Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daure ko P.O.P ne kayi sai mu aurar da kai....ga Rahima 'yar karama da ita har ta bani tausayi"


Kamar zaiyi kuka ya ce "wayyo Hamma ya na neman fassara ni"


"Me kaji nace? Daga cewa 'yar karama to ba karamar bace?" Ya kuma yin dariya.


"Wallahi zama da Adda ya fara nunawa a jikinka ni dai sai da safe" Emzee ya bata rai ya rakoshi waje.


Tare da su Yousuf suka tafi. Yana zuwa shima kwanciya yayi yana rungume da Radhiyansa. Washegari akayi gagarumar dinner da daddare inda ma'auratan suka yi shigar buzaye su da iyayensu. Da safe kuwa kowa ya kama gabansa. Yousuf da Arifah Hawaii suka wuce honeymoon daga can kuma zasu tafi France inda gidansa yake kusa da na iyayensa. 


Su Awwab ma a ranar da suka koma washegari bakwai na safe suka tashi zuwa Athens babban birnin Greece zasuyi kwana goma kafin ya koma aiki.


Duk wannan abu da akeyi babu wata alama ko kadan da Rahima ke nunawa ta damuwa sai dare yayi ta kwana tana kuka. Sabanin Halifa da yake namiji ita abin ya tsaya mata a rai fiye da kima. Da ciwo matuka ace mahaifiyarka ta cutar da wani, wanin ma kanwarta ta hanyar asiri har tayi shekaru goma babu ido. Ita nata daya ne yanzu baya bambance mata abubuwa amma yaya take ji bare wanda zai ga tsananin duhu na tsayin lokaci. Abu na biyu bai wuce mahaukacin so da tausayin Emzee da take yi ba. Ko kadan bata ganin laifinsa don ya kyamaceta. Uwa tafi karfin wasa. Ita ma bata guji Salame ba duk munin halinta ta yaya shi ba zai tsayawa tasa mahaifiyar ba..mace kamar Ummi mai kyauta da kyautatawa. Bayan dogon tunani da koke koke a boye ta yankewa kanta shawarar hakura dashi har abada. Emzee ba sa'an aurenta bane da kunya ta iya hada ido dashi bayan abinda Ummanta tayi musu. Sai yanzu ma take dada godiya ga Allah da ita ta samu a ido da wayar ba Radhiya ba. Da zasu barta ta koma Sumaila da tafi jindadi ma. A zahirin mu'amalarta da mutanen gidan duk karancin shekarunta ta iya daurewa ta nunawa Ummi bata da matsala. Har daki Ummin ta kirata akan maganar Emzee ta ce mata ko yana sonta bai taba fada ba. Shi kuma yana makaranta bare ya karyata.


Satinsu guda da gama biki har an kai Rahima sabuwar makarantarsu anyi sa'a sun barta a SS3 amma Daada yasa an dauko mata lesson teacher wuni suke suna karatu saboda ta ci WAEC tunda bata yi rejistar NECO ba kuma an riga an makara. Ummi ma ta soma zuwa Baze tana kuma samun kulawa sosai daga maigida ran gida Zayyan Tureta. Cikinta mai laulayi ne shiyasa daga makaranta sai daki saboda rashin son kamshin gidan.


A yau ana sauran kwanaki hudu su Radhiya su dawo Emzee yayi magana da Awwab wanda yace kada ya manta shawarar da ya bashi game da Rahima. Bayan sun gama hirarsu ne ya tura mata text.


Zaune take tana kokarin solving din wani aiki da lesson teacher din ya bata a physics text din ya shigo. Duk a zatonta irin na layin wayan nan ne shiyasa zuciyarta tayi wani irin bugu da ta ga sunan Emzee. Jikinta wata irin rawa ya kama yi ta bude da sauri.


(Kanwata kwana biyu boko ya boyeki. Ina fata babu wata matsala a sch din taku. All the best Rahima, Allah Ya bada sa'a. Yayanki)


Ta karanta wannan gajeren text yafi sau shurin masaki. Dama malamin nata ya tafi aikin ta zauna yi sai kuma ta kasa fahimtar komai dole ta tashi ta shiga ciki. Wayarta a hannu lokaci lokaci sai ta duba ta kuma karantawa duk da tana kwabar zuciyarta da take jinya har yanzu.


Da safe ma tana shirin tafiya makaranta wani text din ya kuma shigowa shima dai addu'a ce yake yi mata da fatan alkhairi. Baiwar Allah sai ta koma ruwa tsundum dan karfin halin nata ya guje mata. Haka dai akayi karatun ta dawo gida. Daga bakin kofa take jin muryar Salame tana cewa maiaikin nan gidan kanwarta ne ita bazata ci dan wake ba a dafa mata sabon abinci.


"Banda ta raina ni ai tasan yau zan taho amma shine da zata tafi makarantar bata bar muku sallahun dafa min komai ba sai danwake? Ko ki dauke shi ko na yanko masa tsinuwa dashi da hannun da ya tsumbula shi a ruwan zafi"


A kidime yarinyar tace "Ta fada mana zaki zo amma kinfi son danwake"


"Da kenan! Amma Yasin bazan zo Abuja inci danwake ba kamar wadda iyaye suka cewa jeki kya gani"


"Harda farfesun da salad din ma na kwashe?" Mai aikin ta tambaya a tsorace.


Salame ba kunya ta karbe tray din "kece bakiyi bayani ba, cha nake mai da yaji zaku bani."


Da gudu-gudu Rahima ta shigo ga takaici ga dariya ta fada jikinta.


"Umma?"


Salame ta washere baki kamar gonar auduga ta rungumota "Rahimata...."


Allah Sarki zuciya na wuya sai kawai ta soma kuka tana kankame a jikin mahaifiya mai dadi ko da kuwa ta buzuzu ce. Da kyar Salame ta samu Alh Indararo ya barta ta taho sai da tayi karyar zuwa zata yi suyi magana akan yaran da za ta basu. Malamijo kuwa cewa yayi indai tasan rigima ce za ta kawota Abuja bai yafe mata ba idan ta je. Damuwa ce fal a zuciyarta akan Rahima. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da yarinyar sosai. Daga baya ta fahimci dama can tana son abarta wasu abubuwan ta saka a gaba kawai.


Wannan kuka na Rahima ya tada mata hankali fiye da tunani ta kama hannunta zuwa dakin baki da yake kasa.


"Rahima wani abin kika sake ji nayi?" Ta tambayeta a tsorace tana fata yanzu kuma ba labarin ta taba son Zayyan Tureta bane ya fito.


Girgiza kai tayi hawayenta yana karuwa cikin rawar murya ta ce "Umma nace ki rinka yi min addu'a Allah Ya cire min Ya Emzee daga raina Umma ba kya yi...Umma ko sau daya kiyi min addu'a a rayuwata" ta durkushe a kasa tana matsanancin kuka.


"Ina miki addu'a duk sallah Rahimata, idan ban miki ba wa zanyiwa bayan duk abinda naja miki" Salame ji tayi ta tsani kanta tana Allah wadai da son zuciya. Ita bata girbe da hannunta ba 'yar da take jin kunya ita ce take mata dakon wahala. 


A wannan lokacin Mairama ta nufo dakin saboda an sanar da ita zuwan Salame. Nan ta jiyo kukan Rahima ta bude kofar da sauri sai ta ga sabanin abinda ta zata wato tana dukanta rungumeta tayi.


"To me yasa bana jin komai, kirjina kullum ciwo yake. Ki koma gida dani ina kunyar Ummi, ina kunyar Daada dasu Adda Radhiya"


Fuska sharbe da hawaye Salame take shafa bayan Rahima "kiyi hakuri zan roki Mairama na santa da hakuri za ta duba lamarinki tunda tana sonki"


Rahima sai girgiza kai take yi "a'a Umma bazan taba auren Ya Emzee ba ko...."


"Ya isa haka Rahima zo ki fita" Mairama ta yi mata tsawa cikin bacin rai "ina zaune da ke ina bibiyar me ya sameki ni kin kasa fada min saboda ni baki daukeni uwa ba?"


"Ba haka bane Ummi kiyi hakuri" tace tana dawowa kusa da ita tana wani irin kuka.


 Rungumeta Mairama tayi sannan ta ce "Karami ya taba cewa yana sonki?"


Kai ta daga kawai jiki na rawa. Wannan wane irin so ne mai cin ruhi da ba za ta iya hakura kamar yadda take son yi ba.


Cikin kulawa ta sassauta muryarta "indai ni na haifi Zayyan in sha Allahu sai kin amsa sunan matarsa tunda shi ya fara nemanki"


"Ummi a'a" tace saboda sanin da tayi cewa yanzu baya sonta.


Salame ta galla mata harara ga hawaye har yanzu "ke kaniyarki, ku ji min yarinya ana baki kina kin karba"


Mairama murmushi tayi sannan ta ce "Kina so muyi fada ne?"


"A'a"


"To kada na sake jin zancen me ya hadani da Addata a bakinki ko na 'yan uwanki sai na saba muku. Babu ruwanku tare kuka ganmu. Karami kuma ki tattara shi ki zuba a kwandon shara ki fuskanci karatunki sai ya nemeki da kansa. Akwai wani namiji da ya isa ya ja wa RAHIMATA aji ne" ta kalli Salame da jin baki taji me zata ce.


"Na fada miki Mairama ba dai hakuri ba ke dai barta da zuciya kamar kuturwa" cewar Salame tana fyace hanci da mayafinta.


Rahima tayi murmushi ta ce "kai Umma"


Mairama tayi 'yar dariya ta ce "Kin dai ga yadda nake hakuri da ita ku ma sai kuyi ta yi. Kiyi wanka ki ci abinci. Yau ranar zuwan malamin islamiyyar ne ko na lesson?"


"Lesson ne"


"Kici ki kwanta zan kira shi nace ya bari sai gobe....idan na sake ganin hawayenki akan wata damuwar da ba taki ba ni da ke ne"


Fita Mairama tayi Salame ta bi bayanta da sassarfa. Kamar ba ta ji ta ba sai da ta shiga dakinta itama ta shigo kawai ta durkusa a gabanta tana  kuka. Itama Mairaman kuka ta saka tana tsaye Salame na durkushe tana yinsa mai cin rai da zuciya abin tausayi.


Lallai duniya mai yayi duniya juyi juyi yau ita Salame Ali ita ce durkushe a gaban Mairama Ali tana kuka irin wannan "Ki gafarceni Mairama wallahi ban kyauta ba, soyayya ba hauka bace ni ban san me yake damuna ba ko tunanin me nake har na rinka yi miki irin wannan diban albarka. Da gaskiyar mijinki hassada na dorawa zuciyata gashi ina nan jiya e-yau. Don Allah ko bayan raina Mairama ki aurawa Karama Rahima ko ta sami saukin cutarwar da nayi mata. Kinga ni ce da laifin amma ita ke da wahala banda haka ina ita ina wata soyayya mai zafi haka..."


"Adda ki tashi ki zauna muyi magana"


"Idan kinga na zauna to yafe min kika yi"


"Ke fa kika ce mun wuce wannan matakin tun a Nijar" inji Mairama


"Lokacin ma wasa ne nake yi mutum baya wasa da rokon gafara." Salame ta sake kwantar da kai.


"Komai ya wuce a wurina, dama can ke kika jawo muna zaman zamanmu kika canja hali. Allah Ya kara mana hadin kai"


Wani kallo mai cike da girmamawa da mutuntawa take yiwa kanwarta. Idan tana da sauran shakku na cewa Mairama tayi mata fintinkau a komai ya kau a yanzu. Za ta iya rantsewa cewa idan ita ce Mairama sai ta baro mata rashin mutumci kwando kwando kafin ta hakura. Halinsu ba daya ba haka nan zuciyarsu da bambanci. Kila shiyasa ita ta kare a kasa marainiyar wayonta ta haye ta barta.


"Nagode, nagode, nagode...amma nace ba, maganar Karami da Rahimata za ki sanar da maigidan naki da wuri ko" 


Dariya ta baiwa Mairama "Adda Salame kenan maganar aure ai babu ita?"


"Cewa zakiyi baki yafe min ba!" Salame ta saka sabon kuka.


Zaunar da ita Mairama tayi don ta gaji da tsayuwar ta soma magana a nutse "Adda daga Karami har Rahima yara ne masu karancin shekaru. Shi yanzu yana ashirin da biyu da watanni ita ko sha bakwai bata rufa ba haka ne?"


"Eh to amma auren wuri ba yafi ba ko don fitintinun zamani"


"Nima zanfi son haka amma shi da yake namiji bai gama karatu ba. Ita ma bana so a yanke mata ba hanzari muke yi ba. Wannan soyayyar da suke yiwa juna wuta-wuta kamar yaki harda kuruciyar da take cinsu su duka da kuma isharar Allah akanmu ni da ke. Mu barsu su kammala, su kara nutsuwa su sake hankali sai mu ga abinda Allah zaiyi. Kada kiyi min mummunar fassara duk duniya babu matan da Karami zai kawo min a matsayin suruka nayi farinciki sama da Rahima ko Zayyana saboda su ne 'ya'yana. To Alhamdulillahi ba tare da wata dabara daga garemu ba sun daidaita kansu. Mu kara hakuri kadan wannan hayakin ya sauka hankali ya game jikinsu musamman shi namiji da ragamar gida za ta hau kansa"


Kallonta Salame take cike da sha'awa tana murmushi "lallai boko ya ratsaki Mairama ji yadda kike fito da bayani mai ma'ana da kuma hangen nesa. Hakan yayi min wallahi dama burina ni dai in hada zuri'a dake duk tsiya ko albarkacin jikoki sai kin yafe min" ta kare da murmushi.


Sai da Mairama ta dara don tasan tsokanarta take yi "zan yiwa Rahiman bayani da kaina ba rabasu zanyi ba amma a maida kai wurin karatu. Babban tashin hankalinta kuma kinsan akan yadda kike yi ma ta ne ina rokon arziki ki gyara ko zamu ji dadi"


Dofana mazaunanta tayi a kusa da kanwarta sai ta ga bata kyareta ba sannan ta saki jiki "Mun riga mun shirya da ita fa...zancen gaskiya ma ina ganin laifinku a yadda na canza ke da Malamijo"


"Da muka yi me?"


"Tunda abin nan yake ta faruwa da kun sani kun karbo min taimako ko da na ruqiya ne don jikina yana bani me yiwuwa shafar jinnu ke damuna"


Mairama ta kwashe da dariya "idan jinnu basu shafeki ba ai wannan annakiyar kazantar za ta shafeki. Adda ji hakoranki don Allah koraye babu kyaun gani. Na san da wuya idan Alh Indararo yana iya kusantar wannan bakin naki"


Salame ta rike haba "su Mairama babu ranar girma, kada dai kice min kuna nan kun daddangwalar bakunan juna ke da mijinki"


Dariyar da Mairama tayi ta jima rabonta da irinta "wai dangwalar baki...to naji ko ma me kike kiranshi ku ba kwa yi ne?"


"Allah Ya agajeni ni ko magana yake min kaina baya matsowa kusa da bakinsa mai dan uban wari"


"Wai Kura ce za ta ce da Kare maye, ke ma me zai kawo shi gaban naki. Ina ku ka baro brush da makilin?"


"Tabbb..mu sami na kai wa bakin salati dai shine magana." Tashi tayi tana murza hannuwa "yanzu dai tunda hankalinki ya kwanata Salame ta dawo gareki a taimaka a bani abinci"


"Au ni kadai ce hankalina ya kwanta? Shikenan jeki abinki kowa yayi ta kansa"


"Daga wasa sai ki hade rai kamar zawo" Salame ta ce tana murmushi. Babu abinda zai faranta mata yanzu kuma sama da ganin ko yaya ita da Mairama sun fahimci juna.


Wata dariyar Mairama tayi kawai tana cewa ta kula kazanta ta sami mazauni a tattare da yayarta.


Abinci Salame taje taci ita kuma Mairama tayi wanka ta sauko kasan. Salame dai kasa sakin jiki tayi duk yadda ta so saboda wani girma da kwarjini da Mairama ta kara a idonta. Masu aiki take gani su na rawar jikin cika umarninta kuma ba wai don ita din ta kasance mai tsanantawa ba. Ko kadan, tsabar iya mu'amala da nuna musu cewa su da ita abu guda ne ya janyo hakan. Nasiha da jan kunnen da ta yiwa Rahima ya sake ninninka girmanta a idon Salame. Cikin hikima da sanin ya kamata take nuna mata ta ajiye komai tayi karatu. Ga mamakin Salame har ji tayi tana cewa,


"Karami ba autan maza bane kada ki bari tun ba ku daidaita ba ya san cewa kina son shi haka. Kuma kada ki sakawa zuciyarki lallai sai shi, rayuwa bata da tabbas, kiyi kokarin inganta rayuwarki da ta iyayenki da kuruciyarki"


Kunya sosai Rahima ta ji. Sai yanzu da maganganun Ummi ta soma rarrabe abubuwa ba kamar da ba da ta afkawa soyayya da ka babu wani ilimin sanin duniya. Ummi uwa ce ta gari kuma mace da ta san girman zumunci. Ba don zumuncin ba Allah kadai Ya san irin rayuwar da za tayi da 'ya'yanta. Mutane da dama sun taimaka mata albarkacin zumunci ba ta da dalilin kin kwatanta alkhairi bayan itama anyi mata.


Da Zayyan ya dawo Salame har kasa ta durkusa ta gaishe shi ta kuma roki gafararsa wannan karon da zuciya daya take yi saboda duk abinda zai kawo hawaye a idanun Rahima gudunsa take. Kwananta biyu ta tattara ta koma da shatara ta arziki daga wurin Mairama. Rayuwa bata da tabbas, yadda ka dauketa haka za ta zo maka.


Rayuwarsu ta cigaba da tafiya gidan Mami shiru da ga ita sai Zayyana su Fauziyya an koma Katsina, Zahra kuma rana daya ma su ka tashi da su Awwab sun koma Germany. Ibrahim yana Kano, Emzee a Kaduna kowa ya cigaba da harkokinsa.

***********


Zaune suke a cikin jirgi kamar Radhiya za ta shige kirjinsa ta dora kan ta a kafadar Awwab, yatsun hannuwansu na sarke da juna yana yi mata rada a kunne tana dariya.


Dago kai tayi tana tura baki "ka ga bana so"


"Ni ina so baby, ina jira ki kirani bayan na koma ki tabbatar min kawai"


Gabadaya zancen ma kunya yake bata so take a canja wani. Ta yaya zaiyi ta cewa wai yana jin tana da ciki zai fara siyayyar haihuwa tun yanzu.


"Wane suna kike son mu saka kinsan tun yanzu zamu fara shawara"


"Kai Hamma wai me yasa kake min haka ne. Ni wallahi kunyarka nake ji"


Ido ya bude yana mata wani irin kallo "Really? Da gaske kunyata kike ji with all the......"


"Shhhh" tayi saurin rufe masa baki da hannunta ya rinka cizon cikin hannun sai da ta dauke tana kai masa duka. 


"Ke ce da wani abu za ki hanani fadar gaskiya"


"Ni dai mu bar zancen nan ko na canja seat"


Alamun zip ya yiwa bakinsa ya koma ya narke mata  jiki tana biye masa suna hirarsu ta masoya. Kwanaki goman da su kayi a Greece sun kafa tarihi a rayuwarsu domin kuwa sunyi su ne cikin kulawa da tsantsar kaunar juna. Kowa kokarin zarta dayan yake wurin kyautatawa ga shakuwarsu ta kara karfi kusan komai tare suke yi. Wani lokacin sai su cinye rabin dare suna hira kawai da bawa juna labarai. Yawo kuwa anyi kamar kafafu zasu tsinke.


Shiru Radhiya ta ji Awwab ya dena magana ashe bacci ne ya kwashe shi. So da tausayinsa take ji saboda idan sun sauka a Abuja yau jibi da yamma zai tafi. Sabon da su ka yi da juna a kwanakin su tare yayi karfin da ba karamin ji zasuyi a jikinsu ba idan sun rabu. Gashi zaiyi a kalla sati uku ko hudu kafin ya sami kansa. Saboda tsarin aikin nasu mutum zaiyi aiki na wasu awanni ne masu yawa sannan ya sami break wani ya karba. Haka suke yi shiyasa su kan dauki kwanaki ko watanni batare da iyalansu ba. Kullum suna tare kamar cingam idan tayi nesa dashi bata san yadda zasu ji ba. Hannunsa ta kara damkewa a hankali itama bacci yayi gaba da ita.


Sanarwar saukar jirgin cikin mintuna kalilan ne ya tashesu. Radhiya ta gyara fuskarta ta gyarawa Awwab wuyan rigarsa da ya lankwashe su ka jira saukar jirgin.


Dreban Daddy ne yazo daukarsu tare da Zayyana da Rahima wadanda su ka kankame Radhiya suna murna. Anje shiga mota Awwab ya ja Radhiya gefe.


"Schatzi ki rage tsallen nan kada ki taba lafiyar ajiyata" yayi maganar yana kallon saitin cikinta.


Dariya ta yi "Na shiga dari Hammana idan ya zama gaske za ka barni na sakata na wala kuwa?"


"Sosai ma, indai ba zai dami babyna ba"


Gidan Mami su ka wuce Radhiya ta sami kanta da matsananciyar jin kunyarta kuwa. Mami ta taho da murnarta za ta rungumeta ta zube a kasa tana kwasar gaisuwa. 


"Kaniyarki Radhiya, surukar ki na can Maitama" tayi nuni da kofar gidan tana nufin Ummi "zo nan in gani idan ya kula min da ke yadda ya kamata"


"Mami ni zaki fara dubawa ko tana kula dani" Awwab yace yana zama a hannun kujera.


"Waye yake ta katon mutum kamar ka? Zayyana dauko musu mukullinsu aje a huta abincinku ma yana can"


Duk wani nauyi ya kama Radhiya da kyar ta iya tashi bayan Mami ta matsa mata. Suna fita su ka shiga gidan Mama Radhiya ta dauki DK yaron sai girma yake karawa ga wayo. Da murna ta rungume Maman ita kuwa baki yaki rufuwa ganin 'ya'yan nata sunyi shar da su gwanin ban sha'awa. Abincin da ta dafa musu ita ma su Rahima sun kai musu nasu gidan.


Awwab ne ya bude kofar yana rike da hannunta "finally we are home...shiga da kafar dama kuma kiyi addu'a"


Umarninsa ta bi su ka shiga tare. Numfashinta ne ya tsaya a bakinta saboda irin dukiyar da mahaifinta ya narkar a falon kawai. Awwab ne ya ke janta sai da su ka shiga kitchen, store da dakunan gidan guda uku wanda daya da yafi kusa da kofa falo aka maidawa Awwab saboda baki maza.


Wanka da salloli su ka gabatar sannan aka ci abinci. Ranar kafin tara sun kwanta jiki kamar anyi musu duka. Washegari ma kafin fa dora komai an kawo daga gidajen biyu shiyasa ba ta dafa komai ba. Gidan Mami da Mama suka je su kai musu tsarabarsu sannan su ka wuce gidan Ummi.


Daada baki yaki rufuwa ya ga Alheran dinsa ta kara kyau ta ciko.


"Awwab me kake bata ne?"


Kunya ta kama Awwab ya sunkuyar da kai. Ummi tana ta jansa da hira sai ya kasa sakin jikinsa. Radhiya ta rinka masa dariya saboda itama sai da ya tsokaneta wai ta gama hada shi da jambaki ta kasa kallon Mami. Ya san dariyar ta meye shiyasa ya rinka harararta. Falon sama su ka koma ita da Ummi ta dame ta da tambayar wai don Allah Yaushe za ta haihu.


"Wai ke ba kya jin kunya ne? Da girmanki kinyi aure mamanki za ta haihu kamata yayi ko maganar kika ji ki gudu" cewar Ummi


Wata jaka mai kyau irin ta babies Radhiya ta daukowa tana cewa "Humm uhmm...da ga wannan ma ki haifo wani ina so ni dai"


"Allah Ya tsareni ke dai kuje kuyi mun bar muku a haifa mu goya"


Abinka da sarauniyar shirme budar bakin Radhiya sai cewa tayi "Kinsan Hamma yanzu kullum addu'a yake wai Allah yasa ina....." tunowa tayi da tabargazar da za ta tafka ta tashi da gudu "na shiga ukuna Ummi baki ji ba ko"


Mairama dai dafe kai tayi sai da ta ji alamun ta sauka kasa tayi murmushi. Ance hali zanin dutse gara ta dena damun kanta da yawan damuwa idan tayi wani shirmen. Dadinta daya yadda Awwab yake sonta a hakan ta. Allah Ya kara musu zaman lafiya da fahimtar juna tace a zuci. Jakar ta dauka baka ce 'yar madaidaiciya mai kyau ta farke ledar da aka nadeta. Gefe ga aljihu hudu biyu a gaba da baya sai kuma wurin zura feeder da karamin flask. Da dan nauyinta ta bude sai da taji kwalla. Kaya ne a jere an ninke suna wani irin kamshi a sama da 'yar takarda ta rubuta (welcome to the world baby Tureta).


Overall ce fara da farar hula na auduga masu bala'ain laushi. Sai vest da pant mai zebra stripes. Da wasu unisex kayan babies guda uku, tawul din wanka, shawl yellow shima mai laushi amma ba na sakar kulu ba. Sai feeder, siririn flask da kayan wanka harda baby perfume.


Ummi ta rinka murmushi tana yiwa Radhiyanta da Emzee addu'a. Shima kullum idan ya kira sai yace Ummi jikinki babu matsala ko? Ba zai fito kai tsaye yace ciki bane wai shi kunya. Idan tace lafiya sai yace Allah Ya kaimu lafiya. Tana nan Daada ya sameta ta nuna masa.


"To ai tunda ta saya in sha Allah da ita zamu je haihuwar"


"Da kai za'a?"


"In sha Allah" ya bata amsa.


Tare su ka sauko yiwa Awwab sallama sun ce sun yafe masa zuwa gobe. Mami tayi musu tayin abinci da su ka koma amma Awwab ya rufe ido yace na Radhiya zai ci.


Murmushi tayi "kinyi girkin ne Radhiya?"


Kai a kasa tace "banyi ba Mami"


"To kaji sai ku dauka a nan a daren nan za ka takurawa 'yata"


"Haba Mami gobe fa zan tafi banci abincinta ba kuma" ya turo baki.


Yayi sa'a Mama na gidan ta tare masa kafin Mamin ta tsige shi tace su tafi gida. Sai da su ja fita tace "Mami 'yan hana ruwa gudu"


"Yanzu laifin me nayi?"


"Shi girkin da mace za ta yiwa miji akwai sirrin dankon soyayya. Kyalesu taje ko karfe nawa ne ta dafa masa tunda yana so."


Kitchen Radhiya ta shiga Awwab ya tafi yin wanka. Aikin nata ya dauki kusan awa guda da rabi har ya gama shiri ya shigo tace ya fita kada kamshin girki ya kama masa kaya.


"Tayaki zanyi"


"Nagode Hammana just wait for me a falo"


Kallo ya zauna yi amma zaman duk ya isheshi saboda yau baya son abinda zai nesanta shi da ita. Tunanin yadda zaiyi managing rayuwarsa idan ya tafi ya addabe shi sai gata ta fito tara da arba'in da wani tray mai murfi silver. Murfin zurfi gareshi da fadi marikinsa a mulmule.


Kan dinning table ta ajiye ta koma ta dauko banana and coconut shake da ta hada tun kafin ta fara komai yayi sanyi sosai.


"Hammana na gama"

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment