Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace tana fiddo plates.


"Inzo inyi miki wanka sai mu ci?" Yace yana murmushi.


"Na yafe please ka zo kaci kafin nayi wanka"


Hannunsa ta kama ta ja masa kujera ya zauna sannan ta ce ya ci ta shige dakin. Murfin ya bude saboda kamshin da ya cika masa hanci. Kaza ta gasa tayi golden brown irin gashin larabawa ta zagayeta da hadin salad wanda ta kawata da kayan lambu daban daban ga chips a gefe daya. Rufewa yayi bazai iya ci ba bata nan.


Wankan yau na daban ne komai has to be extra special yadda Hammanta zaiyi ta tunaninta idan ya koma. Mimi skirt ta saka da wata top mai hannu three quarter ta bata lokaci tayi kwalliya ta gyara gashinta sannan ta fito tana kwas kwas da wani heel shoe dinta.


A tsakiyar falon Awwab ya tarota ta bata rai ganin bai ci ba. Kunnuwansa ya kama da hannu.


"So nayi ka fara cin abincin sai nayi presenting maka sabuwar member ta Awwab crew" ta kashe masa ido.


"Fully employed with all benefits baby...mu ci abincin nan kafin hankalina ya barshi gabadaya"


Daga cin abinci aka kwana ana sallama da kyar ya samu tayi bacci saboda kuka. Kuma da kukan ta tashi ta kasa sakin rai karshe yace ba zata bishi airport ba tunda haka ne. Sai da ta ga da gaske yake idan bata yi shiru ba bazai yarda ta bishi ba ta goge hawayen amma kana ganinta kasan kukan take yi a boye.


Da suka je yiwa su Mami da Mama sallama gabadaya tausayinta su ka rinka ji saboda fuskarta tayi ja alamun tayi kuka ta gode Allah. Ita da shi suna bayan mota sai dreba su ka tafi yana aikin rarrashi da kwantar mata da hankali. Da su ka dawo gidanta ta shige ta rushe da kuka ko abinci ta kasa ci a haka tayi bacci Zayyana tana dayan dakin za ta rinka tayata kwana.


Sai bayan kwana biyu ta saki ranta Awwab yana shan rigima da koke koke a waya dai. Shima dauriya yake yi tare da karfafa mata gwiwa. Kwanansa takwas da tafiya Daddy ya gama yi mata shirin tafiya Nijar ta karasa aikinta. Katsina suka tafi tare da Mami aka bar Zayyana da Rahima gidan Ummi. Kwanansu biyu ya hadata da 'yar kanwarsa matashiya da su ke kusan sa'anni Na'ima saboda kada tayi tafiya daga ita sai dreba da daracta Bigman da cameraman.


A can Nijar da connection din kakanni da iyaye aka samu aka hadata da wadanda ya dace cikin sauki tayi aikin sati biyu ta gama hada komai. Lokacin sati hudu ya rage mata ta koma France amma Awwab yace ko zai kara lokaci lallai ta jira shi yazo ya maidata.















 
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: A Katsina su ka sauka Mami da Daddy su na nan amma bangarensu take zama saboda nauyinsu da take ji ga rashin 'yan hira. Gidan Fauziyya take wuni ko ita tazo. Cikinta ya fito ga Jawad ya kara wayo.


Sun zaga gidajen 'yan uwa saboda jan magana na Fauziyya ta kaita gidan Ghazalatu. Nura yana gida su ka zo ya rinka makalewa a jikin matarsa ba ta da damar motsi yana biye da ita. Duk haushi ya isheta wannan aure babu ranar rabuwa ta sake samun wani cikin. Ta kwantar da hankalinta amma rashin kunyarsa tana damunta. Duk wayewarta ta baya Nura kwararren dan duniya ne amma dai ya canja hali tunda yanzu da gaske son matarsa yake yi. Kadaran kadahan ta karbesu aka rabu lafiya.


Emzee yana nan yana takurawa Rahima da text idan ta ga dama tayi masa takaitacciyar amsa guda daya tace lafiya. Wannan abu yana damunsa amma ya san shi da fita daga makarantar nan da kyar idan ba sai ya gama ba. Jan ajin nata wani burge shi yake yi ma amma yaki yarda ya kirata a waya.


Cikin Ummi ma ya fito tana fama da karatu ga laulayi yaki sauki indai tana gida a kwance take. Yanzu an cigaba ta bangaren Salame tana yawan kiranta su gaisa.


Kwana hudu kafin dawowar Awwab saura kuma sati Radhiya ta koma makaranta Mama ta sa a gyara mata 'ya. Gyaran jiki na musamman aka yi mata tana ta saka lalle a kasan gashinta saboda sanin da tayi yana son hakan. Tun dare take jin cikinta a daure da safe ma daurewa kawai tayi tana girki Zayyana tana shara yau bata da lecture. Suna cikin yin breakfast ta ji ciwon cikin ya karu da kyar ta iya tashi tsaye ta ce "Zayyana kirawo min Mami cikina..."


Sai da ta taimaka mata ta kwanta akan doguwar kujera sannan ta fita da hanzari. Ko sallama bata yi ba ta fada gidan Daddy na tambayarta me ya sameta tace Adda Radhiya ke ciwon ciki. Cikin sauri Mami ta fito tana tunanin ko ciki ne da ita.


Nishi take a wahale Mami ta taimaka mata ta tashi "Zayyana dauko mata hijab ko mayafi mu tafi asibiti"


An gama saka mata hijabin jiri na kwasarta ta daga kafa Mami na rike da ita jini ya biyo kafafunta. Basu kula ba sai da ta daga daya kafar tare da zubewa a jikin Mami saboda wani matsanancin ciwo da bata taba jin irinsa ba da ya dirar mata lokaci guda da fitar gudan jini. Tana jin Mamin a rikice tana cewa Zayyana ta fadawa Mama da Daddy daga nan ciwo yaci karfinta jikinta ya saki.


Asibitin da suke zuwa na Sami Wadata su ka je jinin yaki tsayawa har lokacin aka shigar da ita emergency. Sai bayan minti talatin aka gangarota zuwa wani dakin likitan yace saidai suyi hakuri bari tayi kuma saboda yadda take zubar da jini sai da suka yi mata wankin ciki. Mami harda hawayenta saboda tausayi Radhiya tayi fayau da ita. Mama ce ta sanar da Ummi itama hankalinta ya tashi ta fadawa Daada shi kam nasa yafi na kowa ma. A asibitin su ka wuni har ta tashi daga bacci. 


"Mami cikina zafi" tace tana runtse idanu.


"Sannu kinji Radhiya zai dena in sha Allahu. Bari na hada miki tea ki sha"


So take ta tambayesu me ya sameta amma ganin iyayenta maza sai taji jikinta yayi sanyi a hankali take share kwalla duk da bata san me ya faru ba. Ta riko hannun Zayyana ta ce "me ya sameni ne?" 


Zayyana sai ta fashe da kuka Mama ta fara fadan za ta daga mata hankali. A tausashe ta dafa kafadar Radhiyan ta soma magana.


"Radhiya bari kika yi"


Gabanta ne ya fadi ta tuna cewa kwanaki sun shude da tayi missing period dinta tunda Awwab ya tafi shine ta siyo PT strip take ajiyarsa sai ya dawo su duba tare. Ashe ma ba mai zama bane. Iyakar daurewa ko don kada ta bawa Umminta kunya ta tattaro tayi da abin ya ci tura kukan ya matsota sai ta juya musu baya. Kowa na ganin yadda jikinta yake rawa alamun tana kuka Mami tace su fita a barta ta ji saukin zuciyarta saboda cikin fari akwai shiga rai. Kukanta tayi mai isarta bayan sun fita. Ta saka rai da cikin sosai saboda yadda Awwab bashi da aiki sai kwadaita mata haihuwa da irin son da yake yi ya ga 'ya'yansu.


A waje Daddy yace yaji shiru Awwab bai kira ba ga matarsa a kwance. Daada yace kada su fada masa tunda dai zai dawo nan kusa. Kuma bai kamata a tayar masa da hankali ba duba da yanayin aikinsa rayukan jama'a a wuyansa.


Shadayan daren Nigeria Awwab yayi landing jirgi a Canada. Kamar kullum yana isa masaukinsu ya kira Daddy da Mami sannan Radhiya. Yayi ta waya shiru ta na shiga ba'a dauka an manta ta a gidan. Mami ce za ta kwana da ita kuma ta riga ta yi bacci sai ya nemi Zayyana taki dauka saboda bata san me za ta ce masa ba. Lokaci ya duba ya san dare yayi amma Radhiya ta rike schedule dinsa sosai na satin ta san lokacin tashin jirginsa da sauka wani zubin kafin ya kira ta neme shi. Komai dare a Nigeria sai ta jira shi duk fadan da zaiyi ba ta ji.


Washegari da asuba yayi ta kira shiru ya kuma kiran Zayyana tace masa bacci take yi. Ya dai ji ne bai yarda ba . Mami ya kira da gari ya waye ya kusa tashi yace mata ya kasa samun Radhiya jikinsa na bashi babu lafiya kuma Zayyana na yi masa wasa da hankali. Hakuri ta bashi tace da kanta za ta kaiwa Radhiyan wayarta ce ta fadi. Shiru lokacin boarding yayi ya sake tashi back to Germany cike da damuwar da ake guje masa. Sai daren ranar aka kai mata wayar yana sauka ya kuma kira. Fada yayi niyar yi mata saboda ko faduwa wayarta tayi ya bar mata kudi da za ta iya sayen wata sannan ga wayoyinsu Mami. Amma yana jin weak voice dinta ya ajiye makaman yakin. Karyar mura tayi masa ya bi ta da toh ba don ya yarda ba.


Da yamma ranar aka sallameta Mami ta hanata komawa nata gidan tana kulawa da ita sosai. Karamin wankan jego ta yi mata ta rinka gasa mata jiki ga abinci mai gina jiki ita da Mama su yi Ummi da Rahima sai dai su zo dubiya.


Ranar da Awwab zai dawo taji karfin jikinta sosai tayi masa abinci. Naman sa ta yiwa yanka madaidaita ta tafasa da kayan kamshi su, citta, tafarnuwa, black pepper da albasa. Ruwan naman bayan ta tafasa shinkafa ta wanke ta juye shi ta karasa dafata da shi. Butter ta zuba a non-stick pan mai zurfi ta soya sausage da lawashi wanda ta yanka kananu juye shinkafar a kai batare da ta saka curry ba ta soyata. Naman shima soya shi tayi sannan ta hada attaruhu da albasa wadatacciya tayi grating ta soyasu da maggi da

 curry sannan ta hade da soyayyan naman. Sai kuma coleslaw da kunun aya. Gidan ya sha turaren wuta ga girkin amarya da sanyin AC Ba ta je airport din ba ta zauna kwalliya.


Motar na tsayawa a gurguje taje ya gaishe da iyayensa da su Baba Hadir ya tashi Mama tana zolayarsa bai iya cewa komai ba sai dariya ya taho gida. Yana kama handle din kofar kafin ya murda ta riga shi. Kallon kallo su ka tsaya yiwa juna shi ya kara yi mata kyau da cika. Awwab na yi mata kallon fuskarta ta fada duk da kyaun da tayi mai fizgarsa. Rungumeta yayi tun a bakin kofa ya saki jakarsa yana kissing dinta cike da kewa. A hannu ya shige daki da ita sai da ta ga da gaske yake ta dakatar dashi saboda jininta da bai dauke ba. Bai damu ba ya rungumeta kawai a jikinsa yana fada mata yadda yayi kewarta. 


"Tashi kayi wanka kaci abinci Hammana" ta ja hancinsa.


Wasa yake da gashinta ya dago ta su ka zauna "babu ko daya da zanyi sai kin fada min abinda ake boye min baby. Me ya sameki 4 days ago?"


Babu hanyar guduwa ta sunkuyar da kai ta ce "Hammana miscarriage nayi"


Jikinsa a take ya soma rawa ya janyota ya kankame "Schatzi dama kina da ciki?"


Kuka ta saka a hankali "Ban tabbatar ba shine na siyo abin PT idan ka dawo mu duba"


Ya dago fuskarta yana kallo "was it painful?"


Ta gyada kai ya sake rungumeta yana bata hakuri da rashinsa a kusa lokaci irin wannan. Sabuwar jinya aka koma yi kamar yau abin ya faru ya hanata yin komai. Iya kwana ukun da suka yi kulawa yake bata sosai. Ranar juma'a da daddare su ka tashi zuwa France inda ya cinye hutunsa ita kuma tana zuwa makatanta amma da ta dawo sai yawo tare da su Arifa ko ita kadai da Awwab. Ranar da zai tafi kuka tayi da kyar Tante ta shawo kanta.


**********


A hankali kwanaki ke tafiya cikin Ummi ya shiga watan haihuwa ga jarabawarsu ta karshe da suke yi. Lokacin Fauziyya ta kusa arba'in din Sahla jaririyarta. Zahra kuma cikinta yana wata biyar.


Cikin ikon Allah sai bayan kwana takwas da gamawa ta tashi da nakuda. Allah Ya taimaketa yadda ta sha wahalar cikin sai haihuwar ta zo mata cikin sauki saboda ko minti talatin basuyi ba da zuwa asibiti aka fito musu da sankacecen saurayi kamar Radhiya tayi kakinsa har dimple din gefe dayan. 


Farincikin Zayyan Tureta a wannan rana ba zai fadu ba. Mairama ta sha addu'a sosai a wurinsa sai da tayi kuka. Ya kira Malamijo yace a yiwa shanu uku kudi a garkensa a yanka ayiwa mabukata sadaka. Mami ce ta yi mata wanka saboda a ganinta duk girman Mairama bata da wani cikakken experience game da haihuwa. Mama kuma ta sille jariri aka yi masa hoto ana turawa yayyensa da ke nesa. Radhiya ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta iso gida wurin baby da Ummi amma tana da sauran jarabawa daya sati mai zuwa. Ita da Tante da Arifah mai tsohon ciki suke zuwa siyayyar kayan baby saboda su Mammee sun ce ta hado kayan barka na gani da fada. Akwati biyar tayi manya manya uku na baby biyu na maijego.


Emzee da Ibrahim su ma makaranta ta sarke musu wuya ana ta jarabawa. Su Fauziyya ke rokon alfarmar kada ayi suna babu su Ummi ta ce babu taron da zata yi. Mama da Mami su ka ce sai anyi. A zahiri Ummi bata son yi saboda rashin Radhiya da Emzee amma kunya ba zata bari ta fada ba. Ita dai burinta ace 'ya'yan da suka sha gwagwarmaya tare dasu za'ayi komai.a lokacin da Allah SWT Ya dube su. Shima uban gayyar mijin nata kasa fada masa tayi sai da hillata ya ganota.


"Su Fillo wasa wasa kina da son 'ya'ya fa" yace yana dora jaririn a kafadarsa.


Tayi dariya "Duk abuna na kai dan mutan Tureta ne?" 


"Ko kusa a bayana kike saboda haka ki rinka komawa gefe idan suna kusa ba ta ke nake yi ba"


"Naji amma ka bani jaririna don kasan shi dai bana jin kunyarsa kamar sauran"


Zama yayi kusa da ita ya ce "na rasa sunan da zan saka masa Fillo. Ga Major, Hadir da Baban Arifah cikinsu waye baiyi min halacci ba? Kinga ko da Hadir yake mai lalura nayi imanin da yana da hali kamarsu Mairama zai iya sadaukar da komai nasa domin iyalina."


"Na sani Sojana ko dai na haifo wasu ne a cike sunayen" ta ce tana dariya.


Ranar kwana hudu kenan da haihuwa nauyin 'yan uwan nasa rabin jiki yana damunsa ya rasa wa zaiyiwa takwara a cikinsu.


Washegari da aka kawo Mami tare da Daddy da Baba Hadir su ka zo. Daddy ya mika hannu ya karbi kyakyawan jaririn daga hannun Zayyan ya mikawa Hadir.


"Ni na yiwa Alheran yau kuma kaine da danka ka zaba masa suna don na rasa me yake damun abokinka sai wasa yake mana da hankali"


Murmushi Baba Hadir yayi ya duka ya yiwa yaron addu'a sannan ya dago kai yace "Allah Ya raya mana NASURULLAH"


Daddy yayi murmushi ya karbi yaron ya sumbace shi kumatun hagu da dama "hakika Allah mai kyauta da kari cikin nasarar da Ya bamu ne muka wayi gari mu ka ga wannan rana ace Zayyan ya dawo garemu har Allah Ya azurta shi da sake samun karuwa."


Kwalla ce ta taru a gefen idon Zayyan ya sa hannu yana kade ta Daddy yace "me nake gani haka? Are you still a Lady?"


Baba Hadir da Zayyan sai dariya yana cewa "wallahi namiji ne ranka ya dade"


Excellency Nasiruddeen Aliyu wanda ya sake samun kujerar gwamnan Plateau a daren ranar ya sauka a Abuja ganin wannan dan baiwa da za'a iya cewa alkawarin Allah Ya cika domin haihuwarsa baiwa ce. Sunansa da na Nasrullah daya ne duka daga nasara sai dai bambanci kadan shiyasa yace shi aka karrama aka yiwa takwara saboda haka gagarumar kyauta yayi masa wadda ta tsorata iyayensa sai dai yace babu abinda zai yiwa jinin Zayyan ya fadi domin ko me ya zama a rayuwa sanadiyar zubar jini da hawayen Tureta ne. 


Kamar lokacin DK dan gidan Zayyan don babu abinda ya kware a fada irin Daada shima Nasrullah an dage taron sunansa sai yayyensa sun dawo nan da sati biyu ake sa ran kowa yana gida banda Zahra.


Tante ta tafi Nijar da kwana biyu Radhiya ta koma gidan Yousuf jiran Awwab yazo zasu tafi Abuja. Kafin.ya iso yayi booking hotel online daga airport ya gudu da matarsa sai washegari su ka hadu dasu Arifah a wurin convocation din Radhiyan. Kyaututtukan da ta samu ba kadan ba musamman saboda shirin Military Voice. An yaba mata sosai basu bar makarantar ba sai da a gaban shugaban makarantar tasu da Awwab ma'aikatan Aljazeera su ka kawo contract na shekara hudu wanda su ka bata tayi Military Voice Africa (MVA). Da amincewarta kuma anyi alkawarin acknowledging dinta a matsayin wadda ta samar da shirin suka nemi izinin yin Military Voice Asia da Europe. Kudin da zasu biyata ba na wasa bane bukatarsu duka kasashen Africa guda 53 taje ta gana da sojojinsu da matansu su kuma zasu ware lokaci domin sanya shirin sau daya a sati. Yadda za'a rinka dauka da gabatarwa duk yana cikin contract din. Awwab baiyi gaban kansa ba ya kira Daddy da Daada suka bashi goyon baya sannan ya yarda ta amince aka saka sunansa a matsayin wakilinta. 


Kwana biyu su ka kara sai gida Nigeria da kwalinta na degree wanda ta fito da sakamako mai kyau. Iyaye da 'yan uwa an tayata murna. Da gudu ta shiga gida sai da ta dauki Nasrullah hankalinta ya kwanta. Kasa ta sauko dashi wurin Awwab ya rungumeta da babyn yana cewa Allah Ya nuna masa ranar da za ta haifa musu nasu. 


**********


Shirye shiryen zuwa P.O.P din Emzee suke yi Daada yace Ummi babu inda zata saboda Nasrullah baiyi kwari ba. Sai da ta ajiye kunya ta dangana da hadashi da Daddy ya barta taje.


As expected Second Lieutenant Muhammad Zayyan Tureta ya fita da sakamako mafi kyau a wannan shekarar saboda kokari da kwazonsa musamman akan abinda ya shafi training dinsu. Ya sami lambar yabo kala kala iyayensa basu da abin cewa sai godiya ga Allah. A wannan rana Malamijo sai da yazo halartar taron sai dai ganin sojoji a kowace kusurwa rike da bindiga ya kada masa hanji. Tare su ka dunguma zuwa Abuja yau dai gashi a muhallin Mairama Daso. Yana rungume da karamin jikansa yana mai mika godiya ga Allah da Ya tsawaita kwanakinsa ya ga haduwar kan 'ya'yansa. Gida MashaAllah ya cika da 'yan uwa daga rugar Barkindo, Sakkwato, Nijar da Sumaila.


Sunan da ba'ayi ba aka hade da murnar kammala karatun Radhiya, Emzee, uwar gayya Mairama da bakon duniya Nasrullah. Major General Zayyan Tureta sai da yayi kukan farinciki a daki kafin ya sauko faefajiyar gidan inda ake taron. Yau shine Allah Ya yiwa arzikin ganin wannan rana wadda da sai dai ayi babu shi. Kyauttuka kam an sha su.


Ibrahim kamar ya lashe Zayyana don so shi kuwa Emzee da Rahima tsakaninsu sai satar kallon juna. Ta gama makaranta abinta tana jiran a fara karatu a school of nursing da ta sami gurbi. Emzee ya mamayeta yadda Awwab yace duk motsinta yana wurin amma babu yiwa juna magana. Ita ta sakawa ranta ta hakura dashi ne duk da tasan cewa yaudar zuciyarta take yi. Kullum sai ta jira text dinsa wanda babu kalmar soyayya sai nuna tarin kulawa.


Sai dare su Radhiya suka koma gida Awwab ya jikata da salon soyayyarsa. Washegari ya damka mata mukullin hadaddiyar motar da ya saya mata a matsayin graduation gift.


*********

SALLAMAR BANKWANA


Wata hudu bayan gama karatun Radhiya suka je gidan Daada da Awwab gaishesu. Emzee ya tafi wani training a Warri yanzu mukaminsa ya koma Lieutenant. A falo su ka yada zango tana yiwa Nasrullah uban 'yan kyuya wasa ya hade rai abinsa yana neman Ummi da idanu ta ce,


"Indai nice za ka zo ka sameni ne har gida kuma ba bari zanyi ka shigo ba"


"Ba dole ya rinka gudunki ba kina zare masa idanu" cewar Awwab ya karbe shi.


Kusa da Daada ta koma suna hira a hankali ta soma hade fuska tana sansana jikin kujera da su labule tana dagawa.


"Lafiya dai kike min dage dage?" Cewar Ummi.


Sake baza hanci tayi da kyau tace "Ummi warin magani ko dai maganin Nasr ne ya zube a wani wuri?"


Daada na jin haka ya ajiye jaridar hannunsa yana kallonta "maganin kamar panadol yake Alheran?"


Ta tafa hannu "eh wallahi Daada ka canka..."


Ummi ya kalla ya soma dariya yana cewa "kina ji kamar ma ya rube ne?"


Awwab ne ya bashi amsa "jiya sai da tasa na na juya gado da shirin falo gabadaya muna neman maganin da ya rube. Kuma ni bana jin komai wallahi ita kadai take ji"


Dariya sosai Daada yake yi Ummi ta bar wurin da sauri don kunya tana ji yana cewa "wannan warin bazaka taba jinsa ba Awwab. Ke kuma sai hakuri yanzu kika fara ji amma ku je asibiti kiyi musu complain. Ina jin likita kika hadiya"


Ta zaro ido "likita kuma Daada?"


Ummi na jinsu ta dawo da sauri saboda ba karamin aikin Zayyan bane sakin baki a gaban suruki shiyasa tace yazo wayarsa na ringing. Ita kadai ta dawo daga baya suka yi sallama Awwab ya wuce asibiti da ita duk da tana cewa babu inda yake maga ciwo sai warin maganin. Gwajin ciki suka yi mata tana dashi har na sati tara.


Murna a wurin Awwab ba sai an fada ba. Auren nasu shekara guda da watanni kadan ga Arifah tana nan da Nasrin dinta wadda sunan Tante taci aka juya mata shi. 


Tare suke kula da cikin yana ta girma har yayi wata bakwai. Laulayi gareta kamar Ummi shiyasa idan zai koma aiki sai dai Zayyana ta dawo gidan ko Rahima.


Ranar wata asabar tafiya ta kama Daada zuwa Asaba aiki shi da wasu a karkashin jagorancinsa. Convoy din motoci biyar suka yi ciki Emzee da yake ta fushin kasa samun kan Rahima yace zai raka shi. Basu taba tafiya daga shi sai dan nasa ba saboda haka wannan ta basu damar yin hira sosai irin ta uba da da. Zayyan yasan komai game da lamarin Rahima ya rinka bashi shawarar yadda zaiyi ya shawo kanta su daidaita.


Sun wuce wani kauye da kadan su ka kula motoci da yawa suna dawowa a guje wasu ma da ribas suke tafiya. Nan da nan yaransa su ka fara kiransa suna tambayarsa ko su ma su juya.


"Are you crazy?" Ya dakawa mai tambayar tsawa "civilians su gudu muma mu gudu to waye zai kai taimako idan ana bukararsa"


Kai tsaye ya bada umarnanin kada a tsaya. Kowa yana sanye da kayan sojoji tunda official tafiya ce banda Emzee dan rakiya. Suna karasowa motoci suka gani guda shida da 'yan fashi su ka kama sun kashe titin ta daya bangaren babu mai karasowa ga harbi suna yi kamar hauka sun kashe drebobi uku masu kokarin guduwa. Ganin motocin sojoji ga su suna dirowa da shirinsu yasa ogansu kiran wadansu ashe mugun yawa garesu. 


Tashin hankali ne muraran mutanen da suka biyo hanyar suka tsinci kawunansu a ciki. Baka jin komai sai tashin harsashi da kukan mutane. Abin ya wuce zatonsu dan karamin kauyen da yake gefen wurin shima sun yiwa mutanensa mummunar barna saboda rashin basu mafaka. 


Jikin Emzee a take ya fara rawa yau gashi a filin daga na gaske. Major General Zayyan tuni ya fito daga mota a sukwane babu wani tsoro ko fargaba  yana bada umarnin duk wanda su ka kama zaiyi gardama su harbe shi a inda zai raunata shi sannan su tabbatar anyi saving mutanen wurin.


Bindiga kirar AK47 ya dauko ya damki hannun Emzee ya bashi cikin rawar hannu ya saketa a kasa ga sautin harbi da kukan mata daga wannan kauye ya yawaita.


Dauko bindigar Zayyan yayi ya ratayata a hannunsa kamar yadda ya rataya wadda zaiyi amfani da ita ya rike fuskar Emzee a tafukan hannunsa.


"MUHAMMAD" ya kira shi da murya ta umarni babu wasa ko rangwame saboda dan cikinsa ne "this is why you became a soldier Lieutenant. You live and die for your country. Wancan kukan da akeyi da firgici aikinka ne ka tsayar dashi ka tseratar da mutanen nan"


Jiki na rawa ya gyada kai yana jin kunnuwansa na neman toshewa saboda bala'i. 


Bindigar Zayyan ya sake mika masa yana jin wani karfin gwiwa su ka fara hawa dan tudun da zai karasa dasu kauyen Zayyan yana ta bada umarnin a kwashe tseratar da mutanen da aka kamawa motoci

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment