Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idona za’ayi komai har rabawar don bana so ake kwarar wasu. ‘Ya’ya dai duka nawa ne”

Gidan tuni ya kaure da ihun murna ya shige ya sako silifas zai tafi gonar kafin su ma wurin aikin naman su kwashi rabonsu su boye.

Yana fitowa yayi kicibus da sojoji biyu a kofar gidan da wani yasha shadda sai kyalli take na sabunta. Su kuwa sojojin ya ganesu ne saboda kayan jikinsu wanda suka yi matukar kyau a cikinsu. Sai kuma dan Ta Madina wato kanin Salame da ta aiko rannan. Gaban Malamijo yayi wata irin faduwa baki ya soma rawa.

“Uhmm ince dai lafiya ko”
Hadir ne ya amsa fuskarsa dauke da murmushi “lafiya kalau dama akan Mairama da Salame ne…”

Ko gaisuwar da suke masa bai iya amsawa ba ya koma ciki jikinsa na bari.

Wanke-wanke ya hango Mairama tana yi yayi kanta a fusace.

“Ashe ba banza ba dazu kike murmushi abinda baki saba ba, wato kunje Kano idon ku ya bude shine kika kai karata wurin hakuma ko?”

Dago kai tayi da sauri Salame ma ta fito daga dakinsu don maganarsa ta hasko mata su waye. Kenan batayi sa’ar rabasu ba.
Shi kuwa a harzuke yake matuka ya shiga nuna su da yatsa “nasan kece mai bakar zuciya ke ki ka ingiza Salame ku ka kai karar, amma ku sani babu wanda zai kamani akanku, biki ne na barku kunje kuma san nan nace za’a kawo muku ku ci me ya rage”

Kana ganinsa kasan a tsorace yake sauran matansa su ma duk sun tsure. Yadikko ce tayi karfin halin riko hannun Mairama

“kin san ko su waye a wajen?”

Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta Yadikko ta kuma maimaita tambayar. Ganin ta ki magana sai ta sake cewa “kodai surukai ne daga Kanon?”

A guje Mairama ta yi hanyar dakinsu cike da kunya. Yadikko ta fadada murmushinta tana yiwa Malamijo da yayi saroro a wurin bayani. Sai gashi yana wani kasaitaccen murmushi yana kada kai.

“O’oh kaga su Mairama Daso ‘yar Ma’aikin Allah. Ashe dai da farinjinin ta ban sani ba. Baku ga sojojin ba fa gwanin ban sha’awa. Ganinsu kadai ya sani shauki na tono lokacin da muka fara zuwa gwaji Jaji a can kasar Kaduna…”

Hajjo ta tuntsire da dariyar rainin wayo don tasan kawai sakin kwai zaiyi duk labaransa bata taba ji yace yaje barikin sojoji ba.

Hankalinsa ya koma ga Salame yana tambayarta ko ita ma da bakonta. Ciwon da yake cin ranta bai bari ita ta gwada kunyar ba kawai ta hade rai ta koma daki.

Mairama ya kwalawa kira ita ta bashi tabbacin akwai wanda yake son ‘yar uwar ta ta. Sai ga Malamijo baki yaki rufowa “Ka ga Ummassalama abu yayi kyau. Allah dai Yasa mai shaddar ne naki don bazaki iya da hakuma ba, wannan sai ‘yar kunama. Bari dai na koma wajen bakin”

Su na tsaye ya barsu da kokonta sai gashi ya dawo da fara’arsa har babbar riga ya doro akan kayan jikinsa.

Tabarma aka shimfida musu a zure shi kuma yana daga kan wata kujerar karfe ya baza riga don ya cika ido. Gaishe shi suka sake yi Hadir yayi masa bayanin komai game da zuwansu da bukatar idan ‘yan matan sun amince ayi komai da wuri musamman saboda su basa samun damar fitowa daga barikin suyi dogowar tafiya batare da dalili ba. Yawonsu baya wuce cikin gari kada a nemesu sunyi nisa.

“Ku kwantar da hankalinku Kano dai ba bakuwata bace sannan a can birnin Shehun ma akwai wanda na sani don na taba zuwa garin. Kunsan wani mai kilishi a hanyar Dange shuni? Yana nan wani dan firit haka yace min asalinsa ma mutumin Zaria ne. Kila zai iya tuna ni don naji dadin kilishinsa na sayi da yawa lokacin…”

Duk sun dauka wata alaka zai ce tsakaninsu ko karin bayani sai suka ji zancen yakare, Zayyan sarkin dariya tunda yace mai kilishi dan firit ya daga kai ya kalli Malamijo sai kawai ya kunshe dariyarsa kada ya jawowa kansa. Sun ji dadi ya ce ya basu yaran sai su fara shiri. Tashi yayi yace su jira zai turo su ko gaisawa suyi tunda su Zayyan a ranar zasu koma Sakkwato.
Kusan a shirye Mairama take kira kawai take jira yayin da Salame ta nade akan katifa wai zazzabi ke damunta. Mairama tayi mata sannu ta bi bayan kanwarta da ta sanar da ita Malamijo yace taje wurin bakin.

Sai da tazo bakin kofar da zata sa da ta da zauren da suke, kunya ta hanata shiga. Da Hadir ya hangota, ya fara zolayarta cewa ko sune bata son gani bari su basu wuri. Kai a kasa ta rufe fuska ta shiga ta gaishesu. Salisu yana cigiyar gimbiya Salame ta sanar masa bata da lafiya. Yanayin fuskarsa ya nuna baiji dadi ba.

“Ki dai taimaka min naga alama so take ta saka min ciwon zuciya”

Zayyan da Hadir ne suke kwantar masa da hankali har suka fita don a bar Zayyan suyi magana da Mairama.
“Mairam tafiya ba sallama ko?”

Kanta a kasa ta amsa “kayi hakuri”

“Nayi tunda zuwan nawa ya haifar da da mai ido gashi an bani ke”

Wata matsananciyar kunya ce ta shigeta ta sake dukar da kai. Shima yasan a hanya suke shiyasa bai ja ta sosai ba yace zaiyi kokarin dawowa kafin magabantansa su zo. Yau a hanya suke suna sauri. Wata leda ya mika mata, yayi yayi, taki karba sai ya tashi ya barta a wurin. Iyakarta bakin kofa tayi musu sallama da kyakkyawar addu’ar tafiya.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: E
*TUN RAN GINI…*


Tana shiga daki ta sami Salame a tsaye sai safa da marwa take saboda zulumi. Yanzu shikenan abinda take so sai ta hakura dashi saboda Mairama. Gaskiya bazata iya ba domin son da take masa ba kadan bane. Kuma ma dai ai ita ce ya kamata yaso tunda danginta ne, Mairama kara kawai akayi mata. Ta nisa a cikin tunani taji Mairama tana mata magana.

“Adda jikin ne dai? Ko na sanar da Yadikko a fadawa Malamijo?”

Hade rai tayi ta koma ta zauna akan tabarma “ke yanzu banda rashin kamun kai me ya kaiki dadewa wurin saurayi daga zuwansa na farko? Mutumin da ba wani saninsa ki ka yi ba don iya zubar da aji.”

Kwarai Mairama tayi mamakin kalaman Salame don a iya sani da kuma shaidar da za’ayi mata a gidan tafi kowa saukin kai da dadin mu’amala. To amma meye ya kawo wannan zantuka haka? Kasa daurewa Mairama tayi ta koma bakin katifarsu ta zauna ita ma.

“Adda Salame wai me nayi miki ne haka don Allah? Kwana biyu kenan sai kiyi ta harara ta kina fada min maganganu”

“Ji rainin wayo ki min kwace kizo kina min dadin baki” tace a ranta amma a zahiri sai ta daure tayi mumushi “gani nayi daga yin saurayi kin haukace a kansa ko tunanin idan kin bar gidan nan da wa zan zauna ba kya yi?”

Jikinta sai yayi sanyi ta sake matsowa kusa da Salamen “kai Adda me ya kaiki wannan tunanin? Shine kike ta fushi…ohh ni wallahi duk kin tayar min da hankali na damu. Kema ga Salisu ba sai mu bar gidan tare ba.”

Turo baki Salame tayi “dena min zancensa wallahi baiyi min ba, ke dai kinyi sa’ar Zayyan kawai kina murna”

Rarrashinta Mairama ta soma yi a zatonta da gaske tunanin rabuwarsu a gaba ke damunta. Sauran kannensu mata babu sa’anninsu, maza biyar ne su ke binsu. Koda Salisu ta shiga yi tare da bata sakon gaisuwarsa ta yi tsaki da gaske dai bata son zancensa.

“To na bar zancen nasa Allah Ya kawo wanda ya fishi alkhairi. Shima yace na gaisheki da jiki kuwa”

“Shi wa?” Salame ta fada cikin gatsali wanda Mairama duk ta sawa ranta duk a cikin rashin son su rabu ne.

Tambayar kunya ta bata ta soma inda-inda ba ta san da me za ta kira shi ba. Sunansa dai da wahala ta iya fada a yadda take matukar jin nauyinsa.

Zungurinta Salame tayi da kafa tana mata wani irin kallo mai tattare da kishin da ake kokarin sakayawa.
“Zayyan kike nufi?”

Kai ta gyada ga mamakinta sai ta ga fuskar Salame ta washe sosai tana murmushi “ashe bai manta ni ba. Me yace? Ina nufin da yaya ya baki sakon? Ki gaishe da Salame yace ko me?”

Dadi taji ganin sauyi a tare da yayarta ta kuwa biye mata tana fada mata yadda yace da zai bada sakon gaisuwar. Har dare ranar Salame motsi kadan sai ta tuna wai Zayyan yace a gaisheta, sai taji wani dadi yana ratsata.

**********

Matafiya sun sauka a cikin garin Sakkwato lafiya. Ba wata gajiya su ka yi ba don sun dade da fara sabawa da wahala suna jure mata sosai. Gidansu Zayyan su ka wuce zai dauki kayansa da ya bari sai su koma barrack dinsu.

Gidan yanzu dama daga Jume sai Maikudi, Rayyan da Badaru wadanda sune Zayyan yake bi dukkansu babu mai aure. Matan kuwa Fiddausi, Mubaraka da Hafsatu duk suna dakunansu. Kwasar tuwo Jume take yi Badaru yana zaune akan turmi da ya kifa sai Maikudi kwance a kofar daki yana faman firfita su ka ji sallamar Zayyan din.

Babu wanda ya amsa masa cikinsu sai harara da suke binsa da ita. Dakinsa ya wuce kai tsaye ya dauko jakar kayansa a ransa yana bakincikin halayyar ‘yan uwan nasa. Ba haka ya bar jakar ba alamu sun nuna an bude an yamutsa masa kaya wurin neman abin da yake zaton kudi ne, sai dai ko kwandala bai bari a ciki ba. Ratayo abarsa ya yi ya fito ya kulle dakin.

“Sai Allah Ya sake dawo damu ni zan wuce” yace daga tsaye yana dan rissinawa Jume.

Maikudi ya tashi zumbur yana kallonsa, ita ma Jume ta juyo da kujerar da take zaune a kai yadda za ta fuskance shi da kyau.

“Zayyanu ni zaka wulakanta a gidan nan? In baka umarni saboda ba uwarka bace sai kasa kafa ka take. Kwana nawa ina sawa a dubo ko gidan Aminun ka makale babu kai babu labari sai yau. Shine har kake da bakin cewa zaka wuce.”

Baya son ya kai ga yi mata abinda zai zo yana nadama nan gaba ga darajarta na matsayin wadda ta rike shi kuma matar babansa, da idan ya fada mata wata maganar ko hanyar da ya bi bazata so ta sake bi ba.

“Jume Kano naje biki ba maganarki naki ji ba”

Maikudi ya dawo kusa dashi ya miko hannu kamar wanda ya bawa ajiya “ina kudin da tace ka karbo a wurin wancan tsohon munafukin?”

“Yanzu aminin Baba kake kira munafuki?”

“Kaga kafin ka fara dogon surutu bani kudin ka wuce bana son rigima da al’murun nan” Jume ta fada tana kara tamke fuska.

Dago idanu yayi ya zube mata a kanta sai gashi jikinta ya yi lakwas. Rayyan da Badaru ma kowa ya sha jinin jikinsa. Maikudi ne kawai hankalinsa bai kai wurin ba.

“Jume!”

“Eyye” ta amsa a dan tosrace.

“Kudi dai gadona ne ni kadai kamar yadda a gabana aka bawa kowa nasa...”

“Kai, rashin kunya za ka yi mata a gabanmu?” inji Maikudi.

“Idan na fahinceka Zayyanu kudin ne ba za ka bani ba saboda ban isa in nemi abu a wurinka in samu ba?”

Tausayi ta bashi yadda ta hakikance akan rashin gaskiyarta bata ko tunani sai son bukatarta ta biya. Hannu ya zura cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dari ‘yan ashirin guda biyar ya mika mata.

“Ga wannan ku kara cefane” yace cike da nutsuwa, bai kuma jira cewarta ba ya fice waje inda Hadir yake jiransa.

Yana fita Maikudi ya warce kudin a hannunta yana jaddada mata tasan yadda zata yi ta karbo musu ragowar idan ba haka ba shine zaiyi ajalin Zayyanu sai ya ga ta inda zaiyi amfani da kudin.

“Banza shashasha to sai ka dawo, kafin kayi ajalin nasa shi zaiyi naka. Har mamaki kake bani yadda kake manta zuciyar Zayyanu da kuma kasancewara soja. Yanzu idan yasa aka kamaka duk duniya bana jin kana da wanda zai fito da kai. Nima kaina tsoronsa nake ji dan jakar uba, daurewa kawai nake ina masa barazana. Amma muje zuwa sai na dawo dashi tafin hannuna. Uwarsa ma mai suna kamar na tsuntsaye bata iya karawa dani ba”

**********

Sati uku da dawowarsu a tsukun lokacin iyayen Hadir sun zo daga Kano an daidaita maganar aurensa da Zainab. Kullum ya dawo ya ishi Zayyan da labarin hirarsu ko maganar biki. Ranar da ya bishi kuwa yadda ya kula suna son juna musamman Zainab da duniya bata ganin kowa da gashi sai Hadir sai yaji muguwar kewar Mairama.

Ranar lahadi ya samu da babu training sosai ya fita yaje ya sanar da Mal Aminu da mutum biyu cikin ‘yan uwan mahaifinsa game da auren da yake nema. Sunyi farinciki da alkawarin bayan ya koma Kanon ya fadawa mahaifin yarinyar zasu je bayan sati daya da zuwan nasa. Godiya yayi musu ya nemi matar Mal Aminu mai suna Gwaggo Ladi matar da ta maye masa gurbin uwa wurin kulawa da bashi abinci da sauran abubuwa lokacin da kowa ya gane gashin kuman da Jume take yi masa. Kudade ya bata da yake so a fara siyayyar kayan aure ta yadda idan zasu tafi zasu je ne a shirye saboda nisa.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: F
Sai da ya nemi izinin fita na kwana biyar, da kyar kuwa bukatarsa ta biya saboda ba kasafai ake son suna yin nesa da barikin ba. Ranar da zai tafi sai da ya bi ya sallama da Captain Mustapha. Yanzu alakarsu tamkar wa da kani ga kuma yaransa sun mayar da Zayyan uba na biyu. Shi Captain Mustapha asalinsa da Katsina ne daga shi har matarsa don auren gida ma su ka yi.

Asubancin fita yayi ya shiga cikin gari gidajen dangin Mal Muhammadu. Daga can ya wuce tasha sai Kano.

Yayi sa’a masu kilishi sun fito ya sayawa Malamijo. Shi dai a dan zamansu na farko bai hango komai a tattare da shi ba sai barkwanci.

Kwanakin da suka gabata Salame ta dami Mairama wai me ya hana Zayyan dawowa saboda Salisu ya matsa lamba kuma Malamijo ya riga ya bashi. Ganin akwai kudi yaron ya kara shiga ransa. Salame so take ta tabbatar Zayyan bazai dawo ba sai ta amince masa ko babu komai zata huta. A haka tana tsoron saurin amincewa ya dawo a bashi Mairama ita kuma ta rasa. Akwai ranar da ta tambayi Mairaman ko ta fadawa Zayyan yanayin gidansu.

“Kinsan boye-boyen babu amfani gara yasan wa zai aura kada Malamijo ya nuna masa hali”

Bata rai Mairama tayi “yau da kanki Adda Salame kike cewa Malamijo zai nuna hali? Ni dai soyayya bazata sa na kwashe sirrin gidanmu na kaiwa saurayi ba. Idan bai aureni ba shikenan ya gama sanin komai nawa. Kuma ko yaya Malamijo yake ai babanmu ne dole mu so a mutunta shi”

Waskewa Salame tayi amma a ranta tana ganin ta sami hanyar rabasu “irin wannan sharhi ba wani abu nake nufi ba, abar maganr dai”

Yau kamar daga sama sai ga dan aike wai ana sallama da Mairama inji Zayyan.

Wanka take yi lokacin ta gama aikin fura Salame ce taji sakon. Jikinta har bari yake tsabagen murna ta fada dakinsu da sauri. Kaya ta sauya da sauri ta shafa hoda harda janbaki ta sako daya daga cikin kayan da Ta Madina ta dinka mata. Komai da azama take kada Mairama ta fito ta sameta. Tazo fita ta koma ta cire mukullin sif din kayansu bayan ta kwashe duk wani kayan sawa ta saka a ciki ta jefa a karkashin sif din ta fita tana dariyar mugunta.

Bata yiwa kowa sallama ba don basa tsakar gidan ta fice zaure. Dama niyarta da an tambayeta ina zuwa tace wurin Innarta zata je.

Kamshin turare wanda Salisu ya kawo mata zuwansa na karshe ya fara ji kafin ya ganta. Ta gumbuda turaren sosai kuwa a ransa yaji dadi ba Mairamansa bace take wannan aika-aikan. Fuska ya saki yana mata murmushi. Ta sunkuyar da kai tana ‘yar dariya don jin kanta take kamar yau take sallah saboda ganin Zayyan.

“Babban bakonmu barka da sauka, yaya hanya?”

“Lafiya kalau Saude ya mutanen gida”

Wani abu taji ya soki zuciyarta, wato ku sunanta bai rike ba. Bata nuna damuwar a fuska ba sai ma wani kasha murya da ta tsiri yi “Salame dai ko, baka ma rike sunana ba saboda baka damu dani ba”

Banbarakwai yaji zancen nata “Afuwan kada ki fadawa Mairama tace ta fasa na yiwa Addarta ko ince Addarmu laifi”

“Ba wani abu ai, ita ma bata soma fada ba yadda ta matsu tayi auren nan. Allah Ya dube mu, masu gudunmu saboda Malamijo zasu sha kunya”

Zayyan mutum ne mai saurin dago ina mutum ya dosa idan suna magana, yanzu ma tuni ya fahimci akwai abinda Salame take son fada masa tun hirar bata tsawaita ba.

“Ban gane masu gudunku saboda Malamijo ba, ba babanku bane?”

Hannu ta dora akan bakinta kamar gaske tana ware idanu “ba dai Mairama bata yi maka bayani ba? Irin haka ai da wuri ake fada saboda toshe matsala don kada kaji a waje. Idan na koma zan fada mata gara ta sanar da kai komai da wuri zai fi. Sai ka danyi hakuri ta gama aikin furar sayarwa ne ta shiga wanka”

Wai shi za ta jawa rai, kawar da kai yayi abinsa yana kallon waje. Haka nan bata yi masa ba tun haduwarsu ta farko a gidan Gwaggonta da akayi bikin yaranta. Sai tayi ta wani kifi-kifi da idanu amma sau goma idan zai dago kai sai sun hada ido.

Yanzu da ta ji bashi da niyar tambaya sai ta sake salo. Jan hanci yaji tana yi alamun tana kuka. Dawo da hankalinsa yayi gareta da sauri.

“Ya dai?”

Goge hawayen da ko digonsu babu tayi sannan ta dan tabe baki duk yana kallonta “gara kawai na fada maka don abin zai yiwa Mairama nauyi”

Halin Malamijo kaf da yanayin zamantakewar gidansu ta kwashe masa. Hatta dangin mahaifiyar Mairama sai da ta kwancewa zani. Jinjina kai kawai yake yi yana kara tausayin Mairama sosai. Yanayin rayuwarta kusan daya da tashi wato dukkansu basa jindadi a gidan iyayensu.

Salame sai ta dauki sauyin yanayinsa a matsayin tarkonta ne ya fara kamu ta dan murmusa “nasan rashin dangin uwa lokacin aure a kusa da ciwo…..” ta dan ciji labbanta “…uhmmm ni kaga dangin Innata suna garin nan kuma bikin da muka hadu ma nasu ne, Mairama kara kawai aka yi mata”

Yanzu ya gama gane manufar wannan dogon sharhin. Kaurara murya yayi ya hade rai “Salame!....”

Bai karasa maganar ba sai ga Mairama ta fito da sassarfa sanye da kayan da tayi aikin furar ta makale a bayan kyaure.

“Adda” ta kira Salame tana kunyar fitowa.

Zayyan ne ya amsa yana mai jindadin ganinta “Mairam yau a nan zamuyi tadin?”

Kai ta sunkuyar ta sake yafito Salame sai kawai tayi gaba abinta ta fice don tasan me take nema. Kusan minti goma tun bayan fitowarta take ta neman mukullin sif din bata gani ba. Baki ta saki ganin ta fice bayan tasan kiranta take. Duk sai taji ta muzanta saboda Zayyan ma ya gani kuma baiyi mamaki ba duk da bai san me take bukata a wurinta ba.

“Nima in zo bayan kyauren ne?”

“A’a ina zuwa don Allah kaya zan sauya”

Hannu ya daga ya dakatar da ita “dawo abinki nima nan kayan jikina sun sha wahala da kurar hanya amma na kasa hakuri ko masauki ban nema ba nayo nan”

Jikinta ta kalla musamman zanin taji babu dadi. Zayyan ya matsa mata akan ta fito ba zai dade ba sai dare zai dawo. Busu-busu haka ta fito kayan jikinta masu saurin nuna datti ne dama saboda haskensu.

Kanta ta sunkuyar tana kallon kasa ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a sake. Lura yayi a takure take sai ya mika mata ledar kilishin Malamijo yace ta shiga gida sai anjima zai dawo.

Yana tafiya a hanya amma zuciyarsa ta fada kogin tunanin kalaman Salame da kuma yanayin da ya ga Mairama. Yana da yakinin Salame ko dai tana son sa ko kuma kawai bata son cigaban kanwarta ne. Ko ma meye zaiyi kokarin sanin wacece Mairama Ali kafin ya koma bakin aikinsa.

A cikin gidan kuma Mairama sake komawa tayi neman mukulli har ta hada gumi amma ta rasa ina ya fada.

Da ta gaji da nema ga rashin sanin ina Salame ta tafi sai kawai ta cire kayan jikinta taje ta wankesu. Dije ce ta kasa hakuri tace mata me take yi da daurin kirji ta fada mata bata ga mukulli bane.

“Kin tambayi Salame?”

“Ta fita”

“Taje gidan uban wa?” suka ji Malamijo ya daga murya yana fada.

Tsoro taji da tasan zai shigo gidan a lokacin bazata fada ba.

Tsawa ya sake yi mata “baki da baki ne?”

Da ya ga bata da niyyar amsawa saboda rashin sani da kuma kokarin rufa mata asiri sai ya mayar da akalar tambayar ga Dije.

Hannuwa ta yarfe “ina dakina ina zan sani, dama tunda yaron nan mai kudi ya fara zuwa daga birni naga take takenta so take tafi karfin kowa”

“Babu mai fin karfina a gidan nan, idan ta dawo a turo min ita inji da izinin wa ta fita”

Zai shiga dakinsa Mairama tayi saurin dauko masa kilishin “Malamijo gashi yace na baka”

Ledar ya karba da sauri yana lekawa. Ganin kilishi yayi gari guda ya soma dariya “soja yazo kenan Mairama”

Kanta ta kawar gefe tana murmushi ya bantaro mai dan girma kamar tafin hannunsa ya mika mata

“gashi kema ki taba, ko ya baki?”

Sai da ta karba din tace masa nasa ne kawai. Dije tuni yawu ya tsinke tayi kasake tana jiran ya bata amma sai ta ga bashi da niyya.

“Bani nawa mana zan fara aikin tuwo ne”

Harararta yayi yana kanne ido “iyayen kwadayi ungo kafin a tara min taragutsan nan su fara min kallon nama”

Wani dan guntu ya bata ta jefa a baki a kan idon Hajjo. Fitowa tayi itama tana bata rai “ko a bani ko na gayyato jama’ar gidan nan”

Bashi da zabi haka ya dangwara mata a tafin hannunta. Jefashi tayi duka a baki sannan ta daga murya tace kowa ya fito Malamijo yana rabon kilishi.

Ai kan kace kwabo sun soma taruwa mutum kadan ne basa nan. Malamijo kamar ya hadiyi zuciya haka ya rinka yafita musu yana badawa ba da zuciya daya ba.

Ana tsaka da kiran magariba Salame ta shigo gidan. Can wurin Ta Madina da taje bacin rai kawai ta karo don sosai take fushi da ita har yanzu saboda abinda tayi mata a Kano. Sallama tayi a dakin Mairama ta amsata ciki-ciki. Tsaki ta doka ta ajiye gyalenta ta fita yin alwala. Bayan tayi sallah ne Mairama ta tambayeta ko ta ga mukullin sif din.

“Ajiya kika ban ko me?”

Zuciya ta soma cin Mairama saboda ta tabbatar dazu da gangan Salame ta fita duk da tasan kiranta take yi. Wai ma me ya kaita wurin Zayyan din.

“Shikenan”

“Shikenan me?”

Maimakon amsar fatar baki sai gani tayi Mairama tasa iyakar karfinta tana jijjiga kofofin sif din tana neman ballesu. Da saurinta ta mike don ta dakatar da ita.

“Meye hakan?”

“Dame yayi miki kama? Balleta zanyi tunda mukullin ya bata in nemi kayan sawa”

“Saboda saurayinki zai zo?”

Salame tace da kaushin murya.

“Adda Salame idan wani abu nayi miki ki fito fili ki fada min amma ba ki zauna kullum kina jin haushina kina min tsaki ba. Kin sani wallahi ba don ke Addata bace ….”

“Sai ki dakeni ko ba haka ba”

Wata fuzga ta kaiwa kofar sai gata ta bude ta dauko kayan da zata saka bata sake kula Salame ba. Gefe ita ma ta koma tana ta hucin kishi ganin yadda Mairama ta zage tana kwalliya saboda Zayyan.

“Aikin banza ki gama adon yace ya fasa tunda yanzu yasan daga wane irin gida ki ka fito.”

A tsorace ta waiwayo “fada masa kika yi?”

Salame sai ta tsame kafarta tayi waje. Tana zaune tana jira a raba tuwon gidan na al’ada a bata nata Mairama ta fito bayan an fada mata dawowar Zayyan. Da tazo wucewa tana jin uban tsakin da Salame taja har sai da Dije ta soma sababi ko da ita take.

Hira suka yi cikin nutsuwa rabi duk shi yake maganar saboda kunya irin ta Fulani. Tana son tambayarsa game da abubuwan da take zargin Salame ta fada masa amma ta gaza. Kamar ya sani kuwa da kansa ya shiga bata labarin asalinsa da rayuwarsa ta baya zuwa yanzu. Tausayinsa taji har idanunta su ka ciko da kwalla.

“Bana so yanayin rayuwar gidanku ya sanya ki fara tunanin zan gujeki ko hakan

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment