka. 


"Ke mahaukaciyar ina ce Salame? Na fuskanci burinki bakincikinki ya kaini lahira to amma baki isa ba. Ko Amiru da yake yawon jagaliya bai samin bakincikin da kike kunsa min ba"


"Duk wannan abin akan Radhiya ne saboda ita kuna kaunar uwarta tunda babanta yana da kudi ko"


"Rufewa mutane baki mutuniyar banza" cewar Nene tana jin kamar ta maketa. 


Jan bakinta tayi ta tsuke kowa a tsakar gidan ita yake yiwa kallon da take fassara shi da tsana.


Mairama ta dubi iyayen nasu "Malamijo yau gani ga ka ga kuma babbar 'yarka. Ban san me nayi mata ba tsayin shekarun nan tun farkon aurenmu amma wallahi na gaji. Daga yau sai yau idan ta kuskura ta sake taba min yara zan dauki matakin da mu duka nan sai ran kowa in yayi dubu ya baci." Ta mayar da idanu ga Salame "Wai da nake ta taraki ki sani ba tsoro bane kawai ina yi ne da sa ran wata rana zaki ajiye makaman yakinki mu zauna lafiya. Amma tunda kince ba haka ba mu zuba nida ke shege ka fasa. Duk wani zafin rai da kike takama dashi kin kwana da sanin Mairama tana da dubunsa a ajiye"


"Kinga malama ni dai ba da niya na taba Radhiya ba. Rahima zan daka ta tare wayar ta sauka a bayanta ko ba haka ba?" Ta tambayi iska tunda babu mai bata amsa jikinta yana kadawa kada a cigaba da maganar nan allura ta tono garma.


Malamijo zaiyi magana Mairama ta riga shi "assha 'yar uwa, kada kiyi tunanin dukan Alheran kadai ya kawoni ko daya. Gobe kafin wannan lokacin zaki baiwa ubanta bayanin dalilin dukan masa 'ya, kuma kada ki manta matar aure ce ban san me zai faru ba idan mijinta ya ji. Wannan diban albarka da kike yiwa Rahima kadai ya isheni. Don ta ni kin dade baki yi min rashin mutumci ba. Ranar da duk na gaji na fyatoki ba ganuwa zakiyi ba"


Dariyar Alh Indararo ce ta katse Mairama "wai ke nan duk masifar akan dukan da tayiwa Rahima ne dama? To ni tunda na auri Salame ban taba ganin yarinyar nan ta shigo gidan nan ta fita babu kwalla a idonta ba. Wannan kuma kadan ne cikin abubuwan da tayi miki"


"Me kake nufi Alhaji? Wai me kika dauki Rahima ne Salame?" Baffan Rahima ya tambaye shi a zatonsa ta yiwa 'yar tasa abinda yafi wanda ya gani "yanzu ashe alkhairi zai iya zama sharri, sharrin ma ka rasa

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment