Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har a makarantunsu. Tarbiya ce irin ta musulunci batare da ta fito zahiri ta tallata musu addinin ba. A fakaice ta rinka kwadaita musu tana fatan wataran idan da rabo su karba. Farkon zuwanta sun so hanata zuwa da lullubi ko karamin hijab. A take tace ta bar aikin. To amma amanar da suke gani daga gareta yasa da kansu suka sake nemota.


Aikin Mami a gidan yana daga cikin abinda Major bazai taba mantawa a rayuwarsa ba. Wai shi Mustapha da ya kai matakin Major a soja shine matarsa take aikatau. Abinda yafi karfi a kasarsu yazo lalura ta cinye komai nasa yafi karfinsa. Bashi da tamkarta a duk duniya. Ya amince samun kamarta sai wata matar sojan. Jarumar mace matar jarumin namiji.


Katuwar harabar gidan tasha gyara da fitilu da flowers ko ina yana kyalli ga kayan abinci a gefe debi wanda kake so.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Max, Anna da Liam sune 'ya'yan da suka tashi a hannun Mami. Suna ganin shigowarsu lawn din suka taho suna murna. Idanun Anna jazur taci kuka tun safe take abu daya.


Rungume Mami tayi "bana so ki tafi Naanaa" tace cikin yaren jamusanci.


Da yaren Mami ta maida mata "kiyi hakuri Anna, watarana zan zo ziyara ko ke kizo mana Nigeria ko"


"Zaki zo aurena next year?"


"In sha Allah"


Hawaye Anna take ta rinka sumbatar kumatun Mami ita kuwa sai dariya. Liam da Max hannuwanta suka rike suka kaita tsakiyar wurin suna nunawa jama'a Naanaa dinsu. Mai aiki ce amma wadda take a inda aka san darajar masu aiki har masu gida suke karrama su.


Ta sami kyaututtuka da yawa daga abokan aikinta da abokan arziki.


Frau Marie Schmidt ta kawo envelop da kudi a ciki ta bata sannan ta bawa Fauziyya da Zahra wasu setin dankunne da sarka 'yan ubansu wai su saka da bikinsu. Zayyana ma an bata katon teddy kusan kansu daya. Tana ta murna Mami a ranta tayi dariya kawai. 'Yan kasarmu ina muka wani san darajar teddy. 


Hotunan tarihi suke dauka Major ya daga waya yana fadin inda suke. Ko minti biyu ba'ayi ba sai ga matashin saurayi kyakkyawa wankan tarwada mai cike da kwarjini da haiba ya shigo wurin sanye da uniform dinsa na matukin jirgin KLM mallakar kasar Germany. Jacket da wando ne navy blue sai farar shirt a ciki kansa sanye da hula irin ta Captain din jirgi. Mata hudu ne a gefensa hagu da dama air hostess kowacce da uniform riga da skirt sky blue suna rike da flowers masu kyau.


Shigowar tasu ta kayatar da mutanen wurin bare iyayensa. Yana shigowa kai tsaye wurin Major ya nufa ya rungume shi. Mami ta saki baki sai kuma ta daure fuska cikin wasa.


"Awwab, yau din ma?"


Sai da yayi mata dariya sannan ya rungume Maminsa a kunnenta yana cewa "sorry Mamina"


'Yan matan da suke abokan aikinsa kowacce ta mika mata flower da dan gift suna mata fatan alkhairi.


Awwab ya fiddo tickets biyar daga aljihun sa ya mikawa Major.


"Daddy ga nawa gift din...Captain M.A Mustapha shine zai ja jirginku zuwa birnin Abuja. Sai da na duba schedule dina na sayi ticket. Tafiya ta dawo nan da sati biyu. I hope it is okay"


Zayyana tayi tsalle ta dane shi tana ihun murna. Mami sai murmushi kawai na jindadi. Major kuwa tsokanarsa yake yi wai bazai shiga ba kada ya zubar dasu a teku.


An gama party lafiya suka koma gida tare dashi. Shirye shirye ya kankama inda suka hada ya nasu ya nasu sai gida Nigeria.


***********


Iyayen Zainab sun sakata a gaba kowa da abinda yake cewa tun da ta sanar musu cewa a yiwa iyayen Hadir magana akan aurensu.


"Wai shin idan kin koma soyayya zaki rinka zuba muku a kwano kuna ci? Ke ba aiki shi a zaune. Ni har yau ban gamsu da ba ke kika kashewa kanki aure ba" mamanta tace a hasale.


Babanta ne ma mai dan sauki a gareta "Zainab nasan kila ko a wurin Ibrahim kina ji cewa jikin Hadir babu wani sauki sai na musulunci. Kinje kin shafe shekaru tare da Musa kin saba da jindadi. Ta ina zaki koma gidansu?"


"Baba na fada muku ya bani gida a Kano sannan ya kara min jari akan wanda ya bani tun da nake zuwa Dubai saro kaya dashi. Alhamdulillah Allah Ya wadatani Abbansu Aisha ne sila. Ni zan cigaba da tafiya kasuwancina ne Ibrahim ya rinka kula dashi idan bana nan"


Mamanta ta kara kulewa "sannu uwar tsari, waro har kin gama tsara yadda komai zai kasance"


Allah Ya sani tana son iyayenta kuma tana girmama su. Amma wannan karon tana jin tayi girman da ya kamata a karbi uzurinta idan tazo dashi.


"Idan ba kwa so na komawa Hadir bazan koma ba. Amma wallahi bazan kara aure ba har na mutu"


Tsam ta tashi daga dakin Baban nata. Sun san Zainab da taurin kai. Anyi sa'a ma zamanta da Musa Allah Yayi da tsayin kwana. Tufka suke da warwara suna guje mata matsala a gaba. Karshe mahaifinta yace su barta Allah kadai Yasan dalilin wannan soyayya da take yi masa.


Bayan kwanaki ana muhawara da 'yan uwa babanta da kansa yaje Kano da dan uwansa ya gabatarwa Baban Hadir bukatarsu. Sunyi matukar mamaki ace har yanzu Zainab tana son dansu. Matar da sun sani yanzu ita dashi kamar wutsiyar rakumi ne da kasa. Daga irin suturun da take yiwa Ibrahim da abubuwan zamani da take wadata shi dasu zaka san Haj Zainab take don tayi Hajji da Umara albarkacin Musa.


"Idan na fadawa Hadir bazai yarda ya aureta ba saboda lalurarsa" Babansa ya amsa musu a sanyaye. Hadir ya riga ya karbi kaddarar rayuwarsa.


"Sai kayi shiru mu kulla abinmu a tsakaninmu ba shikenan ba" Kawun Zainab ya bashi amsa.


Da izinin Allah a ranar basu tashi ba sai da aka mayar da auren Zainab jaruma mai sadaukarwa da Hadir jarumin kasata da kasar ta dade da mantawa dashi.


Da aka kirata da wannan kyakkyawan labari tayi kukan farinciki sosai. Sati daya aka diba tariya inda Baba ya sa Ibrahim ya kwashe kayan sawarsu ya rinka maidawa gidanta da yake Janbulo. Hadir yana kallo bai iya tambaya sai ya sawa ransa ko gyara za'ayi a dakin.


**********


"Wayyo Innawuro, kiyi min rai....Ummiiiii ki ceceni" 


Ihun Radhiya kenan da ya karade gidan tana zaune Emzee ya danneta Innawuro zata yi mata aski.


Mairama hakuri take bata akan ta bari ayi "idan ba'a magance kwarkwatar nan ba wallahi duka sai kin shafa mana. Har na gama makarantar kwana ni banyi ba. Ku baku iya kula da kanku sai kazanta da gayun banza"


Kyabe fuska ta sake yi hankalinta yana kara tashi "zan wanke Ummi harda karkashi in gumbuda musu gishiri Yasin duk su mutu"


"Innawuro ko za'a bari ta gwada saka karkashin?" Mairama tace a hankali tana jin kunyar shigarwa 'yarta.


"Kyaleta Mairama don baki ga kan bane. Makero ya cinye keyar sai gashi kadan, gaban kuma amosani da kwarkwata. Yarinya mai cikar gashi da laushi duk ya lalace saboda rashin kula. Na fada miki Mairo ta biyo a cikar nan zai tofo da wuri"


"Ayya Ummi ki tausaya min mana" tace a wahale.


Emzee ya sake sakar mata nauyinsa akan cinyarta da ya dora kafafunsa yana dariya.


"Mugu daga ni"


Sake danneta yayi tayi kara Mairama ta kasa hakuri "Karami ka kiyayeni fa, me kake mata ne?"


Innawuro ya kalla suka sa dariya wai ta tarewa abokiyar fadanta sai ta kama bakinta ta kunshe.


Radhiya na ganin gashinta ya soma zuba ta soma wani sabon kukan "kiyiwa Allah da ManzonSa Innawuro ki bar min na zaman falo. Kina ji fa Baffa Gide yace duk aurar damu zaiyi"


Wannan karon dariya harda Mairama "wanne ne na zaman falo kuma?"


"Wanda zan rinka daurewa da ribbon inyi kwalliya"


Innawuro da Emzee suka cigaba da tunzurata tana ta zuba ana kwashe gashin "ance miki aure za'ayi miki ne kike neman gashin zaman falo?"


"Aure kuma Innawuro ai kamar habo ne. Yanzu idan kika kwashe gashin nan miji yazo yay...." shiru tayi da ta ji ana kankarar kan nata da reza.


Wani uban ihu ta saka an gama askin Innawuro tana mata kwaryar molo na gasken da reza ana kwashe sauran gashin da fatar da makero ya gama cinyewa tayi wani fari da tudu-tudu.


"Wayyo Allahna na shiga uku na lalace, wayyo, wayyo, wayyo"


Mairamu maficin hannunta ta daga zata kwada mata "wane irin sakarci ne wannan kike mana ihu kamar wata mara hankali"


Sai da ta tashi ta makawa Emzee harara da daradaran idanunta sannan tayi gaba tana cewa "dama Ummi wane hankali ne zaiyi saura akan budurwar da bata da gashi ai sai gyaran Allah"


Baki ta rike tana kada kai "anya yarinyar nan ba dabanci ta koyo a bodin din ba?"


"Ummi gang garesu fa na fitinannu inji wata kanwar abokina"


Daga cikin daki tana kuka ta leko "almunafunfun me ya kaika makarantar mata har ka jiyo gulma. Ummi ta sani dai SS ne ba wata kungiya ba"


Tsawa Mairama tayi mata akan ta dena amfani da kalmomi irin wadannan ga kaninta. 


Innawuro tace "kema kinsan yau tunda da amincewarki akayi askin nan to dukkanmu sai ta nuna mana fushi take yi. Kai Karami zuba gashin nan a leda kaje ka kona. Kwarkwata harda ta sayarwa."


Hannuwansa yayi saurin nadewa a kirji cike da kyama "kwarkwatar zan taba? Ashe kowa zaiyi susa a gidan nan"


Dama Umminsa yake son tsokana ta fara fada yana dariya ya kwashe yaje bakin murhu ya zazzage. Waje yayi bayan ya wanke hannunsa aka bar su Mairama su kadai a tsakar gidan. Tayi zurfi a tunani da kwadayin ina ma ace zata iya ganin kamanin yaran a yanzu da suka kara girma. Alheran da Zayyan dinta suna da shekaru sha takwas da sha bakwai.


"Radhiya kyakkywa ce kamar wata dan daren goma sha hudu, Karami kuwa yadda kika san sojan maigidanki ba maraba sai haskenki da ya dauko"


Murmushi Mairama tayi kunya na kamata "Innawuro me ya kawo wannan bayanin kuma?"


"Daga yin abin arziki, godiya kawai zaki yi tunda na faranta miki"


Karamar dariya tayi ta lalubi sandarta ta tashi. Yanzu ta gane hanyar dakunan gidan ko babu dan jagora. Nasu ta karasa tana mitar wane irin jan kunne zata yiwa Alheran mai tambotsai. Kwanansu hudu tun washegarin dawowarta daga makaranta wai a saya mata form din makarantar sojoji. Tun Mairama na daukar abin wasa sai ga zance har kunnen su Ardo. Shine aka fara zancen aurar dasu. Ita kuma tana da burin Radhiya tayi ilimi mai zurfi amma bazata iya watsa musu kasa a ido ba. Tunawa da tayi anyi aski yau gidan kowa mai laifi ne a wurin 'Yar soja ya saka ta dariya ba shiri.


**********



Hadir sai tunani yake yi ina zasu je bayan masallaci maimakon su wuce gida. A motar kaninsa da yake kaisu sallar juma'a suke tare da Ibrahim. Yau sababbin kaya Ibrahim din ya saka masa iri daya da nasa, yadi ne mai kyau da laushi ruwan kwanduwar kwai anyi musu dinki iri daya wanda akayi da zare coffee color. Hatta hulunansu iri daya ne masu kalar zaren dinkin. Sai kamshi suke bazawa sunyi wani irin kyau. Tarin tambayoyi fal a zuciyar Hadir tun da aka fara komai. Mai aski har gida Ibrahim ya kawo yasa yayi masa gyaran fuska sabanin da da yake masa a gida da clipper da Zainab ta siyo masa.


Sun taimaka sun dora shi akan kujerarsa wheelchair bayan sun shiga gidan. Daga gefen matattakalar shiga anyi shafen sumunti alamun hanya ta hawa da wheelchair din. Gangara babansa yayi cikin ni'imtaccen falon da ya wadatu da sanyin AC da kamshi. Daga nan kanin Hadir yayi musu sallama ya juya abinsa. 


Idanunsa na nuni da tashin hankali sai waige yake yi Ibrahim ya barshi ya nufi bakin wasu steps hudu da za'a taka abi hanyar dakuna. Su ma a gefe akwai wurin tura kujerar.


Wai kunya ce ta hana Zainab fitowa tana jinsu ta makale a daki. Ibrahim na taba kofar ta taso da wayoyinta a hannu kamar fitowa dama zata yi.


Wani kayataccen murmushi yayi mata na jindadi "Mama kinyi kyau wallahi"


Irin yadin jikinsu ta saka. Hatta zaren dinkin iri daya ne nata doguwar riga anyi mata surfani siriri mai kyau adon. Daurinta shima yayi kyau ga sarkar gwal dasu awarwaro. Haj Zainab kenan mata a gidan Hadir.


Murmushi tayi sai kuma tace "Wuce muje ni"


"Fara zuwa Mama naji cikina yana juya min"


Bai jira ta amsa ba ya fita da sauri ya shige sabon dakinsa ya dire akan gado yana murna. Abokinsa ne ya bashi shawarar kada ya tsaya musu a ka ya barsu su kadai.


Hadadden kamshinta ne ya fara zuwa hancin Hadir kafin yayi tozali da Zainabu Abunsa. Rufe ido yayi ya sake budesu  a kanta. Wai da gaske Zainab ce kuwa?


A nutse ta iso har gaban kujerar tasa sai ta durkuso ta daidaita fuskarta da tasa. Hawayen farinciki ne ya sauko mata shi kuma idanunsa sunyi ja ya kasa dauke ido daga kanta.


Hannu tasa a kasan habarsa ta dago kansa tana masa kallon ido da ido ta sumbaci bakinsa sannan ta rungumo shi a jikinta tana mai kankame shi sosai ta saki kuka.


Hamdala Hadir ya rinka yi a jejjere a zuciyarsa don ya tabbata abu daya ne ma'anar kawo shi nan gidan da kuma kasancewarta a cikinsa.


**********


Danginsu Major na kusa da na nesa sai tururuwa suke domin ganinsu da yi musu barka da dawowa. Shekaru a kalla sha hudu ba wasa ba. Anyi haihuwa anyi rashi duk basa nan. Gidan kullum a cike da baki. Satinsu biyu kafin suka samu damar kai kayansu sabon gidan da suka rinka turo kudi domin ginawa a GRA. Sun sayi filin tun farkon fara aikin Mami kafin abubuwa su kara tsada.


 Kwanansu biyu suna aikin son ganin gidan ya dau saiti abu yaci tura suka hakura sai sun dawo daga wurin su Hadir da Mairama.


Wannan Sojan mai alkawari da suke turawa kudin Mairama shine ya binciko musu Hadir yana Kano gidan iyayensa. Major yayi ta mamakin to me ya same shi yake gida. Mairama kuma wan Zayyan wato Maikudi tun a baya yace masa tayi aure amma Alheran tana Sakkwato wurinsa. Da wannan suka yi amfani akayi shawarar  Kano zasu fara zuwa sannan su wuce Sakkwaton.


Basu riga sun sayi mota ba Daddy Harun da yake Abuja yanzu shine ya basu wata bus fara mai kyau da iyalinsa ke amfani da ita wurin tafiye tafiye tare da dreba.


Doki da fargabar yaya rayuwa ta kasancewa bayin Allahn nan sun cika zukatan su Mami da Major. Zahra da Fauziyya suna ta kokarin tuna Antinsu Zainab da Ibrahim da suke fada akan daukarsa. Babu wadda tayi shekara goma cikinsu lokacin. Labaran duka wanda Mami ke basu ne don babu abinda suke tunawa. Awwab kuma tuni 'yan kwanakin hutun nasa ya cinyesu a Katsina gashi tsarin aikinsu ba na zama wuri daya bane.


Da tambaya Allah Ya kaisu gidansu Hadir can cikin lungu. Bayan gaishe gaishe da iyayensa Major ya gabatar dasu. Sai da ta share hawaye tace yau kwanansa ashirin da shida da barin gidan an mayar da aurensa da Zainab tsohuwar matarsa.


"Bangane ba, da auren nasu ya mutu ne?" Yayi mata tambayar don neman karin bayani.


Murmushi tayi masa ganin hankalinsa ya tashi "Bari dai nasa a kaiku can gidan nasu sai kuji daga bakinta"


Wayar Zainab tasa aka kira mata bata shiga saboda suna asibiti. Kwanansu biyu da aure ta mayar dashi asibitin koyarwa na Kano wato Aminu Kano Teaching Hospital. Gwaji da bincike tasa ayi masa sosai inda aka gano matsalar da ya samu a kashin bayansa yayin fadawa wannan kwazazzabon a Liberia ita ce silar mutuwar jikinsa kashi ya danne wane bangaren na lakar bayansa. Rashin magana kuwa Likita ya tabbatar mata da cewa shock wato firgici ne ya haifar dashi. Da ace tun a baya sun tsananta dabarun dauke masa damuwa kila da tuni an manta da ya taba dena magana..


"Duk da haka Hajiya mijinki zai iya samun lafiya amma shawara mafi a'ala gaskiya ki fitar dashi ko da Egypt ne idan da hali. Lalurar ta dade a jikinsa yana bukatar kwararru a kansa da ingantattun kayan aiki"


Kallon Hadir tayi ta saki murmushi "Doctor ka taimaka ka tayani duba asibiti da kuma rough estimate na abinda zan bukata"


Bata ankara ba ta bayan kujerar taji an rungumo wuyanta sosai ta sa hannu tana dukan hannayen Ibrahim "dan gidanku shakeni zaka yi?"


Hadir yayi murmushi suna bashi sha'awa zamansu tamkar kaka da jikanta. Ibrahim dinsu matashi ne wanda kana kallonsa sai ka sake bare yanzu da mamansa ke kara wadata shi da kaya sa suka dace da zamani.


Kin sakinta yayi yana kara manna kansa a wuyanta "Mama mungode injini da Babana"


Kwalla taji a idonta da ta kalli Hadir ta ga ya gyada kai "ni ku tashi mu tafi kuna neman saka mutane kuka."


Ibrahim ke tura kujerar babansa bayan ta yiwa likitan godiya suka kama hanyar wurin ajiye motoci. Gasu dai suna tafiya miji na zaune amma dole su baka sha'awa yadda duk suka yi kyau ga kuma alamu sun nuna iyali ne da ke matukar kaunar juna.


"Mama ki koya min tuki don Allah"


"Da wannan rawar kan"


"Baba ai bani da rawar kai ko?" Ya dukar da kansa yana tambayar Hadir shi kuwa ya gyada kai yana supporting dansa.


"Kuma sunana zaka fara fada idan ka warke ko"


Hararar da Zainab tayi masa ce ta saka shi wata dariyar shakiyanci "baka isa ba yaro"


Dariya suka rinka yiwa juna kowa ba cewa dashi za'a fara ba kace uwa da danta bane.


Tana tuki Ibrahim ke nuna mata hanya don bata waye da garin Kano ba wayar autansu Hadir ta shigo yace yana tare da baki a kofar gidansu. Ya sanar dashi suna hanya sun kusa karasowa. Da ya fadawa Zainab tace su waye.


"Bari na kira na tambayeshi"


"A'a barshi kawai"


Bus ta gani a kofar gidanta da mutane a ciki. Mami tun da Zainab ta karyo kwana ta ganeta. Jikinta na rawa tana sauri ta bude kofar motar ta fito. Major ma haka ya fito yana hango Hadir a daga bayan motar.


Hannunta taji yana rawa da ta tabbatar da su waye a kofar gidan. Ta juya a hankali za ta cewa Hadir ya gane su sai ta ga yana hawaye. Bata iya gyara packing ba ta kashe motar ta fito da sauri ko takalmanta bata saka ba.


Hannu ta dora akan bakinta ta toshe kukan da yake barazanar yin sautin da kila sai makota sun leko ta suka tako gaban juna sunyi sharkaf da hawaye.


"Mami?"


"Antin su Zahra"


A wajen nan suka rungume juna suna kuka, kuka na gaske. Major ya karasa ya budewa Hadir kofar bayan fuskarsa cike da annuri.


"Lieutenant fito mu gaisa"


Hadir ko motsi baiyi ba sai rufe ido da yayi hawaye mai dumi na sauko masa. Da yana da lafiya wallahi zai sarawa Major Mustapha ne domin soja ne a gaban ubangidansa.


Ibrahim ya fuskaci bai san yaya baban nasa yake ba ya cire kai ya kira mamansa.


"Mama zo mu fito da Baba daga motar"


A kidime Major yace "me ya same shi?"


Zainab ta dawo tana kuka tana dariya tace Ibrahim ya bude gate su shiga ciki. Kallonsa su Mami suke yi ya budw gate din ta shigar da motar sannan duka suka shigo. 


Wheelchair Major ya ga Ibrahim ya dauko a boot yaji zuciyarsa ta karye Zainab tazo zata taimaka su dora shi yace bari yasa hannu. Hadir ba kiba gareshi ba shiyasa ma suke jin saukin daga shi din.


Sai da ya zauna Major ya dube shi da tausayawa "kai kuma taka lalurar kenan Hadir?"


"Baba baya magana"


Zainab ta share hawaye ta bude musu kofar gidan. Mami da Major mamaki ya kara kama su da jin wai baya magana kuma.


Sai da suka zazzauna yaran suka sake gaishe su Zainab ta rike baki "yanzu Zahra da Fauziyya ne haka? Ikon Allah, Inna Awwab din Mairama. Ita kuma wannan 'yan matan kamar a tafi a barmin ita wace"


"Zayyanatu sunana" ta amsa da kanta.


Mami tana murmushi tace "Daddy yaso yiwa Zayyan takwara sai tazo a namiji"


"Allah sarki Mairamu da Zayyan ban san yaya suke ba"


Hadir sai runtse idanu yayi Mami da Major na kallonsa da ita. Mami ta daure tace "ashe baki san Allah Ya karbi ran Zayyan tun a Liberia wurin ceton rayukan mazajenmu ba"


A gigice tace "ME??? Baban Radhiya ya rasu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"


Kuka suke yi sosai mazan na hawaye harda Major duk dakiya irin tasa. Zainab ta tsahirta tace su Zahra da taga suna tayasu kukan su shiga dakinta bari ta aika a siyo abinci don bata yi girki ba.


"Turasu kitchen kawai su dafo mana"


"Ayi haka ko ware gajiya basuyi ba. Naga alamun daga nesa kuke"


"Babu komai ku shige kitchen ku duka kowa tasa hannu"


"Ibrahim jeka sai ka nuna musu. Su dafa mana abin da suke so, ko motsi bana son yi daga wurin nan"


Sun san dai wai wayo ake son yi musu. Suna yin hanyar kitchen din Ibrahim ya dawo da baya ya labe sai ga Zayyana ita ma ta dawo kusa dashi tana kara kunnenta a jikin kofa.


"Meye haka" ya dan sha kunu.


A shagwabe tace "Your mummy and daddy are making mine to cry" 


Wane kallon sama da kasa yayi mata "sannu baturiya ai ni ya kamata nace haka"


Kunnuwansu Zahra ta rike su biyun Fauziyya kuma tace "ku rufe mana baki dalla can muji me ake cewa sosai"


Duka su hudun suka sami wurin tsayawa suna jiyo labaran ban tausayi daga iyayensu. Yadda su Mami ke kuka a falon haka suma suke yi.


Sun tausayawa juna sosai kowa da irin tasa kaddarar. Damuwarsu sai kuma ta karkata kan Mairama da Radhiya.


Sun share kusan awa suna jajantawa juna sannan Mami ta dan bude murya "yaya ne shiru babu ku babu abinci"


Zahra ce ta fara fitowa taje ta fada jikinta tana kuka.


"Kuji min yaran nan, labe kuka yi kenan?"


Zayyana ta gyada kai tana sababbin hawaye. Zainab tayi dariya "to yau kunji rayuwar iyayenku ko"


Ibrahim ba kunya ya koma gefen Zainab kamar zai shige mata ciki yana kara son mahaifiyarsa.


"Anya wannan zaiyi soja kuwa?" Inji Major


"A'a wallahi ni malamin makaranta zan zama." yace da dukkan gaskiyarsa.


Suna ta dariya Zainab ta dauko kudi ta bashi "kayi sauri ka siyo mana abinci tunda labe ya hana ku girki"



Kwanan Radhiya biyu da yiwa gidan Ardo yaji tunda aka yi mata aski. Yaran dangi sa'aninta duk Emzee ya fesa musu sai ta wuni suna zuwa gidan tsokanarta. Na yau yafi bata haushi harda cire mata dankwali gashi Zakari dan gidan Baffa Habubakari da take hasashen yana son ta yana gidan.   'Yar yayarsa ce ta cire mata kullin maganin da take yi a kanta yanzu kunya ta isheta. Zakari sai ya rufe yarinyar da fada ya fita.


Zaune take a daki tana kwafa don idan ta kamata sai jikinta ya fada mata, dazu ma albarkacin kawunta taci kada abin kunyar yayi yawa. Muryar Baffa Gide taji yana fada yana sanar da matarsa ya rasa taurin kan da yake damun Mairama. Maza sun fi biyar masu neman aurenta amma kowa yazo sai tace wai ita makauniya ce. Yayi iya kokarinsa ya samu makaho dan wani attajiri a cikin Giade mai mata biyu shine yaje ya sanar da ita ta watsa masa kasa a ido.


"Na fuskanci yarinyar nan dama can fakewa take da makanta amma bata son yin aure"


"To banda abinka Malam ku kyaleta mana."


"Sai ta rayu babu aure? Yaran nan suna nasu auren fa zata soma jin shiru da kadaici. Ni gata nake son yi mata amma taki gani. Fitowa nayi na barta tana ta kuka"


Hijabinta ta figo bayan ta gama jin bayanin Baffa Gide tace zata tafi gida.


"Dena hararata ba kinji nace na barta tana kuka ba ni ban taba miki uwa ba"


Iyalle matarsa ta soma dariya don fuskar Radhiya a hade take.


" 'Yar soja a gaida gida"


Tana zuwa gidan ko dakin Innawuro bata je ba ta tafi wurin Umminta. Hotuna ne a hannunta tana shafawa tana kuka. Babu mai sanin yanayin da zuciyarta take ciki sai wadda ta tsinci kanta a irin yanayin. Zayyan ya tafi ya barta kuma babu wani kwakkwaran bayani da zata kama taji salama a ranta game da mutuwarsa. Ko ranar da ya rasu bata sani ba sai kiyasin lokaci da aka bata. Saurin daga pillow tayi zata boye su da taji motsin mutum.


Radhiya ta rigata ta hanyar karba tana kallon iyayenta a ranar bikinsu.


"Ummi"


Share hawayen take da sauri kafin ta fara tsareta da tambayoyi.


"Meye, ba yaji kika yi mana ba mai kwal kwabo"


Radhiya tayi dariya duk da ta tsani askin. Tana son farantawa mahaifiyarta.


"Kaina yanzu fa yafi dadin wanka. Insa sabulu harda soso in dirje shi. Idan na shirya na mulke abina da man

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment