Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gaba akan zuwa gidan Gambo sai cewa yake zaije amma har yau shiru. Ni dama abin nasu da Hussaina ya dena bani mamaki. Biki ne zasu yi na huce haushi anki sakani cikin komai ba sai na kawo ido na saka musu ba"


"Kece babba fa Hassana, lokaci yana tafiya. Ina ganin ya kamata kiyi yunkuri da kanki kamar yadda Mairama ta baki shawara. Kunje kuna rigimarku ta mata kun bar min yaro yana hanging"


"Ya bar kansa dai. Idan yayi sake wani ya nemi Radhiya a Nijar shi ya sani"


Daddy ya mike "to ba dama na baki ba ki saka min yaro a gaba."


"Na nawa kuma" tace tana murmushi.


Washegari da yamma Major, Baba Hadir da Awwab suka tafi gidan gwamnatin Plateau da yake unguwar Asokoro a Abuja. Kofar gida ya fito da kansa ya tarbesu bayan an bude kusu gate sun shigo. Da murmushi a saman fuskarsa yace "wannan me Awwab ko?"


Awwab ya rissina kai Excellency ya kamo hannun damansa suka yi musabaha sannan suka shiga ciki.


"Nayi zaton zaku taho da iyalinku shiyasa muka taho da Arifah da mamanta. Bari na kirasu ku gaisa"


Waya ya kira sai ga matarsa Haj Rabi da Arifah sun fito. Suna shigowa idanun Arifah suka sauka akan Awwab mamaki karara ya bayyana akan fuskarta. Sunfi shekara da haduwa amma ina zata manta shi bayan bata sati biyu bata kira shi a waya ba. 


 "Captain M.A Mustapha?" Tace tana rike baki.


Excellency ya saki fuska "kin san shi ne?"


Murmushi tayi ta gyada kai tana hango nasara a tattare da soyayyar da take yi masa. Ace gashi har cikin gidansu kuma da ga mutumin da Dad dinta ya daukesu da matukar kima a idanunsa.


"Ikon Allah, ashe sun san juna mu sai yanzu Allah Ya nufa"


Arifah dai murna kamar me ta fita taje ta sake kwalliya ta tura wata mai aikin ta kira mata shi zuwa garden din gidan.


Mai aikin kuwa taje ta isar da sako gashi a gaban mahaifinta dole ya tashi. Shi gabadaya tunaninsa ya kasa tuna wacece ita.


Takunsa kadai abin kallo ne a lokacin da yake tahowa gareta cikin shiga ta manyan kaya. Dinkin irin wanda matasa suke yayi ne riga ta dan zarce gwiwa amma hannunta da kadan ya wuce gwiwar hannu. Yadin yayi masa kyau sosai babu hula a kansa sai gyaran fuska da yayi batare da sake aski ba.


Tana zaune akan wata kujera karkashin wani abu da akayi da kaba ya bada sassanyar inuwa ya iso ya tsaya bayan tafiyar wadda tayi masa jagora.


"Zauna mana" Arifah tace tana murmushi.


Kamar bazai zauna ba sai kuma dai ya tuna cewa nan gidansu ne ga kuma irin karamcin mahaifinta ga nasa iyayen. Tunda ya zauna bata ce komai ba sai aikin kallonsa tana yaba komai na halittarsa.


"Ya dai?" Ya tambayeta yana hade rai.


"Hmmm Captain baka ganeni ba da gaske?"


Kalmar Captain din kawai tasa ya tuna a ina ya saba jinta "kece mai kirana?"


"Arifah sunana" ta bashi amsa da murmushi "Captain ka wahalar dani ko ince kana kan wahalar dani sai kuma ga ka a gidanmu abinda ban taba zata ba"


"Allah Yasa dai bazaki sa a kulleni ba a yar da key din"


Dariya tayi "ko daya sai dai ina neman sanin dalilin wannan mugun jan aji da yakamata ace ni nake yi maka"


Kai tsaye yace mata "na sha fada miki na kusa aure"


"Na dade ina kiranka Captain amma har yau ba'ayi auren ba sai kora da hali da kake yi min."


Kunyar abubuwan da ya rinka yi mata yaji da kuma rashin dacewarsu "kiyi hakuri maybe mun fara on the wrong side. Sunana Awwab ke fa?"


"Arifah"


"Arifah ina da wadda nake so sabani ya shiga tsakaninmu. Kiyi hakuri idan hakan ya bata miki amma iya gaskiyata shine bazan iya hadata da kowa ba"


Ya dade yana fada mata shiyasa bata yi wani mamaki ba "she is lucky amma nima zan gwada tawa sa'ar idan ka amince"


"Kada muyi haka dake Arifah. Akwai danganta mai girma yanzu tsakaninmu. Mahaifinki ya taimakawa nawa iyayen kamar yadda naji labarin wadda nake so din itama nata mahaifin ya taimaki naki. Mu duka wata alaka ce tsakaninmu da bazan so soyayya ta sake batawa ba kamar yadda tayi min a abaya."


"Wai kana nufin Alheran kake so?"


"Ya akayi kika gane?"


"Saboda ita kadai ce wadda nasan babanta ya yiwa Dad abinda kullum baya gajiya da bada labarinsa yana binsa da addu'a"


Awwab da ya koma mai wuyar sha'ani sai gashi saboda hirar Alheran ce ya sake yana yiwa Arifah labarinta. Taji tausayinsu matuka da taji dalilin rabuwarsu.


"Na hakura ba don bazan iya ba sai don Alheran din nan da ban taba gani ba nasan tafi karfina indai a kan ka ne. Dad dina da naka duka owe their lives to hers. Ina son Dad dina dole ne in taya shi kyautatawa Alheran da family dinta"


"Nagode sosai Arifah" Awwab yace yana mikewa tsaye.


"Tunda na zama kanwarka Allah Yasa ka dena kin daukar wayata"


Yana tafiya ta jiyo shi yace "daga yanzu da kaina zan rinka kiranki"


Kyakkyawar alaka da aka gina bisa gaskiya da amana ita ce ta cigaba da wanzuwa tsakanin gidajen mutanen nan guda hudu. Wato gidan gwamna, Major, Baba Hadir da Mairama matar Tureta.


His Excellency Nasiruddeen ya cika alkawari domin kuwa har cikin gida aka je aka dauko masa Maikudi yasa aka kulle shi. Idan mutum yana cin kasa ya kiyayi ta shuri.


Radhiya ta mayarda kai sosai a karatunta Nasara tana goya mata baya. Akwai shakuwa mai karfi tsakaninta da Yousuf yana bata kulawa sosai duk domin sharar fagen gabatar da soyayyarsa gareta a gaba. Abubuwa da dama na halayenta rashin Awwab ya sanyata ta barsu sai dai shagwaba kam ko Zayyana albarka. Tazo Nigeria daga Niger ta zaga dangi sosai lokacin Awwab ya koma aiki. 


A lokacin ne kuma akayi bikin Ghazalatu da Nura. Hadadden gift Awwab ya aiko mata dashi na aure amma bai sami damar zuwa ba saboda training course da ya tafi na shekara daya a Ukraine zai sami karin mukami idan ya dawo. Habaici da bakaken maganganu duk da Mami tana bakin kokarinta akan kannen nata sai da suka rinka yaba mata. Ummansu har tara su tayi ta sanar dasu cewa saboda zumuncinsu kada ya baci Mairama ta raba 'yarta da Awwab gashi har yanzu ya kasa aure. Hussaina sai cewa tayi dama can kwadayi ne ya kawosu da suka ga anfi karfinsu sai suka ja baya. Maganar ta yiwa Mami ciwo amma bahaushe yace wai gani ya kori ji. Idan kuwa hakane to zata basu mamaki su duka wallahi. Bazata ce musu komai game da tsatson da Radhiya ta fito ba sai dai ido ya gani anayi.


Duk wannan maganganun anyisu ne ranar Kamun Ghazalatu a Katsina kuma Mama taji saboda cikinta ya fara nauyi tafi son zama wuri daya shiyasa tana dakin suke yi. Da daddare suna dakin Mami a gidansu na Katsina daga ita sai Ummi ta tayar da maganar.


"Mairama dan taso muyi magana don Allah" 


"Allah Yasa lafiya uwar 'yan hudu"


"Ba amin ba wallahi wannan addu'a sai 'ya'ya"


"Matsoraciya, tunda kika kunso gara kiyi da yawa kawai"


Dariya tayi tana fatan Allah Ya kawowa Ummi miji tayi aure itama.


"Dama magana ce akan Radhiya da Awwab. Ki taimaka mu fitar da Mami kunyar marasa kunya Mairama. Dazu idan kinji irin kalaman batanci da suke fadawa Mami a gidan da akayi kamu sai kin kusa kuka."


Shiru Ummi tayi tana nazari. Itama sun yi da ita batare da sun gane ita bace suka zageta tas akan ta likewa Mami ita da 'ya'yanta. Ai kuwa zata taya Mami nuna musu kurensu ita ce fa Mairo 'yar kunamar Malamijo. 


"Zainab kisha kuruminki kawai ki zuba min ido wannan karon. Ni har za'a nuna min rashin mutumci ina diyar Ali Gidado? Kawaici ne kawai nake yi domin inganta musu zumunci amma tunda abin ya zama haka idan kinje gida ki fadawa Baba Hadir suyi magana da Major. Awwab na dawowa daga Ukraine a daura musu aure da yarinyar nan"


Da karfi Mama ta mike saboda farinciki har sai da cikinta ya amsa amma bata hakura ba ta rungume Ummi.

"Wani sha'ani sai bikin 'yar mutan Agadas. Kin biyani ko ba soso da sabulu kin wanke ni da kyau. Su Awwabu za'a shiga sahun manya kice"


Ummi ta dafe kai da kunya "wannan zancen ba dani ba"


"Wai da mu fara gyara amarya tun yanzu in soma aike" ta fada da shakiyanci ai kuwa tayi nasarar korar Ummi daga dakin tana cewa abu kusan wata goma gaba take wannan tunani tun yanzu.


**********


"Is it true you be Aboki?" Inyamurin ya tambayi Zayyan da gurbataccen turancinsa wanda aka fi sani da pidgin english.


"Ni bahaushe ne idan abinda kake nufi kenan" ya amsa masa da turanci cikin calm and gentle voice dinsa.


Ko a zaman kurkuku Zayyan ya fita daban saboda yadda zuciyarsa take mai kyau Allah Ya sanya masa kwarjini da haiba a cikin mutanen da yake.


Inyamurin ya daka tsalle yaga dan kasarsu ya rungume shi. Zayyan bai nuna kyama ga mutumin ba shima ya rike shi. Magana ya koma yi da normal turanci


"Sati na biyu a Wing B cikin wahalar mutanen da muke daki daya dasu. Wani Warden (gandiroba) ne jiya yace idan sun sake tabani nace ni dan uwan Zayyan ne."  Kallon Zayyan din yayi sosai "kasan me ya bani mamaki?"


"Sai ka fada"


"Ina ambaton sunanka nace kasarmu daya suka watse. Nayi mamaki matuka gaskiya. Who are you?"


Bai cika son yawan magana ba amma kuma baya son wulakanta mutum ba farko da ya gani a wurin da yake matsayin dan uwansa na kasa daya. Takaitaccen tarihin rayuwarsa ya bawa mutumin sai gashi yana hawaye.


"Yanzu kai soja ne kuma kayi wadannan shekarun babu wanda ya taba nemanka?"


"Nawa kundin qaddarar kenan"


"Aboki ni sunana Chibuzor Kalu. Matata ce 'yar kasar nan amma a UK muke da zama. Ta haihu ne tazo ganin gida da baby, to dama munyi da ita ni zanzo daukarsu. Ni dai bansan yaya akayi ba aka kamani da kwayoyi a jakata. Ka ganni nan ko taba bana sha amma anyi mana kudin goro kowa ya ga Igbo man sai yayi masa kallon mai ha'inci. Sun kulleni ne ana can ana binciken ainihin wanda ake zargin ya saka min kwayoyin a cikin kayana"


Zayyan ya tausaya masa domin yakan sami labarai akan masu harkar kwayoyi irin tsananin da suke shiga idan an kama su.


Shi da yake da saurin sabo sai gashi Chibuzor ya zama tamkar wani dansa. Ko ina tare zaka gansu a cikin prison dinnan har aka gama zaman shari'arsa na tsahon wata bakwai ana fafatawa aka gano sharri ne kawai aka yi masa. Ranar da zai fita yayi kuka har ya gode Allah. Bai san haka shakuwa take da tasiri ba sai da zai rabu da Lt Zayyan Muhammad Tureta.


"Sir please ka bani address dinka, a ina zan sami Maman Alheran?"


Karo na farko tun bayan shigowarsa wannan kangi Zayyan ya sami kansa da zubar hawaye. Shin yasa rai da zai sake shakar iska freedom ko kuwa? Akwai rabon idanunsa su sake kallon na Mairama masoyiyarsa da Alheran da kuma abinda Allah Ya azurtasu dashi? Rungume Chibuzor yayi yana hawaye ya fada masa sunan barrack din da ya zauna.


"Tell them Lieutenant Zayyan Muhammad Tureta is alive"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Alheran ZM Tureta"


Gajeren faduwar gaba taji lokacin da daya daga cikin malamansu kuma supervisor dinta ta leko da kanta ta kofar seminar hall din ta kira ta.


Duka daliban da suke aji daya tare su kadai suke zaune banda ita. Nasara tana zaune a kusa da ita cikin kujerun da aka zube a korido din domin zama ko hutawa tana karfafa mata gwiwa.


"Tante" Radhiya tace kamar tayi kuka.


"Ina nan ina jiranki kinji ko...jeki" Nasara tace da murmushi.


Kungiyar ma'aikatan jarida na kasar France ne suka rarraba kudade a fitattun jami'o'insu suna neman zaratan dalibai. Gasa ce suka saka na neman zakaran gwajin dafi inda aka baiwa daliban damar kowa ya kawo wata matsala da yake tunanin zaiyi kyau a bude program a kanta imma ta gidan TV ko rediyo domin wayarwa al'umma kai da kuma taimakawa ga wadanda abin ya shafa.


Dalibai uku ake son zaba a kowacce jami'a 'yan aji uku ko hudu za'a basu grant (tallafi na kudi) suje suyi aikin da suka kawo na wata shida su dawo makarantar dashi. Wandanda suka yi nasara kofa ce babba zata bude musu ta arzikin samar da program da kila duniya duka sai tasan da zamansu. Radhiya ta kusa wata tana ta bincike akan topic din da ya kamata tayi karshe ta tsaya akan abu guda bayan tayi magana da Ummi da Baba Hadir. Su kadai suka sani sai Nasara. Jiya ko runtsawa ta kasa yi ta gama hada slides na power point da zata yi presenting sannan ta dukufa sallah da addu'a. Yousuf shine babban malaminta na addini bayan ta dawo kasar. Bakin gwargwado tana da nata ilimin tun a gida don kafin su gama secondary ita da Emzee sunyi sauka. To amma ilimi na sauran fannonin addini Yousuf yayi fice wurin zaburar da ita a kansa shiyasa matsayi daban ta bashi. Tana girmama shi sosai idan suna tare sai ka rantse wata muguwar nutsattsiya ce babu rigimar nan.


Sai da ta gama addu'ar Annabi Yunus da salatin Annabi SAW sannan ta kalli zoben hannunta mai harafin A, aa hankali ta kaishi bakinta ta sumbata. Computer dinta ta bude aka jona ta projector wakilan kamfanin Dupont Broadcast Corporation (DBC) da malaman jami'ar da suke musu alkalanci suka fuskanceta.


Bakar abaya ta saka mai kyau da karancin ado irin wadda wuyata zagaye ne kawai bai sauka kasa ba. Adon duwatsunta maroon ne shiyasa tayi nadi da maroon din mayafi tana sanye da loafers suma maroon da suka zame mata yawancin takalman zuwa makaranta. Hall din an kashe duka fitilu babu sauran haske sai wanda yake fita daga makeken screen din projector din.


Bata ce musu komai ba sai wani gajeren video na sakan goma sha biyar da ta kunna musu. Filin yaki ne baka jin komai sai tashin bomabomai da harbi gami da ihun mutane da kukan yara. Wuri ne na firgici da tsoratarwa ga wanda bai san yaya mutanen da suke da 'yan uwa a wuraren da rikici ke ballewa suke ji ba. A tsakiyar wannan tashin hankali sojoji ne wani ya kwanta akan yara biyu ya toshe musu kunne saboda karar bomb. Wani ya dauko wata mata mai tsohon ciki yana gudu da ita ga jini ya wanke masa fuska alamun shima yaji rauni. Wani likita ne a cikin sojojin ya duka gaban dan uwansa soja da hannunsa ya fita saboda tashin bomb. Kai jama'a mutane ne a cikin tsanani basu san ina suka dosa ba. Duka mutanen da suke wurin tuni Radhiya ta kwashe hankulansu da tunaninsu ya dawo ga abinda zata gabatar.


Hoton karshe ya tsaya ne akan wadannan sojoji kowa da abinda yake yi na ceton al'ummar da babu lallai ma na kasarsa ne ta dora musu katon question mark (alamar tambaya).


Cikin turancinta da sautin muryarta zai baiwa mai sauraro damar gane cewa faransanci ya zaunu a bakinta tace.


"Who are they?"


Alkalai basu san me zata gabatar ba amma sun fara gyada kai in approval.


Murmushi tayi da ya kawata fuskarta ta dora da cewa "My name is Alheran and this. Is. The Military Voice"


Hotunan screen din sai suka sauya inda zaka ga wani sojan rungume tsakanin iyayensa, wani da 'ya'yansa, wani amaryarsa, wani matarsa da tsohon ciki wani kanne da yayyensa suna dariya, suna murmushi ko suna hawaye.


"Tun farkon lokaci yana daga abinda yake daga darajar kasashe yawan rundunar sojoji ko mayakansu. Sai dai mukan manta da cewa wadannan sojoji 'ya'ya ne, maza, iyaye kuma 'yan uwa ga wasu. Suna tafiya filin daga a lokutan da iyalansu suke tsananin bukatarsu. Sauran mutane suna zuwa wurin aiki su koma gida soja idan ya fita filin daga shi da jindadi sai ranar da yayi sa'ar komawa ga iyalansa lami lafiya. Cikinsu ko kunsan mutum nawa ne suka tafi iyalansu suna kuka suma suna na zuci amma basu dawo ba?"


Hotunan suka karkata ga iyalan sojoji suna kuka, wani wurin kuma gawarwarkin sojoji ne, wasu kuwa sojojin ne da nakasar rasa wasu bangarori na jikinsu.


"Kama daga KIA (killed in action), MIA (missing in action), dawowa gida da nakasa ta gabobi ko lalurar da take shafar kwakwalwa wadannan sojoji suna wahala matuka a duniya. Amma duk wanda ya dawo da wata tawaya ta jikinsa sai ya zama mutum mara amfani ga al'ummarsa. Babu abinda suka sani ko suka iya sai tsaro amma tunda basu da lafiyar yinsa shikenan amfaninsu ya kare. A haka rayuwar sojoji nawa muka manta saboda babu abinda zamu mora a tare dasu. Idan sun mutu iyalansu kadai ke da asara. Wasu sai dai su koma garuruwansu babu abokai, wasu matansu sun kasa zama dasu, yaransu kila sun girma sai dai su kare rayuwarsu cikin kadaici da jin kawunansu tamkar basu da wani sauran amfani"


Hotunan da suke ta tafiya akan screen din masu ban tausayi ne da taba zukata. Wani ka ganshi a gidan giya, wani fuska da jiki bab u gyara, wani ya zama manomi a kyauye, wani yana nan banda tuna lokutansa a filin yaki ko azabar da yasha a hannun abokan gaba babu abinda yake yi. Wasu ma karamin hauka suke dawowa dashi duka a dalilin bautawa kasarsu.


"Da wannan nake rokon ku bani dama in zaga in fito da rayuwar sojojin nan duniya ta sansu ta kuma san cewa ko yaya suka dawo duk abinda ya samesu ya faru ne a kokarinsu na kare dukiya da rayukan al'umma. Ina so sojoji da iyalan da suka bari duniya ta kasa dubansu su sani cewa har yau har gobe suna daga cikin mutane mafiya girman daraja a bainar al'umma saboda sadaukarwasu garemu. Nagode"


Fitilun hall din aka kunna gabadaya mutanen wurin suka mike tsaye ana tafawa Radhiya. Cikin matan kuwa harda masu zubar da hawaye saboda tausayi daga hotuna da video din da ta nuna musu. Sallamarta akayi akace ta jira tare da sauran da suka gabatar da nasu. Sai bayan kusan awa guda an gama sauraron kowa aka kirasu domin jin sakamako.


Tante Nasara tana nan a korido din ta kasa zaune ta kasa tsaye motsi kadan sai ta kira Ummi tace wallahi ta saka mata 'ya a addu'a. Ummi sai dai tayi dariya tace ai tana yi.


"Tanteeeee" taji muryar Radhiya kafin ta farga daga ina ne taji ta rungumeta tana murna.


"Nayi ta daya Tante, zanyi Military Voice a Nigeria da Nijar"


Nasara ta rungume Radhiya tana ta murna. Ita take tuka su zuwa gida  yayin da Radhiya take ta waya da mutanen gida. Ummi, Mama da Baba, Daddy da Mami, Mammee dasu Alh Sidi. Ibrahim da Emzee babu wanda bata kira ba tana sanar dasu cewa su fara shiri tana nan tahowa Nigeria nan da sati daya.


***********

Sai kai kawo Ummi da Mami suke yi a hanyar dakin theatre din da aka shiga da Mama. Ciki ya wuce kwanakin da ake sa ran haihuwarsa harda sati takwas yana cikin wata na goma sha daya yayi mugun girma. An so inducing dinta da wuri taki saboda tsoro ga dadewa bata haihu ba. Daga baya da kyar Baba Hadir ya lallabata sai da Ummansa da Mamanta suka sa baki ma. Shine aka yi inducing din nata kwana biyu tana fama da matsananciyar nakuda amma haihuwa shiru. Yammacin rana ta biyu ne aka yanke shawarar yi mata CS.


Baba Hadir yana mota hankalinsa ya tashi matuka. Shiyasa ya bar inda su Mami suke kada su ga shima namijin yayi rauni. Zainab dinsa bazai taba iya hada soyayyarta da ta kowa ba. Tayi masa abinda har ya mutu bazai taba iya biyanta ba. Inama cikin zai dawo jikinsa da ya hutar da ita. Text din Ibrahim ne ya shigo wanda tun safe yake yinsu ya kasa amsa masa. Sauran kwanakin tana daurewa ta dauki wayarsa su gaisa. Sauransa jarabawa biyu ya gama level 2. Ummi ta riga shi gamawa dama ba department dinsu daya ba amma tare suke tafiya a karatun. Kwana biyu taje tayi a Sumaila ta wuto Abuja saboda sanin halin da Mama ke ciki haihuwa ko yau ko gobe. Yau da ciwo yaci karfinta har aka shiga cs din Ibrahim bai sami kowa ya daga wayarsa ba shiyasa gabadaya ya kasa sukuni.


Baba Hadir yana kokonton amsar da zai turawa dan nasa Major ya kira shi ba wai don ya amsa masa da baki ba, ya dai san zaiji me yace.


"Hadir ka bar mata a ciki suna ta nemanka an fito da Zainab. Mun sami namiji"


Kabbara Baba Hadir ya shiga yi a zuci yana ta kokarin ya iya fitar da sauti da bakinsa ma. Waye zai karyata Kadaitar Allah a matsayin Ubangijin talikai? Shi Hadir da ya shafe shekaru yana kwance sai yadda akayi dashi. Fitsarinsa da kashinsa tun dansa Ibrahim yana da karancin shekaru yake wannan dawainiya shine a karo na biyu ya sake haihuwa da Zainab. A take ya turawa Ibrahim kyakkyawan reply sannan ya fita daga motar ya koma ciki.


Dakin da aka tura Zainab din aka nuna masa. Ummi na rumgume da baby din an nado shi da shudin shawl mai laushi sai raba idanu yake yi. Mami kuwa ta saka shi a gaba wai yasan yana son kallon duniya me ya zauna yiwa kanwarta a ciki.


Sai da ya dan kwankwasa sannan ya tura kofar ya shiga. Zainab baki ya mutu tana kwance allurar anasiziya bata gama sakinta ba. Sai dai da yake ta ido biyu ce tana jin me suke yi tana murmushin wahala. A kusa da ita ya zauna a gefen gadon Ummi ta dora masa jajirinsa a hannuwansa da ya bude.


"Zz..Zayyyyan" Baba Hadir yace da dukkan dagewar da zai iya yana rungumar yaron a jikinsa.


Idanun Ummi tuni sun ciko da kwalla har ta fara zuba Mami ta riko hannunta suka fita domin a basu wuri.


"Hadir magana kayi?" Mama tace tana kallon fuskarsa.


Murmushi yayi mata yana shafa kanta da hannu daya ya kuma cewa "Zayyan"


"Alhamdulillah...don Allah ka rinka kokarin magana kaji. Ina son jin muryarka Baban Ibrahim da Zayyan"


Kai ya gyada yana ta murmushi idanunsa na yawo tsakanin baby Zayyan da Zainab. Tun ranar da aka tabbatar mata da cewa namiji ne ta sani ko bai fada ba sunan yaronta Zayyan. Ko yana da rai tasan su biyun masu musayar sunayensu ga 'ya'yansu ne bare kuma daya baya nan ya bar musu wawakeken gibi a zukatansu.


Kafin gari ya waye duk wanda ya kamata yaji haihuwar nan yaji. Iyayen Mama da na Baba murna ba'a cewa komai. Har waya suka yi suna yiwa juna barka. Soyayyar nan daga Allah ce. Dubi shekarun da tayi a gidan Alh Musa sau daya tayi bari sai gashi daga samun lafiyar Hadir anyi ciki har an haife. Wannan shine dan soyayya inji Mami.


Radhiya kamar ta jawo tafiyarta da ta rage kwanaki uku. Wani babban mall ta shiga ta jidowa kanin nata kaya na ga na fada ta kara akan tsarabar da ta gama hadawa. Duk zuwa gida sai tayi wannan tsarabar saboda bata ga me zata yi da kudaden da suke jibge a account dinta ba. Mijin Nasara yayi daga Nijar kakaninta kamar masu gasa da juna wurin yi musu aike ita da Emzee. Ga uwa uba His Excellency ya mayar dasu kamar masu daukar albashi.


Kwananta Mama biyu a asibitin aka sallamota. Ummi ita ce uwar da tsakaninsa da Mama shayarwa ce sai kuma dare idan zata koma gidanta. Mami kuma duk wata bukatar maijego tana wuyanta. Baba Hadir gani yake sunfi kowa sa'ar zumunta a duniya. Babu ta inda jini ya hadasu amma dangantakarsu kullum kara karfi take yi.


Fauziyya ta matsawa Bilal da zaiyi tafiya Lagos wani aiki ya kaita Abuja ita da Jawad dinta da ya fara yawo ko ina. Zahra ma Radhiya tana sayen ticket ta fara yi mata famfo har yau bata taba ganin Femi a zahiri ba. Ba don yaso ba Raji yace zai kawota amma da sharadin idan ya kasa hakuri zata ganshi kuma dole su tafi. Shima yana son zuwa gaishe da yan uwan iyayensa ne a Osun state shine zasu fara zuwa kafin.ya dawo da ita Abuja.


Gidajen uku sun fara shiri duk da an dage suna ma sai sunyi sati biyu maijego ta kara samun sauki.


Yau da wuri Ummi taje ta yiwa baby wanka ta dawo gida. Dakuna uku ne a gidan daya nata sai na Emzee da Radhiya idan sun zo hutu. Rigima irin ta Radhiya wai dambun

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment