Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa dadin abin itama an goge mata nata janbakin yau da tayi kwanan tausayin kanta.


Komai nasu abin sha'awa musamman wannan hadin kan da ya samo asali daga jajircewar iyayensu.


**********


Washegari wuraren shadaya na safe a can gefe guda na katon falon gidan Zahra ce da kannen nata Fauziyya da Radhiya Rahima tana yi musu lalle iya yatsun hannu kawai banda kafa. Su na cikin yi Mami da Mama suka shigo Zayyana da tun daren jiya aka yi mata nata ta tashi da sauri tayi bakin kofa za ta karbi DK ta ga baya hannun Mama ko Mami.


Baki ta tura tana leka waje "Mama ina DK?"


Mami ta daure fuska tace "Meye haka babu gaisuwa ni matsa ki ban wuri yana wurin Ibrahim a mota"


Murmushi tayi kafin ta matsa tana gaishesu. Mama tace taje ta karbo shi kunya take tana ganin idan ta fita kowa zai gane meye tsakaninsu. Ganin Hibbah ta taso zata karbo shi yasa ta fita da sauri. Hibbah tayi dan murmushi suna hada ido da Rahima.


Fauziyya ta hararesu "gulmammu ko dai ku fasa mana kwan nan ko yau na danneku a daki ayi muku balotelli ko ya kike gani babbar yaya" ta kalli Radhiya.


Dariyarsu kadai ta isa tona asiri amma Zahra tace "ku bari ta dawo mu sakata a daki ta fada ko yau ayi taro tana gida"


Hibbah da Rahima dai sai dariya Fauziyya tace su din ma duk sai ta binciko nasu tunda Radhiya ta kauce su ne next.


Wata irin tafiya Zayyana ta rinka yi kamar bazata isa wurin motar ba saboda irin kallon da Ibrahim yake yi mata. Tana zuwa ya fito da DK a hannu yana murmushi.


"Kawo shi" tace tana mika hannu.


Kara makale shi yayi a jikinsa yana harararta "dama ba wurina kika zo ba?"


"Ni kanina nazo dauka"


Wani irin kallo ya bita dashi "Ya kina ganina amma ta wannan yaron kike yi. Tun wuri ki sani bazan yarda da wasan kanin miji ba."


Kamar gaske ya hade rai ita kuwa dariya ma take yi "Ka jira a haifi kanin mijin wannan dai twin dina ne ko ba ka ji sunansa ba...Zayyan da Zayyanatu" tayi masa gwalo.


Bata fuska Ibrahim yayi ya tale baki yadda take yi ta cigaba da dariya. Muryar kuka ya soma yi mata "idan ba kin janyo na rage masa matsayi ba tunda haka ne. Tun farko ni me yasa ba'a saka min Zayyan din ba shi a saka masa Ibrahim?"


"Saboda shi Zayyan kanina ne, shi kuma Ya Khaleel...." juya idanu tayi bata karasa ba ta kama hanya za ta gudu.


Ibrahim kamar wanda aka dora a gajimare yake yawo don dadi ya biyota ya mika mata shi. Tana karbarsa ta kai hancinta jikin nasa tana gogawa tare da yi masa murmushi "baby DK dinaaaa"


Jingina Ibrahim yayi da bango yana kallonta da jin sabuwar soyayya na dibansa "yaro kaji dadinka ko yaushe ni kuma zan sami arzikin ayi min haka wa ya sani"


Kai ta dago ya kashe mata ido bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta ji ta shige ciki ta barshi a tsaye yana ta murmushi.


Emzee ne ya shigo ta karamin gate da ledar mangaro masu kyau wanda ya sauka daga motar ya tsallaka siyowa da suna hanya kafin su shiga kwanar gidan. Yana karasowa motoci uku suka shigo manyan mata wayayyu suka rinka fitowa daga ciki. Mom Arifah kadai suka gane suka gaisa da ita da sauran matan tace Emzee ya kaisu wurin Mairama.


Yana gaba sauran duka suna bayansa da ita suka shigo. Su Radhiya suka gaishesu sannan Zayyana ta hau sama ta fadawa su Ummi. Gayyar lallen ce ta tashi dama sun saka wata leda a wurin basu bata ko ina ba suka tafi daki.


Dukkaninsu matan manya ne su takwas. Biyu matan gwamnoni, uku matan sanatoci, karamar ministan ilimi sai matar ministan ilimin wai sun zo sake yiwa Mairama murna ne zasu koma garuruwansa. Duka Mom Arifah ce ta gayyato su. Abubuwan ci da sha aka kawo musu Salame tana daga daki take jin muryoyin manya don su Yadikko bayan gidan suka tafi wurin aikin nama kafin isowar su Mama da Mami da zasu hadu ayi abinci da Tante. Ko da wasa bata hangi kanta tana taya aikin komai ba a gidan banda kwanan bakinciki da tayi jiya saboda yadda ganin Alh Salisu ya kara tada mata hankali shi da matarsa. Fitowa tayi tana hura hanci Mairama kuwa tace musu ga yayarta tana nunata.


A mutumce suke gaisawa da ita sai ta saki fuska ta samu ta zauna a kujerar da tafi kusa da Mom Arifah tana ta wangale baki.


Hannun Ummi da Mom Arifah ta gani ta yaba "gaskiya ina son lallen nan Mairama yaya zamuyi? A ina mai yi take? Yayi kyau sosai"


Dadi Ummu taji " 'yata ce tayi min sunanta Rahima"


Matar gwamnan Abia kasa hakuri tayi tana shafa hannun tare da kallon kafar gwanin sha'awa "ni dai a kirawo ta idan tana kusa tayi min inje dashi gida yarana su gani...nawa ake biyanta don basira irin wannan nasan da tsada"


Salame an dade ba'a shiga aji ba amma dai tana fahimta kan bai gama toshewa ba. Ji tayi jikinta ya soma rawa taji kudi hankalinta a tashe 'yarta zata yiwa matar gwamna lalle. Sauran ma kowa tace tana so saboda yadda zanen ya fito radau sannan kalar tayi maroon sosai. Bude baki tayi za ta ce ko dari uku ne ma su kawo sai Ummi ta riga ta.


"Ku da 'yarku ko nawa ne ma kuka bata sai dai muyi godiya"


Mugun kallo Salame ta watsa mata sai dai babu wanda a kula a zuci tace "shegiya 'yar bakin ciki"


"No, no please Ummin Alheran ki fada a biya don nima zanyi. Muna da yawa bare ace alakoro ne" Mom Arifah tace suna dariya.


"Yanzu kuke magana" Salame ta sake cewa a ranta.


Ummi dama ko kadan bata da niyar manyan matan nan suci bulus. Ta dai fadi haka ne don kada a ga kamar bata da kara. Amma wannan ai kofa ce da Rahima zata samu. Aunawa tayi ta ga a garin Abuja suke inda komai kudi ne.


"N2000 take yin hannu da kafa"


Wata Dr. Lara 'yar lukuta da ita karamar ministan ilimi tace "kirawota ta fara yi mana ko a gama da wuri tunda kuna da aiki a gabanku"


Matar gwamnan Abia kuwa jakarta ta balle ta dauko bandir din dubu daya ta mikawa Ummi "take this hundred k  sister Maryam for the eight of us."


Baki Ummi ta bude zata yi godiya Mama ta rigata a gayance don kada a rainasu "Thank you Madam"


Hannun Salame har wani kaikayi yake yi burinta Mairama ta miko mata tunda duniya ta shaida ita ta dau cikin Rahima ta haifeta ta shayar. Saboda haka tafi kowa hakki akan dukiyar 'yarta.


Gilmawar Emzee Mami ta gani yana dauke da plate da ya bawa mai aikinsu ta yanka masa mangwaron zasu sha shi da Ibrahim tace ya kirawo Rahima. Zuciyarsa har wani dan tsallen murna tayi ya hau sama ya kwankwasa musu kofa. Radhiya ce ta amsa ya dan daga murya don kofar a rufe take.


"Turo min Rahima ana kiranta"


Kululu haka cikin Rahima ya kada da taji muryar Emzee. Hannunta kasa rike ledar lallen nata tayi sosai saura yatsa daya ta gama yiwa kanwarta Khadi ta tashi bayan ta lallaba ta gama.


Hijabinta ta gyara ta bude kofar yana tsaye ya jingina da bango yana shan mangwaron da fork. Mika mata yayi ta girgiza kai cike da kunya. Kofar fita daga falon ta nufa yana tsaye har lokacin a inda ta ganshi da ta fito.


"Kawar soja"


Dakatawa tayi amma bata juyo ba har ya iso inda take ya tsaya a gefenta. A hankali yace "abinda muka yi jiya bai yi kyau ba ko?"


Sai lokacin ta kalle shi da idanuwan da suke narke masa zuciya cikin sanyinta tace "yayi kyau sosai"


"Amma kika kasa fada min?" Yace kamar yana fushi.


"Kayi hakuri Ya Emzee" ta kira shi yadda taji Zayyana na fada.


"Kowa fa ya fada ke kadai ce banji kince komai ba"


"Kayi hakuri yayi kyau"


"Sosai?" Yace excitedly


"Sosai sosai"


Murmushin fuskarsa ya dauke "kai duk da haka ban hakura ba. Yau idan an shirya za'a tafi idan baki ganni ba a wurin kada ki shiga motar kowa I will come for you"


Idanunta ta zare tana kallonsa ya nuna mata kasa da ake jiranta suma jin Mama na cewa ya fada mata ta taho da kayan lallenta.


"Idan baki jirani ba zamu dena kawancen nan so please ki jira ko bana nan zan dawo" Kallonsa tayi ta dauke kai ya dan sake matsowa ya rage murya "Rahima please do this for me"


Bai jira amsarta ba ya sauka ita kuma ta koma ta dauko kayan lallen ta sauka gabanta na wata irin faduwa tana jin kamar rayuwarta bazata taba dadi ba idan babu shi a cikinta. Sai dai kuma tunanin yafi karfinta ta kowace fuska yana karyar mata da gwiwa.


Jikinta ne yayi sanyi da Ummi ta nuna mata su wa za ta yiwa. Da wane hannun za ta taba wadannan matan masu kwarjini haka. Da kyar ta iya cewa bari ta kwaba wani saura kadan wancan.


Yawun bakinta har bushewa yayi tana tsoron kada taje tayi musu mistake. Ummi ta lura da ita sai ta tashi tabi bayanta zuwa kitchen din da ta shiga da ledar kayan lallen. Salame ma sai ta bisu da sauri kafin Mairama taje ta bata dubu biyar ta murkushe sauran ta cinye ita kadai. A fusace take tazo shiga maganarsu ta dakatar da ita.


"Ummi kingansu kuwa? Ni dai tsoro nake ji"


Ummi ta tayata dibo ruwa tana tsiyaya mata a robar da ta zuba lallen da kayan hadi "na fiki tsorata in fada miki wai nice da matan gwamnoni a gidana"


Rahima tayi murmushi "kema da kanki?"


"Ahh tabdi to ni na taba ganinsu ne?"


Murmushi ta sake yi sai kuma damuwa ta bayyana "kada hannuna ya rinka rawa"


Kafadunta Ummi ta dafa "Rahima! So nake kasuwa ta bude miki ace matan manyan nan kike yiwa kunshi kina jina. Ki ajiye tsoro ki tuna cewa neman halak kike yi zaki taimaki Baffanki ko?"


"Eh"


"To ki nutsu yanzu haka dubu dari aka baki amma zan ajiye sai zaki koma gida na baki"


"Dubu dari Ummi?" Rahima tace mamaki ya isheta ta rungume Ummin tana murna "in bawa Baffana da ke da Umma sai mu raba sauran da kannena"


"Kut..." Salame tace tana yunkurin shiga kitchen din. 


"Banda ni ki bawa Baffanki da Addata su sa miki albarka kinji Rahima. Allah Yasa budi ne zai zo miki da hakan."


Kasa boye murnarta tayi ta kuma rungume Ummi "Ummi nagode...dama kece Ummana da naji dadi"


Dammm zuciyar Salame ta buga taji wani irin abu ya tokare mata wuya. Ka haifi da ya rinka fatan dama wata ta haifeshi...kenan fa Rahima bata sonta ko?


"Kada na sake jin magana makamanciyar wannan kina jina. Ko me Adda Salame za ta yi miki kiyi hakuri domin duk duniya ba ka da masoyi sama da mahaifiyarka. Allah Yana fushi da mai sabawa iyaye"


Hawaye ne ya ciko idanun Rahima ta fashe da wani irin kuka "Ummi bata sona"


Da sauri Mairama ta sake rungumeta ko damuwa da lallen da ta cambala mata a jikin riga bata yi "tana sonki Rahima, nima kuma ina sonki. Baki san kece autar Ummi ba...Karami da kike gani dan karo ne kece autar"


Murmushi Rahima tayi saboda Emzee da Ummi ta ambata. 


"Ko ke fa...wanke fuskar muje mu caski naira"


Da gudu gudu Salame ta bar wurin kafin su fito ta nufi dakinsu. Abin da ya zame mata sabo a rayuwarta tayi wato kuka akan yadda Rahima ta dauketa. Yanzu ashe abinda take yi mata ya isa ya sanya Rahima jin inama ba ita ce mahaifiyarta ba? Hawaye sosai take yi zuciyarta ta kuntata. Tabbas ta cutar da 'yarta saboda wani dalili mara tushe wato rashin arzikin mahaifinta. Zama tayi a dakin tana ta tunane tunanen abubuwan da ta rinka yiwa mata. Sai kuma shaidan ya tuna mata da kudin da aka bada na kunshi. Kamar an tsikareta ta tashi tayi sama saboda bata ga Ummi a falon ba. Gara ta samu ta daidaita da 'yarta yadda ko arzikin yazo tare zasu ci abinsu.


Banka kai tayi cikin dakin kai tsaye ta sameta tana nade gift da wrapping paper. Kallon banzan da ta saba tayi mata sannan ta rike kugu ta mika mata hannu.


"Bani kudin"


Sai da Ummi ta bawa iska ajiyarta na cikakken minti daya ta karasa abinda take yi kafin ta dago kai "kin bani ajiyar kudi ne Adda?"


"Kada ki raina min hankali Mairama ina kokarin muyi komai cikin lumana tunda gidan da mutane. Kudin da aka bawa 'yata ta cikina Rahima na kunshi dubu dari nake magana a kai"


Ummi ko ci kanki bata ce mata ba ta tashi ta dauko kudin a cikin wani kit ta mika mata.


"Wato da har kinyi musu mazauni a cikin kayanki saboda bakar mugunta"


"Adda Salame..."


"Sunana kenan. Idan kinso kice Salamen kai tsaye ba damuwa zanyi ba"


"Kudi kika zo karba kuma na baki saboda haka ki fice min daga daki kafin ranmu yafi haka baci" Ummi tace a haka ma kokarin danne zuciyarta take yi sosai akan halin yayarta da yadda take yiwa Rahima.


"Oho dai, da fa bamu san asali bane sai ayi mana burga. Kunje kuna ta kwantar da kai a gaban mutane saboda ace kuna da kudi"


Kashingida Ummi tayi akan gado ta nuna mata kofa "sauka kije ga irinsu can kema ki kwantar da kan ko za'a dace"


Gani tayi da gaske bazata biye mata ga bakar magana ta yaba mata sai ta sauka kawai tana kunkuni. Rahima na ganinta da envelop din kudin taji wani irin kunci a zuciyarta don tayi imani da wuya ko kwandala ta bata a ciki wanda zata bawa Baffanta da Iya. Hawaye ke neman subuce mata taji sallamar Emzee.


Matan wurin ke ta yabon abinda su ka yi jiya ana cewa iyayensu sunji dadi shi da yayarsa kowa da baiwarsa. Duk zancen da akeyi Rahima yake kallo da take duke tana yiwa wata lalle a kafarta. Kin kallonsa tayi saboda a haka ma da kyar take yi jikinta ke rawa. Yadda take motsa hannuwanta yayi ta kallo har ta gama yiwa matar ta soma na wata sannan ya tafi.


**********


Karfe uku da rabi Awwab, Raji, Yousuf da Bilal suka fito daga gidan Mami kowa sanye da fararen kaya masu ado da koren zare da hula koriya. Saidai kowa dinkinsa daban ne amma shigar kenan kore da fari.


Awwab nasa kayan wani lallausan yadi ne fari kal mai kyau anyi masa riga iya gwiwa sai hannu dogo ya saka links masu wani stone green. Aljihun gaban rigar rabin yadin da aka yi shi fari ne daya rabin kuma green sai yayi kamar triangle. Maballan rigar har wuya su ma duka green dinne sai wani siririn ado na green din zare daga gefe saya. Hular kansa da tasha kari hadin zare green da fari ce dai. Kafarsa farin takalmi cover shoe sai silver agogon dior. Kamshi yake fitarwa mai dadi shi kadai yake murmushi yana tsaye a gefen mota ya zura hannu daya a aljihun wandonsa yana danna waya.


Text ya turawa amaryarsa cewa zasu dauko Arifah su biya su dauketa sannan su wuce. 


(Ni kunyar ganinka nake yi) ta rubuta masa.


(Ni kuwa kwana nayi mafarkinki...can't wait to see you baby)


Hoton fuskar kunya ta tura masa na whatsapp shine yake murmushi.


"Mintuna kadan ya rage ka ganta kake wannan murmushin kai kadai" Bilal yace yana bude gaban motarsa. 


"Bazaka gane bane dan uwa....I love her to the moon and back" yayi maganar yana lumshe idanu.


"Yau da bani da Fauziyya da ka saka ni neman aure amma yanzu sai dai nayi maka dariya don duk abinka sai ka jira anyi biki zamu bari ka dauketa"


"Kayi hankali kada ku ja mu bar abin fada har jikoki"


"Me kenan?" Yousuf yace yana bude motar da zasu tafi shi da Awwab.


"Bari dai nayi shiru wadannan mazajen kannena ne kada su raina ni"


Sai da suka gama barkwancin Raji da Bilal suka shiga mota daya Awwab da Yousuf guda daya. 


Su Awwab gidan Excellency suka wuce ko shiga basu yi ga Yousuf ya kira Arifah. A shirye take ta fito daidau gate inda suka yi parking. Shaddarta fara ce itama sai paint work green da stones daga wuya har kasa amma ba'a cika adon ba. Ashoke aka yi mata dauri dashi mai hawa-hawa tayi matukar kyau fuska tasha make up. Ga mayafinta green ta yafa a wuyanta. Yousuf gabadaya ya rikice ya fita ya bude mata kofar baya tana zama Awwab ya fito ya karbe key din motar.


"Ina hauka ne zan bari ka tuka ni idanunka suna bayan mota? Shiga kawai muje kada kayiwa matata asara"


Arifah dai kunya take ji murmushi kawai tayi tana gaisheshi. Yousuf dama jira yake yana shiga ya rungumota yana mata rada a kunne wai jiya basu gama taya juna murna ba. Da hannu ta rinka nuna masa saitin Awwab dake tuki.


"Wannan yafi kowa fitina ki kyale shi kawai"


Shiru yayi bai ce komai ba albarkacin Arifah da yake ganin mutumcinta sosai. Suna zuwa gidan an shimfida katuwar darduma wadda su Daada suka yi jam'in sallar la'asar. Su biyu suka tada tasu Arifah ta shige ciki.


Yau ma Mairama da kanta ta shirya Zayyan kamar kullum ya saka shadda army green dinkin tazarce. Dayake tsayi gareshi ba karamin kyau yayi ba.  Sai da ta tabbatar ya gama fitowa ta rinka masa wankan turare sannan ta dauko nata kayan. Itama farar shadda ce riga da zani amma dinkin Nijar anyi mata aikin green din zare ga mayafinta to-match. Ankon kenan dama su fito a 'yan Nigeria sak banda masu taro wato Major General Zayyan,  Muhammad Zayyan (Emzee), Zayyanatu Mustapha da Zayyan Hadir. Nasu kayan iri daya ne army green shadda.


Suna fitowa daga dakin Radhiya ta fito da ashokenta a hannu tayi wata kwana da ribas ta dawo kawai sai ta daga tsalle ta dane Daada.


"Anya banyi garajen aurar dake ba, Fillo yarinyar nan bata girma ba fa"


Ummi sai dariya "kunfi kusa soja da 'yarsa."


"Ni dai ku tsaya nayi muku hoto" tace tana gyara musu tsayuwa "wayyo ni Daada da Ummina sunyi kyau"


Dariya ta basu ta matsa baya zata dauka da wayarta Zayyan ya rungumo Mairama a jikinsa. Ita kunya Radhiya kuma ta kanne ido daya wai a zuwan bata gani ba. Sunyi bala'in kyau ta rinka daukarsu Zayyan yana biye mata suna yi a tsaye ko a zaune. Muryar Arifah da ta jiyo ne ta bar wurin da sauri taje ta karasa shiri. 


Hudu da ashirin kowa ya sauko sai fararen kaya kake gani da koren mayafi ko hula. Zayyana gown dinta aikin da farin zare aka hada shiyasa ta saka farin mayafi bayan anyi mata daurin yayi wanda dukkansu matan shi suka yi mai hawa-hawa da dankwalin kayan. 


Mutane ke ta fitowa babu wanda ya lura Rahima bata fito ba. Ita kadai take kokonto idan Emzee yaki dawowa ta kade. To amma babbar matsalarta yanzu bai wuce bayanta da yake ciwo saboda dukawa ba don yau ta aikatu. 


Irin kayan Arifah sak hatta takalmi da jaka Radhiya ta saka rigar tasu mai high neck. Basu saka sarka ba sai wasu doyayen dankunne green and white masu tsada da daukar ido.


Ta kware da tafiya da heel bata jin wahalarsa ko kadan tana taku daidai ta iso gaban motar. Zagayawa yayi ya bude mata daya gefen gaban yana tsaye zata shiga wani ni'imtaccen kamshi na shigarsa ta ko ina ya rike mata hannu. Kallonsa tayi sau daya ta dauke kanta.


"You look sweet baby"


"Ka fini yin kyau Hammana" tace tana murmushi.


Hannu kawai yasa ya janyota ta fito ya sake matso da ita jikinsa sosai yayi musu selfie.


"Akwai bil adama a bayan mota" cewar Yousuf bayan ya sami chance din kaiwa Arifah kiss a kan hancinta tana rufe idanu.


Dariya Awwab yayi wai yanzu damarsa ce sun gama nasu bai ce komai ba. Zama Radhiya tayi ya gyara mata rigarta ya rufe kofar sannan ya ja suka tafi kana leka motar taurarin soyayya sun mata kawanya.


Wani katafaren events hall suka nufa inda suke iya ganin taron motoci sun cike wurin parking din ciki an fara layi a gefen titi. Suna shiga Emzee yana fita bayan ya karbi mukullin motarsu daga hannun Ibrahim da su suka ajiye su Laila da Zayyana.


"Ina kuma zaka je kasan yanzu su Daada zasu iso a fara"


"Yanzu zan dawo Rahima zan dauko please kace bazan dade ba idan an nemeni"


"Emzee kodai-kodai?" Ibrahim yace yana daga gira.


Cike da shauki Emzee yace "fadi ka kara bros yarinyar nan ta cuceni...ko shiryawa banyi ba kawai na nemi zuciyata na rasa ashe ita ta dauka. Da tayi warning dina kasan kai zan fara sanarwa"


Duka Ibrahim ya kai masa a baya yana kyakyata dariya "shege malamin soyayya ya fada ruwa....tabdi amma har ta bani tausayi ta kwaso Emzee chewing gum"


"Me ka mayar dani?"


"Irin mazan da idan suna son mace zasu iya sadaukar da komai nasu domin kyautata mata mana"


"To kai din ba shi bane?"


Bangaren da Zayyana take Ibrahim ya kallo "I can die for her man"


"I feel you bros nima haka nake ji. Ina bukatar time da ita ne domin in san ko wacece. Na dai fi tunanin tana da alaka da gidansu Halifa maybe cousin dinsu ce tunda ina ganinta da Hibbah."


Gaban Ibrahim ne ya fadi ya soma tunanin yaya akayi Emzee bai san wace Rahima ba. Tunawa yayi da yadda ya tsani Gwaggo Salame yaji jikinsa yayi sanyi. Bai taba ganin Emzee so cheerful ba irin yanzu, gaskiya bazai iya rushe masa wannan sabon farincikin ba. Zai bari ya gano da kansa kila sanadiyar shiryawar iyayensu kenan.


"Na tafi" yaji Emzee yace.


A gurguje ya tada motar ya koma gida. Minti goma ya kaishi saboda babu nisa da gidansu. Sai yanzu ya tuna bashi da nambar wayarta to ta yaya zai kirata. Idan kuma ta tafi wurin bata jira shi ba fa. Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan sai ga mai aikinsu 'yar budurwar ta fito itama a shirye fes da ita.


"Yauwa don Allah kirawo min Rahima a dakin Adda Radhiya."


"Kowa ya tafi fa muma Ummi tace yanzu dreba zai dawo daukarmu shine na fito dubawa da ka shigo"


Gwiwarsa ce tayi sanyi ya koma motar sai ya sake dawowa zuciyarsa na fada masa Rahima na jiransa "daure ki duba min nasan tana nan"


Ba musu ta shiga gidan. Dakin kasa da suke ta shiga tayi sa'ar ganin Rahima a shirye cikin nata kayan kamar kowa Ummi ta dinka mata sai dai ita dasu Zahra dankwalin kayan suka saka. Arifah da Radhiya ne kawai masu ashoke manyan amare. Mayafinta daidai da ita har ka ta lulluba shi yadda ta saba tayi kyau sosai.


"Karami ke kiranki a waje"


Da faduwar gaba ta tashi tana tunanin karfin halinta na zama don yace ta zauna. Sai dai bata jin akwai ranar da za ta yi fatan yi masa musu saboda babban matsayin da ya kwata ta karfin tsiya a zuciyarta don itama bata shirya ba.


Kayansa hatta hula sak na mahaifinsa yana tsaye a bakin kofa ta fito. Ido suka hada ya sakar mata murmushi ta janyo mayafin ta rufe rabin fuskarta.


"Hey kada ki cuceni ki hanani ganin fuskarki yau ba kawance"


Langabe kai tayi suna tafiya wurin motar "sai me?"


"Muhammad da Rahima"


Sake rufe fuska tayi komai nata yana burge shi matuka ya dora hannunsa a saitin zuciyarsa "my God, she is so adorable"


Sun kusa kaiwa motar yaji an kwala masa kira daga cikin gidan "kai Karami ku jirani wannan dreban da za'a turo ban ga ranar zuwansa ba"


Ba kowa bace illa Salame ta taho buguzum cikin wata kodaddiyar shadda wadda take yiwa kallon mai kyau har yanzu tana goye da Khadi kamar wata jaririya.


Gaban Rahima ya fadi zuciyar Emzee kuma tamkar ta fito ta baki saboda bacin rai har ta iso bakin motar ta bude gaba ta shige kwam abinta.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Dan duka kanta tayi tana lekensa ta sake daga murya "kai shigo mu tafi mana" ta kuma lekawa ta daya bangaren "kema shiga kin yiwa mutane wani kikam"


Emzee alama ya yiwa Rahima da ta tsaya don bai ga dalilin daukarta da makiyar Ummi a mota daya ba. Sannan abu na biyu baya son a matsayinta na yayar Ummi tayi abin zubar da mutumci a gaban Rahimansa.


Khadi da ke kan cinyar Salame kuma duk maganar da take kusan akan fuskarta tayi sai sa hannu tayi ta toshe hanci babu kunya tana yiwa babarta wani irin kallon haushi "hmmm Umma hmmm wali-wali a bacinci"


Da sauri Emzee ya fitar da kansa kafin ya

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment