Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai dai kafin ta fita jikinta ya soma rawa likitan da yafi kusa da ita yayi saurin karbe jaririn ta fara neman faduwa tana wata irin jijjiga ga jini ya balle mata. 


Nos da daya likitan ne suka kamata aka dora akan gado suna neman ceto rayuwarta.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Kwana biyu da rabin wuni Mairama tayi kafin ta gane inda take da babbar jarabawar da ta tunkaro rayuwarta. Ta farfado da misalin uku na rana washegarin ranar da ta haihu. Idanunta a rufe suke amma tana iya jiyo maganganu kamar ana fada. A hankali ta fara fuskantar me ake cewa wanda yayi sanadin fitowar hawaye daga idanunta, kuma har lokacin a rufe suke.


"Ni dai na fada miki gobe zan tura Rayyanu yaje garinsu ya sanar da iyayenta su zo su dauketa don bazan iya jigila ba."


"Haba Maikudi kai kuwa baka ganin ga danyen jego ga rashin lafiya. A barta ta huta mana"


Gwaggo Ladi da tayi maganar ya kalla darajar mijinta Mal Aminu ya kasa bata amsar da yayi niyya. Wani dan tunani yayi ya kara tabbatarwa gara yabi komai a hankali don samun biyan bukata.


"To naji sai ta zauna har sai ta gama takaba an raba gado. Ince ko hakan yayi" ya mayar da kallonsa ga Mal.Aminu da ya dauke kansa saboda takaicin halin Maikudi. Yaron ya fita zakka tamkar ba jinin Mal Muhammadu ba.


Mal Aminu da ya gama tofe jariri da addu'a ya dago kansa "bana son hauka Maikudi. Takaba dai tana haihuwa ta fita. Sannan tun muna shaida juna kada inji kada in gani, kaf abinda Zayyanu ya bari na matarsa ne da 'ya'yansa tunda yana da da namiji."


A fusace ya juyo "inji uban wa?"


"Inji ubanka"


Mamaki kamar ya kashe shi saboda Jume ce ta bashi wannan amsar. Akan tabarma take tana bawa Radhiya abinci. Daga jiya zuwa yau tayi wuri-wuri da ita. Rasuwar Zayyan ta tabata fiye da zato da tsammaninta. Duk wata mugunta da ta taba yiwa mahaifiyarsa dashi kansa sune suka yi mata dabaibayi. Cikinsu babu wanda ya taba nufinta da sharri gashi sun bar mata duniyar tayi yadda take so. Nadama ce ta gaske take nukurkusar zuciyarta. Ga Maikudu don abin kunya daga jiya zuwa yau banda rashin mutumci babu abinda yake zubawa a dakin. Daure fuska ta sake yi


"Saboda baka san me kake yi ba ace kaninka ya rasu amma ko a jikinka?"


"Kina ji fa aka ce yayi wata guda harda dorin kwanaki, duk dacin mutuwa ai yaci ace tayi sauki an fara fuskantar gaba"


Mairamu ta kasa boye kukan zucin ta koma yi a fili. Ashe har yafi wata da rasuwa bata da masaniya. Shine take ci tasha har tayi wasa da dariya? Ashe Sojanta ya koma ga Allah take ta tunanin dawowarsa. Yanzu shikenan nata mijin saboda soja ne ko kabarinsa babu wani danginsa da zai sani? Anyi masa wankan gawa? An sallace shi? Wace irin mutuwa yayi duk basu sani ba.


Kukanta ya tsananta Gwaggo Ladi ta tashi ta matsa kusa da ita ta tsaya a gefen gadon.


"Mairama hakuri zakiyi da yawaita yi masa addu'a"


Rarrashinta suke ta yi ita da Jume sannan Mal Aminu ya fita saboda ance ta shayar da jaririn.


Maikudi yayi qiqam kamar sanda sai da Jume tace ya fita, yayi waje yana surutai.


Yaron ta karba wanda rabonta dashi tun jiya. Yaji yunwa kuwa sai ruwa aka rinka bashi da tana kwance. 


Gwaggo Ladi tace Malam yayi masa huduba da Muhammad Zayyan. Ina fata hakan yayi miki" 


Hawayen Mairama har fuskar jaririn tayi murmushi "Sojana Allah Ya raya min kai."


**********


"Wai Zayyanu dai Zayyanu soja mijin 'yata Mairama kake nufi?" Malamijo yayi maganar kamar zaiyi kuka.


"Shi nake nufi. Allah Yayi masa rasuwa a kasar da suka je" Rayyanu ya bashi amsa. Shi da Badaru da 'yan uwansu mata kaf mutuwar Zayyan ta shigesu sosai. Mutum mai barkwanci da saurin manta bacin rai. Duk yadda su ke bata masa bai hana shi kyakyawan zumunci dasu ba ko da su bazasu yi masa kallon arziki ba.


Malamijo ya daga hannu ya dora a ka "Laaaaahhhh ha'ila ha ilallahu, kaico Mairama, 'yar marainiyata ta rasa miji kuma"


Lokaci kankani a tsakani zance ya bazu ko ina mijin Mairama ya rasu a filin daga. Mutane suka fara zuwa yiwa Malamiji ta'aziyya yana cewa nan da kwana biyu zai wuce Sakkwato. 


A cikin gidan ma jikinsu duk yayi sanyi. Ba wani haduwa suke yi sosai ba saboda nisan garuruwansu amma duk da haka a iya lokutan da su ka ganshi anyi masa shaidar arziki. Malamijo yasa a dafa abincin sadaka ya saki bakin aljihu abinda basu saba gani ba. Cikin yaransa maza ya tura babban mai bin Mairama a shekaru yaje Balan ya sanar da Nene Marka. Idan zata bisu ta'aziyya ta taho washegari su wuce jibi. Sannan ya tura mai bi masa Kano gidan Salame.


Suna zaune shi da 'yan gaisuwa wani yake tambayar yaya Zayyan din ya rasu don shi ma akwai dan uwansa soja a kudu, yana tsoron a tura shi yaki. Malamijo bai tashi bada amsa ba sai da yaga Rayyanu ya tashi zai zaga ya soma jawabi.


"Hmm ai ba'a cewa komai Haladu. Yaron nan harbi, harbi dai da kake ji da gani a finafinan su Amita Bachan sai da aka sakar masa harsashi kusan goma amma a haka ya rinka kutsa kai cikin abokan gaba yana gamawa dasu. Bawan Allah ya tafi ya barwa Mairama da yaranta komai nasa. Ko sati batayi da haihuwa ba. Shine ma zanje domin na tattaro dukiyar na kawo nan sai na juya mata da kaina saboda duk yadda ka kai da yarda da wani ba kamar naka ba. Nakan ma mahaifi"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Maikudi ne tsaye a ofishin da aka tura shi cikin barikin su Zayyan akan maganar kudi ne dai.


"Jiya Babanku yazo akan zancen nan mun fada masa bamu da komai. Ya bada adireshinsa duk lokacin da kudi yazo zamu nemeku" officer din ya bashi amsa bayan ya gama jero tambayoyi.


Yana hargaginsa na rashin mutumci yace "Ashe cewa yayi shine babanmu don ya ci kudin gado. To wallahi karya yake. Babu wata alaka ta jini tsakaninmu"


Wani sojan ne ya shigo yana tambayar wancan me yake faruwa cikin harshen turanci. Sai da ya sara masa ya bashi amsa da gani ya fishi mukami.


Maikudi yana jin ana bayani duk da bai iya gane duka maganar amma ya dan fahimci me akeyi ya katse wancan "You understant Zayyan Muhammad Tureta is die? Me. Biggggggggg broza. Is me faza dinmu daya ai" ya nuna kansa yana murmushi yana so su fahimci shine babban wan Zayyan.


Mutumin ya hade rai yace a kore shi kuma idan ya kuskura ya sake zuwa ba'a neme shi ba a kulle shi saboda yana mudu hayaniya. Dayan yana soma fassara masa bai tsaya jin karshen ba ya fice yana ta Allah Ya isa an kashe masa kani. A hanyarsa ta komawa ne ya rinka tunanin dole fa akwai abinda Zayyan ya barwa matarsa. Idan ba haka ba da me suke rayuwa duk tsahon lokacin nan? Yafi karfin ita da kwadayayyen babanta suyi masa wayau akan hakkinsa.


Yana zuwa dakin da Malamijo yayi masauki ya shiga. A shirye suke suna jiran dawowar Mairama. 


"Dama nazo akan yaran nan ne Radhiya da Zayyan. Nace ko zaka yiwa Mairama magana idan ta yaye shi zan zo na dawo dasu gabanmu saboda gatansu dai bai wuce wurin dangin mahaifinsu. Idan kun tafi yanzu kai ma nauyi ne kawai zai kara hawa kanka. Sannan bazan zuba ido bane tayi aure 'ya'yana su koma agolanci a gidan wani"


Malamijo an tabo inda yake masa kaikayi kuwa. Ina zai kai karin bakuna uku a gidansa. Gara Mairama yana son abarsa, amma yaran nan da aka ha'ince shi yayi ta yiwa babansu kallon kitse ashe rogo ne "indai wannan ne babu damuwa. Zanyi magana da ita kuma dole ta amince don nima bazan so suyi rayuwar agolanci ba azo ana wulakantasu"


Maikudi ya fita da wani mugun murmushi. Soro ya koma ya zauna jiranta. Ilai kuwa babu jimawa sai gata tana ta sauri kada a gaji da jiranta. Dukawa ta danyi ta gaishe shi ya yafito ta da hannu.


"Yaki zo Mairama. Magana nake son yi da ke"


Kanta a kasa ya fada mata yadda ya fadawa Malamijo. Ai tuni ta saka kuka iya karfinta tana rokansa ya rufa mata asiri ita bata da niyar sake aure.


"Kinga da har mun gama magana da babanki"


Gabanta ne ya fadi. Ta san halin Malamijo kuma tas zai bada yaran nata.


"Don Allah kayi hakuri"


"Naji, amma bazaki bar garin nan ba sai kin fito da dukiyar kanina. Dole ne a raba gadonsa saboda a sauke masa nauyi"


Hannunta yana rawa ta zaro envelop dinnan daga jakarta ya warce gabadaya. Sakar masa tayi kafin ya hada da hannunta.


"Daren jiya na gansu shine nace dama yanzu zan fito dasu ayi abinda ya kamata"


Kankance idanu yayi yana kallonta bayan ya zaro takardun gidan da kuma damin kudi da aka nannade da kyauro "ashe ke mutuniyar banza ce ban sani ba? Wato da guduwa zakiyi da komai saboda tsabar mugunta da bakin hali kamar na tsohonki"


Ta shiga girgiza kai tana hawaye "a'a wallahi"


Wasikarta ta hango ta fadi ta mika hannu ya taketa da sauri da kafa "meye a ciki?"


Hankalinta yayi matukar tashi "wallahi Allah wasika ce ya bar min. Ba takardar komai bace"


Sai ta ga yayi murmushi saboda ya fuskanci yadda ta rude "soyayya manya" yatsansa ya kada mata "kalli nan, zan cire takardun gidan saboda dama ina binsa bashi da bai biya ba. Ina jin gidan ma bazai isa ya biyani ba amma dai su kadai zan dauka. Muje ciki idan munafukan dattijan nan sun zo ki basu kudin a rabawa wanda aka ga damar bawa. Ni kuma nayi miki alkawarin babu wanda ya isa ya rabaki da 'ya'yanki kuma zaki koma Kano da wasikar masoyinki"


Mairama kallon mugunta irin ta Maikudi ta tsaya yi ta rasa shawarar yankewa. A zatonta zaa raba gado a barwa yaranta gidan sai su zauna a ciki. Ita kuma a cikin kudin ta nemi abinyi domin kula dasu. Wani hawaye ke bin kuncinta tana jin zafinsu har zuciyarta "hakan yayi maka?"


Ya dage gira "yayi...ki sani idan kina tunanin juya magana ko Jume tayi kadan tasa na bar miki yaran nan balle kuma wancan tsohon Mal. Aminu. Mahaifinki kuma a yadda na fahimta ko sadakarki na nema zai iya hada min"


Share idanunta tayi tabi bayansa. Kowa yayi zaton kukan tafiya ne take yi da mutuwar mijinta. Su Mal.Aminu sun zo ta dauko kudi ta mika masa. A take aka kira wani malami ya kasafta da aukinsu kuwa aka bata nata aka ware na yaran yace batun bashi fa Mairama tace ya tabbatar mata babu msi binsa komai kafin ya tafi. Maikudi ko tari baiyi ba ganin babu mai gadon nashi sai su kadai. Jume har dadi taji yayi hankali.


Nasiha da ban hakuri aka sake yiwa juna sannan Mal.Aminu ya roki alfarmar kada ta tafi ta yanke zumunci dasu albarkarcin 'ya'ya "mu kuma nan babban kalubale ne a garemu mu da gwamnati. Mu dubi marayun yaran nan da mahaifiyarsu kafin mu ga me Allah Ya tsara musu. Haka ma gwamnatin ta dubi rayuwar sojojin da take takama da sadaukarwarsu. A dubi masu ran wanda suke a bakin aiki, a dubi masu rauni da nakasa sannan a dubi iyalan mamatan domin a gaskiya akwai nakasu mai girma a rayuwar iyalan bayin Allahn nan"

 

Sun fara fitowa mata ana ta kuka Maikudi ya samu ya tarar da Malamijo shi kadai iska tana ta kada yalolon yadin jikinsa yana manne masa ramar tana kara nunawa. Takardun gidan ya nuna masa yana murmushin samun nasara.


"Naga ka kawo idanu ka dora akan dukiyar da baka da alaka da taruwarta shine nace bari dai na nuna maka waye Maikudi."


Ware ido Malamijo yayi ya karewa takardun kallo "na meye?"


"Na gidan Zayyan ne wanda yanzu ya zama nawa. Kana iya kaini kotu don a kwatarwa 'yarka da jikoki hakkinsu amma ka sani kana yin hakan zan rabata da yaran nan ni kuma. Ta fada min akan ta baka dukiyarta gara kowa ya rasa don baka ragawa kowa akan kudi"


Kallon Mairama yayi zuciyarsa tana tafarfasa. Wato Zayyan yana da gida shine ta dauka ta bawa wan mijinta tana tunanin zata dawo masa gida ta jabe ya ciyar dasu. Lallai Mairama bata gama saninsa bane shiyasa har taje tana tona masa asiri. Har shi zata ha'inta yana mahaifinta. Kwafa yayi yana jiran su kebe don bashi da bukatar magana a gaban mutanen da ya kula bakinsu duka daya. 


Maikudi kuwa dariya yayi bayan ya tafi. Alamun Malamijo da ya gani ne yasa shi wannan magana sai gashi tazo daidai da halin nasa. Mairama da Zayyan ma ta kasa tonawa mahaifinta asiri a gabansa me zai kaita fada a gaban Maikudi?


Radhiya ta dauka Hajjo ta goya Zayyan suka tafi tashar da zasu sami motar Kano. Sai da suka dau hanya don Salisu ya biya su kadai ne a ciki Mairama tana hawayenta Nene Marka na bata baki kawai Malamijo ya soma fada akan bayar da takardun gida da tayi. Kai, ita kam da me zata ji ne a rayuwarta. Tana kuka tayi musu bayanin yadda abin ya kasance.


"Ko dai mu koma ne a karbo takardun? Duk tsiyarsa baifi karfin hukuma ba fa Mairama" Salisu yace nasa ran a bace.


Tsorata tayi "don Allah ku kyale shi. Yaran nan zai karbe, babansu ma baiji dadin zama dashi ba"


Nene tace "Duk da haka Mairama mu zamu tsaya miki. Gidan a ina yake?"


"A Kano ne"


Salisu ya tabo dreban "Malam don Allah kayi hakuri ko zamu koma"


"Babu inda zamu je. Idan kuma sai kun koma to ni a ajiyeni a nan."


Nene Marka tace "haba Malamijo meye hakan?"


Rufe idanu yayi yana ta fada don sosai yaji haushin maganar Maikudi da rasa gidan da yayi. Ace 'yarsa da yafi so da tausayi a cikin 'ya'yansa ita ce tayi masa haka.


"Ina nan kan baka na bazan koma ba sannan kuma ki shirya tunda dangin miji sunfi uba ni bazan dauki nauyin kowa ba. Gida dai gaki gashi kuje a baku daki. Sai yanzu na raina waye Zayyanun ma. Har me yayi miki wanda ni ban miki dubunsa ba. Ji gidan da ya ajiyeki...."


Ta daure matuka amma bata jin zata taba jurewa wani ko da kuwa Malamijo ne ya zagi Zayyan. Ko bata aure shi ba yanzu ta san daraja da kimar soja....wallahi yafi karfin raini.


"Yayi min komai Malamijo" tace cikin kuka tana rungume Nene iya karfinta har Radhiya sai da ta tsorata "ko a kango muka zauna dashi har abada bani da tamkarsa. Wayyo ni ashe haka mutuwa take da daci da tona asiri? Lokacin da nayi maraicin uwa bansan ciwon rashi ba saboda bamu saba ba. Allah Ka jikan Zayyan ko Ka dauki raina nima na huta"


Zubar hawayenta ya taba Malamijo bare da ya ga ta rike kirjinta da yake mata mugun zafi. Dreban yace wa su juya ta dago rinannun jajayen idanunta.

"Allah Ya kaimu masu gidan su girma zasu karbi abinsu da izinin Allah. Amma a yanzu tunda yace yaji ya gani zai ci haram bazan shiga tsakaninsu ba"


Duk rashin halin Hajjo sai da tayi kukan tausayin Mairama. A haka suka tafi Kano Salisu yana ta mamakin halin Malamijo. Ashe Salame gado tayi na munin hali ba taka haye ba.


Tare suka sauka a tasha ya ja Mairama gefe ya fito da kudi masu tsoka ya damka mata sannan suka nemi motar Sumaila shi kuma ya shiga hayis zuwa gidansa. Dama ya riga ya gama shawararsa tun a hanya shiyasa yana ganin yadda Salame ta fito muzumuzu ita a dole tana cikin alhinin mutuwar masoyi ko sannu bata yi masa ba ya dakatar da ita zata tashi ta bar falon saboda ta ganshi.


"Salame ki hada kayanki ki tafi gida na sakeki saki daya"


Kiris...sauran kiris irin mai riss dinnan zawo ya tsinke mata. Tunda take bata taba jin fargaba da tsoro kamar wannan lokacin ba. Ya saketa ta tafi ina? Sumaila? Allah Ya kiyaye. A iya zurfin tunaninta Salisu yana mata son da zai iya hadiye kowane abu tazo dashi. Shiyasa take yadda taga dama iyaka yayi fada anjima ya dawo yana bibiyarta. To ko dai kunnenta baiji da kyau bane.


"Ni ka saka?"


"Halifa da muka haifa da ana komawa baya Salame bazan so hada jini dake da mahaifinki ba. 'Yar cikinsa tana cikin magagin rashin miji amma dukiya yake nema duk arzikinsa. Wallahi bazan iya ba. Kije Allah Ya baki daidai dake."


Kande ya kwalawa kira tazo ya cire naira goma yace ta wuce ta kaiwa mamansa Halifa yana tafe. Dayake daga can gidansu aka kawota ta riga tasan gidan.


Salame tana kame ta kasa motsawa ya wuceta ya shiga daki. Sai da abin ya sami wurin zama a kwanyarta ta shiga ta fara masa ihun masifa.


"Wato akan Mairama ka sakeni saboda Malamijo ya bata mata rai. Bazaka burgeni ba sai naga ta tare a gidan nan ranar asabar"


"Ki fita sawunki a likkafa kafin na tashi" yace daga kwance


Tafa hannuwa tayi " nima na huta da auren kaddara zama da mijin da baka so"


Duk inda zata cusa masa haushi ta rinka nema ko a jikinsa tunda ya rabu da kwallon mangwaro ya huta da kuda.


Gidansu ta koma ko ta kan Halifa bata bi ba. Awa uku tsakanin saukar su Malamijo da dawowarta gidan.


Yadikko ta tareta ganinta da akwati niki niki "ke kuma daga ina?"


"Sakoni yayi" ta fada cikin yanayin ko in kula.


Ashar Malamijo ya lailayo ya saki yana kara tunzura da yadda take magana ko a jikinta "wai nufinku duk kun dawo min gida kenan?"


"Ya son ranka? Ca nake mata biyu ka saki a dan tsukin lokaci guda, ai gara ka dana" Hajjo ta fada masa sannan ta saki labulen dakinta.


"To Al-Qur'an daga ke har Mairaman kowa taji da kanta bazan iya ba. Yara masu bakin hali kun fita a talauce kun dawo a tsiyace"


Dakinsu na da ta shige abinta ta barshi tsaye. Nan taci karo da Mairama da kyawawan 'ya'yanta. Kamar ta shareta sai ta fasa tace mata ya hakuri.


"Mungode Allah"


"Allah Ya jikan shi"


"Amin"


Daga haka babu wadda ta sake kula 'yar uwarta har suka yi shirin kwanciya. Ganin Mairama da yaranta ya tuna mata da Halifa sai taji wani iri gashi bata yaye shi ba dama. 


Kyandir Mairama ta kunna a gefen katifar da suke kwance ta kwanto wasikar Zayyan ta soma karantawa.


_(Na rubuta wannan takardar tun ranar da sunana ya fito a cikin masu tafiya Liberia. Sai nake ganin kamar jiya muka yi aure har zan tafi na barki. Mairam ban sani ba ko zan dawo ko shikenan tafiyar. Don Allah alfarma daya nake roko kada bakinki ya taba gajiyawa da sanyani a addu'a. Idan kewa ta isheki kinyi kukan rashina ki sani cewa nima ko a ina nake idan na tunoki sai na zubar da hawaye. Ina sonki Fillo Allah Ya sani amma ina son ki saka a ranki mijinki yayi alkawarin bautawa kasarsa ne. Zanfi kowa son son ace ina tare da iyalina kamar kowane magidanci. Sai gashi aikina yayi min tsakani da hakan. Lokaci zuwa lokaci zan rinka tafiyar da babu lallai na dawo. Duk da haka ina alfahari da aikina kema ki tayani kinji. Idan kin haihu kafin na dawo ki zabawa abinda muka samu suna. Ki kular min da 'Yar Soja Alheran innar Daadaa. Sauran kalaman da suka rage a kirjina sai na dawo gareki zaki ji su. Idan ban dawo ba na baki amanar kanki da ta 'ya'yana. Allah Yayi muku albarka. Lt Zayyan Muhammad Tureta)_


**********


BAYAN SHEKARA TAKWAS
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Ahayye nanaye, wallahi mutum ya yi min ba kyalewa zanyi ba don kaji in gaya maka yaro" tafa hannuwa tayi sannan ta rike kugu tana girgiza jiki a dole ranta ne a bace.


Abokin fadan nata wani sangamemen yaro ne don shima akwai kuruciya sai girman jiki.

"An fada din" yace sannan ya cigaba da wakar da ta hadasu fada "Malamijo Malamijo tsolon rake. Ga kwadayi ga rowa yaki yin gaba"


Wani kukan kura Radhiya tayi ta dire a gabansa ta nuna kasa "in ba tsoro ba dangwali" ta nuna masa kasar wurin. Dabi'arsu kenan 'yan makarantar wadda ta kasance firamare ta gwamnati idan ka yarda zaku dambace to kowa ya dangwali kasa. Daga nan sai a kaure karfinka ya kwace ka.


Dukawa yayi zai dangwala ga tsirarun abokansu da basu bar makarantar da wuri ba sun tsaya kallo. Sai da ta daidaici yayi kasa da fuskar nan kawai ta dauke shi da mari ta ranta a na kare. Kai tsaye staffroom ta wuce inda malamai suke wurin Umminta. 


Tana shiga ta cukwikuye jikin Mairama  tana kuka wai su Danmama ne suka dake ta. Tahowa suka yi Danmama ne a gaba kayansa duk kura saboda faduwar da yayi garin bin Radhiya. Kofar staffroom din taje ta saka su kneeldown har Radhiya sannan ta nemi jin ba'asi. Sai aka rasa me fada mata. Duk fitsarar Danmama yasan da kunya dai ya maimaita wakar a gabanta. Radhiya dama ko me zata yi mata bazata fada ba don kada ranta ya baci.


Daga bayanta taji wani malami yace "Anti barni dasu kiyi tafiyarki gida. Idan na gama zanesu zan taho da wannan mai kunnen kashin"


Mairama ta gyara zaman farin gilashinta tayi dan murmushinta da ta saba yanzu da wuya kake ganin bacin ranta ta koma ta dauko 'yan tarkacenta tayi hanyar fita daga makarantar don dama an riga an tashi.  Daga karkashin wata katuwar bishiyar marke take hango yara suna 'yan wasanninsu. Idanunta suka sauka akan Emzee yana zaune yayi shiru yadda ya saba yana jiranta.


"Karami zo mu tafi" tace da dan karfi don ta kula bai ganta ba sai gashi ya taso da saurinsa. 


Kayan hannunta zai karba tace ya barsu su tafi "Ummi ina Adda?"


"Kyale wannan yau ma fada tayi"


Sunyi gaba wasu 'yan ajinsu suka rinka kwalo masa kira suna Emzee sai an dawo hutu. Wannan suna da Mairama ta hakura da yakar sa dole shine sunan da yabi Muhammad Zayyan har gida. Mutane kalilan ke kiransa Zayyan ko Karami kamar yadda take fada. Yace wani malami da suka yi a firamare two ne yake kiransa MZ Tureta. Shikenan abu na yara ya koma Emzee.


A makaranta kuma gurfane gaban Uncle Idris su Radhiya ne da Danmama. Sai da Mairama ta tafi Radhiya ta fada masa sunan da suke kiran kakanta dashi. Uncle Idris ya tabbatar zasu aikata yayi musu bulala biyar biyar mai zafi da dorinarsa ita kuma biyu ladan biye musu. A waje ta jira shi shima ya dauko kayansa tunda yau take ranar hutu suka tafi yana mata nasihar fada da maza.


A cikin shekarun da suka gabata rayuwar Mairama sai dai godiyar Allah. Zamanta a gidan Malamijo tamkar zaman gidan haya ne. Iyakar gaskiyarsa shi nauyi ya masa yawa fitar da kudi kamar ana mintsininsa ne. Ya kara kudin cefane da kyar da sudin goshi amma daga nan fa ko me mutum ke bukata mace ko namiji cikin iyalinsa sai dai su nemawa kansu. 


Abu na farko da Mairama ta fara yi shine adana kudaden gadonsu a ranta tana tanadinsu ne domin karatun yaran a gaba. Sai da ta fuskanci sabulun wanka wannan idan bazata saya ba sai dai su watsa ruwa kawai ta fara taba kudin. A hankali kudi suka fara samun gibi dole ta fara neman sana'a. Tashin farko ta saro zobo tunda ta tsira da firig dinta ta soma yin zobo da lamurje na saidawa. TV da bidiyo da duka kayan gadonta banda katifar da ta ajiye kusu suke kwana da yaran duka suma saidawa tayi don ta kara jari. Allah Ya dubi halin da suke ciki ya buda mata kasuwa tana ciniki sosai.


Salame tana gefe kullum tana yawo tsakanin nan gidan nasu da wurin Ta Madina wadda da fari ta dauki fushi mai tsanani da ita sakamakon mutuwar aurenta. Har gida suka tura aka nemo Salisu ko zai maidata yace idan ta sami miji tayi aure shima auren zaiyi.


Zaman gaba, bakinciki da hassada ta dauka tana yi da Mairama. Kayan dakinta Ta Madina ta sayar ne ana bin malamai domin karkato hankalin Salisu. Shiya janyo ita bata da komai gashi jiki ya saba da jindadi an manta wanki, shara da wanke-wanke.


Wahalar gidansu a yanzu har tafi ta da tsanani ko don zawarci suke oho. Hankalin Mairama yana kan inganta rayuwar 'ya'yanta, na Salame yana kan me zata yi ta kere Mairama ko ta hanata cigaba. 'Ya'yanta musamman Radhiya sun

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment