Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarsa ya fara matsuwa da su tafi gida haka. Hoton Chibuzor ya daukesu su biyu dashi da Zayyan sun sakala hannuwa a kafadun juna sannan aka shige dashi wani daki da manyan sojoji aka rufe kofa.


Tambayoyi ne dai kamar bazasu kare ba daga manya manyansu da aka hada comittee na bincike akansa. Komai nasu anayi ne bisa tsari daki daki. Da ya gama bayani a dauko wani.  Suna yi suna duba takardun da aka basu daga can Liberia da kuma information da suke dashi akansa saboda har file dinsa sai da aka binciko wanda aka buga masa KIA wato killed in action. Sai gashi suna bin komai da kyau aka gane gaskiyarsa daga kwanakin wata da abubuwan suka gudana.


Babu wanda ya iya tafiya saboda su ma takaitaccen lokaci Mr President  ya basu su hada komai. Ga Excellency shima nasu ne tsohon soja ya roki alfarma shima. Lokaci ne da siyasa ta gabato zabe saura wata uku. Dawowar Zayyan wata gagarumar sa'a ce da dama da ta fadowa shugaban kasa mai ci a lokacin zaiyi amfani da ita wurin karkafa kamfen dinsa. A matse yake da ya samu a fito da komai fili domin duniya ta shaida irin kokarinsa da jajircewa. Su kansu sojojin yana son samun hadin kansu ne. Da farko ranar da aka ce masa gwamnan Plateau na son magana dashi kamar bazai amince da wuri ba saboda dan jam'iyyar hamayyarsu ne wanda suka tsayar da wani jajirtaccen tsohon soja a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sai da yaji me yake faruwa shine fa ya sako kansa ayi dashi. Shine fa tun daga saukar jirgin da ya dauko su zuwa yanzu ana ta daukar komai a video ne da hoto. Idan komai ya tafi daidai a saki al'ummar Nigeria ta shaida. 


Karfe uku na dare ranar talata shabiyu ga watan november 2015 aka kammala bincike akan Lt Zayyan Muhammad Tureta. Babu wanda bai nuna gajiyawa ba sai shi kadai. Da sun bukaci a wayi gari a haka da matukar wahala su ga gazawarsa. Ko da ba a filin training bane, Zayyan ya horo matukar horuwa da hakuri da juriya a zaman gidan yari. Wani Lt. Gen mai mukami daidai da Cheif of army staff ne ya fara tasowa zuwa gaban kujerar da Zayyan yake zaune sai ya mike shima. Hannu ya mika masa yana murmushi da alama shine yake shugabantar committee din.


"Welcome home Lieutenant"


Zayyan ya karbi hannun ya rike kafin kuma ya gyara tsayuwarsa. Sauran mutum hudun da akayi tare dasu kowa yazo ya bashi hannu suka gama sannan shugabansu a zaman da ya fisu nuna shekaru ya murmusa.


"Nasan akwai dan sauran kananun abubuwa da suka rage kamar cike-ciken takardu da sake daukar biodata dinka. Da kuma daukar statement din Rtd Major Mustapha da Rtd Lt Hadir. Amma duk da haka ina da tabbacin cewa a karshen komai da zamu iya gamawa a cikin sati guda kaine zaka fito da nasara kamar yadda muke tsammani."


Kansa ya sunkuyar kawai,  emotions kala kala suna kai kawo a zuciyarsa. Mutumin ya sake kallonsa yace "kana da ra'ayin cigaba da bautawa kasarmu ko kafi son yin retire? Wannan tambaya ce da ya kamata nayi maka idan an kare komai..." ya dakata yana dariya "but I realy can't wait naji amsarka"


Zayyan ya kalli mutanen nan daya bayan daya. Dukkaninsu a shekaru sun girme masa amma kayan jikinsu sune suka fi komai fito da cikarsu a matsayin zaratan sojoji irin wadanda kasa take tinkaho dasu.


"With all due respect Sir, I remain a soldier"


Gyada kai suke yi in approval. Shugaban ya kallesu sannan ya dafa kafadar Zayyan yace "Although unofficial amma bazan iya tafiya gida ba batare da na gabatar muku da precious mutum kamar wannan ba. GENERALS, I GIVE YOU A HERO LIKE NO OTHER...MAJOR GENERAL ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"


Gaisawa suka sake yi dashi sannan shugaban ya sake cewa Zayyan "strictly unofficial" wato yana nufin yayi shiru har sai sun gama. Doki ne kawai ya debe shi da yadda Zayyan din ya burge shi.


Bude musu kofa akayi daga waje aka kaishi wani babban hall sanyin AC na ratsa ko ina. Chibuzor yana ta gyangyadi, Awwab na kallon agogo. Shi kuwa Excellency kamar ba dare ba amsa waya yake ta yi ta 'yan uwansa 'yan siyasa da suke akan kayar zabe mai zuwa. 


Basu sha wahalar shawo kan Zayyan akan ya hakura gobe zasu kaishi gida ba saboda shima ya san yanzu dare yayi da yawa kada ya firgita iyalin nasa.


Kalle kallen garin yake kamar ba cikin duniyar da ya sani ba har suka isa gidan gwamnatin Plateau din. Maman Arifah tasan maigidan nata zai zo da baki amma bata san ko su waye ba. Dawowa cikin dare da baki kuwa ba sabon abu bane ga 'yan siyasa irinsa bare ma saboda harka da kamfen. Dakunan da za'a basu a gyare ga abinci sai da Zayyan fa yaci alwashin wallahi shi da abinci sai na matarsa. Awwab out of solidarity sai yaki ci shi ma. Chibuzor ne kawai yaci bacci ya kwashe shi. Awwab da Zayyan kuwa sabuwar hira suka bude idanunsu sun soye. Hirar dai game da iyalinsa ne shiyasa Awwab ya rinka kaucewa wasu abubuwan saboda yana gudun tayar masa da hankali daga dawowarsa. Ai bazai so jin kalubalen da suka fuskanta su duka gidajen uku ba kafin komai ya daidaita yanzu. Zayyan tuni ya fahimce shi. Dama can yana da saurin karantar mutane shiyasa ya hakura aka mayar da hirar ta Alheran. Ai kuwa baiyi danasani ba don ya sha dariya sosai. 


Bayan sallar asuba Excellency ya kawo musu kayan sakawa da kansa. Duka kayansa ne dai sun yiwa duka su ukun har Chibuzor yawa.


"Ko nasa a dinko maka kaya kafin muzo tafiya anjima?"


"Na fuskanci kamar da gayya kake son ja min lokaci. Wane irin dinki kuma ana zaune kalau."


"Kasan Allah bazaka je wurin Maman Alheran a haka ba. Infact mai aski za'a dauko yazo ya aske maka wannan kasumbar a gyara fuska sannan kayi wanka. Ko so kake su rinka mafarkinka idan kaje a haka?"


"Baka tausayi na ne ko? To askin ma bazanyi ba" Zayyan ya koma ya zauna ya bata rai.


Excellency yace idan ta kama ya danne shi zai danne shi ne ayi askin kuma a kulle shi a bandaki yayi wanka.


Awwab yana kallonsu yana dariyar yadda suke wannan rigima. Rtd Col Nasiruddeen tamkar babban wa yake ga Zayyan. Ya dauke shi kamar kaninsa da suka fito ciki daya. Sarai ya fahimci yana kewar iyalinsa amma ko yaki ko yaso bazai barshi yaje garesu a mummunar kama ba. 


"Kai Awwab kalli babanka da kyau banda aski me ya kamata ayi masa" yace a commanding voice.


Shima bai tsira ba sai da ya sami guzurin harara daga Daadaa. Ya daga kai yace "da dai zamu samu a gyara harda farce"


"Kai Awwab haka zaka yi min?" Yace da muryar ban tausayi. 


Excellency bai saurare shi ba ya kira PA dinsa ya fada masa abubuwan da yake bukata saboda yana so yau Zayyan yayi sallar azahar a cikin iyalinsa. Harkar kudi sai da kudi. Karfe  goma na safiyar laraba an siyowa Zayyan kaya readymade shadda da yaduka kala goma da takalma. Shima wai kawai don ya zabi wanda zai saka ne. An dauko mutum biyu daga wani sanannen wurin aski na zama masu shegen tsada kamar idan anyi askin baza'a kuma yi ba. Suna zuwa suka fara aiki. Mutum daya yana askin dayan kuwa dakalalliyar kafa da faratan Zayyan ya tasarma da gyara. Bakinsa bude yana ta al'ajabi wai ace zamani ya kai harda masu gyaran kaushi.


Ana wannan aikin Awwab ya samu ya kebe kansa ya kira Mama. Cikin rawar jiki ta dauka a can kuryar dakinta duk da cewa ma babu kowa a bangaren nata sai Ibrahim da Emzee suna nasu dakin.


"Awwab yaya" tace cikin tashin hankali. Jiya da kyar ta iya bacci tana ta juye juye ga fargabar kada ta kira taji mummunan labari ko wani yaji.


"Mama na turo miki sako ta whatsapp. Ki duba zan sake kiranki" yace yana karamar dariya.


Ita ta fara kashe wayar don sauri ta duba whatsapp dinta. Alamun Awwab ya turo mata hoto ta gani. Hannu na rawa ta bude. Bata san lokacin da ta saki wayarta ta fadi a kasa ba ganin hotonsa da mutumin da babu tantama aminin mijinta ne.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zayyan...." dukawa tayi ta dauki wayar ta sake kunnawa daidai da kiran Awwab ya shigo.


Kuka kawai ta fashe dashi "Awwab kuna ina?"


"Zamu taho daga gidan baban Arifah tare muke. A nan gida zamuyi azahar in sha Allahu. Sai dai tun jiya yaki cin komai wai sai yazo gida zaici na Ummi"


Dariya tayi ga hawaye a idanunta "Zayyan kenan, yaushe Mairama zata iya girki idan ta ganshi. Amma kada ka damu abincinta zai ci in sha Allah. Sai kun iso"


Mayafi ta yafa ta fita zuwa gidan Ummi. Baby Zayyan yana can a bayanta tun da tayi masa wanka. Tayi mamakin fitowar Maman saboda sun hanata yin komai ita da Mami.


"Jikin ne Zainab?" Ta tambaya da kulawa.


Jiya tsabar damuwa kasa komai tayi sai tsananin fargaba. Da aka dameta da tambaya tace zazzabi ne da ciwon kai suke damunta. Karshe dai Mami tace a dage taron sunan da ya kamata suyi a jibi sai wani satin ta kara samun sauki. A ganinsu cikar da gidan yake yi ne ya hanata hutawa. 'Yan uwa masu tahowa a yau kenan duka ta dakatar dasu da kanta. Bata san me zai faru ba amma bata da wani kuzarin yi taron suna wanda su Ummi ne suka takura sai anyi.


"Na ware sosai. Gajiya nayi na fito, kina da garin masara kiyi min tuwo? Miyar kukar rannan kinsan ta min dadi sosai"


"Kinyi sa'a akwai saura kuwa."


Fauziyya na wurin tace bari ta yi Mama tayi saurin cewa akwai fruits a bangarenta ko zasuyi fruitsalad kada su lalace. Radhiya taje ta kira suyi tare duk tayi laushi saboda rashin wayar Awwab da shareta da ya rinka yi kwana biyu. Ta ma kudurta a ranta ta dena basarwa idan ma dalilin haka ya janyo ya dena kulata.


Ummi bata kawo komai ba taje ta jika busasshen kifinta da ruwan zafi ta bara ta wanke shi tas. Bata rabo da jajjage ba bata lokaci ta hada wake, naman sa da kifin nan ta soma dafawa tare da daddawa da gishiri bayan ta kara albasa da kayan kamshinta da Innawuro take hada mata garin tafarnuwa, citta, kaninfari da masoro. Maggi sai miya ta dauko dahuwa. Girkin baifi na mutum uku zata yi ba yadda zai ishi Mama har dumame. Tana yi suna taba hira Mama sai ta kalleta ta kawar da kai ta share kwalla. Mairama komai nata da nutsuwa take yinsa gwanin sha'awa. 


Sabon flask da ba'a taba budewa ba Mama tasa Radhiya da suke aikin fruitsalad ta kawo mata ta zuba tuwon da ta kukkulle a leda. 


"Yau kice da Baba Hadir za'a ci tuwon nan"


"Ko daya ki boye min a dakinki sai anjima zan zo naci" Mama tace tana mikewa.


"A daki kuma? A kawo miki mana"


"Ke dai ajiye min ko a nan ne kada a taba. Da zaki taimaka min da wannan shayin naki mai kayan kamshi da kin gama min komai"


Ummi ta girgiza kai "anya baki kunso wani ba? Wannan abu kamar me yaron ciki"


"Rufan asiri ina fama da kaina. Zainabu tayi sanyi in fada miki. Idan ba gani nayi ya fara takawa da kafarsa ba ko kallon babansu na dena yi"


Me Ummi zata yi kuwa banda dariyar mugunta. Allah Sarki Mama an ga haza. Dakinta suka koma da hira da dabara Mama tasa ta kuma gyara shi duk da ma Radhiya ta gyara da safe ta wanke toilet. Amma Mama tace wai ana sanyin nan da yakunno kai gadan gadan ina ita ina bedsheet single. Ta fito da mai hade da duvet ta shimfida mana. A take Ummi ta fara zargin wani abu amma duk iya tunaninta ta kasa. Wani mai masifar kyau da laushi tsarabar da Radhiya tayi musu su uku zuwanta na karshe kafin wannan ta shimfida. 


Tana gamawa Daadaa wato baby Zayyan ya farka. Yana cinyar Mama dama da zata gyara gadon. Shigewa tayi tana wanka zuciyarta na tunanin manufar Mama. Gabanta ne ya fadi da tayi tunanin ko shammatarta akayi ne aka daura mata aure? Idan ba haka ba meye na sa ta a gaba ta gyara daki. Hmmm zasu sha mamaki kuwa idan aka nemi turo wani cikin rayuwar da bazata taba sake irinta ba tunda ta rasa Sojanta.


**********


Shabiyu da rabi kowa yayi wanka mata na gidan Ummi maza na bangaren Mama wurin Raji suna ta hira. Mama ta koma wurin Ummi ta sallami duka yaran nan zuwa gidanta tace baki zasu yi zata kira su su gaishe su. Ya rage daga ita sai Mami da Ummi. Zahra ce karshen fitan tana tafiya Mami tace


 "Wallahi Zainab mun gaji da wannan nuku nukun naki. Yanzu Daddy yace wai Excellency ma ya kirasu su dawo gida, suna hanya shi da Baba Hadir. Kin saka mu a duhu"


Kwalla ta share duk yadda taso daurewa "kuyi hakuri nan da mintuna kadan ne komai zai fito"


**********


Zayyan kallon kansa yayi yana karawa. Babu abinda ya kai tsafta da gyara dadi. Shi da mayar da jikinsa da yin kyau sosai sai an kwana biyu amma ko a haka sai dai ace Alhamdulillahi. Fuskarsa ta fito an gyare shi sosai. Wanka kuwa kamar bazai fito ba saboda jindadin ruwan da yayi da yadda yake cire dattin jikinsa. Lallausan yadi irin na masu hannu da shuni fari kal Awwab ya zaba masa a cikin kayan da aka siyo da bakar hula. Yau ya ga me ake kira turare designer da ko sunansa bai taba ji ba a da. Komai na shiryawa hatta links din hannu Awwab ne ya saka masa. Shima yayi wanka amma kayansa ya mayar suka fito duka aka dunguma motocin da suke jiransu. Yau mota biyu akayi saboda gwamna baya son a gane shine.


Tafiyar minti shabiyar suka shigo cikin estate din bangaren gidajen guda uku da suke gefe da gefe da juna.


Ana tsayawa Zayyan ya damki hannun Awwab.


"Tabani in tabbatar nine" yace muryarsa tana rawa da iyakar gaskiyarsa.


Awwab sai ya kara karfin rikon dake tsakanin hannuwansu. Gabansu duka faduwa yake Zayyan ya runtse ido ya kuma budewa a hankali yake cewa "Ya Allah kasa ba mafarki nake yi ba. Idan kuma mafarki ne Allah kasa na mutu a cikinsa"


Hannunsa Awwab ya sake rikewa suka fara takawa sannu a hankali bangaren Mairama Ali Gidado uwar Alheran da Muhammad Zayyan.


"Ba mafarki kake yi ba Daadaa. Ka tsaya a nan minti daya in fara shiga" yace lokacin da suka taka matattakala biyun da ake hawa kafin ya shiga gidan.


Da sallama ya shiga ya sami iyayen nasa duka a zazzaune sun saka Mama a gaba harda Major ana son jin bayaninta. Tana ganin Awwab ta mike sa sauri.


"Yauwa Awwab kun iso? Ina yake?"


Sai suka kara daurewa kowa kai da Awwab yace yana bakin kofa zai shigo dashi.


Komawa yayi da baya ya bude kofar ya riko hannuwan Zayyan suna tsaye da Excellency ya iso wurin.


Awwab ne ya daga labule yayin da muryar Zayyan ta karade falon a lokacin da yake cewa "Assalamu alaikum" 
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Gabadayansa ya bayyana a gabansu kafin muryar ta gama shiga kunnuwansu. 


"Daddy, Baba...." Awwab ya soma cewa sai dai tuni Zayyan yayi gaba haka ma Daddy din da Baba sun taso daga wurin zamansu sun tare shi a tsakiyar falon.


"Zzzzayyyannn kaine?" Baba Hadir yace da karfinsa.


Manyan maza magidanta duniya ta sanyasu kuka tamkar yara. A wannan lokacin Hadir ne tsaye a gaban Zayyan dinsa. Hannuwansa yasa yana shafa shi kafin su kankame juna. 


Major da ya tabbata ba mafarki ne ba ya ware hannuwansa ya rungume su su duka biyun a tare yana nasa hawayen. Excellency ma nasa yake yi a gefe yana jinjina karfin soyayyar wadannan mutane.


Duk abinda suke yi Mairama tana zaune kamar an dasata ta kasa motsi. Tana iya jiyo kukan Mami da Mama sama sama ita kuwa ta kasa. Wai shin ta cigaba da zama ne a wurin tana kallon Sojanta ko kuwa ta tashi itama taje ta rungume shi ko sau daya ne kafin ta farka daga wannan daddadan mafarki. Tunda take mafarkin Zayyan bata taba irin wannan da zata gansu a wuri daya duka tare ba. Ina ma Radhiya da Emzee zasu shigo suma su karasa cike mata mafarkin.


Tayi nisa a wannan tunani bata san Zayyan ya iso gabanta ya duka ba. Hannuwanta da ya rike masu laushi wani irin shock yaji na soyayya, tausayi da girmamawa a gareta da ta dauki shekaru ashirin da biyu tana dakon soyayyarsa bata yi aure ba. Runtse idanu tayi tana ayyana da gaske ne haka Zayyan zai dawo mata duk ya rame? Ashe kuwa zata dauki lokaci wurin ganin ta ciyar dashi duk abinda zai taimaka ya sake gina masa jiki.


Rikon da yayiwa hannunta da kakkarfan hannunsa sai kuma yatsansa da yasa yana kore mata hawayen dake gudana a fuskarta batare da ta sani ba shine ya sanyata dawo cikin hayyacinta daga tunanin da tayi zurfi tana yi. Tsigar jikinta ke tashi a lokacin da Zayyan ya mikar da ita tsaye ya dora hannuwansa akan kafadunta yana tayata kukan.


"Wai kuka zamuyi ta yi ne? Bazaki yiwa mijinki barka da dawowa ba?" Yayi maganar kamar baya so saboda shaukin dake dibarsa.


Wani hawayen ta matse ta hanyar runtse idanunta sannan ta budesu ta kalle shi da kyau wani abu yana sauka a kahon zuciyarta. A hankali ta daga hannunta daya ta shafa kumatunsa da wahala ta ramar.


"Ashe ba mafarki nake yi ba" tace lokaci guda ta sulale a jikinsa ta fadi sumammiya.


"Fillo" ya kira sunanta hankalinsa a tashe. Mama ta daure tace ya kwantar da hankalinsa abin ne yayi mata yawa. Ita kuma Mami ta samo ruwa a kitchen. 


Ana shafa mata ta bude idanu suka sauka acikin na Zayyan. 


"Da gaske ba mafarki nake yi ba?" Hawaye na gudana a idanunta take yi masa wannan tambaya.


"Nima tsoro nake kada a tasheni daga bacci"


"Ina ka tafi ka barni?" Tace tana fashewa da wani irin kuka.


"Wurin da ko makiyina bana fatan yaje. Kiyi hakuri Fillo na aureki na barki cikin..."


Kai ta shiga kadawa tana daga zaune akan kujerar da aka kwantar da ita da ta suma "kada kace komai sai godiyar Allah"


Sun bawa kowa na wurin tausayi. Major ya katse maganar tasu saboda kada aji kunya gasu a wurin ga Awwab da yake ta aikin share kwalla ya zama a koke.


Zayyan ya dago ya sake kallonsu yana fitar da murmushin mai karawa fuskarsa annuri. Ya tambayi Awwab "ina kannenka?"


Da sauri ya nemi nambar Zahra tana dauka yace su zo su duka falon Ummi anyi bako. Duka suka taho harda Raji. Baby Zayyan yana kafadar yayansa Ibrahim wanda Allah Ya sanyawa kaunarsa daga haduwarsu jiya.


Daya bayan daya suka shigo falon. Kowa na zaune banda Awwab da yake daga gefen kofa sai kuma wani dogon mutum da suna fara shigowa ya tashi yana murmushi.


Awwab yace da kannen nasa da dan karfi "introduce yourselves"


Radhiya ta juyo suka hada ido ta kawar da kai ita tana fushi kuma a ranta bata da niyar fadin nata sunan.


Fauziyya ce ta farko ta matso gabansa zata gaishe shi ya mika hannu ya karbi Jawad "Fauziyya?"


Tayi mamaki har ya nuna a idanunta. Shi kuwa ya tuna ta ne kasancewar duka 'ya'yan Major ita kadai ya sani fara sauran duka wankan tawarda suke.


Yaronta ya bata saboda ganin wani da yayi a hannun ta kusa da ita ya karbe shi shima "Zahra?"


Duk da bata sanshi ba taji dadi ko waye wannan mutumin mai kwarjini itama ya santa.


Wani jaririn ya kuma gani a hannun wani matashi da babu tantama kamanni sun nuna dan Zainab da Hadir ne. Kafin ya ambaci sunansa Ibrahim yana murmushi tare da mika masa yaron yace cikin alfahari "Ibrahim Hadir da Zayyan Hadir"


Zayyan ya juya ya kalli Hadir ya yi murmushi sannan ya bashi yaron. Wata 'yar budurwa ya gani ta kusa da wadda yake kallo tun shigowarsu  wato Radhiya ta turo ta gaba ita kuma sai kunya take ji ya dan rage tsayi "kema in daukeki ne?"


'Yan uwanta ta kalla ta dan marairaice a kunyace "a'a nima ka fadi sunana"


Ibrahim ya girgiza kai, ashe bata dena shagwaba ba. Ji yadda take tale baki ita da ta gama secondary. 


"Kiyi hakuri ki fada min da kanki inyi miki babbar kyauta"


"Zayyanatu Mustapha" tace saboda taji Ibrahim ma ya fadi harda sunan babansu.


Baki bude Zayyan ya kalli Major da ya kafe shi da ido kamar idan ya rufe zai bude ya neme shi ya rasa.


Emzee ne ya rage a gabansa. Yaron tunda suka shigo yake ta kallon wannan mutumi yana tunanin a ina ya taba ganin fuska shigen wannan. Kallon kallo suke yi Zayyan yana jin kamar yana kallon younger version dinsa ne. Ashe Radhiya ma ta soma tunanin inda tasan fuskar ita da ta haddace kamanin mahaifinta a hoto.


Emzee ya bude baki kenan ta matso da sauri tana jin jikinta yana rawa. Tunda suka shigo ya gama gane wacece dinsa shiyasa ma ya bar yi mata magana sai a karshe.


"Kamar na san ka wallahi" tace muryarta a kasa kamar mai rada.


Hannu yasa ya janyota gabansa sosai ta tsare shi da manyan idanunta "Alheran Radhiya baki gane Daadaa ba?"


"Ya Allah" ta furta a gigice ta rungume shi tana kuka mai sauti. Bayanta kawai yake shafawa yana kokarin mayar da nasa hawayen.


"Ehemm..ni sunana..." Emzee yayi gyaran murya shima yau dauriya ta kare sai hawaye "Muhammad Zayyan Tureta"


Haba...koda yaji wannan yaro zuciyarsa ta bashi cewa jininsa ne. Sakin Radhiya yayi hawayen da yake kokarin kada ya zubar a gaban 'ya'ya suka fito suka rungume juna cikin farinciki suna kuka. Zayyan ya dago yana ta shafa fuskar Emzee wai wannan ma nasa ne.


"Kafi jindadin ganinsa a kaina ko?" Yaji Radhiya tace a raunane tana kara karyar masa da zuciya.


"A'a Alheran" yace yana sakin Emzee ya sake rungumeta.


"Kenan ni bakayi murnar ganina ba?" Shima Emzee yace yana jin haushin tayi masa kauron jin dumin babansa ya koma wurinta.


Zayyan sai ya rikice yana soma cewa "ba haka bane" ya ga Alheran ta kafe shi da ido shima Emzee ya tsaya yana jiran amsarsa.


Dariya suka ji daga bayansu. Falon da ake ta kuka ma'abota cikinsa sun koma dariyar wannan haduwa ta uba da 'ya'yansa. Hadasu yayi kowanne a bari daya ya rungumesu kamar za'a kwace masa su

**********


Kowa yana son jin yadda ta kasance dashi su duka suna zaune a falon. Emzee da Radhiya kusan danne masa kafafu suka yi kowannensu yana so ya rabi jikinsa. 


Dagawa yayi suka hada ido da Ummi da take ta kallonsa sai taji kunya sosai ta kama ta. Major ne yayi gyaran murya yace a yiwa Annabi SAW salati. A tare suke yi da karfi suka karanta Fatiha, Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul sannan ya dade yana jan su da addu'a duka domin godiya ga Allah SWT.


"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah...wannan rana ce da bazamu taba mantawa da ita ba har mu bar duniya. Amma kafin mu zauna jin yadda al'amura suka kasance  Zayyan ka zauna kaci abinci ka huta. Ku kuma kowa ya tashi mu bashi wuri ya huta"


Dukkaninsu suka fita Ummi ta tashi tayi kitchen tana godewa dabara irin ta Mama aka bar Zayyan da 'ya'yansa an rasa wanda zai fara tashi cikinsu.


Emzee yasan ya kamata su tashi amma Radhiya ita ta ga wurin kwana. Kallon babanta kawai take yi tana cewa Daadaa yana amsawa da murmushi. Ta kira yafi sau goma bai gajiya da amsawa.


"Emzee kuma wai nan ba mafarki nake yi ba ko?" Tace tana lumshe ido tana sake budewa a kansa.


"Ko in mintsineki ne?"


"A gabana Zayyan?"


Wani dadi yaji ya kama shi mahaifinsa ga kira sunansa da sunan raba gardama tsakaninsa da Addarsa. Kai wannan abu da me zai kwatanta shi. Muryar Umminsu suka ji tana cewa "in fara kawo maka abinci ko tea?"


"Duk wanda kika kawo zanci Fillo. Saboda jiran abincinki rabona da saka wani abu a bakina tun safiyar jiya"


Wai da irin dabarar nan Emzee sai ya yiwa yayarsa alama da ta tashi su ma su fita. Shiru bata gane rangwada kan da yake yi ba sai da yace "Adda taso muje muma Daada yaci abinci"


Hannunsa da ya riko nata ta ture "kai kyaleni ka tafi idan kana so. Ni ban gaji da ganinsa ba." Matsowa ta sake yi jikin kafar Zayyan tana murmushi  "Daada na chanja kama daga

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment