Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai shafi zamantakewarmu. Gidajen da muka fito daban, sannan gidan da zamu samarwa kanmu da ‘ya’yan da nake burin ki haifa min shima daban.”

Tamkar kasa ta zage ta hadiyeta taji saboda kunyar kalaminsa na karshe. Da dabara ya samu ya rinka kwantar mata da hankali da kwadaita mata irin tanadin da yake mata idan ta zama mallakinsa. Ba shi ya bar gidan ba sai tara da rabi na dare. Washegari ya sake zuwa kuma a ranar ne ya sanar da Malamijo zuwan kawunnansa idan ya koma.

“Abin da nake so da kai shine ka fada musu su taho da sadakinsu ayi komai a kare. Yaran nan sun zaunu babu dalilin ayi ta jan lokaci. Budurwa kamar Mairama ta bawa shekaru shatakwas baya harda watanni ina kallonta tana kallona. Ga yayarta ita ma zan fadawa yaron nan Salisu sai ayi a lokaci guda”

Dadi maganar ta Malamijo tayi masa yayi na’am da ita. Ana gobe zai koma yana jiran fitowar Mairama sai ga Salame da ta shiga tashin hankali sakamakon gabatowar aurenta da Salisun da bata so. Hanyar waje tayi a daidai inda yake zaune ta jefa masa takarda ta fita. Ba nisa tayi ba tana layin bayan gidansu tana jiran ya karanta wasikar yazo ya sameta.

Layuka kadan ya karanta inda take sanar dashi son da take masa da kuma jiransa da take a bayan layi idan ya amince yazo ya sameta. Mairama ce tayi sallama sai kawai ya yayyaga takardar ya dunkuleta a hannunsa.

Sun jima suna hira yana fada mata haduwarsu ta gaba ta zama tasa tana dariya a hankali Salame ta dawo kamar kububuwa. Ta kwashi awa guda da doriya tana jiransa bai zo ba. Yanzu da ta shigo takardar hannunsa ya watsa a iska ko kallonta baiyi ba. Zuciyarta kamar za ta fashe saboda bakinciki ta wuce ciki.

Bahaushe ma yasan babu wanda ya isa ya sauya kudurar Ubangiji ga bayinSa shiyasa mu kan ce wai tun ran gini….Bayan duka wasu shirye shirye da hassada daga bangaren ‘yan bakinciki irin su Jume da ‘ya’yanta da kuma Salame mai son maso wani, da azahar din wata asabar aka daura auren Zayyan Muhammad Tureta da Mairama Ali Gidado. Sai kuma Salisu Lawan da Ummusalma Ali Gidado. Kowacce cikinsu angonta yayi bajinta gwargwadon aljihunsa ya yi mata kayan lefe. Ko ba’a fada ba kayan Salame sun kere na Mairamu duk da Zayyan din ma baiyi kasa a gwiwa ba, amma a haka Salame ta dauko ido ta sakawa kayan Mairama a ganinta da ita su ka fi dacewa.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: G
*….TUN RAN ZANE*


Hakan take domin kuwa yau ne za’a kai amaren dakunansu. Dakin Yadikko aka tarasu Malamijo ya shigo zaiyi musu nasiha ta karshe safiyar lahadi.
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan ya juya wurin Yadikko.

"Me ake cewa ne idan za'a kai amarya?"

"Ko addu'a ai ka yi musu"

Hularsa ya turo gaba "abi miji sau da kafa shine shawarata gareku. Banda tsiwa ko rashin kunya sannan ayi ta hakuri. Duk wadda ta kaso aurenta babu abinda ya shalleni ah to. Allah bada zaman lafiya ku tashi ku tafi kada ayi dare Mairama tana da nisa. Birnin Shehu kwai dan karen tafiya daga nan kamar za'a ya da shege"

Wannan magana ma sai da ta taba ran Salame. Babu wanda ya damu da cewa ita ke son Zayyan har ake wani zancen nisan garin. Haka su ka fito suna ta kuka, kowacce da abinda take yiwa. Salame kukan rabuwa da masoyi take yi don tasan an riga an cuceta an rabata da Zayyan. Mairama kuwa kukanta bai wuce na rabuwa da 'yar uwarta da gidan nasu duk da ba dadinsa suke ji ba, sai kuma fargabar sabuwar rayuwar da zata fara.

Akori kura biyu ke biye da motocin daukar amaren na kayan dakinsu da aka samu Malamijo yayi. Gadaje daidai ne da saitin kujeru da kuma kayan kitchen. Gidan Salame aka fara tsayawa a Kofar na'isa babban gida ne mai bangare uku na Salisu da 'yan uwansa. Yadikko da Hajjo su ne zasu tsaya a nan ayi jere tare da 'yan uwan Ta Madina. Basuyi mamaki ba ganin har sunyi jeren katon gado a daki daya da kwaba da madubi masu kyau daidai da zamani wanda Ta Madina da 'yan uwanta suka yi. A falon ma sunyi mata kujeru manya da suka fi na wajen Malamijo an malale kasan da leda mai ado da ta dace da labulen da suka yi mata. Kayan da suka zo dasu wani daki guda aka nuna musu suka jera kujerun da gadon ya dauke su tsaf saboda ba wani yawa garesu ba.

Kannen Ta Madina suna aiki suna yabawa su Yadikko magana wai kudin Malamijo bai tsinana musu komai ba. To su din ma basu tanka ba tunda idan anbi ta barawo abi ta mabi sawu.

Dije da Inno su ne jagora a tafiya kai Mairama nata gidan. Yamma likis suka isa Allah Yasa ba wata gayya ce ba basu fi su biyar ba. Sanin cewa idan ya kaisu gidansu Jume sai ta saka shi jin kunya ya nemi alfarmar kanin babansa zai saukesu a gidan kafin su yi jeren. Nan su ka kwana ana ta tarairayarsu. Mami matar Captain Mustapha ita ma tayi abinci mai yawa suka je aka yi taro a gidan. Jume ko zuwa bata yi ba amma 'ya'yanta mata sun je suna ta yada magana wai kalen dangi ya guji nasa asalin. Haka nan 'yan uwan Mal.Muhammadu sun je da yawansu.

Da safe Hadir ne yaje daukosu aka kaisu gidan da aka bawa Zayyan a bangaren gidajen da suke cikin barikin. Daki daya ne kato da bandaki a cikinsa sai falo madaidaici da kitchen karami. Bata zo da komai ba sai iya kayan da Malamijo yayi mata. Anyi jere lafiya a daren aka kawo amarya dakinta su kuma suka koma Sumaila washegari.

Zaman Zayyan da Mairama abin burgewa ne da sha'awa ga duk wanda ya sansu kuma yake mu'amala dasu. Babu abinda ya rageta dashi ta fannin soyayya da kyautatawa. Ita ma a nata bangaren tana binsa sau da kafa da biyayya da tattali. Yanayin gidansu yasa ta iya girki bashi da matsala ta wannan fannin ma.

Satinsu biyar da aure Zainab ta tare matar Hadir. Mami dadi ya isheta ga hausawa 'yan uwanta a kusa duk da nasu gidajen suna bangare daban. Sunfi girma da kyau. Su Mairama kuwa layinsu daya da Zainab. Hade kai suka yi suna zaman gaskiya da bawa juna shawarwari. Mami ce babba amma Zainab duk ta fisu wayewa. Mairama kuwa dama albarkacin boko ta san wasu abubuwan amma kifin rijiya ce. Idan suna hira abin dariya, Mairama kana jin hausarta zaka gane bafillatana ce, Zainab sakkwatanci ziryan ita kuma Mami Hausar Katsina.

Yau juma'a Mairama tana cikin girki kafin dawowar Zayyan taji sallamar Awwab. Kowa yasan dan gidanta ne na gaban goshi. Zainab har ta gaji da mita ta kama kannensa Zahra da Fauziyya a matsayin nata.

Kitchen din ya shigo ya sameta tana yanka salad.

"Anti kawo in yanka"

"So ka ke Anti Zainab ta shigo ta soma tsokanarka ko" tace tana murmushi.

"Mami tace in gaisheki kuma zata zo kiyi mata kalba anjima"

"Kaje kace mata nace sai ta shigo sannan ka dawo ka ci abinci"

Fita yayi zai tafi ya ga ta biyo bayansa a guje ta shige bandaki tana kakarin amai. Awwab ya rasa me zaiyi sai kuka yana mata sannu. Ita ke fama da matsananciyar tashin zuciya da amai kamar zata fitar da kayan cikinta amma kuma ita ke bashi hakuri saboda yadda ya gigice mata.

"Awwab ka dena kuka mana" tace cikin rashin kuzari.

Kuka yake sosai "to ki dena aman"

"Na gama muje ka zuba abincin idan kaci sai ka tafi"

Kallonta yayi tana dafa bango tana daga kafa da kyar. Hannunta ya rike har kan kujera yace "In fadawa Mami ko Anti Zainab?"

Da sauri ta dakatar dashi "a'a kada ka fadawa kowa na ji sauki"

"To kiyi dariya in gani"

Dariya ya bata ya kafeta da ido wai tayi dariya. Motsin mutane suka fara ji daga waje ya tashi da sauri ya bude kofar. Zayyan ne da wani security soja sun kinkimo katon kwali ga wasu kwalayen biyu kuma a kasa daga gefe. Yana ganin Awwab yace ya je ya fadawa Mairama ta koma daki zasu shigo da kaya. Ta ji me yace kafin Awwab din ya dawo ta koma ciki ta kwanta.

Suna shigo da kayan ya fadawa Zayyan tana amai. Nan fa hankalinsa ya tashi ya bishi dakin bayan sun gama shigo da kayan.

A kwance take tana jin ya shigo ta tashi zaune.

"Mairam me ya same ki?"

Sai da ta harari Awwab ta bashi amsa "ulcer ta ce ta tashi tun dazu da na sha coke kirjina ke suya"

"Shine baki taba fada min kina da ulcer ba suk sati nake ajiye miki crate din minerals? To anyi an gama"

Bata da wata ulcer a iya saninta amma ta ki jinin asibiti. Kitchen din yaje ya zubo abinci.

"Nasan baki ci ba, tashi"

Wani aman taji ya taho mata daga ganin abincin ta daure "Awwab baici ba ka bashi zan ci anjima"

"Nima bazan ci ba sai kinci" Awwab din yace yana marairaicewa.

Zayyan ya janyo hannunsa ya zauna a kusa dashi da kyar ya samu ya karba yana ci yana mata hira.

"Kayi min kwacen mata kirikiri yaron nan"

Mairam ta soma dariya da Awwab ya dage sai ya fada masa me yake nufi. Sai can yamma ya tafi ya fadawa Maminsa bata da lafiya. Taso zuwa amma tunda Zayyan yana gida sai ta hakura sai gobe.
Sai dare Zayyan ya bude kwalayen da suka zo dasu. Daya firinji ne madaidaici mai kofa daya amma da freezer daga sama. Sai kuma TV da bidiyo duka sababbi. Mairama godiya harda kuka don murna.

Bayan kwana biyu kullum tana fama da amai da jiri ya kaita asibiti aka basu tabbacin ciki ne da ita. Tamkar ya hadiyeta don farinciki. Gani yake yanzu zai sami abinda zai kira nasa, jininsa sosai.

**********

Lokaci yana tafiya al'amura suna faruwa garesu. Captain Mustapha ya sami karin girma zuwa mukamin Major bayan ya dawo daga wani aiki da aka tura shi Warri. Zayyan da Hadir kuma sun zama Lieutenants.
Cikin Mairama yana da wata shida amma idan ka ganta sai ka rantse bazata kara kwana ba zata haihu. Su Mami sun gama sadakarwa ‘yan biyu ne a cikin. Bata wani laulayi sosai sai cin abinci akai akai tayi bulbul ta sake kyau da cikowa. Kwakkwaran motsi idan tayi Zayyan ya rinka cewa yaya akayi. Zainab ma cikin gareta wata uku amma ita laulayi yake saka ta don bata iya komai yanzu sai kwanciya duk ta rame abin tausayi. Mazajensu na fita suke tarewa a gidanta su taimaka mata da aikin gida. Mami tayi ta kokarin hana Mairama amma bata ji, tafi ganewa motsa jikin dama kuma haka ake so ga mai juna biyu.

Yau litinin suna tare a gidan Zainab su Awwab suka dawo daga makaranta. Tun da suka ga gidan a rufe sun san inda Maminsu ta tafi sai suka bita. A falo suke zaune suna hira yau Zainab din jikinta da kwari ba kamar kwanaki ba.

Kowa yana cin abinci an hadawa yaran a tray karami na silver iyayensu su ma sun hada tare. Zainab ce ta kula da Awwab gabadaya idanunsa suna kan Mairama. Idan ta yamutsa fuska sai yayi kamar zaiyi kuka.
“Awwabu ya aka yi ne kake ta kallon mamanka?”

“Anti baki ga cikinta ba kullum yana kato kamar na maman Ebere”

Mami ta tuntsire da dariya “kai kuma baka son cikinta yayi irin na maman Ebere din ne?”

Ya gyada kai “saboda fashewa zaiyi watarana, haka Ebere tace na mamansu ya fashe a asibiti.”

Zahra ta kai masa bugu a kafada “Kai Hamma haihuwa zatayi fa mu sami baby” Hamma shine sunan da Mairama tace su rinka kiransa dashi don da fari Awwab kawai suke cewa.

Maminsu ya kalla a tsorace “kinji tana rashin kunya Mami, ni dai ba ruwana”

Tsokanarsa Zainab ta shiga yi tana cewa Mairama danta yakware a wautar ‘yan fari. Da abun ya ishe shi sai ga hawaye Zahra da Fauziyya aka sami na yi. Mairama ta janyo shi kusa da ita.

“Kyalesu baby zan dauko maka a asibiti idan nawa cikin ya fashe kai kadai zaka rinka dauka.”

Wata dariya ya saki da ta kara masa kyau da nuna kuruciyarsa yana murna, har da yiwa su Fauziyya gwalo. A haka rayuwarsu take tafiya komai nasu cikin aminci tamkar ‘yan uwa na jini.

Ranar da nakuda ta kama Mairama Zayyan sun tafi gidan gwamnati shugaban kasa zai kawo ziyara. Nauyi da kunya ya sanya ta kasa fada masa tun gabanin asuba da ta fara ciwon har ya fita. Gashi abu yafi karfinta zamani ba na waya ba bare ta nemi taimako. Allah ne ya kawo mata Awwab tana cikin wannan matsanancin halin ta daure tace yaje gida ya kira Mami kuma ya tabbata ta taho yanzun nan. Ya kusa shekara tara a lokacin shiyasa duk da bata fada ba jikinsa ya bashi ba lafiya ba.

A guje ya koma gida sai gasu cikin mintuna kalilan. Tana ganinta tace ya fita ta shiga daki ta taimaka mata su fito kawai ta fara nishi. Mami ta san babu yadda zatayi tun da ta hango kai yana neman fitowa a take Allah Ya sako mata karfin zuciya ta karbi haihuwar santaleliyar yarinyar da Mairama ta haifa.

Tubarakallah yarinyar akwai girma da kiba taci ta koshi tun a ciki ga kyau. Kukan da ta chanyara ne ya sanar da gidan da yake jikin nasu an sauka. Matar gidan bayerabiya ce suna kiranta Maman Dolapo ta shigo da sallamarta domin su ma musulmai ne. Awwab aka tura ya kira Zainab itama tazo suna ta murna aka dora musu ruwan wanka. Yarinya tana ta wutsil wutsil kakkarfa da ita.

Mami girman yana gareta ita ta yiwa Mairama wanka. Jaririya kuwa Maman Dolapo ta roki alfarmar a barta tayi mata irin nasu na yarbawa. Babu wanda ya hana saboda zaman mutumci suke yi da ita. Sun kuwa ga wanka ba irin wanda suka saba ba. Ta wanke yarinyar nan sosai ga mamakinsu harda manja mai kyau ta dauko daga gidanta ta shefe jikin yarinyar ta mitstsiketa sosai sannan aka fara wankan da kyau ana fitar da datti da maikon manjan. Ko da ta gama yarinya kana tabata jikin nan subul ta kara wani haske kamar jini ya fito. Lallausan kayan sanyi aka sanya mata lokaci na damuna sannan akace Mairama ta bata nono. Nan fa ake yinta kunyar jama’a ko karbarta ta kasa. Zainab ta kamata ta maidata daki. Zata rufe mata kofa Awwab yayi kekam dole ta barshi ya bi bayan mamansa ana musu dariya.

Babu abinda makota basu yiwa Mairama ba. Daki ta shiga tayi kukan rashin dangin uwa da basu damu da ita ba. Da kanta ta nemi Zayyan akan bata son zuwa gida wanka saboda ta sani ba wata kulawa da zata samu. Bayan auren nasu sunje sau daya bata ji dadin gidan ba ko kadan. Wani kallo na kyashi ake watsa mata, Yadikko ce kadai mai janta a jiki. Malamijo kuwa zubar da girma yayi gaban Zayyan yana fada masa yadda yake cikin mawuyacin halin kula da iyali. Allah Yasa sunyo musu tsaraba irin ta Sakkwato amma duk da haka sai da ya bashi kudi. Kurewar lokaci yasa basu tsaya a gidan Salame ba. Abin da bata sani ba da gangan Zayyan yayi haka don ko kadan baya kaunar yadda Salamen take yiwa matarsa ita kuma bata gani.
Ba su suka dawo gida ba sai daya saura na dare. Lokacin kowa ya watse hatta Mami ta tafi saboda yara sun fara bacci. Mairama da jaririyarta ma baccin suke jiki ya gaji ga wankan da suka sha. Ko ina a gyare tsaf gidan ya bude kofar dakin a hankali don kada ya tasheta ko fitila bai kunna ba. Kayansa ya cire yaje yayi wanka ya fito yana komai a nutse don baya son damunta. Duhun dakin yasa garin neman robar mai ya tunkudu wani abu daga kan madubin ya fado da karfi. Karar ce ta tashi baby din yaji ana inya inyaa.

Hanyar kofa ya nufa da fari ya ajiye sojancin na wucin gadi, sai yaji muryar Mairama tana cewa shhhh. Da mugun sauri ya kunna fitila idanunsa a kan gadon. Kyakkyawan gamo yayi. Masoyiyarsa abar kaunarsa ya gani tare da baby kunshe cikin shawul fari tas.

Zuciyarsa ce tayi wani irin nauyi ya tako gaban gadon a hankali ya zauna a gefenta. Murmushi ta sakar masa kafin ta dora masa jaririyar a kan hannuwan da ya miko mata. Rungumesu yayi tare yana fidda numfashi da sauri. Mairama sai ta soma hawayen farinciki ta kara shiga jikinsa yana yiwa baby addu’a. Sun dauki lokaci a haka kafin ya bude fuskarta tana tandar baki.

“Yunwa take ji ko?” ya kalli Mairama

Karbarta tayi ta juya masa baya zata shayar da ita ya hawo gadon ya zagaya gabanta “kada ki cuceni da kunya”

Ba yadda ta iya yana ta kallonsu cike da sha’awa kamar wani zai ce ba nasa bane. Bai iya tashi ba har ta gama ya ga babyn tayi bacci ita ma idanu sun fara rufewa.

Kwanciya ya gyara musu ya dauko darduma ya shimfida yana nafilar godiyarsa ga Allah. Duk gajiyar da ya kwaso ranar babu wani bacci da ya iya yi sai gadinsu har asuba tayi. A masallaci Major Mustapha da Hadir su ka yi masa barka tare da sauran abokan aikinsu ana taya shi murna. Papa Dolapo ya tsokane shi wai Allah Yasa dai ba mai kiriniya bane kamarsa akayi dariya.

Aikinsu bai kare ba zasu koma gidan gwamna. Kafin su tafi Major Mustapha da Hadir su ka je gidan ganin baby da kuma yi mata addu’a. Zayyan ya dan taba Hadir yana yi masa magana da ido. Ya san zancen shiyasa ya dubi Major din.

“Sir kaine zaka rada mata suna fa, kayi mata huduba”

Wani iri yaji yadda yaran nan suke matukar girmama shi tamkar yayansu na jini “wane sunan zan saka mata?”

Shiru Zayyan yayi sai ya koma ciki da sauri wurin Mairama a daki.

“Mairam bamu tsayar da shawarar suna ba ga Major can yana jira”

“Sunanta Alheran” tace tana gyara daurin zaninta.

“Nace sunan Innarmu ta Sumaila zamu fara sakawa”

“Don Allah Sojana sunanta Alheran, idan na sake haihuwa sai a saka sunan Innar”

Muhawara suke yi sosai ya gaji ya karbi nata “baki da wani suna da kike son a saka mata? Suna biyu nake son a saka”

Sarai ta fahimce shi, a dole yana son bata dama ita ma ta sanyawa yarinyar suna. Sai dai duk yadda take son saka sunan innarta tana ganin shi yafi dacewa da ya fara sakawa. Bata yi dogon tunani ba tace “Radhiya”.

Murmushi kawai yayi ya fita ya sanar da Major sunan ‘yarsa Alheran Radhiya Zayyan Muhammad Tureta. Hadir yace “mutumina wannan sunaye haka”

“ ‘Yar soja ce, ya kamata a komai ta fita daban” ya bashi amsa yana magana a hankali kada a ji.

Major Mustapha ya gama yi mata huduba sannan yace ya maidata ciki suyi shirin tafiya bakwai ta kusa.

Kwanaki hudu da haihuwa duk wanda ya kamata ya sami labarin haihuwa daga danginsu ya sani. Tasha Zayyan yaje ya bada sakon wasika zuwa ga Kawunsa Ghoumar domin a sanar da sauran dangi abinda aka samu. Sai wasikar ta isa akan gaba suna shirin zuwa saboda aurensa da yazo da gaggawa basu sami damar halarta ba.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: H
**********

“Kasan Allah Malamijo idan naje Sakkwato haka zikau Allah shi tsinan”

Fuskarsa a murtuke kamar zai kai mata duka ya tashi daga kwanciyar da yayi “ wai ni dake waye ya haifi yarinyar nan ne eyyee?”

Yadikko ta galla masa harara “kaine ubanta wanda na sani da ana sakewa wallahi bana jin ko tsinken ashanar gidan nan zai so a alakanta shi da kai. Me kake yiwa yaran bayan haihuwarsu? Nan haka muka kaita gidan miji abin kunya babu wani kayan arziki wai kuma ‘yarka ce, kai da garin nan kowa ya shaida arziki gareka”

“Sa ido, sa ido…kowa zaiyi ya bari tunda ba da uban mutum muke kiwon ba”

“Ba sai ka zageni ba, gaskiya ce dai dole na fada maka. Mairama baka fitar da ita kunya da biki ba dole kayi bajinta ita ta fara kawo maka jika a gidan nan. Ka kuma hada da gara tunda ba’ayi musu komai ba da bikin. Salame ba don mahaifiyarta tana kusa ba itama da haka za ta tare ba garar”

Malamijo ya mike yana kada hannuwa yana kumfar baka saboda an bukaci kudi “garo ba gara ba, idan sai na bada kudi kunyi mata gara zaku je don Allah kuyi zamanku na yafe. Yo dangin uwarta ma suka bace bat a doron kasa basa waiwayarta tunda ta rasu balle ku”

“Laifin waye to idan bana ka ba? Kowace mace ka gani kana so saboda zalama. Kuma ba dole su bace ba. Kayi auren biyan bashi tana haihuwa kace ka saketa kuma sai sun biya rabin kudin. Tsoro yasa sun gudu bakinciki kuma ya kashe yarinya karama ta bar marainiya”

Yadikko kin hakura tayi sai da kyar da sudin goshi Malamijo ya bata dubu uku da kuma tinkiya guda daya “gashi nan a tafi a kaiwa ‘yar kunama kafin na fara ganinki cikin bacci na. Ke dai da mayya ce da tuni na dade a tukunya”

Warce kudin tayi a hannunsa “fadi ka kara, aradu da ina maita da tuni an dade da raba gadon ka”

Hanjin cikin Malamijo ne ya kada da gaske furucinta ya bashi tsoro. Ko dai mayyar ce ne? shiyasa kullum baya gaba sai dai baya kamar kudin guzuri.

**********

Kwance take akan doguwar kujera a falonta lokaci lokaci ta dago kai ta tsartar da miyau a duk inda ta ga dama tana faman yatsina fuska. Salisu ne ya shigo da langa cike da gurasa da tsire irin wanda take so.

“Salame tashi kici abincin”
Kallonsa tayi ta watsar tana kokarin zubar da wani yawun ya taho da sauri ya mika mata kurtun da ya ciko da kasa “zuba a nan kinji don Allah Salame na” yace da rarrashi.

Kamar bazata zuba ba sai kuma ta tofa ya mayar ya ajiye jiki na rawa ya miko mata langar ta amshe ta soma ci don yunwa take ji dama. Ta dauko yanka na biyu ya saki fuska yana dariya “yau da albishir na dawo, me zaki bani tukwici?”

“Rike kayanka indai sai na bada wani abu zaka fada”

Baiyi fushi ba don ya saba da halinta. Bata boye masa kiyayya har yanzu da take dauke da ciki na wata biyu. Tsiyarta take tsulawa a gidan tana cin karenta babu babbaka kawai don tasan Salisu yana masifar son ta.

“Mairama ta sauka yau kwana hudu an sami mace”

Naman da take shirin hadiya ne ya makale mata a makoshi ta soma tari. Ruwa ya bata ko kalla bata yi ba bare ta karba.

“Me kace?”

“Mairama….”

“Dakata malam, wannan har wani labarin fada ne?”

Mamaki ya kama shi “ke, Mairama kanwarki nake nufi”

Zuciyarta ce take tafasa da bakin kishi. Yanzu Mairama har ciki Zayyan yayi mata ta haihu. Saboda shi tafi wata uku Salisu bai sami kanta ba sai da ya hada da fin karfi. Rigima sosai suka kwasa kamar auren bariki tana ta yi masa Allah Ya isa. Ganin babu sarki sai Allah daga baya ta hakura ba don tana son sa din ba sai don kawai ba ta hango mafita daga kaddararren aurensa ba. Da ciki ya bullo kamar ta zare don bata kaunar komai tsakaninsu lokacin da za ta kasha auren ta nemi hanyar shiga gidan Zayyan. Indai soyayya na saka hauka, kan Salame ya dade da kwancewa akan mijin kanwarta. Kuka ne ya kwace mata mai cin rai da zuciya. Mairama ta rigata samun abinda take muradi. Salisu ya tsaya kallon ikon Allah yadda take kuka haikan.

“Yanzu meye abin kuka bayan kema kina da cikin nan” a tunaninsa ko don ta riga ta haihuwa ne.

“Allah Ya sauwake nayi kuka don ta rigani haihuwa” tace cike da tsiwa.

Tsareta yayi da idanu “to kukan me kike yi?”

Gabanta ne ya fadi ta soma inda-inda “banda abin Mairama da kwarewa a rashin kunya daga auren sai ta bashi kanta. Wannan ai zubar da mutumci ne. A lissafina sai nan da kwana hudu ma zamu cika wata tara da aure amma gashi ita ta haihu. Anya ma kuwa cikin nan….”

“Ke Salame! Shiga taitayinki. Kanwar ta ki kike neman jifa da kazafi saboda wani shirmenku na banza da hofi. Na dade da kula ko sunanta na

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment