Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya aka cigaba da harbe harbe.


Col. Nasiruddeen ya sauka ta daya barin yasa gudu yayin da aka duba masu rai cikin 'yan tawaye harda Zayyan aka yi awon gaba dasu.


Taimako daya aka yi musu shi da sauran masu ran an cire musu bullets din jikinsu. Amma an gwada musu izaya da azaba nau'i daban daban domin su fadi inda sauran suke abu yaci tura. Sauran uban taurin kai ne yake damunsu shi kuwa Zayyan banda rashin sanin komai ya dage shi dan Nigeria ne. Da suka ga ya dage sai suka yi bincike akan unit da yace a cikinsu yake. Tashin farko akace wani mai suna Hadir Murtala ne kadai ya tsira a cikinsu tare da mutum daya daga wani unit din wato Major Mustapha. 


Abu na ceton rai sauran ma kowa ya fara cewa shima wani ne baya cikin wadannan 'yan tawaye. Zasu fara dogon bincike aka kaiwa wani babban barikin sojojinsu mummunan hari wanda ya janyo gabadaya mutanen da aka kama harda 'yan wani kauye da tsautsayi ya ritsa dasu duka aka maka su a kurkuku.


Da fari Zayyan kusan hauka yayi a wurin. Tunanin iyalinsa yake yi. Mairama da Alheran da cikinta da yake tsammanin ta riga ta haife shi yanzu. A wane hali suke koma waye yake duba iyalansa? Yakan dauki tsahon lokaci yana zubar da hawaye masu zafi da kona zuciya. Uzurinsa na cewa shi ba dan tawaye bane bai karbo ba domin mutanen da ake kamowa sun hada da magidanta da matasa bisa tsautsayi. Kowa cikinsu kuma ya dage shima ba dan tawaye bane. Sai ake rasa gane waye mai gaskiya da makaryaci. Dadin matsakar kasar babu zaman lafiyar da zai bada damar a bata lokaci wurin sauraren korafinsu. A irin haka sojojin kasashe da dama suke riskar kawunansu a kurkuku daga zuwa kai dauki ga kasashen da suke cikin rikici.


Sannu a hankali ya karbi kaddararsa da hannu bibbiyu ya fawwalawa Allah lamuransa. Baya shiga harkar kowa a wurin sai ma shi da akan sami masu shiga tasa. Sai ayi masa duka bai ko daga yatsa. Rayuwarsa ta kuntata komai ya fice masa a rai. Daga baya ne ya sake rungumar addini fiye da baya har kusan kowa ya sallama masa hadda wadanda ba musulman ba kuwa. Zaman lafiyarsa da yanayin mu'amala yasa ya shiga zukatan jama'ar wurin. Zayyan Muhammad Tureta tun asalinsa mutum ne mai shiga rai shiyasa a nan din ma ya zama na kowa. Babu wanda zai yi yunkurin taka Zayyan wasu basu saita masa zama ba.


Col. Nasiruddeen yayi nasarar komawa gida ga iyalinsa. Satinsa guda da komawa yasa aka binciko masa barikin su Zayyan. Daga can ya sami kwatancen gidan iyayensa. Da kansa yaje Sakkwato ba sako ba har kofar gidansu. Da yake wahala bata yankewa su Mairamu ba a wannan lokaci da yasa ayi masa sallama da dan uwan Zayyan ba wanda ya fito sai Maikudi. Ya ga mutum a fige saboda tsabar wahala sai hanci dan firit. Yanayinsa gabadaya kama yayi masa da mutanen Nijar yayi zaton aiko shi akayi saboda basu yarda da bayanin da yayi musu ba. Rufe ido yayi ya maimaita masa cewa Mairama ta haifi da ba rai, ita da 'yarta kuma sunyi hatsari sun mutu. Col. Nasiruddeen yaji babu dadi jikinsa yayi mugun sanyi ya koma Jos wurin iyalinsa cike da damuwa. Zayyan ya rasu a dalilin ceton ransa kuma iyalansa ma duka babu su. A satin yaje ya kai takardarsa ta barin aiki. A wurinsa rayuwar soja ba tasa bace. Asibiti ya koma neman aiki sai dai lokuta da dama idan ya ga yawaitar jini musamman idan hatsari ne jikinsa ya rinka rawa kenan. Likita da tsoron jini aiki bazai taba yiwuwa ba bisa dole ya hakura ya tsunduma cikin harkar siyasa ka'in da na'in.


***********


SABON SHAFI
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Asibitin Nasarawa aka tura su Awwab domin samun kwararren likitan ido. Da za'a basu daki yace dakin mutum daya yake bukata kada a hadata da kowa. Sunyi sa'a kuwa an samu. Dakin a gyare yake amma duk da haka ya dage sai an sake karkade shi an wanke toilet. Da ya ga matar zata yi masa gardama wai sai da safe zata sake zuwa ya bata dubu biyu. Kafin Mama ta iso da su Emzee da 'yan tarkacen bukata na kwana irinsu bargo da zanin gado an gyara dakin.


Daure idanun Ummi aka yi da farin bandeji likitan yace bazai bude ba sai gobe a wurin gwajin ido. Budewar idanun lokaci daya da yawaitar haske ne ya janyo mata wannan ciwon kan saboda haka tana bukatar hutu. Da an sabunta mata glass din ido komai zai daidaita in sha Allahu. 


Emzee fa rai bai so ba. Abinda aka fi gani wurin Radhiya yau sai gashi yana yi. Zama yayi kusa da ita a kan gadon yana rokonta wai ko dan yaya ta janye daurin idon ta kalle shi.


"Kayi hakuri mana Zayyanu gobe fa za'a bude mata."


"Nene shikenan sai ta kwana ni bata ganni ba." Yau abin nasa harda turo baki musamman da Radhiya take masa gwalo.


Ibrahim ya kalli yadda yake yi ya jinjina kai "yau kuma Zayyana ka koma? Ita ce bakinta kullum a tabe tsabar shagwaba"


"Kai kuma sarkin sa ido ko" inji Mama ta kalli Emzee tana bashi hakuri.


"Ka fita idona Surbajo" ya yi maganar yana nuna shi da dan yatsa.


"Sunan nan ya fita a bakinka fa"


"Kunga ku tashi mu tafi haka nan kafin ku cika mata kunne. Ummi bari mu gudu dare na kara yi"


Kwanukan da suka bata na abinci Radhiya ta hada zata kai mota Mama tace tayi musu sai da safe don tare zasu wuce Nene kadai ce zata kwana.


"Wayyo Mama nidai ki barni"


"Shagwababbun da yawa ashe, ai kuwa sai mun tafi don bazan bari ki zauna ki dameta ba"


Ibrahim da Emzee suka soma tsokanarta. A bangare daya kuma tasu rigimar su biyu bata kare ba. Mama dai kada su tayi duka suka fito wurin da ta ajiye motarta. Layin Awwab ta shiga nema don ya kusa awa daya baya dakin daga zuwa amsa waya.


Ghazalatu ce take kiransa dama shiyasa ya fita daga dakin. Mota ya koma suna waya. Ta sanar dashi cewa tana tunanin Daddy Haroun yau ya yiwa Alh Baba zancensu don ta ga ya tambayeta da safe. Hira yake da ita babu wannan irin dokin da yake ji akan Radhiya da ya hadu da ita kwanaki kadan da suka wuce. Har ga Allah sai yake jin babu dadi saboda baya son zama maci amana kuma baya son wulakanta kanwarsa. Biye mata yayi suna hirar kawai don ya faranta mata.


Wayar Mama da take ta shigo masa yace mata yana zuwa ya amsa kiran.


"Awwab ina kayi parking ne? Ka taho mu tafi gida don nasan bazaka gane hanya ba. Nima ba don Ibrahim ba bata zanyi"


"To Mama gani nan"


Zagayawa yayi inda suke Ibrahim da Emzee suna rige rigen shiga tasa motar saboda rigimarsu ta dazu tace Radhiya taje ta shiga su bisu a baya. Ibrahim da Emzee su shiga tata.


"Amma Mama ba mune maza ba sai mu bishi ki tafi da ita" cewar Ibrahim suna hada ido da Emzee suna dariyar shakiyanci.


"Ita tasan hanyar ne? Ko mu biyu kuke son mu bata?"


"Sai ku biyo mu a baya. Amma a haka kamar kinfi son ta bishi"


Ganin idon Mama kadai ya hana Radhiya kaiwa Emzee duka. Kunya ce ta kama ta sosai. Allah Ya taimaketa Mama ta kama kunnuwansu shi da Ibrahim ta gwara musu kai sannan tace su wuce itama tana murmushi.


Kwandon kayan abincin da ta dauko Awwab ya karba ya ajiye a baya sannan ya bude mata gaban. Ibrahim da Emzee kamar ba fada suke ba suka sake kwashewa da dariya harda tafawa.


"Shakiyai Allah Ya shirya min ku" Mama tace kawai tana tada mota.


Radhiya a kunyace ta shiga motar duk da cewa dazu tare suka zo a hakan daga Sumaila amma da Nene da Ummi. Yanzu kuwa su kadai duk bakin ma sai ya mutu.  Bangaren window ta karkata gabadayanta tana kallon waje.


Yatsantsa ya kada mata ta juyo amma taki kallonsa "tunanin me kike yi?"


"Babu komai"


"To in baki abin da zaki je kiyi tunani a kai?"


Da ka ta amsa masa yace "baki da wani course da kike sha'awar karantawa?"


"Duk ban sansu ba, soja kawai na sani"


"Sojan ma ai yana karatu"


"Training din kuma ayi yaushe? Na zata fada kawai ake koya musu da harbin bindiga"


"Sai kace wasu 'yan ta'adda? Kinga kamar Daddy da yayi soja amma computer engineer ne."


Dena kallon wajen tayi ta gyara zamanta yana mata bayani yadda zata gane. 


"Kin dami mutane da son zama soja bayan baki san komai akansu ba"


Baiyi tsammani ba kawai yaji tace "Hamma ka zaba min wanda kake so in karanta"


Kallonta da ya tsaya yi saura kiris motar Mama ta bace masa "kina son mass comm.?"


"Na 'yan jarida?"


"Yes"


Zata bashi amsa wayarsa ta hau ruri. Da yake a kusa da giya ya ajiyeta idonta ya kai inda hasken yake ta ga ansa My G. Wani irin abu taji ya soki zuciyarta ta dauke kai da sauri ta koma kallon waje. Awwab sai yaji gabadaya hankalinsa ya tashi. Wai haka ake yi da mata biyu dama? Shi tun kafin yayi auren kowacce yana kokarin ya ga ya kawar da abinda zai tuna mata da 'yar uwarta saboda alamun kishi da yake ganin suna dashi su duka. Wannan shine dauko ruwan dafa kai. Bai taba tunanin hada girlfriends biyu ba ma a lokaci daya balle mata. Shi irin mutanen nan ne da rigima ta taho ta hagu sai yabi dama babu karkace hanya. Duk abinda zai tada masa da hankali gudunsa yake. Shi kadai yake kwankwasar kansa da cewa sai ya jajirce ne fa komai zai tafi daidai. Yadda Alheran tasan ba ita kadai bace yana komawa Katsina gobe Ghazalatu ma zata sani. Kai iyayensa ma zasu sani don ya fara ji a ransa wannan shekarar da ya diba ko kadan bazai iya jira ba. Zamanta yanzu cikin motar ba karamin jinsa yake a ransa ba. Kiran ya katse wani ya sake shigowa ya dauka yace mata tuki yake zai kira idan ya tsaya.


Radhiya kuwa sai juya sunan take a ranta wai My G. Lokacin da ya gabatar mata da ita tun farko da haka ya ambaceta amma yanzu tafi jin abin a ranta. Har ya gama wayar bata kalle shi ba. Tunawa tayi da wayar da ya bata wadda bata samu nutsuwar dubawa ba ta dauko a hankali harda karewa da hijab don kada ya ga me take yi ta budo wurin sunaye. Suna daya tal ta gani a cikin contacts din. Hamma. To saura fatan akwai kudin kira. Satar kallonsa tayi idanunsa akan titi yana tunanin yadda zata kaya masa gobe a Katsina yaji waya ta sake kara. Ko kalla baiyi ba tunda yace zai kira yafi so ta kyale shi ya kira din.


Kamar ba wadda ranta yake a bace ba Radhiya tace cikin karamar murya "Hamma ana maka waya"


"Bari kawai zan kira idan na tsaya"


So take ta ga da wane suna yayi saving number dinta. Ko bai ma saka sunan ba. Gashi ya tura wayar a aljihu.


Da ta katse sai ta sake kira "Hamma ka dauka mana"


"Yadda kika bata rai dazu idan na dauka kila kuka zaki yi min" yace daidai lokacin da Emzee yake bude gate Mama tana shigar da motarta Ibrahim kuma ya shige ciki ya fadawa kawunsa kanin Baba da ya zauna dashi sun dawo.


Sake kiransa tayi na ukun ta turo baki "ni dai ka duba mana"


Bai taba kawowa ita ke kiran ba ya dauko wayar da saurinta kuwa ta leka. Shi yana mamakin kiran me take yi masa ita kuma tsabagen bakinciki tana mamakin wannan wane irin suna ne ya lakaba mata.


"Meye wannan Hamma? Nawa sunan kenan, meye sha...sha me ma?" Ta daga kai tana kara kallon rubutun wayar kuma ta katse bata gama hada harufan ta karanta ba.


Idanunta taf da kwalla ta dagosu ta zuba masa "sake nuna min nawa sunan" tace kamar me bashi umarni. Ya kuwa danno sunan nata ya bata wayar.


Kallon sunan ta sake yi ta ma kasa karantawa. Wata uwar harara ta doka masa ta kama kofar zata fita ya danna lock kafin ta bude.


Dukan kofar ta shiga yi "ka bude min in fita, kuma na fasa soja zanyi, kuma likita zan aura"


"Allah baki isa ba Awwab ne mijinki" 


"Ni na fasa ka bude min" sunan kawai take tunani ranta yana kara baci. Anya ma ba shashasha yake nufi ba. Kwafa tayi tana jinjina kai.


"Calm down Schatzi, me ya faru?"


Sai ga digon hawaye ya ziraro "nice shazi din? Ni ko? Ni ko?"


Dariya ta bashi yadda ta kwabe fuska da gaske wai ranta ne ya baci. Gyara motar yayi a cikin gidan suna kallo kowa ya shige ciki ya sake tambayarta ta fada masa laifinsa.


"To ba kaine..."


"Me nayi ni Hamman Alheran sarkin laifi"


Sai kuma taji nauyi amma dai dole ta fada ayita ta kare. Bazata yarda kawai don ita tana da hakuri ba a cewarta kuma yayi mata haka tun yanzu ba.


"Ita da ta kiraka ba my G ka saka mata ba...."


Ido ya lumshe yana dariyar kuruciyarta "shine kika kira ki ga me na saka miki?"


"Eh, kuma kiran yayi min amfani gashi ni nawa sunan ko ma'ana babu. Mu sake gani ma don na kasa karantawa"


"Schatzi" yace da wata irin siga da ta sauke mata tarkacen rigimar da ta debo ba shiri. Idanunta yake nema su hada da nasa taki dagawa "Schatzi yana nufin sweetie in german." Cusa kanta kawai tayi a tsakanin cinyoyinta saboda tsabar kunyar da ta dirar mata. Tana ji yana tambayarta "Idan kuma ba kya so sai na koma kiranki my A. Bari na chanja miki" ya fara danna wayar.


"Don Allah ka bari"


"Kina so?"


Ta wani rufe fuska tana dariya ya kada kai ya bude motar suka fito tare. A daidai bakin kofa zasu shiga ciki yace "rigimammiyar Awwab". Da dan gudu ta shige ciki ta barshi a nan yana jin kamar an bashi dukkan farincikin duniya.


**********

Washegari Awwab bai bar Kano ba sai da ya tabbatar an gama komai na gwajin da za'a yiwa Ummi. Ko kwandala basu biya ba shi yayi komai. Ummi da Nene sai addu'a kawai suke masa yayin da Radhiya take jin sonsa yana kara shigarta. Duk wanda zai mutunta maka iyaye hakika masoyi ne na kwarai.


Ya fito daga dakin zasu raka shi bakin mota Emzee ya kawo mata wayar Ummi "Kawu Zakari ne yake son magana dake"


Murmushi ta saki ta mika hannu zata karbi wayar "Allah Sarki Kawu Zakari kwana biyu"


Yadda Awwab ya juyo da sauri Emzee sai da yaja baya ya fasa bata wayar.


"Ba ka gaisa dashi ba?"


"Eh mun gaisa"


"To kace tana gaishe shi, ke kuma muje ki rakani"


Sumsum ta wuce Emzee ya yi murmushi. Hamma yana burge shi kuma ya tabbatar da gaske yake son 'yar uwarsa shiyasa yake kara ganin girmansa. Mutum biyu ne damuwarsa a duniya, daga Ummi sai Adda Radhiya. Farincikinsa shine ya gansu cikin farinciki da kwanciyar hankali. A dole yayi masa karyar bata kusa. Yace to babu matsala gobe suna tafe duba Ummi dasu Innawuro.


Saboda tsokana Emzee sai ya daga murya yadda zasu ji "Adda yace zaku hadu gobe zasu so duba Ummi"


Tsayuwa Awwab yayi ya juya zai yanka masa magana tuni Emzee ya bace yana ta dariya. Hararar sai ta koma kan Radhiya ta dan ja da baya.


"Ni kuma me nayi?"


" 'Yar karamarki dake yarinyar nan kina da crush. Allah Yasa yazo kije kina masa murmushi zan sani ne"


"Shi kuma meye crush din?"


"Ko mutum baiyi niyya ba sai kin sashi dariya" yace yana murmushi.


"Crush din wani ne?"


"Yana nufin wani ya rinka burgeki kiji inama zai zama masoyinki"


Sai da tayi dariya tace ko kishi yake yi ya amsa mata da cewa "sosai ma kuwa, Allah Schatzi kada na tafi ki fara kula likitocin asibitin nan. Gabana ya soma faduwa kada suyi min kwace"


Wata dariyar take yana kallon fuskarta yana jindadi. Komai na Radhiya abin so ne a gareshi. Da kyar ya iya jan motar ya tafi tana ta daga masa hannu har ya fita daga harabar asibitin.


Tunda ya hau hanya bai tsaya ko ina ba sai cikin gidansu. Wata irin gajiya yaji ta dirar masa ya samu yayi bacci bayan yayi wanka.


**********[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Gagarumin taro aka hada na 'ya'yan marigariyi Alh Ghousman da jikokinsa manya. Hankulansu duka a tashe sai maganganu ake yi cikin harshen tamasheq.


Alh Ghoumar da Alh Sidi sune manya a iyaye maza. Hamshakan 'yan kasuwa ne wadanda noma da kiwon da suka gada a wurin mahaifinsu ya zama tushen arzikinsu. Har ila yau a cikin taron akwai Ministan yada labarai Alh Issa Bouba miji ga Gwaggon Zayyan Aghaisha. Tana zaune a kusa da 'yan uwanta tana ta zubar da hawaye.


"Abinda ban gane ba shine a wane dalili wannan yaro Maikudi zai ce mana sun rasu gabadaya?" Alh Sidi yayi maganar cikin kunar rai. Duk tsayin shekarun nan iyalin Zayyan suna raye babu wanda ya sani cikinsu. A tunaninsu tsatson Alheran 'yar uwarsu ya riga ya kare basu da wani ko wata da zasu kalla su dangantata dasu.


"Ba wannan ba ma, ina suka zauna? Me yasa matarsa bata neme mu ba?"


Cikin kuka Gwaggo Aghaisha wadda suke kira Mamme tace da Alh Ghoumar "ka manta yanzu fa mutumin nan da yace tare suke da Zayyan a filin yaki yace har makancewa tayi. Kuma yaushe zaka ga laifinta ma. Mune muka san inda take ita bata taba zuwa Agadez ba."


"Haka ne kuma" yace jiki a sanyaye.


"Duk shekarun nan kila ta yisu ne cikin jin haushinmu. Tana ganin kamar mun rabu da ita saboda babu idon mijinta a duniya" Mamme ta sake fashewa da kuka.


Ko cikakken rabin awa basuyi ba da yin waya da Major Mustapha wanda yayi musu bayanin da zai yiwu ta waya. Bayan ya tura a binciko masa inda suke da takaitaccen bayanin cewa Mairama da 'ya'yanta suna da rai shine suka hadu cikin tashin hankali da mamakin wannan labari suka kira nambar da ya bayar. Sun dade suna waya inda ya fada musu abubuwan da suka sami wannan iyali. Basu da dalilin karyata shi tunda harda hoto ya tura musu domin shaida a lokacin da yace a nemo su.


Sai da hankula suka dan natsa sannan Alh Sidi yace "ina ganin ya kamata mu shirya muje mu gansu. Yaran mu kawosu su ga 'yan uwa don kada irin haka ta sake faruwa"


Kowa yayi na'am da wannan shawara. To sai kuma batun su waye zasu je. Babu wanda yake so a barshi a baya. Jirgi suka fara tunanin bi daga baya aka soke saboda zasu bukaci motocin hawa idan sun je.


"Babu wani abin damuwa tunda zamu daukosu. A sanar da sauran dangi idan yayi muku nan da kwanaki kadan sai mu shirya duk abinda ya kamata mu tafi"


Sati dayan ma suna ganin tsayinsa to amma tafiyar basu dauketa ta garaje ba. Danginsu, jininsu da kaddara ta rabasu. Ya zama wajibi a garesu su yiwa wannan tafiya shiri na musamman.


**********


Bayan sallar magariba Awwab sunyi da Ghazalatu zai je wurinta. Yana shiryawa suna waya da Radhiya tana masa shagwaba yana biye mata. Kwankwasa masa kofa akayi tare da sallama yana makale da wayar a kafada ya budewa Fauziyya kofar.


"Daddy yana kiranka"


Da ka ya amsa ya koma ya gama fesa turare sannan ya yiwa Radhiya sallama da sakon gaisuwa ga Umminsa.


A dakin Daddy din ya samesu tare da Mami. Yana shiga Daddy yace mata tayi hakuri ta basu wuri.


"Ba sai kun koreni ba na dade da sanin kuna wareni. To dadin abin ina da 'yan mata na"


"Zahra da Fauziyya ko? Kinsan dai ko da kudi bazaki saye min Zayyanatu ba" Daddy yace da murmushin dole saboda kwata kwata baya cikin nutsuwarsa tun jiya. Mami ta kula kuma ta tambayeshi sau daya yace babu komai sai taja bakinta tayi shiru. Ita ma din tana da danuwar da take dannewa bata so ta fada masa game da Zahra.


Murmushin ta mayar masa "ka manta jiya baka bata kudin kanwar amarya day ba mun ganku a rana? Yanzu zanje na sayeta"


Bayan fitarta Daddy ya maida kallonsa ga Awwab da yake zaune a kasa daga gefen wata duguwar kujera.


"MUHAMMAD"


Dago kai yayi da sauri saboda yadda kiran ya ratsa ko ina a jikinsa. Baya tunanin idan ba a makaranta ba ko za'a fadawa wani sunansa Daddy yana kiransa da Muhammad balle da irin wannan yanayi da yake nuni da babu wasa cikin maganar da zasu yi.


"Na'am Daddy"


"Meye tsakaninka da kanwarka Ghazalatu?"


Dama yayi tunanin wannan maganar ce tunda Ghazalatu tace tana tunanin Daddy Haroun ya sani ko ma yayi zancen da Alh Baba.


"Daddy maganar aure ce"


"Awwab meyasa baka sanar dani ko mahaifiyarka ba?"


Sunkuyar da kansa yayi yana mai takaicin biye mata da yayi tun a lokacin suka boye. Da an sani a gida zasu iya rokar alfarmar ta gama karatun kafin ayi aure tunda shine babbar damuwarta. Haka nan dai ya sanar da Daddy dalilin boyewar tasu.


"Rashin sanin kana nemanta ya sanya nayi maka karambani. Zuwanmu Rugar Barkindo na yiwa kakannin Radhiya alkawarin za ka aureta saboda sharadin da suka gindaya min kenan na bani ita na dawo da ita cikinku tayi karatu."


Murmushi sosai ya ga Awwab yayi ya sake dukar da kai. Wannan ya tabbatar masa da zancen Mami da tace tana ganin kamar yana sonta.


"Daddy nagode kuma na karba"


"Yaya zaka yi da kanwarka kuma?"


Babu kwauron baki ya fadawa mahaifinsa cewa dama ya dawo ne domin neman shawararsa akan yadda ya kamata ya bullowa lamarin.

"Bazan wulakanta Ghazalatu saboda Alheran ba, itama kuma ko ba ni na nemeta da kaina ba Daddy bazan bari kaji kunyar iyayenta ba"


Hakika tunani da hangen nesa irin na Awwab suna daga cikin dalilin da suka sa Major yake matukar son yaron. Sai aka samu kyakkyawar shakuwa a tsakaninsu wadda tasa suke shawartar juna akan abubuwa daban daban. Yaji dadin amsar dan nasa sosai amma kuma ba abinda nasa iyayen suke so ba ne.


"Ina zaka kai mata biyu a lokaci guda?"


Cikin yanayi na damuwa yace "Daddy nima ban sani ba amma don Allah kada kace na hakura da kowacce bazan iya ba. Dukkansu ni na kai kaina garesu kuma suka amince min"


"Muhammad kayi hakuri da Radhiya, su Alh Baba sun ce na bawa iyayenta hakuri Ghazalatu kadai zaka aura"


A firgici ya dago kai yana mikewa tsaye baki daya "Daddy?"


"Bana son jan zancen nan har Maminku taji. Alhaji yace a bari su gama biki to zan jira a gama din naji hukuncin da zasu yanke. Na sanar da kai ne saboda idan da gaske ka fara neman Radhiya ka janye. Bana son ka cigaba da sa mata rai har sai na gama iya kokarina akan neman amincewarsu ka hada biyun"


Gumi ne sosai ya soma wankewa Awwab fuska. Idan zai iya hakura da Alheran dinsa tabbas zai iya hakura da aure baki daya. Gurfana yayi a gaban Major kamar mai rokon gafara.


"Don Allah Daddy kasa baki wallahi zan iya aurensu su duka."


"Tashi kaje dama yace yana nemanka idan ka dawo. Ka yawaita addu'ar zabin Allah"


Jikinsa sam babu kwari haka ya fita kamar mara lafiya. Mami tana kallon fitarsa Zahra na yi masa magana bai ma san tana yi ba. Jikinta itama sai yayi sanyi. Tabbas akwai abinda yake faruwa wanda Daddy baya son ta sani. To ko ya gane abinda take boyewa na Zahra ne? Kai da wahala tace a ranta tana girgiza kai. Zahra bazata taba fada ba ta sani. Kallon yarinyar tayi a zaune bayan fitar Awwab bai kulata ba tayi shiru. Zuciyarta ce tayi mata nauyi ta rasa da wa zata yi maganar nan ta saukewa kanta nauyi. Fitarta kuma ba karamar illa zai iya janyowa zumunci ba. Shirun dai da ta yi kuma ta roki Zahra da tayi itama shine take ganin kamar zai zame musu maslaha.


Kafin ya isa gidan Alh Baba missed calls din Ghazalatu sun kai goma. Kiransa take tun yana wurin Daddy tana masa tuni akan shiru da ta ji. Ransa gabadaya a cunkushe ya shiga ya gaishe da Mummy kafin ya fito da niyar gaisawa da kakaninsu mata.


"Yayana ka bari sai zaka tafi kaje. Yanzu cinye mana lokacin hira zasuyi"


"Kinfi so dare yayi sosai lokacin na shiga sunyi bacci? Ba dadewa zanyi ba"


"Daddy yace in fada maka kaje wurin Alh Baba shima yana son ganinka. Ni duk za'a cinye min lokacina"


Murmushi yayi duk don ya nuna mata komai lafiya "My G baki da dama, yanzu

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment