Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shinkafa take so taci shiyasa Ummi ta koma gida ta dora. Idan ba haka ba tunda da Nasara zasu zo tasan sai sun hanata sakat da mita. Hadi na musamman ta yiwa dambun nan da kayan lambu da hanta gida ya kaure da kamshi. A wadace tayi shi kuwa saboda dawowar Radhiyan rana dayane da Zahra. Dama shirya abinsu suka yi wai sun dade basu hadu ba ana kewar juna. Mami ta aiko mata da farfesun kayan ciki cikin flask wanda ta hada dasu da zata yiwa Mama saboda a nan duka zasu ci abinci bangaren Ummin. Fauziyya tuwo tayi musu Zayyana 'yan mata kuma salad da drinks ta hada aka jere komai a gidan Ummi. Su Zahra da azahar zasu sauka Radhiya kuma sai biyar na yamma.


 Major jiran zuwanta kawai yake yi saboda murnar nasarar da ta samu na project dinta. Ita da Zayyana da ta gama secondary bana ya tanadar musu wani babban surprise.


Duka suna wannan abu Mama ta kira Awwab kwanaki biyu da suka wuce ta tambayeshi yaushe zai dawo ne yace sai nan da sati uku. Yanzu haka ya koma Germany babbar hedikwatar kamfanin nasu akwai abubuwan da zai karasa ya taho gida.


"Babu yadda za'ayi ka dawo ranar Juma'a?"


"Mama so nayi na gama komai yadda idan na dawo sai na cike wata biyuna kafin na koma aiki" ya bata amsa.


"Ni dai idan da hali ka taho ina son ka taho iyayenka na bukatarka. Ka kusa shekara fa rabonka da gida duka ka barmu da kewa."


"To Mama zanyi kokarin tahowa tare da Zahra tace min jibi zata taho. Idan na kwana biyu sai na koma na karasa aikin"


"Allah Ya shi albarka Awwabun Ummi"


"Amin amma naki ne yanzu. Ummi ta dade da yayeni ai. Kada ma kice musu zanzo ita da da Mami ba murna zasu yi ba."


Mama sai murna ta dana tarko zata sha kallo. Ta san idan Radhiya ta iso baifi sati biyu zuwa uku zata yi ba zata fara aikin da ya dawo da ita. Shi kuma kullum yana sama kamar tsuntsu har sai yaushe zasu daidaita ta ga ta fara shirin bikinsu.


An gama komai dreban Daddy ya tafi dauko masu fara sauka idan ya kaisu ya dawo daukar na biyun saboda motar tayi musu kadan kuma babu mai tuka ta Mama. Ibrahim sai laraba zai dawo shi kuma Emzee nasa zuwan sai kwana biyu kafin suna. Ya gama mita wai kiran me ake yi musu don za'ayi suna Ummi tace yaushe rabon da su taru lokaci guda duka. Kuma ma ana gama sunan Rugar Barkindo zasu je da Sumaila kafin Radhiya ta fara aikinta.


Su uku suka fito daga cikin airport din. Raji, Zahra da kuma Awwab da yake dauke da Femi. Mutan gida kowa yayi mamaki da murnar ganinsa. Yayi wani irin haske da kyau saboda kasar Ukraine akwai sanyi sosai. Ga girma da cika ido tamkar Major zamanin kuruciya. Dukkansu gidan Mama suka shiga ya mikawa Fauziyya Femi ya koma gefen Ummi da hannuwansa a mike yana jira ta ajiye masa baby Zayyan.


"Naki din, yanzu zaka zo Awwab sai dai in ganka kuma jiya ma munyi waya fa" tace tana bata rai.


"Ummi kin dena sona ne, a wayar ma fada kike yi min" yace yana dariya.


Sauran ma sai suka soma dariya ana tsokanar Ummi wai Mama tayi mata kwacen da.


"Ga sabo me zanyi da wannan katon nima. Na barwa Mama dama haka take so"


"Ke dai kawai don kinga munfi shiri yanzu shine zaki tashi hankalinki"


Sosai ta rinka zolayar Ummi ta kuwa hana shi baby din ya gama nacinsa ya hakura.


"Abincinku yana gidan Ummi. Zahra mijinki zai ci a can ko a kai masa dakin Awwab?" Mami ce tayi tambayar tana rike da Jawad da ya hanata zama yace wannan ya nuna wancan.


"Ni dai na koshi" Awwab yace ya tashi zai tafi daki.


Ummi ta tabe baki "kun gani irin halin nasa, mutum yaki cin abinci kullum koshi yake kira alhalin baici komai ba"


"Ummi ki rabu dashi yunwa ai ba kanwar uwa bace. Zata koro miki shi anjima"


Daga shi har su Zahran a gajiye suke. Dakinsa wanda aka gyara domin zuwan Raji suka shiga suyi wanka. Fauziyya ce ta yiwa Femi ya ware suna wasa da Jawad. Mami sai murmushi wadannan yaran jikokinta ne.


Sai karfe shida da rabi su Radhiya suka iso gidan suma a gajiye sai dai murna da doki bazasu bari taji da gajiyar jikin nata ba. Ita da Tante Nasara ne da Yousuf. Suna sauka daga mota tayi gidan Mama da sauri. Irin shigar da ta saba tayi na skirt mai fadi da riga iya cinya mai dogon hannu madaidaiciya wadda bata kamata ba bare ta fito da shape din jiki sai rolling din mayafi da tayi. Yousuf yana kallon yadda take sauri ya girgiza kai. Wani zubin kamar ta girma amma idan abin ya motsa sai tasa mutum dariyar dole. Yanzu ma saurin da take yi wai kada a gama rigata daukan baby ne.


Tunawa tayi da jan kunnen da Tante take yi mata akan rashin nutsuwa sai ta tsaya ta daidaita kanta sannan ta shiga da sallama. Mama tana zaune kasa hakuri tayi ta taso ta tarbi 'yar tata cike da farinciki.


"Radhiya kece kuwa? Bari dai maman taki tazo naji ko an baro min tawa a can ta kawo min ta bogi"


"Kai Mama" tace tana murmushi amma duk iya dauriyarta rashin ganin baby din yasa ta soma bata rai "Mama ina Daada?"


"Wai da gaske haka zaki rinka kiran sa?"


"Oui Maamon" Ta amsa da dariya tana mata salute suka sa dariya tare.


"Yana bayan Mami yanzu ta fita zata dawo am....."


Radhiya har ta kofa tafiyar da bata kai minti guda ba ta kaita gidan Mamin. Tana iya jiyo muryoyinsu Zayyana ta fada da sauri tana murna. Su duka Mami ce tace su fita a bar Mama tayi bacci ko ta huta dai.


Kan kace meye wannan sun cika gidan ba babba ba yaro daga kan Zahra har Zayyana. Murnar ganin juna suke yi sosai. Kowa yayi mamakin Radhiya ta canja sosai ta zama wata rabin baturiya. Ta dauki Jawad da Femi duka lokaci guda tana juyi dasu.


"To dai ku rage hayaniya kunga mijin Zahra yana ciki kada ku hana shi hutawa" Mami ta fada tana ficewa da baby a bayanta don bazata yarda suna wannan hayaniyar ta damka musu dan amana ba. Suje can su karata da nasu 'ya'yan tunda su da kwarinsu.


Zahra ta dora hannu a baki tana kunshe dariya "Hamma Awwab kai Mami, shi yafi kowa gudun hayaniya yanzu."


Dif Radhiya tayi gabanta na faduwa. Hamma Awwab yana cikin gidan bata sani ba. Da yaran a hannu ta juya zata fita ta rasa murna ce ko tsoro ko kuma bacin rai na shareta da yayi. Suna zuwa kofa Femi ya bare baki yana mikawa Zahra hannu.


"Tafi can nima bana yi da kai mai kyuya kawai. Kuma zaka ganni na goya Jawad ne na bashi chocolate" tace tana mikawa Zayyana shi tunda tafi kusa.


Kukansa da Raji yaji yasa shi bude kofar dakin Awwab kuma a lokacin ne tayi wannan maganar a kunnuwan Awwab din. Comb ne mai brush mai laushi yake sake kwantar da sumar kansa duk da yayi aski saisaye amma gashin ya soma fitowa. Dena brushing kan nasa yayi ya kallo kofar yayi sa'ar ganinta tana hararar Femi da ganin babansa yasa shi dariya.


Murmushin da baiyi niyya bane ya kwace masa yana kallon yadda take hararar yaro a gaban iyayensa kuma wai nan fushi ne kawai don yaki binta "Silly girl" ya furta a hankali idanunsa a kanta har ta fita daga gidan.


Ko da ta isa gidan Tante da Yousuf suna tare da Ummi suna cin abinci. Dukkansu dama yunwa suke ji tun a hanya. Wurin Ummi taje ta rungumeta tana dariya.


"Umminaaaa"


"Meye haka, tashi ni ki dagani" Ummi tace tana jin kunyar Tante ba don bata murna ta ganin 'yarta ta ba.


"Alheran rabu da ita kinji. Zuba abinci ki ci"


"Wanka zan fara yi. Ummi yaushe Emzee da Ibrahim zasu zo?"


"Kafin ki fara aikin in sha Allahu. Kiyi wankan sai kuci tare da su Zahra su ma basu ci ba muna gidan Zainab tun dazu ana hira"


"Ai sai an dawo da komai baya bari na shirya dai."


Dakinta ta wuce akwatunan Fauziyya da Zahra suna gefen inda Ummi ta tura mata nata. Su ukun a nan zasu kwana. Yousuf a dakin Emzee ita da Nasara a dakin Ummin. A can gidan Mami kuma Zayyana ce kawai sai Awwab da Raji.


Tana wanka tana tunanin wai Awwab yazo. Yaushe rabon su da haduwa. Gabanta har wani faduwa yake ta koma shiryawa a hankali. Duk yadda yace yana sonta ko sau daya bai nemeta a waya ba tunda ta tafi wai shi fushi. Kwafa tayi ita kadai. Ranta taji ya baci tayi siririn tsaki tana tazar gashinta da ya zarce kafadunta. Dama ita kanta akwai cika ga santsi shiyasa duk gyaran da take masa bai wuce amfani da shampoo masu kyau ba sai steaming da Tante take mata a shafe shi da mayuka. Tana daure shi yake kwanciya a kanta sai tayi rolling dinsa a keya ko tsakiya da ribbon. Ita da kitso sai sunzo Nigeria ko Nijar.


Doguwar riga ta saka ta wani yadi mai laushi anyi mata free style da dogon hannu. Karamin mayafi ta yafa bayan ta shafa hoda, kwalli da wani lip gloss light brown. Sassanyan body spray ta feshi jikinta dashi ta kuma saka turarensa a kayanta. Kamshinsa bashi da karfi very cool daidai da mata.


Ta bata lokaci sosai sai da tayi sallar magariba da isha ta fito. Fauziyya da Zahra ta gani da yaransu su Ummi suna gidan Mama har Tante.


"Kunci abincin?"


"Au wai da baki ci ba Radhiya? Shine kika makale a daki" Inji Zahra


Hira suka dasa suna yiwa juna tambayoyin yaushe gamo ta durkusa gaban kwanukan abincin da aka sauke a tsakar falon ta debi dambun yadda take jin zai isheta da farfesun a karamin bowl. Kan dinning table ta ajiye komai ta karkata kujerarta yadda zata ji dadin hira dasu Zayyana ta shigo tana waya da Emzee. Wuri ta samu ta zauna a kujerar kusa da Radhiya suka ji wannan deep voice din ta Awwab yana sallama.


Kowa ya amsa sallamar harda Yousuf da ya fito daga daki a lokacin amma Radhiya ta kasa bude baki kamar wadda ta hadiyi kota. Ko dago kai ma ta kasa yi tana rike da cokali a hannu tayi kasa da kanta. Zuciyarta na tsananta bugu.


Fuskar Awwab a sake yaje ya mikawa Yousuf hannu suka gaisa tare da fadawa juna sunayensu. Zama Yousuf yayi a kan daya daga kujerun falon suka gaisa da su Zahra.


Shi kuma Awwab ya tako a nutse zuwa dinning table din da yake kusa da bango daga bayan kujerar da Yousuf ya zauna.


"Bani wuri" yace da Zayyana yana mata nuni da kujerar da take zaune a kai. Da sauri ta tashi ta koma wurin su Fauziyya shi kuma ya zauna. Gabadaya ji tayi falon yayi mata kadan tamkar cikin akurki aka kulleta tare dashi. Bai ce mata komai ba ya karbi cokalin hannunta ya zuba farfesun akan dambun ya diba yasa a baki sannan ya mika mata. Sai a lokacin ta dago kanta suka hada ido. Babu wanda zuciya da gangar jikinsa bai aika masa da sako mai girma a tattare da dan uwansa ba. Sun chanja sosai shekara kusan uku ba yau ba. Sauke nata idon tayi da sauri ya sake mika mata spoon din.


Dan cije lebenta tayi tana tuno wani lokaci da abu makamancin haka ya taba faruwa dasu a Kano da Sumaila. Tana ji a jikinta ma mutanen falon kallonsu suke yi sai kawai ta dake ta karba. Idan bata basar ba zato zaiyi ta wani damu dashi ne har yanzu. Diban abincin tayi ta saka a bakinta cike da kunya. Kafin ta mika masa ya zura hannu ya sake karba ya ci sannan ya bata. Falon kamar anyi ruwa an dauke. Ita ta kasa kallon gefen da sauran suke shi kuma nasa idanun a kanta suke ba ma kallon plate din gabansa yake yi sosai ba. Yousuf yana ganin wannan abu yaji wani daci daci na taso masa dole ya tashi ya koma dakin Emzee. Awwab yayi wani murmushin gefen baki. Shi kuwa tunani yake wai dama Hamma din da take fada saurayinta ne ko me? Anya shakuwa zata sa Alheran cin abinci plate daya dashi kuwa? Ko da wasa duk zamansu bata taba kwatantawa ba. 


Sun cinye abincin dama ba wani yawa ne dashi ba Awwab ya janyo flask din "in kara miki?" Yace yana kallon zoben nan da ya bata har yanzu yana yatsanta


To a gaskiya ba koshi tayi ba ta langabe kai har yanzu taki yarda su hada ido "kadan"


Zubawa ta ga yana yi fiye da yadda take bukata ta kuma dago kai tana ware masa idanu "its ok"


Sai da ya zuba wanda yake ji zai ishesu su biyun ya sake mika mata spoon din taci ta bashi. Da za'a ce mata kyat a guje zata bar wurin saboda kunyar da take ji amma ita a dole sai ta basar kada ya rainata. Shi kam rabonsa da jin nishadi irin na yau ya manta. Ya kasa dena kallonta kamar ba Alheran dinsa ba. Tayi masa kyau sosai ga wata zazzafar soyayyarta tana fizgarsa kamar yadda ya kamu da sonta farkon haduwarsu. Ba don abinda tayi masa ba da yanzu kila suna da yara kamar nasu Zahra. Ba komai ya kawo shi gidan Ummi ba a lokacin sai zuwansa wurin Mama suka shigo da Tante Nasara. Mama da gayya ta dauko zancen Yousuf saboda yaji. Ai kuwa ta tayar masa da hankali.


"Haj Nasara wato kin mana kwacen 'ya sai munyi da gaske muke ganinta"


Dariya tayi tace "kuma ko na tafi wallahi a bar min yarinya ta sake. Ni da Yousuf duk mun shagwabata. Idan naji ba daidai ba ke zan fara kamawa"


"Bama zaki ji komai ba. Yaron nan naki akwai nutsuwa Nasara. Naji kamar Radhiya tace likita ne ko?"


Gaban Awwab sai da yayi wata rawa kamar ance masa anyi auren Radhiya ne. Likita??? Alheran da shegen son likitoci shikenan Ummi ta cuce shi wallahi. Wa ya sani ma ko sun fara soyayya an barshi a nan akan su Ghazalatu. Bai ko zauna ba ya wuce gidan Ummin sai yayi sa'ar ganin Yousuf din shine ya tsiri cin abinci tare da ita.


Juice din kankana mai sanyi ta zuba a glass cup bayan sun gama ci ta kurba sau biyu ta ajiye masa a kusa da hannunsa ta mike abinta ta koma wurinsu Zahra. Daukar cup din yayi ya shanye ya yi hanyar kofa tare da kiran Zayyana wai zai bata sako.


Wani shu'umin murmushi takeyi na abinda ta gama gani wanda dole ma ta labartawa 'yan uwanta Emzee da Ibrahim amma suna hada ido da ta ga kallon da yayi mata ta gyara fuskarta.


Radhiya na jin karar rufewar kofar ta tashi da sauri tana dafe kirji.


"Kuturin bala'i...wai... kunji kirjina kuwa? Har wani zazzabi zazzabi ne ya kamani fa" 


Zahra da Fauziyya suka kwashe da dariya harda kyakyatawa. Fauziyya ta karkace kai tana kallonta a tsaye hannuwa a kirji tace "shegiya Radhiya ashe kina nan baki mutu ba"


"Lallai ma Adda to wace wannan a gabanki?"


"Nufina Radhiyanmu dai mai balotelli ashe tana nan kin boyeta."


Dariya suke sosai su ukun Zahra tace "Fauziyya auren bakatsine ya koya miki zagi"


Juya idanu tayi tana dariya "Ke Radhiya auren Katsinawa akwai riba wallahi ku dena gulmar nan haka don naga take taken Hamma wata rana sai yayi hugging dinki a gaban mutane"


Kunya taji harda dora hannu a ka "haka kika koma maman Jawad?"


"Gaskiya ta fada miki ai, ni da wannan spoon exchange din da aure kuka yi kawai sai ayi wacce za'ayi ko Fauzi"


"Na shiga uku zasu bata yarinya" Radhiya tace tana dariya sosai.


"Wallahi balotelli na nan ashe kike disguising dinta da wannan hot chick din"


"Kinsan Allah Radhiya ki hana Hamma zaman lafiya...yarinya kill him with love sai ya dawo yana baki hakurin wannan fushin nasa mara dalili" cewar Fauziyya.


"Ni dai kiyi masa a hankali amma bance a sassauta ba" Zahra ta kawo tata shawarar.


"Ance muku son sa nake yi ne?" Ta basu amsa tana dage gira.


Fauziyya tace "Eh to gaskiya baki ce ba. Na fuskanci shi da Arifah kamar akwai wata a kasa don yarinyar tayi 100%. Kamar ance zata zo kuwa gobe zanyi kana confirming meye tsakaninsu"


Nan da nan fuskar Radhiya ta chanja  tana jin dan mutumcin da suka fara da Arifan ta waya yazo karshe. Zahra da Fauziyya sunyi dariya son ransu bayan ta fice zuwa gidan Mama.


**********


Washegari tsabar gajiya kasa tashi sukayi da wuri gashi sun raba dare suna hira. Ummi bata sauraresu ba ta shiga kitchen tare da Tante Nasara da ta biyota itama ta tashi da wurin. Cikinsu Fauziyya ce ta fara tashi taje ta karbi aikin kusan komai ita ta karasa shi kafin Ummi ta dawo daga yiwa Daadaa wanka don Radhiya ta lakaba masa daga zuwanta tace ita bata yarda a kira mata sunan baba ba.


Goma saura kowa ya tashi banda Radhiya. Tafi sati bata baccin kirki kullum yawon tsaraba da kuma kammala shirye shiryen project din ga tafiya a gabanta. Ummi tayi magana Tante tace a kyaleta ta gaji ne.


Sai shadaya ta tashi babu kowa a dakin. Wanka tayi ta gyara gadon sannan ta shirya cikin atampa blue da baki riga da zani wrapper. Tayi missing irinsu don bata cika sakawa ba a France. Ta gama daurinta mai kyau ta tuna ba zama zata yi ba sai kawai ta tuge shi ta tafi dakin Ummi. A can ta sami bakin mayafi mara nauyi ta yafa ta sake gyara fuskarta ta fito falo. Nan ma shiru, tana son magana da Yousuf amma bashi da sim din Nigeria. Ba ya nan yana wurinsu Awwab da Raji duk sun hadu dasu Daddy da Baba Hadir ana hira a gidan Mami.


Tasan basa wuce gidan Mama shiyasa ta tafi can. Ko neman abinci bata yi ba ta gaishe da iyayen nasu itama ta zauma zaman hira. Daadaa ta dauka ta shagala da yi masa wasa sai hamma yake.


"Kawo shi na goya shi bacci yake ji tunda akayi wanka bai koma ba" Ummi ta mika hannu za ta karbe shi.


"Don Allah goya min Ummi" tace tana ajiye mayafinta a gefe ta duka baya.


Ummi ta gyara tsayuwa "me? Rufa min asiri indai goyon ne ga masu karfi nan ki dauka"


"Tante" tace tana tura baki.


"Don Allah goya mata mana Mairama"


"Nasan halinta sarai. Dama can ba wani iya raino tayi ba bare yanzu da ta dade babu wani yaro a inda take. Da dai girki ne sai na sakar mata"


Zahra tace "Ummi ni zan bada labari. Cewa take fa na zunguri Femi don kawai taji muryarsa"


Dariya suke ta yi mata Tante na tarewa. Mama ma dai sai ta goyi baya "idan bata koya ba yanzu ba sai yaushe ni da nake fatan kafin shekara ta zagayo mun rike sabon jika"


"Yauwa Mama" tace tana murmushi ta sake dukawa.


Ummi tace babu ruwanta Mami ce ta goya mata shi aka daure shi sosai don Radhiya kam bata iya goyo ba. Ana goya mata shi kuwa ta mayar da mayafinta aka bude fuskarsa. Zama tayi akan kujera ko motsi bata son yi tana tsoron kada goyon ya kwance ya fadi. Tashi su Fauziyya suka yi zasu je suyi wanka Ummi tace bayan azahar su hadu duka da yaransu Awwab ya kaisu gidan Daddy Haroun su gaishe su. Bashi da labarin fitar tace Zayyana ta turo shi don tasan a waya bazaiyi yadda take so ba.


Can ya baro sauran mazan ya shigo falon da sallamar da ta tsinka zuciyar Radhiya.


Dauke kai tayi tana wasa da wayar hannunta ya shigo yana kamshi ya tsaya a bayan kujerar da take zaune. Na shiga uku tace a ranta tana jin kusancin dake tsakaninsu yana affecting dinta. Rikicewa tayi sosai amma bata so ta nuna shiyasa taki yarda ta dago kanta.


"Ummi gani"


"So nake bayan azahar ka hada kan kannenka ku je gidan mamanku Gambo ku gaishe su. Ga Raji da Yousuf ma duk ku tafi tare"


Shiru yayi amma yasan yanzun nan sai ta fara fada idan yaki amincewa ga mutane a wurin "to Ummi"


"Radhiya kun gaisa da yayanki ne?" Mama tace saboda dazu ya shigo sauran duka sun gaishe shi.


"Ina kwana" tace a hankali ko shi da yake bayanta baiji sosai ba. Kin amsawa yayi tunda dama baiji me tace da kyau ba.


"Nasara muje ki huta ko kin tashi da wuri ga gajiyar tafiya" Ummi tace suka tashi tare sai Mami da Mama. 


Mami ma sai tace zata tafi gida a turo mata Zayyana ta tayata girkin rana. Yana kallonsu duka suka fice Mama ma ciki tayi abinta dama duk hanyar barinsu tare nemanta take yi.


Dukuwa yayi da kansa gefen fuskarta taji tsigar jikinta na tashi abinda shi yaji fiye da haka "kin dena gaisuwa ne?" Taji yace muryarsa na dukan dodon kunnenta.


Muryarta ta sake ragewa tace "na gaisheka fa" 


"Sai a sake tunda banji ba"


Humm'umm bai san itama taci ganye bane yanzu ko. Kin magana tayi yana nan tsaye a bayanta har lokacin har ya soma amsa wayar Arifah tana masa barka da dawowa da sanar dashi zasu shigo gari da Mamanta kafin suna.


Haushi ya kama Radhiya da ta fahimci da mace yake magana. Gara ta bashi wuri idan ma akwai wata I love you da zamanta a wurin ya hana a fada sai yaji dadin sakewa. Tashi tayi da karfinta ai kuwa goyon nata taji gabadaya yayi sako-sako yana neman kwancewa baby ya fado. Yadda gabanta ya fadi sauri tayi ta duka jikinta na rawa ta tallafo Daadaa da hannuwanta ta baya. A hankali ta saki tana kokarin gyara gaban da ya kwance duka yaron yayi motsi a gigice tace "Hamma"


Yana da kallonta amma a zatonsa goyon zata gyara. Kuma tsabar tsoro ta kasa daga murya kada yaron ya tsorata ya fado.


"Hamma ka ajiye wayar mana" tace tana daga murya.


Sai lokacin ya cire wayar daga kunnensa "me kika ce?"


Kafafu biyu Daadaa yake dan shureta dasu alamun baya jindadin yanayin da yake.


Kuka ne ya taho mata kada ta saki dan mutane "Hamma please help" tace tana rike gaban zanin sosai kuma taki dagowa.


Wayarsa ya ajiye da sauri akan kujerar da ta tashi ya zagayo yana dukawa ya ga me ya sameta "meye?"


A rikice take bata san ya zasu kwashe da Ummi ba idan ya fado "goyon ya kwance"


"To ki gyara mana" yace yana mikewa ya gyara tsayuwarsa.


"Ban iya ba fa Hamma"


"Seriuosly?" Shima ya soma rikicewar ganin tana ta saka hannu daya a gaba daya a baya.


"Zai fadi" ta sake cewa da yayi wani irin zillo yana canyara ihu ya gaji.


"Kwace zanin da sauri" yace yana saka hannu a bayan yaron ita kuma ta kwance gaban "tashi a hankali"


Tana tashi yaron ya fada a hannunsa ya kankame shi a kirjinsa "are you okay?" ya tambayeta yana kallon yadda tayi wuri wuri.


"Allah Ya soni da ya fado..."


"Da sai mu haifi wani" yace yana kallon dimple dinta.


Idanunta ta dauke daga kansa maganar tana dada shiga kwanyarta. Duk wasu matakan nuna masa yanzu ba da bane ta nemesu ta rasa sai uwar kunyar da ya hadata da ita. Ya san me yayi mata amma sai ya wayance irin yadda ta taba yi masa.


"Silly girl, me kike tunanin ina nufi?"


"Ba nufinka idan ka haifi naka nima na haifi nawa sai mu kawo mu hada mata ba?" 


Kanta tsaye tayi maganar kafin ya gama gano lagonta ta tafi ta barshi da baby a hannu.


**********


"Wurin wa kazo?"


"Waye shugabanku a nan barrack din?"


Dariya ya basu suna masa kallon wanda bai san me yake yi ba. Barrack ai ba wurin da zaka zo kai tsaye bane idan baka san wanda kake nema ba.


Chibuzor ya rasa wa zaice musu. Sai da yayi sati a garinsu ana ta jajantawa iyayensa abinda ya same shi sannan da kyar ya kwaci kansa ya taho Sakkwato saboda cika alkawarin da ya daukarwa kansa da Zayyan. Bai san komai game da tsarin sojoji ba kamar chanjin mukami shiyasa kawai yace "Lieutenant Hadir nake nema" yana fata daidai ya fadi sunan.


Duk wani hargagi da zasu yi masa sunyi a ganinsu bai san me yake yi ba. Gashi dai a haka yayo fes dashi. Kin tafiya yayi tun safe har yamma ana ta abu daya yana tsaye a bakin gate. Wani ne cikinsu ya shiga ciki bangaren ofisoshinsu suna hira da wani da

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment