Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baiyi magana da matarsa ba. Falon gidan ya nufa lokacin wurin takwas na dare. Tun kafin ya shiga yake jin murya kamar ta Ghazalatu da Mummy Gambo. Mamaki yake me suke a gidan a daren nan.


Yana shiga Mummy Gambo ta soma dariya "ango kasha kamshi"


A ladabce ya gaisheta yana tambayarta Daddy Haroun. Mami ya tambaya Daddy tace yana daki ya shiga.


Tunda ya shigo Ghazalatu ta kasa sukuni sai aukin murmushi tana fari da idanu sai da Mummy ta zungereta "baki gaishe da yayanki ba"


Ta turo baki "to ba shi bane kamar bai ganni ba"


Wucewa yayi abinsa duk da yana jin Mami tana cewa me yasa zai share mata 'ya. A ransa yace "Mami kenan, kema dai kin fada ne kawai don kada ace baki damu ba"


Mummy Gambo tace "jira kike yi ya fara gaisheki ko me da zaki ce kamar bai ganki ba? To ni dai bana son rashin kunya. Ku sulhunta ke da dan uwanki a cigaba da zumunci kamar da"


Murmushi Mami tayi don kada ta gwasale kanwarta a kokarinta na son farfado da zumuncinsu "kyalesu Gambo sun fi kusa ai, tashi Ghazalatu ki shiga wurin Zahra nasan tana daki tunda har yanzu Bilal da Raji basu dawo ba"


Tana tafiya Mami ta cewa Gambo gobe ta shirya su je gidan Hussaina.


"Babu inda zani Mami ki barta kawai. Tunda ita ta gina min gadar zaren nan na rufta sai ta kare kalau"


"Ba'a haka Gambo. Kada mu sake bari shaidan yayi galaba a kanmu. Ki duba sau nawa Umma tana kuka akan wannan sabanin. Indai ba so muke muma wata rana mu zubar da hawaye a dalilin faruwar irin haka ga namu 'ya'yan ba to mu bar komai ya wuce"


A can dakin Daddy kuma waya suke da Zayyan ya fada masa yadda su ka yi da Mairama.


"Ka bani shawara me ya kamata na yiwa matar nan. Idan banyi mata abinda za ta ji sosai ba komawa wurin boka ko wani tsibbu ba wahala zaiyi mata ba"


"Na rasa yadda akayi zumunci ya lalace haka wallahi. A fito tsatso daya ko ma ciki daya amma ka ga mun rufe ido muna neman ganin bayan juna. Hassada tayi mana mummunan kamu ita ce tushen komai" cewar Daddy cike da takaici.


"Akwai wanda zaiyi sama da abinda Maikudi yayi min kuwa? Banda kwashe komai ya kara da toshe hanyoyin da taimako zai iya samun Mairama...wani abin sai dai muyi kawai domin Allah ba don halin mutum ba"


Daddy tunawa yayi da yadda Maikudi ya jigata a hannuwansu saboda ba karamin bakinciki suka ji ba da abubuwan da ya yiwa iyalin Zayyan sannan ya auna da makantar shekara goma "daga shi har ita yayar Mairaman babu gwara. Makanta ko ta wuni daya ce fa ba abin mantawa bane"


Shawara Daddy ya bashi daidai da yadda yake ganin ko shine abinda zaiyi kenan. Yana dariya ya kara da cewa "ba don mun fara tara jikoki ba da mun kwashi 'yan kallo a garin Sumaila gobe."


Zayyan ma dariya yayi yana jin Daddy na cewa Awwab ya zauna ya jira shi ya gama waya.


"Ka fada masa abinda ya faru don nasan Alheran ba fada masa zata yi ba kuma hakkinsa ne ya sani."


"To sarkin taya bera bari"


"Zancen gaskiya fa kaga matarsa ce, don dai kawai mun biyewa mata ance sai anyi biki da tana gidansa babu mai shiga cikin case dinnan cikinmu duk wanda ya tabata da shi zasu gamu. Kace ya sameni a Kano kafin shabiyu goben kawai"


"So kake ku hana matar mutane kwanciyar hankali ne kake ta tara mata gayya?"


"Tsuntsun da yaja ruwa..." Zayyan yace yana shafa sajensa.


Suna gama wayar kuwa Daddy ya fadawa Awwab saboda duk a zatonsu duka sosai Salame ta yiwa Radhiya tunda da ta kira Daada kuka take yi fiye da yadda dukan yake mata zafi. Ita kuwa tayi ne kawai don yazo ya a kawo karshen mulkin Gwaggo Salame.  Ai kuwa Awwab ya shiga tashin hankali sosai bai iya bacci ba har garin Allah Ya waye yana tunanin wane irin duka ne aka yi mata. Ganin ba iya bacci zaiyi ba kawai karfe shida da rabi ya shirya cikin kananun kaya wandonsa chinos ruwan toka da polo shirt fara. Agogo yake daurawa lokacin da maganar Emzee ta fado masa da yace Rahima ba kanwarsa bace, ba mamaki dalilin faruwar wannan abu ne. Sai yaji ya kara tsorata da zumuncin yanzu. Kafin takwas yana hanya don shi bai dauki tuki a bakin komai ba.


Shima Zayyan jirgin bakwai da rabi ya biyo yana ta jujjuya maganganunsu da Hadir da Major na daren jiya. Kafin ya sauka Captain Onomza ya turo mota aka dauke shi zuwa Janguza barrak. Tara da rabi Emzee ya iso su ka jira Awwab shi ma goma da 'yan kai yana barrack din don ma bai san hanya ba da kwatance ya karasa.


Sun gama shirinsu motoci biyu cike da sojoji ta ukun Major General Zayyan Tureta ne da dreba da kuma escort dinsa da suke yawo tare sai kuma motar bayansu Emzee da Awwab.


Kafin su bar barrack din ya kira Mairama inda ya bata umarnin ta tabbatar gidan nan babu yara kafin ya iso.


"Ina nufin ko su Alheran bana son na tarar sannan kananun yaran gidan duka kowa ya fita."


"An gama ranka ya dade" tace tana kirkirar murmushi.


Kebewa tayi da su Yadikko ta fada musu su ka sanar da Malamijo. Nan yace su tattara duka yaran su tafi ainihin gidan iyayensa wanda yanzu sai 'yan uwa baya son kowa ya dawo saboda zasu yi taro na manya. Babu wanda ya kawo tangarda sai Halifa shima kuma hankalinsa ne a tashe saboda Salame da ba'a gani ba tun jiya Alh Indararo yana ta babatu. 


Ummi ta kira shi gefe ta kwantar masa da hankali sannan tace yaje gidan Ta Madina ya daukota. Gani tayi yana son yi mata tambaya ta dafa shi.


"Kada ka damu Malamijo ya gano inda ta kwana tun jiya kuma yana son shi da Ta Madina suyi mata magana ne."


Sai lokacin hankalinsa ya kwanta ya tafi. Bai dade ba ya kawo Ta Madina shima ya tafi inda su Radhiya suke. Yau dai bayanta yayi tsami a dan rankwafe take tafiya ita kuma Rahima sai dankwali tasa ta daure idonta saboda ko yaya ta motsa tana jin kamar kwayar idon fitowa zata yi. Ragowar shatin wayar kuwa yana nan kwance a fuskarta ba kyaun gani sai hijabi ta janyo ta rufe fuskarta sosai. Da Halifa ya shiga dakin da suke ya ganta kuka ta saka masa Radhiya sai ta fice kawai ta basu wuri. Itama kukan take yi tana tausaya musu. Babu dan da zai zo jin ana zagin iyayensa bare kuma a kai ga kowa yana jin haushinsu saboda wani abu da suke yi ba daidai ba.


**********


Tunda tazo gidan Mal. Kallamu abokin Malamijo Salame banda aikin kuka babu abinda take yi. Ta rasa me yake yi mata dadi kowa ganin laifinta yake yi. Duk abinda tayi ba karya aka yi mata ba amma babu mai fahimtarta. Duk wata rayuwa da take so da buri Mairama ta haye kai ita take yi. Rahima kuma ba komai ke dawainiya da ita akan yarinyar ba sai neman inda za ta sauke damuwarta. Ta rasa farinciki komai ba ya yi mata dadi gashi iyaye da 'yan uwa sun juya mata baya. Fuskar Mairama ta tuna lokacin da ta ke yi mata alkawarin bazasu sake haduwa ba taji wani iri a ranta. Wai shin mene ne takamaiman abinda ya rabata da Mairama idan ka cire auren Zayyan wanda ita Mairaman bata da masaniyar tana son shi. Kan nata ya toshe ta kasa tunanin kirki kawai sai ji tayi ana bubbuga kofofin gidan da karfi maza suna hayaniya ana kiran sunanta.


"Come out" taji wani ya doka kofa da karfi yana fada.


Ciwon ciki ne haka siddan taji ya kamata da tsananin bukatar zagawa bayan gida saboda tsabar firgici da tsoro. Kofa kofa sojojin suke budewa suna hargaginsu idan sun so tsorata mutane. Mal. Kallamu da matarsa duk da Malamijo ya kira ya fada musu yanzu sojoji zasu zo fitar da Salame amma bai hana shi shiga tashin hankali ba. Murdaddun maza ne majiya karfi babu tsoro babu rissina suke ta kiran Salame cikin wata irin murya. Dakin ta kalla babu wurin buya gashi muryoyinsu da bugun kofar yana ta matsowa kurkusa.


Jiki na kyarma ta tashi ta mikar da katifar dakin ta jinginata da bango sannan ta shige bayan ta buya a zuci tana cewa "sai nayi magana ace bani da hankali amma ta ina talauci yayi saboda Allah tashin hankali yazo wa mutum gida babu wurin buya. 'Yar kwabar nan ko gado da za'a iya shiga karkashi a labe duk babu"


Gidaje biyu ne tsakanin Malamijo da aminin nasa kuma har can gidan ana jin abinda sojojin suke yi shiyasa mutane kowa ya shige gida baka jin wani motsin kirki tamkar babu mutane. Dattijuwar matar Mal. Kallamu da tsoro ya isheta bata ci nanin ba nanin za ta ci ta tayi saurin nuna musu kofar dakin da Salame ta kwana. Gyada kai babban cikinsu yayi su ka yi shiru gabadayansu na dan lokaci har sai da ta soma sauke ajiyar zuciya a zatonta sun tafi.


"Allah Ya soni....amma bari na fito sai na nunawa Mairama har yanzu gaba nake da ita. Nice zasu turowa sojoji saboda........."


Haske ta gani wal daidai da faduwar katifar a kasa. Saura kiris ta saki fitsari ganin sojoji da kafta kaftan takalma kai kace filin daga zasu je suna nuna mata hanyar kofa wani ya daka mata tsawa.


"Get going my friend"


Jiki na tsuma numfashinta sai ka rantse fita zaiyi saboda tsananin kidima ta fito ko takalmi babu sai mayafi tayi gaba suna biye da ita. Motocin da ta gani ne suka sa ta hadiyar wani yawu mai mugun daci sannan aka nuna mata kofar gidansu ta shiga a darare.


Zayyan yana mota ya hango shigarta ya kada kai. Mace da kimarta da komai ta zabi wulakanta kanta kamar wata mara daraja. Babu abinda yake tunzura zuciyarsa kamar makantar masa da mata na shekara goma. Fitowa yayi daga motar sanye da kayansa na sojoji yayi matukar kyau sai dai fuskar nan babu alamun wasa ko kankani kai baka ce Zayyan bane. A hade take tamkar hadari mai shirin zubar da ruwa. Cikin wani irin taku da dogayen kafafunsa yake tafiya da sassarfa yaransa suna kamewa suna sara masa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya da ya shiga soron gidan yana fatan bukata ta biya domin idan Salame ta sake gangancin taba masa iyali bayan zamansu na yau to ko Mairama bazata sami labarinta ba sai yasa an gama koya mata hankali. Wasu mutanen basa gane yaren laluma da bi a hankali. Magana tafi shigarsu da tasiri idan su ka ji an taba lafiyar jikinsu.


Katuwar tsakar gidan gabadaya iyayensu ne. Malamijo, Yadikko da Hajjo sauran amaren nasa yace kowacce ta zauna a daki. Gefe ga Innawuro da Nene Marka sai Ta Madina. Mairama da Mama Zainab suna daki. Can daya barin kuma Alh Indararo ne da Baffan Rahima. 


Kusan tafiyar yaji Zayyan yayi da Salame tana labe a bayan kofa ta kasa karasa shiga tsakar gidan. Takun da taji daga bayanta da hadadden kamshi mai tafiya da hankalin duk wanda ya shaka su ne suka sa ta farga ta juya baya. Ai tana hada idanu dashi kallon da yayi mata sai ji tayi fitsarin da take makalewa yana diga. Zayyan kuma ya dauke kai kamar bai ganta ba ya taho fuuu shine ta shiga kamar wadda aka koro.


Babu wanda cikinsa bai yamutsa ba da Zayyan ya shigo duk da cewar da yawansu sun sanshi amma babu wanda yayi masa wannan sanin ta fuskar sojoji. Escort dinsa na bayansa sauran suna waje ya nufi gaban Malamijo. Mal Ali Gidado sai ji yayi hantar cikinsa na kadawa kamar ba surikinsa bane. Yanzu yaron nan idan allurar sojansa ta tashi ya manta da matsayinsa a gareshi yace zai hada dashi a kulle ai ya shiga uku. Wani tunani ne ya darsu a zuciyarsa ya kara tsorata wato tunanin ko Mairama ta fada masa yadda baya ciyar da ita da yaranta sosai lokacin da ta dawo gidan. Dan sakin fuska yayi ya gaishe shi sannan yace ina Innar Salame.


Ta Madina jiki na rawa taja jiki ta fara yin hanyar kofa za ta gudu Hajjo tace "ga ta can a bayanka...Ta Madina ana magana"


Idanunta su ka soma kadawa ta dafe kirji "banda abinki Hajjo idan da kara ai Yadikko zaki nuna matsayin Innarta. Ni dai haihuwar Salame kawai nayi amma komai nata da tarbiyarta a hannun Yadikko suke. Yau ko wani abu tayi ba daidai ba tarbiyar Yadikko ce da Malamijo"


Yadikko ta zaro idanu ganin kowa ita yake kallo "daga abin arziki kuma sai kice nice na haifeta. Irin wannan tunda ya nemi ainihin mahaifiyar nasan cewa akwai dalili."


Shi dai Malamijo gumi ne ya cika masa tafin hannu ya kalli Salame ta firirice gabadayanta a ta manne da bango.


Zayyan ya sake daure fuska yana kallonta sannan yace "Malamijo ina son ganinka da mahaifiyarta muyi magana"


Kan kace kwabo su Hajjo da sauran kowa ya bace sun shige dakunansu. Alh Indararo ma da Baffan Rahima cewa suka yi zasu jira a soro su ka tafi. Ta Madina ba don taso ba aka bude musu wani dan daki suka shiga ita da Malamijo. Zayyan zai bi bayansu ya kalli Salame ya daka mata wata razananniyar tsawa da ta kadawa hatta Mairama da ke daki ciki "zaki zo ki shige ko sai...."


Bai rufe baki ba ta shige dakin itama ta sami jikin bango ta kuma rabewa sannan Zayyan ya shigo ya zauna. 


"Salame" taji ya ambaci sunanta da wata irin kakkaurar murya. Jinin jikinta ya sake tsinkewa bakinta kamar ansa kwado ta kasa budewa ta amsa.


Ta Madina kuwa ta kai mata duka "ke dallah bude baki ki amsa kina ji ana kiranki"


"Barta dai so take ta nunawa sojoji iyakarsu" cewar Malamijo a hasale.


Kai ta dago a hankali su ka hada ido da Zayyan sai ji tayi har abada bata fatan sake kallon wadannan idanuwan masu tsorata mutane su kada masa zuciya da hanta. Sunkuyar da kanta tayi tana kallon kasa.


Gyara zamansa yayi ya dan rankwafo kansa "naji labarin duka abubuwan da kika yi tun daga tafiyata zuwa jiya da yamma."


Gumi take yi sosai tsoro iyaka tana ji kuma tayi imanin idan sun nemi tafiya da ita babu mai hanasu. Yadda ake bada labarin rashin imanin sojoji itama yanzu haka zasu je su rinka azabtar da ita? Muryar Zayyan ce ta katse mata tunani.


"A jiya da aka fada min abubuwan da kika yi babu abinda yazo raina sama da son kulleki a dena jin duriyarki har abada...." kallonta yayi na abinda baifi sakan goma ba ya kula hankalinta yana gareshi kamar yadda yake so "...sai dai kinci darajar haihuwa Salame. 'Ya'yanki daidai har bakwai idan na rufeki ko kadan banyi musu adalci ba musamman kananan. Yanzu ina so a gaban mahaifanki ki fada min me Mairama tayi miki wanda ya janyo faruwar wadannan abubuwa"


Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta ya daga murya "ba dake nake ba?"


Zabura tayi ta sake yin baya "uhmm, uhmmm"


"Kin zama bebeya ne ko me?" Ya sake yi mata tsawa.


"Uhmmm babu komai" tace da kyar iyayenta suna kallonta cike da haushi.


"To ni bari na fada miki me ya hadaku. Shekaru ashirin da hudu da suka wuce nazo gidan nan tadi wurin kanwarki kika kawo min wasikar tayin soyayya, anyi haka ko ba'ayi ba?"


"Anyi" tace da sauri.


"A lokacin na amsa miki ko nayi wani abu da zai nuna miki cewa ni Zayyan ina da fuska biyu ta ha'inci in nemi kanwa in nemi yayarta?"


Girgiza kai ta soma yi a hankali tana tuna yadda ya yayyaga wasikar ya watsar.


"Salame nasan cewa soyayya babu ruwanta da dacewa ko akasin haka. Amma ance wai ana barin halal ko don kunya. Kanwarki wadda bata da zance sai naki kuma kema a yadda na fahimta wancan lokacin kina sonta ita ce kike son manemin aurenta. A tunani na ke mai iya hakuri ce ki bar mata ko da ina sonki balle tun farko ita na nema. A matsayinki na musulma tun lokacin ya kamata ki karbi kaddara ki rungumi kyautar da Allah Yayi miki ta Salisu. Ko kinsan cewa Zainab matar Hadir nine na fara nemanta? Ni na nemi kwatancen gidansu duk da ba wata muguwar soyayya naji ta kamani a lokacin haduwarmu ba amma kinsan indai saurayi ya nemi gidansu budurwa ko yaya ya ga abinda yake so ne. Amma abin mamaki ranar da Hadir yaje  gidansu da zummar fada mata ni bazan samu damar cika alkawarin zuwa ba su ka kamu da son juna. Tun daga wannan ranar har rana irin ta yau ban taba sake yiwa Zainab kallon da ya wuce kanwata matar dan uwana ba."


Malamijo da Ta Madina sai jinjina kai suke yi yayin da Salame tayi shiru kawai tana sauraron maganganunsa.


"Ko da kina sona to ba da zuciya daya bane hasali ma nafi danganta abinda kika yi da hassadar kanwarki. Kun rayu kece 'yar gata saboda kina samun kulawar mahaifiya ita kuma babu uwa babu dangin uwa. A kullum Mairama ce a kasanki ki bata saura tayi miki godiya. Lokaci daya kinga abinda kike so shi kuma ya karkata gareta shikenan kika juya waccan soyayya da kike yi mata zuwa kiyayyar da hassada ta zama musabbabinta. Kin manta cewa kowane bawa da irin rayuwar da Allah Ya tsara masa. Wallahi Salame tunda kika ga baki aureni ba ki sani cewa bazaki taba iya rayuwar da Mairama tayi ba. Duka duka ba don rabon haihuwa ba zaman har na wata nawa muka yi a karkashin inuwa guda? Mun rabu da kuruciya batare da mun mori komai a zamantakewarmu ba mun sake haduwa farin gashi na wahala da zuwan shekaru ya zo gareni.  Matata da na bari da kuruciya na dawo ta koma babbar mace. Kinsan yadda muke ji kasancewar shekarun da ya kamata mu zauna mu fuskanci juna sun kare bama tare. Duka duka Salame shekara nawa kuma ya rage mana da zamu sake maimaitawa a doron kasa? Na tafi na bar yarinya ko tafiya bata yi na dawo watanni kadan ga aurenta. Cikin da bansan meye a ciki ba na dawo na sami katon saurayi yana shirin zama soja. Salame zaki iya wannan rayuwar da Mairama tayi cikin kunci, kewa da makanta ga marayu a gabanta???"


Damm taji zuciyarta ta buga sai ga hawaye daga sama yana sintiri akan kumatunta.


Ta Madina ma kuka take yi Malamijo ya sake jin kunyar abinda yayi a baya. Kuncin da ya baro a baya ne ya tuna shi ma Zayyan din yasa yatsansa ya kore hawayen da ya taru a gefen idanunsa.


"Labari yazo Zayyan ya mutu amma kika cigaba da nunawa Mairama kiyayya wadda har ta kaiki ga makanta ta. Abinda nake so ki gane Salame shine ba Mairama kika tsana ba kuma kiyayyarki ba gareta bane. KIYAYYAR SALAME GA SALAME TAKE. Rayuwarki ce gabadaya bata yi miki ba saboda kin ginata tun farko da hassada da bakinciki shiyasa komai baya burgeki sai abinda wani ya samu. Wanin ma wadda kika dauka kishiyarki baki son ta fiki da komai. Da ace kin kasance mai godiya ga Allah da karbar kaddara ina me tabbatar miki sai kin kwance zani kin baiwa Mairama kwance. Dubi irin dimbin arzikin tsohon mijinki yanzu. Ni fa banda kaddara babu wanda yayi tsammanin dawowata harda ni kaina. Dama kece babba a gidan nan amma da kin karbi rayuwarki ta farko da duk gidannan sai sunci arzikinki. Kin sake aure kin dauki karan tsana kin dorawa Rahima saboda ba auren bane a gabanki lokacin. Burinki ace kin yiwa Mairama zarra kuna zawarci ke kin rigata samun mijin aure saboda kin fita da komai. Nasan akwai kaddara da rabon haihuwa a kanki amma duk da haka yadda kike tafiyar da rayuwarki shine ya munanaki a gaban 'yan uwanki."


Mayar da hankalinsa yayi ga Malamijo da Ta Madina "ga iyayenki nan kowa cikinsu fushi yake da ke. Duk wanda kika raba kin zalince shi musamman 'ya'yanki kin bar musu abin fada wanda nake fata zancen ya mutu a gidan nan. Ki gyara rayuwarki wannan shawara nake baki idan kuma kinki ji to na tabbata jikinki yana kaikayi ne na son a taba lafiyarsa mu kuma zamu taba"


Shiru dakin yayi na wanu dan lokaci kafin Malamijo yayi gyaran murya ya soma magana "Zayyanu nasan Salame tayi ba daidai ba amma ina tuhumar kaina da zama silar komai. 'Ya'yana ban basu damar girma da iyayensu mata ba bare su samu ingantacciyar tarbiya. Babu wanda nasan damuwarsa a cikinsu hankalina yana kan dabbobina da yawan aure aure. Gashi an wayi gari ana ta sako min 'ya'yan bayan dogon jinkirin da suke samu kafin manema su fito. Nima ban rike Mairama da 'ya'yanta rikon da ya dace uba ya yiwa 'yarsa da take cikin halin bakincikin mutuwar miji ba ta yaya 'yar uwarta da ta bari shaidan yayi galaba a kanta zata yi. Ka yafe min do Allah do Annabi"


Kunya ce ta kama Zayyan yace masa dama daga shi har Mairama basu rike shi a rai ba.


"Ke kuma mutuniyar banza tashi zakiyi ki roki kowa gafara musamman Mairama da Rahima da kika rinka zalinta" cewar Ta Madina.


A sanyaye Salame ta fara cewa su iyayenta su yafe mata zuciyarta tana ta harbawa ta ma kasa gane wane hali take ciki. Bayan sun ce sun yafe ta koma ga Zayyan shi kuwa kofa ya nuna mata "kije ki sasanta da kanwarki sannan yanzu zan tura su Rahima su dawo ki daidaita tsakaninki dasu. Wannan magana bana so su sani kwatakwata burina kawai ki rungumi 'ya'yanki ki basu tarbiya mai kyau musamman wannan yarinyar da kika zo min gida da ita sai kin tashi tsaye." Yace yana tuna irin rashin kunyar da yaji Khadi tana yiwa Rahima watarana a Abuja.


Mikewa yayi zai fita ya dan dawo sai da gabanta ya doka "yauwa zanyi magana da shi baban Rahima yanzu sai dai ina son yi a gabanki so ki biyoni don ina sauri ne"


"To" tace da azama tana bin bayansa.


Suna zuwa soron su ka same su zaune akan tudun nan kowanne cikinsu ya mike da sauri. Zayyan hannu ya mika musu suka yi musabaha sannan ya kalli Baffan Rahima saboda kamanni da suka nuna shine baban nata.


"Ni sunana Zayyan" yace dashi.


"Idris nake" Baffan Rahima yayi masa murmushi.


"Ni kuma Alhaji Indararo aka fi sanina dashi" cewar maigirma miji na Salame.


"Mal Idris alfarma nake nemarwa kaima da iyalina Mairama"


"Haba Yallabai ni kuwa har wace irin alfarma kake tunanin zan iya yi maka?"


Zayyan ya kalli Salame sannan ya kuma kallonsa "Rahima nake so ka bamu idan babu takura. Dan zaman da mukayi da ita ta shiga ran kowa a gidan musamman ita Umminsu. Don Allah ka bamu ita kafin nan da Allah Ya kawo mata mijin aure ta sami soyayya da gatan da ta rasa na mahaifiya"


Baffan Rahima bai san lokacin da murmushi mai hade da dariya suka kwace masa ba "Yallabai Rahiman tawa ita ce kuke so?"


"Ta cancanci soyayyarmu kuma nayi maka alkawarin zamu riketa kamar 'yar cikinmu"


"To Yallabai za ku rinka kawota in ganta ko?" Yace a raunane harda 'yar kwallarsa.


"Wannan kuma dole ne" Zayyan yace yana dariya.


Mal.Idris ya kamo hannunsa "na baka Rahima amana Yallabai duk da nasan bata baki nake yi ba sai na fada ba. Nagode nagode sosai"


Juyawa Zayyan yayi ya tambayi Salame  "kina da abin fada game da hakan?"


Kada kai tayi a sanyaye. Alh Indararo ya murmusa "sannu da kokari Yallabai nima ina da yaran wallahi biyar ta haifa min duka mata. Bari na garzaya gidan na turo maka su sai ka zaba"


Dariya Zayyan ya danne a ransa kuwa yana tunanin ko ganinsa bazasuyi ba. Su ai 'ya'yan so ne basu da matsala. Ra hima kuwa ya fuskanci abinda Mairama keso kenan amma ta kasa fada masa saboda gudun kada yaki amincewa saboda halin Salame.


"Kina iya tafiya ki turo min matata idan kin shiga" Zayyan yace da Salame.


Ciki ta koma jiki a sanyaye yawancin kowa ya fito sun cigaba da harkokinsu  murya na rawa tace wane daki Mairama take. Da hannu Nene Marka ta nuna mata.


"Dama kiranta yake yi maigidan"


"To ni zanje in fada mata?" Cewar Nene.


"A'a" tace da sauri sannan ta shiga dakin yau harda sallama.


Mama ce ta amsa mata a fili Mairama kuwa a zuci ta amsa ta kawar

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment