Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan kafin ya koma aiki.

Kitchen ta leka ya siyo karamin risho, tukwane biyu da yan kayan bukata. Wani sabon shafin amarci su ka bude a gidan ga diyarsu a gefe tana samun kulawa. Wasa-wasa kwanansu goma sha biyu sannan su ka fara shirin komawa Birnin Shehu. Duk yadda taso kuwa yaki kaita gidan Salame don baya kaunar duk wani dalili da zai sa su hadu.

**********

Watansu biyu da komawa Zainab ta haihu. Sai dai ita a gidan iyayenta ta zauna su Mairama da Mami ke zuwa kullum har akayi suna. Jariri yaci sunan kanin baban Hadir da ya rasu gabanin haihuwarsa Ibrahim.

Rayuwar wadannan bayin Allah haka ta cigaba da tafiya cikin so, yarda da aminci. A kowane mataki su na kokari wurin ganin sun tsayawa juna cikin dadi ko akasinsa. Da Salame ta haihu ya barta taje ta kwana hudu a Kano inda ta rinka fuskantar Gadara da wulakanci daga wurin yayarta ta. Da yake ta fara sabawa da wannan bakon hali sai ta daure zuciyarta don kada ayi batacciya.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ....ALLAH NA NASA

"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a yiwa kishiya"

Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan rama. Kuma ke shaida ce ina cin abinci sosai"

"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki bari ku je asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"

Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya kullum kara habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi anyi daukan rungumarni mu fadi.

Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana takaicin wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu rigima da kuka ga fada duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai yakushi tana doke doke duka wataninta tara a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na gaskiya yake kira idan yana jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.

A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara kunya ko? Mu da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har Awwab bata yiwa"

Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana cewa "Ummi wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"

Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda kiba ne?" Cewar Mami

Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman yi ya tafi dakinsu Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy. Gajiya tayi da wasan ta soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya sabata yana haki "gaskiya kin fiye kuka Alheran dinnan"

Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a gefen idonsa na hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara. Zainab da Mami ke rige rigen shiga dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta yayin da Mami babu tambayar ba'asi ta dauke Awwab da mari.

"Me kayi mata take wannan kukan?"

Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin "yakushi na tayi fa"

"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.

Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"

Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na fada masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin rarrasheta ko kuwa"

Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta fara shayar da ita amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata ko tashi da kafafunta ta kasa. Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki. Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin kenan.

Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin Mairama har wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga kunyar ace yarinya bata shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami tace mata ya kamata kafin su Zayyan su dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren ta tafi ta barwa Mami ita sai kayanta da ta turo Awwab dasu.

Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da amana ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar Mairama da uban laulayi sai Zainab dake sintirin zuwa wurinta.

A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na sabo. Da murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major ta tafi yaye.

"Yaye Mairam? Ko shekara bata yi ba"

Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"

Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba sai yaye?"

Baki ta tura masa "to ba..."

"Me?"

"Ciki" tace tana rufe fuska da tafukan hannayenta

Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"

Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai sabon amarci don ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma sannan Mami ta dawo da ita da kaya da tarkacen wasa.

******

Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi alala da rana Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito wurinsa.

"Sojana ya dai yau ka dawo da wuri"

Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa mata.

"Me kike dafa mana ne?"

"Alala zanyi"

Hanci ya dage "Uhmm kayan bata ciki"

Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba ne. Sai na canja abincin, waken...."

Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama fadin me tayi niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin Zainab tana rusa kuka kamar ranta zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.

Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin dole jikinsa a sanyaye yace "ka fada mata ne?"

Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir take kallo tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"

"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"

Kanta ya sake shiga duhu "ba dai saki bane ko?"

"Liberia zai tafi"

Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin barikin da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin tana basu gudunmawar sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci ana turawa. Rawa taji jikinta yana yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.

Cikin tsantsar tashin hankali tace "da kai za'ayi tafiyar?"

Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta kalli yadda Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban baki abokan sun lalubo domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa itama tana son Hadir fiye da zato da tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma gidansu aka bar Zayyan da Mairama.

Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi yake bata. Ita kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai ba sai cikin dare ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashi

"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"

"Yaushe zaku dawo?" Ta tambaye shi murya a dashe.

Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu in Allah Ya yarda"

Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai "Ashe haka ki ke so na ban sani ba?"

Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani abu da zan fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya wanke min kuncinsu. Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa naji dadin bautawa kasata."

Wani irin abu take ji yana mata yawo a jikinta. Idan a da tana tunanin tana son mijinta to a yau sonsa yana neman ranta ne. Gani take kamar bazata iya jurar rashinsa a tare da ita ko da na kwana daya bane. Ashe baka sanin mahimmancin abun da ka ke dashi sai yayi nisa da kai. Bata san lokacin da bacci ya dauketa ba sai ajiyar zuciya da take ta saukewa.

Sai da ya tabbatar tayi bacci ya tashi ya dauro alwala. Yasan yaudarar kansa zaiyi idan yace zaiyi bacci a wannan daren. Nan da kwana biyar zasu bar kasar, zai bar iyalinsa wanda basu dogara da kowa ba sai Allah sai kuma shi da nauyinsu yake wuyansa. Yayi nafila raka'a goma tare da witri sannan ya zauna yana jero addu'o'i. Motsin Radhiya yaji yayi saurin fita da ita daga dakin don kada ta tashi Mairam yaje ya hada mata tea a feeder ta shanye. Yana jiran ta koma bacci yarinya ido ya soye ta fara kiriniya. Bata tafiya sai rarrafe da mikewa. Biye mata yayi suna wasan. Sai gabanin asuba ta bingire a jikinsa tayi bacci. Kan ta ya rinka shafawa baiyi zato ba sai hawaye ya ziraro masa ya goge da sauri yana baiwa zuciyarsa hakurin cewa wata uku a wurin Allah kamar kiftawar ido zasu zo su wuce.

**********

Gidan Hadir ma basuyi bacci ba don Zainab kwana tayi kuka. Mami da sauki tunda ba zuwan Major na farko wurin rikici ko yaki kenan ba. Sai dai itanma kukan tayi don ba'a sabo da rabuwa.

Washegari harabar gidajen nasu kaf babu wata hayaniyar kirki. Sojoji ashirin ne zasu tafi a cikin magidantan da suke wurin. Kowa yana gida tare da iyalinsa.

Bayan la'asar Zayyan ya dauki Mairam su ka je gidansu da gidan kawunansa da Mal Aminu ya fada musu zaiyi tafiya. Kowa yayi masa addua da fatan alkhairi ban da Jume da bata dena jin zafin rashin basu kudi ba. Duk da haka ya yi musu kyauta ita da su Maikudi tunda sunyi aure. Matan ma a ranar sai da ya kai musu ziyara.

Sukuku su Mairam su ka koma babu walwala a tare dasu ita da Zainab. Mami ce tayi musu fada akan idan sun cigaba da haka a wane yanayi suke so mazajensu su tafi. Sun ji maganarta don kowacce sai da tayi kokarin gyarawa. Mairam dambun nama ta yiwa Zayyan gari guda sai da ya dibarwa Hadir da Major. Ta kuma saki jiki tana bashi kulawa fiye da yadda ta saba.

Sauran kwana biyu su tafi tana goge masa khakinsa Radhiya ta fito daga daki da kafafunta a hankali saboda rashin kwarin tafiyar. Murna ta kama Zayyan ya sunkuceta yana sumbatar kumatunta.

" 'Yar soja ta girma, yau yawo zamu je tunda anyi kafa"

Kamar taji me yace ta rinka bangala dariya. Ajiyeta yayi zai chanja kaya su fita tasa masa kuka "Daaadaa" yaji tace tana dago masa hannuwa.

A nutse ya juyo ya tabbatar shi take kira. Har yanzu hannuwanta take miko masa "Daaadaa". Ya kalli Mairam ita ma mamakin yarinyar ya kamata. Awwab bashi da aiki sai koya mata Ummi da Daddy wai dole sai tayi magana. Yau gashi ta kira mahaifinta dadi yasa yaji idonsa na alamun zafin kwalla. Daukanta yayi ya shiga dakin su ka bar Mairam tana guga tana diga masa hawaye a kayansa.

Ranar ashirin da daya ga watan Mayu na 1993 ne Giginya Barrack dake cikin garin Sakkwato ta kwashi sojojinta za'a kaisu Lagos washegari su tashi zuwa Liberia ta ruwa.
Daren ranar ya kasance dare na soyayya, jaddada alkawura da kuma sabunta matsayi a zukatan su Zayyan da iyalansu. Daga shi har Mairam babu wanda ya runtsa kuma hakan take a wurin Hadir da Zainab da Major kansa da Mami.

Komai Mairam ce ta yiwa Zayyan hatta abinci a baki take bashi. Tayi ta daurewa kada tayi kuka zuciyarta ta kasa daukan wannan lamari. Ko kadan baya son nuna mata damuwar da yake ciki shiyasa ya fake da yiwa Radhiya wasa.

Jiniya mai sanar da su fito ce tayi kara sai da cikin Mairama ya murda kawai ta fashe da kuka iya karfinta.

"Zayyan"

Tashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa "ashe kin iya fadin suna na"

"Ka ajiye aikin nan mu koma Nijar ko kiwo ka rinka yi"

Fuskarta ya zagaye a tsakiyar tafukan hannunsa.

"I love you Maryam Ali Gidado. Ki rike wannan a zuciyarki har na dawo. Nayi miki ajiya a kan mudubi idan na tafi ki duba"

Hade bakinsu yayi tamkar ranar su ka fara haduwa yana jin karar jiniyar a karo na biyu ya saketa ya dauki Radhiya.

"Ki tayani kula da Umminki da baby kinji mamana."

"Daaadaa" tace tana washe hakoranta biyu dimple dinta ya lotsa ciki sosai.
Ita ma ya sumbaci kuncinta hagu da dama kafin Mairam ta farga ya fice daga gidan.[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Daga tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke dake Lagos su Zayyan zasu tashi a jirgin ruwa zuwa babban birnin Liberia wato Monrovia. Akan tekun Atlantika jirgin nasu ya dau hanya sai da suka wuce Benin republic wadda mu ka fi sani da Cotounou, sai Togo, Ghana, Cote d'voire sannan Allah Ya saukesu a kasar da rikici na cikin gida ya kaurewa tun shekarar 1989.

Motocin yaki aka turo domin daukarsu. Zayyan da Hadir zuwansu sansanin yaki irin wannan na farko kenan. Major Mustapha yazo ne a matsayin babban soja don ba wuri daya zasu zauna ba. Shi Computer Engineer ne saboda haka aikinsa yafi karfi ne daga bayan fage musamman da a wannan lokacin babu masu karatu irin nasa da yawa saboda karancin kayan aiki.

Cikin garuruwa ko kauyuka da rikicin yafi shafa ake watsa sojojin. Sune suke kwantar da tarzoma da fitina idan ta taso a tsakanin mazauna garin da kuma 'yan tawaye.

Ranar farko su Zayyan da sauran da su ka zo tare da yawansu basu iya rintsawa ba. Daki ne kato kowa da yalolowar katifarsa akan gadon karfe mai hawa biyu. Wasu kuma a kasa katifunsu suke saboda rashin wadatar gadajen. Zayyan da Hadir a kusa da juna suka shimfida katifun da aka basu. Shi dai tunanin Mairama da Radhiya yake yi. Ko me sukeyi a wannan lokaci? Tafiyar Radhiya ta kara kwari a kwanakin da suka shafe a kan ruwa? Idan ya koma zata yi masa kyuya? Gajeren tsaki yayi da wannan tunanin. Burinsa ace kowane mataki na rayuwar 'yarsa ya faru a kan idanunsa.

Hadir yace "kaima ka kasa bacci ko?"

"Yadda ka san nayi tsuntsuwa naje na gansu na dawo" yayi maganar cike da kewa.

Muskutawa Hadir yayi ya gyara kwanciyarsa. Shi kuma Zayyan yayi rub da ciki ya rike fuskarsa a tafukan hannunsa da ya tokare kansa dasu.

"Bansan yaya Zainab take yi da Ibrahim ba yanzu. Kusan wata guda yaron nan ba ya iya bacci sai akan kirjina"

Dariya Zayyan yayi "kace akwai daru, don ma bai kai Alheran rigima ba abin zai zo da sauki."

Wani cikin wadanda suka tarar a sansanin yana daga gefe yana jin hirarsu ya soma dariya "kusan kowa ranar farko sai yayi hirar gida"

Gwangwani ya dauka a kusa da shi ya bubbuga da hancin katuwar bindigarsa. Sai ga sojoji suna tashi zaune wasu akan gado wasu a katifa. Kalilan ne masu bacci. Mutumin yace "kunga yau anyi baki ku tashi mu san juna." Ya kalli bangaren da yawancin bakin nasu suke "babu wani abin debe kewa a wurin nan sai hira da muke samun yi da juna cikin dare"

Na kan gado na dirowa na kasa na matsawa sai gasu sunyi da'ira sun zagaye katifar wanda yayi maganar. Da gani zai girmi da yawansu. Kallonsa ya ga suna yi ya kada kafada.

"Ok, ok ni zan fara"

Ihu wasu suka fara su Zayyan dai abin duka sabo ya zame musu. Duk wata hayaniya sun saba da ita a irin training da suke zuwa. Amma wannan karon fa a filin yaki suke tare da sojojin wasu barracks din da basu taba haduwa ba. Muryar mutumin yaji ya soma magana.

"Nine shugabanku a harkar abinci" sai sowa da tafi yayi murmushi "Chief cook kuke gani. Suna na Captain Ogbonna Odili. Ina da mata Mabel da yara hudu a Enugu. Ogechi, Uloma, Nneka da Kachiku muna kiransa Kachi. Kamar kowa a nan ina matukar son family dina. Musamman ma Uloma saboda tana da kokari sosai a school. Yanzu zaka rubuta mata abu indai ta karance shi daga farko zuwa karshe to ya gama zama. Da kuke ganina kudi nake nema domin na kaita wata babbar makaranta a garinmu ta gifted children. Uloma is born to be a great doctor"

"So shall it beeeee" wasu suka amsa da ihunsu na sojoji. Capt. Ogbonna yana ta dariya ya cigaba da hirar iyalinsa ana tayashi murna.

Bayan shi sai aka ce mutum daya cikin newcomers ya gabatar da kansa. Papa Dolapo ne ya fara shima yana bayani ana dariya da kuma nuna tausayi musamman da yace ya baro matarsa da tsohon ciki suna jinjina masa.

Zayyan sai ya tuna cikin jikin tasa matar ya daga hannu "I am next please, please"

Dariya suka sa ana tsokanarsa ya dake yana basu labarin Mairama da Radhiya "babban farincikina kafin na taho Alheran ta iya kiran suna na"

"Fada mana ya take cewa" wani yace sauran na goya masa baya.

"Daaadaa"

Ihunsu ya karade dakin masu baccin ma sun tashi anayi dasu.

"Kuma nima matata tana da ciki amma sai mun koma zata haihu In sha Allah. Sorry Papa Dolapo kaine za'ayi ba kai"

Hadir yayi dariya yana cewa Zayyan yayi masa wayo "muna komawa da wata tara zaka ji Zainab ta haihu"

Tafawa suka yi wani mutumin Adamawa Austin Bakari dan kabilar Chamba ya fara bada labarin iyayensa tsofaffi wanda sun dora duk wani buri nasu akan cigabansa. Labarin iyayen nasa akwai ban tausayi domin dukkansu guragu ne da basu da mataimaki sai shi kadai. Dan albashin nasa shine cinsu shine shansu. Ya sanya sauran cikin yanayi na jimami kowa na fadin albarkacin bakinsa sai su ka ji wata muguwar kara mai razanarwa.

Basu gama da wannan firgicin da ya sanyasu daukan bindigoginsu cikin sauri ba kuma sai ga daya daga cikin masu patrol na wannan daren ya shigo bindigarsa tana kan saiti ya fada musu 'yan tawayen da su ka addabi wannan sansanin nasu sun kawo musu hari.

Idan da suna jin wai-wai, yau ga su zahiri a filin daga. Harbi ne yake tashi ko ta ina suka firfito kan kace meye wannan wurin ya kaure. Anyi musayar harsashi sosai duk da duhun dare sun sami damar fatattakar mutanen har da nasarar cafke mutum daya.

Wani bacci dama babu shi a lissafi maza suna filin daga. Kwana ukun farko sunyi su ne cikin rudani da tashin hankali. Da gasken gaske 'yan tawayen suke son korar sojojin Nigeria daga wurin. Akwai wuraren da suke tsammanin samun nasara su janyo mutanen garin domin a hadu a ture gwamnatin shugaba mai ci a lokacin. Rigima ta cikin gida a ganinsu mai zai kawo wasu baki da abin bai shafa ba a matsayin peacekeepers.

Kafin wani lokaci su Zayyan sun kara gogewa da halin da suka tsinci kansu yanzu. Shine ya koma yi musu limanci bayan tafiyar Abdulwahid Gbenga wanda ya kasance da shine limamin. Duk daren da babu gajiya sosai a tare dasu suna zaman hira a daki ko a waje. Su kunna wuta su zagaye wurin suna jin dumi saboda shigowar sanyi gadan gadan. Da safe kuma masu manyan mukami su ke jagorantar training dinsu don ba zama.

Watansu daya da kwanaki annobar cholera ta shigo kauyen da yafi kusa da inda suke. Garin kai taimako wurin fitar da marasa lafiyan zuwa asibiti a cikin gari wasunsu suka dauko ciwon suka kawo musu.

Cikin kwanaki bakwai mutum tara sun kamu. Amai suke yi sosai da gudawa. Suna ta kokarin neman agajin babban sansanin domin a kawo musu magunguna sannan a dauke marasa lafiyan cikinsu zuwa asibiti amma abu yaci tura. Ba wai sakon bai isa garesu bane, yaje amma su ma suna jiran command daga babbar headquarter saboda komai na soja bisa doka da oda ake yi.

Major Mustapha da ya ankara cewa sansanin su Zayyan ne ya matsa lamba sosai ranar da za'a kai musu maganin bayan kwanaki shadaya da fara cutar yabi bayan ma'aikatan lafiyan cikinsu. Su ma din sojoji ne amma hannuwan rigarsu daga dantse akwai wani farin abu da yake nuni da alamun cewa su likitoci ne.

Major Mustapha har yanzu bashi da magana sosai amma ya damu kwarai da kannen nasa Zayyan da Hadir. Motarsu ta iso sansanin a daidai lokacin da Zayyan yake limancin sallatar gawar Papa Dolapo wanda yayi ta fama da cutar ta amai da gudawa na kwana uku kafin rai yayi halinsa. Jikin Major yayi sanyi haka na likiticin da suke tare dasu. Zagaye sansanin nasu akayi da wasu irin wayoyi masu kaifi aka rubuta musu QUARANTINE da manyan harufa. Ma'ana an kebesu daga shiga ko fita har sai an sami kyakkyawan tabbacin cutar babu sauranta a tare dasu. Ana gudun su sanyawa wasu sojijin ko kuma su sakawa mutanen wani kauyen garin kai taimako.

Likitocin kadai aka bari suka shiga suma sun rufe jiki sosai da wasu kaya hatta fuskokinsu ba'a gani. Sunyiwa kowa allura sannan aka shiga bawa marasa lafiyan taimakon da ya dace. Ta bayan wayar suke magana da Major yana tambayarsu halin da suke ciki. Nuna masa suke yi babu wani abu lafiya kalau suke.

Ta'aziyar Papa Dolapo yayi musu wanda aka saka gawarsa a cikin motar da zasu koma da ita nasu sansanin. Idan sunyi sa'a za'a bari gawar ta koma Nigeria. Idan basuyi ba kuma to a nan za'a binne shi iyalinsa su dau hakuri.

"Shekaranjiya da aka toro wani troop din wannan wasikar tazo. Ta Lt Badmus ce"

Wasikar ya dago musu kowa jiki a sanyaye domin Papa Dolapo ne Lt Badmus.

Major Mustapha ya kara da cewa "duk da ban bude ba amma an fada min matarsa ce ta haihu. Zayyan makotanku ne ko?"

Kai ya gyada ya kasa cewa komai ya juya ya bar wurin zuciya tayi nauyi.

"Follow him Lieutenant" ya umarci Hadir.

Sai da ya ga sun shiga cikin wurin da yake mazaunin dakinsu ya koma motar da ta kawusu suka bar wurin.

**********

Rayuwar matan da mazajensu basa nan a barikin babu dadi. Ci da sha bai yanke ba tunda ana basu albashinsu to amma fa kowacce kullum kwanan duniya da fargaba take kwana matsawar ba mijinta ta gani ya dawo ba.

Mairama, Mami da Zainab dauriya suke yi kowacce tana son nuna ita ma jarumar kanta ce mai hakuri da juriya. A gefe daya basu fasa yiwa mazajensu addu'a da fatan alkhairi ba.

Awwab kusan ya dawo gidan Mairama da zama. A nan yake kwana idan ya dawo daga makaranta ya lalace wurin wasa da Radhiya. Sunyi shakuwar da har Mairama tana tabawa kyuya musamman idan zai fita. Kyalesu take yi tana fama da cikinta don ma laulayin yayi sauki yanzu.

Awwab ya fita da Radhiya sun tafi wurin Mami sai Mairama ita kadai a cikin gida. Hayaniya ta soma ji daga waje ta yafa mayafi ta leka. Can ta hango Zainab da wasu matan da suke tare sun zagaye wata. Fitowa tayi cikin sauri jin kamar ana kuka.

"Innolillahi wa inno ilaihi raji'oon....Oko mi tikú" kuka Maman Dolapo take tana tumani a kasa ga danyen jego.

Mairama ta

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment