Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko da Mairama ta makance nan nazo na fada musu matar da zan aura ta sami matsalar ido kuma tana da marayu. Idan ta tare duk wadda ta cutar da ita a bakin aurenta. Amma duk wannan abu lokaci guda naji zan iya rabuwa da kowa a kanki Salame. To albishirinki aikin boka yayi ci da kyau domin ke da gidan nan sai dai kiyi min takaba ko a fitar da gawarki. Kinzo kenan 'yar kundun uba"


Wayar da ta gama dukan su Rahima da ita ya dauko daga kan kujera ya daga kawai ya shiga lafta mata. Saukar farko Salame ta zabura za tayi rawar 'yan bori. Ashe ba dadi ta sa matar da ya saki karshe sai da yayi mata dukan kawo wuka kawai saboda ta dakar mata 'ya. Dukan da yake mata ya soma firgita Radhiya da uwargidansa duk haushinta da suke ji Radhiya sai ta sami kanta da janyo Salame bayanta yayin da Maman Danmama ta rike hannun Alhajin yana ta kumfar baka yana masifa kamar ya ari baki. 


Numfarfashi Salame take saukewa su ka ji sallama daga waje wadda mai yinta ko ba'a fada ba yana cikin bacin rai ne da fushi. Ba'a dena sallamar ba cikin daga murya tare da dukan kofar gidan a fusace.


Alh Indararo shima cikin bacin rai ya fita yaci karo da Idris rungume da 'yarsa Rahima idonta daya ya kumbura ga shatin waya yayi bororo a rabin fuskarta har wurin idon da samansa.


Mutum mai hakuri ba sawa ba fitarwa irin Baffan Rahima yau shima an kure shi karshe ko gaisawa basuyi ba ya soma fada "Billahillazi huwar Rahmanu Alhaji ka gargadi matarka idan ba haka ba zan tube rigar mutumci in shiga har cikin gidan nan inci mutumcinta. Dubi wannan diban albarka da ta yiwa Rahima. Yau yarinyar nan ko zaman kishi suka yi da uwarta a yanzu da babu aure a tsakaninmu bata cancanci wannan abu ba bare kuma 'yar cikinta."


Saukowa Alh Indararo yayi saboda yadda yarinyar ta bashi tausayi "dakata muyi magana Baban Rahima"


"Wace irin dakatawa zanyi? Kullum da fargaba da komai ni ko Iya muke matsanta mata tazo gidannan saboda uwa uwace komai lalacewarta. Babu ranar da Rahima bazata dawo min gida da hawaye ba amma yau ka duba ka gani don Allah. Dubi yadda fuskarta ta koma daga zuwanta"


Motar su Mairama ce ta tsaya suka firfito gabadayansu. Kafin su karaso Rahima ta kwasa a guje ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi. Hajjo ce ta fara ganin fuskar ta dago kanta da sauri. Mairama ma ta gani a tsorace tace "meye wannan Rahima?"


"Umma ce ta dakeni"


Mairama cije lebenta kawai tayi ta damki hannun Rahima ko Alh Indararo da Baffan Rahiman bata tsaya yiwa kwakkwaran kallo ba ta shige cikin gidan tana cewa "SALAME kina ina?".
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Washegari kafin a kira assalatu Emzee ya gama shirinsa. Ana kiran sallah yayi tare da Daada a nan wurin masu gadi sannan yace zai tafi.


"Ba ka ci komai ba Zayyan, Umminka bazata ji dadi ba"


Agogonsa ya kalla "Daada so nake kafin 9 ina cikin NDA in sha Allah"


Addu'a da fatan alkhairi Zayyan ya yiwa dansa suna jiran karasowar Ibrahim ya kaishi tasha saboda ba a gidan ya kwana ba. Kan wasu kujeru masu kyau daga gefen kofa suka zauna suna hira irin ta uba da da gwanin ban sha'awa. Ummi ce ta fito sanye da hijabi akan doguwar rigar baccinta da ta daura zani ta ciki da tray yana ta turiri ta taho inda suke.


"Inata saurin kada ka tafi ba ka ci komai ba. Ungo kuma ban yarda ka rage ba"


Indomie ce guda biyu da daffafen kwai biyu sai kofin orange juice mai sanyi. Tasan halinsa baya shan abu mai zafi da safe sai dare.


"Wayyo Ummi kinsan bana iya cin abinci da sassafe" yace yana kallon Daada yana neman agaji.


Daure fuska tayi "baka isa ba kuwa, ina fitowa kitchen na hadu da Rahima a falo ina jin ma ruwa ta fito sha idonta alamun bacci bai isheta ba amma ta karbi girkin tayi kuma kace na mayar"


Karba yayi da sauri bai gama jin me take cewa ba ya soma ci yana murmushi. Rankwashi ta sakar masa tana zaune akan kujerar da Zayyan ya tashi ya koma bayanta ya tsaya. Kuma ya hana Emzee tashi ya dauko masa wata. Ya kusa cinyewa suna ta masa tsiyar dama da yunwar Ibrahim ya shigo. Kafin yayi parking Zayyan ya duku kansa tsakanin Ummi da Emzee.


"Jama'a wai ni yaushe zaku koya min mota ne? Da kunya fa ace Zayyan Tureta bai iya dan murza sitiyarin nan da kowa keyi ba"


Me kuwa zasu yi banda dariya shi kuwa ya cukule yana cewa a motar Emzee zai koya yadda zaiji dadin bubbugeta kuma bazai ba da kudin gyara ba.


Ibrahim yana karasowa bayan ya gaishesu ya karbe fork din hannun Emzee wai zaici. Emzee ya damke hannun ya hana shi.


"Yanzu ko loma daya bazan samu ba?"


A daidai kunnensa Emzee yace "Idan ka dawo Zayyana ta dafa maka"


Yana jin haka ya gane wace ta dafa ya tasa Emzee a gaba karshe a tsaye ya karasa ci yana ta juya baya Daada da Ummi suna cewa da mai kwadayi da mai rowa. Cikin sauri sauri su ka bar gidan Ibrahim ya ajiye shi ya dawo. A hanya ya turawa Rahima text yana godiya da girkin da tayi masa da rokon kada ta bar gidan sai ya dawo.


A ranar ne kuma Aishatou kawar Tante ta iso za ta fara gyaran amarya Alheran Radhiya. Tante Nasara tace mata ta tabbata ta fito mata da 'yarta ta yadda ko ita kanta Radhiyan idan ta kalli mudubi sai tace bata gane kanta ba. Sai da Ummi taci dariya tace to ayi mata wankan inji mana daga nan.


Ba bata lokaci suna gama baccin gajiyarsu da kwana biyu aka fara gyara ciki da waje. Baki kuma kowa ya kama gabansa su Salame duka sun koma Sumaila na Nijar da Sakkwato suma sun tafi.


**********


Wayar gaggawa Daddy ya samu daga Katsina da daddare Alh Baba yana son ganinsa tare da iyalinsa. An tabbatar masa kowa yana lafiya sai shi Alhajin ne ma da yake ta fama da ciwon suga. 


Washegari kuwa ya hada kan iyalinsa su ka tafi. Dama kuma a ranar Bilal yaso tafiya da Fauziyya idan an fara bikin sai ta dawo. 


Awwab sallamarsa da Radhiya da ga nesa-nesa akayi. Tun ranar da akayi taron nan da suna waya yace mata akwai sauran rawar da za ta yi masa. Wani mugun kida kamar zai tsaga mata waya ya tura mata yace tun wuri ta koya suna sake haduwa zata yi masa. Shikenan take gudunsa duk da yayi ta magiyar cewa wasa yake yi. Ana fara gyaran jiki Aishatou tace shima mijin sai ana masa rowar ganinta domin a haka ne idan sun hadu zai fi ganin kyaun da tayi. Haka yayi ta korafinsa da mita ya hakura tunda ya fuskanci da gaske maigyaran jikin da Tante Nasara suke. Zamu hadu kawai yake cewa Radhiya don sai ya fanshe wannan punishment din na babu gaira babu dalili an hana shi ganin matarsa.


Mota uku su ka yi ranar da zasu tafi. Daddy da Mami a motarsa dreba na jansu. Sai Awwab da ya dauko Zahra, Raji da Zayyana. Mota ta uku kuwa Fauziyya ce da Bilal ana tuki ana shan soyayya wai kara'i take yi saboda laulayi ya sa ka ta a gaba kwana biyu yanzu kuwa anyi lafiya.


Wani masallaci su ka tsaya sallah irin na matafiya kafin su shiga Kaduna Zayyana ta tsaya sakawa Jawad takalminsa su Daddy Haroun su ka shigo wurin. Mummy Gambo, Ghazalatu da kanwarta suna shiga masallacin su ka ga su Mami suna sallah. Su din ma sallar suka yi an idar sai yiwa juna kallon kallo saboda abinda ake cewa ta ciki na ciki. Ko kadan sun kasa sakewa da juna ayi hira yadda aka saba. Ba su Mamin ba, ba kuma ga yaran nasu ba. Nama da lemuka Awwab ya siyo ya kira Zayyana tazo ta karbar musu. Ghazalatu na can gefe da kanwarta Fauziyya ta fara yunkurin jawosu jiki.


"Kuzo muci abinci"


"Mun koshi" Ghazalatu tace a kunyace saboda nauyinsu da take ji idan ta tuna duk abinda ya faru saboda ita ne.


Basu sake cewa komai ba amma cin abincin baya yi musu dadi saboda ga 'yan uwansu a gefe. Su kuma saboda sunce sun koshi babu damar zuwa su sayi wani.


Mummy Gambo sai ta rasa yadda za ta yiwa Mami magana saboda kunyar kowa yanzu yasan bayan sun gama yi mata tijara ga yadda auren ya kare. Mami kuwa sai ta yi kamar bata lura da yadda ta takura ba ita da yaran tana cin abincinta hankali a kwance. A zuci tausayin Gambo take ji sai dai dole ne ta nuna mata kuskurenta. Can da abin ya ishi Mummy Gambo gashi Daddy Haroun ya tsaya suna magana da Daddy wadda duka akan yanayin sabanin iyalansu ne ta dan matso kadan kusa da Mami.


"Ina ta zuba ido ko zaki gayyacemu taron da kuka yi na dawowar uhmmm baban yarinyar nan amaryar Awwab sai muka ji shiru"


"Banyi zaton zaki so zuwa bane" Mami tace kai tsaye.


Mummy Gambo dama neman kofar magana kawai take yi amma ba ta zargin yayarta don ba ta gayyacesu ba "Mami...hmmm...Mami kiyi hakuri akan duka abubuwan da suka faru"


Zahra na jin haka ba ta jira Mami tayi magana ba yace duka su tashi su bar wurin don ta san maganar ta manya ce. Ghazalatu har ta soma hawaye. Mami ta kalli kanwarta tana tuna irin batancin da suka yi mata har gida.


"Ki bar maganar nan mu karasa Katsina nan ba muhallinta bane"


"Naji amma kice kin hakura don Allah" Mummy Gambo ta fada a raunane tana kara tsanar abubuwan da tayi.


"Na yafe amma a bar zancen haka."


Gaba Mami tayi da sauri don kada ta soma hawaye a wurin suka tafi kowa ya shiga mota. A jere suke tafiya har Katsina gidan Alh Baba. Anyi abinci sosai na tarbar bakin gidajen guda biyu. Sai da su ka yi sallar la'asar aka ci abinci sannan Alh Baba ya kira kannensa, Ummansu Mami sai kuma Mami, Hussaina da Gambo kowacce da mijinta da kuma 'ya'yan da abin ya shafa wato Awwab, Ghazalatu da Nura. Ba tare da bata lokaci ba Alh Baba ya soma magana.


"Maman Biyu gani da 'ya'yanki da kowa a wurin nan kamar yadda nayi miki alkawari zanyi kokarin yi musu sulhu." Kallonsu yayi daya bayan daya  "Hassana, Hussaina da ke Gambo mun taba zama daku shekara uku da suka wuce akan auren Muhammad da Ghazalatu. A wancan lokacin nawa idon ne ya fara rufewa da son ganin kamar yadda da yawa cikin 'ya'yanmu su ka auri juna su ma jikokin suyi haka. A zatona zumunci zan karawa karfi ashe ruguza shi nake yi. Kuma sai akayi rashin sa'a zumuncin na 'ya'yan mutum daya na bata. Maman Biyu kiyi hakuri"


Mami da kannenta kowa sai sharar kwalla yake yi saboda ganin Ummansu tana kuka. Tayi bakin kokarinta ta shiryasu abu ya faskara shiyasa ta kawowa Alh Baba kukanta kuma bata ji nauyin fada masa gaskiya ba kai tsaye ta dora masa laifin bata zumuncin 'ya'yanta.


Alh Baba ya koma ga su Awwab "Muhammad da kai zan fara. Kai da kanwarka kun hada kai bisa rashin sanin mahaifinka har ya nema maka wani auren. Tabbas ka fini gaskiya a lokacin da ka nemi hada mata biyu domin fitar da mahaifinka kunya."


A hankali Awwab ya daga kai ya kalli Alhajin ya mayar da kansa kasa yana saurarensa lokacin da ya koma kan Nura yayi masa kaca-kaca akan irin tozarcin da ya yiwa Ghazalatu.


"Wannan abu duk mun sanya son kai a ciki karshe bamu ji dadi ba. Gambo kin biyewa 'yarki tace bata son kishiya...."


Awwab na jin zancen ya koma kan iyaye ya kalli Nura da yake tsananin jin haushi da Ghazalatu wadda tamkar a zare allura babu wata soyayya da ta rage masa a zuciya game da ita sai ta 'yan uwantaka da tausayin halin da ta fada a gidan miji.


"Ku tashi mu fita"


"Ban gama ba dreban sama ku koma ku zauna" cewar Alh Baba.


"Alhaji zamu dawo tunda na ga maganar yanzu ba tamu bace" karamar tsawa ya dakawa Nura dama ya girme shi "kai tashi mana"


Da sauri ya mike su ka fita su ukun. Alh Baba da sauran kakanin sun yabawa Mami wurin tarbiyantar da 'ya'yanta gashi har yasan su tashi saboda iyayensu za'ayiwa fada.


Fada, nasiha da jan kunne sosai Alh Baba ya yiwa su Mami musamman Hussaina da ya dorawa alhakin ingiza wutar rikici tsakanin Mami da Gambo. 


"Abinda akayi ta rigimar dominsa gashi sai da ya faru..." Baba Karami yake cewa dasu "munje mun karbawa Muhammad auren yarinyar nan Radhiya. Ku kuma da kuke ta tada jijiyar wuya gashi gayyar ta watse. Kunyiwa yaranku auren huce haushi sun kare da hadaku fada da juna"


Hussaina tafi kowa jin kunya ga ishrar da take gani a wurin Hany har yanzu bata da lafiya dangin saurayin kuma sunki amincewa.


"Nasan hakkinku ne yake bibiyata Hassana da Gambo ku yafe min don Allah"


Ummansu ma kukan take yi a dole su ka rinka cewa sun yafewa juna. Iyayensu albarka suka saka musu sannan aka sake kiran su Awwab. Baban Biyu yace yana bukatar daidaituwar zumuncinsu ko me zaije ya dawo tsakanin iyaye daga yau bai yarda su juyawa juna baya ba. Sun tashi zukata wasai. Daddy ne yayi saura da iyayensa yake fada musu irin alkhairin da Zayyan yayi masa da duk wanda ya rabe shi.


"Banda ceto rayuwarmu da yayi kudin da gwamnatin tarayya ta bashi a matsayin diyyar wahalar da yasha wallahi yake ta bin mutane da alheri. Nasan ana cewa ka haifi mutum baka haifi halinshi ba amma ina kyautata zato akan cewa Radhiya a cikin namu dangin alkhairi ce. Ban taba kin Awwab da Ghazalatu ba. Duk abinda nayi nayi shi ne domin kulawa da bayan wanda ya sadaukar da rayuwarsa dominmu. Nasan gabadaya rigimar nan ta samo asali ne akan auren da na nema masa saboda haka ina mai rokonku da ku yafe min"


Kowa yace ya yafe duk da ba laifi yayi ba. Hasali ma yayi abin yabawa ne sosai saboda bai kasance mai manta alkhairi ba.


A hankali hira ta barke a tsakanin 'yan uwan inda su Zahra sosai suke jin zafin Nura da abinda ya yiwa Ghazalatu. Ana haka ta hango Awwab a kan kujera can gefe a cikin falon yayi nesa dasu. Murmushi tayi ta karasa inda yake wata sabuwar wutar sonsa tana ruri a zuciyarta. Chatting yake da Radhiya yana ta murmushi ta zo ta zauna a kujerar gefensa.


"Ango kasha kamshi" tace tana rausayar da kai da murmushi.


Hankalinsa na kan wayar yana yiwa Radhiya reply yace "Kamshi sai mata"


Murya ta karyar alamun kuka take shirin yi "kaji irin zaman da muka yi da Nura ko?"


Wayar yasa a aljihu ya maida hankali gareta "naji Ghazalatu sai dai ince kiyi hakuri komai mukaddari ne."


Gwauron numfashi ta sauke tana tararrabin abinda za ta fada. Hannu ta ga ya mayar zai dauko wayar tayi saurin cewa "Yanzu shikenan tsakaninmu Ya Awwab?"


Karo na biyu ya kuma mayar da wayar "ban fahimceki ba"


Sunkuyar da kai tayi kafin ta bashi amsa "nasan cewa ban kyauta ba amma kayi hakuri idan da hali zan jiraka"


Ya fara gane me take son cewa sai dai baya son zumuncin da ake kokarin fardadowa dashi ya kuma sake sumewa a dalilinsa "Ghazalatu mun riga mun wuce wannan matakin. I am happily married matata ko tarewa bata yi ba so please kada ma mu komawa abinda ya wuce"


Hawaye ne ya zubo mata "yanzu baka tausayin halin da na shiga? Ban taba cireka daga zuciyata ba kuma a shirye nake na zauna da kai ko a ta biyun ne"


Ransa yaji ya soma baci amma baya son janyo hankalin kowa garesu "Allah zai baki wanda ya fini amma bani da niyar mata biyu yanzu"


Wani irin murmushi tayi "wato nice baka so wancan lokacin shiyasa har ka iya amincewa wata kuma ka fada da bakinka kana sonta ba wai don Daddy Mustapha ya nema maka aurenta ba"


"Wai ni Ghazalatu Nura ya sakeki ne kike min wannan zancen?"


Da murnarta ta amsa "ya hakura yayi min saki daya"


"Idan dai ba lissafina ya baci ba ina tunanin har yanzu kina cikin kwanakin iddah ko"


"Nasan da wannan amma bazai hana na fada maka abinda yake raina ba"


Neman abinda zai fada mata yake yi wayar Radhiya ta shigo. Yana dauka ta soma kukan shagwaba wai baiyi mata reply ba. Dama hirar tafiya honeymoon suke yi ya bata zabin kasashe uku yace ta zabi daya shine ta tura masa inda take so bai duba ba.

Hakuri ya soma bata Ghazalatu sai ta daga murya tana cewa wai yace gata zasu gaisa. Gudun kada ta zargi wani abu tunda ta riga taji muryar mace a wurin yace mata ga Ghazalatu zasu gaisa.


Mika mata wayar yayi ta koma kan kujera ta zauna tana magana a gayance kamar bata so "amaryarmu ko ince uwargida sarautar mata yaya shirye shiryen biki?"


Zuciyar Radhiya har ta fara tafasa da kishi musamman saboda yanayin yadda Ghazalatu ke fitar da harufa daki daki tana wani yauki.


"Lafiya kalau" ta daure tace.


"To ga amanar Yayana nan dai ki kula mana dashi sosai...idan kina bukatar shawarwari game da hanyoyin sace zuciyarsa ki karbi numberta a wurinsa." Wata shu'umar dariya tayi "kinsan na karance shi kamar tafin hannuna"


"Abinda ba'a sani ba ake karantawa, ni da Hammana kuwa warin takalmi ne komai namu iri daya....how do I put it?" Radhiya tace muryarta na fita cikin nutsuwa. Dariya tayi a hankali saboda samo kalmar da ta dace ta fada "Alheran is the female version of Awwab...amma duk da haka nagode da tayin da kika yi min"


Awwab tsabar mamakin abinda Ghazalatu tace kasa yi mata magana yayi sai jinjina kai yake da halin mata. Kallonsa tayi ta saki murmushi duk da ranta in yayi dubu ya baci da amaar Radhiya amma ai ba'a fara komai ba ma "Ga angon namu.....Yayana sauran maganar tamu fa?"


Fizgar wayarsa yayi ransa a hade ta sake maimaita tambayar da dan karfi yace zasu karasa daga baya. Da sauri ya saka wayar a kunne yana cewa hello Radhiya ta katse kiran. Yasan za'a rina sai dai yana sake kira yaji ta kashe wayar gabadaya.


***********


Ko sati ba'ayi ba da taji Mami tana fadawa su Ummi matsalar gidan Ghazalatu da mutuwar auren shine daga zuwansa Katsina yau zasu tada tsohuwar soyayya. Allah Ya bada sa'a tace a zuci ranta yana kuna tayi jifa da wayar ta kifa kai tana kuka. 


Kamar wasa ta kwashe yafi awa guda tana zubar da hawaye. A haka Rahima tazo ta sameta sai dai bata ga fuskar ba tayi zaton bacci kawai take yi. Awwab tun yana daukar abin wasa har ya fuskanci fushin nata na gaske ne. Bai san sau nawa yana gwada wayarta ba amma duk kira a kashe. Gashi layi daya gareta bare ya nemi wani. A ranar su biyun da kyar suka yi bacci saboda tunani. Asubar fari yana dawowa daga masallaci ya sake gwadawa nan ma shiru har bayan azahar. Bashi da kwanciyar hankali lokacin kana kallonsa za ka gane akwai abinda ke damunsa. Mami tana ta yi masa magana akan cewa su Umma da sauran matan kakanin sun ce lallai idan an dauko Radhiya daga Sakkwato nan Katsina za'a kawota ayi budar kai kafin su wuce Nijar.


Sama-sama yake jin muryar Zahra tana cewa gaskiya tana tausayin Radhiyan saboda zasu sha yawo. Wayarsa a hannu yana yi mata text bai amsa ba Mami ta kira shi da dan karfi "wai meye yake damunka ne ana magana ka kasa amsawa? Ka ji abinda nake fada ma kuwa?"


Saurin kallonta yayi "Mami naji, gajiya ce dai kowa sai yayi a tanadi maganin ciwon jiki kawai"


Murmushi tayi tana cigaba da fadawa Zahra ta rubuta abubuwan bukata na walimar da za suyi ranar budar kan "tunda wahalar saboda ku ne ai kai ya dace ka siyo mana maganin"


Murmushi kawai yayi ya tashi kamar jira suke Mami da Zahra su ka tambayi juna me yake damunsa ne.


Kasa hakuri yayi ya kira Ummi saboda ba karamin kewar Radhiya yake yi ba ga damuwa tunda yasan fushi take yi dashi. Lokutan da ya sami damar kasancewa da ita kadai idan ya tuna sai yaji kamar ya budi ido ya ganshi tare da ita. Sun gaisa da Ummi lafiya kalau yadda su ka saba ya rasa da yadda zai nemi Radhiya. Ita da kanta ta fuskanci me yake damunsa.


"Awwab kaima ka kira kanwarka baka samu ko?"


Da sauri yace "eh"


Murmushi tayi "Jiya Karami sai da ya kirani na hadasu, dazu ma ya sake cewa na bata su gaisa wai ya kirata shiru kuma bata kira shi ba. Ban san me yake damunta ba sai aikin kwanciya...."


Rahima ta bawa wayar ta kai mata. Har ta mika hannu tana tambayarta ko Emzee ne Rahima tace ba shi bane. Tunda taji haka tasan ko waye sai cewa tayi ta mayarwa da Ummi wayarta yanzu za ta kunna tata ta kira shi. Awwab yana jin duk abinda tace kamar yayi ihu saboda yadda ya matsu ta amsa masa taki.


Fitar Rahiman ke da wuya ta sake fashewa da wani kukan ko abinci ta kasa ci sai tunanin yana can suna soyayya da Ghazalatu.


Zuwa dare jikinta yayi mugun zafi da ciwon kai saboda ita dama ba mutum bace mai sa abu a rai. Wannan karon da tayi shiru sai yake neman yi mata illa. Ummi ta gaji da wannan zaman daki da tsura da ga jiya zuwa yau take tambayar Aishatou mai gyaran jiki ko ta ga wani chanji game da ita.


"Shiru shirun da take yi ne ke damuna dai Ummin Radhiya. Kuma kamar kuka tayi ma shiyasa jiya da yau aikin namu bamu dade ba. Ina jin fargabar aure ce ta fara taba ta. Kinsan fa ance aure yakin mata"


Ummi ta soma dariya "yakin matan zamaninmu ko, yanzu budurwa ko ita ce ta hudu banda rawar kai me su ka sani"


Hira suke abinsu akan bambancin matan da da na yanzu Mami ta kira suke zancen walimar da dole yanzu sai tayi a Katsina. Ummi ma tace dalilin da yasa ta kira dazu kenan Malamijo yace kafin su fara bikinsu a kawo masa jikarsa suyi nasu taron tunda ya kula wannan bikin ba na zama bane yawo za'ayi ta yi.


"Yaran nan zasu wahala musamman Radhiya da take mace ko dai mu matso da bikin kada mu cure komai cikin sati guda muzo ana 'ya kwance uwa kwance" inji Mami.


"Ke da 'yarki ne zaku kwanta ni kam garau zaku ganni don ko suyar albasa bazan tayaku dashi ba" Ummi ta bata amsa da dariya.


"Kyale wannan 'yar rabona da ita tun jiya"


Sai yanzu Ummi ta fara damuwa "Mami bari na dubo yarinyar nan. Jiya da yau a daki ta wuni muna cewa ko fargabar aure ne amma dai bari na duba" tace tana hawa sama zuwa dakin Radhiya.


Bata ajiye wayar ba ta shiga ta same kwance a kasa ta rike kai da hannu biyu. Da sauri ta durkusa a gabanta tana dora hannu a kan goshinta da yayi zafi ga idanu a kumbure anci kuka an gode Allah.


"Ke me ya sameki?" Ummi tace a tsorace tana ajiye wayar a gefe. Tayar da ita tayi ta koma kan gado.


"Kaina zai tsage Ummi" tace a wahale.


Mami na jinsu hankalinta ya tashi ta soma kwalawa Awwab kira ta ma manta suna Katsina ne Radhiya na Abuja. Tare da Daddy su ka shigo daga waje ta fada musu me taji Radhiya na fada. Sosai hankalin Awwab yayi matukar tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ummi aka sake kira tace musu zazzabi ne da ciwon kai amma ta bata magani. Idan bata ji sauki ba zuwa wayewar gari sai suje asibiti. 


Zayyan a dakin Radhiya ya zauna har wurin dayan dare bayan ya lallabata taci abinci da kyar. Maganar Ghazalatu keyi mata yawo a ka wai tasan Awwab kamar tafin hannunta kuma a gabansa amma bata ji yace komai ba. Ita bata taba sanin kishi ba sai akansa. Irin son da take masa ya saka mata wani irin kishi da take jin yafi karfinta. Idan yace zai auri kanwarsa ba hanawa zata yi ba amma ita ta yarda dari bisa dari da kazantar da baka gani ba tsaftace. Duk abinda zasuyi ayi a bayan idonta ba sai an nuna mata

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment