Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata zuciyar ta tuna mata. Harda guntun hawaye sai da tayi bata ankara ba kafin ta daure ta fito inda suke.


"Uhmm nace Malamijo yau me za'a dafa da rana ne? Naga ana ta hira shine baku kirawoni ba" wai ita nan za ta bagarar kamar bata san me suke yi ba. Daga nan ta samu ta arce. Ofishin 'yan sanda zata je ta shigar da kara kafin turawan mayun su iso azo a fitar mata da yaranta.


To shima ba wai yana cikin hayyacinsa bane duk ya gama tsorata ya fara danasanin kiran Radhiya. Yarinyar nan da ya gama sanin halinta me ya kaishi kiranta da kansa. Wayarta ce tayi kara a lokacin taken wakar Celine Dion ta film din Titanic wanda ta sanyawa Awwab. A wurinta wakar bata tsufa sai ma nishadin da take saka ta idan ta tuna masoyinta.


Idanun Malamijo da na Hajiyayye basu da na biyun kwatance a lokacin. Tsoro ne karara ya bayyana ita kuwa tana dauka da turance tace masa "Chèri please follow my lead i'll explain everything later. Say something in German" (ka biyewa duk yadda kaji nayi, zanyi maka bayani daga baya. Ka yi magana da yaren Jamus)


Yana cikin office dinsu a lokacin ya kirata. Abinda tace kawai ya isa ya saka shi gane cewa akwai abinda take yi. Alheran dinsa bata ji, sai dai kuma idan ta canja daga yadda take ta tashi daga yarinyar da ya fara so daga haduwar farko kenan. Fitinanniyar dai ita ce tashi mai sanya shi nishadi a kowane lokaci. 


Speaker ta sanya kowa na ji ya rinka yi mata kalaman soyayyar da yasan cewa ba fahimta take yi ba ita ma.


"Amaryar Malamijo kin dai ji me yace. Wai ku jeru a daki ke da yaran naki yanzu zasu shigo. Idan anyi binciken sun ware mayu a cikinku sai su saki sauran"


"Inji uban wa akace mu mayu ne? Garin nan waye bai san gidan iyayena ba? Malamijo kace wani abu mana" ta fada a raunane hawaye na zuba.


"Ince me? Na auro mayya tayi sanadin da majalisar dinkin duniya ta mayu zata zo gidana" ya ce gumi na karyo masa. Gidan gabadaya yayi masa zafi dari bisa dari ya yarda da zancen Radhiya.


Wayar ta dan kara a bakinta "ranka ya dade ko za ka danyi mata hausa ta fahimta. Mayyar da ta auri kakan nawa ce ta fito" ta kalle su "shine wakilinsu da yake kula da hausawan mayu"


"Bata wayar" Awwab yace dariya na ciwo shi. Wace mai tsautsayin ce wannan ta shiga tarkon Alheran?


Ai Hajiyayye na jin haka ta zube a kasa ta fashe da kuka. Tsoro yayi mata yawa zawon ya fara tsartuwa daga ma'ajiyarsa saboda tsoro. Muryar Awwab dama irin wannan deep voice din ce mai tahowa daga kirji. Mata da yawa suna fadawa soyayyarsa a kanta yayin da take razana marasa gaskiya irin Hajiyayye.


"Kayi min rai ranka ya dade aradun Allah karya nake ni ba mayya bace. Mutum ce kamar kowa kuma indai aurene ko bai sakeni ba ni na saki kaina yanzu zan tafi ba sai kun zo ba"


Dariya yake neman yi Radhiya tace da sauri "ranka ya dade bari na tayaku binciken kafin ku iso zan tabbatar da gaskiyarta" kashe wayar tayi ta ga kowa ya fara ja da baya saboda zawon Hajiyayye. Wari ya isheta amma haka ta daure bata matsa ba.


"Me kike cewa?"


"Nace ba, aurena da Malamijo wallahi duk shiri ne tsakanina da Talle. Rabonmu kawai muka zo yaga mu tafi amma bani da alaka da mayu. Kuyi hakuri yarana akwai marayu a ciki. Waye zai kula dasu?" 


"Tunda har kun iya kulla cuta ki shirya ko ba'a kamaku an cinye ba zaki shiga prison. Kurkuku nake nufi" Emzee yace yana cin magani.


Rarrafawa tayi wurin Malamijo wanda hankalinsa ya kwanta da ya gano me Radhiya ta shirya. Dage hanci yayi ga wari ya dame shi "ki kwashe yaranki kada ki koma min cikin dakin Hajjo. Daga nan ki tsaya ki kirawo su. Sannan shanuna...."


Tana kuka tuni ta mike tana gyara zani babu kyan gani tace "suna gidan Talle"


"Me kike jira ne baki fita ba sun kusa isowa" Radhiya ta dada tsorata ta. Yaran ta kira suka fito a gurguje kan kace meye wannan sun fita Malamijo yana daga murya yana sanar da ita saki uku yayi mata.


Suna fita gidan ya kaure da hayaniya da murna. Malamijo tsananin farinciki yace "kowa ya shaida wallahi na bawa 'Yar Soja kyautar tunkiya, akwai wata mai ciki ta zama taki"


"Ahhh nifa gaskiya tayi min kadan" tace tana tura masa baki.


Baiyi fushi ba ya saki fuska "to me kike so Alherin babanta"


"Alheran ne fa ba Alheri ba"


"To ni dai sammakal...me kike so? Kai ku fito kowa yayi shaida zan yiwa babbar jika ta kyautar bajinta"


"Ni dai kada ka kasa fa"


"Ke! Dube ni nan da kyau Ali Gidado nake. Ciki lafiya baka lafiya. Da kudina a jikina"


Kowa ya fito harda maijego Atine. Hassana da Usainanta suna bayan Zayyana da Hibbah da suke jindadin daukar yaran. Radhiya ta dan hadiyi yawu kafin tace "Malamijo za ka dawo da Hajjo ko?"


"Kamar da kasa yarinya. Ai da shike Allah Ya taimakemu dole mata suke idda kinga bata gama ba har yanzu da damar kome tsakaninmu"


"To dama so nake tunda ka yarda za ka min abinda nake so su duka matan nan ka hada da Nene Marka da kai kanka Hajji me zuwa ayi daku"


Yawu mai daci ne ya tokare masa a wuya da yaji me tace. Dan murmushin nasa ya bace bat. Hajji har mutum shida kamar tana son talauta shi. Bai bata amsa ba yace Emzee su zo su tafi gidan Talle a fito masa da shanunsa. Radhiya tace to a bata tinkiyar mara ciki a yanka.


"Indai nama ne muje gonar sha Allah an dena miya lami a gidan Malamijo amma ki sake shawara akan batun zuwa hajji. Idan ba kaina zan sayar ba dame zan biya kudin"


***********


Safiyar laraba washegarin tahowarsu daga Abuja jiki a sanyaye Ummi ta ajiye wayarta tana matsar kwalla a boye. Ashe Daada yana kula da ita. Fita tazo yi daga dakin saboda kukan da ya taho mata ya yi saurin tare hanyar.


"Haba Fillo me zaki boye min? Waye ya rasu kike kuka kuma baki son na sani?"


Kukan gabadaya ya taho mata yana rarrashinta sannan da kyar ta fada masa cewa matar Badaru ce ta kirata wai yau sadakar uku na rasuwar Mal. Aminu abokin mahaifinsa mai matsayin uba a gareshi wanda yake ta dokin zuwa ya gani. Jikinsa ne ya saki ya zauna ya dafe kai.


"Sojana kayi hakuri" tace wata kwallar na taruwa a idonta.


"Waye ya isa yaja da ikon Allah? Zamu iya tafiya a yau ko kin gaji?"


Da sauri ta tashi "muje yau din."


Ba wasu kaya suka baza ba, abinci ma siya sukayi jiya da yau din shiyasa cikin abinda bai kai minti shabiyar ba sun gama kimtsawa dreban kawai suke jira yaje siyan mai. A hanyarsu ta zuwa Sakkwaton babu wata hira. Zayyan yaci burin zaman hira da Mal. Aminu Allah bai nufa ba. Sun isa da sauran haske Ummi ta rinka kwatantawa dreban Daddy din da ya kawosu. Zayyan ganin garin yayi kamar ba Sakkwaton da ya sani ba. Kamar sauran wuraren da ya gani nan ma an sami chanji na fasalin abubuwa da cigaban rayuwa. Karuwar tituna da gine gine yasa bai gane lungun gidan nasu ba. Har yanzu dai mota bata shiga amma duk da haka wurin ya sauya. Sun fara tafiya Ummi ta dan dakatar dashi da suka karya kwanar gidan Mal. Aminu maimakon su mike hanyar gidan nasa iyayen.


"Ko za ka jira na fara zuwa na sanar dasu kada ganinka ya tsorata mutane da yawa."


Bai musa mata ba don yasan gaskiya ta fada. Ita kadai ta karasa kofar gidan daga gefe an saka rumfa inda maza suke nasu zaman makokin. Kan ta a kasa taji an kira sunanta "Maman Radhiya kece da yamman nan?"


Rayyanu ne yayan Zayyan wanda yake bi. Gefe ta dan matsa yazo ya sameta suka gaisa.


"Kinje gidan babu kowa ko? Da yake yau za'a rufe zaman makokin duka muna nan"


Ta'aziyya ta fara yi masa kafin cikin nutsuwa ta sanar dashi dawowar Zayyan a takaice. Ikon Allah kawai ya rinka ambata kafin yace ta shiga ciki zai taho dashi. Tana kallonsa ya duka yana yiwa Badaru rada kafin ta karasa shiga gidan. A tare suka nufi hanyar da ta baro da sauri kamar zai tafi kafin su karasa.


Dan uwa dan uwane komai lalacewarsa. Lokacin da yake tare dasu a shekarun da suka gabata kiyayya, kyara, hassada da bakinciki ne kadai abinda yake gani a idanun 'yan uwan nasa. Yanzu kuwa kafin su karasa gaban juna daga shi har su hawayen farinciki suke zubdawa. Dayake dreban Daddy yana da labarin yadda akayi zaton Zayyan ya rasu da dawowarsa baiyi mamaki ba da ya ga magidanta irinsu rungume da juna suna hawaye. Hakuri ya rinka basu amma sai da kyar suka iya mallakar kawunansu don ma a waje suke.


"Muje Jume ta ganka Zayyan." Badaru ya ja hannunsa kamar ya kama yaro.


A ciki kuma bayan yin gaisuwa ga Gwaggo Ladi da 'ya'yanta mata dake wurin Ummi ta matsa kusa da su Mubaraka da matan su Badaru ta fada musu dawowar Zayyan. Matan mazan na alhini yayunsa mata suna kuka. Jume ta zaga bayi sai Gwaggo Ladi suka fadawa. Hankula suka tattara suka koma kofar gida sai suka fara tunanin ko dai su koma nasu gidan ne tunda nan gidan gaisuwa ne ga matan mutane a zazzaune.


"Ku barni na ganshi kafin ku tafi. Allah bai kaddari haduwarsa da babansa ba ku bari na gane masa Zayyanu" cewar Gwaggo Ladi.


Sallamar babban dan Mal. Aminu da kannensa maza dasu Badaru ita ta sanya matan kuka da ganin Zayyan da yake tsakiyarsu. Idonsa a kan Gwaggo Ladi tana dago masa hannu ya taho gareta. Girma ya kamata sosai tafiya tana wahalar da ita. A gabanta ya durkusa gidan ya koma tamkar yanzu akayi mutuwar. Daga inda Jume take bayan ta fito daga bandakin take jiyo koke koke. A tsaye suke ita da wata jikarta ta wurin 'yarta mace ta saka ta kiran Maikudi a waya. Kare masa tanadi tayi rai a bace har anyi uku bai zo ba. Yana gidan ma aka aiko da rasuwar yaki fita wai ciwon jiki yake yi. Ya riga ya sakawa ransa cewa Mal. Aminu makiyinsa ne bai ga dalilin zuwa jana'iza ko gaisuwa ba. Sai da ta gama fadan ta ajiye wayar ta tako itama din kafafun sai a hankali.


Kamar ance ta kalli gaban Gwaggo Ladi sai ganin mutum tayi a durkushe gabanta 'yan uwansa sun kusa rufe shi. Gaba na faduwa da rawar murya tace "wa nake gani kar Mal. Muhammadu?"


Kama yayi mata sosai da mijinta matar Rayyanu ta kamo hannunta a hankali ta zaunar a gefen Gwaggo Ladi. Zayyan ya matso yana murmushi da 'yar kwallarsa.


"Jume Zayyanu ne ya dawo"


Idanunta ta shafa harda gogewa da zaninta tayi murmushi mai ciwo "ko dai nima na mutu ne?"


Sai ta sake tsinkewa jama'a zukata aka cigaba da kuka. 


"Jume ni din ne dai Zayyanu ba mutuwa nayi ba"


"Nagode Allah da bakina zan rokeka gafara" tace tana wani irin kuka da take tuna bakar izayar da ta rinka gana masa tun kuruciya. Maikudi da ya gagareta har yanzu waye silar lalacewarsa idan ba ita ba. 


Basu barta ta cigaba da magana ba suka tattara duka iyalin gidan Marigayi Muhammadu Tureta suka tafi nasu gidan. Murna a wurin 'yan uwansa da 'ya'yansu da suka sanshi a matsayin baban su Radhiya ba kadan ba. 


"Me zan dafa maka Zayyanu? Ban yarda ka ci abincin kowa ba sai girkina. Kai ku hura min wutar icce ni ba son girkin risho nake ba" 


Zaunar da ita Zayyan yayi yana dariyar yadda ta tashi hankalinta "ki zauna nayi ta kallonki Jume"


"Har me zaka kalla a jikin matar da taci zalinka ta kasa rike amanar maraya"


Mairamu da kowa ma hawaye suke yi na tausayinsu. Ga su Badaru da suka san yadda rayuwar gidan nasu ta kasance tun da su ma sai rokonsa gafara suke yi.


"Bana jindadin yadda kuke yi min. Jume ke uwa ce a gareni mai cikakken iko akan danta. Da dadi da babu dadi kinci kashina kinci fitsarina. Wahalar da nasha ta kuruciya ita ta samar da Zayyan din da yake gabanki mai hakuri da juriya" ya juya ga 'yan uwansa "idan kuna biye mata za ku tabbatar min da cewa ni din dan uba ne kawai baku daukeni kaninku ba"


Kalamansa sunyiwa Jume dadi haka ma yayunsa. Tashi tayi da sauri tayi hanyar bangaren Maikudi. Yadda baije gidan gaisuwa ba haka ya hana matarsa da 'ya'ya suna zaune kowa rai a bace amma basu da yadda zasuyi dashi. Matarsa har tafi jindadin lokacin da aka tsareshi su ka sakata suka wataya son rai a gidan. Yana daga uwar dakinsa a kwance ya bararraje matarsa tana yi masa tausa. Daga bakin kofa take ta kwala masa kira ya taso a fusace.


"Jume ya haka zaki zo min har kofar daki. Wannan ai rashin tunani ne, waye yake zuwa kofar dakin mai aure. Gaisuwa ce dai nace bazanje ba ko ana dole ne inji"


"Ba wanan ya kawoni ba Maikudi kazo ga dan uwanka ya dawo"


Da yana da kudi bai ga dalilin da zaisa shi zaman gidan nan ba. Ya tsani ya farka ya ga kowa cikinsu saboda babu mai kaunarsa. Haka ya karaci zamansa da shan wahala a rufe sai sun bushi iska suke lekawa.


Zayyan da sauran suna jiyo yadda yake daga mata murya shiyasa ya tashi yabi bayanta.


"Ko ma waye dan uwan bai san inda nake bane da bazai karaso ya gaisheni ba sai kin taso da kanki? Wato gani matsiyaci nine zan fito gaida irin mutanen da kuke yiwa maula ke da su Badaru....."


Numfashinsa ne ya nemi daukewa a lokacin da Zayyan ya bullo tsakar gidansa inda ya tsare kofa ya hana Jume wucewa sai ma kukan bakinciki da take yi.


Zayyan yana shigowa bai tsaya ko ina ba sai a gabansa ya cire hannu ya kwada masa mari. Bude baki yayi yana neman hada kalma ko daya ce ya fada Zayyan ya kara masa wani. Marinsa ya rinka yi hagu da dama kumatunsa ya dauki radadi kamar garwashin wuta a take. Idanunsa a rufe suke da takaicin halin Maikudi. Banda bakincikin da yake ji na muguntar da ya yiwa iyalinsa kuma shine ya kara masa da rashin da'ar da yake yiwa Jume. Mahaifiyar da duk abinda tayi a baya mai kyau ko akasinsa tayi ne domin farincikin 'ya'yanta. Shi fa babu abinda zai dorar game da uwa sai labari. Wane irin farinciki zaiyi da za'a bashi damar kasancewa da tasa uwar ko da na rana daya ne. Shi wanda ya sami damar yana takewa ta hanyar cusa mata bacin rai.


Marin karshe da ya kai masa sai da bakinsa ya fashe. Mairama na ganin haka ta kama hannunsa "ya isa haka Sojana ban sanka da fushi ba, kamata mu koma dakinta"


Rungumo Jume yayi a jikinsa suka bar wurin bayan wani mugun kallo da ya yiwa Maikudin. 


Sawu na daukewa Maikudi ya kwalla kara yana riko matarsa ta zaro idanu a tsorace kada ya huce a kanta "kin ga abinda na gani yanzu? Kema kin ga fatalwar Zayyan?"


"Ni banga kowa ba" tace cikin halin ko in kula sai ma murnar marin da ya sha da take ganin rama mata akayi.


Kansa yaji yayi nauyi yasa hannu ya shafi jinin bakinsa ya tabbatar fa gaske an mare shi din ya fito zuwa dakin Jume. A zaune ya ga Zayyan din yana bata baki akan tayi hakuri da abinda Maikudi yayi mata.


Buguzum buguzum haka ya shiga dakin babu sallama ya sa hannu a kafadar Zayyan don ya tabbatar cewa mutum ne da gaske. Yadda idanun Zayyan din suka yi lokacin da ya dago kansa ya sa Maikudi yin baya da sauri jikinsa na bari.


"Baka mutu ba?"


"Ba haka kaso ba ko? Yadda ka tsara shine na mutu matata ta haifi da ba rai ita da 'yata suyi hatsari su mutu su ma kaci dukiyar da zata zame maka wuta ranar lahira"


Da borin kunyarsa ya kalli Mairama "sannu munaf...."


"MAIKUDI!!!" Zayyan ya daka masa tsawar da hatta Mairama sai da ta razana. Da dan allinsa ya nuna shi yana kada masa shi a gaban fuska "ko da wasa kada ka sake yunkurin yiwa matata magana balle kuma ka hadata da kalamai na batanci. Kai ba ita da Jume ba wani ma a gidan idan ya sake kuka da kai wallahi sai kayi mamakina. Abu na karshe daga yau har na bar gidannan kada ka bari ko inuwarka ce na sake ganin gilmawarta a gabana. Get out"


"Ni da gidan ubana kai ka isa kayi min turanci. Ba tsoronka nake ji ba" yace daga bakin kofa yana sauri kada Zayyan din ya biyo shi. Babu wanda ya sake saka shi a lissafi. Jume duk yadda yaso hanata da kanta tayi masa tuwon alkama da miyar karkashi akan wutar murhu. Zaman hira kuwa an raba dare ne ana bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa shima kuma ya fada musu nasa.


**********


Numfarfashi kawai Malamijo yake saki yana daga kwance a dakinsa ko zama baya iyawa sai an tada shi. Ga mutane cikin 'ya'yansa da jikoki ana ta yi masa sannu. Sallamar Nene Marka tare da Radhiya su ka shigo dakin. Ba arziki ya tashi yana nuna Radhiya.


Ba don kada a raina shi ba kuka zaiyi ko yaji sassauci a ransa "Wai da gaske so kike ki karasa ni ne? Dame kike so naji? Shanuna, shanuna shegen yaron nan Talle ya gudu dasu sannan kin kawo Marka wato tazo in biya musu kudin Hajji da yawun bakina ko"


Murmushi Radhiya tayi har ranta tana tausayinsa tace "duba ka tazo yi...ku taso mu basu wuri ko" Tace da su Emzee. Murmushi yayi yayar tasa ta fara daukan haske ta gane inda ya kamata ta rinka tashi musamman idan manya ne zasuyi magana. Nene Marka ma ta kalli bayanta har ta saki labulen da suka gama fita tayi dan murmushi. Radhiya fa tana da hankali idan aka tabota ne kawai bata da dadi. Daure fuska tayi lokaci guda tana kallon yayanta.


"Ali" tace da kaushin murya.


"Alin ma kai tsaye Marka, wato tunda na soma talaucewa an sace min shanu ga kaji ance suna murar tsuntsaye shine dan girman da kike bani ya kau. Kada ki manta dai sunan Malam ne kakanmu ehe. Idan kin kirani Ali kamar kin kira sunan Malam ne babu kara"


"Kaga dakata min ba wannan ya kawoni ba. Zumunci nazo yi zan duba ka nayi maka nasiha ta karshe don babu lallai na cigaba da hakurin zuwa gidanka"


Jikinsa ne yayi sanyi kuma. Gidansu ita kadai ce mai hakurin zumunci dashi sauran har wadanda ya hada uwa dasu sai abu ya kure suke zuwa. Ita kuwa 'yan dakinsu har gori suke yi mata wai tasa kwadayin abin hannunsa a rai shiyasa take like masa. Gashi dai shine babba amma sai aci a cinye a gidajen sauran babu shi babu 'ya'yansa saboda kawai kada ace yayi gudunmawa.


"Yanzu kuma me nayi?"


"Meye ma baka yi ba? Dubi yadda ka koma sai mokadewa kake yi kamar ragowar yunwa. Ni dinnan da bana takama da komai sai dan rufin asirin da Allah Ya yiwa mijina, ba da ba jika na fika kyaun gani da cika ido"


"Ku mata dama banda ci me kuka iya?"


Gyara zama tayi bata sake magana ba har yarinyar da ta kawo mata ruwa ta fita sannan ta cigaba "Malamijo wallahi ka guji haduwarka da Allah akan yadda kake rayuwa"


"To, tohhh zaki fara ko. Idan kina abu sai kace kin saki nono ne Hajjo ta kama. Kuyi ta zakulowa mutane laifuka kawai don a rubuta min zunubi to dai kowa mugun fatanta a kanta zai kare"


Girgiza kai tayi cike da takaici "kaga irin halin naka...ni ka saurareni don banzo da shirin kwana ba." Sassauta murya tayi ta kafe shi da ido don yasan zancen nata babu wasa a ciki.


"Malamijo ina tsammanin ko rantsuwa zanyi babu kaffara a kaina cewa duk garin nan babu mai arzikinka. Tunda Baffanmu ya raba mana shanu tun yana raye ba'a shekara biyu ba naka suka ninka abinda ya bamu. Ni ko wuka aka saka min a wuya bana ce ga abinda na tsinana da nawa ba. Amma kai kam ka sami albarkar kiwo. Nafi shekara arba'in a gidan miji ban taba batan wata ba sai gashi kai da kayi naka bayan ni yanzu a lissafina mutum talatin da daya ne naka masu rai banda biyar da suka rasu da masu bari"


"Hakkun" ya gyada kai maganar ta soma samun shigarsa.


"Wadannan 'ya'ya amanar Allah ne kuma kai dai kaci wannan amana. Ko kadan baka rikesu yadda musulunci ya tanada ba. Rashin wadatasu da abincin kirki ba shi yafi damuna ba kamar sakaci da zumuncinsu. Yawansu na banza ne saboda babu wanda ya damu da dan uwansa. Ka ga duk iskancin Salame....."


"Kyale wannan mara mutumcin ko ni kaza ta fini mutumci a idanunta"


"Kaga matsalar ai kayi ta aibatasu. Salame ko tana da mugun hali da sa hannunka a kara lalacewarta. Duk yadda duniya take wasan gare gare da ita a gidan miji bai sa tayi hankali ba har yau. Yadda ka banzatar dasu haka ta fita harkar Halifa da Rahima. Albarkacin kudin uban Halifa yanzu take jansa. Amma Rahima fa?"


Langabe kai yayi "ko a waje muka hadu bazan shaidata ba wannan"


"Shikenan so kake idan kasa ta rufe idanunka sun gama zumunci kenan sai a lahira idan an hadu a filin hisabi?"


"Kai Markajo ni dai fadi me kike so nayi duk kinbi kin tsorata ni. Kina kallo ba lafiya gareni ba."


"Ka hada kan zuri'arka. Kafin ka bar duniya ka dinke barakar dake tsakaninsu. Banda Mairama da Ayuba babu wanda yake nuna damuwarsa a kanka. Abu na biyu yau ka gani da kaki sharar masallaci ai kayi ta kasuwa. Wata can da bata da gadonka ta kwaso iyalinta suka tagayyara ka sai jikoki suka kwaceka. Da gidan nan a hade yake wadancan zaratan samain yaran naka ba ubanta zasu ci ba ta koma inda ta fito daren da ta tare. Wai ma shin auren bai isheka ba. Kayi lukuta, siririya, fara da baka, mai kyau da mummuna. Babu kalar da baka taba ajiyewa ba amma kaine har yau aure kake"


Jikin Malamijo yayi mugun sanyi domin kuwa ya soma ganin ishara. Marka ce kadai ya tabbatar zata fada masa gaskiya batare da sanya son zuciya ba. Ko Radhiya sai da ta hado da cewa a kai wasu hajji sai kace zuwa Zaria ne abin. 


"Nagode Marka kuma sha Allahu kafin ki tafi zaki ga sauyi. Taron hadin kai zanyi a gidan nan Mairama tana dawowa daga Nijar"


Sai yanzu tayi murmushi "ya dai kamata, ai Radhiya ta fada min dawowar baban nasu da alkawarin zasu zo min."


Hirar zumunci suka yi sosai tana ta bashi shawarwari. Rokonta yayi ta taimaka taje masa bikon Hajjo kafin ya shawo kan Yadikko.


"Wani hanzari ba gudu ba Malamijo" Nene Marka tace kafin ta tashi "ka kira Salame kayi mata jan ido irin na uba mahaifi wanda ya isa da gidansa . Ita ce fa babba a gidan nan"


"Ina jin fa kanta ya kwance wannan. Jiya ta bani mamaki wai sai gata. Nayi zaton dubiya tazo yarinyar nan sai cewa tayi wai tayi magana da wani Malami suna tantamar ingancin auren Mairama da Zayyan. Wai yace mata shekara hudun farko da basa tare matsayin saki daya ne, ta biyi kuma saki biyu ta uku saki uku. A takaice dai wai na rabasu a barshi ya nemi wata itama ta sami daidai ita. Ni dai kaina daurewa yayi sosai nace Salame ko ta fara hauka ne"


Nene Marka bata taba niyar fallasa maganar son da Salame take yiwa Zayyan ba amma jin wannan magana ranta in yayi dubu to ya baci. Da za ta ga Salame yanzu wallahi sai ta mareta. Nan take ta warwarewa Malamijo wannan batu da kuma kakkarfan zargin da take na cewa ita ta makanta kanwarta Mairama tsahon shekaru goma saboda ta auri Alh Indararo.


A kidime ya tashi zaune sosai "Kin gane min 'yar jakar uba"


"Shiyasa nace ka hade min kan yaran nan"


Kan Emzee wata irin sarawa yayi da jin wannan mummunan labari. Kawunsa Ayuba ne yazo da abokansa malamai shine ya turo shi yi musu iso wurin Malamijo kafin ya gama yiwa tagwayen kannensa addu'a.


Kai tsaye Emzee ya shiga dakin cikin bacin ran

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment