Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ta dawo da kallonta ga Radhiya da Mairama da suke tsaye kawai a wurin.


Gani tayi har yanzu Malamijo yaki magana ta cewa Mairama "muje dakinki kinji 'yata"


Mamaki ne fal cikinta bata san ko su waye ba. 


"Ke muje daki" ta ce da Radhiya


Hannunta cikin na Radhiya suka shiga dakin da komai ya kare masa yanzu sai katifa da shirgin kayansu. Rage tsayi Mairama tayi daidai kunnen Radhiya "ina bakuwar take? Kin taba ganinta?"


 Innawuro tana kusa dasu kuma taji tambayoyin da tayi mata. Radhiya sai ta dago kai tayi mata murmushi tana dan jin kunya. Mairama ta matsa mata hannu


"Ki bani amsa mana, idan rigima kika sake kwaso min zaneki zanyi wannan karon" 


Hayaniya ce ta cika tsakar gidan. Maza ne matasa da magidanta harda dattijai haka ma mata suka rinka tururuwar shigowa. Malamijo yayi tsamo dashi yana kallonsu zuciyarsa ta cika da firgici da ya ga cikin matasan harda masu sanduna. Sandarsu ce ta fulani da ado baya cika sai da ita, amma da yake ba gaskiya gareshi ba sai ya manta da wannan al'adar ya luluka tunanin ko dai duka zasu yi masa. Fulatanci suke ziryan baka jin komai sai sunan Mairama. To shima dai yaren gidansa kenan sai dai suna taba Hausa sosai.


Gaban Radhiya sai da ya fadi da ta hangosu q ta tabota  "Ummi sun kara yawa wallahi harda sanduna."


A kidime tace "dan gidan wa kika tabo kuma?"


Harda dan guntun hawayenta na tsoro tace "ni da bana fita wa zan taba?"


"Mairama kwantar da hankalinki muje wajen don nan bazai daukemu ba. Ni da su duka dangin Mairo ne mahaifiyarki"


"Me? Da gaske?" Matsawa tayi daga jikin Radhiya hannuwanta suna neman kofa da sauri zata fita.


Innawuro jiki ya kama rawa ganin da yadda Mairama ta fita. Radhiya ta kalla hawaye suna wanke fuskarta.


"Bata gani ne?"


Radhiya tabi bayan Mairama don ta karasa da ita gabansu tana cewa "eh"


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta iya fada tana kuka har wajen suna jin sautinta. 


Duka idanunsu sun koma kan Mairama tana kuka take tambayar Radhiya da ta rike mata hannu su nawa ne?


Baffa Gide kamar yadda 'ya'yan 'yan uwa suke kiransa ji yayi kamar iska zata daga shi don tashin hankali da yaji me takw cewa kuma tamkar ya ga Mairo haka kamanin Mairama suke da na 'yar uwarta. Kyaunta ne yasa Malamijo zabarta da biyan bashi duk da a lokacin Innawuro ta girme mata kuma itama bata yi aure ba.


Tsakar gidan kamar gidan kallo ya koma. Ga dangin mahaifiyar Mairama ga ahalin gidan Malamijo kacokan.


Shi Baffa Habubakari kuka yake ma saboda rauninsa yafi na dan uwansa. 'Ya'yansu jiki yayi sanyi. Basu san Mairo ba don manyan ma suna kanana komai ya faru amma sun san wannan makauniyar da ta nufosu jininsu ce. Ga dai idanu a bude amma basa ganin komai.


Sai da suka zo tsakiya Radhiya taja hannunta don su gaishesu tunda ta ga akwai manya "ummi mu gaishesu"


Emzee sai ya baro gefe shima ya dawo ya durkusa tare da Umminsa da Addarsa.


"Ina wuninku, yaya hanya....Allah sarki ashe baku manta dani ba" shine abinda Mairama take cewa tana ta waige hagu da dama saboda rashin sanin a ina suke.


Su Radhiya ma gaishe su suka yi bakin Mairama kamar gonar auduga duk da bata san mutum nawa bane. Ganinsu su ukun nan ya ishi bawa tausayi. Ga uwa mai cike da kuruciya amma makauniya mai marayu biyu a gabanta. Ga kuma 'ya'yanta tamkar zakuna suna gadin farincikinsu, jigon rayuwarsu.


Sautin kuka Mairama ta fara ji daga yawancin matan da suke wurin ta rinka murmushi tana jiran taji wani cikinsu ya tabata taji dumin uwa. Kamar Innawuro ta sani ta durkusa a gabanta ta rungumeta suna sakin kuka a tare.


Ardo Barkindo ya kalli Malamijo ya fito a tsolon rakensa yace "a bamu wuri mu zauna ko"


Sai kuma ya farga ya dawo daga duniyar tunani "kai, kai ina kuke ne, ga baki a shimfada musu tabarmi daga jikin bangon can yafi inuwa."


Tabarmin aka kawo suka zazzauna ya sake dubansu "wace mai girki ne a kawo musu abinci"


Hajjo sarkin bakar magana ta tabe baki "Binta ce kuma yanzu ka dankara mata saki ko a kirawo ta ne?"


Kunya tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara haka Malamijo yaji ya muzanta a gaban mutanen da ya taba wulakantawa yau suka taru suka yi masa kwarjini.


Allah Ya taimake shi Yadikko ta dawo yace "Uhmm, uhmmm....Yadikko fito da kwanuka aje gidan Tsahare ayi musu hadin wake da shinkafa amma da miya za'a siyo da salak. Idan akwai taliya 'yar gwamnati duka ta bada saboda ya ishesu. Sannan tasa nama a wadace do Allah" 


Yau wace rana Malamijo zaiyi abin kai. Ya zura hannu zai zaro kudi yaji hankalinsa ya tashi...mutanen nan fa da yawa, anya ba duka rugarsu Gide ya kwaso ba?


Ardo ya dakatar dashi don bai manta bayanan da yaji game da Malamijo ba.


"Kaga Malam Ali ba zama zamuyi ba a kan hanya muke. Ka zauna muyi magana"


A tsorace ya zauna daga gefen Baffa Gide don kallon da yake masa kamar zai wafto shi ya shiga dukansa ne. Bangaren matan kuwa Mairama sai dai taji wannan ta rike mata hannu ko an shafa bayanta suna fadin sunayensu.


Da addua ga marigayiya Mairo Ardo ya fara bude zaman nasu sannan ya ari bakin duka dangin nasu ya baiwa Mairama hakuri akan zumunci da suka yi sakaci dashi. Daga karshe ya gabatar da bukatarsu da cewa a yau dinnan ba gobe ba suke son daukarta da 'ya'yanta zasu koma da ita wurinsu.


"Don Allah da gaske?" Mairama ta sami kanta da fada cike da farinciki. Bata sansu ba kuma bata san halayensu ba amma ko don samun nutsuwarta tana so ace gata da dangin mahaifiyarta.


Matar Baffa Habubakari tace mata "Allah Yasa ki yarda ki bimu"


Ita kuwa me zai hanata yarda idan ba rashin sanin ciwon kai ba. Ardo ya umarci yaran nasu maza da su je su shigo da kayan da suka zo dasu. Malamijo ya baza ido ya ga wane shirgin suka kawo sai kukan tumaki ya ratsa kunnensa.


Raguna hudu ne da katoto kuma kosasshen sa guda daya. Kwanduna manya manya guda biyu cike da kwan zabi, buhun shinkafa daya 'yar gwamnati mai doki sai 'yar hausa daya da kuma buhun gero shima biyu.


"Tun daga haihuwar Mairama har aurenta, haihuwar jikokinmu da rasuwar mijinta da muka sami labari babu wani abu daya da muka halarta balle mu bada gudunmawa a matsayin iyayenta. Mal Ali ga wannan kayan, ba wai sakayya bace sai dai ihsani ne daga garemu kuma muna godiya a madadin marigayiya Mairo na kula da marainiyar Allah da kayi" Baffa Gide ya ce sauran suna gyada kai.


Innawuro ta riko hannun Emzee ya zauna a gefenta "ba rabaka zamuyi da ita ba. Mairama har abada 'yarka ce. Muna so ne dai ta bimu ta sanmu muma mu santa"


Yake Malamijo yake ya rasa dalilin da yasa suka yi masa kwarjini "bama zan hanaku tafiya da ita ba"


Kasa magana Malamijo yayi sai tarin kunya kamar ya tona rami ya binne kansa. Ba Mairama ba kadai kaf 'yayansa me zai bugi kirji yace yayi musu. Hajjo sai da ta magantu taji dadi ta fake da yi musu godiya "Allah Ya saka da alkhairi mungode. Ohh Malamijo baki sun zo gari -e- gari ko ruwa ba'a basu ba sai karbar kyauta daga hannunsu. Ke Radhiya tashi muje na tayaku hada kaya yau kakarku ta yanke saka"


Cike da zumudi Radhiya ta mike tana kallon yadda Mairama take ta fara'a a tsakanin mutane. Idan ma kuruciya tasa bata gane mahimmancin zumunci ba a iya hankalinta ta sani cewa Umminta tana cikin farinciki. Wannan kuma ya isheta komai.


Yadikko bata hakura ba sai da ta dafa musu dafadukan shinkafa da wake. Babu bama dai bare kifi amma tayi nata kokarin. Abin kunya ne ace wannan bakin sun zo sun tafi basu ci komai ba ga nisan hanya. Tasan tsiyar da suka tarar a gidan ita ta kara tunzura komawarsu a ranar.


Batare da bata lokaci ba suka fito an gama shiri. Wani dan akwati da take ajiyar mahimman abubuwa kamar khakin Zayyan, wasikarsa da kuma hotuna tace Radhiya ta tabbata ta dauko. Dariya tayi don ta gama haddace komai na ciki. Hotunan yawanci na bikin iyayenta ne da na sunanta. 


Karfe biyar da kwata sun gama shiga mota. Baffa Gide yana tsaye a gefen mota kusa da Malamijo suka sake yin musabaha "yanzu da muka dena yawo idan kana nemanmu mun koma Giade can asalin garinmu amma rugarmu tana daga ciki da dan tafiya daga garin. Wannan da kake gani mijin Innawuro shine Ardo na biyu bayan kafuwar rugar" 


Sallama Mairama tayi da kowa daga ita har su Radhiya ko digon hawaye irin na kewa dinnan. Rabuwa da Yadikko da Hajjo da kuma sauran 'yan uwa ya dan sa sunji wani iri to amma fa ko kadan bikin Magaji bazai hana na Magajiya ba.


**********

WAIWAYE....
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Mairama ta ga gata da ya amsa sunan gata a Rugar Barkindo. 'Yan uwa ke tururuwar ganinta har ana fadan gidan wa zata zauna. Ardo yayi tsalle ya dire yace matarsa ce zata dauka ai ita ce mace. Dole sauran suka amince aka barwa Innawuro. 


Idan manya ko dattijai cikin danginsu sunzo sai ayi ta kallonta ana cewa kaza dinta irin na Mairo ne. Murmushi kawai take yi don ko hoton mahaifiyarta bata taba gani ba. Sun tausaya mata da jin labarin rasuwar mijinta ga makanta. 


Radhiya da Emzee sai gasu cikin 'yan uwa sa'anninsu ana ta nishadi. Abinci da nama anci an ture. Kafin sati ya zagayo jikinsu ya fara nuna kwanciyar hankali da koshi.


Mairama kullum cikin godiya take ga Allah da Ya dawo mata da dangin mahaifiyarta. Ba jimawa sabo ya kullu sosai a tsakaninsu baki daya. So da tausayawa suke nuna mata da 'ya 'yanta. Ardo ke cewa su duka marayu ne ababen dubawa.


Bata cuci kanta ba ta roki alfarmar su Radhiya su koma makaranta. Tare aka nema musu JSS 1 ita da Emzee da ya gama aji biyar. Ita a makarantar kwana ta gwamnatin jaha ta mata shi kuma jeka ka dawo ta maza. Ranar da dan gidan Baffa Habubakari ya kawo takardun tubure musu Radhiya tayi da kuka wai bata so.


"Karatun kike yiwa haka Radhiya?" Innawuro tace tana kokarin bata baki.


"Dama saboda bama cin abinci mu koshi ne fa Ummi ta kaini makaranta inyi kudi" 


Mairama kunya ta isheta tasa hannu tana nemanta "haka muka yi dake? Kuji min yarinya"


"Da naga ko nama bama ci irin na gidan Baba Kallamu shine nayi zaton haka ne" ta mayar mata da amsa tana shure-shure.


"Idan bata yi ba ai ba'a kirata jikar Ali ba" Innawuro tace tana dariya.


Radhiya ta turo baki "Malamijo muke kiransa mu dai"


"Ina yaga malanta sai bakar rowa da mammakon tsiya"


"La la lahhhh baban Ummi ne fa"


Ardo yana jinsu yana rubutu a jikin allo yace "da kyau 'yar albarka ki kare masa kinji ko. Duk tsiyar naka ai naka ne Innawuro"


Dariya rigimar Radhiyan ke bata tace "kasan ni ba bakuwar zafi bace Allah Ya baki hakuri. Nima kizo na baki labarin 'yar uwata Mairo. Ga kyau ga kirki kamar wata dan daren goma sha hudu"


Idanu Radhiya ta bude sosai da mamaki "wata dai irin na sama Innawuro?"


"Akwai wata a kasa ne?" Mairama ta fada tana jin kamar ta mangareta.


"Tabdi, Ummi kenan Innar taki a mulmule take kamar wata. Ga Malamijo kamar tsolon rake. Mu dai Allah Ya taimakemu ke daidai kike."


Mairama ta fusata ta fara wawurarta "Karami dauko min yayarka ko ka janyo min ita. Yau tambotsan nata harda iyayena kuma"


A guje ta tashi "Ardo don Allah ba Innawuro ce ta fada ba."


Innawuro ta dauko muciya "bari na mulmule ki kema sai aji dadin kiranki jikarta"


Hanyar waje tayi tana gudu wai ita gidan Malamijo zata koma.


Mairama ta daure fuska "da ya fi miki mu ma mu huta. Kuma karatu ki ma fara shiri sai kinyi"


Dawowa tayi da baya tana murza yatsan kafarta a cikin kasa tana tura baki "to don Allah ki kaini soja irin na babana indai kina so nayi karatu"


Gaban Mairama ne ya fadi ba shiri sai ga hawaye. Innawuro da ta dauki abin wasa tana biyewa Radhiya ta shiga bata hakuri tasan bazai wuce mijinta ta tuna ba.


Radhiya ma sai ta soma kuka tana cewa tayi hakuri zata yi karatun ko wanne ne.


**********


Alheran Radhiya Zayyan Tureta irin fitinanun daliban nan ne marasa tsoro ga kin ji. Duk inda akace 'yan aji daya sunyi laifi to in sha Allahu Radhiya tana cikinsu. Kan kace kwabo tayi kaurin suna tsakanin dalibai da malamai. Kirikiri tace sunanta 'Yar soja haka babanta yake kiranta daga Mairama ta bata labari. Shikenan makaranta suka santa da wannan sunan. Anyi sa'a tana dan taba karatun babu laifi. 


Wata rana suna layin dibar ruwa suna ta hayaniya irin ta 'yan makaranta ta dage tana ta zuba.


"Allah Ya kaimu siniya wallahi zan warwasa a makarantar nan. Duk wasu jiniya a lokacin sun shiga talatin a hannuna"


Kawarta Ruqayya tace "ke 'Yar soja so kike yadda muke tsinewa su senior Jummai kema a tsine miki?" 


"Ke baki gane ba. Lokacin kannen su senior Jummai mai tafiyar agwagwa ne a makarantar. Ramuwa zan zauna yi"


Wata tace "ai kuwa nima zan so, rannan fa kwai tace nayi mata a karkashin gadonta"


Radhiya ta daka tsalle "inama nice wallahi, na samu na sassaka mata kashi mai waaaaaari"


Dariya suke duniya sweet kampo sai ga senior Jummai ta taho da tafiyar catwalk dinta da su Radhiya suke yiwa lakabi da tafiyar agwagwa. Ta gama jinsu tsaf suna bayan ginin da famfon yake.


Idonta ya kyallo mata ita sai kawai ta canja hirar amma saboda tsoro muryarta har rawa take yi.


"Allah Yasa senior Jummai tace in zama daughter dinta a makarantar nan. Daga ranar wanki da debo ruwanta duka zan rinka yi"


Sauran sai suka fara mamakin me take nufi tunda dai haduwa suka yi ana zaginta. Yadda tayi  maganar ne idanu har sun ciko da hawaye yasa Jummai da sauran seniors din dariya. Kawayen Radhiya ciki ya duri ruwa. Ita kanta a tsorace take. Jummai ta dafa kafadarta kamar ta saki fitsari don tsoro sai ji tayi tace daga yau kada wani ya sake ko da aiken daughter dinta ne.


Kowa yayi mamaki harda kawayenta tace Radhiya tana burgeta saboda ko me za'ayi mata sai ta aikata abinda tayi niya. Idanunta kawai zaka kalla kasan fitina da rigima suna dawainiya da ita.


Wata kungiya da aka bude a makarantarsu SS wato School Soldiers a nan aka samu kanta. Da jikinta da zuciyarta take wannan aikin na kare hakkin dalibai. Gashi da kayan makarantarsu riga da zani ne amma an basu hula irin ta sojoji mai lankwashewar nan suna sakawa akan hijabansu. Radhiya jin kanta take kamar sojar gaske. An kamanta gaskiya da amana sannan an gurji seniors masu hana sababbin dalibai sakat. Idan kaji ana Officer 'Yar soja a makarantar zaka rantse wani babban soja ne saboda yadda ake shayin shiga tarkonta. Zaman SS shine babban jindadinta a makarantar.


A haka aka yi karatun cikin ikon Allah tayi nasarar fita da credit bakwai. Emzee kuma duka taran ya haye. Sai dai ko kadan a yadda ilimin ya tabarbare bazaka hada makarantar gwamnati dake kauye da wadda take birni ba.

***



Tana jin shigowarsa dakin nata tayi saurin rufe ido kamar mai bacci. Murmushi kawai yayi yana kada kai. Zainab bazata taba canjawa ba indai tare dashi ne. Shekarun da suka yi a matsayin ma'aurata bai sa ta canja komai daga yadda ta faro ba. Akan doguwar kujera irin ta hutawar nan ta dakin ya zauna sannan ya soma yi mata magana.


"Tashi magana zamuyi"


Kin motsawa tayi sai da taji yace bari ya hawo gadon ya tabbatar ko idonta biyu.


Juyowa tayi a hankali tana jin kunyar ya gano karyarta. Bata son yadda take yiwa Musa amma zuciyarta ta kasa rissina.


"Shawara nazo nema"


"A wurina?" Ta tambaya mamaki yana bayyana a fuskarta.


"Eh, aure nake son karawa sai dai na kasa tsayar da shawara akan na dawo da mamansu Aisha ko na auro wata daban"


"To ni me kake so nace? Ka auri wadda tafi kwanta maka"


Fuskarsa ta nuna ba haka yaso ba kuma shima bai boye ba yace "zan so kiyi min rigima irin wadda kowace mace take yiwa mijinta a lokacin da ya tashi yi mata kishiya"


Cikin yanayin rashin damuwa don har ranta ita bata ga abin rigima ba tace "saboda me?"


"Saboda nasan cewa ko yaya Zainab ta damu dani kamar yadda na damu da ita. Sai dai nafi kowa sanin zaman hakuri kike yi a gidan nan. Na tauyeki na hanaki walwala da jindadin zama da wanda kike so"


An tabo inda yake mata kaikayi sai hawaye sharrr tana gogewa da bayan hannunta. 


Musa yana jin kukan har ransa amma yasan ba nasa bane na wani ne "kinyi hakuri sosai Zainab, naso ace mun haihu don in samu abinda zan cigaba da garkuwa dashi in ki rabuwa dake amma Allah bai kawo ba. Sai nace zan barki ko don su Aisha. Yanzu kuma gashi suna shirin aure nan da watanni kadan. Ina ganin kamar bani da sauran dalilin cigaba da zama sanadin kuncinki"


Kukan Zainab sai ya koma mai sauti. Tana tausayin Musa bisa soyayyar da yake mata. Tayi iya yinta amma zuciyarta taki amsarsa a matsayin masoyi. 


"Kayi hakuri da dukkan bata maka da nake yi, zanyi kokarin gyarawa"


Murmushi yayi mata yana mika mata takardar hannunsa "ni na gyara mana matsalar ina fata Allah Yasa nayi abinda ya dace. Zainab na sakeki saki daya"


A gigice ta kalle shi hawayenta yana karuwa. Idan ya saketa fa kenan babu sauran shamaki tsakaninta da Hadir. A gaggauce ta bude takardar sai ta kula guda uku ne a hade da stapler. Daya takardar saki, daya check na miliyan biyu, dayar kuma takardar mallakar wani gida ne a Kano da ya saya mata dan madaidaici. Dago kai tayi sharbe da hawaye harda majina.


Cikin nutsuwarsa yake magana daki-daki "tukwicin kulawar da Aisha da Anisa suka samu daga gareki ne. Bana son fada amma yabon gwani ya zama dole. A kanki na yarda ba sojoji bane kadai jaruman kasata harda matansu. Soyayyarki ga baban Ibrahim ita tafi komai kara miki kima a idanu na. Nayi zaton kudina zai sa ki manta da wanda yake talaka mai nakasa amma bakiyi ba. Kin so zama da mutumin da bautar kasa ta nakasa farincikinku domin cikar soyayya. Nagode da lokacinki da kika ara min muka zauna tare"


Maganganun sunyi mata tsauri sun taba mata zuciya. Tashi yayi zai fita Zainab ta taho da sauri ta rungume shi tana kuka. Bata taba yi masa haka ba idan ba shi ya nema ba sai yau.


"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min Abban Aisha. Ka yafe min duk laifukan da nayi maka a zamanmu tare"


Dago kanta yayi kana ganin damuwa a cikin idanunsa "yanzu dai ki soma hada kayanki kafin na chanja shawara"


Da hawayen take murmushi "nagode"


"Nima nagode" yace ya sa kai ya fita yana jin a ransa kamar an sauke masa wani kaya mai nauyi. Ya dade yana tsoron hakkinta kada ya kama shi saboda son zuciyarsa yau Allah Ya bashi iko ya rabu da ita ba don yana so ba.


Ajiyar zuciya ta saki bayan fitarsa ta mika godiyarta ga Allah sannan cike doki ta kira Ibrahim.


Labaran tara na NTA ya kunnawa Hadir yana gefe game ya dauke masa hankali a wayar kiranta ya shigo. Murmushi yayi ya dauka.


"Hello Mama"


Hadir ya juyo ya kalle shi sai kuma ya dauke kai. Ina ma zai iya tambayar lafiyarta da yayi. 


Daga daya bangaren tace "Ibrahim yaya su Umma?"


"Lafiya kalau, ya su Anti Anisa da Baba?"


"Su ma lafiya kalau. Ibrahim nace me kake so gift din graduation ka ki fada min kamar wata surukar ka ko, na kula ko hira baka son yi dani" tayi karamar dariya.


"Ina naga fuskar" yace a zuci. Ita da bata sakin jiki da kowa bare ayi batun hira. Daga gaisuwa sai ta fada kogin tunane tunanenta ta bar mutum zuru. Yana mamakin yadda idan yaje hutu take hira da su Anisa duk da ba wata hirar kirki suke yi ba.


"Ya kayi shiru ne?"


"To kiyi hakuri zan gyara"


"Shikenan, ina babanka?"


Hadir ya kalla suka hada ido. Anya Mama ce kuwa yace a ransa. Bata taba tambayarsa babansa ba sai su Umma kawai.


Kara kashe shi tayi da wani mamakin ta hanyar cewa ya dora masa wayar a kunne "saura ka sani a speaker"


Bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba. Wai dama Mama ta iya wasa haka? 


Hankalin Hadir gabadaya yana gare shi sai kawai ya dora masa. 


Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta da taji sautin numfashinsa. Soyayyar da ta dade tana dannewa ce ta taso mata. Da suna tare yanzu shekararsu goma sha tara da aure.


Cikin wani yanayi na shauki da begen da yake nuna soyayya bata tsufa tace "Hadir"


Allah Sarki rayuwa, yaji sunan har tsakiyar kansa amma bazai iya amsa mata ba.


"ASTAGFIRULLAH" tace da sauri ta katse wayar. Shaf ta manta cewa har yanzu tana karkashin Musa har sai ta gama iddah. Tashi tayi ta bude wardrobe ta dauko akwatunanta.


Da safe Musa da kansa ya sanar da su Aisha cewa mamansu zata dawo sannan Antinsu Zainab zata tafi. Sun saba da ita sosai a hannunta suka girma. Tana kuka suna kuka har airport suka rakata. Motarta Musa yace zai bayar a kawo mata har gida. Tayi ta masa godiya da kyakkyawar addu'a ta shige jirgi zuwa garinsu tana mai fatan samun sauyin rayuwa mai dadi.


**********


A firgice Rtd Major Mustapha ya tashi jike da gumi daga mafarkin da yake yawan yi wanda yake daga masa hankali ya shiga laluben kafar katakonsa. Mafarkin ya tsananta a gareshi tun bayan da suka sanya ranar komawa kasar haihuwarsu. Korido din da zai sada shi da kitchen ya nufa don ya sha ruwa ya hango Mami ta barbaza kaya a gabanta na tsaraba da take ta warewa tana saka sunaye.


Kasa tafiya yayi duk motsinta yake bi da kallo. Wannan kyakkyawar matar kanwarsa ce, matarsa kuma uwar 'ya'yansa. Hakika a kullum baya gajiya da sanya Hassana cikin addu'o'insa domin ta cancanci fiye da haka. Tayi hakuri dashi iyakar hakuri musamman a lokutan da yake ganiyar ciwo har yakan nemi rayuwarta ba a cikin hayyacinsa ba. Tunanin kawai kan sa tsigar jikinsa tashi. Tabo uku ne a jikin Mami wanda suka samu a dalilin PTSD dinsa.


Jikinta ya bata yana kallonta haka kawai, ta daga kai suka hada ido. Murmushi suka yiwa juna ya dawo falon ya zauna.


"Me ya hanaki bacci shabiyu har ta wuce?"


"Aikin nan yaki karewa Daddy. List din mutanen ma kamar bamu yi rabi ba" ta dan bata rai.


"Ku kuma mata da baku da nutsuwa indai akan tsaraba ne ko"


Tattara kayan ta soma yi gefe sannan ta dube shi "me ya tasheka ne?"


Shirunsa ya fahimtar da ita komai. Kusa dashi taje ta zauna "nan da kwanaki goma in sha Allah muna gida. Muna kwana biyu an gama gaisawa da 'yan uwa babu inda zamu je sai wurin Ummin Awwab da Hadir. Lokaci yayi da zaka kore komai daga ranka ka rungumi kaddara."


"Yes Ma" yace yana murmushi.


Maida masa martanin murmushin tayi ita ma "Tashi muje mu kwanta kasan gobe is a big day" 


Suna kwance tuni Mami tayi bacci amma shi ya kasa sai rarraba dayan biyu yake. Ko yaya iyalin Zayyan? Allah Yasa suna cikin mafi kyaun yanayi. Sai kuma ya koma tunanin auren Zahra da Fauziyya da za'ayi nan da wata biyu. Kowaccensu tuni ta hada degree dinta. Hadi ne na gida zasu auri 'ya'yan 'yan uwa kamar yadda ya kusan zamewa danginsu al'ada. Har nan aka turo mazan suka daidaita kawunansu. Bai san lokacin da bacci yayi awon gaba dashi ba.


Washegari kuwa banda shirin tafiyarsu da yaki karewa karfe bakwai na dare suka tasarma gidan da Mami take aiki. Major sanye yake sa suit sky blue da light grey din shirt a ciki. Yayi gyaran fuska yayi kyau yana rike da sandarsa da take taimakawa wurin rage masa rashin jindadin tafiya da kafar katako duk da ya saba yanzu.


Mami, Zahra, Fauziyya da Zayyana duka abaya ne a jikinsu masu kyau kowacce tayi nadi da mayafin da ya dace.


Party ne na bankwana iyalin Herr(Mr) da Frau(Mrs) Schmidt suka shiryawa Mami a matsayinta na shugabar ma'aikatan katon gidan. Sun matukar jindadin zama da ita tun lokacin da suka basu wuri a gidansu kafin daga baya su kama wani mai dan girma a waje. Iyalin babu abinda yasa suka likewa Mami kamar tsantsar tarbiyar da yaransu suke koyi da ita

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment